1 Corinthians

WASIƘAR BULUS TA FARKO ZUWA GA
KORINTIYAWA

1

Gaisuwa

1Daga Bulus, manzo kirayayye na Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Sastanisu, 2zuwa ga ikilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.

3Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Godiya saboda Bayebaye na Ruhu

4Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu, 5har ta kowace hanya aka wadata ku a cikinsa, a wajen yin magana duka da ilimi dukaū 6domin kuwa an tabbatar da shaida a kan Almasihu a cikinku. 7Har ma ku ba kāsassu ba ne a wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 8Wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijinmu.

Tsattsaguwa a Ikilisiya

10Na roƙe ku 'yan'uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra'ayinku ɗaya. 11Don kuwa, ya 'yan'uwana, mutanen gidan Kuluwi sun ba ni labari, cewa akwai jayayya a tsakaninku. 12Abin da nake nufi, shi ne kowannenku yana faɗar abu dabam, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afolos ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “Ni na Almasihu ne.” 13Ashe, Almasihu a rarrabe yake? Ko Bulus ne aka gicciye dominku? Ko kuwa an yi muku baftisma ne da sunan Bulus? 14Na gode Allah da ban yi wa waninku baftisma ba, banda Kirisbus da Gayus, 15kada wani ya ce da sunana ne aka yi muku baftisma. 16Ai, kuwa lalle na yi wa jama'ar gidan Istifanas ma. Amma banda waɗannan ban san ko na yi wa wani baftisma ba.

17Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.

Almasihu Ikon Allah Ne, da Hikimarsa

18Maganar gicciye, maganar wauta ce ga waɗanda suke hallaka, amma ƙarfin Allah ce a gare mu, mu da ake ceto. 19Domin a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”

20To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba? 21Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara. 22Yahudawa kam, mu'ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suka nema su samu, 23mu kuwa muna wa'azin Almasihu gicciyeyye, abin sa yin tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga al'ummai, 24amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al'ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah. 25Domin abin da aka zata wauta ce ta Allah, ya fi hikimar ɗan adam, abin da kuma aka zata rauni ne na Allah, ya fi duk ƙarfin ɗan adam.

26Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku 'yan'uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa. 27Amma Allah ya zaɓi abin da yake wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da ke rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa. 28Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin ya shafe abubuwan da suke akwai. 29Wannan kuwa duk don kada wani ɗan adam ya yi fariya a gaban Allah ne. 30Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa. 31Saboda haka, “Duk mai yin alfarma, yă yi da Ubangiji” (abin da yake a rubuce ke nan).

2

Shelar Almasihu Gicciyeyye

1Sa'ad da na zo wurinku, 'yan'uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta wurin iya magana ko gwada hikima ba. 2Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye. 3Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai. 4Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu, 5kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.

Bayani daga Ruhun Allah

6Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba. 7Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu. 8A cikin masu mulkin zamanin nan, ba wanda ya gane hikimar nan, don da sun gane ta, da ba su gicciye Ubangiji Maɗaukaki ba. 9Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa, “Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, Kunne bai taɓa ji ba, Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”

10mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah. 11Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake. 13Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al'amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.

14Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su. 15Mutumin da yake na ruhu kuwa yakan rarrabe da kome, shi kansa kuma ba mai jarraba shi. 16“Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.

3

Abokan Aiki na Allah

1Amma ni, 'yan'uwa, ban iya yi muku jawabi ba, kamar yadda nake yi wa mutanen da suke na ruhu, sai dai kamar yadda nake yi wa masu halin matuntaka, kamar jarirai a cikin bin Almasihu. 2Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba, 3don har a yanzu ku masu halin mutuntaka ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu halin mutuntaka ba ne, kuna kuma aikata halin mutuntaka? 4Don in wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afolos ne,” ashe, ba aikata halin mutuntaka kuke yi ba>

5To, wane ne Afolos? Wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi? 6Ni na yi shuka, Afolos ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar. 7Don haka da mai shukar, da mai banruwan, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, shi da ya girmar. 8Da mai shukar, da mai banruwan, duk daidai suke, sai dai ko wanne zai sami tasa ladar gwargwadon wahalarsa, 9gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai. 11Harsashin kam, ba wanda yake iya sa wani dabam da wanda aka riga aka sa, wato, Yesu Almasihu. 12To, kowa ya yi ɗori da zinariya a kan harsashin nan, ko da azurfa, ko da duwatsun alfarma, ko da itace, ko da shuci, ko da kara, 13ai, aikin kowane mutum zai bayyana, domin ranar nan za ta tona shi, gama za a bayyana ta da wuta, wutar kuwa za ta gwada aikin kowa a san irinsa. 14In aikin da kowane mutum ya ɗora a kan harsashin nan ya tsira, to, zai sami sakamako. 15In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai ya yi hasara, ko da yake shi da kansa zai tsira, amma kamar ya bi ta wuta ne.

16Ashe, ba ku sani ku Haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a zuciyarku? 17In wani ya ɓāta Haikalin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama Haikalin Allah tsattsarka ne, ku kanku Haikalinsa ne.

18Kada kowa ya ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai ya mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima. 19Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah, domin a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima da makircinsu.” 20Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.” 21Saboda haka kada kowa ya yi fariya da 'yan adam. Don kuwa kome naku ne, 22ko Bulus, ko Afolos, ko Kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan yanzu, ko da na gaba, ai, duk naku ne. 23Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.

4

Aikin Manzanni

1Ta haka ya kamata a san mu da zama ma'aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al'amuran Allah. 2Har wa yau dai, abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce. 3A gare ni kam, sassauƙan abu ne a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a gaban kowace mahukunta ta mutane. Ni ma ba na gwada kaina. 4Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni. 5Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.

6To, 'yan'uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afolos saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa, kada ku zarce abin da yake a rubuce, kada kuma waninku ya yi fahariya da wani a kan wani. 7Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba>

8Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku! 9Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa ke jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane. 10An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance! 11Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida. 12Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure. 13In an ci mutuncinmu, mukan ba da haƙuri. Mun zama, har a yanzu ma, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

14Ba don in kunyata ku na rubuta wannan ba, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa, ku 'ya'yana ne, ƙaunatattu. 15Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara. 16Don haka, ina roƙon ku, ku yi koyi da ni. 17Saboda haka, na aika muku da Timoti, wanda yake shi ne ɗana ƙaunatacce, amintacce kuma a cikin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka'idodina na bin Almasihu, kamar yadda nake koyarwa a ko'ina, a kowace ikilisiya. 18Waɗansu har suna ɗaga kai, kamar ba zan zo wurinku ba. 19Amma kuwa zan zo gare ku ba da daɗewa ba, in Ubangiji ya yarda, zan kuma bincika, in ga ƙarfin mutane masu ɗaga kan nan, ba maganganunsu ba. 20Domin Mulkin Allah ba ga maganar baka yake ba, sai dai ga ƙarfi. 21To, me kuka zaɓa, in zo muku da sanda, ko kuwa da fuskar ƙauna da lumana>

5

Hukunci a kan Fasikanci

1Ana ta cewa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ba a yi ko a cikin al'ummai, har wani yana zama da matar ubansa. 2A! Har kuwa alfarma kuke yi! Ashe, ba gwamma ku yi baƙin ciki ba, har a fitar da wanda ya yi wannan mugun aiki daga cikin jama'arku>

3Ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan, kamar ma ina nan ne, har ma na riga na yanke wa mutumin da ya yi abin nan hukunci da sunan Ubangijinmu Yesu. 4Sa'ad da kuka hallara, ruhuna kuma yana nan, da kuma ikon Ubangijinmu Yesu, 5sai ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don ya hallaka jikinsa, ruhunsa kuma ya tsira a ranar Ubangiji Yesu.

6Fāriyarku ba da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa? 7Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu. 8Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.

9Na rubuta muku a cikin wasiƙata, cewa kada ku yi cuɗanya da fasikai. 10Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita, da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai ya zama dole ku fita daga duniya. 11Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasiki, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan. 12Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda suke a cikin Ikilisiya za ku hukunta ba? 13Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.

6

Kada a Kai Ƙara gaban Marasa Bi

1In waninku yana da wata ƙara a game da ɗan'uwansa, ashe, zai yi ƙurun kai maganar a gaban marasa adalci, ba a gaban tsarkaka ba? 2Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari'a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari'a, ashe, ba za ku iya shari'ar ƙananan al'amura ba? 3Ba ku sani ba, za mu yi wa mala'iku shari'a, balle al'amuran da suka shafi zaman duniyar nan? 4In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikilisiya? 5Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe, wato, ba ko mutum ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin 'yan'uwa? 6Amma ɗan'uwa yakan kai ƙarar ɗan'uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma>

7Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku? 8Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma 'yan'uwanku kuke yi wa!

9Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo, 10ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah. 11Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.

Ku Ɗaukaka Allah da Jikinku

12“Dukan abubuwa halal ne a gare ni,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Abu duka halal na a gare ni,” amma ba zan zama bawan kome ba. 13“Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci”ūAllah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da wancan. Jiki kam, ba don fasikanci yake ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki. 14Allah ya ta da Ubangiji daga matattu, haka mu ma zai ta da mu da ikonsa.

15Ashe, ba ku sani ba jikinku gaɓoɓin Almasihu ne? Ashe kuma, sai in ɗauki gaɓoɓin Almasihu in mai da su gaɓoɓin karuwa? Faufau! 16Ashe, ba ku sani ba, duk wanda ya tara da karuwa, sun zama jiki ɗaya ke nan? Domin a rubuce yake cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.” 17Duk wanda kuwa yake haɗe da Ubangiji, sun zama ɗaya a ruhu ke nan. 18Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne. 20Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.

7

Damuwar da take a cikin Aure

1To, a yanzu, a game da abin da kuka rubuto, yana da kyau mutum ya zauna ba aure. 2Amma don gudun fasikanci sai kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3Miji yă ba matarsa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta. 4Matar kuwa ba ta da iko da jikinta, sai dai mijin, haka kuma mijin ba shi da iko da jikinsa, sai dai matar. 5Kada ɗayanku ya ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu'a, sa'an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan ya zuga ku ta wajen rashin kamewa. 6Na fadi wannan ne bisa ga shawara, ba bisa ga umarni ba. 7Da ma a ce kowa kamar ni yake mana! Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.

8Abin da na gani ga waɗanda ba su yi aure ba, da kuma mata gwauraye, ya kyautu a gare su su zauna ba aure kamar yadda nake. 9In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai, gwamma dai a yi aure da sha'awa ta ci rai.

10Masu aure kuwa ina yi musu umarni, ba kuwa ni ba, Ubangiji ne, cewa kada mace ta rabu da mijinta 11(in kuwa ta rabu da shi, sai ta zauna haka ba aure, ko kuwa ta sāke shiryawa da mijinta), miji kuma kada ya saki matarsa.

12Ga sauran, ni nake faɗa, ba Ubangiji ba, in wani ɗan'uwa yana da mace marar ba da gaskiya, ta kuma yarda su zauna tare, to, kada ya rabu da ita. 13Mace kuma mai miji marar ba da gaskiya, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi. 14Don miji marar ba da gaskiya, a tsarkake yake a wajen matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma, a tsarkake take a wajen mijinta. In ba haka ba, zai zamana 'ya'yanku ba masu tsarki ba ne, amma ga hakika masu tsarki ne. 15In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya. 16Ke mace, ina kika sani ko za ki ceci mijinki? Kai miji, ina ka sani ko za ka ceci matarka>

Zaman da Ubangiji ya Nufa

17Sai dai kowa ya yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi. 18Duk wanda Allah ya kira, wanda dā ma yake da kaciya, to, kada ya nemi zama marar kaciya. Wanda kuwa ya kira yana marar kaciya, to, kada ya nema a yi masa kaciya. 19Don kaciya da rashin kaciya ba sa hassala kome, sai dai kiyaye umarnin Allah. 20Kowa yă zauna a maƙamin da Allah ya kiraye shi. 21In ya kira ka kana bawa, kada ka damu. In kuwa kana iya samun 'yanci, ai, sai ka samu. 22Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai, 'yantacce ne na Ubangiji ne. Kuma, wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu. 23Da tamani aka saye ku. Kada fa ku zama bayin mutane. 24To, 'yan'uwa, duk halin da aka kira mutum a ciki, sai ya zauna a kai, yana zama tare da Allah.

Marasa Aure da Mata Gwauraye

25A game da matan da ba su yi aure ba kuwa, ba ni da wani umarnin Ubangiji, amma ina ba da ra'ayina ne a kan ni amintacce ne, bisa ga jinƙan Ubangiji. 26Na dai ga ya yi kyau mutum ya zauna yadda yake, saboda ƙuncin nan da yake gabatowa. 27In da igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi tsinkewa. In kuwa ba igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi aure. 28Amma kuwa in ka yi aure, ba ka yi zunubi ba, ko budurwa ma ta yi aure, ba ta yi zunubi ba. Duk da haka dai, duk masu yin aure za su ji jiki, niyyata kuwa in sawwaƙe muku. 29Abin da nake nufi 'yan'uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ƙure. A nan gaba masu mata su zauna kamar ba su da su, 30masu kuka kamar ba kuka suke yi ba, masu farin ciki ma kamar ba farin ciki suke yi ba, masu saye kuma kamar ba su riƙe da kome, 31masu moron duniya kuma, kada su ba da ƙarfi ga moronta. Don yayin duniyar nan mai shuɗewa ne.

32Ina so ku 'yantu daga damuwa. Mutum marar aure yakan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda zai faranta wa Ubangiji rai. 33Mutum mai aure kuwa, yakan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda zai faranta wa matarsa rai. 34Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, takan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka a jiki, da kuma a rai. Mace mai aure kuwa takan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta rai. 35Na faɗi haka ne, don in taimake ku, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36Ga zancen 'ya budurwa, wadda ta zarce lokacin aure, idan mahaifinta ya ga bai kyauta mata ba, in kuwa hali ya yi, sai ya yi abin da ya nufa, wato, a yi mata aure, bai yi zunubi ba. 37In kuwa ya zamana ba lalle ne ya yi wa 'yar tasa budurwa aure ba, amma ya tsai da shawara bisa ga yadda ya nufa, ya kuma ƙudura sosai a ransa, a kan tsare ta, to, haka daidai ne. 38Wato, wanda ya yi wa 'yar tasa budurwa aure, ya yi daidai, amma wanda bai aurar da ita ba, ya fi shi.

39Igiyar aure tana wuyan mace, muddin mijinta yana da rai. In kuwa mijinta ya mutu, to, tana da dama ta auri wanda take so, amma fa, sai mai bin Ubangiji. 40Amma a nawa ra'ayi, za ta fi farin ciki, in ta zauna a yadda take. A ganina kuwa ina da Ruhun Allah.

8

Abincin da aka Miƙa wa Gumaka

1To, yanzu a game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun sani dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi. 2Duk mai gani ya san wani abu, ai, har a yanzu, bai san yadda ya kamata ya sani ba. 3In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.

4A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya. 5Ko da yake, akwai waɗanda ake kira alloli a sama ko a ƙasa, don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa, 6duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.

7Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al'amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu. 8Abinci ba zai ƙare mu a game da Allah ba. In mun ci, ba mu ƙaru ba, in kuma ba mu ci ba, ba mu ragu ba. 9Sai dai ku lura, kada 'yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba. 10Amma in wani mutum, wanda yake da rarraunan lamiri, ya gan ka, kai da kake da sani, kana ci a ɗakin gunki, ashe, wannan ba zai ƙarfafa lamirinsa har ya ci abincin da aka miƙa wa gunki ba? 11Wato, ta sanin nan naka, sai a rushe rarraunan nan, ɗan'uwa ne kuwa wanda Almasihu ya mutu dominsa! 12Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa 'yan'uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu. 13Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don haka in sa ɗan'uwana tuntuɓe.

9

Hakkokin Manzo

1Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijinmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin Ubangiji? 2Ai, ko waɗansu ba su ɗauke ni a kan manzo ba, lalle ku kam, ni manzo ne a gare ku, domin kuwa ku ne tabbatar manzancina a gaban Ubangiji.

3Wannan ita ce kariyata ga masu son tuhumata. 4Ashe, ba mu da iko a ba mu ci da sha? 5Ba mu da ikon tafiya da matarmu ta aure mai bi, kamar yadda sauran manzanni, da 'yan'uwan Ubangiji, da kuma Kefas suke yi? 6Ko kuwa dai ni da Barnaba ne kawai, ba mu da iko a ɗauke mana aikin ci da kai? 7Wa yake yin aikin soja, sa'an nan ya ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, ya kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, ya kasa shan nonon>

8Wato, ina faɗar haka bisa ga ra'ayin mutum kawai ne? Ba haka ma Attaura ta faɗa ba? 9Ai, haka yake a rubuce a Shari'ar Musa cewa, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi a sa'ad da yake sussuka.” Da shanu ne kawai Allah yake kula? 10Ba saboda mu musamman yake magana ba? Hakika saboda mu ne aka rubuta. Ai, ya kamata mai noma ya yi noma da sa zuciya, mai sussuka kuma ya yi sussuka da sa zuciya ga samun rabo daga amfanin gonar. 11Da yake mun shuka iri na ruhu a zuciyarku, to, wani ƙasaitaccen abu ne, in mun mori amfaninku irin na duniya? 12Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba? Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta ko ƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa. 13Ashe, ba ku sani ba, masu hidima a Haikali daga nan suke samun abincinsu? Masu hidimar bagadi kuma, a nan suke samun rabo daga hadayar da aka yanka? 14Haka nan kuma Ubangiji ya yi umarni, cewa, ya kamata masu sanar da bishara, a cishe su albarkacin bishara.

15Amma ni kam, ban mori ko ɗaya daga cikin halaliyan nan ba, ba kuma ina rubuta wannan ne, don a yi mini haka ba. Ai, gara in mutu a kan wani ya banzanta mini fahariyata. 16Don ko da yake ina yin bishara, ba na fahariya da haka, gama tilas ne a gare ni. Kaitona in ba na yin bishara! 17Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba ni da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan. 18Ina kuma hakkina? To, ga shi. A duk lokacin da nake yin bishara, sona in yi ta a kyauta, kada in ƙurashe halaliyata a game da bishara.

19Ko da yake ni ba bawan kowa ba ne, na mai da kaina bawan kowa, domin in rinjayi mutane masu yawa. 20Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari'a take iko da su, sai na zama kamar wanda Shari'a take iko da shi, ko da yake ba Shari'a take iko da ni ba, domin in rinjayi waɗanda Shari'a take iko da su ne. 21Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne. 22Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu. 23Na yi wannan ne duk saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

24Ashe, ba ku sani ba, a wajen tsere dukan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai yake samun kyautar ci? To, sai ku yi ta gudu haka nan, don ku ci. 25Duk masu wasan gasa, sukan hori kansu ta kowane hali. Su kam, suna yin haka ne, don su sami lada mai lalacewa, mu kuwa marar lalacewa. 26To, ni ba gudu nake yi ba wurin zuwa ba, dambena kuwa ba naushin iska nake yi ba. 27Amma ina azabta jikina ne, don in bautar da shi, kada bayan da na yi wa waɗansu wa'azi, ni da kaina a yar da ni.

10

Kashedi kan Bautar Gumaka

1To, ina so ku sani, 'yan'uwa, dukan kakanninmu an kara su ne a ƙarƙashin gajimare, dukansu kuma sun ratsa ta cikin bahar. 2Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin. 3Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu, 4duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne. 5Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.

6To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, “Jama'a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa.” 8Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak. 9Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su. 10Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su. 11To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12Don haka duk wanda yake tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi. 13Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.

14Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka. 15Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da make faɗa. 16Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba? 17Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci. 18Ku dubi ɗabi'ar Isra'ila. Ashe, waɗanda suke ci daga hadayu, ba tarayya suke yi da bagadin hadaya ba? 19Me nake nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkun ne ainihin wani abu? 20A'a! Na nuna ne kawai cewa abin da al'ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu. 21Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu. 22Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne>

Yi Kome saboda Ɗaukakar Allah

23“Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba. 24Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan'uwansa. 25Ku ci kowane irin abu da ake sayarwa a mahauta, ba tare da tambaya ba saboda lamiri. 26Don an rubuta, “Duniya ta Ubangiji ce, da duk abin da ke cikinta.” 27In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya ba saboda lamiri. 28In kuwa wani ya ce muku, “An yanka wannan saboda gunki ne fa,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan mai gaya muku, da kuma saboda lamiri, 29nasa lamiri fa na ce, ba naka ba. Don me fa lamirin wani zai soki 'yancina? 30In na yi godiya ga Allah a kan abincina, saboda me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah>

31To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah. 32Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikilisiyar Allah, 33kamar dai yadda nake ƙoƙarin kyautata wa dukan mutane a cikin duk abin da nake yi, ba nema wa kaina amfani nake yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.

11

1Ku yi koyi da ni kamar yadda nake koyi da Almasihu.

Mata su Rufe Kansu

2Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni a cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka'idodin nan da kyau, daidai yadda na ba ku. 3Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne. 4Duk mutumin da ya yi addu'a ko ya yi annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa ke nan. 5Amma duk matar da ta yi addu'a, ko ta yi annabci da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma. 6In mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta sausaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace sausaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta. 7Namiji kam, bai kamata ya rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce. 8(Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take. 9Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.) 10Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato, alamar ikon namiji, saboda mala'iku. 11Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba. 12Wato kamar yadda mace take daga namiji, haka namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke. 13Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu'a ga Allah da kanta a buɗe? 14Ashe, ko ɗabi'a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba? 15In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ce ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin. 16In kuwa wani yana da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al'ada ba, ikilisiyoyin Allah kuma haka.

Ƙasƙantar da Cin Jibin Ubangiji

17A game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce. 18To, da farko dai sa'ad da kuka taru, taron ikilisiya, na ji har akwai rarrabuwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku. 20Ashe kuwa, in kun taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba! 21Domin a wajen cin abinci, kowa yakan dukufa a kan akushinsa, ga wani yana jin yunwa, ga wani kuwa ya sha ya bugu. 22A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A'a, ba zan yaba muku ba.

Cin Jibin Ubangiji

(Mat 26.26-29; Mar 14.22-25; Luka 22.14-20)

23Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa, 24bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura, ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka tunawa da ni.” 25Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa'ad da kuke sha, domin tunawa da ni.” 26Wato, duk sa'ad da kuke cin gurasar nan, kuke kuma sha a ƙoƙon nan, kuma ayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.

Cin Jibin Ubangiji da Rashin Cancanta

27Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a ƙoƙon nan na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa ke nan. 28Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon. 29Kowa ya ci, ya kuma sha, ba tare da faɗaka da jikin Ubangiji ba, ya jawo wa kansa hukunci ke nan, ta wurin ci da sha da ya yi. 30Shi ya sa da yawa daga cikinku suke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci. 31Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za a hukunta mu ba. 32In kuwa Ubangiji ne yake hukunta mu, to, muna horuwa ke nan, don kada a yanke mana hukunci tare da sauran duniya.

33Saboda haka, ya 'yan'uwana, in kuka taru don cin abinci, sai ku jiraci juna. 34In kuwa wani yana jin yunwa, sai ya ci a gida, kada ya zamana taronku ya jawo muku hukunci. Batun sauran abubuwa kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.

12

Bayebaye na Ruhu

1A yanzu kuma 'yan'uwa, a game da baye-baye na ruhu, ba na so ku rasa sani. 2Kun sani fa a sa'ad da kuke bin al'ummai, an juyar da ku ga bin gumakan nan marasa baki yadda aka ga dama. 3Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa'an nan ya ce, “Yesu la'ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

4To, akwai baiwa iri iri, amma Ruhu ɗaya ne. 5Akwai fanni iri iri na ibada, amma Ubangiji ɗaya ne. 6Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu. 7An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka. 8Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu. 9Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta wurin Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta wurin Ruhun nan, 10wani kuma yin mu'ujizai, wani kuma annabci, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri iri, wani kuma fassara harsuna. 11Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.

Dukkanmu Gaɓoɓin Jiki guda Ne

12Wato kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu. 13Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.

14Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa. 15Da ƙafa za ta ce, “Da yake ni ba hannu ba ce, ai, ni ba gaɓar jiki ba ce,” faɗar haka ba za ta raba ta da zama gaɓar jikin ba. 16Da kuma kunne zai ce, “Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gaɓar jiki ba ne,” faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba. 17Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da dukan jiki kunne ne, da me za a sansana? 18Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa. 19Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya. 21Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai ya ce wa ƙafafu, “Ba ruwana da ku.” 22Ba haka yake ba, sai ma gaɓoɓin da ake gani kamar raunana, su ne wajibi, 23gaɓoɓin jiki kuma da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mukan fi ba su martaba. Ta haka gaɓoɓinmu marasa kyan gani, akan ƙara kyautata ganinsu. 24Gaɓoɓinmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu kome ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙasƙantacciyar gaɓa, 25kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya. 26Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.

27To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28A cikin ikilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri. 29Shin, duka manzanni ne? Ko duka annabawa ne? Ko duk masu koyarwa ne? Su duka masu yin mu'ujizai ne? 30Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne ke magana da waɗansu harsuna? Ko kuwa duka ne suke fassara? 31Sai dai ku himmantu ga neman mafafitan baye-baye. Har ma zan nuna muku wata hanya mafificiya nesa.

13

Ƙauna

1Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala'iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama ƙararrawa mai yawan ƙara ke nan, ko kuwa kuge mai amo. 2Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne. 3Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba.

4Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. 5Ƙauna ba ta sa ɗaga kai ko rashin kārā, ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo. 6Ƙauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. 7Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.

8Ƙauna ba ta ƙarewa har abada. Annabci zai shuɗe, harsuna za su ɓace, ilimi kuma zai bushe. 9Ai, hakika iliminmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. 10Sa'ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan ya shuɗe. 11Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya. 12Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai. 13To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

14

Harsuna da Annabci

1Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman bayebaye na ruhu, tun ba ma na yin annabci ba. 2Duk wanda yake magana da wani harshe, ba da mutane yake magana ba, da Allah yake yi, ba kuwa wanda yake fahimtarsa, domin asirtattun a al'amura yake ambato ta wurin Ruhu. 3Wanda kuwa yake yin annabci, mutane yake yi wa magana domin ya inganta su, ya ƙarfafa su, ya ta'azantar da su. 4Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ingantawa. 5To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikilisiya.

6To, 'yan'uwa, in na zo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba? 7In abubuwan nan marasa rai, kamar su sarewa da molo, muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8In ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9Haka ma yake a gare ku. In kun yi magana da wani harshe, wanda ba a fahimta ba, yaya wani zai san abin da ake faɗa? Kun yi magana a banza ke nan! 10Hakika akwai harsuna iri iri a duniya, ba kuwa wanda ba shi da ma'ana. 11In kuwa ba na jin harshen, sai in zama bare ga mai maganar, mai maganar kuma ya zama bare a gare ni. 12Haka ma yake a gare ku. Tun da ya ke kun ɗokanta da samun bayebaye na Ruhu, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikilisiya.

13Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai ya yi addu'a a yi masa baiwar fassara. 14In na yi addu'a da wani harshe, ruhuna ne yake addu'a, amma tunanina bai amfana kowa ba. 15To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu'a da ruhuna, zan kuma yi a game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan yi a game da tunanina. 16In ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda ke jahili zai ce, “Amin,” a kan godiyar da kake yi, in bai san abin da kake faɗa ba? 17Ko da yake ka gode wa Allah sosai, ai, ɗan'uwanka bai ƙaru da kome ba. 18Na gode Allah ina magana da waɗansu harsuna fiye da ku duka. 19Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.

20Ya ku 'yan'uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako. 21A rubuce yake a cikin littattafai masu tsarki cewa, “Zan yi magana da jama'an nan ta wurin mutane masu baƙin harsuna, da kuma ta harshen baƙi, duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba, in ji Ubangiji.” 22Wato, ashe, harsuna a kan alamu suke, ba ga masu ba da gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa domin masu ba da gaskiya ne, ba don marasa ba da gaskiya ba. 23Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da wani harshe dabam, waɗansu jahilai kuma ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun ruɗe ba? 24In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa, 25asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.

A Yi Kome yadda ya Dace, a Shirye

26To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa. 27In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma ya yi fassara. 28In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu ya yi shiru a cikin taron Ikilisiya, ya yi wa Allah magana a zuci. 29Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar. 30In kuwa an yi wa wani wanda yake zaune wani bayani, sai na farkon nan mai magana ya yi shiru. 31Dukanku kuna iya yin annabci da ɗaya ɗaya, har kowa ya koya, ya kuma sami ƙarfafawa. 32Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci, 33domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka. 34Sai mata su yi shiru a cikin taron ikilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce. 35In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikilisiya. 36A kanku ne maganar Allah ta fara, ko kuwa a gare ku kaɗai ta isa>

37In wani yana zato shi annabi ne, ko kuwa mai wata baiwa ta ruhu, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuto muku umarni ne na Ubangiji. 38In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. 39Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da waɗansu harsuna. 40Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, ya zauna a natse kuma.

15

Tashin Almasihu daga Matattu

1A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi, 2wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba.

3Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa, 4cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa, 5ya kuma bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun. 6Sa'an nan ya bayyana ga 'yan'uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har zuwa yanzu, amma waɗansu sun yi barci. 7Sa'an nan ya bayyana ga Yakubu, sa'an nan ga dukan manzanni. 8Daga ƙarshen duka ya bayyana a gare ni, ni ma da nake kasasshe, marar cancanta. 9Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikilisiyar Allah. 10Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata. 11To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka muke wa'azi, ta haka kuma kuka gaskata.

Tashin Matattu

12To, da yake ana wa'azin Almasihu a kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku suke cewa, babu tashin matattu? 13In dai babu tashin matattu, ashe, ba a ta da Almasihu ba ke nan. 14In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa'azinmu a banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce. 15Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu. 16Don kuwa in ba a ta da matattu, ashe, Almasihu ma ba a ta da shi ba ke nan. 17In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe, bangaskiyarku banza ce, har yanzu kuma kuna tare da zunubanku. 18Ashe, waɗanda suka yi barci a kan su na Almasihu, sun hallaka ke nan. 19Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaɗai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi.

20Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci. 21Tun da yake mutuwa ta warin mutum ta faru, haka kuma tashin matattu ta wurin Mutum yake. 22Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da su saboda Almasihu. 23Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa'an nan a ranar komowarsa, waɗanda suke na Almasihu. 24Sa'an nan sai ƙarshen, sa'ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko. 25Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa. 26Magabciyar ƙarshe da za a shafe, ita ce mutuwa. 27“Gama Allah ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An sarayar da kome karƙashin ikonsa” a fili yake shi wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, a keɓe yake. 28Sa'ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa'an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.

29In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su? 30Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci? 31Na hakikance 'yan'uwa, saboda taƙama da ku da nake yi a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu, a kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa! 32Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?” 33Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.” 34Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.

Tashin Jiki

35Watakila wani zai yi tambaya, “Ta yaya ake ta da matattu? Da wace irin kama kuma suke fitowa?” 36Kai, marar azanci! Abin da ka shuka, ai, ba zai tsiro ba sai ya mutu. 37Abin da ka shuka kuma, ba shi ne ainihin abin da zai kasance ba, ƙawai, ko ta alkama ce, ko kuma, wata iri dabam. 38Amma Allah yakan ba ta kama, yadda ya nufa, kowace ƙwaya da irin tata kama. 39Don ba dukan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi ma da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu. 40Akwai halitta irin ta Sama, akwai kuma irin ta ƙasa. Amma ɗaukakar irin ta Sama dabam, ɗaukakar irin ta ƙasa kuma dabam. 41Ɗaukakar rana dabam, ta wata dabam, ta taurari kuma dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen ɗaukaka.

42Haka kuma yake ga tashin matattu. Akan shuka su da halin ruɓa, akan kuma ta da su da halin rashin ruɓa. 43Akan shuka da wulakanci, akan tasa da ɗaukaka, akan shuka da rashin ƙarfi, akan tasa da ƙarfi. 44Akan shuka da jikin mutuntaka, akan tasa da jiki na ruhu. Da yake akwai jiki na mutuntaka, lalle kuma akwai jiki na ruhu. 45Haka kuma yake a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki,” Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne mai rayarwa. 46Amma ba shi na Ruhun nan ne ya fara bayyana ba, na mutuntaka ne, daga baya kuma sai na Ruhu. 47Mutumin farko daga ƙasa yake, na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama yake. 48Kamar yadda shi na turɓayar nan yake, haka kuma waɗanda suke na turɓaya suke. Kamar yadda shi na Saman nan yake, haka kuma waɗanda suke na Sama suke. 49Kamar yadda muka ɗauki siffar na turɓayar nan, haka kuma za mu ɗauki siffar na Saman nan. 50Ina dai gaya muku wannan 'yan'uwa, ba shi yiwuwa jiki mai tsoka da jini ya sami gādo a Mulkin Allah, haka kuma mai ruɓa ba ya gādon marar ruɓa.

51Ga shi, zan sanar da ku wani asiri! Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, amma dukanmu za a sauya kamanninmu, 52farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu. 53Domin lalle ne, marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan. 54Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa, “An shafe mutuwa da aka ci nasararta da ita.”

55“Ke mutuwa, ina nasararki? Ke mutuwa, ina ƙarinki?”

56Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, Shari'a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi. 57Godiya tā tabbata ga Allah wanda take ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

58Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

16

Gudunmawa ga Tsarkaka

1To, a yanzu kuma ga zancen ba da gudunmawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikilisiyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi. 2A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa. 3Sa'ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima. 4In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.

Shirye-shiryen Tafiya

5Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi. 6Watakila zan jima a wurinku, ko ma in ci damina, don ku yi mini rakiya duk da za ni. 7Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a'a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda. 8Amma zan dakata a Afisa har ranar Fentikos. 9Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.

10In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11Kada fa kowa ya raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo a gare ni, domin ina duban hanyarsa tare da 'yan'uwa.

12Ga zancen ɗan'uwanmu Afolos kuwa, na roƙe shi ƙwarai, don ya zo wurinku, tare da saurar 'yan'uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa a yanzu ba. Zai zo dai sa'ad da ya ga ya dace.

Gargaɗi da Gaisuwa

13Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi. 14Duk abin da za ku yi, ku yi shi da ƙauna.

15To, 'yan'uwa, kun sani fa jama'ar gidan Istifanas su ne nunan fari a ƙasar Akaya, sun kuwa ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. 16Ina roƙonku ku yi wa irin waɗannan mutane biyayya, har ma ga duk waɗanda suke abokan aikinmu da wahalarmu. 17Na yi farin ciki da zuwan Istifanas, da Fartunatas, da Akaikas, domin sun ɗebe mini kewarku. 18Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.

19Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da ke taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji. 20Dukan 'yan'uwa suna gaishe ku. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.

21Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. 22Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la'ananne. Ubangijinmu fa suna zuwa! 23Alherin Ubangijinmu Yesu yă tabbata a gare ku. 24Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙauna, albarkar Almasihu Yesu.