1 Timothy
1Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu, 2zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya. Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.
3Kamar yadda na roƙe ka, ka dakata a Afisa sa'ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi waɗansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam, 4kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al'amuran Allah da bangaskiya. 5Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya. 6Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza. 7Suna burin zama masanan Attaura, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle matsalar da suke taƙamar haƙiƙicewa a kai.
8To, mun san Shari'a aba ce mai kyau, in mutum ya yi aiki da ita yadda ya wajaba, 9yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, 10da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan, 11bisa ga bishara mai daraja ta Allah abar yabo, wadda aka danƙa mini.
12Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijinmu, wanda ya ƙarfafa ni, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa, 13ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya. 14Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu. 15Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu. 16Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami. 17Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.
18Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau, 19kana riƙe da bangaskiya da lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunna ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20Cikinsu har da Himinayas da Askandari, waɗanda na miƙa wa Shaiɗan, don su horo su yin sāɓo.
1Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu'a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane, 2da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu, 4wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya. 5Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum, 6wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa. 7Don haka ne aka sa ni mai wa'azi, da manzo kuma (gasikya nake faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa al'ummai al'amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
8Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu'a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba. 9Mata kuma su riƙa sa tufafin da suka dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu'ulu'u, ko tufafi masu tsada ba, 10sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu. 11Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya. 12Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru. 13Ai, Adamu aka fara halitta, sa'an nan Hawwa'u. 14Ba kuma Adamu aka yaudara ba, amma matar ce aka yaudara, har ta keta umarni. 15Duk da haka kuwa, ta wurin haifar 'ya'ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da zama a tsarkake, da kuma kamunkai.
1Maganar nan tabbatacciya ce, cewa duk mai burin aikin kula da ikilisiya, yana burin yin aiki mai kyau ke nan. 2To, lalle ne mai kula da ikilisiya yă zama marar abin zargi, ya zama mai mace ɗaya, mai kamunkai, natsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, gwanin koyarwa kuma. 3Ba mashayi ba, ba mai saurin dūka ba, amma salihi, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba. 4Lalle ne yă iya sarrafa iyalinsa da kyau, yana kuma kula da 'ya'yansa, su yi biyayya da matuƙar ladabi. 5Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikilisiyar Allah? 6Lalle ne kuma, kada ya zama sabon tuba, don kada ya daga kai ya burmu a cikin hukuncin da aka yi wa Iblis. 7Banda haka kuma, lalle ne ya zama mai mutunci ga waɗanda ba su a cikinmu, don kada ya zama abin zargi, ya faɗa a cikin tarkon Iblis.
8Haka kuma masu hidimar ikilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba. 9Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta. 10Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar. 11Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu amince ta kowace hanya. 12Masu hidima kuma su zama masu mata ɗaya ɗaya, masu sarrafa 'ya'yansu da sauran iyalinsu da kyau. 13Masu hidimar da suke aikinsu sosai, suna samar wa kansu kyakkyawan suna, da kuma ƙaƙƙarfar amincewa ga bangaskiyarsu ga Almasihu Yesu.
14Ina sa zuciya in zo a wurinka ba da daɗewa ba, amma ina rubuto maka waɗannan abubuwa. 15Don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta. 16Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.
1To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu, 2ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas. 3Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya, 5gama an tsarkake shi ta wurin Maganar Allah da addu'a
6In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau. 7Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah. 8Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba. 9Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum. 10Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
11Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyar da su. 12Kada ka yarda kowa ya raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka. 13Kafin in zo, ka lazamci karanta wa mutane Littattafai, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa. 14Kada ka shagala da baiwar da aka yi maka, wadda aka ba ka ta wurin annabci, sa'ad da dattawan ikilisiya suka ɗora maka hannu. 15Ka himmantu ga waɗannan abubuwa, ka kuma lazamce su ƙwarai, don kowa yă ga ci gaban da kake yi. 16Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.
1Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka roƙe shi kamar mahaifinka. Samari kuma ka ɗauke su kamar 'yan'uwanka, 2tsofaffi mata kuma kamar uwayenka, 'yan mata kuwa kamar 'yan'uwanka, da matuƙar tsarkaka.
3Ka girmama gwauraye mata, waɗanda ba sa da mataimaka. 4In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah. 5Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu'a dare da rana. 6Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye. 7Ka umarce su a game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. 8Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.
9Kada a lasafta gwauruwa a cikin gwauraye, sai dai ta kai shekara sittin, ba ta yi aure fiye da ɗaya ba, 10wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari. 11Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa'adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure, 12hukunci yā kama su ke nan, tun da yake sun ta da wa'adinsu na farko. 13Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba. 14Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su yi tafiyar da al'amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu. 15Gama waɗansu ma har sun bauɗe, sun bi Shaiɗan. 16Duk mace mai bi, da take da dangi gwauraye mata, sai ta taimake su, kada a nauwaita wa ikilisiya, don ikilisiyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.
17Dattawan ikilisiya da suke a riƙe da al'amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa'azi da koyarwa ba. 18Domin Nassi ya ce, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi sa'ad da yake sussuka.” Ya kuma ce, “Ma'aikaci ya cancanci ladarsa.” 19Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikilisiya, sai dai da shaidu biyu ko uku. 20Masu yin zunubi kuwa, sai ka tsawata musu a gaban dukkan jama'a, don saura su tsorata. 21Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala'iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra. 22Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanku a tsarkake.
23A nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dai ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.
24Zunuban waɗansu mutane a fili suke, tun ba a kai gaban shari'a ba. Zunuban waɗansu kuwa, sai daga baya suke bayyana. 25Haka kuma, kyawawan ayyukan waɗansu a fili suke, waɗanda ba haka suke ba, ba za su tabbata a ɓoye ba.
1Duk ɗaukacin masu igiyar bauta a wuyansu, su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci a girmama su matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwar nan. 2Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su 'yan'uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su.
Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu. 3Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba, 4girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san kome ba, yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda suke jawo hassada, da husuma, da yanke, da mugayen zace-zace, 5da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu. 6Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa. 7Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba. 8To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.
9Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha'awace-sha'awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.
11Amma, ya kai, bawan Allah, ka guje wa waɗannan abubuwa, ka dimanci aikin adalci, da bin Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimri, da kuma tawali'u. 12Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa. 13Na gama ka da Allah mai raya kome, na kuma gama ka da Almasihu Yesu, wanda ya yi shaida, kyakkyawar shaidar nan, a gaban Buntus Bilatus, 14ka bi umarninsa, ba tare da wani aibi ko zargi ba, har ya zuwa bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu, 15wannan kuwa makaɗaicin mamallaki, abin yabo, Sarkin sarakuna. Ubangijin iyayengiji zai bayyana shi a lokacinsa. 16Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.
17Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa. 18Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri. 19Ta haka suke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don nan gaba, domin su riƙi rai wanda yake na hakika.
20Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi. 21Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya. Alheri yă tabbata a gare ku.