1 Kings
1Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi. 2Saboda haka fādawansa suka ce masa, “Ranka ya daɗe bari mu nemo maka budurwa, wadda za ta zauna tare da kai, ta riƙa yin maka hidima, ta kwanta a ƙirjinka don ka riƙa jin ɗumi.” 3Suka kuwa nemi kyakkyawar yarinya a dukan ƙasar Isra'ila. Sai suka sami Abishag a Shunem, suka kawo ta wurin sarki. 4Ko da yake yarinyar kyakkyawa ce ƙwarai, ta zama mai lura da sarki, ta kuwa yi masa hidima, amma sarki bai yi jima'i da ita ba.
5Adonija, dan da Haggit ta haifa wa Dawuda, ya ɗaukaka kansa cewa, “Zan zama sarki.” Ya kuwa shirya wa kansa karusai, da dakarai, da zagage hamsin a gabansa. 6Tsohonsa bai taɓa tsawata masa ba. Shi kuma mutum ne kyakkyawa, an haife shi bayan Absalom. 7Ya gama baki da Yowab ɗan Zeruya, da Abiyata, firist. Su kuwa suka yarda su goyi bayansa, su taimake shi. 8Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.
9Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza. 10Amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benaiya, ko masu tsaron lafiyar sarki, ko Sulemanu ɗan'uwansa ba.
11Natan kuwa ya ce wa Bat-sheba tsohuwar Sulemanu, “Ba ki ji cewa Adonija ɗan Haggit ya zama sarki ba? Sarki Dawuda kuma bai sani ba! 12Yanzu sai ki zo in ba ki shawara domin ki tsira da ranki da na ɗanki Sulemanu. 13Ki tafi wurin sarki Dawuda, ki ce masa, “‘Ran sarki ya daɗe, ashe, ba ka rantse mini ba cewa, Sulemanu ɗana zai yi mulki bayanka, shi ne kuma zai hau gadon sarautarka? Me ya sa Adonija ya zama sarki?” 14Sa'ad da kike magana da sarki, ni ma zan shigo in tabbatar da maganarki.”
15Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima. 16Bat-sheba ta rusuna, ta gai da sarki. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so?”
17Ta ce masa, “Ranka ya daɗe, ka riga ka rantse mini da sunan Ubangiji Allahnka, ka ce, “‘Sulemanu ɗanki zai yi mulki bayana, shi ne zai hau gadon sarautata.” 18To, ga shi Adonija ya zama sarki, ko da yake kai ba ka sani ba. 19Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba. 20Ranka ya daɗe, yanzu idanun dukan jama'ar Isra'ila suna kallonka don su ga wanda za ka nuna musu ya gāji gadon sarauta a bayanka. 21In ba haka ba, zai zama sa'ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”
22Tana cikin magana da sarki, sai annabi Natan ya zo. 23Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi. 24Sa'an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka? 25Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, “‘Ran sarki Adonija ya daɗe.” 26Amma ni da Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da ɗanka Sulemanu, bai gayyace mu ba. 27Ranka ya daɗe ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fādawanka, cewa ga wanda zai gāje ka ba?”
28Sai sarki Dawuda ya ce, “A kirawo mini Bat-sheba.” Ta kuwa zo gaban sarki. 29Sa'an nan ya ce mata, “Na yi miki alkawari da Ubangiji mai rai wanda ya fanshe ni daga dukan wahala, 30a yau ne kuma zan cika alkawarin da na yi miki da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, cewa Sulemanu, ɗanki, zai yi mulki a bayana, shi ne zai hau gadon sarautata ya gāje ni, haka kuwa zan yi yau.”
31Bat-sheba kuwa ta rusuna har ƙasa, domin girmamawa, ta ce, “Ran ubangijina sarki ya daɗe har abada!”
32Sarki Dawuda kuma ya ce, “Ku kirawo mini Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada.” Su kuwa suka zo gaban sarki, 33ya ce musu, “Ku tafi tare da fādawana, ku sa Sulemanu, ɗana, ya hau alfadarina, ku kai shi Gihon, 34a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, “‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.” 35Sa'an nan ku zo da shi ya hau gadon sarautata, gama shi ne zai zama sarki a maimakona, na sa shi ya zama mai mulkin Isra'ila da Yahuza.”
36Sai Benaiya ɗan Yehoyada ya ce wa sarki, “Za a yi haka, Ubangiji Allah na ubangijina, sarki, ya tabbatar da haka. 37Kamar yadda Ubangiji ya kasance tare da ubangijina, sarki, haka kuma ya kasance tare da Sulemanu, ya fifita gadon sarautarsa fiye da na ubangijina, sarki Dawuda!”
38Saboda haka sai Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki, suka tafi, suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki Dawuda. Suka kuma kai shi Gihon. 39A can ne Zadok, firist, ya ɗauki ƙahon mai wanda ya kawo daga alfarwa ta sujada, ya zuba wa Sulemanu. Sa'an nan suka busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka ce, “Ran sarki Sulemanu ya daɗe.” 40Mutane duka kuwa suka bi shi, suna bushe-bushe, suna murna da yawa, kamar ƙasa ta tsage saboda sowarsu.
41Adonija da dukan baƙin da suke tare da shi suka ji amon sowa bayan da suka gama cin abinci. Da Yowab ya ji busar ƙaho, sai ya ce, “Mene ne dalilin wannan hargitsi a birni?” 42Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”
43Jonatan kuwa ya ce wa Adonija, “A'a, gama ubangijinmu, sarki Dawuda, ya naɗa Sulemanu sarki. 44Sarki ya aiki Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki. Su kuwa suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki. 45Zadok firist, da annabi Natan kuma suka zuba masa mai a Gihon don ya zama sarki. Daga can suka tashi da murna don haka ake hayaniya a birnin. Wannan ita ce hayaniyar da kake ji. 46Sulemanu ne sarki yanzu. 47Banda wannan kuma, fādawa sun tafi su kai caffa ga sarki Dawuda, suna cewa, “‘Allahnka ya sa Sulemanu ya yi suna fiye da kai, ya kuma fūfita gadon sarautarsa fiye da naka.” Sai sarki ya sunkuyar da kansa a gadonsa. 48Sa'an nan ya ce, “‘Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila wanda ya sa ɗaya daga cikin zuriyata ya hau gadon sarautata yau, idona kuwa ya gani.”
49Sai baƙin Adonija duka suka tashi suna rawar jiki, kowa ya kama hanyarsa. 50Adonija kuwa ya ji tsoron Sulemanu, sai ya tashi, ya tafi, ya kama zankayen bagade. 51Aka faɗa wa Sulemanu cewa ga Adonija yana jin tsoron sarki Sulemanu, gama, ga shi, ya kama zankayen bagade, yana cewa, “Bari sarki Sulemanu ya rantse mini tukuna, cewa ba zai kashe ni ba.”
52Sulemanu kuwa ya ce, “Idan ya nuna kansa nagarin mutum ne, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba, amma idan aka iske shi da mugunta, to, lalle kashe shi za a yi.” 53Sarki Sulemanu kuwa ya aika aka kawo shi daga bagaden. Da ya zo, sai ya rusuna, ya gai da sarki Sulemanu. Sulemanu ya ce masa, “Tafi gidanka.”
1Sa'ad da lokacin rasuwar Dawuda ya gabato, sai ya yi wa ɗansa Sulemanu gargaɗi na ƙarshe, ya ce, 2“Ina gab da rasuwa yanzu. Saboda haka, ka ƙarfafa, ka yi jaruntaka. 3Ka yi abin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka. Ka yi biyayya da dokokinsa, da umarnansa, kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, domin ka yi nasara da dukan abin da kake yi da inda ka nufa duka, 4domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, “‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.”
5“Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra'ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da suke ƙafafunsa. 6Ka san abin da za ka yi, kada ka bar shi ya mutu ta hanyar lafiya.
7“Amma ka nuna alheri ga 'ya'yan Barzillai daga Gileyad, ka lura da su da kyau, gama sun nuna mini alheri sa'ad da nake gudu daga ɗan'uwanka, Absalom.
8“Ga kuma Shimai ɗan Gera, daga garin Bahurim ta Biliyaminu. Shi ne ya yi mini mugun zagi sa'ad da na tafi Mahanayim, amma sa'ad da ya zo taryata a Urdun, sai na rantse masa da Ubangiji, na ce ba zan kashe shi ba. 9Don haka dole ka hukunta shim, ka dai san abin da za ka yi da shi, lalle ne kuma za ka ga an kashe shi.”
(1 Tar 29.26-30)
10Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima. 11Ya yi shekara arba'in yana sarautar Isra'ila. Ya yi mulki shekara bakwai a Hebron, sa'an nan ya yi shekara talatin da uku yana mulki a Urushalima. 12Sulemanu kuwa ya hau gadon sarautar ubansa, Dawuda. Mulkinsa kuma ya kahu sosai.
13Sa'an nan Adonija ɗan Haggit ya tafi wurin Bat-sheba, tsohuwar Sulemanu. Ta ce masa, “Ka zo lafiya?” Ya ce, “Lafiya lau.” 14Sa'an nan ya ce, “Ina da wani abin da zan faɗa miki.” Ta ce, “To, sai ka faɗa.”
15Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra'ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al'amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena, gama tasa ce bisa ga nufin Allah. 16Yanzu dai ina da roƙo guda zuwa gare ki, kada ki hana mini.”
17Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.” Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”
18Bat-sheba kuwa ta ce, “Da kyau, zan yi wa sarki magana dominka.”
19Sa'an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa'an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa. 20Sai ta ce, “Ina da wani ɗan roƙo a gare ka, kada ka hana mini shi.” Sarki ya ce mata, “Ya tsohuwata, sai ki faɗi abin da kike so, gama ba zan hana miki ba.”
21Ta ce, “Bari a ba Adonija, ɗan'uwanka, Abishag daga Shunem, ta zama matarsa.”
22Sai sarki Sulemanu ya amsa wa tsohuwarsa, ya ce, “Don me kika roƙar wa Adonija Abishag? Ki roƙar masa sarautar mana, gama shi wana ne, Abiyata, firist kuma, da Yowab ɗan Zeruya suna goyon bayansa.” 23Sai sarki Sulemanu ya rantse da Ubangiji ya ce, “Allah ya kashe ni nan take idan ban sa Adonija ya biya wannan roƙo da ransa ba. 24Ubangiji ya kafa ni sosai a gadon sarautar tsohona, Dawuda, ya kuma cika alkawarinsa, ya ba ni mulki da zuriyata. Na rantse za a kashe Adonija yau.”
25Sai Sarki Sulemanu ya aiki Benaiya ɗan Yehoyada, ya kashe Adonija.
26Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.” 27Saboda haka Sulemanu ya kori Abiyata daga aikin firist na Ubangiji, ta haka aka cika maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Eli a Shilo.
28Da Yowab ya ji labari, gama har shi ya goyi bayan Adonija, ko da yake bai goyi bayan Absalom ba, sai ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ya kama zankayen bagade. 29Sa'ad da aka faɗa wa sarki Sulemanu, Yowab ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ga shi, yana wajen bagade, sai Sulemanu ya aiki Benaiya, ɗan Yehoyada, ya je ya kashe shi. 30Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.” Amma Yowab ya ce, “A'a, a nan zan mutu.” Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.
31Sarki kuwa ya ce masa, “Ka yi yadda ya ce, ka kashe shi, ka binne shi, ta haka za ka kawar mana da hakkin jinin da Yowab ya zubar ba dalili. 32Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza. 33Don haka alhakin jininsu zai koma a kan zuriyar Yowab har abada, amma da Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da gadon sarautarsa, albarkar Ubangiji za ta zauna a kansu har abada.”
34Benaiya ɗan Yehoyada kuwa ya shiga alfarwar ya kashe shi. Aka binne shi a gidansa a karkara. 35Sa'an nan sarki ya naɗa Benaiya ɗan Yehoyada, shugaban sojoji a maimakon Yowab, ya kuma naɗa Zadok, firist, a maimakon Abiyata.
36Sai kuma sarki ya aika a kirawo Shimai. Sa'an nan ya ce masa, “Ka gina wa kanka gida a Urushalima, ka zauna a nan, kada ka fita ko kaɗan zuwa wani wuri. 37Gama ran da ka fita, ka haye rafin Kidron, ka tabbata fa za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”
38Shimai kuwa ya ce wa sarki, “Abin da ka faɗa daidai ne, abin da ka ce in yi, zan yi, ranka ya daɗe.” Sai Shimai ya zauna a Urushalima kwanaki da yawa.
39Amma bayan shekara uku, sai biyu daga cikin bayin Shimai suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma'aka, Sarkin Gat. Da aka faɗa wa Shimai, cewa bayinsa suna a Gat, 40sai ya tashi, ya yi wa jakinsa shimfiɗa, ya tafi Gat wurin Akish don neman bayinsa. Ya kuwa komo da bayinsa daga Gat. 41Da aka faɗa wa Sulemanu, cewa Shimai ya fita Urushalima, ya tafi Gat, ya komo 42sai ya aika a kirawo Shimai, ya ce masa, “Ashe, ban sa ka ka rantse da Ubangiji ba, na kuma dokace ka da ƙarfi, cewa ka tabbata ran da ka fita zuwa ko'ina za ka mutu? Kai kuma ka ce mini, “‘Abin da ka ce daidai ne, zan yi biyayya.” 43To, me ya sa ka karya rantsuwar da ka yi da sunan Ubangiji, da kuma umarnin da na umarce ka?” 44Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka. 45Amma Ubangiji zai sa mini albarka, ya kuma tabbatar da gadon sarautar Dawuda har abada.”
46Sa'an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.
1Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima. 2Mutane suka yi ta miƙa hadayu a al'amudai dabam dabam, domin ba a gina haikalin Ubangiji ba tukuna. 3Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al'amudai dabam dabam.
(2 Tar 1.3-13)
4Sarki kuwa ya tafi Gibeyon don ya miƙa hadaya, gama a can ne akwai babban al'amudi. Ya miƙa hadayu na ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade. 5Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”
6Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona, domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana. 7Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba. 8Ga ni kuwa a tsakiyar jama'arka wadda ka zaɓa, jama'a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu. 9Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama'arka shari'a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama'arka mai yawa haka?”
10Ubangiji kuwa ya ji daɗin abin da Sulemanu ya roƙa. 11Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama'a, 12to, zan yi maka yadda ka roƙa, zan ba ka zuciya ta hikima da ganewa har ba wanda ya kai kamarka, ba kuwa wanda zai kai kamarka. 13Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba. 14Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”
15Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa'an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.
16Wata rana waɗansu mata masu zaman kansu, su biyu, suka zo gaban sarki. 17Sai ɗayar ta ce, “Ran sarki ya daɗe, ni da wannan mata a gida ɗaya muke zaune, sai na haifi ɗa namiji, ita kuwa tana nan a gidan. 18Bayan kwana uku da haihuwata, ita ma sai ta haihu. Mu kaɗai ne, ba kowa tare da mu a gidan. 19Ana nan sai ɗan wannan mata ya mutu da dare, domin ta kwanta a kansa. 20Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa'ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa'an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina. 21Sa'ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”
22Amma ɗaya matar ta ce, “A'a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!” Sai ta fari ta ce, “A'a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!” Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.
23Sa'an nan sarki ya ce, “To, kowaccenku ta ce mai ran shi ne nata, mataccen kuwa shi ne na waccan.” 24Sai ya umarta a kawo takobi. Da aka kawo takobin, 25sai ya ce, “A raba ɗan nan mai rai kashi biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”
26Saboda zuciyar mahaifiyar ta ainihi ta cika da juyayin ɗanta, ta ce wa sarki, “Ranka ya daɗe kada a kashe yaron! A ba ta!” Amma ɗayar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu, a ci gaba a raba shi.”
27Sa'an nan Sulemanu ya ce, “Kada ku kashe yaron! Ku miƙa wa ta farin, ita ce mahaifiyarsa ta ainihi.”
28Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.
1Sarki Sulemanu shi ne sarkin dukan Isra'ila,
7Sulemanu kuma ya naɗa mutum goma sha biyu a lardunan Isra'ila. Su ne za su tanaji abinci daga lardunansu domin sarki da iyalinsa. Kowane hakimi yakan kawo abinci wata guda a shekara.
20Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna. 21Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.
22Abincin gidan Sulemanu na rana ɗaya garwa talatin na lallausan gari ne, da garwa sittin na gari, 23da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
24Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da take yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta. 25Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.
26Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000). 27Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba. 28Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.
29Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa. 30Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar. 31Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba'ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, 'ya'yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi. 32Ya yi karin magana dubu uku, ya kuma yi waƙoƙi fiye da dubu. 33Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al'ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye. 34Sarakuna daga ko'ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.
(2 Tar 2.1-18)
1Hiram, Sarkin Taya, ya aiki jakadunsa zuwa wurin Sulemanu, sa'ad da ya ji ya gāji tsohonsa, gama Hiram abokin Dawuda ne ƙwarai dukan kwanakinsa. 2Sai Sulemanu ya aika wurin Hiram, ya ce, 3“Ka sani tsohona, Dawuda, bai iya gina Haikalin yin sujada ga Ubangiji Allahnsa ba saboda fama da yaƙe-yaƙe da maƙiyan da suke kewaye da shi, kafin Ubangiji ya mallakar masa da su. 4Amma yanzu Ubangiji Allahna ya hutasshe ni ta kowace fuska, ba fitina ko masifa. 5Ubangiji kuma ya yi wa tsohona Dawuda alkawari ya ce, “‘Ɗanka, wanda zai gāje ka, shi zai gina mini Haikali.” Yanzu kuwa na yi niyyar gina wannan haikali domin sujada ga Ubangiji Allahna. 6Saboda haka sai ka sa a saro mini itatuwan al'ul na Lebanon. Barorina za su haɗu da barorinka, ni kuwa zan biya ka aikin da barorinka za su yi bisa ga yadda ka ce, gama ka sani ba wani daga cikin mutanena da ya iya saran katako kamar mutanenka.”
7Da Hiram ya ji maganar Sulemanu, sai ya yi murna ƙwarai, ya ce, “Yabo ga Ubangiji saboda wannan rana, gama ya ba Dawuda ɗa mai hikima da zai shugabanci wannan babbar jama'a.” 8Sa'an nan Hiram ya aika wurin Sulemanu, ya ce, “Na ji saƙonka da ka aiko mini, a shirye nake in yi maka dukan abin da kake bukata a kan katakan itacen al'ul, da na fir. 9Barorina za su kawo su daga Lebanon zuwa teku. Zan sa a yi gadon fito da su, su bi teku zuwa inda kake so, a can mutanena za su warware su, sa'an nan naka mutane su kwashe su. Kai kuma ka ba da abinci ga mutanena.”
10Sai Hiram ya ba Sulemanu dukan katakan itacen al'ul da na fir da yake bukata, 11Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma'auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.
12Ubangiji kuwa ya ba Sulemanu hikima kamar yadda ya yi masa alkawari. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Hiram da Sulemanu, suka kuma ƙulla yarjejeniya da juna.
13Sarki Sulemanu kuwa ya sa a yi aikin tilas daga cikin Isra'ila duka. Waɗanda aka samu da za su yi aikin tilas ɗin mutum dubu talatin (30,000) ne. 14Ya riƙa aikawa da su zuwa Lebanon, ya raba su mutum dubu goma goma (10,000) su yi wata ɗaya ɗaya, sa'an nan su komo gida su yi wata biyu biyu. Adoniram shi ne shugaban aikin tilas ɗin. 15Sulemanu kuma yana da mutum dubu saba'in (70,000) a ƙasar tuddai masu haƙar duwatsu, da dubu tamanin (80,000) masu ɗauko duwatsun. 16Banda waɗannan kuma, Sulemanu ya sa shugabanni dubu uku da ɗari uku (3,300) waɗanda suke lura da aikin, da mutanen da suke yin aikin. 17Bisa ga umarnin sarki Sulemanu suka sassaƙa manyan duwatsu kyawawa don kafa harsashin ginin Haikali. 18Sai maginan Sulemanu, da na Hiram, da mutanen Gebal suka shirya duwatsu da katakai da za a gina Haikalin.
(2 Tar 3.1-14)
1A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji. 2Haikalin da sarki Sulemanu ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kamu talatin ne. 3Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne. 4Ya yi wa Haikalin tagogi, suna da fāɗi daga ciki fiye da waje. 5Ya kuma gina bene mai ɗakuna a jikin bangon Haikalin daga gefe, da kuma bayan Haikalin, har hawa uku, kowanne kamu bakwai da rabi. 6Fāɗin ɗakuna na ƙasa kamu biyar ne. Fāɗin ɗakunan hawa na biyu kamu shida ne. Fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa kamu bakwai ne. Bangaye a ƙasa sun fi na saman kauri, don ɗakunan su zauna sosai, ba tare da an kafa ginshiƙai a cikin ɗakunan ba.
7An gina Haikalin da duwatsun da aka sassaka tun daga can wurin da aka haƙo su, don haka ba a ji amon guduma, ko na gatari, ko na wani kayan aiki irin na ƙarfe ba, sa'ad da ake ginin Haikalin.
8Ƙofar domin ɗakuna na ƙasa tana wajen dama na Haikalin. Akwai matakai zuwa hawa na tsakiya da zuwa bene na uku. 9Ta haka ya gina Haikalin, ya rufe shi da katakan itacen al'ul. 10Benayen da ya gina kewaye da Haikalin, kowane bene tsayinsa kamu biyar. An haɗa su da Haikalin da katakan itacen al'ul.
11Ubangiji ya ce wa Sulemanu, 12“Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda. 13Zan zauna tare da mutanena, wato Isra'ila, a wannan Haikali da kake ginawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”
14Haka fa Sulemanu ya gama gina Haikali.
15Ya yi bango na ciki da katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama, ya kuma rufe daɓen da itacen fir. 16Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama. 17Tsawon sauran Wuri Mafi Tsarki kuwa kamu arba'in ne. 18Katakan itacen al'ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al'ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
19Ya shirya Wuri Mafi Tsarki na can cikin Haikalin domin a ajiye akwatin alkawari na Ubangiji. 20Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al'ul. 21Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa'an nan ya dalaye su da zinariya. 22Ya dalaye dukan cikin Haikalin da zinariya, ya kuma dalaye bagaden da yake Wuri Mafi Tsarki na can ciki, da zinariya.
23Ya yi kerubobi guda biyu da itacen zaitun, ya sa su cikin Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
29Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki. 30Har daɓen ƙasa, ya dalaye shi da zinariya.
31Ya yi ƙofa biyu na shiga Wuri Mafi Tsarki na can ciki da itacen zaitun. A saman ƙofar ya yi baka. 32Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa'an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya. 33Ya yi wa Haikalin madogaran ƙofa masu ƙusurwa huɗu da itacen zaitun. 34Ya kuma yi ƙyamare biyu a haɗe, ya yi su da itacen fir, 35ya zazzāna ya adanta su da siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya bai ɗaya.
36Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al'ul.
37A shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu aka kafa harsashin ginin Haikalin Ubangiji a watan biyu, wato watan Zib. 38A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.
1Sulemanu ya yi shekara goma sha uku yana gina gidansa kafin ya gama shi duka.
2Ya kuma gina wani ɗaki da katakai daga kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, faɗinsa kuma kamu hamsin, tsayinsa kuwa kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al'ul. Aka shimfiɗa katakan itacen al'ul a bisa ginshiƙan. 3Aka rufe shi da katakan al'ul a bisa ɗakuna arba'in da biyar da suke gefe, waɗanda suke bisa ginshiƙai. Ɗakuna goma sha biyar a kowane jeri har jeri uku. 4Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana daura da 'yar'uwarta, har jeri uku. 5Dukan ƙofofin da madogaransu murabba'i ne, taga kuma tana daura da 'yar'uwarta har jeri uku.
6Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa. 7Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari'a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al'ul.
8Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. Ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.
9Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa'an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna. 10An kafa harsashin ginin da manyan duwatsu masu tsada, waɗansu kamu takwas waɗansu goma. 11Daga sama kuma akwai duwatsu masu tsada waɗanda aka yanka su bisa ga ma'auni, da kuma itacen al'ul. 12Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.
(2 Tar 2.13-14; 3.15—5.1)
13Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne. 14Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.
15Ya kuwa yi ginshiƙi biyu na zubi da tagulla. Kowane ginshiƙi tsayinsa kamu goma sha takwas ne, da guru mai kamu goma sha biyu kewaye da shi. 16Ya kuma yi dajiya biyu ta zubi da tagulla don a sa a kan ginshiƙan. Tsayin kowace dajiya kamu biyar ne. 17Ya yi wa kowace dajiya da take kan ginshiƙan ragogi da tukakkun sarƙoƙi. Kowace dajiya tana da guda bakwai. 18Ta haka ya yi ginshiƙai jeri biyu kewaye da raga don rufe dajiya wadda take da siffofin rumman, haka kuma ya yi wa ɗaya dajiyar.
19Dajiyar da take kan ginshiƙai na cikin shirayin an yi su da fasalin bi-rana kamu huɗu huɗu. 20Dajiyar tana kan ginshiƙan nan biyu kusa da wani abu mai kama da gammo, wanda yake kusa da ragar. Akwai jeri biyu na siffofin rumman guda ɗari biyu a kewaye da dajiyar.
21Ya kafa ginshiƙan a shirayin Haikalin. Ya kafa ginshiƙi ɗaya a wajen dama, ya sa masa suna, Yakin, wato Allah ya kafa. Ya kafa ɗaya ginshiƙin a wajen hagu, ya sa masa suna Bo'aza, wato da ƙarfin Allah. 22A bisa kawunan ginshiƙan akwai dajiya masu fasalin bi-rana. Haka aka gama aikin ginshiƙan.
23Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne. 24Akwai goruna kewaye da gefensa. Gora goma a kowane kamu ɗaya. Suka kewaye kwatarniya. Gorunan jeri biyu ne, an yi zubinsu haɗe da kwatarniyar. 25Aka ɗora ta a kan siffofin bijimai goma sha biyu. Siffofin bijimai uku suna fuskantar gabas, uku kuma suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. An ɗora kwatarniya a kansu. Gindinsu duka na wajen ciki. 26Kaurin kwatarniya ya kai taƙin hannu guda. An yi gefenta kamar finjali, kamar kuma furen bi-rana. Takan ci garwa dubu biyu.
27Ya kuma yi dakali goma da tagulla. Kowane dakali tsawonsa kamu huɗu, faɗinsa kuma kamu huɗu, tsayinsa kuwa kamu uku ne. 28Yadda aka yi dakalan ke nan, dakalan suna da sassa, sassan kuma suna da mahaɗai. 29Aka zana hotunan zakoki, da na bijimai, da na kerubobi a kan sassan. A kan mahaɗan kuma akwai gammo, aka zana hotunan furanni a ƙarƙashin zakokin da bijiman. 30Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na karusa, da sandunan tagulla don sa kwatarniya. A kusurwoyin akwai abubuwa na zubi don tallabar kwatarniya. An zana furanni a kowane gefensu. 31Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da'ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba'i ne, ba da'ira ba. 32Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne. 33Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne. 34Akwai ginshiƙi huɗu daga ƙarƙashin kowane dakali. Ginshiƙan suna haɗe da dakalan. 35Akwai wani abu kamar gammo mai tsayi rabin kamu a kan dakalin. Ginshiƙan kuma da sassan a haɗe suke da dakalin. 36Ya zana siffofin kerubobi, da na zakoki, da na itatuwan dabino a jikin ginshiƙan da sassan a duk inda ya ga akwai fili. Ya kuma zana furanni kewaye da su.
37Haka aka yi dakalai, dukansu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya ne.
38Ya kuma yi daruna na tagulla guda goma. Kowane daro yana cin misalin garwa tamanin. Kowane daro kamu huɗu ne. Kowane dakali yana da daro ɗaya. 39Ya kafa dakali biyar a gefen dama na Haikalin, ya kuma kafa biyar a gefen hagu na Haikalin. Ya kuma sa kwatarniya na zubi a gefen dama na Haikalin, wajen kusurwar gabas maso kudu.
40-45Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi. ginshiƙai biyu dajiya da take a kawunan ginshiƙan raga biyu don rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙai siffofin rumman ɗari huɗu domin raga biyu ɗin, da jeri biyu na siffofin rumman domin kowace raga don a rufe dajiyar da take a kawunan ginshiƙan dakalai goma daruna goma a kan dakalan kwatarniya ɗaya siffofin bijimai guda goma sha biyu da kwatarniya take zaune a kai, tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da kwanoni Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla. 46Sarki ya sa a yi zubinsu a filin Urdun a ƙasar yumɓun da yake tsakanin Sukkot da Zaretan. 47Sulemanu bai auna nauyin kayayyakin aikin ba domin sun cika yawa. Ba a kuma san nauyin tagullar ba. 48-50Sulemanu ya yi dukan kayayyakin aikin da suke na Haikalin Ubangiji. bagaden zinariya teburin zinariya inda ake ajiye gurasar ajiyewa alkuki na zinariya guda biyar a gefen dama, biyar kuma a gefen hagu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki furanni fitilu arautaki finjalai na zinariya hantsuka daruna cokula farantan wuta na zinariya tsantsa almanani na zinariya domin ƙofofin ɗaki na can cikin Haikali, wato Wuri Mafi Tsarki, da ƙofofin Haikalin
51Haka sarki Sulemanu ya gama dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sai ya kawo abubuwan da tsohonsa Dawuda ya keɓe, wato azurfa, da zinariya, da kayayyakin aiki, ya ajiye su cikin taskokin Haikalin Ubangiji.
(2 Tar 5.2—6.2)
1Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali. 2Dukan jama'ar Isra'ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai. 3Dukan dattawan Isra'ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin, 4suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su. 5Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama'ar Isra'ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa. 6Sa'an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji suka sa a cikin Wuri Mai Tsarki na can ciki a Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi. 7Gama fikafikan kerubobin suna buɗe a bisa wurin da akwatin alkawarin yake domin su rufe akwatin alkawarin da sandunansa. 8Sandunansa suna da tsawo har ana iya ganinsu daga ɗaki na can ciki daga Wuri Mai Tsarki, amma ba a iya ganinsu daga waje. Suna nan haka har wa yau. 9Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama'ar Isra'ila sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar.
10Sa'ad da firistoci suka fito daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya rufe Haikalin Ubangiji, 11har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji. 12Sa'an nan Sulemanu ya yi addu'a ya ce, “Ubangiji ya ce zai zauna cikin gizagizai masu duhu.
13Yanzu na gina maka ɗaki mai daraja, Wurin da za ka zauna har abada.”
(2 Tar 6.3-11)
14Sa'an nan sarki Sulemanu ya juya, ya fuskanci jama'a suna tsaye, ya roƙi Allah ya sa musu albarka. 15Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa, 16“‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.”
17Sulemanu ya ci gaba, ya ce, “Tsohona, Dawuda ya yi niyyar gina wa Ubangiji Allah na Isra'ila ɗaki, 18amma Ubangiji ya ce wa tsohona, Dawuda, ya ji daɗin niyyar da ya yi ta gina Haikali, 19amma duk da haka ba zai gina Haikalin ba, sai ɗansa wanda za a haifa masa shi ne zai gina Haikali domin sunan Ubangiji. 20Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra'ila. 21A cikin Haikalin kuma na shirya wa akwatin alkawari wuri, inda alkawarin Ubangiji yake, wato alkawarin da ya yi wa kakanninmu sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar.”
(2 Tar 6.12-42)
22Sa'an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama'ar Isra'ila. Ya ɗaga hannuwansa sama, 23ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya. 24Kai wanda ka cika abin da ka faɗa wa bawanka, Dawuda, tsohona, i, abin da ka faɗa da bakinka ka cika shi yau. 25Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, “‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.” 26Yanzu fa, ya Allah na Isra'ila, sai ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka, Dawuda, tsohona.
27“Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina? 28Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu'ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu'ata da nake yi a gabanka yau. 29Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu'ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin. 30Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra'ilawa, idan sun yi addu'a, suna fuskantar wurin nan, sa'ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.
31“Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali, 32ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara'anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.
33“Lokacin da abokan gāba suka ci mutanenka Isra'ila da yaƙi, saboda sun yi maka zunubi, idan sun komo wurinka, suka yabe ka, suka yi addu'a, suka roƙe ka a wannan Haikali, 34sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama'ar Isra'ila zunubinsu, sa'an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.
35“Idan an hore su da rashin ruwan sama, saboda sun yi maka zunubi, idan sun tuba, suna fuskantar wannan Haikali, suka yi addu'a, suka kuma yabe ka, 36sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama'arka Isra'ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama'arka gādo.
37“Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama'arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu, 38sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Idan ɗaya daga cikin jama'arka Isra'ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'a wajen wannan Haikali, 39sai ka ji addu'arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi, 40domin mutanenka su yi tsoronka a dukan kwanakinsu a ƙasar da ka ba kakanninmu.
41“Sa'ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka, 42da manyan al'amura da ka yi wa jama'arka, ya zo domin ya yi maka sujada, da kuma addu'a gare ka a wannan Haikali, 43sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.
44“Idan jama'arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu'a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka, 45sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Ka ji daga sama, ka ba su nasara.
46“Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa, 47idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu'arsu, ya Ubangiji. 48Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka, 49sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, wurin zamanka, ka amsa, ka ji ƙansu. 50Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu. 51Gama su jama'arka ne, mallakarka, waɗanda ka fito da su daga Masar, daga tsakiyar azaba.
52“Ya Ubangiji Allah, ka dubi jama'arka Isra'ila da sarkinsu da idon rahama, ka kasa kunne gare su duk lokacin da suka yi roƙo a gare ka. 53Gama ka keɓe su daga sauran dukan al'ummai domin su zama jama'arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa'ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”
54Da Sulemanu ya gama wannan addu'a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama. 55Ya tsaya, ya sa wa taron jama'ar Isra'ila albarka da babbar murya, ya ce, 56“Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa. 57Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu. 58Ka sa zukatanmu su juyo gare ka, mu yi tafiya cikin tafarkunka, mu kiyaye umarnanka, da ka'idodinka da dokokinka, waɗanda ka umarci kakanninmu. 59Ya Ubangiji Allahnmu, ka sa wannan roƙo da na yi ya kasance a gabanka, dare da rana. Ka biya bukatar bawanka, da bukatar jama'arka, Isra'ila, ta kowace rana, 60domin dukan al'umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani. 61Ku kuma jama'arsa, sai ku amince da Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, ku kiyaye dokokinsa da umarnansa, kamar yadda kuke yi a yau.”
(2 Tar 7.4-10)
62Sa'an nan sarki Sulemanu, tare da Isra'ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji. 63Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji. 64A wannan rana kuma ya keɓe tsakiyar filin da yake gaban Haikalin Ubangiji, gama a nan ne ya miƙa hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama, gama bagaden tagullar da yake gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta ƙwarai da za a yi dukan waɗannan hadayu a kansa.
65Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu. 66A rana ta takwas ya sallami jama'ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa'an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama'arsa, Isra'ilawa.
(2 Tar 7.11-22)
1Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi, 2sai Ubangiji ya sāke bayyana gare shi, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibeyon. 3Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum. 4Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka'idodina, 5sa'an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra'ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa'ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba. 6Amma idan kai, ko 'ya'yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada, 7sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane. 8Wannan Haikali kuwa zai zama tsibin juji, duk wanda zai wuce ta wurin, zai yi mamaki, ya yi tsaki, ya ce, “‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa ƙasar nan da Haikalin nan haka?” 9Waɗansu kuwa za su amsa su ce, “‘Saboda sun bar bin Ubangiji Allahnsu wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, domin haka Ubangiji ya ɗora musu wannan masifa.”
(2 Tar 8.1-18)
10Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa. 11Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al'ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili. 12Amma sa'ad da Hiram ya zo daga Taya domin ya ga garuruwan da Sulemanu ya ba shi, sai ya ga ba su gamshe shi ba. 13Don haka ya ce wa Sulemanu, “Dan'uwa, waɗanne irin garuruwa ke nan da ka ba ni?” Saboda haka har yanzu ana kiran ƙasar Kabul, wato marar amfani. 14Hiram kuma ya aika wa Sulemanu da zinariya mai nauyin talanti ɗari da ashirin.
15Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer. 16Gama Fir'auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa'an nan ya yi wa 'yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin. 17Sulemanu kuwa ya sāke gina Gezer. Ya kuma sa aka gina Bet-horon ta kwari ta aikin tilas, 18da Ba'alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza, 19da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.
23Sulemanu yana da masu lura da aiki su ɗari biyar da hamsin, suna lura da masu aikin tilas a wurare dabam dabam da ake wa Sulemanu gini.
24Da 'yar Fir'auna matar Sulemanu ta fita birnin Dawuda, zuwa gidan kanta wanda Sulemanu ya gina mata, sa'an nan ya gina birnin Millo.
25Sau uku a shekara Sulemanu yakan miƙa hadayu na ƙonawa, da na salama, da hadayar turare, a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji. Ta haka aka gama ginin Haikali.
26Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom. 27Sarki Hiram ya aiki barorinsa, gogaggun matuƙan jiragen ruwa, da jiragen ruwa tare da barorin Sulemanu. 28Sai suka tafi Ofir suka kawo wa sarki Sulemanu zinariya mai nauyin talanti ɗari huɗu da shirin.
(2 Tar 9.1-12)
1Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. 2Ta iso Urushalima da 'yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta. 3Sulemanu ya amsa tambayoyinta dukka, ba abin da ya gagare shi amsawa.
10Sa'an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya, da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.
11Bayan wannan kuma jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itacen almug da yawa, da duwatsu masu daraja daga can. 12Da itacen almug ne sarki ya yi ginshiƙai na Haikalin Ubangiji da gidan sarki, ya kuma yi molaye da garayu domin mawaƙa. Har wa yau ba a taɓa samu, ko ganin irin itacen almug kamar wannan ba.
13Sarki Sulemanu ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ta nuna tana bukata, banda kyautar karamcin da ya yi mata. Sai ta koma ƙasarta tare da barorinta.
(2 Tar 9.13-24)
14Yawan zinariya da akan kawo wa Sulemanu kowace shekara yakan kai talanti ɗari shida da sittin da shida na zinariya. 15Banda wanda ya sa wa 'yan kasuwa, da fatake, da harajin dukan sarakunan Arabiya, da na hakimai.
16Sarki Sulemanu ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu da zinariya. Anyi kowace garkuwa da shekel ɗari shida na zinariya. 17Ya kuma yi waɗansu garkuwoyi guda ɗari uku da zinariya. An yi kowace garkuwa da shekel dari uku na zinariya. Sarki kuwa ya ajiye su a ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon.
18Ya kuma yi babban gadon sarauta na hauren giwa, sa'an nan ya dalaye shi da tattacciyar zinariya. 19Gadon sarautar yana da matakai shida da siffar kan maraƙi a bayan gadon sarautar, a kowane gefen mazaunin kuma, akwai wurin ɗora hannu da siffofin zaki biyu suna tsaye a gefen wuraren ɗora hannun. 20Akwai siffar zaki goma sha biyu suna tsaye a kowane gefen matakan nan shida. Ba a taɓa yin irinsu a kowace masarauta ba.
21Dukan finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya aka yi su, haka kuma finjalan da suke cikin ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon, ba a yi wani finjali da azurfa ba, domin ba a mai da azurfa kome ba a kwanakin Sulemanu. 22Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.
23Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima. 24Dukansu suna so su zo wurin Sulemanu don su ji hikimarsa wadda Allah ya ba shi. 25Kowannensu yakan kawo masa yawan kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai kowace shekara.
(2 Tar 1.4-17; 9.25-28)
26Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima. 27Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar dai duwatsu a Urushalima, itacen al'ul kuma ya zama kamar jumaiza na Shefela. 28Sulemanu kuwa ya sayo dawakai daga Masar da Kuye. 'Yan kasuwar sarki sukan sayo dawakai daga Kuye a kan tamaninsu. 29Akan sayo karusa a Masar a bakin azurfa ɗari shida, doki kuwa a bakin ɗari da hamsin, 'yan kasuwar sarki sukan sayar da su ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa.
1Sarki Sulemanu ya ƙaunaci baƙin mata. Banda 'yar Fir'auna, Sarkin Masar, ya auri matan Mowabawa, da na Ammonawa, da na Edomawa, da na Sidoniyawa, da na Hittiyawa. 2Suna kuwa cikin al'umman da Ubangiji ya umarci jama'ar Isra'ila, ya ce, “Kada ku yi aurayya da su, gama hakika za su karkatar da zuciyarku zuwa gumakansu.” Sulemanu kuwa ya manne wa waɗannan mata da yake ƙauna. 3Ya auri mata ɗari bakwai, dukansu kuwa gimbiyoyi ne. Yana kuma da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa kuwa suka janye zuciyarsa daga bin Ubangiji, 4sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba. 5Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa. 6Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba. 7Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima. 8Ya kuma gina masujadai inda dukan matansa baƙi za su riƙa miƙa turare da hadayu ga gumakansu.
9Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu, 10ya kuma umarce shi kada ya bi gumaka. Amma bai kiyaye umarnin da Ubangiji ya yi masa ba. 11Saboda haka Ubangiji ya ce wa Sulemanu, “Tun da yake ka yi haka, ba ka kuwa kiyaye umarnina da dokokina waɗanda na umarce ka da su ba, to, hakika zan ƙwace mulki daga gare ka, in ba baranka. 12Amma saboda tsohonka, Dawuda, ba zan ƙwace a zamaninka ba, amma zan ƙwace daga hannun ɗanka. 13Duk da haka ba zan ƙwace mulkin duka ba, amma zan ba ɗanka kabila guda, saboda bawana Dawuda, saboda kuma Urushalima wadda na zaɓa.”
14Ubangiji kuwa ya sa Hadad Ba'edome, ya tayar wa Sulemanu. Shi Hadad daga jinin sarautar Edom ne. 15Gama sa'ad da Dawuda ya ci Edom, Yowab, shugaban sojoji, ya tafi don ya binne kisassu, sun yi wata shida a can, shi da mutanensa, sai ya kashe kowane namijin da yake cikin Edom. 16Gama Yowab da dukan Isra'ilawa sun tsaya a Edom wata shida, sai da ya gama kashe mazajen Edom duka. 17Amma Hadad ya tsere zuwa Masar tare da waɗansu Edomawa, barorin tsohonsa. Hadad yana ɗan saurayi a lokacin. 18Suka kama hanya daga Madayana suka zo Faran. Daga Faran suka kwashi mutane tare da su, suka tafi Masar zuwa wurin Fir'auna, Sarkin Masar, wanda ya ba shi gida, ya kuma riƙa ba shi abinci, ya kuma ba shi ƙasa. 19Hadad kuwa ya sami farin jini ƙwarai a wurin Fir'auna, har ya aurar masa da ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes, sarauniya. 20Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir'auna. Genubat kuwa ya zauna tare da 'ya'yan Fir'auna, maza.
21Amma sa'ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir'auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”
22Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?” Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.
23Allah kuma ya sa Rezon ɗan Eliyada, ya tayar wa Sulemanu, shi Rezon ya gudu daga wurin maigidansa, Hadadezer Sarkin Zoba. 24Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban 'yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu. 25Ya zama abokin gāban Isra'ila a dukan zamanin Sulemanu. Ya yi ta ɓarna kamar yadda Hadad ya yi. Ya ƙi jinin mutane Isra'ila. Ya yi mulkin suriya.
26Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki. 27Ga dalilin da ya sa ya tayar wa sarki. Sulemanu ya gina Millo ya kuma faɗaɗa garun birnin Dawuda tsohonsa. 28Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu. 29A sa'ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai, 30sai Ahija ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa ta ƙyalle goma sha biyu, 31ya ce wa Yerobowam, “Kwashi ƙyalle goma, gama haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, “‘Ga shi, ina gab da in kece sarauta daga hannun Sulemanu, zan ba ka kabila goma. 32Amma Sulemanu, zai sami kabila ɗaya saboda bawana Dawuda, da kuma ɗaya saboda Urushalima, wato birnin da na zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka. 33Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka'idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba. 34Duk da haka ba zan karɓe sarauta duka daga hannunsa ba, amma zan bar shi ya yi mulki muddin ransa saboda bawana Dawuda, wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnaina da dokokina. 35Amma zan karɓe mulki daga hannun ɗansa in ba ka, zan ba ka kabila goma. 36Duk da haka zan ba ɗansa kabila guda, domin bawana Dawuda ya kasance da fitila kullum a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa sunana. 37Zan sa ka yi mulki a kan duk abin da ranka yake bukata, za ka zama Sarkin Isra'ila. 38Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila. 39Zan wahalar da zuriyar Dawuda, amma ba har abada ba.”
40Sulemanu kuwa ya nema ya kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tashi, ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak Sarkin Masar, ya zauna a can har rasuwar Sulemanu.
(2 Tar 9.29-31)
41Sauran ayyukan Sulemanu, da dukan abin da ya yi, da hikimarsa an rubuta su a littafin tarihin Sulemanu. 42Sulemanu ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima a kan Isra'ila duka. 43Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima. Dansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.
(2 Tar 10.1—11.4)
1Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra'ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki. 2Sa'ad da Yerobowam, ɗan Nebat, ya ji labari, gama a lokacin yana Masar inda ya gudu saboda sarki Sulemanu, sai ya komo daga Masar. 3Suka aika a kirawo shi, sai Yerobowam da dukan taron jama'ar Isra'ila suka zo suka ce wa Rehobowam, 4“Tsohonka ya nawaita mana, yanzu sai ka rage mana wahalar aikin tsohonka da nawayarsa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
5Sai ya ce musu, “Ku tafi, ku sāke zuwa bayan kwana uku.” Sai suka tafi.
6Sarki Rehobowam kuwa ya nemi shawara daga wurin dattawa, waɗanda suka bauta wa tsohonsa, Sulemanu, lokacin da yake da rai. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?”
7Suka ce masa, “Idan za ka zama mai lura da jama'an nan yau, ka bauta musu, sai ka yi musu magana da kyau, su kuwa za su zama talakawanka har abada.” 8Amma ya yi watsi da shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawara daga wurin matasa, tsararsa. 9Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka roƙe ni cewa in rage musu nawayar da tsohona ya aza musu?”
10Matasa da suke tsara ɗaya da shi kuwa suka ce masa, “Haka za ka faɗa wa mutanen nan da suka yi magana da kai, cewa tsohonka ya nawaita musu, amma sai ka sawwaƙa musu, “‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri. 11Zan ƙara a kan nawayar da tsohona ya aza muku. Shi ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.”
12Yerobowam da dukan mutane suka zo wurin Rehobowam a rana ta uku kamar yadda ya faɗa musu su zo wurinsa bayan kwana uku. 13Da suka zo, sai sarki ya yi musu magana da zafi, ya kuma yi watsi da shawarar da dattawa suka ba shi. 14Ya yi musu magana bisa ga shawarar matasa ya ce, “Tsohona ya nawaita muku, ni kuwa zan ƙara nawaita muku. Tsohona ya yi muku horo da bulala, amma ni zan yi muku da kunamai.” 15Haka kuwa sarki ya ƙi jin roƙon da jama'a suka yi masa, gama Ubangiji ne ya sa al'amarin ya zama haka domin ya cika maganarsa, wadda ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta bakin Ahija mutumin Shilo.
16Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!” Jama'ar Isra'ila fa suka tayar, 17suka bar Rehobowam ya sarauci jama'ar da ke zaune a yankin ƙasar Yahuza.
18Sa'an nan sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, shugaban aikin tilas, sai mutanen Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har lahira. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta, ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima. 19Da haka mutanen Isra'ila suka tayar wa gidan Dawuda har wa yau.
20Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama'a. Suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.
21Da Rehobowam ya komo Urushalima, sai ya tara dukan jama'ar gidan Yahuza, da na kabilar Biliyaminu. Aka sami mayaƙa dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) waɗanda za su yi yaƙi da gidan Isra'ila, don su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowam, ɗan Sulemanu. 22Amma Ubangiji Allah ya yi magana da annabi Shemaiya, 23ya faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen gidan Yahuza da na Biliyaminu, da sauran jama'a, 24Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al'amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.
25Sa'an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel. 26Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda. 27Idan mutanen nan sun ci gaba da zuwa Urushalima don miƙa wa Ubangiji hadayu, zuciyarsu za ta koma kan sarki Rehobowam, na Yahuza, za su kashe ni, su koma wurinsa.”
28Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.” 29Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan. 30Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan. 31Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa'an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.
32Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel. 33Ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, wato watan da ya zaɓa don kansa. Ya kafa wa jama'ar Isra'ila idi. Sai ya tafi don ya ƙona turare a kan bagaden.
1Bisa ga umarnin Ubangiji, sai ga annabi ya fito daga Yahuza zuwa Betel. Yerobowam kuwa yana tsaye kusa da bagaden don ya ƙona turare. 2Bisa ga umarnin Ubangiji, sai annabin ya ta da murya, ya ce, “Ya bagade, bagade, Ubangiji ya ce za a haifi ɗa a gidan Dawuda, sunansa Yosiya wanda zai miƙa firistoci na masujadan tuddai hadaya a kanka, wato firistoci waɗanda suke ƙona turare. Za a ƙone ƙasusuwan mutane a bisa kanka.” 3Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”
4Da sarki ya ji maganar annabin, wato wadda ya yi a kan bagaden da yake Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden, ya ce, “Ku kama shi.” Hannun da ya miƙa kuwa ya sage, bai iya komo da shi ba. 5Aka rushe bagaden, aka kuma zubar da tokar daga bagaden bisa ga alamar da annabin ya faɗa da sunan Ubangiji. 6Sarki Yerobowam ya ce wa annabin, “In ka yarda ka yi roƙo ga Ubangiji Allahnka domina, ka yi mini addu'a don ya warkar da hannuna.” Annabi ya roƙi Ubangiji, sai hannun sarki ya komo daidai. 7Sa'an nan sarkin ya ce wa annabin, “Zo mu tafi gida don ka shaƙata, zan ba ka lada.”
8Annabin kuwa ya ce wa sarki, “Ko da za ka ba ni rabin gidanka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuma zan ci abinci ko in sha ruwa a wurin nan ba. 9Gama Ubangiji ya umarce ni da cewa kada in ci abinci, ko in sha ruwa, ko in koma ta hanyar da na zo.” 10Haka kuwa ya koma ta wata hanya dabam bai koma ta hanyar da ya bi zuwa Betel ba.
11Akwai wani tsohon annabi a Betel. 'Ya'yansa maza kuwa suka tafi suka faɗa masa dukan abin da annabin Allah ya yi a Betel a wannan rana. Suka faɗa wa mahaifinsu maganar da annabin Allah ya faɗa wa sarki. 12Tsohon annabin ya tambaye su, “Wace hanya ya bi?” Su kuwa suka nuna masa hanyar. 13Ya ce musu su ɗaura wa jakinsa shimfiɗa. Sai suka ɗaura wa jakin shimfiɗa, shi kuwa ya hau, 14ya bi bayan annabin nan da ya fito daga Yahuza, ya same shi yana zaune a gindin itace oak. Ya tambaye shi, “Ko kai ne annabin da ya zo daga Yahuza?” Mutumin ya amsa, “I, ni ne,”
15Sa'an nan ya ce masa, “Zo mu tafi gida ka ci abinci.”
16Amma annabin ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ba kuwa zan shiga gida ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri, 17gama Ubangiji ya ce mini kada in ci abinci, ko in sha ruwa a can, ko in koma ta hanyar da na zo.”
18Sa'an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.
19Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin. 20Sa'ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah, 21sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, “‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba, 22amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.”
23Bayan da ya ci abinci, ya sha sai tsohon annabin ya ɗaura wa jaki shimfiɗa don annabin da ya komo da shi. 24Sa'ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar. 25Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.
26Sa'ad da tsohon annabin nan ya ji, sai ya ce, “Wannan annabin Allah ne, wanda bai yi biyayya da maganar Ubangiji ba, saboda haka Ubangiji ya bashe shi ga zaki ya yayyage shi, ya kashe shi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.” 27Sa'an nan ya ce wa 'ya'yansa maza, “Ku ɗaura mini shimfiɗa.” Su kuwa suka ɗaura, 28ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba. 29Tsohon annabin kuwa ya ɗauki gawar ya ɗora bisa jakin, ya kawo ta cikin birni, wato Betel, don yin makoki da binnewa. 30Ya binne gawar a kabarinsa, sa'an nan suka yi makoki suna cewa, “Kaito, dan'uwana!” 31Bayan da ya binne shi, sai ya ce wa 'ya'yansa, “Sa'ad da na rasu, sai ku binne ni a kabarin da aka binne annabin nan. Ku ajiye gawata kusa da tasa. 32Gama maganar Ubangiji da ya faɗa game da bagaden da yake cikin Betel, da masujadai na kan tuddai waɗanda suke a garuruwan Samariya, za ta cika.”
33Bayan wannan al'amari Yerobowam bai bar muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci daga cikin mutane don masujadai da suke kan tuddai. Duk mutumin da yake so, sai ya keɓe shi don ya zama firist na masujada da take kan tudu. 34Wannan zunubi ya zama sanadi ga gidan Yerobowam, har ya isa a shafe gidan, a hallaka shi ƙaƙaf.
1A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo. 2Yerobowam kuwa ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kama don kada a sani ke matata ce, sa'an nan ki tafi Shilo wurin Ahija, annabin nan wanda ya ce mini zan sarauci jama'an nan. 3Ki ɗauki malmalar abinci guda goma, da waina, da kurtun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”
4Matar kuwa ta yi haka. Ta tashi ta tafi Shilo a gidan Ahija. Ahija ba ya gani, saboda tsufa. 5Ubangiji ya ce wa Ahija, “Ga matar Yerobowam tana zuwa don ta tambaye ka abin da zai faru da ɗanta, gama ɗan yana ciwo. To, da haka za ka amsa mata, gama sa'ad da ta zo, za ta nuna kamar ita wata mace ce dabam.”
6Da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin ƙofa, sai ya ce mata, “Ki shigo, matar Yerobowam, me ya sa kike yi kamar ke wata ce dabam? Gama an umarce ni in faɗa miki labari marar daɗi. 7Ki koma, ki faɗa wa Yerobowam, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, “‘Na ɗaukaka ka daga cikin mutane, na sa ka zama shugaban mutanena, Isra'ilawa. 8Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina, ya bi ni da zuciya ɗaya, yana yin abin da yake daidai a gare ni. 9Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni. 10Saboda haka zan kawo masifa a gidanka. Zan datse maka kowane ɗa namiji, ko bawa, ko 'yantacce, daga cikin Isra'ila. Zan ƙone gidanka kamar yadda akan ƙone juji ƙurmus. 11Duk wanda yake naka wanda zai mutu a birni, karnuka za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura tsuntsaye za su cinye shi, ni Ubangiji, ni ne na faɗa.”
12“Ki tashi, ki koma gida. Da shigarki birni, yaron zai mutu. 13Dukan jama'ar Isra'ila za su yi makoki dominsa, su binne shi, gama shi kaɗai zai sami binnewa daga cikin gidan Yerobowam, domin a gare shi kaɗai aka iske abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, yake murna da shi. 14Ubangiji kuma zai ta da wani wanda zai sarauci Isra'ila, wanda kuma zai rushe gidan Yerobowam daga yanzu har zuwa nan gaba. 15Ubangiji zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra'ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi. 16Ubangiji zai rabu da Isra'ila saboda zunuban Yerobowam waɗanda ya yi, da kuma waɗanda ya sa mutanen Isra'ila su yi.”
17Sa'an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu. 18Jama'ar Isra'ila duka suka binne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa, annabi Ahija.
19Sauran ayyukan Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 20Yerobowam ya yi mulki shekara ashirin da biyu sa'an nan ya rasu, aka binne shi. Ɗansa Nadab ya gāji sarautarsa.
(2 Tar 11.5—12.15)
21Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce.
22Mutanen Yahuza suka yi wa Ubangiji zunubi. Suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata fiye da abin da kakanninsu suka yi. 23Gama su ma sun gina wa kansu wuraren tsafi a tuddai, da ginshiƙai, da gumaka a tuddai, da cikin duhuwar itatuwa. 24Fiye da haka kuma akwai mata da maza da suke aikin karuwanci a wuraren da suke tsafin a wurin al'ummai. Mutanen Yahuza sun yi dukan abubuwan ƙazanta na al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora sa'ad da Isra'ilawa suke gab da shigar ƙasar.
25A cikin shekara ta biyar ta sarautar sarki Rehobowam, sai Shishak Sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi. 26Ya kwashe dukiyar Haikalin Ubangiji, da dukiyar gidan sarki duka. Ya kuma kwashe garkuwoyin zinariya waɗanda Sulemanu ya yi. 27A maimakonsu kuwa sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla, ya sa a hannun shugabannin masu tsaro waɗanda suke tsaron ƙofar gidan sarki. 28Duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su ɗauki garkuwoyin, su kuma mayar da su a ɗakin tsaro.
29Sauran ayyukan Rehobowam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 30Kullum akan yi ta yin yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam, 31Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.
(2 Tar 13.1—14.1)
1A shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yerobowam ɗan Nebat, Abaija ya sarauci mutanen Yahuza. 2Ya yi mulki shekara uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa. 3Shi kuma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa sosai, kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi ba. 4Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima, 5domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte. 6Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa. 7Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
8Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.
(2 Tar 14.1-5; 15.16-19)
9A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra'ila, Asa ya sarauci jama'ar Yahuza. 10Ya yi shekara arba'in da ɗaya yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa. 11Asa kuwa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi. 12Ya kori mata da maza da suke karuwanci a wuraren tsafi na arna a ƙasar, ya kuma kawar da gumakan da kakanninsa suka yi. 13Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma'aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron. 14Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba, duk da haka Asa ya yi aminci sosai ga Ubangiji dukan kwanakinsa. 15Ya kawo dukan tsarkakakkun abubuwan da tsohonsa ya keɓe, da kuma azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi, a cikin Haikalin Ubangiji.
(2 Tar 16.1-14)
16Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha, Sarkin Isra'ila a dukan kwanakin mulkinsu. 17Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza. 18Sa'an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce, 19“Bari mu ƙulla alkawari da juna kamar yadda tsohona da tsohonka suka yi, ga shi, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Sai ka tafi, ka warware alkawarinka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, domin ya tashi ya bar ni.”
20Ben-hadad kuwa ya yarda da maganar sarki Asa. Ya kuwa aiki shugabannin sojojinsa su yi yaƙi da garuruwan Isra'ila. Su kuwa suka tafi, suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan Kinneret, da dukan ƙasar Naftali. 21Da Ba'asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.
22Sa'an nan sarki Asa ya gayyaci dukan jama'ar Yahuza, ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi suka kwashe duwatsu da katakai waɗanda Ba'asha yake ginin Rama da su. Da su sarki Asa ya gina Geba ta Biliyaminu, da Mizfa.
23Sauran dukan ayyukan Asa, da dukan ƙarfinsa, da dukan abin da ya yi, da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. Amma da ya tsufa, sai ya sami ciwo a ƙafafunsa. 24Asa kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima, Ɗansa Yehoshafat ya gāji sarautarsa.
25Nadab ɗan Yerobowam ya ci sarautar Isra'ila a shekara ta biyu ta sarautar Asa Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu. 26Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra'ila su yi zunubi.
27Ba'asha ɗan Ahija kuwa daga gidan Issaka ya yi wa Nadab maƙarƙashiya, ya kashe shi a Gibbeton ta Filistiyawa, gama Nadab da mutanen Isra'ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi. 28Haka Ba'asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, ya kuwa ci sarautar a maimakonsa. 29Nan da nan da ya zama sarki, sai ya kashe dukan mutanen gidan Yerobowam, bai bar wani na gidan Yerobowam da rai ba, ya hallaka su sarai, bisa ga maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa bawansa Ahija mutumin Shilo. 30Wannan abu ya faru saboda zunubin Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi, ya tsokani fushin Ubangiji Allah na Isra'ila.
31Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 32Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba'asha Sarkin Isra'ila dukan kwanakin sarautarsu.
33A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba'asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta. 34Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi.
1Ubangiji ya yi magana da Yehu, ɗan Hanani a kan Ba'asha, ya ce, 2“Tun da yake na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaban jama'ata Isra'ila, kai kuwa ka bi hanyar Yerobowam, ka sa jama'ata, wato Isra'ila, su yi zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu, 3to, zan shafe ka da gidansa, in mai da gidanka kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat. 4Duk mutumin da yake naka da zai mutu a cikin birni, karnuka ne za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura, tsuntsaye ne za su cinye shi.”
5Sauran ayyukan Ba'asha, da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 6Ba'asha kuwa ya rasu, aka binne shi a Tirza. Sai Ila, ɗansa ya gāji sarautarsa.
7Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.
8A shekara ta ashirin da shida ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ila ɗan Ba'asha, ya ci sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi sarauta shekara biyu. 9Amma Zimri, shugaban rabin karusan Ila, ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ila yake Tirza, ya sha, ya bugu a gidan Arza wanda yake lura da fāda, 10sai Zimri ya shiga gidan, ya buge shi ya kashe shi. Wannan ya faru a shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza.
11Da Zimri ya zama sarki, nan da nan sai ya kashe dukan mutanen gidan Ba'asha, bai bar masa wani namiji, ko dangi, ko aboki ba. 12Haka Zimri ya hallaka gidan Ba'asha bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa a kansa ta bakin annabi Yehu. 13Wannan kuwa ya faru saboda zunuban Ba'asha da na ɗansa Ila, da zunuban da suka sa jama'ar Isra'ila su yi, har suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu. 14Sauran ayyukan Ila da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
15A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirza. A lokacin nan sojoji suka kai wa Gibbeton ta Filistiyawa yaƙi. 16Da sojojin da suke bakin dāga suka ji an ce Zimri ya shirya makirci, ya kashe sarki, sai dukan Isra'ilawa suka naɗa Omri, shugaban sojojin, can a sansani. A wannan rana ya zama Sarkin Isra'ila. 17Omri kuwa ya tashi daga Gibbeton tare da dukan Isra'ila, suka kai wa Tirza yaƙi. 18Da Zimri ya ga an ci birnin, sai ya tafi ya shiga hasumiyar da take a fāda, ya sa wa fādar wuta, wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu. 19Wannan ya faru saboda zunuban da ya aikata, ya yi mugun abu a gaban Ubangiji, ya bi hanyar Yerobowam da zunubinsa da ya aikata, har ya sa Isra'ilawa su yi zunubi. 20Sauran ayyukan Zimri da makircin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
21Jama'ar Isra'ila suka rabu biyu. Rabi suka bi Tibni ɗan Ginat don su naɗa shi sarki. Rabin kuwa suka bi Omri. 22Amma jama'ar da suka bi Omri suka rinjayi waɗanda suka bi Tibni ɗan Ginat. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki. 23A shekara ta talatin da ɗaya ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Omri ya ci sarautar Isra'ila. Ya yi shekara goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekara shida yana mulki a Tirza. 24Sa'an nan ya sayi tudun Samariya daga Shemer a bakin azurfa dubu shida (6,000), a wurin Shemer, ya kuwa yi gini a kan tudun, ya sa masa suna Samariya saboda sunan Shemer mai tudun.
25Omri kuwa ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi. 26Ya bi duk irin hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, da irin zunuban da ya sa jama'ar Isra'ila su yi. Suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu. 27Sauran ayyukan da Omri ya yi, da kama-karyar da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 28Omri kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Ɗansa Ahab ya gāji sarautarsa.
29A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ahab ɗan Omri ya yi sarautar Isra'ila. Ahab ɗan Omri kuwa ya yi sarautar Isra'ila a Samariya shekara ashirin da biyu. 30Shi kuma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi. 31Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel 'yar Etba'al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba'al, ya yi masa sujada. 32Ya gina wa Ba'al bagade a matsafar Ba'al ɗin, da ya gina a Samariya. 33Ahab kuma ya yi gunkiyan nan Ashtoret. Ahab dai ya yi abin da ya sa Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi. 34A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.
1Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”
2Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya, 3“Ka tashi daga nan ka nufi wajen gabas, ka ɓuya a rafin Kerit, a gabashin Urdun. 4Za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”
5Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa, ya tafi ya zauna a rafin Kerit wanda yake gabashin Urdun. 6Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin. 7Da aka jima sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar.
8Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya. 9“Tashi ka tafi Zarefat ta Sidon, ka zauna a can. Ga shi, na umarci wata mace wadda mijinta ya rasu ta ciyar da kai.”
10Sai ya tashi, ya tafi Zarefat. Sa'ad da ya isa ƙofar garin, sai ga wata wadda mijinta ya rasu tana tattara itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa in sha.” 11Ta juya ta tafi don ta kawo masa ruwan sha ke nan, sai ya sāke kiranta, ya ce, “Ki kuma kawo mini ɗan abinci.”
12Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan gārin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da take cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”
13Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini 'yar waina, ki kawo mini, sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki. 14Gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, “‘Garin da yake a tukunyarki ba zai ƙare ba, man da yake a kurtunki kuma ba zai ƙare ba, sai ran da Ubangiji ya sa aka yi ruwan sama a ƙasar.”
15Ta tafi, ta yi yadda Iliya ya ce, dukansu kuwa suka sami isasshen abinci har kwanaki da yawa. 16Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.
17Bayan wannan sai ɗan macen, wato ɗan uwargijiyar gidan, ya yi ciwo. Ciwon kuwa ya tsananta har ransa ya fita. 18Sai macen ta ce wa Iliya, “Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo don ka nuna wa Allah zunubina, ka zama sanadin mutuwar ɗana?”
19Iliya ya ce mata, “Ki kawo mini ɗanki.” Ya karɓe shi daga wurinta, ya kai shi a bene inda yake kwana. Ya kwantar da shi a gadonsa. 20Sa'an nan ya yi addu'a da gaske ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wa gwauruwan nan da nake zaune wurinta masifa, ka aukar wa ɗanta da ajali?” 21Sa'an nan ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya kuma yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka sa ran yaron nan ya komo cikinsa.” 22Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.
23Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga soro, ya kai shi cikin gida, ya ba uwar. Ya ce mata, “Ki gani, ɗanki yana da rai.”
24Sai macen ta ce wa Iliya, “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuwa yana magana ta wurinka.”
1Bayan 'yan kwanaki, sai Ubangiji ya yi magana da Iliya a shekara ta uku, ya ce, “Tafi, ka nuna kanka ga Ahab, ni kuwa zan sa a yi ruwan sama.” 2Sai Iliya ya tafi. A lokacin kuwa yunwa ta tsananta a Samariya. 3Ahab kuwa ya kira Obadiya, shugaban gidansa. Obadiya kuwa mai tsoron Ubangiji ne sosai. 4A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su. 5Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko'ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.” 6Saboda haka suka rabu biyu don su zagaya. Ahab ya bi waje guda, shi kuma ya bi ɗaya wajen.
7Sa'ad da Obadiya yake tafiya a hanya suka yi kaciɓis da Iliya, Obadiya kuwa ya rabe da shi, sai ya rusuna ya ce, “Shugabana Iliya, kai ne kuwa?”
8Iliya ya amsa masa ya ce, “Ni ne. Tafi, ka faɗa wa shugabanka, sarki, cewa ga ni nan.”
9Obadiya ya ce, “Wane laifi na yi, har da za ka ba da ni a hannun Ahab ya kashe ni? 10Na rantse da Ubangiji Allahnka mai rai, ba al'umma ko mulki da shugabana sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka nan, sai ya sa mulkin ko al'ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba. 11Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa masa, cewa ga ka a nan? 12Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji. 13Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa'ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su. 14Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa wa sarki Ahab, cewa ga ka nan, ai, zai kashe ni.”
15Iliya kuwa ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji Mai Runduna, wanda nake tsaye a gabansa, hakika zan nuna kaina gare shi yau.”
16Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya. 17Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne, wanda kake wahalar da Isra'ila?”
18Iliya kuwa ya amsa ya ce, “Ban wahalar da Isra'ila ba, kai ne da tsohonka, gama kuna ƙin bin umarnan Ubangiji, kuna yi wa Ba'al sujada. 19Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra'ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba'al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtoret kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel yake kula da su.”
20Sai Ahab ya aika wa dukan jama'ar Isra'ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel. 21Iliya kuwa ya zo kusa da jama'a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba'al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba. 22Sa'an nan ya ce wa jama'a, “Ni kaɗai ne annabin Ubangiji da ya ragu, amma annabawan Ba'al ɗari huɗu ne da hamsin. 23To, a ba mu bijimi biyu, su su zaɓi guda su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa a kan itacen wuta, amma kada su kunna masa wuta. Ni kuma zan shirya ɗaya bijimin, in shimfiɗa bisa itacen wuta ba kuwa zan kunna masa wuta ba. 24Za ku yi kira ga sunan Ba'al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.” Jama'a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.
25Sa'an nan Iliya ya ce wa annabawan Ba'al, “Ku zaɓi bijimi guda, ku shirya shi da farko, gama kuna da yawa, sa'an nan ku yi kira ga sunan Ba'al ɗinku, amma fa kada ku kunna wuta.” 26Suka kuwa kama bijimin da aka ba su, suka gyara shi suka yi ta kira ga sunan Ba'al tun da safe, har tsakar ranar suna ta cewa, “Ya Ba'al, ka amsa mana!” Amma ba murya, ba kuwa wanda ya amsa. Suka yi ta tsalle a wajen bagaden da suka gina.
27Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi musu ba'a, ya ce musu, “Ku kira da babbar murya, gama shi wani allah ne, watakila yana tunani ne, ko kuwa ya zagaya ne, ko kuma ya yi tafiya. Watakila kuma yana barci ne, sai a tashe shi.” 28Suka yi ta kira da ƙarfi bisa ga al'adarsu, suna kuma tsattsaga jikunansu da wuƙaƙe, jini yana ta zuba. 29Suka yi ta sambatu har azahar, lokacin ba da hadaya, amma ba muryar kowa, ba amsa, ba wanda ya kula.
30Sa'an nan Iliya ya ce wa jama'a duka su zo kusa da shi. Jama'a duka kuwa suka zo kusa da shi. Sai ya gyara bagaden Ubangiji wanda aka lalatar. 31Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan 'ya'yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra'ila.” 32Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda. 33Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa'an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen. 34Ya kuma sa a kwarara sau na biyu, suka kwarara sau na biyun. Ya ce kuma a kwarara sau na uku, sai suka kwarara sau na ukun. 35Ruwa kuwa ya malale bagaden, ya cika wuriyar da aka haƙa.
36A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka. 37Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”
38Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar. 39Sa'ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka rusuna suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”
40Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba'al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.
41Iliya kuwa ya ce wa Ahab, “Sai ka haura ka ci ka sha, gama akwai motsin sakowar ruwan sama.” 42Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa. 43Sa'an nan ya ce wa baransa, “Ka tafi ka duba wajen teku.” Baran kuwa ya tafi ya duba, ya komo ya ce, “Ban ga kome ba.” Sai ya ce, “Ka yi tafiya kana dubawa, har sau bakwai.”
44A zuwa na bakwai sai ya ce, “Na ga wani ɗan girgije kamar tafin hannu yana tasowa daga teku.” Iliya kuma ya ce, “Tafi, ka faɗa wa Ahab ya shirya karusarsa ya sauka don kada ruwan sama ya hana shi sauka.”
45Jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da gizagizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab kuwa ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel. 46Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.
1Ahab kuwa ya faɗa wa Yezebel dukan abin da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe annabawan Ba'al duka. 2Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.” 3Sai Iliya ya ji tsoro, ya tashi, ya tsere zuwa Biyer-sheba ta Yahuza. Ya bar baransa a can. 4Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
5Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.” 6Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa. 7Mala'ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.” 8Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah. 9A can ya shiga wani kogo domin ya kwana. Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”
10Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”
11Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar. 12Bayan girgizar kuma, sai wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wutar. Bayan wutar sai ƙaramar murya.
13Sa'ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”
14Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”
15Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka juya zuwa jeji kusa da Dimashƙu, idan ka isa can, sai ka zuba wa Hazayel mai, ka keɓe shi, ya sama Sarkin Suriya, 16da Yehu ɗan Nimshi, ka keɓe shi, ya zama Sarkin Isra'ila. Ka kuma zuba wa Elisha, ɗan Shafat na Abel-mehola, mai, ka keɓe shi, ya zama annabi a maimakonka. 17Duk wanda zai tsere wa Hazayel, Yehu zai kashe shi. Wanda kuma ya tsere wa Yehu. Elisha zai kashe shi. 18Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai(7,000) na Isra'ila waɗanda ba su rusuna wa Ba'al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”
19Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa. 20Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.” Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?” 21Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.
1Ben-hadad Sarkin Suriya kuwa ya tara dukan sojojinsa. Sarakuna talatin da biyu kuma suna tare da shi, da dawakai, da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya yaƙi. Ya kuwa yi yaƙi da ita. 2Sai ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce masa, “In ji Ben-hadad, 3“‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, matanka kuma mafi kyau da 'ya'yanka nawa ne!”
4Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya amsa, ya ce, “Ya maigirma sarki, kamar yadda ka faɗa, ni naka ne da dukan abin da nake da shi.”
5Jakadun kuwa suka sāke komawa suka ce wa Ahab, “Ben-hadad ya ce, “‘Na aika maka ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka, da 'ya'yanka. 6Banda haka kuma zan aiko barorina wurinka gobe war haka su bincike gidanka da gidajen fādawanka, su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi da su.”
7Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”
8Dukan dattawan da mutane, suka ce masa, “Kada ka kula, balle ka yarda.”
9Sai ya ce wa jakadun Ben-hadad, “Ku ce wa maigirma, sarki, dukan abin da ya nema a wurina da farko, zan yi, amma wannan na ƙarshe, ban zan iya yi ba.” Jakadun kuwa suka koma da wannan labari. 10Ben-hadad kuwa ya sāke aikawa wurinsa ya ce, “Bari alloli su kashe ni idan ban kai mutane da yawa da za su hallaka Samariya ba.”
11Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa'an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”
12Da Ben-hadad ya ji wannan saƙo sa'ad da yake sha tare da sarakuna a sansani, sai ya ce wa mutanensa, “Kowa ya tsaya a wurinsa.” Sai kowa ya tsaya a wurinsa don yin yaƙi da birnin.
13Ba da jimawa ba, sai ga annabi ya zo wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce, “Ubangiji ya ce, “‘Ka ga wannan babban taron sojoji? Zan ba da su a hannunka yau, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.”
14Ahab ya ce, “Wane ne zai yi jagorar yaƙin?” Annabin ya ce, “Ubangiji ya ce, sojoji matasa, wato na hakiman larduna, za su yi yaƙin.” Sarki ya ce, “Wa zai yi jagorar babbar rundunar?” Annabin ya ce, “Kai ne.”
15Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa'an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra'ila dubu bakwai (7,000).
16Suka tafi da tsakar rana sa'ad da Ben-hadad yake a buge da sha a sansani, shi da sarakuna talatin da biyu waɗanda suka taimake shi. 17Samarin ne suka fara fita. Sai Ben-hadad ya aiki mutane, suka faɗa masa cewa, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”
18Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”
19Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra'ilawa kuma tana biye da su, 20kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai. 21Sarkin Isra'ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.
22Sa'an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra'ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”
23Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka. 24Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu. 25Sa'an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.” Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi hakanan. 26Da shekara ta juyo, sai Ben-hadad ya tara Suriyawa, suka haura zuwa Afek don su yi yaƙi da Isra'ilawa. 27Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.
28Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, “‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama'a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.”
29Suka kafa sansani daura da juna kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin, suka kama yaƙi. Isra'ilawa suka kashe Suriyawa mutum dubu ɗari (100,000) a rana ɗaya. 30Sauran kuwa suka gudu zuwa birnin Afek. Garun birnin kuma ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai (27,000) waɗanda suka ragu. Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga ƙurewar ɗaki, a cikin birnin. 31Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra'ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa'an nan mu tafi wurin Sarkin Isra'ila, watakila zai bar ka da rai.” 32Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra'ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.” Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan'uwana ne.”
33Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan'uwanka, Ben-hadad.” Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.
34Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.” Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.
35Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi. 36Sai annabin ya ce wa wannan aboki, “Da yake ba ka yi biyayya da muryar Ubangiji ba, da tashinka daga wurina, zaki zai kashe ka.” Da ya tashi daga wurinsa, sai zaki ya gamu da shi, ya kashe shi.
37Annabin kuma ya tarar da wani mutum, ya ce masa, “Ina roƙonka ka buge ni.” Mutumin kuwa ya buge shi da ƙarfi ya rotsa shi. 38Sai annabin ya ɓad da kama, ya ɗaure fuskarsa da ƙyalle, ya tafi, ya jira sarki a hanya. 39Sa'ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, “‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.” 40Da na shiga fama da kai da kawowa sai mutumin ya tsere.” Sai Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Haka shari'arka za ta zama, gama kai da kanka ka yanke shari'ar.”
41Annabin ya yi saurim, ya kware ƙyallen a fuskarsa, sa'an nan sarki ya gane, ashe, ɗaya daga cikin annabawa ne. 42Sa'an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, “‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.”
43Sarkin Isra'ila kuwa ya tafi gidansa a Samariya da baƙin ciki.
1Nabot Bayezreyele yana da gonar inabi a Yezreyel kusa da fādar Ahab, Sarkin Samariya. 2Sai Ahab ya yi magana da Nabot ya ce, “Ka ba ni gonar inabinka don in mai da ita lambu, gama gonar tana kusa da gidana, ni kuwa zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta, idan kuma kana so, sai in ba ka tamanin kuɗinta.”
3Amma Nabot ya ce wa Ahab, “Ubangiji ya sawwaƙa in ba ka gādon kakannina.”
4Ahab ya koma gida da baƙin ciki da rai a ɓace saboda abin da Nabot Bayezreyele ya faɗa masa. Ahab ya kwanta a gadonsa, ya mai da fuskarsa bango ya ƙi cin abinci. 5Yezebel, matarsa kuwa ta zo wurinsa, ta ce masa, “Me ya sa ka damu, ka ruɗe haka, har ka ƙi cin abinci?”
6Ya ce mata, “Domin na yi magana da Nabot Bayezreyele, na ce ya sayar mini da gonar inabinsa, idan kuma yana so, sai in ba shi wata gonar inabi a maimakon tasa, amma ya ce ba zai ba ni gonar inabin ba.”
7Yezebel, matarsa, ta ce masa, “Ba kai ne kake mulkin Isra'ila ba? Tashi, ka ci abinci, ka yi farin ciki, zan ba ka gonar inabin Nabot Bayezreyele.”
8Sa'an nan ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da wasiƙun zuwa ga dattawa da fādawan da suke zaune a birnin tare da Nabot. 9Ta rubuta a wasiƙun, “A yi shelar azumi, a sa Nabot a gaban jama'a. 10A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, “‘Nabot ya zagi Allah da sarki.” Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.” 11Mutanen birnin kuwa, dattawa da fādawan da suke zaune a birnin suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika musu. 12Suka kuwa yi shelar azumi, suka sa Nabot a gaban jama'a. 'Yan iska guda biyu suka zauna kusa da shi, suka yi ta zarginsa a gaban jama'a, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” 13Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. 14Sa'an nan suka aika wa Yezebel cewa, “An jajjefi Nabot, ya mutu.”
15Nan da nan da Yezebel ta ji an jajjefi Nabot har ya mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi, ka mallaki gonar inabin Nabot, wadda ya ƙi sayar maka, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu.” 16Da Ahab ya ji Nabo ya mutu, sai ya tashi ya gangara zuwa gonar inabin Nabot Bayezreyele don ya mai da ta tasa. 17Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya Batishbe, 18“Tashi, ka tafi, ka sadu da Ahab, Sarkin Isra'ila, wanda yake a Samariya, ga shi can a gonar inabin Nabot inda ya tafi don ya mallake ta. 19Ka faɗa masa, ni Ubangiji, na ce, “‘Ka kashe mutum, kana kuma ƙwace abin da ya mallaka?” Ka faɗa masa ga abin da na faɗa, “‘A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka.”
20Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?” Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. 21Saboda haka Ubangiji ya ce maka, “‘Ga shi, zan kawo maka masifa, in shafe ka, in datse maka kowane ɗa namiji, bawa ko ɗa, a Isra'ila. 22Zan sa gidanka ya zama kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, da gidan Ba'asha ɗan Ahija saboda ka sa ni in yi fushi, ka kuma sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi.” 23A kan Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, “‘Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel.” 24Duk wanda yake na Ahab da zai mutu a birni karnuka ne za su cinye shi, wanda kuma ya mutu a waje tsuntsaye ne za su cinye shi.”
25Babu wani kamar Ahab da ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Matarsa, Yezebel, ita ce ta zuga shi. 26Ya yi abar banƙyama ƙwarai, ya bi gumaka kamar yadda Amoriyawa suke yi, waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban Isra'ilawa.
27Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.
28Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe ya ce, 29“Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”
(2 Tar 18.1-27)
1Aka yi shekara uku ba a yi yaƙi tsakanin Suriya da Isra'ila ba. 2A shekara ta uku ɗin, sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya ziyarci Sarkin Isra'ila.
3Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa fādawansa, “Ko kun sani Ramot-gileyad tamu ce, ga shi kuwa, mun yi shiru, ba mu ƙwace ta daga hannun Sarkin Suriya ba?” 4Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra'ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.” 5Yehoshafat ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”
6Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?” Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
7Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin da za mu tambaya kuma?”
8Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
9Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya kirawo wani bafāde, ya ce masa, “Maza, ka taho da Mikaiya ɗan Imla.”
10Sarkin Isra'ila da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune a kujerun sarautarsu, saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya. Annabawa kuwa suna annabci a gabansu. 11Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, “‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.” 12Dukan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot, za ka yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
13Bafāden da ya tafi kiran Mikaiya ya ce masa, “Ga shi, maganar sauran annabawan iri ɗaya ce, sun yi maganar alheri ga sarki, sai kai ma ka yi magana irin tasu, ka yi maganar alheri ga sarki.”
14Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”
15Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?” Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
16Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”
17Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, “‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.”
18Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, ba zai yi wani annabcin alheri a kaina ba sai dai na masifa?”
19Makaiya kuwa ya ce, “Ka ji maganar Ubangiji, gama na ga Ubangiji yana zaune a kursiyinsa. Dukan taron mala'ikun Sama suna tsaye a wajen damansa da na hagunsa. 20Ubangiji kuwa ya ce, “‘Wa zai yaudari Ahab, ya tafi ya fāɗa wa Ramot?” Sai wannan ya ce abu kaza, wani kuma ya ce abu kaza, 21har da wani ruhu ya fito ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, “‘Ni zan yaudare shi.” 22Ubangiji ya ce masa, “‘Ta wace hanya?” Sai ruhun ya ce, “‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.” Sai Ubangiji ya ce, “‘Ba shakka za ka yaudare shi, za ka yi nasara, sai ka tafi.”
23Mikaiya ya ce, “Ga abin da ya faru, Ubangiji ya bar annabawanka su faɗa maka ƙarya. Amma Ubangiji kansa ya riga ya zartar maka da masifa.”
24Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”
25Mikaiya ya ce masa, “A ran nan za ka gani, ka kuma gudu ka shiga har ƙurewar ɗaki don ka ɓuya.”
26Sarki Ahab ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki. 27Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”
28Mikaiya kuwa ya ce, “In dai ka komo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana da ni ba.” Ya ƙara da cewa, “Kowa ya kasa kunne ga abin da na faɗa.”
(2 Tar 18.28-34)
29Ahab Sarkin Isra'ila da Sarkin Yahuza suka tafi Ramot-gileyad. 30Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa Sarkin Yahuza, “Zan ɓad da kama in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafinka na sarauta.” Sai Ahab ya ɓad da kama ya tafi wurin yaƙi.
31Sarkin Suriya dai ya riga ya umarci shugabannin karusan yaƙinsa, su talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da kowa, kome matsayinsa, sai dai Ahab kaɗai.”
32Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, sai suka ce, “Lalle shi ne Ahab.” Sai suka juya don su yi yaƙi da shi. Yehoshafat kuwa ya yi ihu. 33Da shugabannin karusan yaƙi suke gane ba Ahab ba ne, sai suka rabu da shi.
34Wani sojan Suriya kuwa ya yi sa'a, ya shilla kibiya kawai, sai ta sami Ahab, ta kafar sulkensa. Saboda haka ya ce wa mai korar karusarsa, “Ka juya, ka fitar da ni daga fagen fama gama an yi mini rauni.”
35A ran nan yaƙi ya yi tsanani. Aka tallafi Ahab a cikin karusarsa a gaban Suriyawa. Da maraice ya mutu. Jinin raunin da aka yi masa ya zuba a cikin karusar. 36A wajen faɗuwar rana aka yi wa sojoji shela aka ce, “Kowa ya koma garinsu da ƙasarsu.”
37Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, aka binne shi. 38Suka wanke karusarsa a tafkin Samariya. Karnuka suka lashe jininsa, karuwai kuma suka yi wanka a tafkin kamar yadda Ubangiji ya faɗa.
39Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 40Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.
(2 Tar 20.31—21.1)
41Yehoshafat ɗan Asa ya ci sarautar Yahuza a shekara ta huɗu ta sarautar Ahab, Sarkin Isra'ila. 42Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba 'yar Shilhi. 43Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan. 44Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra'ila amana.
45Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 46Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.
47A lokacin babu sarki a Edom sai wakili. 48Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber. 49Sa'an nan Ahaziya, ɗan Ahab, ya ce wa Yehoshafat. “Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage.” Amma Yehoshafat bai yarda ba.
50Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.
51Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu. 52Ya yi zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi halin tsohonsa da na tsohuwarsa, da na Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. 53Ya bauta wa gunkin nan Ba'al ya yi masa sujada. Ya kuma sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi, gama ya bi halin tsohonsa.