2 Kings
1Bayan rasuwar Ahab, Sarkin Isra'ila, sai Mowabawa suka tayar wa Isra'ilawa.
2Ahaziya ya faɗo daga tagar benensa a Samariya, ya kuwa ji ciwo ƙwarai. Sai ya aiki manzanni, ya ce musu, “Ku tafi, ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron, ko zan warke daga wannan ciwo.” 3Sai mala'ikan Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe, ya ce, “Tashi, ka tafi, ka sadu da manzannin Sarkin Samariya, ka ce musu, “‘Ba Allah a Isra'ila da za ku tafi ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron?” 4Ku faɗa wa sarki, Ubangiji ya ce, “‘Ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.” Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi. 5Manzannin kuwa suka koma wurin sarki. Sarki ya ce, “Me ya sa kuka komo?”
6Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, “‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra'ila, har aka aike ku ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.”
7Sarki ya tambaye su, “Yaya mutumin yake, shi wanda ya sadu da ku, ya faɗa muku irin wannan magana?”
8Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.” Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”
9Sa'an nan sarki ya aiki shugaba tare da mutum hamsin su taho da Iliya. Mutumin kuwa ya haura wurin Iliya a kan dutse, ya ce masa, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko.”
10Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.
11Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba tare da mutum hamsin. Suka tafi, shugaban ya ce wa Iliya, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko da sauri.”
12Iliya kuwa ya ce musu, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka guda hamsin.” Wuta kuwa daga wurin Allah ta sauko daga sama ta cinye shugaban da mutanensa hamsin.
13Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba, na uku ke nan, tare da mutanensa hamsin. Sai shugaba na uku ya tafi ya rusuna a gaban Iliya, ya roƙe shi, ya ce, “Ya mutumin Allah, ina roƙonka ka ga darajar raina da na barorinka, su hamsin. 14Gama wuta ta sauko daga sama ta cinye shugabanni biyu tare da mutanensu hamsin hamsin, amma ka dubi darajar raina.”
15Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Ka sauka, ka tafi tare da shi, kada ka ji tsoronsa.” Iliya kuwa ya tashi, ya tafi tare da shi har gaban sarki. 16Ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, “‘Domin ka aiki manzanni su yi tambaya wurin Ba'alzabul, gunkin Ekron, ba Allah a Isra'ila ne wanda za ka yi tambaya a wurinsa? Domin haka ba za ka sauko daga kan gadon da kake kwance ba, amma za ka mutu lalle.”
17Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan'uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.
18Sauran ayyukan da Ahaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
1Sa'ad da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa Sama cikin guguwa, Iliya da Elisha suka kama hanya daga Gilgal. 2Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.
3Akwai wata ƙungiyar annabawa da take a Betel suka zo, suka ce wa Elisha, “Ko ka sani, yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?” Elisha ya ce, “I, na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
4Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Elisha, ina roƙonka ka dakata a nan gama Ubangiji ya aike ni Yariko.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Sai suka tafi Yariko.
5Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?” Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
6Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.
7Waɗansu annabawa hamsin kuma suka tafi tare da su. Iliya da Elisha suka tsaya kusa da kogi, annabawa hamsin ɗin suka tsaya da ɗan nisa. 8Sa'an nan Iliya ya tuɓe alkyabbarsa, ya naɗe ta, ya bugi ruwa da ita, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, dukansu biyu fa suka taka sandararriyar ƙasa suka haye. 9Sa'ad da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka faɗa mini abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga wurinka.” Elisha ya ce, “Bari in sami rabo daga cikin ikonka domin in gaje ka.”
10Iliya kuwa ya ce, “Ka roƙi abu mai wuya, duk da haka, idan ka gan ni lokacin da za a ɗauke ni, to, abin da ka roƙa za ka samu, amma idan ba ka gan ni ba, to, ba za ka samu ba ke nan.”
11Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa. 12Elisha kuwa ya gani, ya yi kuka yana cewa, “Ubana, ubana! Mai ikon tsaron Isra'ila! Ka tafi ke nan!” Bai kuwa ƙara ganin Iliya ba.
Da baƙin ciki Elisha ya kama tufafinsa ya kece. 13Sa'an nan ya ɗauki alkyabbar Iliya wadda ta faɗo daga wurinsa, ya tafi ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun. 14Sai ya ɗauki alkyabban nan da ta faɗo daga wurin Iliya, ya bugi ruwan, yana cewa, “Ina Ubangiji, Allah na Iliya?” Sa'ad da ya bugi ruwan, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, Elisha kuwa ya haye.
15Sa'ad da annabawa hamsin da suke Yariko suka ga ya haye ya nufo su, sai suka ce, “Ai, ruhun Iliya yana kan Elisha.” Sai suka tafi su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa, 16suka kuma ce masa, “Yanzu fa, ga mu mu hamsin ƙarfafa. Bari mu tafi mu nemo maigidanka, mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.” Elisha ya ce, “Kada ku tafi.”
17Amma suka matsa masa har suka i masa, sai ya yardar musu su tafi. Su kuwa suka tafi su hamsin. Suka yi ta neman Iliya, har kwana uku, amma ba su same shi ba. Op 18Sa'an nan suka komo wurinsa a Yariko. Sai ya ce musu, “Ai, dā ma na ce muku kada ku tafi.”
19Waɗansu mutanen gari suka ce wa Elisha, “Ga shi, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba kyau, yana sa ana yin ɓari.”
20Elisha kuwa ya ce, “Ku kawo mini gishiri a sabuwar ƙwarya.” Su kuwa suka kawo masa, 21sai ya tafi maɓuɓɓugar ruwa yana barbaɗa gishirin, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, “‘Na warkar da wannan ruwa, ba zai ƙara sa a mutu ko a yi ɓari ba.”
22Ruwan kuwa ya gyaru bisa ga maganar Elisha, har wa yau.
23Daganan Elisha ya haura zuwa Betel. A hanya sai ga waɗansu samari sun fito daga cikin gari, suna yi masa eho, suna cewa, “Ka bar wurin nan, kai mai saiƙo.”
24Elisha ya waiga, ya gan su, ya la'anta su da sunan Ubangiji. Sai waɗansu namomin jeji guda biyu suka fito daga cikin kurmi suka yayyage arba'in da biyu daga cikin samarin.
25Daganan Elisha ya tafi har Dutsen Karmel, sa'an nan ya koma Samariya.
1A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu. 2Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, amma bai kai na tsohonsa da tsohuwarsa ba, gama ya kawar da ginshiƙin gunkin nan Ba'al wanda tsohonsa ya yi. 3Duk da haka, bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
4Mesha Sarkin Mowab kuwa makiyayin tumaki ni. Yakan ba Sarkin Isra'ila 'yan tumaki dubu ɗari (100,000), da raguna dubu ɗari (100,000) duk da ulunsu, gandu a shekara. 5Amma da Ahab ya rasu, Sarkin Mowab kuwa ya tayar wa Sarkin Isra'ila. 6Sai sarki Yehoram ya fita daga Samariya a lokacin, ya tattara Isra'ila duka. 7Ya kuma aika wa Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ce, “Sarkin Mowab ya tayar mini, ko za ka yarda ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowabawa?” Yehoshafat ya ce, “Zan tafi, ni kamarka ne, mutanena kuma kamar mutanenka, dawakaina kuma kamar naka. 8Wace hanya za mu bi?” Yehoram kuwa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”
9Yehoram Sarkin Isra'ila ya tafi tare da Sarkin Yahuza da Sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha. 10Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya ce, “Kaito! Ubangiji ya kirawo mu sarakunan nan uku don ya bashe mu a hannun Mowabawa.”
11Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji ne a nan, wanda zai tambayar mana Ubangiji?” Sai ɗaya daga cikin fādawan Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, na'ibin Iliya.”
12Yehoshafat kuwa ya ce, “Gaskiya ne, maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sai sarakunan nan uku suka ɗunguma zuwa wurin Elisha. 13Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.” Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, don ya bashe mu a hannun Mowabawa.”
14Elisha ya amsa ya ce, “Na rantse da Ubangiji Mai Runduna, wanda nake bautarsa, da ba domin ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuza ba, da ba zan kula da kai har ma in dube ka ba. 15Amma yanzu ku kawo mini makaɗin garaya.” Da makaɗin garaya ya kaɗa, sai ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha. 16Sai ya ce, “Ubangiji ya ce, “‘Ku haƙa kududdufai a kwarin nan. 17Ko da yake ba ku ga iska, ko ruwan sama ba, duk da haka kwarin zai cika da ruwa domin ku sha, ku da dabbobinku.” 18Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji, zai kuma ba da Mowabawa a hannunku. 19Za ku ci kowane birni mai garu da kowane birni na musamman. Za ku sassare kowane kyakkyawan itace, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku lalatar da gonaki masu kyau da duwatsu.”
20Kashegari, da safe a lokacin miƙa hadaya, sai ga ruwa ya malalo daga wajen Edom har ƙasar ta cika da ruwa.
21Da Mowabawa suka ji labari, sarakuna sun kawo musu yaƙi, sai dukan waɗanda suka isa ɗaukar makamai, daga ƙarami zuwa babba, aka kirawo su, suka ja dāga a kan iyaka. 22Sa'ad da suka tashi da sassafe, rana tana haskaka ruwa, sai suka ga ruwan a gabansu ja wur kamar jini. 23Sai suka ce, “Wannan jini ne, hakika sarakunan sun yi yaƙi da juna, sun karkashe juna. Bari mu tafi mu kwashi ganima!” 24Da suka kai sansanin Isra'ilawa, sai Isra'ilawa suka tashi, suka fāɗa musu, har suka gudu. Isra'ilawa kuwa suka bi su, suna ta karkashe su, 25suka lalatar da biranensu, a kowace kyakkyawar gona kuma, kowannensu ya jefa dutse a cikinta, har aka cika ta da duwatsu, suka kuma tattoshe kowace maɓuɓɓugar ruwa, suka sassare kyawawan itatuwa. Babban birnin Kir-hareset kaɗai ya ragu, Isra'ilawa suka kewaye shi suka fāɗa shi da yaƙi.
26Da Sarkin Mowab ya ga yaƙin ya juya masa baya, sai ya zaɓi masu takobi ɗari bakwai ya kutsa kai a wajen ɓayar Sarkin Edom, amma suka kāsa. 27Sai Sarkin Mowab ya kama babban ɗansa, wanda zai gāji sarautarsa, ya miƙa shi hadayar ƙonawa a kan garu. Isra'ilawa kuwa suka tsorata ko allahn abokan gāba zai cuce su, don haka suka janye, suka koma ƙasarsu.
1Matar wani daga cikin ƙungiyar annabawa da ya rasu, ta kai kuka wurin Elisha, ta ce, “Maigidana, baranka, wato mijina, ya rasu, ka kuwa sani shi mai tsoron Ubangiji ne, amma wanda yake binsa bashi ya zo zai kwashe 'ya'yana biyu su zama bayinsa.”
2Sai Elisha ya ce mata, “Me zan yi miki? Ki faɗa mini abin da kike da shi a gida.” Ta ce, “Ni dai ba ni da kome a cikin gidan, sai dai kurtun mai.”
3Sa'an nan ya ce mata, “Ki tafi ki yi aron tandaye da yawa daga maƙwabtanki waɗanda ba kome a ciki. 4Sa'an nan ki shiga ɗaki, ke da 'ya'yanki, ku rufe ƙofa. Ki ɗura mai cikin tandayen nan duka, bi da bi.”
5Sai ta tashi daga wurinsa, ta tafi ta shiga ɗaki tare da 'ya'yanta, ta rufe ƙofar. 'Ya'yan suna kawo tandaye tana ɗurawa. 6Da tandayen suka cika ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tandu.” Ɗan kuwa ya ce mata, “Ai, ba saura.” Sai man ya janye.
7Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da 'ya'yanki.”
8Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci. 9Sai ta ce wa mijinta, “Na gane wannan mutum adali ne, mutumin Allah, wanda kullum yakan wuce ta hanyan nan. 10Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa'ad da ya zo ya sauka a wurin.”
11Wata rana da Elisha ya zo, ya shiga ɗakin, ya huta. 12Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa. 13Ya ce wa Gehazi, “Ka tambaye ta me take so in yi mata saboda dukan wannan wahala da ta yi dominmu? Tana so in yi mata magana da sarki ko da shugaban sojoji?” Sai ta ce, “Ai, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama'ata.”
14Elisha ya ce, “To, me za a yi mata?” Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Ai, ba ta da ɗa, mijinta kuwa tsoho ne.”
15Sai ya ce, “Kirawo ta.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a ƙofar ɗakin. 16Elisha kuwa ya ce mata, “Baɗi war haka za ki rungumi ɗa na kanki.” Sai ta ce, “A'a, ya shugabana, mutumin Allah, kada fa ka yi mini ƙarya.”
17Amma macen ta sami juna biyu, ta kuwa haifi ɗa a daidai lokacin da Elisha ya faɗa mata.
18Da yaron ya yi girma, sai wata rana ya bi mahaifinsa gona zuwa wurin masu girbi. 19Sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo, kaina, kaina.” Uban kuwa ya ce wa baransa, “Ka ɗauke shi, ka kai shi wurin uwar.”
20Da aka ɗauke shi, aka kai wa uwar, sai ya zauna a cinyar uwar har rana tsaka, sa'an nan ya rasu. 21Sai ta hau, ta kwantar da shi a gadon annabi Elisha, sa'an nan ta rufe ƙofa, ta fita. 22Sa'an nan ta aika a faɗa wa mijinta, ta ce, “Ka aiko mini ɗaya daga cikin barori da jaki domin in tafi wurin annabi Elisha, zan komo da sauri.”
23Sai ya ce, “Me ya sa za ki tafi wurinsa yau? Ai, yau ba amaryar wata ba ce, ba kuwa ranar Asabar ba ce.” Ita kuwa ta ce, “Ba kome, kada ka damu.” 24Amma ta yi wa jakin shimfiɗa, ta kuma ce wa baranta, “Yi ta kora mini jakin, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.” 25Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel. Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can. 26Ruga ka tarye ta, ka tambayi lafiyarta, da ta mijinta, da ta ɗanta.” Ta amsa, ta ce, “Lafiya ƙalau.”
27Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”
28Matar ta ce masa, “Na roƙe ka ka ba ni ɗa ne? Ashe, ban ce maka kada ka ruɗe ni ba?”
29Elisha ya ce wa Gehazi, “Yi ɗamara, ka ɗauki sandana ka tafi. Duk wanda ka gamu da shi, kada ka gaishe shi, duk kuma wanda ya gaishe ka kada ka amsa, ka tafi ka ɗora sandana a fuskar yaron.”
30Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta. 31Gehazi kuma ya yi gaba, ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma ba motsi ko alamar rai. Saboda haka ya koma, ya taryi Elisha, ya faɗa masa yaron bai farka ba.
32Da Elisha ya kai ɗakin, ya ga yaron yana kwance matacce a gadonsa. 33Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu'a ga Ubangiji. 34Sa'an nan ya kwanta a kan yaron, ya sa bakinsa a bakin yaron, ya sa idanunsa a idanun yaron, hannuwansa kuma a kan na yaron, ya miƙe jikinsa akan yaron, sai jikin yaron ya yi ɗumi. 35Elisha ya tashi, ya yi ta kai da komowa a cikin gidan, sa'an nan ya sāke hawan ɗakin, ya miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu. 36Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.” 37Ta kuwa zo, ta faɗi a gaban Elisha har ƙasa, sa'an nan ta ɗauki ɗanta, ta fita.
38Elisha kuwa ya koma Gilgal sa'ad da ake fama da yunwa a ƙasar. Sa'ad da ƙungiyar annabawa ke zaune a gabansa, sai ya ce wa baransa, “Dora babbar tukunya, ka dafa wa annabawan nan fate-fate.”
39Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo 'ya'yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba. 40Amma da suka ɗanɗana, sai suka ta da murya suka ce, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyar nan!” Ba su iya cin abincin ba.
41Sai Elisha ya ce, “To, ku kawo gari.” Aka kawo masa, ya kuwa zuba garin a tukunyar, sa'an nan ya ce, “Ku kwaso wa mutanen. Yanzu dai kome lafiya.”
42Wani mutum ya zo daga Ba'alshalisha ya kawo wa annabi Elisha abinci na 'ya'yan fari, da dunƙule ashirin na sha'ir, da ɗanyun zangarkun hatsi. Sai Elisha ya ce wa baransa, ya ba ƙungiyar annabawa su ci, 43amma baran ya ce, “Ƙaka zan raba wa mutum ɗari wannan abinci?” Elisha ya sāke cewa, “Ka ba mutane su ci, gama Ubangiji ya ce za su ci har su bar saura.” 44Sai ya ajiye shi a gabansu. Suka ci, suka kuwa bar saura kamar yadda Ubangiji ya faɗa.
1Na'aman kuwa, shugaban sojojin Sarkin Suriya, shi babba ne mai farin jini ƙwarai a wurin ubangidansa, dominta wurinsa ne Ubangiji ya ba Suriyawa nasara. Shi mutum ne ƙaƙƙarfan jarumi, amma kuma kuturu ne. 2Daga cikin hare-haren da Suriyawa suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra'ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na'aman aiki. 3Wata rana sai ta ce wa uwargijyarta, “Da a ce ubangijina yana tare da annabin nan wanda yake Samariya, da ya warkar da shi daga kuturtarsa!”
4Na'aman kuwa ya tafi, ya faɗa wa ubangidansa, ya ce, “Ka ji abin da yarinyan nan ta ƙasar Isra'ila ta ce?”
5Sai Sarkin Suriya ya ce, “Ka tafi yanzu, zan aika wa Sarkin Isra'ila da takarda.” Na'aman kuwa ya ɗauki azurfa na talanti goma, zinariya kuma na shekel dubu shida (6,000), da rigunan ado guda goma, ya kama hanya. 6Ya kai wa Sarkin Isra'ila tarkardar, wadda ta ce, “Sa'ad da wannan takarda ta sadu da kai, ka sani fa, ni ne na aiko barana, Na'aman, wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa.”
7Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”
8Amma sa'ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra'ila.”
9Na'aman kuwa da dawakansa da karusansa suka tafi suka tsaya a ƙofar gidan Elisha. 10Sai Elisha ya aiki manzo ya faɗa wa Na'aman ya tafi, ya yi wanka a Kogin Urdun har sau bakwai, naman jikinsa zai warke, zai tsarkaka. 11Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni. 12Ashe, kogin Abana da na Farfar, wato kogunan Dimashƙu, ba su fi dukan ruwayen Isra'ila ba? Da ban yi wanka a cikinsu na tsarkaka ba?” Ya juya, ya yi tafiyarsa da fushi.
13Amma barorinsa suka je wurinsa, suka ce masa, “Ranka ya daɗe, da a ce annabin ya umarce ka ka yi wani babban abu ne, ashe, da ba ka yi ba, balle wannan, da ya ce ka tafi ka yi wanka, ka tsarkaka?” 14Sai ya tafi ya yi wanka har sau bakwai a Kogin Urdun bisa ga maganar annabin Allah, sai naman jikinsa ya warke ya zama kamar na ƙaramin yaro, ya tsarkaka.
15Ya kuwa komo wurin annabi Elisha shi da jama'arsa duka, ya zo ya tsaya a gabansa, ya ce, “Yanzu na sani a duniya duka ba wani Allah banda na Isra'ila, saboda haka, sai ka karɓi kyauta daga wurina.”
16Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.” Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi. 17Na'aman kuwa ya ce, “Da yake ka ƙi ka karɓa, ina roƙonka, ka ba baranka labtun alfadari biyu na ƙasa, gama nan gaba baranka ba zai ƙara miƙa hadaya ta ƙonawa ko baiko ga wani gunki ba, sai dai Ubangiji. 18Sai dai Ubangiji ya gafarta mini lokacin da na bi sarki zuwa cikin haikalin Rimmon, gunkin Suriya, don ya yi sujada. Na gaskata Ubangiji zai gafarta mini.”
19Elisha kuwa ya ce masa, “Ka sauka lafiya.” Na'aman ya tafi. Amma tun Na'aman bai yi nisa ba, 20sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.” 21Gehazi kuwa ya bi bayan Na'aman. Da Na'aman ya ga wani yana biye da shi a guje, sai ya sauka daga karusarsa, ya juya ya tarye shi, ya ce, “In ce ko lafiya?”
22Gehazi ya ce, “Lafiya ƙalau, maigidana ne ya aiko ni in faɗa maka, yanzu yanzu waɗansu samari biyu daga ƙungiyar annabawa suka zo wurinsa daga ƙasar tudu ta Ifraimu, yana roƙonka, ka ba ni talanti ɗaya na azurfa da rigunan ado guda biyu in kai masa.”
23Na'aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida. 24Sa'ad da Gehazi ya kai tudu, sai ya karɓi kayan daga hannunsu, ya ajiye a gida, sa'an nan ya sallame su, suka tafi.
25Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?” Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”
26Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba, sa'ad da mutumin ya juyo daga karusarsa don ya tarye ka? Wannan shi ne lokacin karɓar kuɗi, da riguna, da gonaki na zaitun, da na inabi, da tumaki, da shanu, da barori mata da maza? 27Saboda haka kuturtar Na'aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.” Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.
1Ƙungiyar annabawa da ke a hannun Elisha suka kawo masa kuka, suka ce, “Ga shi, wurin da muke zaune ya yi mana kaɗan. 2Ka ba mu izini mu tafi Kogin Urdun, domin mu saro gumagumai a can, mu ƙara wa kanmu wurin zama.” Sai ya ce, “Ku tafi.”
3Ɗaya daga cikinsu kuwa ya ce, “In ka yarda, ka tafi tare da mu.” Elisha kuwa ya yarda, ya ce, “To, mu tafi.” 4Ya kuwa tafi tare da su. Sa'ad da suka isa Urdun, suka sassari itatuwa. 5Amma sa'ad da ɗaya daga cikinsu yake saran wani gungume, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe ya fāɗa a ruwa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Wayyo, maigida, me zan yi? Abin aro ne.”
6Sa'an nan Elisha ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai ya karyi tsumagiya, ya jefa a wurin, ya sa ruwan gatarin ya taso bisa kan ruwan. 7Sa'an nan ya ce, “Ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu, ya ɗauka.
8Wata rana, sa'ad da Sarkin Suriya yake yaƙi da Isra'ila, sai ya shawarci fādawansa, suka zaɓi wurin da za su kafa sansani. 9Amma Elisha ya aika wa Sarkin Isra'ila, ya ce, “Ka yi hankali, kada ka wuce wuri kaza, gama Suriyawa suna gangarawa zuwa can.” 10Sarkin Isra'ila kuwa ya aika zuwa wurin da Elisha ya faɗa masa. Da haka ya riƙa faɗakar da shi, har ya ceci kansa ba sau ɗaya, ba sau biyu ba.
11Zuciyar Sarkin Suriya kuwa ta ɓaci ƙwarai a kan wannan al'amari, don haka ya kirawo fādawansa, ya ce musu, “Wane ne wannan da yake cikinmu, yana goyon bayan Sarkin Isra'ila?”
12Ɗaya daga cikin fādawan ya ce, “A'a, ranka ya daɗe, sarki, ai, annabi Elisha ne wanda yake cikin Isra'ila, yake faɗa wa Sarkin Isra'ila maganar da kake faɗa a ɗakin kwananka.”
13Sai ya ce, “Ku tafi, ku ga inda yake don in aika a kamo shi.” Aka faɗa masa, cewa a Dotan yake. 14Sai ya aika da dawakai, da karusai, da sojoji da yawa. Suka tafi da dare suka kewaye garin. 15Da baran annabi Elisha ya tashi da sassafe, ya fita waje, sai ga sojoji, da dawakai, da karusai sun kewaye gari. Sai baran ya ce, “Wayyo, maigidana! Me za mu yi?”
16Elisha kuwa ya ce masa, “Kada ka ji tsoro gama waɗanda suke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.” 17Sa'an nan Elisha ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa ya gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin, sai ga dutsen cike da dawakai da karusan wuta kewaye da Elisha.
18Da Suriyawa suka gangaro wurinsa, sai Elisha ya yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ka bugi mutanen nan da makanta.” Ubangiji kuwa ya buge su da makanta bisa ga addu'ar Elisha. 19Sa'an nan Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, ni kuwa in kai ku wurin mutumin da kuke nema.” Sai ya kai su Samariya.
20Da shigarsu Samariya, sai Elisha, ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanun mutanen nan su gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanunsu, suka gani, ashe, suna tsakiyar Samariya ne.
21Da Sarkin Isra'ila ya gan su, sai ya ce wa Elisha, “Ya mai girma, in karkashe su? In karkashe su?”
22Amma Elisha ya ce, “Ba za ka karkashe su ba. Ba za ka karkashe waɗanda ba kai ka kama su ta wurin takobinka ko bakanka ba. Ka ba su abinci da ruwa su ci su sha, su koma wurin shugabansu.” 23Sai ya shirya musu babbar liyafa. Sa'ad da suka ci suka sha, sai ya sallame su, suka koma wurin shugabansu. Suriyawa kuwa ba su ƙara dai wa ƙasar Isra'ila hari ba.
24Bayan wannan kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tattara sojojinsa duka, ya haura ya kewaye Samariya da yaƙi. 25Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.
26Sa'ad da Sarkin Isra'ila yake wucewa ta kan garun birni, sai wata mace ta yi masa kuka, ta ce, “Ka yi taimako, ran sarki ya daɗe.”
27Shi kuwa ya ce, “Idan Ubangiji bai taimake ki ba, ƙaƙa zan yi, ni in taimake ki? Ina da alkama ne ko kuwa ina da ruwan inabi? 28Me yake damunki?” Sai ta amsa, ta ce, “Wannan mace ta ce mini, in kawo ɗana mu ci yau, gobe kuma mu ci nata. 29Sai muka dafa ɗana muka cinye. Kashegari kuwa na ce mata ta kawo ɗanta mu ci, amma sai ta ɓoye shi.”
30Da sarki ya ji maganar macen, sai ya keta tufafinsa, sa'ad da yake wucewa ta kan garun birni. Sai mutane suka gani, ashe, yana saye da rigar makoki a ciki. 31Ya ce, “Allah ya yi mini hukunci mai tsanani, idan ban fille kan Elisha ɗan Shafat yau ba.”
32Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”
33Yana magana da su ke nan, sai sarki ya iso, ya ce, “Wannan masifa daga wurin Ubangiji ta fito, don me zan ƙara jiran Ubangiji kuma?”
1Amma Elisha ya ce, “Kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce! Gobe war haka za a sayar da mudu na lallausan gari a bakin shekel guda, da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel guda a ƙofar garin Samariya.”
2Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”
3Akwai mutum huɗu, kutare, waɗanda suke zaune a bakin ƙofar gari, sai suka ce wa junansu, “Me ya sa muke zaune nan har mu mutu? 4Idan mun ce, “‘Bari mu shiga birni,” yunwa tana birnin, za mu mutu a wurin. Idan kuma mun zauna a nan za mu mutu. Saboda haka bari mu tafi sansanin Suriyawa, idan sun bar mu da rai, za mu rayu, idan kuwa sun kashe mu, za mu mutu.”
5Sai suka tashi da magariba, suka tafi sansanin Suriyawa. Da suka isa gefen sansanin Suriyawa, sai suka tarar ba kowa a wurin, 6gama Ubangiji ya sa sojojin Suriyawa suka ji amon karusai, da na dawakai, da na babbar rundunar soja. Sai suka ce wa junansu, “Ai, Sarkin Isra'ila, ya yi ijara da sarakunan Hittiyawa, da na Masarawa, su zo su fāɗa mana.” 7Saboda haka suka gudu da almuru, suka bar alfarwansu, da dawakansu, da jakunansu, suka bar sansanin yadda yake, suka tsira da rayukansu.
8Sa'ad da kutaren nan suka zo sansanin, sai suka shiga wata alfarwa, suka ci suka sha. Suka kwashe azurfa, da zinariya, da tufafi, suka tafi suka ɓoye. Suka koma suka shiga wata alfarwa kuma, suka kwashe abubuwan da suke cikinta. Suka tafi suka ɓoye su. 9Sa'an nan suka ce wa junansu, “Ba mu kyauta ba. Yau ranar albishir ce, idan mun yi shiru, mun jira har safe, wani mugun abu zai same mu. Domin haka bari mu tafi mu faɗa a gidan sarki.” 10Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”
11Sa'an nan masu tsaron ƙofar birnin suka aika a faɗa a gidan sarki. 12Sai sarki ya tashi da dare ya ce wa fādawansa, “Bari in faɗa muku irin shirin da Suriyawa suka yi a kanmu. Sun sani muna fama da yunwa, domin haka suka fita daga sansanin suka ɓuya a karkara, suna nufin sa'ad da muka fita daga birnin, sai su kama mu da rai, sa'an nan su shiga birnin.”
13Ɗaya daga cikin fādawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birnin, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra'ilawan da suka riga suka mutu. Bari mu aika, mu gani.” 14Aka ɗibi mahayan dawakai biyu, sarki kuwa ya aike su, su bi bayan sojojin Suriyawa, ya ce musu, “Ku tafi, ku gani.” 15Sai suka bi bayansu har zuwa Kogin Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko'ina a hanya, waɗanda Suriyawa suka zubar lokacin da suke gudu. Sai manzannin suka komo suka faɗa wa sarki. 16Sa'an nan mutane suka fita, suka washe sansanin Suriyawa. Aka kuwa sayar da mudu na lallausan gari da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel ɗaya ɗaya kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa.
17Sarki kuwa ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa'ad da sarki ya tafi wurinsa. 18Ya faru daidai yadda annabi Elisha ya ce wa sarki, “Za a sayar da mudu biyu na sha'ir, da mudu na lallausan gari a bakin shekel ɗaya ɗaya gobe war haka a ƙofar birnin Samariya.”
19Dogarin ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji da kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu zai yiwu ke nan?” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka amma ba za ka ci ba.” 20Haka kuwa ya zama gama mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu.
1Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.” 2Sai matar ta tashi, ta yi kamar yadda annabi Elisha ya faɗa mata. Ta tafi, ita da iyalinta suka zauna a ƙasar Filistiyawa har shekara bakwai.
3A ƙarshen shekara bakwai ɗin, matar ta komo daga ƙasar Filistiyawa, ta tafi wurin sarki, ta roƙe shi a mayar mata da gidanta da gonarta. 4A lokacin kuwa sarki yana tare da Gehazi, wato baran annabi Elisha, ya ce, “Ka faɗa mini dukan mu'ujizan da Elisha ya yi.”
5A sa'ad da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya ta da matacce, sai ga matar da ya ta da ɗanta daga matattu, ta zo ta roƙi sarki ya mayar mata da gidanta da gonarta. Sai Gehazi ya ce, “Ran sarki ya daɗe, ai, ga matar, ga kuma yaronta wanda Elisha ya tashe shi daga matattu.” 6Da sarki ya tambayi matar sai ta faɗa masa dukan labarin. Sarki kuwa ya sa wani bafade ya mayar mata da dukan abin da yake nata da dukan amfanin gonakin, tun daga ran da ta bar ƙasar har ranar da ta komo.
7Elisha kuwa ya tafi Dimashƙu. A lokacin kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, yana ciwo. Aka faɗa masa cewa, annabi Elisha ya zo, yana nan, 8sai sarki ya ce wa Hazayel, ɗaya daga cikin fādawansa, “Ka ɗauki kyauta, ka tafi wurin annabin Allah ka sa ya roƙar mini Ubangiji ko zan warke daga wannan cuta.”
9Hazayel kuwa ya tafi wurin Elisha tare da kyauta iri iri na kayan Dimashƙu. Raƙuma arba'in ne suka ɗauko kayan. Da ya tafi ya tsaya a gabansa, ya ce, “Danka, Ben-hadad Sarkin Suriyawa, ya aiko ni wurinka don yana so ya ji ko zai warke daga wannan cuta.”
10Elisha kuwa ya ce masa, “Tafi ka faɗa masa zai warke, amma Ubangiji ya nuna mini lalle zai mutu.”
11Sai Elisha ya kafa wa Hazayel ido, yana kallonsa, har Hazayel ya ji kunya. Elisha kuwa ya fashe da kuka. 12Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”
13Hazayel kuwa ya ce, “Ni wane ne? Ina na sami wannan iko? Ni ba kome ba ne.” Elisha ya amsa ya ce, “Ubangiji ya nuna mini za ka zama Sarkin Suriya.”
14Sa'an nan Hazayel ya tashi daga wurin Elisha ya koma wurin Ben-hadad. Ben-hadad ya tambaye shi, “Me Elisha ya faɗa maka?” Sai ya ce, “Ya faɗa mini, cewa lalle za ka warke.”
15Amma kashegari sai Hazayel ya ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa, sa'an nan ya rufe fuskar sarki da shi har ya mutu. Sai ya hau gadon sarautarsa.
(2 Tar 21.1-20)
16A shekara ta biyar ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 17Yana da shekara talatin da biyu da haihuwa sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi shekara takwas yana sarauta a Urushalima. 18Ya bi halin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama ya auri 'yar Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji. 19Duk da haka Ubangiji bai hallaka Yahuza ba, saboda bawansa Dawuda, tun da yake ya alkawarta zai ba shi haske, shi da 'ya'yansa har abada.
20A zamanin Yoram, Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki. 21Sa'an nan Yoram ya haye zuwa Zayar tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare da shugabannin karusansa, ya bugi Edomawan da suka kewaye shi, amma sojojinsa suka gudu zuwa alfarwansu. 22Haka kuwa Edom ta tayar wa Yahuza har wa yau. Alokacin kuma Libna ta tayar wa Yahuza.
23Sauran ayyukan Yoram da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 24Yoram kuwa ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Ahaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.
(2 Tar 22.1-6)
25A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 26Ya ci sarauta yana da shekara ashirin da biyu da haihuwa, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikanyar Omri, Sarkin Isra'ila. 27Ya ɗauki halin gidan Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda gidan ahab ya yi, gama shi surukin gidan Ahab ne.
28Sarki Ahaziya kuwa ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab don su yi yaƙi da Hazayel, Sarkin Suriya, a Ramot cikin Gileyad. Suriyawa suka yi wa Yehoram rauni. 29Sai sarki Yehoram ya koma zuwa Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da yake yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya, ɗan Yoram, Sarkin Yahuza ya tafi ya ziyarci Yehoram ɗan Ahab cikin Yezreyel saboda yana ciwo.
1Elisha kuwa ya kirawo ɗaya daga cikin annabawa matasa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kurtun mai, ka tafi Ramot-gileyad. 2Sa'ad da ka isa can, sai ka nemi Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ka shiga, ka sa ya tashi daga wurin abokansa, ka kai shi cikin ɗaki. 3Sa'an nan ka ɗauki kurtun man, ka zuba masa a ka, ka ce, “‘Ubangiji ya ce ya keɓe ka Sarkin Isra'ila.” Sa'an nan ka buɗe ƙofa, ka gudu, kada ka tsaya.”
4Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad. 5Sa'ad da ya isa, sai ga shugabannin sojoji suna taro. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka, ya shugaba.” Yehu kuwa ya ce, “Wane ne a cikinmu?” Sai ya ce, “Kai ne, ya shugaba.” 6Sai Yehu ya tashi ya shiga ɗaki, saurayin kuwa ya zuba masa mai a ka, ya ce, “Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya keɓe ka sarkin jama'arsa, wato Isra'ila. 7Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel. 8Gama dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan datse wa Ahab kowane ɗa namiji, bawa ko 'yantacce, cikin Isra'ila. 9Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yeroboam ɗan Nebat, da kuma kamar gidan Ba'asha ɗan Ahija. 10Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa'an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.
11Da Yehu ya fita zuwa wurin sauran shugabannin, sai suka tambaye shi, “Lafiya kuwa, me ya sa mahaukacin nan ya zo wurinka?” Sai ya ce musu, “Ai, kun san mutumin da irin maganarsa.”
12Suka ce, “Ba mu sani ba, sai ka faɗa mana.” Shi kuwa ya ce, “Ya faɗa mini, cewa Ubangiji ya ce ya keɓe ni Sarkin Isra'ila.”
13Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa'an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”
14Ta haka Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ya tayar wa Yehoram. A lokacin, Yehoram tare da dukan Isra'ila suna tsaron Ramot-gileyad, don kada Hazayel, Sarkin Suriya, ya fāɗa mata. 15Amma sarki Yehoram ya komo Yezreyel, don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da ya yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Yehu ya ce, “Idan wannan shi ne nufinku, to, kada kowa ya zurare, ya tafi, ya ba da labari a Yezreyel.” 16Sa'an nan Yehu ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel, gama a can ne Yehoram yake kwance. Ahaziya Sarkin Yahuza ya gangara don ya gai da Yehoram.
17Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezreyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa'ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yehoram ya ce, “Ka aiki wani, ya hau doki, ya tafi ya tarye su, ya tambaye su, ko lafiya.”
18Sai wani mutum ya hau doki ya tafi ya tarye su, ya ce, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?” Sai Yehu ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.” Mai tsaro kuma ya ce, “Manzo ya kai wurinsu, amma bai komo ba.”
19Ya kuma aiki wani, na biyu, a kan doki, ya je wurinsu ya ce musu, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?” Yehu ya amsa, ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”
20Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”
21Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa'an nan Yehoram Sarkin Isra'ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel. 22Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?” Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?”
23Yehoram kuwa ya juyar da karusarsa baya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Maƙarƙashiya ce, ya Ahaziya!” 24Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa. 25Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa'ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa, 26“‘Hakika, kamar yaddajiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.” Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
(2 Tar 22.7-9)
27Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan. Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can. 28Fādawansa suka ɗauke shi a cikin karusar zuwa Urushalima, suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.
29Ahaziya ya ci sarautar Yahuza a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Yehoram ɗan Ahab.
30Da Yezebel ta ji Yehu ya zo Yezreyel, sai ta shafa wa idanunta launi, ta gyara gashin kanta, sa'an nan ta leƙa ta taga. 31Da Yehu ya shiga ƙofar garin, sai ta ce, “Kai Zimri, mai kashe maigidansa, me kake yi a nan?”
32Sai ya ɗaga idanunsa wajen tagar, ya ce, “Wa yake wajena?” Sai babani biyu ko uku suka dube shi, 33shi kuwa ya ce, “Ku wurgo ta ƙasa.” Sai suka wurgo ta ƙasa. Jininta ya fantsama a jikin bangon da jikin dawakan da suka tattake ta. 34Sa'an nan Yehu ya shiga gida, ya ci ya sha, ya ce, “Ku san yadda za ku yi da wannan la'ananniyar mace, ku binne ta, gama ita 'yar sarki ce.” 35Amma da suka tafi don su binne ta, ba su tarar da kome ba sai ƙwaƙwalwa, da ƙafafu, da tafin hannuwanta. 36Sai suka komo, suka faɗa masa. Sai ya ce musu, “Wannan, ai, faɗar Ubangiji, wadda ya faɗa ta bakin bawansa Iliya Batishbe, ya ce, “‘Karnuka za su cinye naman Yezebel a cikin Yezreyel. 37Gawar Yezebel za ta zama wa ƙasa taki a Yezreyel don kada wani ya iya cewa wannan ita ce Yezebel.”
1Ahab yana da 'ya'ya maza saba'in a Samariya, sai Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika zuwa Samariya wurin shugabanni da dattawan birni, da masu lura da 'ya'yan Ahab. 2Ya ce, “Yanzu dai, da zarar wasiƙun nan sun iso wurinku, da yake kuke lura da 'ya'yan Ahab, kuna kuma da karusai, da dawakai, da kagara, da makamai, 3sai ku zaɓi wanda ya fi dacewa duka daga cikin 'ya'yan Ahab, ku naɗa shi sarki, ku yi yaƙi, domin ku tsare gidan Ahab.”
4Amma suka ji tsoro ƙwarai, suka ce, “Ga shi, sarakuna biyu ba su iya karawa da shi ba, balle mu.” 5Sai wakilin gidan, da wakilin birnin, da dattawa, da masu lura da 'ya'yan sarki, suka aika wurin Yehu suka ce, “Mu barorinka ne, duk abin da ka umarce mu, za mu yi. Ba za mu naɗa wani sarki ba, sai ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”
6Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.” 'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su. 7Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.
8Da aka faɗa masa cewa an kawo kawunan 'ya'yan sarki, sai ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar garin har safiya.” 9Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan? 10Ku sani fa ba maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Ahab da ba za ta cika ba, gama Ubangiji ya aikata abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya.” 11Haka kuwa Yehu ya karkashe waɗanda suka ragu na gidan Ahab a Yezreyel, wato dukan manyan mutanensa, da abokansa, da firistocinsa. Bai rage masa ko guda ba.
12Yehu kuma ya fita zai tafi Samariya. A hanya, sa'ad da yake a Bet-eked ta makiyaya, 13sai ya sadu da 'yan'uwan Ahaziya Sarkin Yahuza, sai ya ce, “Ku su wane ne?” Sai suka amsa, “Mu 'yan'uwan Ahaziya ne, mun zo mu gai da 'ya'yan sarki ne da 'ya'yan sarauniya.”
14Yehu kuwa ya ce, “Ku kama su da rai.” Sai suka kama su da rai, suka karkashe su a ramin Bet-eked, su arba'in da biyu ne, ba a rage ko ɗaya a cikinsu ba.
15Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa. 16Ya ce, “Ka zo tare da ni, ka ga kishin da nake da shi domin Ubangiji.” Sai suka tafi cikin karusarsa. 17Da suka isa Samariya, sai ya kashe duk wanda ya ragu na gidan Ahab a Samariya. Ya share mutanen gidan Ahab kaf kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi Iliya.
18Yehu kuwa ya tara mutane duka, ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba'al kaɗan, amma Yehu zai bauta masa da yawa. 19Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada. 20Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba'al. Aka kuwa kira taron, 21sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan. 22Sa'an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin. 23Bayan wannan Yehu ya shiga haikalin Ba'al tare da Yehonadab ɗan Rekab, ya ce wa masu yi wa Ba'al sujada, “Ku bincike, ku tabbata, ba wani bawan Ubangiji tare da ku, sai dai masu yi wa Ba'al sujada kaɗai.” 24Sa'an nan Yehu da Yehonadab suka shiga don su miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Yehu ya riga ya sa mutum tamanin a waje, ya ce musu, “Mutumin da ya bar wani daga cikin waɗanda na bashe su a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”
25Nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya ta ƙonawa, sai ya ce wa mai tsaro da shugabannin, “Ku shiga, ku karkashe su, kada ku bar wani ya tsere.” Da suka karkashe su, sai suka fitar da su waje, sa'an nan suka shiga can cikin haikalin Ba'al. 26Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su. 27Suka yi kaca kaca da gunkin Ba'al da haikalinsa, suka mai da haikalin ya zama salga har wa yau.
28Yehu ya kawar da Ba'al daga cikin Isra'ila. 29Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan. 30Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, 'ya'yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra'ila.” 31Amma Yehu bai mai da hankali ya yi tafiya a tafarkin Ubangiji Allah na Isra'ila da zuciya ɗaya ba. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi.
32A kwanakin an Ubangiji ya soma rage ƙasar Isra'ila. Hazayel kuwa ya yaƙe su a karkarar Isra'ila, 33tun daga Urdun har zuwa wajen gabas, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Gad, da ta Ra'ubainu, da ta Manassa, tun daga Arower wadda take kusa da kwarin Arnon haɗe da Gileyad da Bashan.
34Sauran ayyukan Yehu da dukan abin da ya yi, da dukan ƙarfinsa an rubuta su a littafin tarihin sarakuna Isra'ila. 35Yehu kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowahaz ɗansa ya gaji sarautarsa. 36Yehu ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shekara ashirin da takwas.
(2 Tar 22.10ū23.15)
1Sa'ad da Ataliya, uwar Ahaziya, ta ga ɗanta ya rasu, sai ta tashi ta hallaka dukan 'ya'yan sarauta. 2Amma Yehosheba 'yar sarki Yoram, 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba. 3Ya zauna tare da ita shekara shida a ɓoye, a cikin Haikalin Ubangiji sa'ad da Ataliya take mulkin ƙasar.
4A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya aika ya kawo shugabannin Keretiyawa da na masu tsaro a Haikalin Ubangiji. Ya yi alkawari da su, ya sa suka yi rantsuwa a Haikalin Ubangiji, sa'an nan ya nuna musu ɗan sarki. 5Ya kuma umarce su cewa, “Abin da za ku yi ke nan, sai sulusinku da sukan zo aiki a ranar Asabar, su yi tsaron gidan sarki. 6Sulusinku kuma zai kasance a ƙofar Sur. Ɗaya sulusin kuma zai kasance a bayan masu tsaro, haka za ku yi tsaron gidan, ku tsare shi. 7Ƙungiyarku biyu kuma waɗanda sukan tashi aiki ran Asabar, za su yi tsaron Haikalin Ubangiji da kuma sarki. 8Za ku kewaye sarki, kowane mutum ya riƙe makaminsa. Duk wanda ya yi ƙoƙari ya zo kusa, sai a kashe shi. Sai ku kasance tare da sarki duk lokacin da zai fita da duk lokacin da zai shiga.”
9Shugabannin fa suka aikata bisa ga dukan abin da Yehoyada firist ya umarta. Kowa ya zo duk da mutanensa waɗanda za su huta aiki ran Asabar tare da waɗanda za su yi aiki ran Asabar, suka zo wurin Yehoyada. 10Firist kuwa ya ba shugabannin māsu da garkuwoyin Dawuda waɗanda suke cikin Haikalin Ubangiji. 11Matsara suka tsaya, kowa da makaminsa a hannu, daga wajen kudu na Haikalin zuwa wajen arewa. Suka kewaye bagade da Haikali. 12Sa'an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kurma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa'an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”
13Da Ataliya ta ji muryoyin matsara da na jama'a, sai ta zo wurin mutane a Haikalin Ubangiji. 14Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”
15Yehoyada, firist kuwa, ya umarci shugabannin sojoji, ya ce, “Ku fitar da ita daga nan, duk kuma wanda yake son kāre ta, ku sa takobi ku kashe shi.” Ya kuma ce, “Kada a kashe ta a Haikalin Ubangiji.” 16Suka kama ta, suka fitar da ita ta ƙofar dawakai zuwa gidan sarki, can suka kashe ta.
(2 Tar 23.16-21)
17Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama'a, yadda za su zama jama'ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama'a. 18Sai dukan jama'ar ƙasa suka tafi haikalin Ba'al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagaden. Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji, 19ya kuma sa shugabanni, da Keretiyawa, da matsara, da dukan jama'ar ƙasar, su fito da sarki daga Haikalin Ubangiji, suka rufa masa baya ta ƙofar matsara zuwa gidan sarki. Suka sa shi a gadon sarautar sarakuna. 20Dukan jama'ar ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya huta bayan da an kashe Ataliya a gidan sarki.
(2 Tar 24.1-27)
21Yowash yana da shekara bakwai sa'ad da ya ci sarauta.
1A shekara ta bakwai ta sarautar Yehu, Yowash ya ci sarautar. Ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya ta Biyer-sheba. 2Yowash kuwa ya yi abin da yake daidai ga Ubangiji dukan kwanakinsa, domin Yehoyaka, firist, ya koya masa. 3Duk da haka ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba, mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a kan tuddan.
4Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali, 5sai ku karɓa daga junanku, don a gyara duk inda ake bukatar gyara a Haikalin.”
6Amma har a shekara ta ashirin da uku ta sarautar sarki Yowash, firistocin ba su yi wani gyara a Haikalin ba. 7Saboda haka Yowash ya kirawo Yehoyada, firist, da sauran firistoci, ya ce musu, “Me ya sa ba ku gyara Haikalin? Daga yanzu kada ku karɓi kuɗi daga wurin abokanku, sai in za ku ba da shi domin gyaran Haikalin.” 8Firistocin kuwa suka yarda, ba za su karɓi kuɗi daga wurin jama'a ba, ba su kuwa gyara Haikalin ba.
9Sa'an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa'an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji. 10Sa'ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da suke a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka. 11Sa'an nan suka ba da kuɗin da aka ƙirga a hannun waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji, domin su biya masassaƙan katakai, da masu haɗawa da suke aikin Haikalin Ubangiji, 12da masu gini, da masu sassaƙa duwatsu, a kuma sayi katako da sassaƙaƙƙun duwatsu don gyaran Haikalin Ubangiji, da kowane irin abu da ake bukata domin gyaran Haikalin. 13Amma ba a mori kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji domin yin kwanonin azurfa, da abin katse fitila, da tasoshi, da ƙahoni, da kwanonin zinariya ko na azurfa ba. 14Gama an ba da kuɗin ga ma'aikatan da suke gyaran Haikalin ubangiji. 15Ba a nemi lissafin kuɗin a wurin mutanen da aka ba su kuɗin don su biya ma'aikatan ba, gama su amintattu ne. 16Ba a kawo kuɗi na hadaya don laifi da hadaya don zunubi a cikin Haikalin Ubangiji ba, ya zama na firistoci.
17Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima. 18Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.
19Sauran ayyukan Yowash da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20Fādawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidan da yake Millo, a kan hanyar da ta nufi Silla. 21Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.
1A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai. 2Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, gama ya aikata irin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ilawa su yi zunubi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba. 3Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel. 4Sai Yehowahaz ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji shi, gama ya ga wahalar da Isra'ilawa suke ciki, wato yadda Sarkin Suriya yake musguna musu. 5Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā. 6Duk da haka ba su rabu da zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. Sun aikata irin zunuban Yerobowam. Gunkiyan nan mai suna Ashtoret tana nan a Samariya.
7Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.
8Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 9Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.
10A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta. 11Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama'ar Isra'ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat. 12Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfin da ya yi yaƙi da Amaziya Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 13Yehowash kuwa ya mutu, aka binne shi a Samariya, inda ake binne sarakunan Isra'ila, sai Yerobowam na biyu ya gāji gadon sarautarsa.
14Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”
15Elisha kuwa ya ce masa, “Ka ɗauki baka da kibau.” Shi kuwa ya ɗauka.
18Sa'an nan ya ce, “Ka ɗauki kibau.” Shi kuwa ya ɗauka. Sai ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka caki ƙasa da su.” Sai ya caka har sau uku, sa'an nan ya tsaya. 19Elisha kuwa ya husata, ya ce, “Da ma ka caka sau biyar ko shida da za ka yi nasara a kan Suriyawa har ka ci su sarai, amma yanzu za ka yi nasara da su sau uku kawai.”
20Elisha kuwa ya rasu, aka binne shi. Maharan Mowabawa sukan kawo yaƙi a ƙasar da bazara. 21Wata rana ana binne gawa, sai aka ga mahara, aka jefar da gawar a cikin kabarin Elisha. Da gawar ta taɓi ƙasusuwan Elisha, sai ya farko ya tashi ya miƙe tsaye.
22Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya musguna wa jama'ar Isra'ila a dukan zamanin Yehowahaz. 23Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.
24Da Hazayel Sarkin Suriya ya rasu, sai Ben-hadad ɗansa ya gāji sarautarsa. 25Sai Yehowash ɗan Yehowahaz ya ƙwace daga hannun Ben-hadad, ɗan Hazayel, biranen da Ben-hadad ya ci da yaƙi daga hannun yehowahaz, tsohonsa. Sau uku Yehowash ya ci shi da yaƙi, sa'an nan ya karɓe biranen Isra'ila.
(2 Tar 25.1-24)
1A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta. 2Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Yehowaddin ta Urushalima. 3Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma bai kai kamar kakansa Dawuda ba. Ya yi kamar yadda tsohonsa, Yowash ya yi. 4Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadaya, da ƙona turare a matsafai na kan tuddai.
5Sa'ad da mulkin ya kahu sosai a hannun Amaziya, sai ya kashe fādawan da suka kashe tsohonsa. 6Amma bai kashe 'ya'yan masu kisankai ƙin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”
7Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa'an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.
8Amaziya kuwa ya aiki manzanni wurin Yehowash, ɗan Yehowahaz, ɗan Yehu, Sarkin Isra'ila, yana nemansa da yaƙi. 9Yehowash Sarkin Isra'ila ya mayar wa Amaziya Sarkin Yahuza da amsa cewa, “A dutsen Lebanon ƙaya ta aika wurin itacen al'ul ta ce, “‘Ka ba ɗana 'yarka ya aura.” Sai mugun naman jeji na Lebanon ya wuce, ya tattake ƙayar. 10Yanzu kai, Amaziya, ka bugi Edomawa don haka zuciyarka ta kumbura. To ka gode da darajar da ka samu, ka tsaya a gida, gama don me kake tonon rikici da zai jawo maka fāduwa, kai da mutanen Yahuza?”
11Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuzam a Bet-shemesh ta Yahuza. 12Mutanen Isra'ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida. 13Yehowash Sarkin Isra'ila kuwa ya kama Amaziya, Sarkin Yahuza, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-shemesh. Ya kuma zo Urushalima ya rushe garun Urushalima kamu ɗari huɗu daga Ƙofar Ifraimu zuwa Ƙofar Kusurwa. 14Ya kwashe dukan zinariya, da azurfa, da dukan kwanonin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na baitulmalin gidan sarki, da mutanen da aka ba da su jingina, sa'an nan ya koma Samariya.
15Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yadda ya yi yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 16Yehowash ya mutu, aka binne shi a Samariya a makabartar sarakunan Isra'ila, Ɗansa Yerobowam na biyu ya gāji sarautarsa.
(2 Tar 25.25-28)
17Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila. 18Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
19Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can. 20Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. 21Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya. 22Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.
23A shekara goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash Sarkin Isra'ila, ya ci sarauta a Samariya. Ya yi mulki shekara arba'in da ɗaya. 24Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 25Ya kafa iyakar Isra'ila daga ƙofar Hamat har zuwa tekun Araba. Wannan kuwa shi ne abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya faɗa ta bakin bawansa annabi Yunana, ɗan amittai, daga Gathefer.
26Gama Ubangiji ya ga Isra'ila tana shan azaba mai tsanani, gama ba bawa ko ɗa wanda zai taimaki Isra'ila. 27Ubangiji kuwa bai ce zai shafe sunan Isra'ila daga duniya ba, saboda haka ya cece su ta hannun yerobowam na biyu.
28Sauran ayyukan Yerobowam na biyu, da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yaƙi da ya yi, da yadda ya ƙwato wa Isra'ila Dimashƙu da Hamat waɗanda suke na Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 29Yerobowam na biyu kuwa ya mutu, kamar kakanninsa, sarakunan Isra'ila. Zakariya ɗansa ya gaji sarautarsa.
(2 Tar 26.1-23)
1A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam na biyu Sarkin Isra'ila, Azariya ɗan Amaziya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 2Yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara hamsin da biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa, Yekoliya ta Urushalima. 3Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda Amaziya, tsohonsa, ya yi. 4Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai. 5Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama'ar ƙasar.
6Sauran ayyukan Azariya, da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 7Azariya ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Yotam ɗansa ya gāji sarautarsa.
8A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Zakariya ɗan Yerobowam na biyu, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya wata shida. 9Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. Bai rabu da zunuban yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 10Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa'an nan ya hau gadon sarautarsa.
11Sauran ayyukan da Zakariya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
12Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa 'ya'yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.
13Shallum ɗan Yabesh ya ci sarauta a shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza. Ya yi mulki wata ɗaya a Samariya.
14Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa. 15Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 16A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.
17A shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya, Sarkin Yahuza, Menahem ɗan Gadi, ya ci sarautar. Ya yi shekara goma a Samariya. 18Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A dukan kwanakinsa bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 19Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai. 20Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra'ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.
21Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 22Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.
23A shekara ta hamsin ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Fekahiya ɗan Menahem, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara biyu. 24Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 25Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.
26Sauran ayyukan Fekahiya, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
27A shekara ta hamsin da biyu ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Feka ɗan Remaliya ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara ashirin. 28Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
29A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.
30Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa'an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya. 31Sauran ayyukan Feka da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
(2 Tar 27.1-9)
32A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 33Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha, 'yar Zadok. 34Yotam ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Azariya, ya yi. 35Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.
36Sauran ayyukan Yotam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 37A kwanakin nan Ubangiji ya fara aiken Rezin Sarkin Suriya da Feka ɗan Remaliya su yi yaƙi da Yahuza. 38Yotam ya rasu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.
(2 Tar 28.1-27)
1A shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 2Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarautar, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Bai yi abin da yake da kyau a gaban Ubangiji Allahnsa ba, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi. 3Ya bi halin sarakunan Isra'ila. Har ma ya yi hadaya ta ƙonawa da ɗansa, kamar mugayen ayyukan al'ummai da Ubangiji ya kora a gaban mutanen Isra'ila. 4Ya kuma miƙa hadaya da turaren ƙonawa a wuraren tsafi na kan tuddai da ƙarƙashin itatuwa masu duhuwa.
5Rezin Sarkin Suriya kuwa, da Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, suka kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye Ahaz da yaƙi, amma ba su ci shi ba. 6A lokacin nan kuma Sarkin Edom ya sāke ƙwace Elat, ya kori Yahudawa daga cikinta, Edomawa suka zo suka zauna a ciki har wa yau. 7Ahaz kuwa ya aiki manzanni wurin Tiglat-filesar, mai mulkin Assuriya, ya ce, “Ni baranka ne, ɗanka kuma, ka zo ka cece ni daga hannun Sarkin Suriya da Sarkin Isra'ila, waɗanda suke yaƙi da ni.” 8Ahaz kuma ya kwashe azurfa da zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, da wadda take cikin baitulmalin sarki, ya aika wa mai mulkin Assuriya kyauta. 9Tiglat-filesar ya ji roƙonsa, sai ya zo ya faɗa wa Dimashƙu da yaƙi, ya ci ta. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa Kir. Ya kuma kashe sarki Rezin.
10Sa'ad da sarki Ahaz ya tafi Dimashƙu don ya sadu da Tiglat-filesar, Sarkin Assuriya, ya ga bagaden da yake a Dimashƙu, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayaninsa. 11Uriya firist kuwa, ya gina bagaden bisa ga yadda sarki Ahaz ya aika masa daga Dimashƙu. Uriya firist, ya gina bagaden kafin sarki Ahaz ya komo daga Dimashƙu. 12Da sarki ya komo daga Dimashƙu, ya hango bagaden, sai ya tafi kusa da shi. 13Sa'an nan ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayarsa ta gari, da hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta salama a bisa bagaden. 14Sai ya kawar da bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi arewacin sabon bagadensa. 15Sarki Ahaz ya umarci Uriya firist cewa, “Sai ka miƙa hadaya ta ƙonawa ta safe, da hadaya ta gari ta maraice, da hadaya ta ƙonawa ta sarki, da hadayarsa ta gari, da hadaya ta ƙonawa ta dukan jama'ar ƙasar, da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, ka yayyafa dukan jinin hadaya ta ƙonawa, da dukan jinin hadayu a bisa babban bagaden. Amma bagaden tagulla zai zama nawa don yin ibada.” 16Uriya firist kuwa, ya yi dukan abin da sarki Ahaz ya umarta.
17Sarki Ahaz kuwa ya yanke sassan dakalan, ya ɗauke daruna da suke bisansu, ya kuma ɗauke kwatarniya da take bisa bijimai na tagulla, ya ajiye kwatarniya a daɓen dutse. 18Hanyar da aka killace ta Asabar, wadda suka yi a cikin gidan, da ƙofar waje ta shigar sarki, Ahaz ya kawar da su daga Haikalin Ubangiji saboda Sarkin Assuriya.
19Sauran ayyukan Ahaz waɗanda ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 20Ahaz ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Sai ɗansa, Hezekiya, ya gaji sarautarsa.
1A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Ahaz Samariya Yahuza, Hosheya ɗan Ila ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara tara. 2Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar sauran sarakunan Isra'ila da suka riga shi ba. 3Sai Shalmanesar Sarkin Assuriya, ya kawo masa yaƙi, Hosheya kuwa ya zama talakansa, yana kai masa haraji. 4Amma SArkin Assuriya ya gane Hosheya ya tayar masa, gama ya aiki manzanni wurin So, wato Sarkin Masar, ya kuma ƙi ya kai wa Sarkin Assuriya haraji kamar yadda ya saba yi kowace shekara, Saboda haka sai Sarkin Assuriya ya kama shi ya sa shi a kurkuku.
5Sa'an nan Sarkin Assuriya ya kai wa dukan ƙasar yaƙi, har ya kai Samariya. Ya kewaye Samariya da yaƙi shekara uku. 6A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.
7Wannan abu ya sami Isra'ila saboda sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fito da su daga ƙasar Masar, daga hannun Fir'auna, Sarkin Masar. Suka bauta wa gumaka. 8Suka bi al'adun al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora a gabansu, da al'adun da sarakunan Isra'ila suka kawo. 9Jama'ar Isra'ila kuma suka yi wa Ubangiji Allahnsu abubuwan da ba daidai ba, daga ɓoye. Sun gina wa kansu matsafai a dukan garuruwansu daga hasumiya zuwa birni mai garu. 10Suka kuma kafa wa kansu ginshiƙai da siffofin gumakan Ashtarot a kowane tudu da a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. 11Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi. 12Suka bauta wa gumaka waɗanda Ubangiji ya ce musu kada su bauta musu.
13Amma Ubangiji ya faɗakar da jama'ar Isra'ila da jama'ar Yahuza ta bakin annabawa da kowane maigani, cewa su bar mugayen hanyoyinsu, su kiyaye umarnansa da dukan dokokinsa waɗanda ya umarci kakanninsu da su, waɗanda kuma ya aiko musu ta wurin bayinsa annabawa. 14Duk da haka suka ƙi kasa kunne, suka taurare zuciyarsu kamar yadda kakanninsu suka yi, waɗanda ba su yi imani da Ubangiji Allahnsu ba. 15Suka yi watsi da dokokinsa, da alkawarinsa da ya yi wa kakanninsu, da kuma faɗakarwar da ya yi musu. Suka bi gumakan banza, suka zama banza, suka bi halin al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda Ubangiji ya umarce su kada su yi kamarsu. 16Suka bar dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu siffofin zubi na 'yan maruƙa biyu, suka yi gunkiyan nan, Ashtoret, suka yi wa taurari sujada, suka bauta wa Ba'al. 17Suka yi hadaya ta ƙonawa da 'ya'yansu mata da maza. Suka yi duba, suka yi sihiri, suka duƙufa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji, suka sa shi ya yi fushi. 18Saboda wannan Ubangiji ya husata da jama'ar Isra'ila, ya kawar da su daga gabansa, ba wanda aka rage, sai dai kabilar Yahuza.
19Jama'ar Yahuza kuma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba, sai suka bi al'adun da mutanen Isra'ila suka kawo. 20Ubangiji kuwa ya ƙi dukan zuriyar Isra'ila, ya wahalshe su, ya kuma bashe su a hannun mugayen abokan gāba, ta haka ya kawar da su daga gabansa.
21Sa'ad da Ubangiji ya ɓalle Isra'ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam kuwa ya karkatar da jama'ar Isra'ila daga bin Ubangiji. Ya sa su suka aikata babban zunubi. 22Jama'ar Isra'ila suka yi ta aikata dukan zunuban da Yerobowam ya yi, ba su daina aikata su ba, 23har lokacin da Ubangiji ya kawar da su daga gabansa kamar yadda ya faɗa ta bakin bayinsa, annabawa. Saboda haka aka fitar da jama'ar Isra'ila daga ƙasarsu zuwa Assuriya har wa yau.
24Sarkin Assuriya kuwa ya kawo mutane daga Babila, da Kuta, da Awwa, da Hamat, da Sefarwayim, ya zaunar da su a garuruwan Samariya a maimakon jama'ar Isra'ila. Sai suka mallaki Samariya, suka zauna a garuruwanta. 25A farkon zamansu a can, ba su yi tsoron Ubangiji ba saboda haka Ubangiji ya aika da zakoki a cikinsu, suka karkashe waɗansu daga cikinsu. 26Sai aka faɗa wa Sarkin Assuriya cewa, “Al'umman da ka kwashe ka zaunar da su a garuruwan Samariya ba su san shari'ar Allahn ƙasar ba, domin haka ya aiki zakoki a cikinsu, suna ta karkashe su.” 27Sa'an nan Sarkin Assuriya ya umarta a aiki firist ɗaya daga cikin firistocin da aka kwashe daga can, ya tafi, ya zauna can don ya koya musu shari'a Allahn ƙasar. 28Sai firist ɗaya daga cikin firistocin da suka kwashe daga Samariya, ya zo, ya zauna a Betel. Shi kuwa ya koya musu yadda za su yi tsoron Ubangiji.
29Amma duk da haka kowace al'umma ta riƙa yin gumakanta, tana ajiye su a wuraren yin tsafin na kan tuddai waɗanda Samariyawa suka gina. Kowace al'umma kuma ta yi haka a garin da ta zauna. 30Mutanen Babila suka yi Sukkot-benot, mutanen Kuta suka yi Nergal, mutanen Hamat suka yi Ashima. 31Awwiyawa suka yi Nibhaz da Tartak, mutanen Sefarwayim suka miƙa 'ya'yansu hadaya ta ƙonawa ga Adrammelek da Anammelek, gumakansu. 32Su ma suka yi tsoron Ubangiji, suka sa mutane iri dabam dabam su zama firistocin wuraren tsafinsu na kan tuddai. Firistocin nan suka miƙa hadayu dominsu a ɗakunan tsafinsu na kan tuddai. 33Waɗannan mutane su ma suka yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka bauta wa gumakansu ta hanyar da al'umman da aka kwaso su daga cikinsu suke yi.
34Har wa yau suna yin yadda suka yi a dā. Ba su yi tsoron Ubangiji ba, ba su bi dokoki, ko ka'idodi, ko shari'a, ko umarnan Ubangiji ba, waɗanda ya umarci 'ya'yan Yakubu, wanda ya sa wa suna Isra'ila. 35Ubangiji ya yi alkawari da 'ya'yan Yakubu, ya kuma umarce su kada su yi wa gumaka sujada ko su durƙusa musu, ko su bauta musu, ko su miƙa musu hadayu. 36Amma su yi tsoron Ubangiji, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar da iko mai girma da ƙarfi, shi za su yi wa sujada, shi kuma za su miƙa wa hadayu. 37Sai su yi biyayya da dokokinsa da umarnansa da ya rubuta musu. Kada su ji tsoron waɗansu alloli. 38Kada su manta da alkawarin da ya yi da su, kada kuma su ji tsoron gumaka. 39Amma su yi tsoron Ubangiji Allahnsu, shi kuwa zai cece su daga hannun dukan abokan gābansu. 40Duk da haka ba su kasa kunne ba, amma suka yi kamar yadda suka saba yi tun dā.
41Waɗannan al'ummai suka yi wa Ubangiji sujada, amma suka kuma yi ta bauta wa gumakansu. Haka kuma 'ya'yansu da jikokinsu suka yi kamar yadda kakanninsu suka yi. Haka suke yi har wa yau.
(2 Tar 29.1-2; 31.1)
1A shekara ta uku ta sarautar Hosheya ɗan Ila Sarkin Isra'ila, Hezekiya ɗan Ahaz Sarkin Yahuza ya ci sarautar. 2Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abi, 'yar Zakariya. 3Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi. 4Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama'ar Isra'ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan. 5Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra'ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa. 6Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa. 7Ubangiji kuwa ya kasance tare da shi, duk inda ya nufa sai ya sami albarka. Ya tayar wa Sarkin Assuriya, ya ƙi bautar masa. 8Ya kuma bugi Filistiyawa har zuwa Gaza da iyakarta daga hasumiya zuwa birni mai garu.
9A shekara ta huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, a lokacin Hosheya ɗan Ila, Sarkin Isra'ila, yana da shekara bakwai da sarauta, sai Shalmanesar Sarkin Assuriya ya kawo wa Samariya yaƙi, ya kewaye ta. 10A ƙarshen shekara ta uku, ya ci ta da yaƙi. A lokacin Hezekiya yana da shekara shida da sarauta, Hosheya kuwa yana da shekara tara da tasa sarauta. 11Sarkin Assuriya kuwa ya kwashi Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.
12Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.
(2 Tar 32.1-19; Ish 36.1-22)
13A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su. 14Sai Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya aika zuwa wurin Sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka ƙyale ni, duk abin da ka ɗora mini zan ɗauka.” Sai Sarkin Assuriya ya ce wa Hezekiya Sarkin Yahuza ya ba shi talanti ɗari uku na azurfa, da talanti talatin na zinariya. 15Hezekiya kuwa ya ba shi dukan azurfar da take cikin Haikalin Ubangiji, da wanda ke cikin baitulmali na gidan sarki. 16A lokacin sai Hezekiya ya kankare zinariyar da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin Haikalin Ubangiji da ita, ya ba Sarkin Assuriya. 17Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki. 18Sa'ad da suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka fito. 19Sa'an nan Rabshake ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya, cewa mai girma, Sarkin Assuriya ya ce, “‘Ga wa kake dogara? 20Kana tsammani maganganu kurum su ne dabara da ƙarfin yin yaƙi? To, ga wa ka dogara har da ka tayar mini? 21Ga shi yanzu, kana dogara ga Masar, wannan karyayyen sandan kyauro, wanda yakan yi wa hannun mutumin da yake tokarawa da shi sartse. Haka Fir'auna Sarkin Masar, yake ga dukan waɗanda suke dogara gare shi.”
22“Amma idan ka ce mini, “‘Ina dogara ga Ubangiji Allahnmu,” to, ba masujadansa na kan tuddai da bagadansa ne Hezekiya ya rurrushe ba? Yana ce wa mutanen Yahuza da Urushalima, “‘Za ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima?” 23Sai ka zo, ku daidaita da ubangidana, Sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu (2,000), idan za ka iya samun mahayansu. 24Ba ka isa ka kara da ko mafi ƙanƙanta na shugabannin sojojin maigidana ba, amma har kana dogara ga Masar don samun karusai da mahaya? 25Kana tsammani, ba da yardar Ubangiji ba ne na kawo wa wurin nan yaƙi don a hallaka shi? Gama Ubangiji ya ce mini, “‘Ka kai wa wannan ƙasa yaƙi don ka hallaka ta.”
26Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa, suka ce wa Rabshake, “Muna roƙonka, ka yi magana da mu barorinka da harshen Aramiya gama muna jinsa, kada ka yi magana da mu da harshen Yahudanci, har mutanen da suke kan garu su ji.”
27Amma Rabshake ya ce musu, “Ai, ubangidana bai aike ni in yi wannan magana ga ubangidanku da ku kaɗai ba, amma ga dukan mutanen da suke zaune a kan garu, waɗanda aka ƙaddara su tare da ku don su ci najasarsu su sha fitsarinsu.”
28Sa'an nan Rabshake ya tsaya, ya yi kira da ƙarfi da harshen Yahudanci, ya ce, “Ku ji maganar mai girma, Sarkin Assuriya! 29Sarki ya ce, “‘Kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, gama ba zai iya cetonku daga hannuna ba. 30Kada kuma ku yarda Hezekiya ya sa ku dogara ga Ubangiji da cewa lalle Ubangiji zai cece ku, ba za a kuma ba da wannan birni a hannun Assuriya ba.” 31Kada ku kasa kunne ga Hezekiya, gama Sarkin Assuriya ya ce, “‘Ku yi amana da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci 'ya'yan inabinsa da 'ya'yan ɓaurensa, ya kuma sha ruwa daga cikin randarsa, 32har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku. 33Ko akwai wani allah daga cikin allolin al'ummai, wanda ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun Sarkin Assuriya? 34Ina allolin Hamat, da na Arfad, da na Sefarwayim, da na Hena, da na Iwwa? Sun ceci Samariya daga hannuna ne? 35Daga cikin dukan allolin ƙasashe, wane ne ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannuna har da Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”
36Sai mutanen suka yi tsit, ba wanda ya ce masa uffan, gama sarki ya umarta cewa kada a tanka masa. 37Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.
(Ish 37.1-38; 2 Tar 32.20-23)
1Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji. 2Sai ya aiki Eliyakim wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da manyan firistoci, saye da tufafin makoki zuwa wurin annabi Ishaya, ɗan Amoz, 3su ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, 'ya'ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su. 4Mai yiwuwa ne Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun da Rabshake ya yi wanda ubangidansa, Sarkin Assuriya, ya aiko don yi wa Allah mai rai ba'a. Bari Ubangiji Allahnka ya hukunta masa saboda maganganunsa, sai ka yi addu'a saboda sauran da suka ragu.”
5Sa'ad da fādawan sarki Hezekiya suka iso wurin Ishaya, 6sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, “‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni. 7Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.”
8Rabshake kuwa ya koma, ya tarar Sarkin Assuriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji labari sarki ya riga ya bar Lakish. 9Da sarki ya ji labari Tirhaka, Sarkin Habasha, ya fito don ya yi yaƙi da shi, sai ya sāke aikar manzanni wurin Hezekiya, ya ce, 10“Ku faɗa wa Hezekiya Sarkin Yahuza, kada ya yarda Allahnsa wanda yake dogara gare shi ya yaudare shi da yi masa alkawari, cewa Sarkin Assuriya ba zai ci Urushalima ba. 11Ya ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa dukan ƙasashe yadda ya hallaka su sarai. To, shi zai kuɓuta? 12Allolin al'ummai sun cece su ne? Wato al'umman da kakannina suka hallaka, wato Gozan, da Haran, da Rezef, da mutanen Eden da suke Telassar. 13Ina Sarkin Hamat, da Sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarwayim, da Sarkin Hena, da Sarkin Iwwa?”
14Hezekiya ya karɓi wasiƙa daga hannun manzannin ya karanta ta, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji, ya buɗe ta, ya ajiye ta a gaban Ubangiji. 15Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa. 16Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka yi. Ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka gani, ka kuma ji irin maganar Sennakerib wadda ya aiko don a yi wa Allah mai rai ba'a. 17A gaskiya kam, ya Ubangiji, sarakunan Assuriya sun lalatar da al'ummai da ƙasashensu. 18Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su. 19Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”
20Sa'an nan Ishaya, ɗan Amoz, ya aika wa Hezekiya cewa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ji addu'arka, ya kuma amsa.” 21Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba'a. 22Wa kake tsammani ka yi wa ba'a har da zagi? Ba ka ga girmana ba, ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila? 23Ka aiki manzanninka su nuna mini girmankai saboda ka ci duwatsu mafi tsayi da karusanka, har ma ka ci duwatsun Lebanon. Ka yi fariyar a kan ka datse itatuwan al'ul mafi tsayi da na fir, har kuma ka shiga har can tsakiyar kurmi. 24Ka yi fariya a kan gina rijiyoyi, ka sha ruwan baƙuwar ƙasa, ƙafafun sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu, ya ƙafe.
25“Ba ka taɓa ji ba, cewa na ƙaddara wannan tun dā? Abin da yake faruwa yanzu, na shirya shi tun tuni, yadda za ka mai da birane masu garu su zama kufai. 26Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.
27“Na san zamanka, da fitarka, da shigowarka, da fushin da kake yi da ni. 28Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”
29Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci 'ya'yansu. 30Ringin mutanen gidan Yahuza za su yi saiwa a ƙasa, sa'an nan su ba da 'ya'ya a sama. 31Gama daga Urushalima ringi zai fito, daga Dutsen Sihiyona kuma waɗanda suka tsira za su fito. Kishin Ubangiji ne zai yi wannan.”
32Saboda haka Ubangiji ya ce, “Sarkin Assuriya ba zai zo birnin ba, ko ya harba kibiya, ko ya zo kusa da shi da garkuwa, ko ya tsiba masa tudu. 33Zai koma ta hanyar da ya zo. Ba zai shiga wannan birni ba. 34Gama zan tsare wannan birni, in cece shi don kaina, da kuma don bawana Dawuda.”
35A daren nan, sai mala'ikan Ubangiji ya tafi ya kashe Assuriyawa a sansaninsu, mutum dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Sa'ad da mutanen Isra'ila suka tashi da sassafe, sai suka ga gawawwakin nan kwance. 36Sennakerib Sarkin Assuriya, kuwa ya tashi, ya koma gida, ya zauna a Nineba. 37Sa'ad da yake yin sujada a haikalin gunkinsa Nisrok, sai 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takobi, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai ɗansa guda, wato Esar-haddon ya gāji gadon sarautarsa.
(2 Tar 32.24-26; Ish 38.1-22)
1A waɗannan kwanaki sai Hezekiya ya yi rashin lafiya har yana gab da mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya zo wurinsa, ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka, gama mutuwa za ka yi, ba za ka warke ba.”
2Hezekiya kuwa ya juya fuskarsa bango, ya yi roƙo ga Ubangiji, yana cewa, 3“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.
4Kafin Ishaya ya fita daga filin tsakiyar fādar, sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce, 5“Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama'ata cewa, “‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Ubangiji. 6Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuwa cece ka, kai da wannan birni daga hannun Sarkin Assuriya, zan tsare wannan birni don kaina da kuma don bawana, Dawuda.”
7Sai Ishaya ya ce, “Ku yi masa farsa da ɓaure, marurun zai warke.” 8Hezekiya kuwa ya ce wa Ishaya, “Mece ce alama, cewa Ubangiji zai warkar da ni har in haura zuwa Haikalin Ubangiji a rana ta uku?”
9Sai Ishaya ya ce, “Wannan ita ce alama daga wurin Ubangiji, Ubangiji zai cika alkawarin da ya yi. Ƙaƙa kake so, inuwa ta yi gaba da taki goma, ko kuwa ta yi baya da taki goma?”
10Hezekiya ya amsa, ya ce, “Ai, ya fi sauƙi inuwa ta yi gaba da taki goma da ta yi baya da taki goma.”
11Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya komar da inuwa baya da taki goma, bayan da ta riga ta wuce a matakin sarki Ahaz.
(2 Tar 32.27-31; Ish 39.1-8)
12A lokacin nan sai Merodak-baladan, ɗan Baladan, Sarkin Babila, ya ji labarin rashin lafiyar Hezekiya, sai ya aiki manzanni da wasiƙa da kyautai su kai wa Hezekiya, 13Hezekiya kuwa ya marabce su, ya kuma nuna musu dukan taskokin dukiyarsa na azurfa, da na zinariya, da na turare, da na mai mai daraja, da na makaman yaƙinsa, da dukan abin da yake akwai a cikin ɗakunan ajiyarsa. Ba abin da ya rage daga cikin gidansa, ko a mulkinsa wanda bai nuna musu ba. 14Sai annabi Ishaya ya tafi wurin sarki Hezekiya ya ce masa, “Daga ina ne waɗannan mutane? Me suka ce maka?” Hezekiya ya amsa, ya ce, “Sun zo daga ƙasa mai nisa, wato Babila.”
15Ishaya ya ce, “Me suka gani a fādarka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga duk abin da yake ciki, ba wani abu kuma daga cikin taskokina da ban nuna musu ba.”
16Sa'an nan Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji abin da Ubangiji ya ce, 17“‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe duk abin da yake cikin gidanka, da abin da kakanninka suka tanada, zuwa Babila. 18Za a kuma kwashe waɗansu 'ya'yanka da ka haifa zuwa Babila, can za a maishe su babani a fādar Sarkin Babila.”
19Sarki Hezekiya kuwa ya fahimci za a yi zaman lafiya da salama a zamaninsa, don haka ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”
(2 Tar 32.32-33)
20Sauran ayyukan Hezekiya da dukan ƙarfinsa, da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa don ya kawo ruwa cikin birnin, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 21Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.
(2 Tar 33.1-20)
1Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Hefziba. 2Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, gama ya aikata abubuwa masu banƙyama waɗanda al'umman da Ubangiji ya kora a gaban jama'ar Isra'ila suka aikata. 3Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu. 4Ya gina bagadai a Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima zan sa sunana.” 5Ya gina wa taurarin sama bagadai a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. 6Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi. 7Siffar gunkiyan nan Ashtoret wadda ya yi, ya kafa ta a Haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Sulemanu, “A cikin wannan Haikali a Urushalima wadda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila zan tabbatar da sunana har abada. 8Ba zan-sa jama'ar Isra'ila su ƙara fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce su.” 9Amma mutanen Yahuza ba su kasa kunne ba. Manassa kuma ya yaudare su, suka aikata mugunta fiye da abin da al'umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama'ar Isra'ila suka aikata.
10Ubangiji kuwa ya yi magana ta wurin bayinsa annabawa ya ce, 11“Tun da yake Manassa, Sarkin Yahuza, ya aikata waɗannan abubuwa masu banƙyama, ya kuma aikata mugayen abubuwa fiye da dukan abin da Amoriyawa, waɗanda suka riga shi, suka aikata, ya kuma sa mutanen Yahuza su yi zunubi saboda gumakansa, 12saboda haka ni Ubangiji Allah na Isra'ila, zan aukar wa Urushalima da mutanen Yahuza da masifa irin wadda duk wanda ya ji labarinta, sai ya kusa suma. 13Zan gwada Urushalima da magwajin Samariya da kuma ma'aunin gidan Ahab. Zan kuma suɗe Urushalima kamar yadda mutum yakan suɗe akushi sa'an nan ya kifar da shi. 14Zan jefar da ragowar gādona, in bashe su a hannun abokan gāba, za su zama ganima da abin waso ga dukan abokan gābansu, 15saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”
16Banda wannan kuma Manassa ya kashe adalai har ya cika Urushalima daga wannan gefe zuwa wancan da jininsu, banda zunubin da ya sa mutanen Yahuza su yi, har suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
17Sauran ayyukan Manassa, da dukan abin da ya aikata, da zunubin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 18Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.
(2 Tar 33.21-25)
19Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Meshullemet, 'yar Haruz na Yotba. 20Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Manassa ya yi. 21Ya bi halin tsohonsa duka. Ya bauta wa gumakan da tsohonsa ya bauta wa, ya kuma yi musu sujada. 22Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai bi tafarkin Ubangiji ba.
23Fādawansa kuwa suka ƙulla masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa. 24Amma mutanen ƙasar suka kashe waɗannan da suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar. Sai suka naɗa Yosiya ɗan sarki, ya gāji tsohonsa.
25Sauran ayyukan da Amon ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 26Aka binne shi a kabarinsa na gonar Uzza. Ɗansa Yosiya ya gāji sarautarsa.
(2 Tar 34.1-2)
1Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yedida, 'yar Adaya na Bozkat. 2Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.
(2 Tar 34.8-28)
3A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, wato jikan Meshullam, magatakarda, zuwa Haikalin Ubangiji, ya ce, 4“Ka tafi wurin Hilkiya babban firist domin a lasafta yawan kuɗin da aka kawo cikin Haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tattara daga wurin jama'a. 5A ba da kuɗin a hannun masu lura da ma'aikata waɗanda suke gyaran Haikalin Ubangiji, su kuma su ba waɗanda suke gyaran Haikalin, 6wato masu sassaƙa, da magina, domin a sayi katako da dutsen da aka haƙo don gyaran Haikalin. 7Kada a tambaye su yadda suka kashe kuɗin da aka sa a hannunsu, gama su amintattu ne.”
8Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi. 9Sai Shafan magatakarda ya tafi ya faɗa wa sarki cewa, “Baranka ya kwashe kuɗin da ya tarar a Haikali, na kuwa ba masu lura da ma'aikatan Haikalin Ubangiji.” 10Ya kuma ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Ya kuwa karanta wa sarki littafin.
11Sa'ad da sarki ya ji maganar da take cikin littafin dokoki, sai ya kece tufafinsa. 12Sa'an nan ya umarci Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikaiya, da Shafan magatakarda, da Asaya baran sarki cewa, 13“Ku tafi ku yi tambaya ga Ubangiji saboda ni, da jama'a, da dukan mutanen Yahuza a kan maganar littafin nan da aka samo, gama Ubangiji ya yi fushi da muƙwarai saboda kakanninmu domin ba su bi maganar littafin nan ba, har da za su yi dukan abin da aka rubuta mana.”
14Sai Hilkiya firist, da Ahikam, da Akbor, da Shafan, da Asaya suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, wato jikan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiye tufafi. A Urushalima take zaune a sabuwar unguwa. Suka kuwa yi magana da ita. 15Sai ta ce musu, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, a faɗa wa mutumin da ya aiko ku gare ni, 16“‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta, 17domin sun rabu da ni, sun ƙona turare ga gumaka don su tsokane ni in yi fushi da aikin hannuwansu. Saboda haka fushina zai ƙuna a kan wurin nan, ba kuwa zai huce ba.” 18Amma akan Sarkin Yahuza, wanda ya aiko ku, ku tambayar masa Ubangiji, ku faɗa masa Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, “‘A kan maganar da ka ji, 19da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka. 20Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.” Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.
(2 Tar 34.3-7; 29-33)
1Sarki Yosiya kuwa ya aika, aka tattaro masa dukan dattawan Yahuza da na Urushalima. 2Sa'an nan ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan jama'ar Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, da firistoci, da annabawa, da jama'a duka, ƙanana da manya. Sai ya karanta musu dukan maganar littafin alkawarin da aka iske a Haikalin Ubangiji. 3Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama'a kuma suka yi alkawarin.
4Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel. 5Ya kuma tuɓe firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuza suka naɗa don su ƙona turare a matsafai na kan tuddai a garuruwan Yahuza, da kewayen Urushalima, da firistoci waɗanda suka ƙona turare ga Ba'al, da rana, da wata, da taurari, da dukan rundunan sama. 6Sai sarki ya fitar da gunkiyan nan Ashtoret, daga cikin Haikalin Ubangiji a Urushalima, ya kai Kidron, ya ƙone ta a ƙoramar Kidron, ta zama toka, ya kuwa watsar da tokar a makabarta. 7Ya rurrushe ɗakunan karuwai mata da maza da suke a Haikalin Ubangiji, wato wurin da mata suke saƙa labulan gunkiyar. 8Ya fitar da dukan firistoci daga cikin garuruwan Yahuza, sa'an nan ya lalatar da matsafai na kan tuddai inda firistoci suka ƙona turare, tun daga Geba har zuwa Biyer-sheba. Ya kuma rurrushe matsafai na kan tuddai waɗanda suke a ƙofofin shiga ƙofar Joshuwa, hakimin birnin, waɗanda suke hagu da ƙofar birnin. 9Duk da haka firistoci matsafai na kan tuddai ba su haura zuwa bagaden Ubangiji a Urushalima ba, amma suka ci abinci marar yisti tare da 'yan'uwansu.
10Ya kuma lalatar da Tofet, wurin da yake kwarin 'ya'yan Hinnom, don kada kowa ya ƙara miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya ta ƙonawa ga Molek. 11Ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuza suka keɓe wa rana, a ƙofar Haikalin Ubangiji, kusa da shirayin Natan-melek shugaban shirayin da yake cikin farfajiya. Haka kuma ya ƙone karusai waɗanda aka yi wa rana. 12Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron. 13Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa. 14Ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffofin gumakan, sa'an nan ya rufe wurarensu da ƙasusuwan mutane.
15Yosiya ya kuma rushe bagaden da yake a Betel, wanda Yerobowam ɗan Nebat ya gina, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi, tare da tudun, ya farfashe duwatsun, ya niƙe su, sun zama gari, ya kuma ƙone Ashtoret. 16Da Yosiya ya waiwaya, sai ya ga kaburbura a kan dutse. Ya aika a kwaso ƙasusuwan da suke cikin kaburburan, sai ya ƙone su a bisa bagaden, ya lalatar da shi kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi. 17Ya kuma ce, “Kabarin wane ne wancan da nake gani?” Sai mutanen Betel suka ce masa, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuza ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”
18Sarki kuwa ya ce, “A bar shi yadda yake, kada wani ya taɓa ƙasusuwansa.” Sai suka bar ƙasusuwan annabin da ya zo daga Samariya.
19Dukan matsafai na kan tuddai da suke a garuruwan Samariya waɗanda sarakunan Isra'ila suka gina, har suka sa Ubangiji ya yi fushi, Yosiya ya watsar da su. Ya yi da su kamar yadda ya yi a Betel. 20Ya kuma karkashe dukan firistocin matsafai na kan tuddai a bisa bagadan da suke can. Ya ƙone ƙasusuwansu a bisa bagadan. Sa'an nan ya komo Urushalima.
(2 Tar 35.1-19)
21Sarki Yosiya kuwa ya umarci dukan mutane, ya ce, “Ku kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku kamar yadda aka rubuta a littafin alkawari.” 22Gama ba a ƙara kiyaye Idin Ƙetarewa ba tun daga zamanin hakimai waɗanda suka yi hukuncin Isra'ila, ko a zamanin sarakunan Isra'ila da na Yahuza, 23sai dai a shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yosiya an kiyaye Idin Ƙetarewa ɗin nan ga Ubangiji a Urushalima.
24Yosiya kuma ya kori dukan masu mabiya, da masu maita, da kawunan gidaje, da gumaka, da dukan abubuwa masu banƙyama da ake gani a ƙasar Yahuza, da a Urushalima, don ya sa maganar dokokin da aka rubuta a littafin da Hilkiya firist ya tarar a Haikalin Ubangiji ta kahu. 25A gabansa, ko bayansa ba wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Ubangiji da zuciya ɗaya da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa domin ya bi dukan dokokin Musa.
26Duk da haka Ubangiji bai huce daga fushinsa mai zafi da yake yi da jama'ar Yahuza ba, saboda yawan tsokanar da Manassa ya yi masa. 27Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama'ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama'ar Isra'ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”
(2 Tar 35.20ū36.1)
28Sauran ayyukan Yosiya da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 29A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo. 30Fādawansa kuwa suka ɗauko gawarsa a karusa daga Magiddo, suka kawo Urushalima, suka binne a kabarinsa. Sai jama'ar ƙasa suka naɗa Yehowahaz ɗan Yosiya sarki a matsayin tsohonsa.
(2 Tar 36.2-4)
31Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Hamutal 'yar Irmiya na Libna. 32Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. 33Fir'auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya. 34Sai Fir'auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.
35Yehoyakim yakan ba Fir'auna azurfa da zinariya, ya kuwa sa wa ƙasar haraji don ya sami kuɗin da Fir'auna ya umarta. Ya tilasta wa kowa ya biya azurfa da zinariya bisa ga yadda ya sa masa don ya ba Fir'auna-neko.
(2 Tar 36.5-8)
36Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Zebida, 'yar Fediya mutumin Ruma. 37Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda dukan kakanninsa suka yi.
1A zamanin Yehoyakim ne Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo wa Yahuza yaƙi, Yehoyakim kuwa ya zama baransa har shekara uku daganan kuma ya tayar masa. 2Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa. 3Hakika haka ya faru ga Yahuza bisa ga umarnin Ubangiji domin a kawar da su daga gaban Ubangiji saboda dukan zunubin Manassa da ya aikata, 4saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.
5Sauran ayyukan Yehoyakim da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 6Yehoyakim ya rasu. Ɗansa Yekoniya ya gāji gadon sarautarsa.
7Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.
(2 Tar 36.9-10)
8Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima. 9Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa ya yi.
10A zamaninsa ne sojojin Nebukadnezzar Sarkin Babila suka zo Urushalima, suka kewaye ta da yaƙi. 11Nebukadnezzar ya zo birnin lokacin da sojojinsa suka kewaye birnin da yaƙi. 12Sai Yekoniya Sarkin Yahuza ya ba da kansa ga Sarkin Babila shi da tsohuwarsa, da fādawansa da hakimansa. Sarkin Babila ya kama shi yana da shekara takwas da sarautar, 13ya kuma kwashe dukan dukiyar da take cikin Haikalin Ubangiji, da dukiyar da take cikin gidan sarki. Sai ya farfashe tasoshin zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya aikata abin da Ubangiji ya riga ya faɗa. 14Nebukadnezzar ya kwashe dukan mutanen Urushalima, da dukan hakimai da dukan jarumawa, da masu sana'a, da maƙera, har sun kai dubu goma (10,000). Ba wanda ya ragu sai dai matalautan ƙasar.
15Ya tafi da Yekoniya a Babila, shi da tsohuwarsa, da fādawansa, da masu maƙami na ƙasar. 16Sarkin Babila ya kai kamammu Babila, wato jarumawa dubu bakwai (7,000), masu sana'a da maƙera dubu ɗaya (1,000), dukansu ƙarfafa ne, sun isa zuwa yaƙi.
17Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan'uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa'an nan ya ba shi suna Zadakiya.
(2 Tar 36.11-12; Irm 52.1-3)
18Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan tsohuwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, mutumin Libna. 19Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda Yehoyakim ya yi. 20Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai da mutanen Urushalima da dukan mutanen Yahuza, sai ya kore su daga gabansa. Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.
(2 Tar 36.13-16; Irm 39.1-7; 52.3-11)
1A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai. 2Aka kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya. 3A kan rana ta tara ga watan huɗu, yunwa ta tsananta a birnin gama ba abinci domin mutanen ƙasar. 4Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin. 5Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki suka kamo shi a filayen Yariko. Sojojinsa duka suka watse, suka bar shi. 6Da suka kama sarkin, sai suka kawo shi wurin Sarkin Babila a Ribla, inda aka yanke masa hukunci. 7Aka kashe 'ya'yansa maza a idonsa, sa'an nan aka ƙwaƙule masa idanu, aka kuma ɗaure shi da sarƙa, aka kai shi Babila.
(2 Tar 36.17-21; Irm 39.8-10; 52.12-23)
8A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima. 9Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida. 10Dukan sojojin Kaldiyawa waɗanda suke tare da shugaban, suka rushe garun da yake kewaye da Urushalima. 11Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala. 12Amma shugaban sojojin ya bar matalautan ƙasar su zama masu gyaran inabi, da masu noma.
13Sai Kaldiyawa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalansu, da kwatarniyar ruwa na tagullar da yake cikin Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagullar zuwa Babila. 14Suka kuma kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da cokula, da tasoshin tagulla da ake amfani da su don hidimar Haikali. 15Suka kuma kwashe farantan wuta da daruna. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban sojojin ya kwashe. 16Tagullar da Sulemanu ya yi abubuwan nan da su, wato ginshiƙai biyu, da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna. 17Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.
(Irm 52.24-27)
18Nebuzaradan kuma ya tafi da Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofa. 19Daga cikin birnin kuma ya tafi da wani shugaban sojoji, da 'yan majalisar sarki mutum biyar, da magatakardan shugaban sojoji wanda ya tattara jama'ar ƙasar, da mutum sittin na ƙasar waɗanda aka samu a birnin. 20Nebuzaradan shugaban sojoji ya kai su wurin Sarkin Babila a Ribla ta ƙasar Hamat. 21Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can. Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.
(Irm 40.1-9; 41.1-3)
22A kan sauran waɗanda suka ragu a ƙasar Yahuza, waɗanda Sarkin Babila, Nebukadnezzar, ya bari, ya naɗa musu Gedaliya ɗan Ahikam, wato jikan Shafan, ya zama hakiminsu. 23Sa'ad da shugabannin mayaƙa su da mayaƙansu suka ji Sarkin Babila ya naɗa Gedaliya ya zama hakimi, sai suka zo tare da mutanensu wurin Gedaliya a Mizfa, wato su Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan ɗan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, mutumin Netofa, da Yazaniya mutumin Ma'aka. 24Sai Gedaliya ya rantse musu, su da mutanensu, cewa kada su ji tsoron barorin Kaldiyawa, su zauna a ƙasar, su bauta wa Sarkin Babila, haka zai fi zamar musu alheri.
25Amma a watan bakwai, sai Isma'ilu ɗan Netaniya, wato jikan Elishama, daga gidan sararta, ya zo tare da mutum goma ya fāda wa Gedaliya, ya kashe shi tare da Yahudawa da Kaldiyawa da suke tare da shi a Mizfa. 26Sai dukan mutane, manya da ƙanana, da shugabannin mayaƙa, suka tashi, suka gudu zuwa Masar, gama sun ji tsoron Kaldiyawa.
(Irm 52.31-34)
27A rana ta ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu, a shekara ta talatin da bakwai ta ɗaurin Yekoniya Sarkin Yahuda, sai Ewil-merodak da ya zama Sarkin Babila ya yi wa Yekoniya alheri, ya sake shi a shekarar da ya ci sarautar. 28Ya yi masa magana mai kyau, ya kuma ba shi matsayi fiye da sarakunan da suke tare da shi a Babila. 29Sai Yekoniya ya tuɓe tufafinsa na kurkuku. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har muddin ransa. 30Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa.