1 Thessalonians

WASIƘAR BULUS TA FARKO ZUWA GA
1 Tasalonikawa

1

Gaisuwa

1Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da salama su tabbata a gare ku.

Bangaskiyar Tasalonikawa da irin Zamansu

2A kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku a cikin addu'armu, 3ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu. 4Domin mun sani, 'yan'uwa, ƙaunatattu na Allah, shi ya zaɓe ku, 5domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana, 6har kuka zama masu koyi da mu, da kuma Ubangiji, kuka kuma karɓi Maganar Allah game da farin cikin da Ruhu Mai Tsarki yake sawa, ko da yake ta jawo muku tsananin wahala. 7Ku ma har kuka zama abin koyi ga dukan masu ba da gaskiya a ƙasar Makidoniya da ta Akaya. 8Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko'ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba. 9Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya, 10ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato Yesu, mai kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.

2

Hidimar Bulus a Tasalonika

1Ai, ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, ziyartarku da muka yi, ba a banza take ba. 2Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama. 3Ai, gargaɗin da muke yi muku babu bauɗewa ko munafunci a ciki, balle yaudara, 4sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu. 5Yadda kuka sani, ba mu taɓa yin daɗin baki ko kwaɗayi ba. Allah kuwa shi ne shaida. 6Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga waɗansu, ko da yake da muna so, da mun mori ikon nan namu na manzannin Almasihu. 7Amma mun nuna taushin hali a cikinku, kamar yadda mai goyo ku kula da goyonta. 8Saboda kuma muna Kaunarku ƙwarai da gaske ne shi ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.

9Ya ku 'yan'uwa, kuna iya tunawa da wahala da famar da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku, duk sa'ad da muke yi muku bisharar Allah. 10Ku shaidu ne, haka kuma Allah, game da irin halin da muka nuna muku, ku masu ba da gaskiya, wato halin tsarki da na adalci da na rashin aibu. 11Domin kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da 'ya'yansa ne, muna ta'azantar da ku, muna kuma ƙarfafa muku umarnin, cewa 12ku yi zaman da ya cancanci bautar Allah, wanda yake kiranku ga mulkinsa da ɗaukakarsa.

13Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya. 14'Yan'uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa, 15waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu, ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuma da dukan mutane, 16suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.

Nufin Bulus ya sāke Ziyartar Ikilisiya

17Ya ku 'yan'uwa, ko da yake mun yi kewarku saboda an raba mu a ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatanmu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki. 18Mun dai yi niyyar zuwa wurinku, ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma Shaidan ya hana. 19Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba? 20Ai, ku ne abin taƙamarmu, da abin farin cikinmu.

3

1Saboda haka, da muka kasa daurewa, sai muka ga ya kyautu a bar mu a Atina mu kaɗai, 2muka kuma aiki Timoti ɗan'uwanmu, bawan Allah kuma na al'amarin bisharar Almasihu, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku a kan al'amarin bangaskiyarku, 3don kada kowa ya raurawa a cikin tsananin wahalar nan. Ai, ku kanku kun sani an nufe mu da haka ne. 4Domin dā ma sa'ad da muke tare, mun gaya muku tun da wuri, cewa za mu sha wahala. Haka kuwa ya auku, kamar yadda kuka sani. 5Saboda haka, ni ma da na kasa daurewa, sai na aika in sami labarin bangaskiyarku, da fatan kada ya zamana mai ruɗin nan ya riga ya ruɗe ku, famarmu kuma yă zama banza.

6Amma ga shi, a yanzu da Timoti ya dawo daga wurinku, ya yi mana albishir a kan bangaskiyarku da ƙaunarku, da kuma yadda kuke tunawa da mu da alheri a koyaushe, har kuna begen ganinmu, kamar yadda mu ma muke yi. 7Saboda haka 'yan'uwa, cikin dukan wahala da ƙuncin da muka sha, an sanyaya mana zuciya a game da ku, albarkacin bangaskiyarku. 8A yanzu kam a raye muke, in dai kun tsaya ga Ubangiji. 9Wace irin godiya za mu yi wa Allah saboda ku, a kan matuƙar farin cikin da muke yi a gaban Allahnmu ta dalilinku! 10Dare da rana muna nacin addu'a ƙwarai mu sami ganinku ido da ido, mu kuma cikasa abin da ya gaza wajen bangaskiyarku.

11Muna fata dai Allahnmu, ubanmu, shi kansa, da kuma Ubangijinmu Yesu, ya kai mu gare ku. 12Ku kuma, Ubangiji ya sa ku ƙaru, ku kuma yalwata da ƙaunar juna da dukan mutane, kamar yadda muke yi muku, 13har ya tsai da zukatanku ku zama marasa abin zargi cikin tsarki a gaban Allahnmu, Ubanmu, a ranar komowar Ubangijinmu Yesu, tare da dukan tsarkakansa.

4

Zaman da ya Dace a Gaban Allah

1Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske, 2domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu. 3Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci, 4kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci, 5ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba. 6A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri. 7Ai, ba a zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne. 8Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da ke ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

9A game da ƙaunar 'yan'uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10Hakika kuwa kuna ƙaunar dukan 'yan'uwa a duk ƙasar Makidoniya. Sai dai muna muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske, 11kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha'anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da hannunku, kamar yadda muka umarce ku, 12domin ku zama masu mutunci ga waɗanda ba masu bi ba, kada kuma ku rataya a jikin kowa.

Matattu da Waɗanda suke a Raye a Zuwan Ubangiji

13Amma 'yan'uwa, ba mu so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran suke yi, marasa bege. 14Tun da muka gaskata Yesu ya mutu, ya kuwa tashi, haka kuma albarkacin Yesu, Allah zai kawo waɗanda suka yi barci su zo tare da shi. 15Muna kuwa shaida muku bisa ga faɗar Ubangiji, cewa mu da muka wanzu, muke kuma a raye har ya zuwa komowar Ubangiji ko kaɗan ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba, 16domin Ubangiji kansa ma zai sauko daga Sama, da kira mai ƙarfi, da muryar babban mala'ika, da kuma busar ƙahon Allah. Waɗanda suka mutu suna na Almasihu, su ne za fara tashi, 17sa'an nan sai mu da muka wanzu, muke a raye, za a ɗauke mu tare da su ta cikin gajimare, mu sadu da Ubangiji a sararin sama, sai kuma kullum mu kasance tare da Ubangiji. 18Saboda haka, sai ku yi wa juna ta'aziyya da wannan magana.

5

Ku Zauna a Faɗake don Zuwan Ubangiji

1Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba. 2Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare. 3Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira. 4Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, 'yan'uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo. 5Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne. 6Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa. 7Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu. 8Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu. 9Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, 10wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi. 11Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.

Gargaɗi da kuma Gaisuwa

12Amma muna roƙonku 'yan'uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi. 13Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 14Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa. 15Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane. 16Ku riƙa yin farin ciki a kullum. 17Ku riƙa yin addu'a ba fāsawa. 18Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu. 19Kada ku danne maganar Ruhu. 20Kada ku raina annabci, 21sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da yake nagari kankan. 22Ku yi nesa da kowace irin mugunta.

23Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 24Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.

25Ya ku 'yan'uwa, ku yi mana addu'a.

26Ku gai da dukkan 'yan'uwa da tsattsarkar sumba.

27Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan 'yan'uwa wasiƙar nan.

28Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.