1 Peter
1Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya, 2su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.
3Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu, 4mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama, 5wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani. 6A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri. 7Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu. 8Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato, 9kuna samun ceton rayukanku, ta wurin sakamakon bangaskiyarku.
10Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto, 11suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa'ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye. 12An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.
13Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu. 14Ku yi zaman 'ya'ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha'awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku. 15Amma da yake wanda ya kira ku mai tsarki ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka a cikin dukan al'amuranku. 16Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”
17Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa. 18Domin kun sani an fanshe ku ne daga al'adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba, 19sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo. 20An rigyasaninsa a kan haka, tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe. 21To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
22Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya. 23Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya. 24Domin “Duk ɗan adam kamar ciyawa yake, Duk darajarsa kamar furen ciyawa take, Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,
25Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,” Ita ce maganar bishara da aka yi muku.
1Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha'inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe. 2Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto, 3in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.
4Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah. 5Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu, 6Domin a tabbace yake a Nassi cewa, “Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke, Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”
7A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to, “Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”
8Da kuma, “Dutsen sa tuntuɓe, Da fā na sa faɗuwa.” Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.
9Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa. 10Dā ba jama'a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama'ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.
11Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku. 12Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.
13Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba, 14ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a'aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki. 15Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari. 16Ku yi zaman 'yanci, sai dai kada ku fake a bayan 'yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah. 17Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.
18Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai. 19Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba. 20To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.
21Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa. 22Bai yaɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba. 23Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari'ar adalci. 24Shi kansa zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku. 25A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.
1Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba, 2don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku. 3Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa, 4sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah. 5Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu, 6kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma 'ya'yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.
7Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa'a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu'a tare.
8Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u. 9Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka. 10Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, Sai ya kame bakinsa daga ɓarna, Ya kuma hana shi maganar yaudara.
11Ya rabu da mugunta, ya kama nagarta, Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.
12Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci, Yana kuma sauraron roƙonsu. Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”
13To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da yake nagari? 14Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da yake daidai, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu. 15Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali'u da bangirma. 16Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata. 17Zai fi kyau a sha wuya ga yin abin da yake nagari, in haka nufin Allah ne, da a sha don yin abin da ba daidai ba. 18Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu. 19Da ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku shela, 20wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa. 21Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu, 22wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala'iku da manyan mala'iku da masu iko suna binsa.
1Tun da yake Almasihu ya sha wuya a jiki dominmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra'ayi. Ai, duk wanda ya sha wuya a jiki, ya daina aikata zunubi ke nan, 2domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah. 3Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al'ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama. 4Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa, kuna aikata masha'a irin tasu, har suna zaginku. 5Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da yake a shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari'a. 6Shi ya sa aka yi bishara har ga matattu ma, waɗanda ko da yake an yi musu hukunci a cikin jiki kamar mutane, su samu su rayu a ruhu kamar Allah.
7Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a. 8Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa. 9Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba. 10Duk baiwar da mutum ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan'uwansa, a kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne. 11Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
12Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku. 13Amma, muddin kuna tarayya da Almasihu a wajen shan wuyarsa, sai ku yi farin ciki, domin sa'ad da aka bayyana ɗaukakarsa, ku yi farin ciki da murna matuƙa. 14Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku. 15Sai dai kada shan wuyar ko ɗaya daga cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi. 16Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗankaka Allah saboda wannan suna. 17Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba>
18“In adali da ƙyar ya kuɓuta, Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”
19Saboda haka, sai duk masu shan wuya bisa ga nufin Allah su danƙa ransu ga Mahalicci mai aminci suna aikata abin da yake daidai.
1Don haka, ku dattawan ikilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikilisiya, ɗan'uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi, 2ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma. 3Kada ku nuna wa waɗanda ke hannunka iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan. 4Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa. 5Hakanan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
6Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗankakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari. 7Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku. 8Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame. 9Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san 'yan'uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya. 10Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku. 11Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
12Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi. 13Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus. 14Ku gai da juna da sumbar ƙauna. Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.