1 John
1Shi da yake tun fil'azal yake nan, wanda muka ji, muka gani da idonmu, muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, a game da Kalmar Rai, 2wannan Rai kuwa an bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun dā yake tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu, 3to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu. 4Muna kuma rubuto muku wannan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke.
5Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, muke sanar da ku cewa Allah haske ne, ba kuwa duhu gare shi ko kaɗan. 6In mun ce muna tarayya da shi, alhali kuwa muna zaune a duhu, mun yi ƙarya ke nan, ba ma aikata gaskiya. 7In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi. 8In mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta tare da mu. 9In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci, 10In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan. Maganarsa kuma ba ta tare da mu.
1Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci. 2Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka. 3Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarninsa. 4Kowa ya ce ya san shi, ba ya kuwa bin umarninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi. 5Amma duk wanda yake kiyaye maganarsa, wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa. 6Kowa ya ce yana zaune a cikinsa, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.
7Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a'a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai, shi ne maganar da kuka ji. 8Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa. 9Kowa ya ce yana a cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan'uwansa, ashe, a duhu yake har yanzu. 10Mai ƙaunar ɗan'uwansa, a haske yake zaune, ba kuma wani sanadin sa tuntuɓe a gare shi. 11Mai ƙin ɗan'uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.
12Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku ne domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa. 13Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne domin kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku 'yan yara, ina rubuto muku ne domin kun san Uba. 14Ya ku dattawa, na rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, na rubuto muku ne domin kuna da ƙarfi, Maganar Allah tana zauna a zuciyarku, kun kuma ci nasara a kan Mugun nan.
15Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa ke ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. 16Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha'awa irin ta halin mutuntaka, da sha'awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. 17Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.
18Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne. 19Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki. 20Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya. 21Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya. 22Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan. 23Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan. 24Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna cikin Ɗan, da kuma Uban. 25Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.
26Ina rubuto muku wannan ne a kan waɗanda suke ƙoƙarin ɓad da ku. 27Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa ke koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
28To a yanzu, ya ku 'ya'yana ƙanana, sai ku zauna cikinsa, domin sa'ad da ya bayyana, mu kasance da amincewa, kada kunya ta rufe mu a gabansa a ranar komowarsa. 29Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.
1Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne. 2Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. 3Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.
4Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne. 5Kun dai sani an bayyana shi domin yă ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi. 6Kowa da yake a zaune a cikinsa, ba ya aikata zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba. 7Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne. 8Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis. 9Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne. 10Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.
11Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna, 12kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne. 13Kada ku yi mamaki, 'yan'uwa, idan duniya take ƙinku. 14Mu kam, mun sani mun riga mun tsere wa mutuwa, mun kai ga rai saboda muna ƙaunar 'yan'uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman mutuwa yake yi. 15Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi. 16Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa. 17Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa? 18Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.
19Ta haka za mu tabbata mu na gaskiya ne, har kuma mu amince wa kanmu gaban Allah, 20duk sa'ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome. 21Ya ku ƙaunatattuna, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah amincewa. 22Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so. 23Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu. 24Duk mai bin umarnin Allah kuwa a dawwame yake cikinsa, Allah kuma a cikinsa. Ta haka muka tabbata ya dawwama a cikinmu, saboda Ruhun da ya ba mu.
1Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah. 3Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya. 4Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi. 5Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu. 6Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.
7Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah. 8Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna. 9Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa. 10Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu. 11Ya ku ƙaunatattuna, tun da ya ke Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna. 12Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa in muna ƙaunar juna sai Allah ya dawwama cikinmu, ƙaunar nan tasa kuma tă cika a cikinmu.
13Ta haka muka sani muna a zaune a cikinsa, shi kuma a cikinmu, saboda Ruhunsa da ya ba mu. 14Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko Ɗan ya zama Mai Ceton duniya. 15Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa. 17Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari'a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan. 18Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna, 19Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu. 20Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan'uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa da ya ke gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba. 21Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.
1Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa ke ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma. 2Ta haka muku sani muna ƙaunar 'ya'yan Allah, wato, in muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa. 3Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne. 4Domin duk wanda yake haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta sa muka yi nasara da duniya. 5Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne>
6Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini. 7Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya. 8Akwai shaidu uku, wato Ruhun, da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. 9Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba. 11Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. 12Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai.
13Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami. 14Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu. 15In kuwa muka san kome muka roƙa yana sauraronmu, mun tabbata mun sami abin da muka roƙa a gare shi ke nan. 16Kowa ya ga ɗan'uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu'a. Saboda mai addu'ar nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake na mutuwa. Ban ce a yi addu'a domin wannan ba. 17Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.
18Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.
19Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.
20Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami. 21Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku yi nesa da gumaka.