2 Chronicles

LITTAFI NA BIYU NA
Tarihi

1

Addu'ar Sulemanu ta Neman Hikima

(1 Sar 3.3-15)

1Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.

2Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanni. 3Sa'an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can. 4Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima. 5Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama'a suka yi sujada ga Ubangiji a can. 6Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.

7A wannan dare Allah ya bayyana ga Sulemanu, ya ce masa, “Ka roƙe ni abin da kake so in ba ka.”

8Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa. 9Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama'a mai yawa kamar turɓaya. 10Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”

11Allah kuwa ya amsa wa Sulemanu ya ce, “Tun da kana da irin wannan tunani a zuciyarka, ba ka kuwa roƙi dukiya, ko wadata, ko girma, ko ran maƙiyanka ba, ba ka kuma roƙi tsawon rai ba, amma ka roƙa wa kanka hikima da sani domin ka iya yin mulkin jama'ata wadda na naɗa ka sarki a kanta, 12to, na ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka dukiya, da wadata, da girma, waɗanda ba wani sarkin da ya taɓa samun irinsu, ba kuma wani sarkin da zai taɓa samun irinsu.”

13Daga nan sai Sulemanu ya taso daga masujadar da take Gibeyon inda alfarwa ta sujada take, ya zo Urushalima inda ya zauna yana mulkin Isra'ila.

Sulemanu ya Tara Dawakai da Karusai

(1 Sar 10.26-29; 2 Tar 9.25-28)

14Sai Sulemanu ya tara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), sai ya sa su a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da shi. 15Sarki ya yawaita azurfa da zinariya har suka zama kamar duwatsu a Urushalima. Haka kuma ya yi da itatuwan al'ul, suka yawaita kamar itatuwan ɓaure a fadama. 16Wakilan sarki suka ɗauki nauyin shigo da dawakai daga Masar da Kilikiya, 17suka kuma shigo da karusai daga Masar. Suka riƙa sayar wa sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa karusai a kan azurfa ɗari shida shida, kowane doki kuma a kan azurfa ɗari da hamsin.

2

Shirye-shiryen Ginin Haikali

(1 Sar 5.1-18; 7.13-14)

1Sai Sulemanu ya yi niyya a ransa zai gina Haikali saboda sunan Ubangiji, ya kuma gina wa kansa fāda. 2Don haka, sai ya sa mutane dubu saba'in (70,000) don ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) su haƙo duwatsu a tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuma su ne shugabanni.

3Sulemanu fa ya aika wurin Hiram Sarkin Taya ya ce, “Yadda ka yi wa tsohona Dawuda, wato ka aiko masa da itatuwan al'ul domin ya gina gida inda zai zauna, ni ma ina so ka yi mini haka. 4Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila. 5Haikalin nan kuwa da nake niyyar ginawa babba ne, gama Allahnmu ya fi dukan alloli. 6Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa? 7Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo. 8Ka kuma aiko mini da itacen al'ul, da na fir, da katakon algum daga Lebanon, gama na sani barorinka sun san yadda ake yanyanka katakan Lebanon. Barorina za su yi aiki tare da barorinka, 9domin su shirya mini katako mai yawa. Gama Haikalin da zan gina mai girma ne ƙwarai, mai banmamaki. 10Zan ba barorinka masu aikin katako misalin mudu dubu ashirin (20,000) ta sussukakkiyar alkama, da mudu dubu ashirin (20,000) ta sha'ir, da misalin garwar ruwan inabi dubu ashirin (20,000), da ta mai dubu ashirin (20,000).”

11Hiram, Sarkin Taya kuwa, ya ba Sulemanu amsar takardarsa, ya ce, “Saboda Ubangiji yana ƙaunar jama'arsa, ya naɗa ka sarkinsu.” 12Hiram ya ci gaba da cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya yi sama da ƙasa, ya ba sarki Dawuda ɗa mai hikima, mai hankali, mai ganewa, wanda zai gina Haikali dominsa, ya gina fāda kuma domin kansa. 13Yanzu zan aika maka da Huram mutum mai gwaninta, mai ganewa. 14Shi ɗan wata mace mutuniyar Dan, mahaifinsa kuwa mutumin Taya ne. Huram ya gwanance a kan aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da dutse, da itace, da kuma shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau. Shi kuma zai iya sassaƙa kowane irin abu da aka sa shi ya sassaƙa, tare da gwanayenka, da na tsohonka, ubangidana, wato Dawuda. 15To, yanzu, sai ka aiko wa barorinka da alkama, da sha'ir, da mai, da ruwan inabi kamar yadda ka alkawarta. 16Mu kuwa za mu yanko maka dukan katakan da kake bukata a Lebanon, mu kawo maka su a kan gadajen fito ta hanyar teku, zuwa Yafa, domin ka kwashe ka kai Urushalima.”

An Fara Ginin Haikali

17Sarki Sulemanu ya ƙidaya dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila, kamar yadda tsohonsa Dawuda ya yi. Yawan baƙin da aka samu sun kai dubu ɗari da dubu hamsin da uku, da ɗari shida (153,600). 18Sai ya zaɓi mutum dubu saba'in (70,000) daga cikinsu su zama masu ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) kuma don su riƙa haƙo duwatsu daga tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuwa don su zama shugabanni.

3

Sulemanu ya Gina Ɗakin Sujada domin Ubangiji

(1 Sar 6.1-38)

1Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse. 2Ya fara ginin a ran biyu ga watan biyu a shekara ta huɗu ta sarautarsa. 3Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin. 4Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa'an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa. 5Ya jera itatuwan fir a cikin babban ɗakin, sa'an nan ya shafe su da zinariya tsantsa, ya kuma zana siffofin itatuwan dabino da na sarƙoƙi. 6Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim. 7Ya kuma shafe Haikalin duk da ginshiƙansa, da bakin ƙofofinsa, da bangayensa, da ƙyamarensa da zinariya, ya kuma zana siffofin kerubobi a jikin bangaye. 8Sai ya gina Wuri Mafi Tsarki. Tsawonsa daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu ashirin. Ya shafe shi da zinariya tsantsa, wadda jimillar nauyinta ta yi talanti ɗari shida. 9Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya tsantsa.

10Ya sassaƙa siffofin kerubobi biyu na itace, a Wuri Mafi Tsarki, ya shafe su da Zinariya. 11Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin. 12Guda kerub ɗin kuma, fiffikensa guda ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken shi ma ya taɓo fiffiken kerub na farko. 13Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin. 14Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa'an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.

Kayan Haikali

(1 Sar 7.15-51)

15Ya kuma yi ginshiƙai biyu domin ƙofar Haikalin, tsayinsu kamu talatin da biyar ne, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne. 16Ya yi sarƙoƙi, ya rataya wa ginshiƙan, ya kuma yi siffofin rumman guda ɗari, ya maƙala wa sarƙoƙin. 17Sai ya kafa ginshiƙin a ƙofar Haikali, ɗaya a wajen kudu, ɗaya kuma a wajen arewa. Ya sa wa na wajen kudu suna Yakin, na wajen arewa kuwa Bo'aza.

4

1Ya yi bagade na tagulla, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin, tsayinsa kuwa kamu goma. 2Ya yi kwatarniya kewayayyiya ta zubi, kamu goma daga gāɓa zuwa gāɓa, tsayinsa kuwa kamu biyar ne, da'irarsa kuwa kamu talatin. 3A ƙashiyar kwatarniya akwai siffofin bijimai kamu goma kewaye da ita har jeji biyu. Gaba ɗaya aka yi zubinsu da na kwatarniya. 4Kwatarniya tana bisa bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar gabas, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. Kwatarniya tana bisa bijiman, gindin ko wannensu yana daga ciki. 5Kaurin kwatarniya taƙi guda ne, bakinsa kamar bakin finjali ne, kamar kuma siffar furen bi-rana. Kwatarniya kuwa tana iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa. 6Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne.

7Sa'an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu. 8Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.

9Sa'an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla. 10Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin. 11-16Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah: ginshiƙi biyu dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan dakali goma daro goma kwatarniya bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin haikalin Ubangiji

17Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu. 18Haka Sulemanu ya yi kayayyakin nan da yawa ƙwarai, har ba a iya lissafin yawan nauyin tagullar da aka yi amfani da ita ba. 19-22Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su: bagade na zinariya tebur don ajiye gurasar ajiyewa alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara furanni fitilu arautaki hantsuka daruna cokula farantan wuta ƙofofi na can ciki ƙofofi na waje

5

1Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa'an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah.

Sulemanu ya Kawo Akwatin Alkawari a Haikali

(1 Sar 8.1-11)

2Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona. 3Sai dukan mutanen Isra'ila suka hallara a gaban sarki, a wurin bikin, a wata na bakwai ke nan. 4Sa'an nan dukan dattawan Isra'ila suka zo, Lawiyawa kuwa suka ɗauko akwatin. 5Suka kuma kawo akwatin, da alfarwa ta taruwa, da dukan tsarkakakkun kayayyakin da suke cikin alfarwar. Lawiyawa da firistoci ne suka kawo su. 6Sarki Sulemanu da dukan taron mutanen Isra'ila da suka hallara a gaban akwatin suka yi ta miƙa hadayun tumaki da bijimai masu yawan gaske, har ba su ƙidayuwa. 7Sa'an nan firistoci suka shigar da akwatin alkawari na Ubangiji a wurinsa, wato a Wuri Mafi Tsarki na cikin Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi. 8Gama kerubobin sun miƙe fikafikansu bisa a daidai wurin da akwatin yake, wato kerubobin sun yi wa akwatin da sandunansa kamar rumfa ke nan. 9Sandunan akwatin dogaye ne ƙwarai, har ana ganin kawunansu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Amma daga waje ba a iya ganinsu. Suna a wannan wuri har yau. 10Ba kome cikin akwatin sai alluna biyu waɗanda Musa ya sa a ciki sa'ad da suke a Horeb. A Horeb ne Ubangiji ya ƙulla alkawarin da mutanen Isra'ila, sa'ad da suka fito daga Masar.

Ɗaukakar Ubangiji

11Firistocin suka fito daga Wuri Mai Tsarki na Haikalin Allah, gama dukan firistocin da suka hallara, sun tsarkake kansu ba tare da kula da bambancin matsayi ba. 12Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su. 13Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa'ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Gama shi nagari ne, Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.” Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije, 14har ma firistoci ba su iya tsayawa su ci gaba da hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Allah.

6

Maganar Sulemanu ga Mutane

(1 Sar 8.12-21)

1Sulemanu ya ce, “Ubangiji ya riga ya faɗa zai zauna a cikin girgije mai duhu.

2Yanzu kuwa na gina maka ƙasaitaccen ɗaki, Na gina maka wurin da za ka zauna har abada.”

3Sa'an nan sarki ya juya, ya dudduba, ya sa wa dukan taron jama'ar Isra'ila albarka, dukansu kuwa suka tsaya. 4Sai ya ce, “Ubangiji Maɗaukaki ne, Allah na Isra'ila wanda ya yi wa tsohona Dawuda alkawari, ga shi kuwa ya cika shi, gama ya ce, 5“‘Tun daga ranar da na fito da jama'ata daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin dukan kabilan Isra'ila ba, inda zan gina wurin da sunana zai kasance, ban kuma zaɓi wani mutum da zai shugabanci jama'ata Isra'ila ba. 6Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.”

7“Ya zama kuwa tsohona Dawuda ya yi niyyar gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila. 8Amma Ubangiji ya ce wa ubana Dawuda, ya kyauta, tun da yake ya yi niyya a zuciyarsa zai gina ɗaki saboda sunansa. 9Duk da haka, ba shi zai gina Haikalin ba, ɗansa wanda za a haifa masa, shi ne zai gina Haikalin domin sunansa.

10“Yanzu fa Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na gāji matsayin ubana Dawuda, na kuwa hau gadon sarautar Isra'ila, yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuwa gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra'ila. 11A can na ajiye akwati inda aka sa alkawarin da Ubangiji ya yi wa jama'ar Isra'ila.”

Addu'ar Sulemanu

(1 Sar 8.22-53)

12Sulemanu ya miƙe a gaban bagaden Ubangiji a idon dukan taron Isra'ila ya ɗaga hannuwansa. 13Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama, 14ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a duniya, wanda yake cika alkawari, kana nuna madawwamiyar ƙauna ga bayinka masu tafiya a gabanka da zuciya ɗaya. 15Kai ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka, tsohona Dawuda. Abin da ka faɗa ka kuma aikata. 16Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, “‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.” 17Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.

18“Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina. 19Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka. 20Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri, 21ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama'ar Isra'ila, sa'ad da suke addu'a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa'ad da ka ji, ka gafarta.

22“Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali, 23sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.

24“Idan abokan gāba sun kori jama'arka, wato Isra'ila, saboda laifin da suka yi maka, sa'an nan suka juyo suka shaida sunanka, suka yi addu'a, suka yi roƙo a gabanka a wannan Haikali, 25sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin jama'arka Isra'ila, ka komo da su ƙasar da ka ba su, su da kakanninsu.

26“Sa'ad da aka kulle sammai, ba ruwan sama saboda sun yi maka zunubi, sa'an nan suka fuskanci wurin nan suka yi addu'a, suka shaida sunanka, suka juyo suka daina zunubinsu a sa'ad da ka hukunta su, 27sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin bayinka, wato jama'arka Isra'ila, lokacin da ka koya musu kyakkyawar hanya da za su bi. Sai ka sa a yi ruwa a ƙasarka, wadda ka ba jama'arka gādo.

28“Idan ana yunwa a ƙasar, ko annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fārā, ko gamzari, ko da maƙiyansu za su kewaye biranensu da yaƙi, ko kowace irin annoba, da kowace irin cuta da take akwai, 29kowace irin addu'a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama'ar Isra'ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali, 30sa'an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al'amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane, 31don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.

32“Haka kuma baƙo wanda ba cikin jama'arka Isra'ila yake ba, idan ya taho daga wata ƙasa mai nisa saboda girman sunanka da ƙarfin ikonka, in ya zo ya yi sujada, yana fuskantar Haikalin nan, 33ka ji daga Sama wurin zamanka, ka kuwa aikata bisa ga dukan irin roƙon da baƙon ya yi gare ka. Domin ta haka sauran al'umman duniya za su san sunanka, su kuma yi tsoronka, yadda jama'arka Isra'ila suke yi, za su kuma sani cewa wannan Haikali da na gina, ana kiransa da sunanka.

34“Sa'ad da jama'arka za su fita don yin yaƙi da magabtansu, duk dai ko ta ina ne za ka aike su, in sun yi addu'a gare ka, suna fuskantar wannan birni wanda kai ka zaɓa, da Haikalin nan da na gina saboda sunanka, 35sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, ka biya muradinsu.

36“Sa'ad da suka yi maka zunubi (gama ba wani ɗan adam da ba ya yin zunubi), ka kuwa yi fushi da su, har ka bashe su a hannun magabtansu, magabtansu suka kakkama su suka kai wata ƙasa ta nesa ko ta kusa, 37duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, “‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,” 38in sun tuba da zuciya ɗaya, a ƙasar da aka kai su, in sun fuskanci ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, suka yi addu'a, suna kuma fuskantar Haikalin nan da na gina domin sunanka, 39sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu, daga wurin zamanka a Sama, ka sa su yi nasara, ka biya musu muradinsu, ka gafarta wa jama'arka waɗanda suka yi maka zunubi.

40“Yanzu fa, ya Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kasa kunnuwanka, ka saurari addu'ar da ake yi a wannan wuri. 41Yanzu fa, ya Ubangiji ka tashi ka tafi wurin hutawarka, kai da akwatin ikonka. Ya Ubangiji Allah ka yi wa firistocinka sutura da cetonka, adalanka kuma su yi farin ciki da nagartarka. 42Ya Ubangiji Allah kada ka juya baya ga keɓaɓɓenka, ka tuna da madawwamiyar ƙaunarka ga bawanka Dawuda.”

7

Ƙeɓewar Haikali

(1 Sar 8.62-66)

1Sa'ad da Sulemanu ya gama yin addu'arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin. 2Firistoci ba su iya shiga Haikalin Ubangiji ba saboda darajar Ubangiji ta cika Haikalin. 3Sa'ad da dukan Isra'ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa. 4Sa'an nan sarki da dukan jama'a suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji. 5Sarki Sulemanu kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000), da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki tare da dukan jama'a suka keɓe Haikalin Allah. 6Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa'an nan sai dukan Isra'ilawa su miƙe tsaye.

7Sa'an nan Sulemanu ya tsarkake tsakiyar filin da yake a gaban Haikalin Ubangiji, gama a wurin ne ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayu domin salama, saboda bagaden tagulla wanda Sulemanu ya yi bai iya ɗaukar hadayu domin ƙonawa, da ta gari, da ta kitse ba.

8A wannan lokaci, Sulemanu ya yi biki a wurin har kwana bakwai, tare da dukan Isra'ilawa, da waɗanda suka zo tun daga ƙofar Hamat, har zuwa rafin Masar, taron kuwa mai girma ne ƙwarai. 9A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin. 10A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama'a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama'arsa Isra'ila.

Ubangiji ya Sāke Bayyana ga Sulemanu

(1 Sar 9.1-9)

11Haka kuwa Sulemanu ya gama Haikalin Ubangiji da fādar sarki. Ya fa yi nasara cikin dukan irin abin da ya yi niyya game da Haikalin Ubangiji da fādarsa. 12Sa'an nan Ubangiji ya bayyana ga Sulemanu da dare, ya ce masa, “Na ji addu'arka, na kuwa zaɓi wannan wuri domin kaina, domin ya zama Haikalin miƙa hadaya. 13Har idan na kulle sammai yadda ba za a yi ruwan sama ba, ko kuma in umarci fara su cinye ƙasar, ko kuwa in aiko da annoba cikin jama'ata, 14in jama'ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali'u, su yi addu'a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa'an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu. 15Yanzu idanuna za su kasance a buɗe, kunnuwana kuma za su saurari addu'ar da za a yi a wannan wuri. 16Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin. 17Amma kai, idan za ka yi zamanka a gabana kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da na umarce ka, ka kiyaye dokokina da farillaina, 18to, zan kafa gadon sarautarka, yadda na alkawarta wa tsohonka Dawuda, cewa ba za a rasa mutumin da zai yi mulkin Isra'ila ba. 19Amma idan ka juya, ka bar dokokina da umarnaina waɗanda na sa a gabanka, har ka shiga bautar gumaka kana musu sujada, 20to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al'umma.

21“Haikali kuwa, wanda aka ɗaukaka, duk mai wucewa zai yi mamaki ya ce, “‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa wannan ƙasa da wannan Haikali haka?”

22“Sa'an nan kuma za su ce, “‘Saboda sun rabu da Ubangiji, Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar, amma suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, saboda haka ne ya aukar musu da duk wannan bala'i.”

8

Waɗansu Ayyukan Sulemanu

(1 Sar 9.10-28)

1A ƙarshen shekara ashirin waɗanda Sulemanu ya yi yana gina Haikalin Ubangiji da fādarsa, 2sa'an nan ya sāke giggina biranen da Hiram ya ba shi, ya zaunar da Isra'ilawa a cikinsu. 3Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi. 4Sa'an nan ya gina Tadmor a jeji, a Hamat kuwa ya gina biranen ajiya. 5Ya kuma gina Bet-horon ta kan tudu da Bet-horon ta kwari, birane masu kagara kuwa ya gina musu garu, da ƙofofi, da ƙyamare, 6da kuma Ba'alat da dukan biranen ajiya waɗanda yake da su, da birane don karusansa, da birane don mahayan dawakansa, ya gina dukan abin da yake bukata a Urushalima, da Lebanon, da a dukan ƙasashen da suke cikin mulkinsa. 7Dukan jama'ar da suka ragu a ƙasar, wato Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba, 8daga cikin zuriyarsu waɗanda suka ragu a ƙasar a bayansu, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba, su ne Sulemanu ya tilasta su biya gandu, haka kuwa suke har wa yau. 9Amma Sulemanu bai bautar da kowa daga cikin mutanen Isra'ila ba, su ne mayaƙansa, da shugabannin yaƙi, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa. 10Manyan shugabanni na sarki Sulemanu, mutum ɗari biyu ne da hamsin waɗanda suke iko da jama'a.

11Sulemanu kuwa ya kawo 'yar Fir'auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra'ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.” 12Sai Sulemanu ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji a gaban shirayi. 13Sulemanu ya yi bisa ga abin da aka wajabta a yi kowace rana, bisa ga umarnin Musa a miƙa hadayu domin ranakun Asabar, da na amaryar wata, da kuma lokatan idodi uku na shekara, wato idin abinci marar yisti, da idin makonni, da na bukkoki. 14Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta. 15Firistoci da Lawiyawa kuwa, ba su kauce wa umarnin sarki a kan kowane al'amari ba, ko a kan sha'anin taskoki.

16Haka Sulemanu ya kammala aikinsa, da aka aza harsashin gina Haikalin Ubangiji, har zuwa ran da aka gama. Haka kuwa aka kammala aikin Haikalin Ubangiji.

17Sai Sulemanu ya tafi Eziyon-geber da Elat da suke a gaɓar teku a ƙasar Edom. 18Hiram kuwa ya aika wa Sulemanu jiragen ruwa tare da barori waɗanda suka saba da sha'ani a teku. Sai barorin tare da barorin Sulemanu, suka tafi Ofir, suka ɗauko zinariya talanti ɗari huɗu da hamsin, suka kawo wa sarki Sulemanu.

9

Sarauniyar Sheba ta Ziyarci Sulemanu

(1 Sar 10.1-13)

1Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta. 2Sulemanu kuwa ya amsa dukan tambayoyin da ta yi masa, ba wani abu da yake ɓoye ga Sulemanu wanda ya kāsa bayyana mata. 3Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina, 4da irin abincin da yake kan tebur ɗinsa da irin zaman manyan mutanensa, da barorin da suke yi masa hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da irin tufafinsu, ta kuma ga hadayun ƙonawa da yake miƙawa a Haikalin Ubangiji, sai ta ji ba ta da sauran kuzari.

5Sarauniya ta ce wa sarkin, “Ashe, gaskiya ce, labarinka da na ji a ƙasata a kan al'amuranka da hikimarka. 6Amma dā ban gaskata labarinsu ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabin yawan hikimarka ma ba a faɗa mini ba. Ashe, duk labarin da aka faɗa mini, ka zarce haka ƙwarai. 7Masu farin ciki ne mutanenka, da barorinka waɗanda suke yi maka hidima kullayaumin, gama kullum suna jin hikimarka. 8Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”

9Sa'an nan kuma ta ba sarki zinariya talanti ɗari da ashirin, da kayan yaji masu yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Irin kayan yajin da Sarauniyar Sheba ta ba sarki Sulemanu ba irinsa.

10Bayan haka kuma barorin Hiram tare da barorin Sulemanu waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itatuwan algum da duwatsu masu daraja. 11Da itatuwan algum ɗin, sarki ya yi matakan Haikalin Ubangiji da na fādar sarki, ya kuma yi garayu, da molaye saboda mawaƙa. Ba a taɓa ganin irinsu a ƙasar Yahuza ba.

12Sarki Sulemanu kuwa ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ranta yake bukata, da iyakar abin da take so, banda abin da ta kawo wa sarki. Sa'an nan ta koma ƙasarta, ita da barorinta.

Dukiyar Sulemanu da Shahararsa

(1 Sar 10.14-29; 2 Tar 1.14-17)

13Yawan zinariya da Sulemanu yake samu a shekara guda, talanti ɗari shida da sittin da shida, 14banda wadda 'yan kasuwa da fatake sukan kawo masa. Dukan sarakunan Arabiya da masu mulkin ƙasar kuma sun kawo wa Sulemanu zinariya da azurfa. 15Sai Sulemanu sarki ya ƙera manyan garkuwoyi guda ɗari biyu na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari shida ne na zinariya. 16Ya kuma ƙera garkuwa ɗari uku ƙanana na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari uku ne. Sarki fa ya ajiye su a gidan da aka gina da katakai daga Lebanon.

17Sarki ya yi babban gadon sarauta na hauren giwa, ya dalaye shi da zinariya. 18Gadon sarautar yana da matakai da 'yar kujerar zinariya ta ɗora ƙafa haɗe da gadon. A kowane gefen gadon an yi wurin ɗora hannu, akwai kuma siffar zaki a tsaye kusa da kowane wurin ɗora hannun. 19Akwai kuma siffofin zaki goma sha biyu, zaki biyu a kowane mataki, gefe da gefe. Ba ma sarautar da aka taɓa yi irin wannan.

20Dukan tasoshi da finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya tsantsa aka yi su. Hakanan kuma dukan tasoshi da finjalai da suke cikin gidan da aka gina da katakai daga Lebanon, na zinariya ne tsantsa. Ba a mai da azurfa a bakin kome ba a zamanin Sulemanu. 21Sau ɗaya a shekaru uku, sarki yakan aika da jiragen ruwa zuwa Tarshish tare da barorin Hiram, su kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.

22Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima. 23Sarakunan duniya duka suna nema su sadu da Sulemanu, don su ji irin hikimar da Allah ya ba shi. 24Kowannensu yakan kawo masa kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai, masu yawan gaske a kowace shekara.

25Sulemanu kuwa yana da ɗakunan dawakai da na karusai dubu huɗu (4,000), yana da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000) waɗanda suke zaune a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da sarki. 26Ya mallaki dukan sarakuna tun daga Yufiretis, har zuwa ƙasar Filistiyawa har kuma zuwa kan iyakar Masar. 27Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar duwatsu a Urushalima, ya kuma sa itatuwan al'ul su yalwata kamar itatuwan ɓaure a Shefela. 28Dawakan Sulemanu, sayo su aka yi daga Masar, da dukan sauran ƙasashe.

Rasuwar Sulemanu

(1 Sar 11.41-43)

29Sauran ayyukan Sulemanu daga farko har ƙarshe an rubuta su a tarihin annabi Natan. An kuma rubuta su a annabcin Ahaija Bashilone, da kuma a wahayin Iddo maigani, game da Yerobowam ɗan Nebat. 30A Urushalima, Sulemanu ya yi shekara arba'in yana mulkin dukan Isra'ila. 31Sulemanu ya rasu aka binne shi tare da kakanninsa a birnin tsohonsa Dawuda, Rehobowam ɗansa shi ya gāje shi.

10

Kabilan Arewa sun yi Tawaye

(1 Sar 12.1-20)

1Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra'ilawa sun tafi don su naɗa shi sarki. 2Da Yerobowam ɗan Nabat, ya ji wannan labari (gama a Masar yake sa'ad da ya guje wa sarki Sulemanu), Yerobowam kuwa ya komo daga Masar. 3Aka aika a kira shi, sai Yerobowam da dukan Isra'ilawa, suka je wurin Rehobowam suka ce, 4“Tsohonka ya tsananta mana, yanzu sai ka sawwaƙa mana irin tsananin da muka sha daga wurin tsohonka, da irin tilastawar da ya yi mana, sa'an nan sai mu bauta maka.”

5Rehobowam kuwa ya ce musu, “Ku komo bayan kwana uku.” Sai jama'a suka tafi.

6Rehobowam ya nemi shawara a gun dattawan da suke tare da tsohonsa Sulemanu, sa'ad da yake da rai, ya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa jama'ar nan?”

7Su kuwa suka ce masa, “Idan za ka nuna wa jama'ar nan alheri, ka daɗaɗa musu rai, ka kuma yi musu magana mai daɗi, za su zama barorinka har abada.”

8Amma ya ƙi yarda da shawarar da dattawan suka ba shi, ya nemi shawara daga wurin matasa waɗanda suka girma tare, masu yi masa hidima. 9Ya ce musu, “Wace irin shawara za ku bayar wadda za mu amsa wa jama'an nan da suka ce mini, “‘Ka sawwaƙa mana wahalar da muka sha daga wurin tsohonka?”

10Sai matasa waɗanda suka girma tare da shi, suka ce masa, “Ga abin da za ka faɗa wa jama'an nan da suka ce maka, tsohonka ya tsananta musu, yanzu sai ka sawwaƙa musu, “‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun ubana kauri! 11Ubana ya tsananta muku ƙwarai, amma ni zan tsananta muku fiye da shi, ubana ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.”

12Sai Yerobowam tare da dukan jama'a suka koma wurin Rehobowam a rana ta uku, kamar yadda sarki ya faɗa, “Bayan kwana uku ku komo.” 13Sarki Rehobowam ya amsa musu da kakkausan harshe, gama bai karɓi shawarar dattawan ba. 14Sarki Rehobowam ya yi aiki da shawarar da matasa suka ba shi, ya ce, “Ubana ya tsananta muku fiye da shi, ya hore ku da bulala, amma ni, da kunama zan hore ku.” 15Sarki bai kasa kunne ga jama'ar ba, gama wannan al'amari, Allah ne ya aukar da shi, domin ya cika maganar da ya faɗa wa Yerobowam ɗan Nebat, ta bakin Ahaija Bashilone.

16Da Isra'ilawa duka suka ga sarki bai saurare su ba, jama'ar kuwa suka amsa wa sarkin, suka ce, “Wane rabo muke da shi a wurin Dawuda? Ba mu da gādo a wurin ɗan Yesse. Kowa ya tafi alfarwarsa, ya ku Isra'ilawa. Ku bar Rehobowam ya lura da gidansa.” Isra'ilawa duka kowa ya tafi alfarwarsa. 17Amma Rehobowam ya ci gaba da mulki bisa Isra'ilawan da suke a biranen Yahuza.

18Sai sarki Rehobowam ya aiki Adoniram shugaban aikin dole, jama'ar Isra'ila kuwa suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sai sarki Rehobowam ya gaggauta ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.

19Tun daga wannan lokaci kuwa har zuwa yau, Isra'ilawa suka tayar wa gidan Dawuda.

11

Annabcin Shemaiya

(1 Sar 12.21-24)

1Sa'ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama'ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra'ila, su komo wa Rehobowam da mulki. 2Sai Ubangiji ya yi magana da Shemaiya, mutumin Allah, ya ce, 3“Ka faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan Isra'ilawa da suke a Yahuza da Biliyaminu, ka ce, 4“‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, kada ku yi yaƙi da 'yan'uwanku, kowa ya komo alfarwarsa, gama wannan al'amari daga gare ni yake.” Suka kuwa ji maganar Ubangiji, suka koma, ba su tafi yaƙi da Yerobowam ba.

Rehobowam ya Arzuta

5Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuwa gina birane masu kagara a Yehuza. 6Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa, 7da Bet-zur, da Soko, da Adullam, 8da Gat, da Maresha, da Zif, 9da Adorayim, da Lakish, da Azeka, 10da Zora, da Ayalon, da Hebron. Waɗannan su ne birane masu kagara a Yahuza da Biliyaminu. 11Ya kuma ƙara ƙarfin kagaran, ya sa sarakunan yaƙi a cikinsu. Ya tara abinci, da mai, da ruwan inabi a cikinsu. 12Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.

Firistoci da Lawiyawa sun Zo Yahuza

13Firistoci da Lawiyawa da suke a dukan Isra'ila kuwa suka komo gare shi daga dukan wuraren da suke. 14Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da 'ya'yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji. 15Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi. 16Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, daga kowace kabilar Isra'ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu. 17Sai suka ƙarfafa mulkin Yahuza, suka tsare mutuncin Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku. Suka yi shekara uku suna tafiya a tafarkin Sulemanu.

Iyalin Rehobowam

18Rehobowam kuwa ya auri Mahalat 'yar Yeremot ɗan Dawuda, wadda Abihail 'yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa. 19Mahalat ta haifa masa 'ya'ya maza, su ne Yewush, da Shemariya, da Zaham. 20Banda Mahalat kuma, sai ya auri Ma'aka 'yar Absalom, wadda ta haifa masa Abaija, da Attai, da Ziza, da kuma Shelomit. 21Rehobowam ya fi ƙaunar Ma'aka, 'yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. 'Ya'yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, 'ya'ya mata kuwa sittin. 22Sai Rehobowam ya zaɓi Abaija ɗan Ma'aka, ya zama shugaban 'yan'uwansa, gama nufinsa ya zama sarki. 23Sai ya yi hikima ya rarraba waɗansu 'ya'yansa maza ko'ina cikin gundumomin ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, a dukan birane masu kagara, ya tanada musu abinci a yalwace. Ya kuma samo musu mata masu yawan gaske.

12

Shishak ya Kai wa Yahuza Yaƙi

(1 Sar 14.21-31)

1Da mulkin Rehobowam ya kahu, ya kuma yi ƙarfi, sai Rehobowam da dukan Isra'ilawa tare da shi suka bar bin shari'ar Ubangiji. 2A shekara ta biyar ta mulkin sarki Rehobowam, Isra'ilawa ba su bi Ubangiji da aminci ba, saboda haka Shishak, Sarkin Masar, ya hauro don ya yi yaƙi da Urushalima. 3Aka faɗo masa da karusai dubu da ɗari biyu (1,200), da mahayan dawakai mutum dubu sittin (60,000). Mutanen da suka taho tare da sarki Shishak daga Masar, ba a san adadinsu ba, akwai Libiyawa, da Sukkimiyawa, da kuma Habashawa. 4Ya ci birane masu kagara na Yahuza, har ya dangana da Urushalima.

5Sai annabi Shemaiya ya zo wurin Rehobowam da sarakunan Yahuza waɗanda suka tattaru a Urushalima saboda Shishak, ya ce musu, “Ubangiji ya ce kun yashe shi, don haka shi ma ya bashe ku a hannun Shishak.”

6Sai sarakunan Isra'ila tare da sarki Rehobowam, suka ƙasƙantar da kansu, suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”

7Da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai ya yi magana da Shemaiya cewa, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba. 8Duk da haka fa, za su zama bayin Shishak don su san bautata dabam take da wadda ake yi wa mulkokin ƙasashe.”

9Sai Shishak Sarkin Masar ya zo ya fāɗa wa Urushalima da yaƙi, ya kuwa kwashe dukiyoyin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na fādar sarki, ya yi musu ƙaƙaf. Ya kuma kwashe garkuwoyi na zinariya, waɗanda Sulemanu ya yi. 10Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara, masu tsaron gidan sarki. 11A duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su kawo su, daga baya kuma su maishe su a ɗakin matsaran. 12Da sarki Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, sai fushin Ubangiji ya huce, don haka bai sa aka hallaka shi ƙaƙaf ba, har ma halin zama a ƙasar Yahuza ya yi kyau.

Mulkin Rehobowam a Taƙaice

13Sarki Rehobowam kuwa ya kafa mulkinsa sosai a Urushalima, yana da shekara arba'in da ɗaya da haihuwa ya ci sarauta, ya yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra'ila domin ya sa sunansa a wurin. Sunan tsohuwar Rehobowam Na'ama, Ba'ammoniya. 14Amma ya aikata mugunta domin bai nemi Ubangiji a zuciyarsa ba.

15Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam. 16Rehobowam fa ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Abaija ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

13

Sarki Abaija na Yahuza

(1 Sar 15.1-8)

1A shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yerobowam, sai Abaija ya ci sarautar Yahuza. 2Ya yi mulki shekara uku a Urushalima, sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Uriyel na Gibeya. Sai yaƙi ya ɓarke a tsakanin Abaija da Yerobowam. 3Abaija ya tafi da rundunar jarumawansa, dubu ɗari huɗu (400,000) zaɓaɓɓun mutane. Yerobowam shi kuma ya jā dāgar yaƙi don ya kara da Abaija, yana da mutum dubu ɗari takwas (800,000), zaɓaɓɓun mayaƙa ƙarfafa.

4Sai Abaija ya hau kan Dutsen Zemarayim, wanda yake a ƙasar Ifraimu mai tuddai, ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ya Yerobowam da dukanku Isra'ilawa. 5Ashe, ba ku sani ba, Ubangiji Allah na Isra'ila, ya ba da sarautar Isra'ila ga Dawuda, da 'ya'yansa maza har abada, ta wurin alkawarin gishiri? 6Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, baran Sulemanu ɗan Dawuda, ya tashi, ya yi wa ɗan ubangidansa tawaye, 7waɗansu marasa amfani, 'yan iska, suka taru suka goyi bayansa, suka raina Rehobowam ɗan Sulemanu, saboda a lokacin shi yaro ne, ba shi da ƙarfin zuciya, bai iya tsayayya da su ba. 8Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan mayaƙan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku. 9Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, 'ya'yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al'umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.

10“Amma a gare mu, Ubangiji shi ne Allahnmu, ba mu kuwa rabu da shi ba. Muna da firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, masu yi wa Ubangiji hidima, da Lawiyawa masu yi musu hidima. 11Safe da yamma suna miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa, da turare mai daɗin ƙanshi, sukan ajiye gurasar ajiyewa a kan tebur ɗin zinariya tsantsa, sukan lura da alkukin zinariya, da kuma fitilunsa kowane maraice, gama muna riƙe da umarnin Ubangiji Allahnmu, amma ku kun rabu da shi. 12Ga shi kuwa, Allah yana tare da mu, shi ne shugabanmu, firistocinsa kuwa suna da ƙahon da akan busa lokacin yaƙi, don su busa kira na yin yaƙi. Ya ku Isra'ilawa, kada ku yi yaƙi da Ubangiji, Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”

13Ashe, Yerobowam ya riga ya sa 'yan kwanto, su yi musu yankan baya. Ƙungiyar mayaƙan Isra'ila tana fuskantar ta Yahuza, 'yan kwanto kuma suna bayansu. 14Da Yahuza suka duba, sai ga yaƙi a gabansu da bayansu. Sai suka yi kuka ga Ubangiji, firistoci kuma suka busa ƙaho. 15Mutanen Yahuza suka yi kūwwar yaƙi. Da suka yi kuwwar yaƙin sai Ubangiji ya sa Yerobowam da dukan jama'ar Isra'ila su gudu a gaban Abaija da Yahuza. 16Mutanen Isra'ila kuwa suka gudu a gaban Yahuza, Allah ya bashe su a hannunsa. 17Abaija fa, da jama'arsa suka karkashe su, mugun kisa. Mutum dubu ɗari biyar (500,000) zaɓaɓɓu na Isra'ila, aka karkashe. 18Haka kuwa aka ci nasara a kan mutanen Isra'ila a wannan lokaci. Mutanen Yahuza sun yi rinjaye saboda sun dogara ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.

19Abaija ya runtumi Yerobowam, ya ƙwace masa waɗansu birane, wato Betel tare da ƙauyukanta, da Yeshana tare da ƙauyukanta, da kuma Efron tare da ƙauyukanta. 20Mulkin Yerobowam bai ƙara farfaɗowa a zamanin Abaija ba. Ubangiji kuma ya bugi Yerobowam, ya mutu.

21Amma Abaija ya ƙasaita, ya auro mata goma sha huɗu, ya haifi 'ya'ya maza ashirin da biyu, da 'ya'ya mata goma sha shida. 22Sauran ayyukan Abaija, da al'amuransa, da jawabansa, an rubuta su a littafin tarihin annabi Iddo.

14

Sarki Asa na Yahuza

(1 Sar 15.9-12)

1Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa. 2Asa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa. 3Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot. 4Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni. 5Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagaden ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa. 6Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama. 7Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta. 8Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.

9Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su. 10Don haka sai Asa ya fito ya gamu da shi, suka kuwa jā dāga a kwarin Zefata a Maresha. 11Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”

12Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu. 13Sai Asa da jama'ar da suke tare da shi, suka runtume su har zuwa Gerar. Habashawa suka fāɗi duka, ko ɗaya, ba wanda ya ragu da rai, gama an ragargaza su a gaban Ubangiji da gaban sojojin. Mutane suka kwashe ganima mai yawa gaske. 14Suka hallaka dukan birane da suke kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka washe dukan biranen, gama biranen suna cike da ganima. 15Suka kware alfarwan masu kiwon dabbobi, suka kora tumaki, da raƙuma masu yawan gaske. Sa'an nan suka komo Urushalima.

15

Gyare-gyaren da Asa ya Yi

(1 Sar 15.13-15)

1Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Azariya ɗan Oded, 2sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku. 3Isra'ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari'a. 4Amma lokacin da suke shan wahala suka juyo ga Ubangiji Allah na Isra'ila, suka neme shi, suka same shi. 5A waɗancan lokatai, ba salama ga mai fita ko ga mai shiga, gama babban hargitsi ya wahalar da dukan mazaunan ƙasashe. 6An kacancana su, al'umma tana gāba da al'umma, birni kuma gāba da birni, gama Allah ya yi ta wahalshe su da kowace irin wahala. 7Amma ku sai ku yi ƙarfin hali, kada ku firgita, gama za a ba ku ladan aikinku.”

8Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.

9Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra'ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa'ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. 10Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta sarautar Asa. 11A ran nan suka miƙa wa Ubangiji hadayun bijimai ɗari bakwai, da tumaki dubu bakwai (7,000) daga cikin ganimar da suka kwaso. 12Sai suka ƙulla alkawari, cewa za su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu da dukan zuciyarsu da ransu. 13Duk wanda kuma bai nemi Ubangiji, Allah na Isra'ila ba, za a kashe shi, ko yaro ko babba, ko mace ko namiji. 14Sai suka rantse wa Ubangiji da murya mai ƙarfi, suna sowa, suna busa kakaki da ƙaho. 15Dukan Yahuza ta yi murna saboda rantsuwar, gama da zuciya ɗaya suka rantse, suka kuwa neme shi da iyakar aniya, sun kuwa same shi. Don haka Allah ya hutasshe su a kowane al'amari.

16Asa kuma ya tuɓe tsohuwarsa, Ma'aka, daga matsayinta na sarauniya don ta ƙera wata siffa mai banƙyama ta Ashtoret. Sai Asa ya sare siffar nan, ya niƙe ta, ya ƙone a rafin Kidron. 17Amma ba a kawar da masujadan da suke Isra'ila ba, duk da haka zuciyar Asa sarai take, ba wani aibi duk kwanakinsa. 18Sai ya shigar da sadakar da shi da tsohonsa suka keɓe don Haikalin Ubangiji, wato azurfa, da zinariya, da kwanoni da tasoshi, da finjalai iri iri. 19Ba a kuma ƙara yin wani yaƙi ba har shekara ta talatin da biyar ta mulkinsa Asa.

16

Asa ya Haɗa Kai da Ben-hadad

(1 Sar 15.16-22)

1A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, sai Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya haura ya fāɗa wa Yahuza da yaƙi, ya gina Rama don ya hana kowa fita, ko shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza. 2Sa'an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa, 3“Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da take tsakaninka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, don ya janye ya rabu da ni.”

4Ben-hadad kuwa ya kasa kunne ga sarki Asa, ya aika da shugabannin rundunan sojojinsa suka yi yaƙi da biranen Isra'ila. Suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan biranen ajiya na Naftali. 5Da Ba'asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi. 6Sa'an nan sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuza, suka kwashe duwatsun da katakan da Ba'asha yake gina Rama da su, ya gina Geba da Mizfa da su.

Annabi Hanani

7A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka. 8Ai, Habashawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da karusai da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, sai ya bashe su a hannunka. 9Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko'ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al'amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.” 10Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.

Ƙarshen Mulkin Asa

(1 Sar 15.23-24)

11Ayyukan Asa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila. 12A shekara ta talatin da tara ta mulkin Asa, sai wani ciwo ya kama shi a ƙafa. Ciwon kuwa ya tsananta ƙwarai, duk da haka Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba, sai na magori. 13Asa fa ya rasu bayan shekara biyu da ciwon, a shekara ta arba'in da ɗaya ta mulkinsa. 14Aka binne shi a kabarin da shi da kansa ya haƙa a birnin Dawuda. Aka sa shi a makara wadda aka cika da kayan ƙanshi da na turare yadda gwanayen aikin turare suka shirya, suka hura babbar wuta don su darajanta shi.

17

Mulkin Yehoshafat ya Kahu

1Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra'ila. 2Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi. 3Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat saboda ya bi halin tsohonsa da ya yi da fari, bai kuwa nemi Ba'al ba. 4Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba. 5Saboda haka ne Ubangiji ya ba shi ikon riƙon wannan mulki. Yahuza duka kuwa ta kawo wa Yehoshafat haraji, ya kuwa zama riƙaƙƙen mai dukiya, wanda kuma ake girmamawa. 6Zuciyarsa ta ƙarfafa cikin al'amuran Ubangiji. Ya kawar da masujadai, da Ashtarot daga ƙasar Yahuza.

7A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya aika da ma'aikatansa, su Ben-hail, da Obadiya, da Zakariya, da Netanel, da kuma Mikaiya don su yi koyarwa a biranen Yahuza. 8Tare da su kuma akwai Lawiyawa, da Shemaiya, da Netaniya, da Zabadiya, da Asahel, da Shemiramot, da Jonatan, da Adonaija, da Tobiya, da Tob-adonaija, tare da waɗannan Lawiyawa akwai firistoci, Elishama da Yehoram. 9Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari'ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko'ina a biranen Yahuza suka koyar da jama'a.

Gawurtar Yehoshafat

10Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashen da suke kewaye da Yahuza, har ba su iya fāɗa wa Yehoshafat da yaƙi ba. 11Sai waɗansu daga cikin Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa domin haraji. Larabawa ma suka kawo masa raguna dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700), da bunsurai dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700). 12Yehoshafat ya daɗa ƙasaita, ya giggina kagarai, da biranen ajiya a Yahuza. 13Yana kuwa da manya manyan wuraren ajiya a biranen Yahuza. Yana kuma da gwarzayen sojoji masu yawa a Urushalima. 14Ga jimillar sojojin bisa ga gidajen kakanninsu. Na Yahuza mai shugabannin dubu dubu, shugaba Adana yana shugabancin sojoji dubu ɗari uku (300,000) gwarzaye. 15Mai bi masa, sai shugaba Yehohanan yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000). 16Mai biye da Yehohanan kuma shi ne shugaba Amasiya, ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa don bauta wa Ubangiji, shi kuma yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000) gwarzaye. 17Na Biliyaminu kuma sarkin yaƙi shi ne Eliyada, gwarzo ne, yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000), 'yan baka da garkuwa. 18Na biye da Eliyada kuma shi ne shugaba Yehozabad wanda yake da sojoji dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) shirayayyu don gabza yaƙi. 19Waɗannan suke yi wa sarki hidima, banda waɗanda sarki ya sa a birane masu kagara ko'ina a Yahuza.

18

Annabi Mikaiya ya Gargaɗi Ahab

(1 Sar 22.1-28)

1Yehoshafat ya arzuta, ya kuma sami ɗaukaka sai ya yi ma'amala da Ahab ta wurin aurayya. 2Bayan 'yan shekaru sai ya kai wa Ahab ziyara a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki masu yawan gaske, da bijimai da yawa, domin Yehoshafat da mutanen da suke tare da shi. Ahab ya rinjaye shi don su fāɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi. 3Sai Ahab, Sarkin Isra'ila, ya ce wa Yehoshafat, Sarkin Yahuza, “Za ka tafi tare da ni zuwa Ramot-gileyad?” Sai ya amsa, ya ce, “Ni ma kamarka ne, jama'ata kuma kamar jama'arka ce, za mu je yaƙin tare da kai.” 4Yehoshafat kuma ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Sai ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”

5Ahab kuwa ya tattara annabawa, mutum ɗari huɗu, ya ce musu, “Mu je mu faɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi, ko in haƙura?” Sai suka ce, “Ka tafi, gama Allah zai ba da ita a hannun sarki.”

6Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji a nan wanda za mu tambaye shi kuma?”

7Sai Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Akwai sauran mutum guda wanda za mu iya neman nufin Ubangiji daga gare shi, shi ne Mikaiya, ɗan Imla, amma na ƙi shi saboda ba ya yin annabcin kirki a kaina, sai dai na rashin alheri kullum.” Amma Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”

8Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya kira wani jarumi ya ce masa, “Maza ka kawo Mikaiya ɗan Imla.”

9A sa'an nan Sarkin Isra'ila, da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune kowa a gadon sarautarsa, kowane ya caɓa ado, suna kuwa zaune a filin da yake ƙofar Samariya. Dukan annabawa kuwa suna ta yin annabci a gabansu. 10Sai Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, “‘Da waɗannan za ka sassoki Suriyawa har su hallaka!” 11Dukan annabawa kuma suka yi annabci, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot-gileyad ka ci nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannun sarki.”

12Jarumin fa da ya je ya kira Mikaiya ɗin, ya ce masa, “Ka kula fa, dukan maganganun da annabawa suke yi, sun yi wa sarki daɗi. Don haka kai ma ka yi maganar da za ta gamshi sarki kamar yadda suka yi.”

13Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji abin da Allahna ya faɗa mini, shi zan faɗa.”

14Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?” Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”

15Amma sarki ya ce masa, “Har sau nawa zan rantsar da kai don kada ka faɗa mini kome, sai gaskiya da sunan Ubangiji?”

16Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra'ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, “‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.”

17Sarkin Isra'ila fa ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, cewa ba zai yi annabcin alheri game da ni ba, sai na rashin alheri?”

18Sai Mikaiya ya ce, “Ji maganar Ubangiji, na ga Ubangiji yana zaune a bisa kursiyinsa, dukan rundunan sama suna tsaye dama da shi da hagu da shi. 19Sai Ubangiji ya ce, “‘Wa zai ruɗi Ahab, Sarkin Isra'ila, don ya haura zuwa Ramot-gileyad ya fāɗi?” Sai wannan ya faɗi abu kaza, wancan kuma ya faɗi abu kaza. 20Sai wani ruhu ya zo ya tsaya a gaban Ubangiji, ya ce, “‘Ni zan ruɗe shi.” Sai Ubangiji ya ce masa, “‘Ta ƙaƙa?” 21Sai ya ce, “‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.” Sa'an nan Ubangiji ya ce, “‘To, za ka ruɗe shi har ka yi nasara. Je ka, ka yi hakanan.”

22“Saboda haka Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan annabawanka, gama Ubangiji ya faɗa, masifa za ta same ka.”

23Sai Zadakiya ɗan Kena'ana, ya matso ya mari Mikaiya a kumatu ya ce, “Ta wace hanya ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai.”

24Mikaiya kuwa ya ce, “Za ka gani a ranar da ka shiga ƙuryar ɗaki na can ciki don ɓuya.”

25Sai Sarkin Isra'ila ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku komar da shi wurin Amon mai mulkin birnin, da yarima Yowash. 26Ku ce, “‘Sarki ya ce ku sa wannan mutum a kurkuku, ku ciyar da shi da ɗan abinci da ruwa kaɗan har in komo lafiya.”

27Sai Mikaiya ya ce, “Idan har ka komo lafiya, wato Ubangiji bai yi magana da ni ba ke nan.” Sai ya ce, “Ku ji, ya ku jama'a duka.”

Mutuwar Ahab

(1 Sar 22.29-35)

28Sarkin Isra'ila fa, da Yehoshafat Sarkin Yahuza, suka haura zuwa Ramot-gileyad. 29Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama, in shiga yaƙi, amma kai, sai ka sa rigunanka.” Sarkin Isra'ila kuwa ya ɓad da kama, suka shiga yaƙi.

30Sarkin Suriya ya umarci shugabannin karusansa, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da yaro ko babba, sai dai da Sarkin Isra'ila, shi kaɗai.”

31Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, suka ce, “Wannan ne Sarkin Isra'ila,” sai suka juya suka yi yaƙi da shi. Amma Yehoshafat ya yi kururuwa, Ubangiji Allah ya kuɓutar da shi, Allah kuwa ya kawar da su daga gare shi. 32Da shugabannin karusai suka ga, ashe, ba Sarkin Isra'ila ba ne, sai suka daina binsa suka juyo. 33Amma wani mutum ya harba kibiya haka kawai, ya sami Sarkin Isra'ila a mahaɗin kafaɗa. Sai sarkin ya ce wa wanda yake korar karusarsa, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin, gama an yi mini rauni.” 34Ran nan yaƙin ya tsananta, Sarkin Isra'ila kuma ya jingina a cikin karusarsa, yana fuskantar Suriyawa har maraice, rana na fāɗuwa yana rasuwa.

19

Annabi Yehu ya Tsauta wa Yehoshafat

1Yehoshafat Sarkin Yahuza ya koma gidansa a Urushalima lafiya. 2Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka. 3Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da gumakan Ashtarot daga ƙasar, ka sa zuciyarka ga neman Allah.”

Yehoshafat ya Zaɓi Alƙalai

4Yehoshafat ya yi zamansa a Urushalima, ya sāke shiga jama'a, tun daga Biyer-sheba har zuwa ƙasar tuddai ta Ifraimu, ya komar da su zuwa wurin Ubangiji, Allah na kakanninsu. 5Sai ya naɗa alƙalai a ƙasar, a dukan biranen Yahuza masu kagara, birni birni. 6Sai ya ce wa alƙalan, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari'ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa'ad da kuke yanke shari'a. 7Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”

8Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra'ilawa, saboda su yi shari'a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna. 9Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma. 10A duk lokacin da 'yan'uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari'a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari'a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da 'yan'uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi. 11Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al'amuran da suke na wajen Ubangiji. Zabadiya, ɗan Isma'ilu mai mulkin gidan Yahuza, shi ne shugabanku a kan dukan al'amuran da suke na wajen sarki. Lawiyawa kuwa su zama muhimman ma'aikatanku. Kada ku ji tsoro a cikin aikinku, Ubangiji kuwa ya kasance tare da masu gaskiya.”

20

Yaƙi da Mowab, da Ammon, da Edom

1Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me'uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat. 2Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat cewa, “Mutane masu yawan gaske suna zuwa su yi yaƙi da kai daga Edom, da kuma teku, har sun iso Hazazon-tamar,” wato En-gedi. 3Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza. 4Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji. 5Sai Yehoshafat ya tsaya a gaban taron jama'ar Yahuza da na Urushalima, a Haikalin Ubangiji, a gaban sabuwar farfajiya, 6ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai. 7Ya Allahnmu, kai ne ka kori jama'ar ƙasan nan a gaban jama'arka Isra'ila, ka kuma ba da ita har abada ga zuriya masoyinka Ibrahim. 8Suka kuwa zauna a cikinta, suka gina Wuri Mai Tsarki saboda sunanka cewa, 9“‘Idan wani mugun abu ya same mu, kamar takobi, ko hukunci, ko annoba, ko yunwa, to, za mu tsaya a gaban wannan gida, a gabanka kuma, gama sunanka yana cikin gidan nan, idan mun yi maka kuka saboda wahalarmu, kai kuwa za ka ji, ka cece mu.”

10“Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra'ilawa su kai musu yaƙi sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra'ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba. 11Dubi irin sakayyar da suka zo su yi mana, so suke su kore mu daga mallakarka, wanda ka gādar mana. 12Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”

13A sa'an nan kuwa mutanen Yahuza suna tsaye a gaban Ubangiji, su da ƙananansu, da matansu, da 'ya'yansu. 14A tsakiyar taron sai Ruhun Ubangiji ya sauka a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, Balawe, na 'ya'yan Asaf, maza. 15Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, “‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne. 16Ku gangara ku fāɗa musu gobe. Ga shi kuwa, za su haura ta hawan Ziz, za ku tarar da su a ƙarshen kwarin a gabashin jejin Yeruyel. 17Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.”

18Yehoshafat fa ya sunkuyar da kansa ƙasa, dukan Yahuza da mazaunan Urushalima kuma suka fāɗi ƙasa a gaban Ubangiji, suna masa sujada. 19Sai Lawiyawa daga Kohatawa da Koratiyawa suka tashi tsaye suka yabi Ubangiji Allah na Isra'ila da babbar murya.

20Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.” 21Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce, “Ku yi godiya ga Ubangiji, Saboda madawwamiyar ƙaunarsa Tabbatacciya ce har abada.”

22Sa'ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, 'yan kwanto, 'yan kwanton kuwa suka fatattake su. 23Gama mutanen Ammon da na Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa'ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka kansu da kansu. 24Da mutanen Yahuza suka zo hasumiyar tsaro ta jeji, suka duba sai suka ga gawawwaki kawai a kwance, ba wanda ya tsira.

25Sa'ad da Yehoshafat da jama'arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna ta kwasar ganimar saboda yawanta. 26Sai suka taru a kwarin Beraka, wato albarka, a rana ta huɗu, a nan suka yabi Ubangiji. Don haka har wa yau ake kiran wurin, “Kwarin Beraka.” 27Sai kowane mutumin Yahuza da na Urushalima, tare da Yehoshafat shugabansu, suka koma Urushalima suna murna, gama Ubangiji ya sa su yi farin ciki saboda maƙiyansu. 28Suka shigo Urushalima da molaye da garayu, da ƙaho zuwa Haikalin Ubangiji. 29Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa'ad da suka ji Ubangiji ya yi yaƙi da maƙiyan Isra'ilawa. 30Mulkin Yehoshafat kuwa ya sami salama, gama Allahnsa ya ba shi hutawa a kowane gefe.

Ƙarshen Mulkin Yehoshafat

(1 Sar 22.41-50)

31Yehoshafat ya yi mulkin Yahuza. Yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan tsohuwarsa Azuba, 'yar Shilhi. 32Ya bi tafarkin tsohonsa, Asa, bai kuwa kauce ba, ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji. 33Duk da haka ba a kawar da masujadai ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.

34Sauran ayyukan Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra'ila.

35Bayan haka sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya haɗa kai da Ahaziya Sarkin Isra'ila, wanda ya aikata mugunta. 36Ya haɗa kai da shi, suka gina jiragen ruwa don su riƙa zuwa Tarshish. A Eziyon-geber suka gina jiragen ruwan. 37Sai Eliyezer ɗan Dodawahu mutumin Maresha, ya yi annabci gāba da Yehoshafat, ya ce, “Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Don haka jiragen ruwa suka farfashe, suka kāsa tafiya Tarshish.

21

1Yehoshafat ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda tare da kakanninsa, ɗansa kuma ya gāji gadon sarautarsa.

Sarki Yoram na Yahuza

(2 Sar 8.17-24)

2Yoram yana da 'yan'uwa maza, su ne Azariya, da Yehiyel, da Zakariya, da Azariya, da Maikel da kuma Shefatiya. Waɗannan 'ya'ya maza ne na Yehoshafat, Sarkin Yahuza. 3Tsohonsu ya ba su kyautai da yawa na azurfa da zinariya, da abubuwa masu daraja, da birane masu garu a Yahuza, amma ya ba da mulkin ga Yoram, saboda shi ne ɗan fari. 4Sa'ad da Yoram ya hau gadon sarautar tsohonsa, ya kahu sosai, sai ya karkashe dukan 'yan'uwansa da takobi, ya kuma karkashe waɗansu daga cikin sarakunan Yahuza.

5Yoram yana da shekara talatin da biyu sa'ad da ya hau gadon sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara takwas. 6Ya yi yadda sarakunan Isra'ila suka yi, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama matarsa 'yar Ahab ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. 7Duk da haka Ubangiji bai yarda ya hallaka gidan Dawuda ba, saboda alkawarin da ya riga ya yi da Dawuda, gama ya riga ya alkawarta zai ba shi haske, shi da 'ya'yansa maza har abada.

8A zamaninsa Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki. 9Sai Yoram ya wuce, shi da shugabannin sojojinsa tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare ya fatattaki Edomawa waɗanda suka kewaye shi, shi da shugabannin karusansa. 10Har wa yau Edom ya tayar wa Yahuza. A wannan lokaci kuma Libna ta tayar wa mulkinsa, saboda Yoram ya rabu da bin Ubangiji Allah na kakanninsa. 11A kan wannan kuma, ya yi masujadai a tuddan ƙasar Yahuza, ya sa mutanen Urushalima su zama marasa aminci, ya sa Yahuza ta ratse.

12Sai annabi Iliya ya rubuta masa wasiƙa ya ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na tsohonka Dawuda ya ce, “‘Da yake ba ka bi halin tsohonka Yehoshafat ba, da halin Asa Sarkin Yahuza, 13amma ka bi irin halin sarakunan Isra'ila, har ka sa Yahuza da mazaunan Urushalima su zama marasa aminci, yadda gidan Ahab ya yi, ka kuma karkashe 'yan'uwanka, waɗanda kuke uba ɗaya, waɗanda suka fi ka kirki, 14ga shi, ni Ubangiji zan aukar da babbar abboba a kan jama'arka, da 'ya'yanka maza, da matanka, da a kan abin da ka mallaka duka. 15Kai da kanka kuma za ka kamu da ciwon hanji mai tsanani, saboda tsananin ciwo, hanjinka zai tsintsinke ya yi ta zuba kowace rana.”

16Sai Ubangiji ya kuta Filistiyawa da Larabawan da suke kusa da Habashawa, su yi gāba da Yoram. 17Suka zo suka faɗa wa Yahuza da yaƙi. Suka washe dukan dukiyar da aka samu a gidan sarki, suka tafi da ita. Suka kuma kwashe 'ya'yansa, da matansa, ba wanda aka bar masa, sai Ahaziya autansa.

18Bayan haka kuma, sai Ubangiji ya sa masa ciwon hanji wanda ba shi warkuwa. 19Ana nan a ƙarshen shekara biyu, sai cutar ta sa hanjinsa ya zubo, ya kuwa rasu saboda tsananin ciwo. Jama'arsa ba su hura masa wuta ta girmamawa kamar yadda aka yi wa kakanninsa ba.

20Yana da shekara talatin da biyu, ya ci sarauta, ya yi shekara takwas yana mulki a Urushalima, ba wanda ya yi baƙin cikin mutuwarsa. Aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba a kaburburan sarakuna ba.

22

Sarki Ahaziya na Yahuza

(2 Sar 8.25-29)

1Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki. 2Ahaziya yana da shekara arba'in da biyu sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikar Omri. 3Ya kuma bi gurbin gidan Ahab, gama tsohuwarsa ita ce mai ba shi shawarar yadda zai aikata mugunta. 4Ya kuwa aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar gidan Ahab, gama su ne mashawartansa bayan rasuwar tsohonsa, wato shawarar da ta kai shi ga lalacewa. 5Ya kuwa bi shawararsu. Ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab, Sarkin Isra'ila, don su yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya, a Ramot-gileyad. Suriyawa kuwa suka yi wa Yehoram rauni. 6Don haka sai ya koma Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da aka yi masa a Rama, sa'ad da suka yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya ɗan Yoram, Sarkin Yahuza, ya gangara don ya gai da Yehoram ɗan Ahab a Yezreyel wanda yake rashin lafiya.

Yehu ya kashe Ahaziya

(2 Sar 9.27-29)

7Allah ya ƙaddara hallakar Ahaziya ta zo ta wurin ziyarar da ya kai wa Yehoram. Gama sa'ad da ya zo, sai ya fita tare da Yehoram don su yi yaƙi da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya keɓe don ya kakkaɓe gidan Ahab. 8Sa'ad da Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya gamu da sarakunan Yahuza, da 'ya'yan 'yan'uwan Ahaziya, maza, suna yi wa Ahaziya hidima, sai ya karkashe su. 9Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.” Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.

Sarauniya Ataliya ta Yahuza

(1 Sar 11.1-3)

10Da Ataliya tsohuwar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta karkashe duk 'yan sarautar gidan Yahuza. 11Amma sai Yehosheba, 'yar sarki Yoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya, ta sace shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe su ta sa shi da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba 'yar sarki Yoram, matar Yehoyada firist, ta yi, gama ita 'yar'uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya ta kashe shi. 12Yowash yana ɓoye a Haikalin Allah har shekara shida, a lokacin da Ataliya take mulkin ƙasar.

23

An Ƙwace wa Ataliya Mulki

(2 Sar 11.4-16)

1A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya yi ƙarfin hali, ya haɗa kansa da shugabanni na ɗari ɗari, wato Azariya ɗan Yeroham, da Isma'ilu ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, da Ma'aseya ɗan Adaya, da kuma Elishafat ɗan Zikri. 2Sai suka shiga ko'ina cikin Yahuza, suka tattaro Lawiyawa daga dukan biranen Yahuza, da shugabannin gidajen kakannin Isra'ila, suka kuwa zo Urushalima.

3Sai dukan taron suka yi wa sarki alkawari, a Haikalin Allah. Yehoyada ya ce musu, “Wannan shi ne ɗan sarki, sai ya ci sarauta kamar yadda Ubangiji ya faɗa a kan 'ya'yan Dawuda, maza. 4Ga abin da za ku yi. Sulusin firistoci da Lawiyawa waɗanda ba su aiki ran Asabar, su za su yi tsaron ƙofofi. 5Sulusinsu kuma a fādar sarki, ɗayan sulusin kuwa a gangare, sauran jama'a duka kuwa a filayen Haikalin Ubangiji. 6Amma kada kowa ya shiga Haikalin Ubangiji, sai dai firistoci da Lawiyawa masu hidima, su ne za su iya shiga, gama su tsarkaka ne. Amma dukan jama'a su kiyaye shari'a, kada su shiga Wuri Mai Tsarki na Ubangiji. 7Lawiyawa za su kewaye sarkin, ko wanne da makamansa a hannu, duk wanda ya shiga ɗakin, sai a kashe shi. Su kuma kasance tare da sarki in zai shiga ko zai fita.”

8Sai Lawiyawa da dukan Yahuza suka yi yadda Yehoyada, firist, ya umarta. Kowannensu ya kawo mutanensa waɗanda ba su aiki ran Asabar, da masu kama aiki ran Asabar, gama Yehoyada, firist, bai sallami ƙungiyoyin ba. 9Sai Yehoyada firist, ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin Haikalin Allah. 10Sai ya sa mutane duka su yi tsaron sarki, ko wanne da makami a hannu, tun daga gefen kudu har gefen arewa na Haikalin, da kuma kewaye da bagade da Haikali. 11Sai ya kawo ɗan sarkin, ya sa masa kambi, ya ba shi dokoki goma, aka yi shela aka ce shi ne sarki. Yehoyada da 'ya'yansa maza suka naɗa shi, suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”

12Sa'ad da Ataliya ta ji sowar mutane, suna ta ribibi suna yabon sarki, sai ta shiga Haikalin Ubangiji wurin jama'a. 13Sa'ad da ta duba, sai ga sarki yana tsaye wajen ginshiƙin bakin ƙofa, ga shugabanni da masu busa ƙaho kewaye da sarkin. Dukan jama'a suna murna, suna busa ƙaho, mawaƙa kuma da kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushensu, suna shugabancin shagalin. Sai Ataliya ta yayyage tufafinta ta ce, “Tawaye! Tawaye!”

14Sai Yehoyada, firist, ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku kawo ta a tsakiyar sojoji, duk wanda ya bi ta a kashe shi da takobi.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada ku kashe ta a Haikalin Ubangiji.”

15Sai suka kama ta. Da suka kai Ƙofar Doki ta fādar sarki, sai suka kashe ta a can.

Gyare-gyaren Yehoyada

(2 Sar 11.17-20)

16Sai Yehoyada da dukan jama'a, da sarkin, suka ɗauki alkawari za su zama jama'ar Ubangiji. 17Sai dukan jama'a suka tafi gidan Ba'al, suka rushe shi, suka kuma ragargaza bagadansa, da siffofinsa. Suka kashe Mattan, firist ɗin Ba'al, a gaban bagadan. 18Yehoyada kuma ya sa matsaran da za su yi tsaron Haikalin Ubangiji a ƙarƙashin ikon firistoci, Lawiyawa, waɗanda Dawuda ya shirya don su lura da Haikalin Ubangiji, su miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, yadda aka rubuta a Attaura ta Musa, da murna da waƙa kamar yadda Dawuda ya shirya. 19Ya kuma sa 'yan tsaron ƙofa a ƙofofin Haikalin Ubangiji, don kada wani marar tsarki na kowane iri ya shiga.

20Sai ya sa shugabanni, da dattawa, da masu mulki, da dukan jama'ar ƙasar, suka rufa wa sarki baya, daga Haikalin Ubangiji suka bi ta Ƙofar Bisa zuwa fādar sarki. Suka zo suka zaunar da sarki a gadon sarauta. 21Dukan jama'ar ƙasar suka yi murna, zaman lafiya ya komo birnin, bayan da an kashe Ataliya.

24

Sarki Yowash na Yahuza

(2 Sar 12.1-21)

1Yowash yana da shekara bakwai sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi shekara arba'in yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya, daga Biyer-sheba. 2Yowash ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji a dukan zamanin Yehoyada firist. 3Sai Yehoyada ya auro masa mata biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.

4Bayan wannan sai Yowash ya yi niyya ya gyara Haikalin Ubangiji. 5Sai ya tattara firistoci da Lawiyawa, ya ce musu, “Ku shiga biranen Yahuza, ku tattara kuɗi daga dukan Isra'ilawa domin a riƙa gyaran Haikalin Ubangijinku kowace shekara. Ku hanzarta al'amarin fa.” Amma Lawiyawa ba su hanzarta ba. 6Sai sarki ya kira Yehoyada babban firist, ya ce masa, “Don me ba ka sa Lawiyawa su tafi Yahuza, da Urushalima, su karɓo kuɗin da Musa, bawan Ubangiji, ya aza wa taron jama'ar Isra'ila su kawo domin alfarwar sujada ba?”

7Gama 'ya'ya maza na Ataliya, muguwar matan nan, sun kutsa kai a cikin Haikalin Ubangiji, suka yi amfani da dukan tsarkakan kayayyakin Haikalin Ubangiji domin gumaka.

8Don haka sai sarki ya ba da umarni, a yi babban akwati, a ajiye shi a waje a ƙofar Haikalin Ubangiji. 9Sai aka yi shela a Yahuza da Urushalima, a kawo wa Ubangiji kuɗin da Musa, bawan Allah, ya aza wa Isra'ila sa'ad da suke cikin jeji. 10Sai dukan sarakuna, da dukan jama'a, suka yi farin ciki, suka kawo kuɗin da aka aza musu, suka zuba a babban akwatin, har ya cika. 11Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa 'yan majalisar sarki babban akwatin sa'ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na'ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da yake cikin babban akwatin, sa'an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.

12Sarki kuwa da Yehoyada suka ba da kuɗin ga waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji. Suka sa magina, da masassaƙa su gyara Haikalin Ubangiji, suka kuma sa masu aikin baƙin ƙarfe da na tagulla su gyara Haikalin Ubangiji. 13Sai ma'aikatan da aka sa su yi aikin, suka yi aiki sosai, suka tafiyar da gyaran, suka gyara Haikalin Ubangiji, ƙarfinsa ya koma kamar yadda yake dā. 14Da suka gama aikin, sai suka kawo wa sarki da Yehoyada sauran kuɗin. Da waɗannan kuɗin aka yi tasoshi, da kayan girke-girke na Haikalin Ubangiji, da kuma kayan hidima da miƙa hadayu na ƙonawa, da tasoshi domin turare, da kwanoni na zinariya da na azurfa.

An sāke Shirin Yehoyada

Suka yi ta miƙa hadayu na ƙonawa a cikin Haikalin Ubangiji, dukan kwanakin Yehoyada. 15Yehoyada kuwa ya tsufa ƙwarai, ya yi tsawon rai, ya rasu. Ya rasu yana da shekara ɗari da talatin da haihuwa. 16Suka binne shi a birnin Dawuda a inda ake binne sarakuna, saboda ya aikata nagarta a Isra'ila, da kuma a gaban Allah da Haikalin Allah.

17Bayan rasuwar Yehoyada, sai sarakunan Yahuza suka zo suka yi mubaya'a a gaban sarki, sarki kuwa ya karɓa. 18Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi. 19Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba. 20Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama'a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, “‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.” 21Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefe annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji. 22Sarki Yowash bai tuna da irin alherin da Yehoyada mahaifin Zakariya ya yi masa ba, amma ya kashe ɗansa. Sa'ad da Zakariya yake bakin mutuwa, sai ya ce, “Bari Ubangiji ya gani ya kuma sāka.”

23A ƙarshen shekara sai sojojin Suriyawa suka kawo wa Yowash yaƙi suka je Yahuza da Urushalima, suka hallaka dukan shugabannin jama'a, suka kwashi ganima mai yawa, suka aika wa Sarkin Dimashƙu. 24Ko da yake mutanen Suriya kima ne, duk da haka Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan babbar rundunar Yowash, saboda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu. Ta haka suka hukunta wa Yowash. 25Sa'ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba. 26Waɗannan su ne waɗanda suka yi masa maƙarƙashiyar, Yozakar ɗan Shimeyat wata Ba'ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab. 27Labarin 'ya'yansa maza da annabcin da aka kawo a kansa da labarin sāke ginin Haikalin Allah, an rubuta su a sharhin littafin sarakunan. Sai Amaziya ɗan Yowash ya gāji gadon sarautarsa.

25

Sarki Amaziya na Yahuza

(2 Sar 14.2-6)

1Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara ashirin da tara yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yehowaddin ta Urushalima. 2Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji, amma bai rasa aikata laifi a zuciyarsa ba. 3Da ya ga mulkin ya kahu a hannunsa sosai, sai ya karkashe fādawa waɗanda suka kashe tsohonsa, sarki Yowash. 4Amma bai karkashe 'ya'yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari'a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, ba za a kuma kashe 'ya'ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.”

5Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa. 6Ya kuma ɗauko sojan haya, mutum dubu ɗari (100,000) jarumawa daga Isra'ila a bakin talanti ɗari na azurfa. 7Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, kada ka yarda rundunar sojojin Isra'ila su tafi tare da kai, gama Ubangiji ba ya tare da Isra'ila, wato da dukan Ifraimawan nan. 8Amma idan ka zaci ta wannan hanya ce za ka zama da ƙarfi don yaƙi, Allah zai kā da kai a gaban maƙiyi, gama Allah yana da iko ya yi taimako, ko kuwa ya ƙi.”

9Amaziya kuwa ya ce wa annabin Allah, “To, me za mu yi yanzu game da azurfar da muka ba sojojin Isra'ila?” Sai annabin Allah ya amsa ya ce, “Ubangiji yana da iko ya ba ka fiye da haka.” 10Sai Amaziya ya sallami rundunar sojojin da suka zo daga Ifraimu, su koma gida. Sai suka yi fushi da Yahuza ƙwarai suka koma gida cike da hasala mai zafi.

11Amma Amaziya ya yi ƙarfin hali ya shugabanci jama'arsa, suka tafi Kwarin Gishiri, suka karkashe mutanen Seyir dubu goma (10,000). 12Mutanen Yahuza kuma suka kama waɗansu mutum dubu goma (10,000) da rai, suka kai su a ƙwanƙolin dutse, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa daga ƙwanƙolin dutsen, duka suka yi kaca-kaca.

13Amma sojojin rundunar da Amaziya ya sallama, bai yarda su tafi yaƙi tare da shi ba, suka faɗa wa biranen Yahuza da yaƙi, tun daga Samariya har zuwa Bet-horon, suka kashe mutum dubu uku (3,000), a cikinsu suka kwashe ganima mai yawan gaske.

14Da Amaziya ya komo daga kisan Edomawa, sai ya kwaso gumakan mutanen Seyir, ya ajiye su su zama gumakansa, ya yi musu sujada, ya kuma miƙa musu hadaya. 15Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da Amaziya. Ubangiji ya aiki annabi a wurinsa. Annabin ya ce masa, “Don me ka koma ga gumakan da ba su iya ceton jama'arsu daga hannunka ba?”

16Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”

Yaƙi da Isra'ila

(2 Sar 14.8-20)

17Sa'an nan Amaziya Sarkin Yahuza, ya yi shawara ya aika wa Yehowash ɗan Yehowahaz ɗan Yehu, Sarkin Isra'ila, ya ce, “Ka zo mu gabza da juna fuska da fuska.”

18Yehowash Sarkin Isra'ila fa ya aika wa Amaziya Sarkin Yahuza, da amsa ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika wa itacen al'ul na Lebanon cewa, “‘Ka ba ɗana 'yarka aure,” sai wani naman jeji na Lebanon da yake wucewa, ya tattake ƙayar. 19Ka ce, ga shi, ka ci Edom, zuciyarka ta sa ka fāriya. Amma yanzu sai ka yi zamanka, don me ka tsokano wahalar da za ta kā da kai, da kai da Yahuza tare da kai?”

20Amma Amaziya ya ƙi ji, gama al'amarin daga wurin Allah yake, domin ya bashe su a hannun maƙiyansu, saboda sun koma ga gumakan Edom. 21Sarkin Isra'ila kuwa ya haura, da shi da Amaziya Sarkin Yahuza, suka gabza da juna fuska da fuska a Bet-shemesh, wadda take a ƙasar Yahuza. 22Sai Isra'ila ya runtumi Yahuza, kowane mutum ya gudu zuwa gidansa. 23Yehowash Sarkin Isra'ila, ya kama Amaziya Sarkin Yahuza ɗan Yowash, wato jikan Ahaziya, a Bet-shemesh, ya kawo shi Urushalima. Ya rushe garun Urushalima har tsawon kamu ɗari huɗu, tun daga Ƙofar Ifraimu har zuwa Ƙofar Kusurwa, 24sai ya kwashe dukan zinariya da azurfa, da dukan tukwane da tasoshi da aka samu a Haikalin Allah, waɗanda iyalin Obededom suke tsaro, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.

25Sarki Amaziya ɗan Yowash, Sarkin Yahuza, ya rayu shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila. 26Sauran ayyukan Amaziya, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila. 27Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi. 28Sai suka kawo shi a bisa dawakai, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

26

Sarki Azariya na Yahuza

(2 Sar 14.21-22; 15.1-7)

1Dukan jama'ar Yahuza fa suka ɗauki Azariya, ɗan shekara goma sha shida, suka naɗa shi sarki, ya gāji gadon sarautar tsohonsa Amaziya. 2Ya gina Elat, ya komar da ita ga Yahuza, bayan rasuwar sarki.

3Azariya yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu, sunan tsohuwarsa Yekoliya ta Urushalima. 4Azariya ya yi abin da yake daidai saboda Ubangiji, bisa ga dukan irin abin da tsohonsa Amaziya ya aikata. 5Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.

6Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa. 7Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa, da Larabawa, waɗanda suke zaune a Gur-ba'al, da kuma Me'uniyawa. 8Ammonawa kuma suka kawo masa haraji, sunan Azariya ya kai har kan iyakar Masar, gama ya shahara ƙwarai.

9Banda haka kuma, Azariya ya gina hasumiyai a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, da Ƙofar Kwari, da kan kusurwa, ya kuma yi musu kagara. 10Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafuka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.

11Har yanzu kuma, Azariya yana da rundunar sojoji waɗanda suka iya yaƙi ƙungiya ƙungiya, yadda Yehiyel magatakarda, da Ma'aseya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin 'yan majalisar sarki. 12Jimillar shugabannin gidajen kakanni na ƙarfafan mutane jarumawa, dubu biyu da ɗari shida (2,600) ne. 13Suna da sojoji dubu ɗari uku da dubu bakwai da ɗari biyar (307,500) a ƙarƙashin ikonsu waɗanda suke da ƙarfin yin yaƙi sosai, da za su taimaki sarki a kan maƙiyansa. 14Azariya ya shirya wa sojojinsa garkuwoyi, da māsu, da kwalkwali, da sulke, da bakuna, da duwatsun majajjawa. 15A Urushalima ya yi na'urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko'ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske.

An Hukunta Azariya Saboda Girmankai

16Amma sa'ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare. 17Amma Azariya firist, ya bi shi tare da firistoci tamanin na Ubangiji, mutane ne jarumawa. 18Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”

19Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa'ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare. 20Sai Azariya babban firist tare da sauran firistocin suka dube shi, sai ga kuturta a goshinsa! Sai suka tunkuɗa shi waje nan da nan. Shi kansa ma ya hazarta ya fita saboda Ubangiji ya buge shi.

21Ta haka sarki Azariya ya kuturce, har zuwa ranar mutuwarsa. Saboda kuturtarsa, ya zauna a keɓe a wani gida, gama an fisshe shi daga Haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa shi ya shugabanci iyalin gidan sarki, yana kuma mulkin jama'ar ƙasa.

22Sauran ayyukan Azariya, daga farko har zuwa ƙarshe, annabi Ishaya ɗan Amoz ya rubuta su. 23Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

27

Sarki Yotam na Yahuza

(2 Sar 15.32-38)

1Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha 'yar Zadok. 2Ya aikata abin da yake daidai saboda Ubangiji, kamar dukan abin da tsohonsa Azariya ya yi, sai dai bai kutsa cikin Haikalin Ubangiji ba. Amma jama'a suka ci gaba da aikata rashin kirki.

3Ya gina ƙofar bisa, ta Haikalin Ubangiji, ya yi gine-gine masu yawa a garun Ofel. 4Ya kuma gina birane a ƙasar tuddai ta Yahuza, da kagara, da hasumiya a tuddai masu kuramu. 5Ya yi yaƙi da Sarkin Ammonawa, ya kuwa ci nasara, har Ammonawa suka ba shi talanti ɗari na azurfa a wannan shekara, da alkama mudu dubu goma (10,000) da sha'ir mudu dubu goma (10,000). Haka Ammonawa suka yi ta biya a shekara ta biyu da ta uku. 6Yotam ya shahara, saboda ya daidaita al'amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa. 7Sauran ayyukan Yotam, da dukan yaƙe-yaƙensa da al'amuransa, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza. 8Ya ci sarauta, yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. 9Sai Yotam ya rasu, suka binne shi a birnin Dawuda. Ahaz ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

28

Sarki Ahaz na Yahuza

(2 Sar 16.1-4)

1Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. Amma shi bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi ba. 2Ya aikata irin al'amuran da sarakunan Isra'ila suka yi. Ya kuma yi gumakan Ba'al na zubi. 3Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone 'ya'yansa maza bisa ga ƙazantattun al'adun al'ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra'ila. 4Ya miƙa hadayu, ya ƙona turare a masujadai da a bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.

Yaƙin Suriya da Isra'ila

(2 Sar 16.5)

5Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya bashe shi a hannun Sarkin Suriya. Suka ci shi da yaƙi suka kama mutanensa da yawa, suka kai su Dimashƙu. Aka kuma bashe shi a hannun Sarkin Isra'ila, wanda ya ci shi da yaƙi, ya kashe masa mutane masu yawa. 6Gama Feka, ɗan Remaliya, ya kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000) cikin Yahuza a rana ɗaya, dukansu kuwa jarumawa ne, don sun bar bin Ubangiji Allah na kakanninsu. 7Sai Zikri wani ƙaƙƙarfan mutumin Ifraimu, ya kashe Ma'aseya ɗan sarki, da Azrikam, sarkin fāda, da Elkana wanda yake daga sarki sai shi. 8Mutanen Isra'ila kuwa suka kwaso 'yan'uwansu da suka kama, mutum dubu ɗari biyu (200,000), mata, da 'ya'ya mata, da 'ya'ya maza. Suka kuma kwaso ganima mai yawan gaske daga gare su. Suka kawo ganimar a Samariya.

Annabcin Oded

9Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama. 10Yanzu kuwa kuna niyya ku mai da jama'ar Yahuza da ta Urushalima su zama bayinku mata da maza. Ashe, ku kanku ba ku da waɗansu zunuban da kuka yi wa Ubangiji Allahnku? 11Yanzu fa, sai ku saurare ni, ku mayar da kamammun da kuka kwaso daga 'yan'uwanku gama Ubangiji yana fushi da ku ƙwarai.”

12Waɗansu daga cikin shugabannin 'ya'ya maza na Ifraimu, wato su Azariya ɗan Yohenan, da Berikiya ɗan Meshillemot, da Yehizkiya ɗan Shallum, da Amasa ɗan Hadlai suka tashi suka tsayar da masu komowa daga wurin yaƙin. 13Suka ce musu, “Kada ku shigo nan da waɗanda kuka kamo daga wurin yaƙin, gama so kuke ku jawo mana laifi a gaban Ubangiji, a kan manyan zunuban da muka riga muka yi, gama Ubangiji yana fushi da Isra'ila ƙwarai.” 14Don haka sai sojoji suka bar waɗanda suka kamo daga wurin yaƙi, da ganima a gaban sarakuna da dukan taron. 15Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin 'yan'uwansu a Yariko, wato birnin itatuwan dabino, sa'an nan suka koma Samariya.

Ahaz ya Roƙi Assuriya Taimako

(2 Sar 16.7-9)

16A wannan lokaci kuwa sarki Ahaz ya nemi taimako wurin sarakunan Assuriya. 17Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su. 18Filistiyawa kuma sun kai hari a biranen ƙasar Shefela, da Negeb ta Yahuza, har suka ci Bet-shemesh, da Ayalon, da Gederot, da Soko da ƙauyukanta, da Timna da ƙauyukanta, da Gimzo da ƙauyukanta. Sai suka zauna a can. 19Ubangiji kuwa ya ƙasƙantar da Yahuza, saboda Ahaz Sarkin Yahuza ya yi ganganci a Yahuza, ya zama marar aminci ga Ubangiji. 20Sai Tiglatfilesar, Sarkin Assuriya, ya zo ya yi yaƙi da shi, ya wahalshe shi, maimakon ya taimake shi. 21Sai Ahaz ya kwaso kaya daga Haikalin Ubangiji, da fādar sarki, da na sarakuna, ya ba Sarkin Assuriya, amma sam, bai taimake shi ba.

22Duk da wannan wahala da sarki Ahaz yake sha a wannan lokaci, sai ƙara rashin aminci yake yi ga Ubangiji. 23Gama ya miƙa hadaya ga gumakan Dimashƙu, ga waɗanda suka ci shi da yaƙi, ya ce, “Saboda gumakan sarakunan Suriya sun taimake su, ni ma zan miƙa musu hadaya don su taimake ni.” Amma suka zama masa dalilin lalacewa, shi da dukan Isra'ila. 24Sai Ahaz kuma ya tattara tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya farfashe su. Ya kuma kukkulle ƙofofin Haikalin Ubangiji, ya gina wa kansa bagadai a kowane lungu na Urushalima. 25A kowane birni na Yahuza, ya yi masujadai inda zai ƙona turare ga gumaka, ya sa Ubangiji, Allah na kakanninsa ya yi fushi.

26Sauran ayyukansa da dukan al'amuransa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila. 27Ahaz ya rasu, suka binne shi cikin birnin Urushalima, amma ba su kai shi hurumin sarakunan Isra'ila ba. Hezekiya ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

29

Sarki Hezekiya na Yahuza

(2 Sar 18.1-3)

1Hezekiya ya ci sarauta sa'ad da yake da shekara ashirin da biyar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abaija, 'yar Zakariya. 2Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi duka.

Hezekiya ya Tsabtace Haikali

3A shekara ta fari ta mulkinsa, a wata na farko, sai ya buɗe ƙofofin Haikalin Ubangiji ya gyaggyara su. 4Sai ya shigo da firistoci da Lawiyawa, ya tara su a filin da yake wajen gabas. 5Sai ya ce musu, “Ku ji ni, ya ku Lawiyawa. Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake Haikalin Ubangiji Allah na kakanninku, ku kawar da ƙazantar da take a Wuri Mai Tsarki. 6Gama kakanninmu sun yi rashin aminci, sun aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnmu, sun rabu da shi sun ba da baya ga mazaunin Ubangiji. 7Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra'ila. 8Don haka Ubangiji ya yi fushi da Yahuza da Urushalima, ya sa suka zauna da tsoro, abin banmamaki, abin ba'a kamar yadda kuke gani da idanunku. 9Saboda wannan an kashe kakanninmu da takobi, 'ya'yanmu mata, da 'ya'yanmu maza da matanmu, an kai su bauta.

10“Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu. 11'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.” 12-14Sa'an nan sai Lawiyawa suka tashi, na Kohatawa, Mahat ɗan Amasai, da Yowel ɗan Azariya, na Merari, Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yehallelel, na Gershonawa, Yowa ɗan Zimma, da Eden ɗan Yowa, na Elizafan, Shimri da Yehiyel, na Asaf, Zakariya da Mattaniya, na Heman, Yehiyel da Shimai, na Yedutun, Shemaiya da Uzziyel.

15Sai suka tattara 'yan'uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji. 16Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da take a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.

17A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.

An Sāke Keɓe Haikali

18Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da suke ciki. 19Dukan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar a zamaninsa, sa'ad da ya zama marar aminci, mun shirya su mun tsarkake su, suna nan a gaban bagaden Ubangiji.”

20Sarki Hezekiya kuwa ya tashi da sassafe ya tattara manyan gari suka haura zuwa Haikalin Ubangiji. 21Suka kawo bijimai bakwai, da raguna bakwai, da 'yan raguna bakwai, da bunsurai bakwai, domin yin hadaya don zunubi saboda mulkin, da Wuri Mai Tsarki, da kuma Yahuza. Sai ya umarci firistoci, wato 'ya'yan Haruna, maza, su miƙa su a kan bagaden Ubangiji. 22Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin, suka yayyafa a jikin bagaden. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Hakanan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. 23Sa'an nan suka kawo wa sarki da taron jama'a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran. 24Sai firistocin suka yanka su suka tsarkake bagaden da jinin bunsuran, don a yi kafara saboda dukan Isra'ila. Gama sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi saboda dukan Isra'ila.

25Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa. 26Lawiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dawuda, firistoci kuwa suna riƙe da ƙahoni. 27Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra'ila, suka kama. 28Dukan taron suka yi sujada, mawaƙa suna ta raira waƙa, masu ƙahoni suka yi ta busa. Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa. 29Bayan da an gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada. 30Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.

31Hezekiya kuwa ya amsa ya ce, “Yanzu dai kun tsarkake kanku ga Ubangiji. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a Haikalin Ubangiji.” Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, dukan waɗanda suka yi niyya kuwa suka kawo hadayu na ƙonawa. 32Jimillar hadayu na ƙonawa waɗanda taron suka kawo, su ne bijimai saba'in, da raguna ɗari, da 'yan raguna ɗari biyu, waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Ubangiji. 33Abubuwan da aka keɓe kuwa bijimai ɗari shida ne, da tumaki dubu uku (3,000). 34Amma su firistoci kima ne, don haka sun kāsa fiɗa dukan dabbobin da za a miƙa su hadaya ta ƙonawa. Sai 'yan'uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu. 35Banda hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi, akwai kuma kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowace hadaya ta ƙonawa. Da haka fa aka maido hidimar Haikalin Ubangiji. 36Hezekiya da dukan jama'a suka yi murna saboda abin da Allah ya yi wa jama'a, gama farat ɗaya abin ya faru.

30

Yin Idin Ƙetarewa

1Sai Hezekiya ya aika zuwa ga dukan Isra'ila da Yahuza, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga Ifraimu, da Manassa, cewa sai su zo Haikalin Ubangiji a Urushalima, domin su yi Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila. 2Gama sarki da sarakunansa da dukan majalisar da take a Urushalima sun tsai da shawara a yi Idin Ƙetarewa a wata na biyu, 3gama ba su iya yinsa a lokacinsa ba, saboda yawan firistocin da suka tsarkake kansu bai isa ba, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba. 4A ganin sarki da na jama'a duka, shirin ya yi daidai. 5Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra'ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila a Urushalima, gama jama'a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba. 6Sai mazanni suka tafi ko'ina da ina a dukan ƙasar Isra'ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta. “Ya ku jama'ar Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya. 7Kada fa ku zama kamar kakanninku ko 'yan'uwanku, marasa bangaskiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu, saboda haka ya maishe su kufai kamar yadda kuka gani. 8Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku. 9Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”

10Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba'a. 11Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali'u, suka zo Urushalima. 12Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.

13Mutane da yawa kuwa suka zo Urushalima don su yi idin abinci marar yisti a wata na biyu, aka yi babban taro. 14Sai suka kama aiki, suka kawar da bagadan da suke cikin Urushalima, da dukan bagadan ƙona turare suka kwashe suka zubar a kwarin Kidron. 15Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji. 16Sai suka ɗauki matsayinsu wanda aka ayyana bisa ga dokar Musa, mutumin Allah, firistocin suka yafa jinin da suka karɓa daga hannun Lawiyawa. 17Gama akwai waɗansu da yawa daga cikin taron waɗanda ba su tsarkake kansu ba, saboda haka ya zama tilas Lawiyawa su yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa saboda dukan wanda ba shi da tsarki, domin a tsarkake shi ga Ubangiji. 18Gama akwai jama'a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu'a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne 19wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko bai yi bisa kan dokar tsarkakewa na Wuri Mai Tsarki ba.” 20Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama'ar. 21Jama'ar Isra'ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji. 22Hezekiya kuwa ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna fasaha a hidimar Ubangiji.

An Ƙara Yin Idin

Mutane fa suka ci abincin idin har kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta yin godiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu. 23Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna. 24Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu. 25Dukan taron Yahuza, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan taron jama'a da suka zo daga Isra'ila, da baƙi waɗanda suka zo daga ƙasar Isra'ila, da baƙin da suka zauna a Yahuza, suka yi murna. 26Saboda haka an yi babban farin ciki a Urushalima, gama tun daga zamanin Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ba a yi wani abu kamar haka a Urushalima ba. 27Sai firistoci da Lawiyawa suka tashi suka sa wa jama'a albarka, aka kuwa ji muryarsu, addu'arsu kuma ta kai wurin zamansa a Sama.

31

Shirin Hezekiya domin Firistoci da Lawiyawa

1Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.

2Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo. 3Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.

4Hezekiya ya kuma umarci jama'ar da ke zaune a Urushalima su riƙa ba da rabon firistoci da na Lawiyawa, domin su mai da hankali ga dokar Ubangiji. 5Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko'ina, sai jama'ar Isra'ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu. 6Jama'ar Isra'ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi. 7A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai. 8Sa'ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama'arsa Isra'ila. 9Hezekiya kuma ya yi wa firistoci da Lawiyawa tambaya a kan tsibi tsibin. 10Sai Azariya, babban firist na gidan Zadok, ya amsa masa, ya ce, “Tun lokacin da suka fara kawo sadakarsu a Haikalin Ubangiji, mun ci mun ƙoshi, abin da ya ragu kuwa yana da yawa, gama Ubangiji ya sa wa jama'arsa albarka, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”

11Sai Hezekiya ya umarce su su shirya ɗakuna a Haikalin Ubangiji, suka kuwa shirya. 12Da aminci suka kawo sadakokinsu, ta zaka da ta keɓaɓɓun abubuwa. Babban shugaban da yake lura da su kuwa, shi ne Konaniya, Balawe, da Shimai ɗan'uwansa, shi ne na biyu, 13sa'an nan da Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimai waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban Haikalin Allah suka naɗa. 14Kore kuwa ɗan Imna Balawe, mai tsaron ƙofar gabas, yake lura da hadayu na yardar rai ga Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki. 15Eden, da Miniyamin, da Yeshuwa, da Shemaiya, da Amariya, da Shekaniya suna taimakonsa da zuciya ɗaya a biranen firistoci, don su rarraba wa 'yan'uwansu rabonsu, tsofaffi da yara, duka ɗaya ne, bisa ga ƙungiyoyinsu, 16da su kuma waɗanda aka rubuta bisa ga asali, 'yan samari masu shekara uku zuwa sama, duk dai waɗanda za su shiga Haikalin Ubangiji don yin hidima, kamar yadda aka tsara, bisa ga matsayinsu yadda aka karkasa su. 17Aka kuma rubuta firistoci bisa ga gidajen kakanninsu, na wajen Lawiyawa kuwa, tun daga mai shekara ashirin zuwa sama, bisa ga matsayinsu, ta yadda aka karkasa su. 18Aka rubuta firistoci tare da dukan ƙananan 'ya'yansu, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, dukansu gaba ɗaya, gama da zuciya ɗaya suka tsarkake kansu. 19Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa 'ya'yan Haruna, firist, maza kuwa, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namiji da aka rubuta na Lawiyawa, nasa rabo.

20Haka kuwa Hezekiya ya yi a dukan Yahuza, ya aikata abin da yake daidai, da aminci, a gaban Ubangiji Allahnsa. 21Kowane irin aiki da ya kama na hidimar Haikalin Allah, wanda yake kuma bisa ga doka da umarni, na neman Allahnsa, ya yi su da zuciya ɗaya, ya kuwa arzuta.

32

Assuriyawa sun Yi Barazana ga Urushalima

(2 Sar 18.13ū19.19; Ish 36.1-22)

1Bayan waɗannan abubuwa, da waɗannan ayyukan aminci, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa Yahuza yaƙi, ya kafa sansani kewaye da garuruwa masu garu, yana zaton zai ci su da yaƙi su zama nasa. 2Da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo da nufin ya yi yaƙi da Urushalima, 3sai ya yi shawara shi da jarumawansa da manyan mutanensa, su datse ruwan da yake fitowa daga maɓuɓɓugar da take bayan birni, suka kuwa taimake shi. 4Don haka mutane da yawa suka taru suka daddatse dukan maɓuɓɓugai da rafuffuka da suke gudu cikin ƙasar, suna cewa, “Bari mu hana sarakunan Assuriya samun ruwa idan sun iso Urushalima.” 5Sai ya kama aiki gadangadan, ya sāke gina dukan garukan da suka rushe, ya gina hasumiya a kai, ya kuma gina wani garu bayan wannan, ya ƙara ƙarfin Millo a birnin Dawuda, ya kuma yi makamai na yaƙi da garkuwoyi masu yawan gaske. 6Sai ya sa manyan sojoji su shugabanci jama'a. Su tattaro su gare shi a dandalin ƙofar birni, ya yi musu magana ta ƙarfafawa ya ce, 7“Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda Sarkin Assuriya, da dukan taron da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su. 8Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.

9Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa'an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa, 10“Ga abin da Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya ce, “‘Ga me kake dogara, da har yanzu kuka dāge a cikin Urushalima, ga shi kuwa, yaƙi ya kewaye ta? 11Ai, Hezekiya, ba ruɗinku yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi sa'ad da yake ce muku Ubangiji Allahnku zai cece ku daga hannun Sarkin Assuriya? 12Ashe, ba wannan Hezekiya ba ne ya ɗauke masujadansa da bagadansa, ya kuma umarci Yahuza da Urushalima, su yi sujada a gaban bagade guda, a kansa ne kuma za su ƙona hadayu? 13Ashe, ba ku san abin da ni da kakannina muka yi wa dukan jama'ar waɗansu ƙasashe ba? Gumakan al'umman waɗannan ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna? 14Daga cikin dukan gumakan waɗannan al'ummai waɗanda kakannina suka hallakar da su sarai, ba wanda ya iya ceton jama'arsa daga hannuna, har da Allahnku zai iya cetonku daga hannuna? 15Yanzu fa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, ko ya ɓad da ku haka, kada kuwa ku gaskata shi, gama ba wani gunki na wata al'umma, ko wani mulki wanda ya taɓa ceton jama'arsa daga hannuna, ko kuma daga hannun kakannina. Wane Allah naku har da zai iya cetonku daga hannuna?”

16Barorinsa kuwa suka ƙara yin maganganun saɓo gāba da Ubangiji Allah da bawansa Hezekiya. 17Ya kuma rubuta wasiƙu, ya zargi Ubangiji Allah na Isra'ila, ya yi maganar saɓo, yana cewa, “Kamar yadda gumakan al'umman sauran ƙasashe suka kāsa ceton jama'arsu daga hannuna, hakanan kuma Allahn Hezekiya ba zai iya ceton jama'arsa daga hannuna ba.” 18Da babbar murya, da Yahudanci kuwa, suka yi ta yin magana da jama'ar Urushalima waɗanda suke kan garu, don a tsoratar da su, a kuma firgita su, don su ci birnin. 19Suka yi ta magana a kan Allah na Urushalima, kamar yadda suka yi magana a kan gumakan al'ummai, wato aikin hannuwan mutane.

Ubangiji ya Ceci Hezekiya

(2 Sar 19.35-37; Ish 37.36-38)

20Sai sarki Hezekiya, da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu'a saboda wannan al'amari, suka yi kuka zuwa Sama. 21Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.

22Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska. 23Mutane da yawa suka kawo wa Ubangiji sadakoki a Urushalima, suna kuma kawo wa Hezekiya Sarkin Yahuza abubuwa masu daraja. Saboda haka ya sami ɗaukaka a idon dukan sauran al'ummai, tun daga wannan lokaci har zuwa gaba.

Hezekiya ya yi Ciwo

(2 Sar 20.1-11; Ish 38.1-22)

24A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa, sai ya yi addu'a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ya ba shi alama. 25Amma Hezekiya bai nuna godiya a kan amfanin da ya samu ba, saboda girmankai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuza da Urushalima. 26Amma Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda girmankan da ya yi, shi da mazaunan Urushalima, saboda haka hasalar Ubangiji ba ta faɗa musu a kwanakin Hezekiya ba.

Hezekiya ya Karɓi 'Yan Saƙo daga Babila

(2 Sar 20.12-19; Ish 39.1-8)

27Hezekiya yana da dukiya ƙwarai, yana kuma da girma. Sai ya gina wa kansa taskoki inda zai ajiya azurfa, da zinariya, da duwatsu masu daraja, da kayan yaji, da garkuwoyi, da dukan tasoshi, da kwanoni masu daraja. 28Yana kuma da ɗakunan ajiya na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai. Yana da wuraren turke shanu na kowane iri, yana kuma da garkunan tumaki. 29Ya kuma giggina wa kansa birane, yana da garkunan tumaki da na awaki, da na shanu a yalwace. Gama Allah ya mallakar masa da abubuwa masu yawa. 30Hezekiyan nan kuwa ya datse ruwan da yake gangarawa daga kogin Gihon, ya karkatar da su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dawuda. Hezekiya ya arzuta da dukan ayyukan da ya yi. 31A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da yake a zuciyarsa.

Mutuwar Hezekiya

(2 Sar 20.20-21)

32Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, ga shi, an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila. 33Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa'ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

33

Sarki Manassa na Yahuza

(2 Sar 21.1-18)

1Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana mulki a Urushalima. 2Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya yi irin ayyukan banƙyama da al'ummai waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban jama'ar Isra'ila suke yi. 3Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba'al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu. 4Ya kuma giggina bagadai a cikin Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima sunana zai kasance har abada.” 5Ya giggina bagadai ga dukan rundunar sama a farfajiyan nan biyu na cikin Haikalin Ubangiji. 6Ya miƙa 'ya'yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha'ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji. 7Sai ya kafa gunkin da ya yi a cikin Haikalin Allah, wanda Allah ya faɗa wa Dawuda da ɗansa Sulemanu ya ce, “A cikin wannan Haikali da a Urushalima, inda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila, zan sa sunana har abada. 8Ba zan ƙara fitar da Isra'ila daga ƙasar da na ba kakanninku ba, in dai sun lura, sun kiyaye, sun aikata dukan abin da na umarce su, da dukan shari'a, da dokoki, da ka'idodi da aka bayar ta hannun Musa.” 9Ta haka kuwa Manassa ya lalatar da Yahuza da mazaunan Urushalima. Suka aikata muguntar da ta fi ta al'umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama'ar Isra'ila.

Tuban Manassa

10Ubangiji fa ya yi magana da Manassa da jama'arsa, amma ba wanda ya kula. 11Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila. 12Amma sa'ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa. 13Sa'ad da ya yi addu'a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa'an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.

14Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza. 15Ya kwashe gumaka da siffofi daga cikin Haikalin Ubangiji, da dukan bagadan da ya giggina a bisa dutse na Haikalin Ubangiji da a Urushalima. Ya zubar da su a bayan birnin. 16Ya kuma komar da bagaden Ubangiji, ya miƙa hadayu na salama da na godiya, ya kuma umarci Yahuza ta bauta wa Ubangiji Allah na Isra'ila. 17Duk da haka dai jama'a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadai, amma ga Ubangiji Allahnsu kaɗai.

Ƙarshen Mulkin Manassa

18Sauran ayyukan Manassa, da addu'o'insa zuwa ga Allahnsa, da abubuwan da masu gani suka faɗa sa'ad da suka yi masa magana da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, suna cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 19Addu'arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai. 20Haka fa Manassa ya rasu, suka binne shi a gidansa, sai Amon ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Sarki Amon na Yahuza

(2 Sar 21.19-26)

21Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara biyu yana mulki a Urushalima. 22Shi ma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Manassa, tsohonsa, ya yi. Amon ya miƙa hadaya ga dukan siffofin da tsohonsa, Manassa, ya yi ya bauta musu. 23Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.

24Sai fadawansa suka yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa. 25Jama'ar ƙasar kuwa suka karkashe dukan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar, suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gāji gadon sarautarsa.

34

Sarki Yosiya na Yahuza

(2 Sar 22.1-2)

1Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. 2Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yana bin al'amuran da kakansa Dawuda ya yi, bai kauce dama ko hagu ba.

Yosiya yana gāba da Arnanci

(2 Sar 23.4-20)

3A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi. 4Sai suka farfashe bagadai na Ba'al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu. 5Ya kuma ƙone ƙasusuwan firistoci a bisa bagadansu, ya tsarkake Yahuza da Urushalima. 6A biranen Manassa, da na Ifraimu, da na Saminu, har zuwa Naftali, a kangwayensu kewaye da su, 7ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra'ila, sa'an nan ya koma Urushalima.

An Gano Littafin Shari'a

(2 Sar 22.3-20)

8A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma'aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda yake magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa. 9Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra'ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima. 10Sai suka ba da kuɗin ga ma'aikata masu lura da Haikalin Ubangiji, da ma'aikatan da suke aiki a Haikalin Ubangiji, don gyare-gyare, su maishe shi kamar yadda yake dā, 11sai suka ba masassaƙa da magina kuɗin, don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katako, don yin tsaiko da tankar gine-ginen da sarakunan Yahuza suka bari, har suka lalace. 12Mutanen fa suka yi aiki mai aminci tare da waɗanda suke lura da su domin su gabatar da aiki, wato Yahat da Obadiya, Lawiyawa, 'ya'yan Merari, maza, da Zakariya da Meshullam na wajen 'ya'yan Kohatawa, da waɗansu Lawiyawa da suke da gwanintar bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe. 13Su ne shugabannin masu ɗaukar kaya, suke kuma nuna wa kowane ma'aikaci irin aikin da zai yi, waɗansu daga cikin Lawiyawa, magatakarda ne, da ma'aikatan hukuma, da masu tsaron ƙofofi.

14Sa'ad da suke fitowa da kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya gāno littafin Shari'ar Ubangiji wanda aka bayar ta hannun Musa. 15Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari'a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin. 16Shafan kuma ya kai wa sarki littafin, sa'an nan ya faɗa wa sarki cewa, “Dukan abin da aka sa barorinka su yi suna yi. 17Sai suka juye kuɗin da aka samu don Haikalin Ubangiji, suka miƙa wa masu lura da aikin, da ma'aikatan.” 18Magatakarda Shafan kuwa ya faɗa wa sarki, ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta wa sarki littafin.

19Da sarki ya ji irin maganganun da littafin ya faɗa, sai ya yayyage tufafinsa. 20Sa'an nan sarki ya umarci Hilkiya, da Ahikan ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mika, da magatakarda Shafan, da Asaya baran sarki, ya ce, 21“Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra'ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”

22Hilkiya kuwa tare da waɗanda sarki ya aika suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, ɗan Harhas, mai lura da wurin ajiyar tufafi, tana zaune a Urushalima, a unguwa ta biyu. Suka faɗa mata saƙon sarki, 23sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce in faɗa wa mutumin da ya aiko gare shi, 24“‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la'anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza. 25Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.” 26Amma a kan Sarkin Yahuza wanda ya aike ku ku tambayi Ubangiji, ga abin da za ku faɗa masa, “‘Ni Ubangiji, Allah na Isra'ila na ce, a kan maganar da ka ji, 27da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa'ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka. 28Ga shi, zan kai ka wurin da kakanninka suke, a kabarinka a binne ka da salama, ba za ka ga dukan masifun da zan kawo wa wurin nan da mazaunansa ba.” Sai suka isar da amsa wurin sarki.

Yosiya ya Kawar da Arnanci

(2 Sar 23.1-20)

29Sarki ya aika a kirawo dukan dattawan Yahuza da na Urushalima. 30Sai sarki ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan jama'a, babba da yaro. Sai ya karanta dukan maganar da take a littafin alkawari wanda aka gāno a Haikalin Ubangiji, a kunnen dukansu. 31Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya yi alkawari a gaban Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji, ya kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai yi aiki da alkawarin da yake rubuce a wannan littafi. 32Ya kuma sa dukan waɗanda suke a Urushalima da na Biliyaminu, su tsaya a kan wannan magana. Mazaunan Urushalima kuwa suka yi yadda alkawarin Allah ya ce, wato Allah na kakanninsu. 33Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama'ar Isra'ila suke da ita. Ya sa dukan waɗanda suke a Isra'ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. A dukan kwanakin ransa, ba su kauce daga bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.

35

Yosiya ya Yi Idin Ƙetarewa

(2 Sar 23.21-23)

1Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa. 2Ya sa firistoci a matsayinsu, ya ƙarfafa su a hidimar Haikalin Ubangiji. 3Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila. 4Ku karkasa kanku bisa ga gidajen kakanninku ƙungiya ƙungiya, ku bi bayanin Dawuda, Sarkin Isra'ila, da na ɗansa Sulemanu. 5Ku tsaya a Wuri Mai Tsarki, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin 'yan'uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa. 6Ku yanka abin Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya wa 'yan'uwanku su yi bisa ga maganar Ubangiji ta hannun Musa.”

7Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da 'yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne. 8Da yardar rai manyan ma'aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama'ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma'aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku. 9Konaniya kuma tare da Shemaiya da Netanel, 'yan'uwansa, da Hashabiya, da Yehiyel, da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, su suka ba Lawiyawa abin yin hadayar Idin Ƙetarewa, raguna da 'yan awaki dubu biyar (5,000), da bijimai ɗari biyar.

10Sa'ad da aka shirya yin hidimar, firistoci suka tsaya a wurinsu, Lawiyawa kuwa suka tsaya bisa ga ƙungiyoyinsu, yadda sarki ya umarta. 11Sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewar. Sa'an nan firistoci suka karɓi jinin daga gare su, suka yayyafa, Lawiyawa kuma suka yi ta fiɗa. 12Sa'an nan suka keɓe hadayu na ƙonawa domin su rarraba bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakanni waɗanda su ba firistoci ba ne, don su miƙa wa Ubangiji kamar yadda aka rubuta a littafin Musa. Hakanan kuma suka yi da bijiman. 13Suka gasa ragon hadayar Idin Ƙetarewa bisa ga ka'idar, sai suka dafa tsarkakan hadayu a tukwane, da manyan tukwane, da kwanoni, nan da nan suka kai wa waɗanda ba firistoci ba. 14Daga baya kuma suka shirya wa kansu da firistoci, saboda firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, suna ta hidimar miƙa hadayu na ƙonawa, da kuma na kitse, har dare. Don haka Lawiyawa suka shirya wa kansu abinci, suka kuma shirya wa firistoci, 'ya'yan Haruna, maza. 15Mawaƙa, 'ya'yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama 'yan'uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu. 16Haka fa aka shirya dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Idin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda Yosiya sarki ya umarta. 17Jama'ar Isra'ila waɗanda suke wurin, suka kiyaye Idin Ƙetarewa, da kuma idin abinci marar yisti har kwana bakwai. 18Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama'ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra'ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra'ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima. 19A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya aka yi Idin Ƙetarewa.

Rasuwar Yosiya

(2 Sar 23.28-30)

20Bayan wannan duka, sa'ad da Yosiya ya shirya Haikali, sai Neko Sarkin Masar, ya zo don ya yi yaƙi a Karkemish wadda take a Yufiretis, sai Yosiya ya fito don ya kara da shi. 21Amma Neko ya aika 'yan saƙo su faɗa masa su ce, “Me ya gama mu da juna, ya Sarkin Yahuza? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da Sarkin Assuriya! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada ya hallaka ka.” 22Duk da haka Yosiya bai yarda ya koma ba, sai ya ɓad da kama don ya yi yaƙi da shi. Bai yarda da magana wadda Allah ya faɗa wa Neko ba, sai suka kama yaƙi a filin Magiddo.

23Maharba suka harbi sarki Yosiya, sai ya ce wa barorinsa, “Ku ɗauke ni ku tafi da ni, gama an yi mini mummunan rauni.” 24Barorinsa kuwa suka ɗauke shi daga cikin karusa, suka sa shi a karusa ta biyu, suka kawo shi Urushalima, sai ya rasu. Aka binne shi a hurumin kakanninsa. Yahuza da Urushalima fa suka yi makoki domin Yosiya.

25Irmiya kuma ya hurta makoki domin Yosiya. Hakanan kuma dukan mawaƙa mata da maza, suka ambaci Yosiya cikin makokinsu har yau. Suka sa waɗannan su zama farali a Isra'ila, ga shi kuma, an rubuta su a Littafin Makoki.

26Sauran ayyukan Yosiya, da kyawawan ayyukansa, waɗanda ya yi bisa ga abin da aka rubuta a Shari'ar Ubangiji, 27ayyukansa na fari da na ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza.

36

Sarki Yehowahaz na Yahuza

(2 Sar 23.31-35)

1Jama'ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima. 2Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima wata uku. 3Sai Sarkin Masar ya tuɓe shi daga sarautarsa ta Urushalima, ya sa su biya gandu, su ba da azurfa talanti ɗari, da zinariya talanti guda. 4Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan'uwansa, sarki a Yahuza da Urushalima. Ya sa masa sabon suna Yehoyakim. Amma Neko ya ɗauko Yehowahaz ɗan'uwan Eliyakim ya kai shi Masar.

Sarki Yehoyakim na Yahuza

(2 Sar 23.36ū24.7)

5Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. 6Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya ɗaure shi da sarƙoƙi, ya kai shi Babila. 7Nebukadnezzar kuma ya kwaso waɗansu tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya kai Babila, ya ajiye su a fādar Babila. 8Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.

An Kama Sarki Yekoniya

(2 Sar 24.8-17)

9Yekoniya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. 10Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan'uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.

Sarki Zadakiya na Yahuza

(2 Sar 24.18-20)

11Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima. 12Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.

Fāɗuwar Urushalima

(2 Sar 25.1-7)

13Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra'ila. 14Dukan manyan firistoci da sauran jama'a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al'ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima. 15Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama'arsa da wurin zaman zatinsa. 16Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba'a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba'a, sai Ubangiji ya husata da jama'arsa don abin ya kai intaha.

An Kai Yahuza Bautar Talala

(2 Sar 25.8-21; Irm 39.8-10; 52.12-30)

17Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa. 18Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila. 19Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja. 20Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na 'ya'yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa, 21don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba'in, ta kiyaye asabatai.

22Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

23Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da yake nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”