2 Samuel
1Bayan rasuwar Saul, sa'ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag. 2Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa. 3Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?” Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra'ilawa.”
4Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.” Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”
5Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”
6Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi. 7Da ya waiga, ya gan ni, sai ya kira ni, ni kuwa na amsa, na ce, “‘Ga ni.” 8Ya ce mini, “‘Wane ne kai?” Na ce masa, “‘Ni Ba'amaleke ne.” 9Sai ya ce mini, “‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.” 10Sai na tafi na kashe shi domin na tabbata ba zai yi rai ba bayan ya fāɗi. Na kuma cire kambin da yake kansa da ƙarau da yake a dantsensa. Ga su, na kawo wa ubangijina.”
11Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu. 12Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra'ila domin an Karkashe su a yaƙi.
13Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?” Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba'amaleke.”
14Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?” 15Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin samarin, ya ce masa, “Ka kashe shi.” Ya dai buge shi, ya mutu. 16Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, “‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.”
17Sai Dawuda ya raira waƙar makoki domin Saul da Jonatan, ɗansa. 18Ya umarta a koya wa mutanen Yahuza wannan waƙa. (An rubuta ta a littafin Yashar.)
19“An kashe darajarki, ya Isra'ila, a kan tuddanki! Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!
20Kada a ba da labarin a Gat, Ko a titin Ashkelon. Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna, Kada ku sa 'yan matan arna su yi farin ciki.
21“Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa. Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani. Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance, Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.
22Bakan Jonatan mai kisa ne, Takobin Saul ba shi da jinƙai, Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.
23“Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha'awa, A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare. Sun fi gaggafa sauri, Sun fi zaki ƙarfi.
24“Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul! Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa, Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.
25“Jarumawa sun fāɗi, An kashe su a bakin dāga. Jonatan na kwance matacce a tuddai.
26“Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan'uwana Jonatan, Ƙaunatacce kake a gare ni! Ƙaunarka a gare ni abar al'ajabi ce, Ta fi ƙaunar mace.
27“Jarumawa sun fāɗi, Makamansu ba su da sauran amfani.”
1Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?” Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.” Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?” Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.” 2Dawuda kuwa ya haura zuwa can tare da matansa biyu, wato Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail matar marigayi Nabal Bakarmele. 3Ya kuma tafi tare da mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa. Suka zauna a garuruwan Hebron. 4Mutanen Yahuza kuwa suka zo, suka naɗa Dawuda da man naɗawa domin ya zama Sarkin Yahuza. Da Dawuda ya ji labari mutanen Yabesh-gileyad, sun binne Saul, 5sai ya aiki manzanni da saƙo wurin mutanen Yabesh-gileyad ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka da yake kun yi wa Saul, ubangijinku, wannan alheri, har kuka binne shi. 6Ubangiji ya nuna muku ƙaunarsa da amincinsa. Ni kuwa zan yi muku alheri saboda abin da kuka yi. 7Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”
8Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim. 9Ya naɗa shi Sarkin Gileyad, da Ashiru, da Yezreyel, da Ifraimu, da ƙasar Biliyaminu, da dukan Isra'ila. 10Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba'in sa'ad da ya ci sarautar Isra'ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda. 11Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.
12Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon. 13Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin. 14Sai Abner ya ce wa Yowab, “Bari samarin su tashi su yi kokawa a gabanmu.” Yowab kuwa ya ce, “To, sai su tashi.”
15Sai suka tashi, suka haye. Mutum goma sha biyu a madadin mutanen Biliyaminu da Ish-boshet, ɗan Saul, mutum goma sha biyu kuma a madadin mutanen Dawuda. 16Kowa ya kama abokin kokawarsa a kā, suka soki juna a kwiɓi da takuba. Suka faɗi tare. Aka sa wa wurin suna Helkat-hazzurim, wato filin takuba, wurin yana nan a Gibeyon.
17Yaƙin kuwa ya yi zafi a ranar. Mutanen Dawuda suka ci Abner da mutanen Isra'ila. 18'Ya'yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa. 19Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba. 20Da Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne Asahel?” Ya amsa, “Ni ne.”
21Abner ya ce masa, “Ka daina haye mini, ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka kama shi, ka karɓe masa makaminsa.” Amma Asahel bai daina binsa ba. 22Abner kuma ya sāke ce masa, “Ka daina bina, kada ka sa in kashe ka fa! Idan na kashe ka kuwa, yaya zan yi ido biyu da dan'uwanka, Yowab?” 23Amma Asahel bai daina binsa ba, Abner dai ya nashe shi da gindin māshi a ciki, sai mashin ya fita ta bayansa. Ya fāɗi ya mutu nan take. Duk wanda ya zo inda Asahel ya fāɗi ya mutu, sai ya tsaya cik.
24Amma Yowab da Abishai suka bi Abner, har faɗuwar rana, suka isa tudun Amma, wanda yake gaban Gaiya, a hanya zuwa jejin Gibeyon. 25Mutanen Biliyaminu kuma suka haɗa kansu, suka goyi bayan Abner, suka zama ƙungiya guda, suka tsaya kan tudu. 26Abner kuwa ya kira Yowab, ya ce, “Har abada ne takobi zai hallakar? Ba ka sani ba ƙarshen zai yi ɗaci? Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina runtumar 'yan'uwansu?”
27Yowab ya ce, “Na rantse da Ubangiji, hakika da ba domin ka yi magana ba, da mutanena ba za su daina runtumarka ba har gobe da safe.” 28Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra'ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.
29Abner da mutanensa suka bi dare farai, suka ratsa Araba, suka haye Urdun. Suka yi ta tafiya dukan safiyan nan, suka shige Bitron, har suka kai Mahanayim. 30Da Yowab ya komo daga runtumar Abner, ya tattara mutanensa duka, sai ya ga an rasa mutum goma sha tara daga cikin mutanen Dawuda, banda Asahel. 31Amma barorin Dawuda suka kashe mutanen Biliyaminu mutum ɗari uku da sittin daga cikin waɗanda suke tare da Abner. 32Suka ɗauki Asahel, suka tafi suka binne shi a kabarin mahaifinsa a Baitalami. Yowab kuwa da mutanensa suka bi dare farai, gari ya waye musu a Hebron.
1Gidan Saul da gidan Dawuda suka daɗe suna yaƙi da juna. Ƙarfin gidan Dawuda ya yi ta ƙaruwa, amma na gidan Saul ya yi ta raguwa.
(1 Tar 3.1-4)
2'Ya'ya maza da aka haifa wa Dawuda a Hebron ke nan, Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa ɗan farinsa, Amnon. 3Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom. 4Haggit ta haifa masa ɗansa na huɗu, Adoniya. Abital ta haifa masa ɗansa na biyar, Shefatiya. 5Matarsa Egla ta haifa masa ɗansa na shida, Itireyam. Dukan waɗannan a Hebron ne aka haife su.
6Abner ya ƙasaita sosai a gidan Saul a lokacin da ake yaƙi tsakanin jarumawan Saul da na Dawuda.
7Saul yana da ƙwarƙwara mai suna Rizfa, 'yar Aiya. Sai Ish-boshet ya ce wa Abner, “Me ya sa ka kwana da ƙwarƙwarar tsohona?”
8Abner ya husata saboda wannan magana, ya ce, “Kana zato ni maci amanar ƙasa ne? Kana tsammani ina wa ƙasar Yahuza aiki ne? Tun da farko ina ta nuna alheri ga gidan Saul, tsohonka, da 'yan'uwansa, da abokansa, ban kuwa ba da ka a hannun Dawuda ba. Amma ga shi, yau ka zarge ni da laifin kwartanci game da wannan mata. 9Allah ya la'anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba, 10wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra'ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.” 11Ish-boshet kuwa bai ce wa Abner uffan ba, don yana jin tsoronsa.
12Sai Abner ya aiki manzanni zuwa wurin Dawuda a Hebron, ya ce, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi mini alkawari, ni kuwa zan goyi bayanka, in sa dukkan Isra'ilawa su bi ka.”
13Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi maka alkawari a kan wannan sharaɗi, ba za ka ga fuskata ba sai ka kawo mini matata, Mikal, 'yar Saul, sa'ad da za ka zo wurina.” 14Sa'an nan Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-boshet, ɗan Saul, ya ce, “Ka ba ni matata, Mikal, wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari ta Filistiyawa.” 15Sai Ish-boshet ya aika aka ƙwato Mikal daga wurin mijinta, Falti, ɗan Layish. 16Mijinta ya bi ta yana ta kuka har zuwa Bahurim. Sai Abner ya ce masa ya koma, ya kuwa koma.
17Abner ya shawarci dattawan Isra'ila, ya ce, “Dā ma can kuna so Dawuda ya sarauce ku. 18To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, “‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama'ar Isra'ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.” 19Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa'an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra'ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.
20Abner tare da mutum ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda kuwa ya yi musu liyafa. 21Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra'ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.
22Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya. 23Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”
24Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya? 25Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”
26Da Yowab ya fita daga wurin Dawuda, sai ya aiki manzanni su bi bayan Abner. Suka komo da shi a rijiyar Sira, amma Dawuda bai sani ba. 27Sa'ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan'uwansa, Asahel. 28Daga baya sa'ad da Dawuda ya ji, sai ya ce, “Ni da mulkina baratattu ne a gaban Ubangiji daga alhakin jinin Abner ɗan Ner har abada. 29Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.” 30Ta haka Yowab da ɗan'uwansa Abishai suka kashe Abner saboda ya kashe ƙanensu, Asahel, a wurin yaƙi a Gibeyon.
31Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara. 32Suka binne Abner a Hebron. Sarki ya ta da murya ya yi kuka a kabarin Abner. Dukan mutane kuma suka yi kuka. 33Sarki ya yi wannan makoki domin Abner, ya ce, “Don me Abner zai mutu kamar wawa>
34Hannuwansa ba a ɗaure suke ba, Ƙafafunsa kuma ba a dabaibaye suke ba. Ya mutu kamar wanda mugayen mutane suka kashe.” Dukan mutane suka yi kuka kuma saboda shi.
35Mutane kuwa suka zo su ba Dawuda magana, ko ya ci abinci tun rana ba ta faɗi ba. Amma Dawuda ya rantse ya ce, “Allah ya buge ni in mutu nan, idan na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi.” 36Da mutanen suka lura, sai suka yarda da abin da sarki ya yi, suka kuma ji daɗin kowane abu da sarki ya yi. 37A wannan rana dukan mutanen Dawuda da dukan mutanen Isra'ila suka gane, ashe, ba nufin Dawuda ba ne a kashe Abner ɗan Ner. 38Sarki ya ce wa fādawansa, “Ba ku sani ba, basarake ne, babban mutum ne kuma ya faɗi a cikin Isra'ila yau? 39Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”
1Da Ish-boshet, ɗan Saul, ya ji labari Abner ya mutu a Hebron, sai gabansa ya faɗi. Dukan mutanen Isra'ila kuma suka tsorata. 2Shi ɗan nan na Saul yana da shugabanni biyu na 'yan hari, su ne Ba'ana da Rekab, 'ya'yan Rimmon na ƙasar Biliyaminu daga Biyerot, (gama an lasafta Biyerot cikin yankin ƙasar Biliyaminu. 3Mutanen Biyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.)
4Jonatan, ɗan Saul kuwa, yana da ɗa, sunansa Mefiboshet, amma gurgu ne. Yana da shekara biyar sa'ad da aka kawo labarin mutuwar Saul da Jonatan daga Yezreyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi, ta sheƙa a guje. A sa'ad da take gudu sai ya faɗo, sanadin gurguntakar ke nan.
5Rekab da Ba'ana 'ya'yan Rimmon suka tafi gidan Ish-boshet da tsakar rana, a lokacin da yake shaƙatawa. 6Rekab da Ba'ana kuwa, suka laɓaɓa, suka shiga kamar suna neman alkama. 7Da suka shiga gidan, sai suka iske shi yana kwance a ɗakin kwanansa. Suka buge shi, suka kashe shi, suka datse kansa. Suka ɗauki kansa suka bi ta hanyar Araba, suka yi tafiya dare farai. 8Suka kai wa Dawuda kan Ish-boshet a Hebron. Suka ce wa sarki Dawuda, “Ga kan Ish-boshet ɗan maƙiyinka, Saul, wanda ya nemi ranka. Ubangiji ya rama wa sarki a kan Saul da zuriyarsa yau.”
9Amma Dawuda ya ce wa Rekab da Ba'ana, 'ya'yan Rimmon, mutumin Biyerot, “Na rantse da Ubangiji wanda ya fanshe ni daga kowace masifa, 10sa'ad da wani ya kawo mini labari cewa, “‘Saul ya mutu,” mutumin ya yi tsammani albishir ne ya kawo mini, sai na kama shi na kashe shi a Ziklag. Ladan da na ba shi ke nan saboda labarinsa. 11Balle fa ku da kuke mugayen mutane, da kuka kashe adali a gadonsa, a cikin gidansa, ba sai in nemi hakkin jininsa a hannunku ba, in kawar da ku daga duniya?” 12Sai Dawuda ya umarci samarinsa su kashe su. Suka datsa hannunsu da ƙafafunsu, suka rataye su a gefen tafkin Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-boshet suka binne a cikin kabarin Abner a Hebron.
(1 Tar 11.1-3)
1Dukan kabilan Isra'ila kuwa suka zo wurin Dawuda a Hebron, suka ce, “Ga shi, mu 'yan'uwanka ne. 2A dā sa'ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra'ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, “‘Kai za ka lura da jama'ata Isra'ila, za ka zama sarkinsu.” 3Sai dukan dattawan Isra'ila suka tafi wurin sarki Dawuda a Hebron, shi kuwa ya yi alkawari da su a gaban Ubangiji. Su kuwa suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. 4Dawuda ya ci sarauta yana da shekara talatin. Ya yi shekara arba'in yana sarauta. 5Ya yi shekara jama'ar Yahuza shekara bakwai da wata shida a Hebron. Ya kuma yi sarautar jama'ar Isra'ila duk da Yahuza shekara talatin da uku a Urushalima.
(1 Tar 11.4-9)
6Sarki Dawuda da mutanensa suka tafi Urushalima su yaƙi Yebusiyawa mazaunan ƙasar. Su kuwa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka iya zuwa nan ba, makafi kawai da guragu za su kore ka.” A zatonsu Dawuda ba zai iya zuwa can ba. 7Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.
8A ran nan Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kashe Yebusiyawa, to, sai kuma ya haura zuwa wuriyar ruwa ya fāɗa wa guragu da makafi waɗanda ran Dawuda yake ƙi.” Don haka a kan ce, “Makafi da guragu ba za su shiga Haikali ba.”
9Dawuda ya zauna a kagara. Ya ba ta suna Birnin Dawuda. Ya kuma yi gine-gine kewaye da wurin. Ya fara daga Millo zuwa ciki. 10Dawuda kuwa ya ƙasaita, gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana tare da shi.
(1 Tar 14.1-2)
11Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al'ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida. 12Dawuda kuwa ya gane lalle Ubangiji ya tabbatar da shi sarki bisa jama'ar Isra'ila, ya kuma ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa, Isra'ila.
(1 Tar 3.5-9; 14.3-7)
13Bayan zuwan Dawuda Urushalima daga Hebron, sai ya ɗauki waɗansu ƙwaraƙwarai, ya kuma auri waɗansu mata. Aka kuma haifa masa waɗansu 'ya'ya mata da maza. 14Sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima ke nan, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, 15da Ibhar, da Elishuwa, da Nefeg, da Yafiya, 16da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.
(1 Tar 14.8-17)
17Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila, sai dukansu suka haura zuwa neman ran Dawuda. Da Dawuda ya ji Filistiyawa suna nemansa, sai ya gangara zuwa kagara. 18Filistiyawa kuwa suka zo suka bazu a kwarin Refayawa. 19Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”
20Sai Dawuda ya zo Ba'al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.” 21Filistiyawa suka gudu, suka bar gumakansu a nan, Dawuda da mutanensa suka kwashe su.
22Filistiyawa suka sāke haurawa, suka bazu a kwarin Refayawa. 23Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka. 24Sa'ad da ka ji motsin rausayawar rassan itatuwan doka, sai ka yi maza, ka faɗa musu, gama Ubangiji zai wuce gaba domin ya bugi rundunar Filistiyawa.” 25Sai Dawuda ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya yi ta bugun Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.
(1 Tar 13.5-14)
1Dawuda kuma ya tattara zaɓaɓɓun mutane dubu talatin (30,000) na Isra'ila. 2Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.
6Da suka zo masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa ya riƙa akwatin alkawarin Allah, gama takarkaran sun yi kwarangyasa. 7Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari. 8Sai Dawuda ya ji haushi domin Ubangiji ya fashe haushinsa a kan Uzza. Aka sa wa wurin suna Feresauzza har wa yau.
9Dawuda kuwa ya ji tsoron Ubangiji a ran nan, ya ce, “Ƙaƙa zan ajiye akwatin alkawarin Ubangiji a wurina?” 10Domin haka Dawuda bai yarda ya kai akwatin alkawarin Ubangiji cikin Birnin Dawuda ba, sai ya kai shi gidan Obed-edom Bagitte. 11Akwatin alkawarin Ubangiji yana a gidan Obed-edom Bagitte har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa Obed-edom da dukan iyalinsa albarka.
(1 Tar 15.1ū16.6)
12Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda. 13Sa'ad da masu ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai Dawuda ya yi hadaya da sa, da keɓaɓɓiyar tunkiya. 14Dawuda ya sa falmaran ta lilin. Ya kuwa yi rawa da dukan ƙarfinsa a gaban Ubangiji. 15Shi da mutanen Isra'ila duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da busar ƙaho.
16Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, 'yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci. 17Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suka ajiye shi a wurinsa a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa dominsa. Dawuda ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama a gaban Ubangiji. 18Sa'ad da ya gama miƙa hadayun ƙonawa da na salama, sai ya sa wa mutanen albarka da sunan Ubangiji Mai Runduna. 19Ya kuma rarraba wa dukan taron jama'ar Isra'ila, mata da maza, ƙosai, da nama, da zabibi, sa'an nan dukan mutane suka watse, kowa ya tafi gidansa.
20Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, 'yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra'ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”
21Sai Dawuda ya ce wa Mikal, “Ai, na yi wannan a gaban Ubangiji wanda ya zaɓe ni a madadin mahaifinki da iyalinsa, ya naɗa ni in zama Sarkin Isra'ila, wato jama'ar Ubangiji. Lalle zan yi rawar farin ciki a gaban Ubangiji. 22Zan mai da kaina abin raini fiye da haka, zan kuma zama abin raini gare ki, amma barori mata da kika ambata, za su girmama ni.”
23Mikal, 'yar Saul fa, ba ta haihu ba har ta rasu.
(1 Tar 17.1-15)
1Sa'ad da sarki yake zaune a gidansa, Ubangiji kuma ya hutasshe shi daga fitinar abokan gābansa da suke kewaye da shi, 2sai sarki ya ce wa annabi Natan, “Duba, ga shi, ina zaune a gidan katakon al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana a alfarwa.”
3Natan kuwa ya ce wa sarki, “Sai ka yi abin da yake a zuciyarka, gama Ubangiji yana tare da kai.”
4Amma a daren nan Ubangiji ya yi magana da Natan. 5Ya ce, “Tafi, ka faɗa wa bawana Dawuda, ka ce, in ji Ubangiji, “‘Ɗakin zama za ka gina mini? 6Har wa yau ban taɓa zama a ɗaki ba, tun lokacin da na fito da Isra'ilawa daga Masar, amma a alfarwa nake kai da kawowa daga wannan wuri zuwa wancan. 7A cikin kai da kawowata tare da dukan jama'ar Isra'ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra'ila waɗanda na sa su lura da jama'ata Isra'ila, ya gina mini ɗaki na katakon al'ul ba.” 8Abin da za ka faɗa wa bawana Dawuda ke nan, in ji Ubangiji Mai Runduna, “‘Na ɗauko ka daga makiyaya inda kake kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila. 9Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.
17Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
(1 Tar 17.16-27)
18Sarki Dawuda ya tafi ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ko ni ko iyalina ba mu cancanci dukan abin da ka yi mana ba. 19Ga shi, ka ƙara fiye da haka, ya Ubangiji Allah, gama ka yi magana, cewa, gidan bawanka zai kai kwanaki masu tsawo. Wannan ka'ida ce ta 'yan adam! 20Me kuma zan ƙara ce maka, gama ka san bawanka, ya Ubangiji Allah. 21Bisa ga alkawarinka da yardar zuciyarka ne ka aikata waɗannan manyan al'amura domin ka sa in san su. 22Bisa ga dukan abin da muka ji, kai mai girma ne, ya Ubangiji Allah. Ba kamarka, in banda kai kuma babu wani Allah. 23Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar. 24Ka zaɓar wa kanka jama'ar Isra'ila su zama mutanenka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
25“Ya Ubangiji Allah, yanzu ka tabbatar da maganar da ka yi da bawanka da gidansa har abada. Ka aikata bisa ga faɗarka. 26Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, “‘Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila har abada.” Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka. 27Gama kai, ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kai ne ka sanar wa ni bawanka, cewa, za ka sa gidana ya kahu, saboda haka ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a a gare ka.
28“Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, kai ne Allah, kana cika alkawarinka koyaushe. Ka kuwa yi wa bawanka alkawari mai girma. 29Ka yarda da farin ciki ka sa wa gidan bawanka albarka domin gidansa ya dawwama a gabanka har abada, gama kai ne ka faɗa, ya Ubangiji Allah. Ka sa albarkarka ta tabbata a gidan bawanka har abada.”
(1 Tar 18.1-13)
1Bayan haka kuma sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar.
2Sa'an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa'an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.
3Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin. 4Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari. 5Suriyawan Dimashƙu kuwa, suka zo don su taimaki Hadadezer, Sarkin Zoba, Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa dubu ashirin da dubu biyu (22,000). 6Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi. 7Dawuda ya kwashe garkuwoyi na zinariya waɗanda shugabannin sojojin Hadadezer suka riƙe, ya kawo su Urushalima. 8Ya kuma kwashe tagulla da yawa daga Beta da Berotayi biranen Hadadezer.
9Sa'ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi, 10sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla. 11Dawuda ya keɓe wa Ubangiji kayayyakin nan tare da azurfa da zinariya da ya karɓe daga dukan al'umman da ya mallaka, 12wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.
13Dawuda kuwa ya yi suna. Ya kashe Edomawa dubu goma sha takwas (18,000) a kwarin Gishiri sa'ad da yake komowa. 14Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.
(2 Sam 20.23-26; 1 Tar 18.14-17)
15Dawuda ya mallaki Isra'ila duka. Ya yi wa dukan jama'arsa shari'ar gaskiya da adalci. 16Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban sojojin. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne marubuci. 17Zadok ɗan Ahitub, da Ahimelek ɗan Abiyata, su ne firistoci. Seraiya shi ne magatakarda. 18Benaiya ɗan Yehoyada, shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. 'Yan'yan Dawuda, maza, suka zama mataimakansa.
1Dawuda ya yi tambaya, ko akwai wani da ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna wa alheri saboda Jonatan.
2Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?” Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”
3Sa'an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah. Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”
4Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?” Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.” 5Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.
6Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”
7Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”
8Mefiboshet kuwa ya rusuna, ya ce, “Ni wane ne har da za ka kula da ni, ni da ban fi mataccen kare daraja ba?”
9Sa'an nan sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, “Dukan abin da yake na Saul, da dukan abin da yake na iyalinsa, na ba ɗan maigidanka. 10Kai, da 'ya'yanka maza, da barorinka za ku riƙa yi wa iyalin Saul noma, ku kawo musu amfanin domin su sami abinci, amma Mefiboshet kansa, zai riƙa cin abinci a teburina kullum.” (Ziba kuwa yana da 'ya'ya maza goma sha biyar, da barori ashirin.)
11Ziba ya amsa wa sarki, ya ce, “Baranka zai yi dukan abin da sarki ya umarta.” Mefiboshet kuwa ya riƙa cin abinci a teburin sarki kamar ɗaya daga cikin 'ya'yan sarkin. 12Mefiboshet yana da ɗa sunansa Mika. Dukan waɗanda suke zaune a gidan Ziba kuma suka zama barorin Mefiboshet. 13Mefiboshet kuwa ya zauna a Urushalima ya riƙa cin abinci a teburin sarki kullum. Dukan ƙafafunsa kuwa sun naƙasa.
(1 Tar 19.1-19)
1Sa'ad da Sarkin Ammonawa, wato Nahash, ya rasu, sai Hanun ɗansa ya gāje shi. 2Dawuda ya ce, “Zan yi wa Hanun alheri kamar yadda tsohonsa ya yi mini.” Dawuda kuwa ya aiki manzanni su yi masa ta'aziyya. Amma da suka isa can, 3sai hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne, da ya aiko manzanninsa su yi maka ta'aziyya? Ai, manzannin nan da ya aiko 'yan leƙen asirin ƙasa ne. Sun zo ne su bincika don su san yadda za a ci birnin.”
4Sai Hanun ya sa aka aske wa manzannin nan na Dawuda rabin gyammansu suka kuma yanyanke rigunansu daidai ɗuwawu, sa'an nan suka sallame su. 5Da aka faɗa wa Dawuda sai ya aika a tarye su, gama mutanen sun sha kunya ƙwarai. Sarki Dawuda ya ce musu su zauna a Yariko har gyammansu su toho, sa'an nan su komo.
6Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma'aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000). 7Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab da dukan rundunar jarumawan. 8Ammonawa suka fita suka ja dāgar yaƙi a ƙofar garin, amma Suriyawan Zoba da na Rehob, da mutanen Ish-tobi da na Ma'aka suka ja tasu dāgar a karkara.
9Da Yowab ya ga an ja masa dāgar yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu Isra'ilawa, ya sa su gabza da Suriyawa. 10Sauran mutane kuwa ya sa su a hannun Abishai, ƙanensa. Ya sa su gabza da Ammonawa. 11Ya ce musu, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, ku kawo mini gudunmawa, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinku, sai in kai muku gudunmawa. 12Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”
13Sa'an nan Yowab da mutanensa suka matsa, su gabza da Suriyawa. Suriyawa kuwa suka gudu. 14Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.
15Sa'ad da Suriyawa suka ga Isra'ilawa sun ci su, suka tattara kansu. 16Hadadezer ya aika aka kawo Suriyawan da suke a hayin Kogin Yufiretis. Suka taru a Helam. Shobak shugaban rundunar Hadadezer shi ne ya shugabance su. 17Sa'ad da Dawuda ya ji labari, ya tara Isra'ilawa duka, ya haye Urdun zuwa Helam. Suriyawa kuwa suka ja dāgar yaƙi, suka yi yaƙi da Dawuda. 18Amma Suriyawa suka gudu daga gaban Isra'ilawa. Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa, mahayan karusai ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba'in (40,000). Aka yi wa Shobak shugaban rundunarsu rauni wanda ya zama ajalinsa, a can ya rasu. 19Sa'ad da dukan hakiman Hadadezer suka ga Isra'ilawa sun ci su, sai suka yi sulhu da Isra'ilawa. Suka zama talakawansu. Wannan ya sa Suriyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudunmawa.
1Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra'ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.
2Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka. 3Sai ya aika a bincika kowacece wannan mata, ashe, 'yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte. 4Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa'an nan ta koma gidanta. 5Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.
6Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda. 7Da Uriya ya iso, sai Dawuda ya tambaye shi labarin Yowab, da lafiyar jama'ar, da labarin yaƙin. 8Ya kuma ce masa, “Ka tafi gidanka, ka wanke ƙafafunka.” Da Uriya ya fita daga gidan sarki, sarki ya ba da kyauta a kai masa. 9Amma Uriya bai tafi gidansa ba, sai ya kwana a ƙofar gidan sarki tare da sauran barorin sarki. 10Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”
11Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra'ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”
12Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan. 13Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.
14Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab. 15A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa'an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.” 16Sa'ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske. 17Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.
18Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.
22Manzon kuwa ya tafi ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Yowab ya ce. 23Ya ce, “Abokan gābanmu sun sami sa'a a kanmu. Sun fito su gabza da mu a karkara, amma muka kore su zuwa cikin ƙofar garin. 24Sai maharba suka tsaya a kan garu daga ciki suka yi ta harbin barorinka. Waɗansu daga cikin barorin sarki sun mutu. Baranka Uriya Bahitte shi ma ya matu.”
25Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”
26Sa'ad da matar Uriya ta ji labarin mutuwar mijinta, ta yi makoki dominsa. 27Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.
1Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci. 2Basaraken yana da garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. 3Amma talakan ba shi da kome sai 'yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da 'ya'yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar 'ya a gare shi. 4Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo 'yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”
5Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa. 6Sai kuma ya biya diyyar 'yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”
7Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, “‘Na naɗa ka Sarkin Isra'ila, na cece ka daga hannun Saul. 8Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra'ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka. 9Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka. 10Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka. 11Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā. 12Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra'ila da rana katā.”
13Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.” Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba. 14Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.” 15Sa'an nan Natan ya tafi gida.
Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda. 16Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare. 17Sai fādawansa suka zo suka kewaye shi, don su tashe shi daga ƙasa, amma bai yarda ba, bai kuma ci abinci tare da su ba. 18An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”
19Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?” Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”
20Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa'an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci. 21Fādawansa suka ce masa, “Me ka yi ke nan? Ka yi azumi, ka yi kuka saboda yaron tun yana da rai, amma da yaron ya rasu ka tashi, ka ci abinci.”
22Ya ce musu, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi da kuka, ina cewa wa ya sani, ko Ubangiji zai yi mini jinƙai, ya bar yaron da rai? 23Amma yanzu ya rasu, me zai sa kuma in yi azumi? Zan iya koma da shi ne? Ni zan tafi wurinsa, amma shi ba zai komo wurina ba.”
24Sa'an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta'aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi, 25ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.
(1 Tar 20.1-3)
26Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin. 27Sai ya aiki manzanni wurin Dawuda ya ce, “Na yaƙi Rabba, na kama hanyar samun ruwansu. 28Yanzu ka tara sauran sojoji ka fāɗa wa birnin, ka ci shi da kanka. Gama ba na so in yi suna da cin birnin.” 29Saboda haka sai Dawuda ya tara sauran sojoji duka, ya tafi Rabba, ya yi yaƙi da ita, ya kuwa ci birnin. 30Sarkinsu, wato Milkom, yana da kambi na zinariya a kansa, nauyinsa ya kai talanti ɗaya na zinariya yana kuma da duwatsu masu daraja cikinsa. Dawuda kuwa ya ɗauke kambin daga kan sarkin ya sa a nasa. Sa'an nan ya kwaso ganima mai ɗumbun yawa daga cikin birnin. 31Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.
1Absalom, ɗan Dawuda, yana da kyakkyawar ƙanwa, sunanta Tamar. Ana nan Amnon ɗaya daga cikin 'ya'yan Dawuda, ya ƙaunace ta. 2Amnon ya matsu har ya fara ciwo saboda Tamar ƙanwarsa. Ita kuwa budurwa ce, ba shi yiwuwa Amnon ya yi wani abu da ita. 3Amma Amnon yana abuta da Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda. Yonadab kuwa yana da hila. 4Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?” Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan'uwana Absalom.”
5Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, “‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.” 6Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo. Sa'ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”
7Sai Dawuda ya aika gida, wurin Tamar, ya ce, “Tafi gidan Amnon wanki, ki shirya masa abinci.” 8Tamar kuwa ta tafi gidan wanta Amnon, inda yake kwance. Sai ta ɗauki ƙullu, ta cuɗa, ta toya waina a idonsa. 9Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.
10Sa'an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana. 11Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”
12Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra'ila, kada ka yi halin dabba. 13Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra'ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.” 14Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.
15Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”
16Sai ta ce masa, “A'a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.” Amma bai kasa kunne gare ta ba. 17Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”
18Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar. 19Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.
20Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta. 21Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai. 22Amma Absalom bai tanka wa Amnon da wata magana ta alheri ko ta mugunta ba, gama yana ƙin Amnon saboda ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.
23Bayan shekara biyu cif, sai Absalom ya sa a yi masa sausayar tumaki a Ba'al-hazor, wadda take kusa da Ifraimu. Ya kuma gayyaci dukan 'yan'uwansa, wato 'yan sarki. 24Ya kuma tafi wurin sarki, ya ce masa, “Ranka ya daɗe, ga shi, ina sausayar tumakina, ina roƙonka, ka zo, kai da fādawanka tare da ni.”
25Amma sarki ya ce wa Absalom, “A'a ɗana, ba ma tafi duka ba, don kada mu nawaita maka.” Absalom ya dāge cewa, sai sarki ya je, amma duk da haka sarki bai tafi ba, sai dai ya sa masa albarka.
26Sa'an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan'uwana ya tafi tare da mu.” Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?” 27Amma Absalom ya dāge har sarki ya yarda. Amnon da dukan 'ya'yan sarki suka tafi tare da shi.
28Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa'ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, “‘Bugi Amnon,” sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.” 29Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran 'ya'yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.
30Sa'ad da suke kan hanya labari ya kai kunnen Dawuda. Aka ce, “Absalom ya kashe dukan 'ya'yan sarki, ba wanda ya tsira daga cikinsu.” 31Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu. 32Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan 'ya'yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe. 33Don haka, kada shugabana sarki ya damu, cewa, an kashe dukan 'ya'yan sarki, gama Amnon ne kaɗai aka kashe.”
34Absalom kuwa ya gudu. Sa'an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse. 35Sai Yonadab ya ce wa sarki, “Waɗannan 'ya'yan sarki ne suke zuwa, kamar yadda na faɗa.” 36Yana gama magana ke nan, sai ga 'ya'yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.
37Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.
38Absalom ya shekara uku a Geshur. 39Sai zuciyar sarki ta koma kan Absalom, gama ya haƙura a kan Amnon da yake ya riga ya rasu.
1Da Yowab ɗan Zeruya, ya gane zuciyar sarki ta koma kan Absalom, 2sai ya aika zuwa Tekowa a kira masa wata mace mai hikima. Da ta zo, ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki, ki sa rigunan makoki, kada ki shafa mai. Ki yi kamar wadda ta yi kwanaki da yawa tana makokin rasuwar wani. 3Sa'an nan ki tafi wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai ya faɗa mata abin da za ta faɗa.
4Sa'ad da macen nan da ta zo daga Tekowa ta isa gaban sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma. Sa'an nan ta ce, “Ya sarki, ka yi taimako.”
5Sai sarki ya tambaye ta, “Me ya dame ki?” Ta ce, “Ni mace ce wadda mijinta ya rasu. 6Baranyarka tana da 'ya'ya biyu maza, sai suka yi faɗa a gona, inda ba wanda zai raba su, ɗayan kuwa ya bugi ɗayan ya kashe shi. 7Yanzu kuwa dukan dangi sun tasar mini, suna cewa, in ba da ɗayan wanda ya kashe ɗan'uwansa domin su kashe shi saboda ran ɗan'uwansa da ya kashe. Wato za su hallaka magāji ke nan, ta haka za a yi biyu babu ke nan, su bar mijina ba suna ko zuriya a duniya.”
8Sarki kuwa ya ce mata, “Ki tafi gidanki, zan daidaita maganarki.”
9Sai ta ce wa sarki, “Ya ubangijina, sarki, bari laifin ya zauna a kaina da gidan mahaifina, sarki kuwa da gadon sarautarsa ya barata.”
10Sarki ya ce mata, “In wani ya ƙara ce miki wani abu, ki kawo shi wurina, ba zai ƙara yi miki fitina ba.”
11Sai ta ce, “Ina roƙonka, ya sarki, ka rantse da Ubangiji Allahnka, kada a bar masu bin hakkin jini su yi ramako, don kada su kashe ɗana.” Ya ce mata, “Na rantse miki da zatin Ubangiji, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba.”
12Ta kuma ce, “Ina roƙonka, ya ubangijina sarki, ka bar ni in yi magana.” Sai ya ce, “Yi maganarki.”
13Sa'an nan ta ce, “To, me ya sa ka yi wa jama'ar Allah irin wannan abu? Gama bisa ga maganar bakinka, ya sarki, ka hukunta kanka tun da yake sarki bai yarda ɗansa ya komo gida ba. 14Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba. 15Saboda mutane sun tsorata ni shi ya sa na zo in faɗa wa ubanjijina, sarki. Na kuwa yi tunani na ce, “‘Zan tafi in faɗa wa sarki, watakila sarki zai amsa roƙona. 16Gama sarki zai ji, ya cece ni daga hannun mutumin nan da zai hallaka ni tare da ɗana daga cikin jama'ar Allah.” 17Na kuma yi tunani a kan maganar ubangijina, sarki, za ta kwantar da zuciyata, gama ubangijina, sarki, kamar mala'ikan Allah yake, yana rarrabe tsakanin nagarta da mugunta. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da kai!”
18Sai sarki ya ce mata, “Kada ki rufe mini duk abin da zan tambaye ki.” Ta ce, “To, ka yi tambayarka.”
19Sa'an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha'anin nan naki?” Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka. 20Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al'amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala'ikan Allah domin ya san dukan al'amuran da suke a duniya.”
21Sa'an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”
22Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.” 23Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima. 24Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.
25A cikin Isra'ila duka ba wanda ake yaba kyansa kamar Absalom. Tun daga tafin sawunsa har zuwa bisa kansa ba shi da makusa. 26Sa'ad da ya yi aski yakan auna nauyin gashin kansa, nauyin yakan kai wajen shekel ɗari biyu. Gama a ƙarshen kowace shekara yake aski, sa'ad da gashin ya yi masa nauyi. 27Aka haifa wa Absalom 'ya'ya uku maza da 'ya mace guda, sunanta Tamar, ita kuwa kyakkyawa ce.
28Absalom ya yi shekara biyu cif a Urushalima, amma bai sami izinin ganin sarki ba. 29Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Ya kuma sāke aikawa, Yowab kuwa ya ƙi zuwa. 30Sai ya ce wa barorinsa, “Ga Yowab yana da gonar sha'ir kusa da tawa, ku tafi, ku sa mata wuta.” Barorin Absalom kuwa suka tafi suka sa wa gonar wuta.
31Yowab kuwa ya tashi ya tafi wurin Absalom har gidansa, ya ce masa, “Don me barorinka suka sa wa gonata wuta?”
32Absalom ya ce wa Yowab, “Har sau biyu na aika maka domin ka zo in aike ka wurin sarki, ka tambaya mini, “‘Ko me ya sa na komo daga Geshur?” Da ma ina can har yanzu, ai, da ya fi mini. Yanzu har ni in tafi wurin sarki, idan ina da laifi, ta, ya kashe ni.”
33Sai Yowab ya tafi wurin sarki, ya faɗa masa. Sarki ya sa a kira Absalom. Absalom kuwa ya zo gaban sarki, ya rusuna har ƙasa. Sarki kuwa ya marabce shi, ya yi masa sumba.
1Bayan wannan Absalom ya samo wa kansa karusa, da dawakai, da zagage mutum hamsin. 2Absalom yakan tashi da wuri, ya tsaya a kan hanyar da yake shiga ƙofar garin. Idan wani mai kai ƙara ya zo wurin sarki don shari'a, Absalom yakan kira shi, ya ce, “Daga ina kake?” Idan mutumin ya faɗa masa garin da ya fito daga cikin Isra'ila, 3sai Absalom ya ce masa, “Ƙararka tana da kyau, tana kuma da gaskiya, amma sarki ba zai yi maka shari'a ba.” 4Yakan kuma ƙara da cewa, “Kai, in da a ce ni ne alƙali a ƙasar, zan yi wa duk wanda ya zo wurina da ƙara, shari'ar gaskiya.” 5Sa'ad da mutum ya je kusa da shi ya rusuna don ya gaishe shi, Absalom kuwa yakan rungume mutumin ya sumbace shi. 6Haka Absalom ya riƙa ya wa dukan Isra'ilawan da suka zo wurin sarki don shari'a. Da haka ya saci zukatan mutanen Isra'ila.
7Bayan shekara huɗu sai Absalom ya ce wa sarki, “Ina roƙonka, ka yardar mini in je Hebron in cika wa'adina wanda na yi wa Ubangiji. 8Gama na yi wa'adi sa'ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa'adi cewa, “‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.”
9Sarki ya ce masa, “To, ka sauka lafiya.” Sai ya tashi ya tafi Hebron. 10Amma Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra'ila a faɗa musu haka, “Da zarar kun ji an busa ƙaho, sai ku ce, “‘Absalom shi ne sarki, yana Hebron.” 11Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba. 12Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.
13Ana nan sai wani manzo ya zo wurin Dawuda, ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra'ila suna wajen Absalom.”
14Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da yake tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”
15Fādawan suka ce, “Mu a shirye muke mu yi dukan abin da ubangijinmu sarki ya faɗa.” 16Sarki ya fita, iyalinsa suka bi shi, amma ya bar ƙwaraƙwarai goma su lura da gidan.
17Sarki ya fita yana tafiya da ƙafa, dukan mutane kuwa suna biye da shi. Da suka zo Bet-Merhak, wato gida na ƙarshe sai suka tsaya. 18Dukan fādawansa, da matsaransa, wato dukan Keretiyawa, da dukan Feletiyawa, da dukan Gittiyawa, sojoji ɗari shida waɗanda suka bi Dawuda tun daga Gat suka wuce a gabansa. 19Sarki kuwa ya ce wa Ittayi, shugabansu, “Don me kai kuma za ka tafi tare da mu? Koma ka zauna wurin sabon sarki, gama kai baƙo ne, ɗan gudun hijira kuma daga ƙasarku. 20Jiya jiya ka zo, ba daidai ba ne in sa ka ka yi ta ragaita tare da mu, ga shi, ban san inda zan tafi ba. Koma tare da 'yan'uwanka. Ubangiji ya nuna maka alherinsa, da amincinsa.”
21Amma Ittayi ya amsa wa sarki, ya ce, “Na rantse da zatin Ubangiji da darajar ubangijina, sarki, duk inda za ka tafi ko a mutu ko a yi rai zan tafi.”
22Sai Dawuda ya ce masa, “To, wuce gaba.” Ittayi Bagitte kuwa ya wuce gaba tare da dukan mutanensa da 'yan yaransu. 23Dukan ƙasar ta yi ta kururuwa sa'ad da mutane suka tashi. Sarki ya haye rafin Kidron, mutane kuma suka haye, suka nufi jeji.
24Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin. 25Sa'an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa. 26Amma idan Ubangiji bai ji daɗina ba, to, ga ni, sai ya yi yadda ya ga dama da ni.” 27Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata. 28Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.” 29Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.
30Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa'ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka. 31Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.” Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”
32Da Dawuda ya hau kan dutse inda ake yi wa Allah sujada, sai ga amininsa Hushai Ba'arkite, da ketacciyar riga, da ƙura a kansa, ya zo ya taryi Dawuda. 33Dawuda kuwa ya ce masa, “Idan ka tafi tare da ni za ka zama mini nawaya. 34Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, “‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.” Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel. 35Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci. 36Ga 'ya'yansu biyu suna tare da su a can, wato Ahimawaz, ɗan Zadok, da Jonatan, ɗan Abiyata. Duk abin da ka ji, ka aiko su, su zo su faɗa mini.”
37Hushai, abokin Dawuda kuwa, ya isa Urushalima daidai lokacin da Absalom yake shiga.
1Sa'ad da Dawuda ya wuce ƙwanƙolin dutsen kaɗan, sai ga Ziba baran Mefiboshet ya sadu da shi. Ya zo da jaki biyu ya yi musu labtu da gurasa dunƙule ɗari biyu, da zabibi ɗari, da sababbin 'ya'yan itace guda ɗari, da salkar ruwan inabi. 2Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?” Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da 'ya'yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”
3Sarki kuma ya tambaye shi, “Ina ɗan ubangijinka?” Sai Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima, yana cewa, “‘Yanzu dai mutanen gidan Isra'ila za su mayar mini da sarautar tsohona.”
4Da jin haka sai sarki ya ce wa Ziba, “Dukan abin da yake na Mefiboshet ya zama naka.” Ziba kuma ya rusuna ya yi godiya ya ce, “Bari in zama majidaɗin ubangijina, sarki.”
5Sa'ad da Dawuda ya kai Bahurim, sai ga wani mutum sunansa Shimai, ɗan Gera, daga iyalin gidan Saul, ya fito yana ta zagi. 6Ya jajjefi Dawuda da fādawansa da duwatsu, da sauran jama'a, da dukan jarumawan da suke kewaye da shi. 7Shimai ya yi ta zagi, yana cewa, “Tafi, tafi, kai mai kisankai, sakarai. 8Ubangiji ya sāka maka saboda alhakin jinin gidan Saul, wanda ka hau gadon sarautarsa. Yanzu Ubangiji ya ba da sarautar ga Absalom, ɗanka. Duba, masifa ta auko maka, gama kai mai kisankai ne.”
9Sai Abishai, ɗan Zeruya, ya ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, don me za ka bar wannan kare yana ta zaginka? Bari in tafi in fille masa kai.”
10Amma sarki ya ce masa, “Ba ruwanku, ku 'ya'yan Zeruya. Idan yana zagi saboda Ubangiji ya sa shi, to, wa ya isa ya ce, “‘Don me kake yin haka?” 11Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi. 12Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.” 13Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature. 14Sarki da dukan jama'ar da suke tare da shi suka isa Urdun a rafke. Sai suka shaƙata.
15Absalom kuwa ya zo Urushalima tare da dukan mutanen Isra'ila da suke tare da shi. Ahitofel kuma yana tare da shi. 16Sa'ad da Hushai Ba'arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”
17Sai Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake yi wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
18Hushai ya amsa, ya ce, “Ba haka ba, ni dai zan zama na wanda Ubangiji, da wannan jama'a, dukan mutanen Isra'ila suka zaɓa. Zan zauna tare da mutumin da aka zaɓa. 19Banda haka ma, wane ne ya kamata in bauta wa, in ba ɗan ubangidana ba? Kamar yadda na bauta wa tsohonka, haka kuma zan bauta maka.”
20Sa'an nan Absalom ya juya wajen Ahitofel, ya ce, “To, ka kawo shawararka a kan abin da ya kamata mu yi?”
21Ahitofel kuwa ya ce wa Absalom, “Ka shiga ka kwana, da ƙwarakwaran tsohonka waɗanda ya bar su su lura da gidan. Dukan Isra'ilawa za su sani ba shiri kuma tsakaninka da tsohonka. Dukan masu goyon bayanka kuma za su ƙara ƙarfafa.” 22Sai suka kafa wa Absalom alfarwa a bisa kan soro, ya shiga ya kwana da ƙwaraƙwaran tsohonsa, a idon mutanen Isra'ila duka.
23Shawarar da Ahitofel yake bayarwa a lokacin nan ta zama kamar faɗar Allah ce. Absalom duk da Dawuda, shawarar Ahitofel suke bi.
1Ahitofel ya kuma ce wa Absalom, “Bari in zaɓi mutum dubu goma sha biyu (12,000), mu tafi mu bi Dawuda da daren nan. 2Zan fāɗa masa sa'ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya, in firgitar da shi. Dukan mutanen da suke tare da shi za su gudu. Shi kaɗai zan kashe. 3Zan kawo maka dukan jama'a kamar yadda akan kawo amarya a gidan angonta. Ran mutum guda kaɗai kake nema, sauran mutane duka kuwa su yi zamansu lafiya.” 4Wannan shawara ta gamshi Absalom da dattawan Isra'ila.
5Sa'an nan Absalom ya ce, “A kirawo Hushai Ba'arkite don mu ji abin da shi kuma zai faɗa.” 6Da Hushai ya zo, sai Absalom ya ce masa, “Ga shawarar da Ahitofel ya bayar, mu bi ta? Ko kuwa? Kai, me ka ce?”
7Sai Hushai ya ce wa Absalom, “A wannan lokaci dai shawarar da Ahitofel ya bayar ba ta da kyau.” 8Hushai ya ci gaba da cewa, “Ka san tsohonka da jama'arsa jarumawa ne, yanzu a husace suke kamar damisar da aka kwashe wa 'ya'ya a jeji. Tsohonka kuma ya ƙware da sha'anin yaƙi, ba tare da mutanensa zai kwana ba. 9Yanzu haka yana cikin rami ko dai a wani wuri a ɓoye. Idan an kashe waɗansu daga cikin mutanenka a karo na farko, duk wanda ya ji zai ce, “‘An kashe mutane da yawa daga cikin mutanen Absalom.” 10Wannan zai sa jarumi wanda yake da zuciya kamar ta zaki ya karaya don tsoro, gama dukan mutanen Isra'ila sun sani tsohonka jarumi ne, su kuma waɗanda suke tare da shi jarumawa ne. 11Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra'ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin. 12Da haka za mu tafi mu neme shi duk inda yake, mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo bisa ƙasa. Da shi da mutanensa, ba wanda za a bari da rai. 13Idan ya gudu zuwa cikin gari, sai dukan jama'armu su zarge garin da igiya, su jā har duk ya watse, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”
14Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.
15Sa'an nan Hushai ya ce wa Zadok da Abiyata, firistoci, “Ga irin shawarar da Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Isra'ila, ga kuma irin wadda ni na bayar. 16Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”
17Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin. 18Amma wani saurayi ya gan su, sai ya faɗa wa Absalom. Sai su biyu ɗin suka gudu nan da nan. Suka shiga gidan wani mutum a Bahurim, akwai rijiya a filin gidan. Sai suka shiga rijiyar. 19Matar gidan kuwa ta yi shimfiɗa a bakin rijiyar, ta baza tsaba a kai, ba kuwa wanda ya san abin da ta yi. 20Sa'ad da fādawan Absalom suka zo gidan, suka tambayi matar, “Ina Ahimawaz da Jonatan suke?” Sai ta ce musu, “Ai, tuni sun haye kogi.” Sa'ad da suka neme su ba su same su ba, sai suka koma Urushalima. 21Bayan da fādawan sun tafi, sai mutanen suka fito daga rijiyar. Suka tafi suka ce wa sarki Dawuda, “Ka tashi ka haye kogin nan da nan, gama ka ji irin muguwar shawarar da Ahitofel ya bayar a kanka.” 22Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka haye Urdun. Kafin wayewar gari ko wannensu ya haye Urdun.
23Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.
24Dawuda kuwa ya zo Mahanayim. Absalom kuma da dukan mutanen Isra'ila suka haye Urdun. 25Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab. 26Absalom da mutanen Isra'ila suka kafa sansaninsu a ƙasar Gileyad.
27Sa'ad da Dawuda ya kai Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lodebar, da Barzillai Bagileyade daga Rogelim, 28suka kawo wa Dawuda da jama'arsa waɗannan kaya da abinci, wato gadaje, da tasoshi, da tukwane, da alkama, da sha'ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa, 29da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu. Gama sun sani Dawuda da mutanensa suna jin yunwa, da gajiya, da kishi, a cikin jeji.
1Dawuda kuwa ya shirya sojojin da suke tare da shi, sa'an nan ya naɗa musu shugabanni na dubu dubu da na ɗari ɗari. 2Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa'an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”
3Amma sojojin suka ce, “Ba za ka tafi tare da mu ba, gama idan muka gudu, ba za su kula da mu ba. Ko rabinmu sun mutu, ba za su kula ba, gama kai kana bakin mutum dubu goma (10,000) na mutanenmu. Zai fi kyau kuma ka zauna cikin gari ka riƙa aika mana da taimako.”
4Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu. 5Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.
6Sojojin suka tafi zuwa karkara don su yi yaƙi da mutanen Isra'ila. Suka yi yaƙin a kurmin Ifraimu. 7Mutanen Isra'ila suka sha kashi a hannun jarumawan Dawuda. A wannan rana aka kashe mutane da yawa, har mutum dubu ashirin (20,000). 8Yaƙin ya bazu ko'ina a ƙasar. A ranar abin da kurmin ya ci ya fi abin da aka kashe da takobi.
9Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo. 10Da wani mutum ya gani, sai ya tafi ya faɗa wa Yowab, ya ce, “Na ga Absalom yana reto a itacen oak.”
11Yowab ya ce wa mutumin da ya faɗa masa, “Kai! Ka gan shi! Me ya sa ba ka buge shi har ƙasa ba? Ai, da na ba ka azurfa goma da abin ɗamara.”
12Sai mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a ba ni azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba, gama a kunnuwanmu sarki ya umarce ka, kai da Abishai, da Ittayi cewa, “‘Ku lura mini da saurayin nan, Absalom.” 13In da na ci amana har na kashe shi, ba yadda abin zai ɓoyu ga sarki, sa'an nan kai da kanka ka zame, ka bar ni.”
14Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci haka da kai ba.” Sai ya ɗibi mashi uku ya soki Absalom a ƙahon zuciya, tun yana da sauran rai, a maƙale cikin itacen oak. 15Sa'an nan samari goma masu ɗaukar wa Yowab makamai, suka kewaye Absalom, suka yi ta dūkansa har ya mutu.
16Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra'ilawa. Yowab ya tsai da su. 17Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.
18Tun Absalom yana da rai ya gina wa kansa al'amudi a kwarin sarki, gama ya ce, “Ba ni da ɗa wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Ya kira al'amudin da sunansa. Ana kuwa kiransa al'amudin Absalom har wa yau.
19Ahimawaz ɗan Zadok ya ce wa Yowab, “Ka yarda mini in sheƙa a guje in kai wa sarki labari yadda Ubangiji ya cece shi daga hannun magabtansa.”
20Yowab ya ce masa, “Ba za ka kai labari yau ba, sai wata rana ka kai, amma yau ba za ka kai labari ba, domin ɗan sarki ya mutu.” 21Sa'an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa'an nan ya sheƙa a guje.
22Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.” Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”
23Ahimawaz ya ce, “Duk dai abin da zai faru, zan tafi.” Sai Yowab ya yardar masa ya tafi. Sa'an nan Ahimawaz ya sheƙa, ya bi ta hanyar fili, ya wuce Bahabashen.
24Dawuda kuwa yana zaune a tsakanin ƙofofi biyu na garin. Mai tsaro ya hau kan soron da yake kan bangon garu. Da ya ɗaga kai ya duba, sai ya ga mutum yana gudu shi kaɗai. 25Ya ta da murya, ya faɗa wa sarki. Sai sarki ya ce, “Idan shi kaɗai ne, yana kawo labari ne.” Mutumin ya yi ta ƙara zuwa kusa.
26Mai tsaron kuma ya ga wani mutum yana zuwa shi ma a guje, sai ya ta da murya wajen mai ƙofar garin, ya ce, “Ga wani mutum kuma yana zuwa a guje!” Sai sarki ya ce, “Shi ma labari yake kawowa.”
27Mai tsaron ya ce, “Na ga gudun na farin kamar gudun Ahimawaz ɗan Zadok.” Sai sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana kawo kyakkyawan labari ne.”
28Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”
29Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?” Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa'ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”
30Sarki kuwa ya ce, “Koma waje ɗaya, ka tsaya.” Sai ya koma waje ɗaya ya tsaya cik.
31Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”
32Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?” Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”
33Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”
1Aka faɗa wa Yowab, cewa, sarki yana kuka, yana makoki domin Absalom. 2Saboda haka sai nasarar da aka ya a ranar ta zama makoki ga jama'a duka, gama jama'a suka ji an ce sarki yana baƙin ciki domin ɗansa. 3Sojojin suka shiga birni sururu kamar waɗanda sukan shiga birni a ɓoye da kunya saboda sun gudu daga wurin yaƙi. 4Sarki ya rufe fuskarsa, ya yi kuka da ƙarfi, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ya Absalom, ɗana, ɗana!”
5Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan 'ya'yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka. 6Gama kana ƙaunar maƙiyanka, amma kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Gama yau ka bayyana a fili, shugabannin sojojinka da fādawanka ba a bakin kome suke a gare ka ba. Gama yau na gane da a ce Absalom yana da rai, mu kuwa muka mutu duka, da daɗi za ka ji. 7Don haka sai ka tashi yanzu, ka fita ka yi wa mutanenka magana mai daɗi. Gama na rantse da Ubangiji idan ba ka fita ba, ba wanda zai zauna tare da kai da daren nan. Wannan kuwa zai fi muni fiye da kowane irin mugun abin da ya taɓa samunka tun daga ƙuruciyarka har zuwa yanzu.” 8Sa'an nan sarki ya tashi, ya zauna a dandalin ƙofar garu. Aka faɗa wa mutanensa duka, cewa, ga sarki yana zaune a dandalin ƙofar garu. Mutanensa duka kuwa suka zo suka kewaya sarki.
Bayan wannan sai dukan Isra'ilawa suka gudu, kowa ya tafi gidansa. 9Dukan mutanen ƙasar Isra'ila suna ta jayayya, suna cewa, “Sarki Dawuda ne ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya cece mu daga hannun Filistiyawa, to, ga shi, ya gudu daga ƙasar don ya tsere wa Absalom. 10Ga shi kuma, Absalom ɗin da muka naɗa ya zama sarkinmu, an kashe shi a yaƙi. Yanzu fa, me ya sa muka yi shiru ba mu komo da sarki ba?”
11Da labarin abin da Isra'ilawa suke cewa, ya zo gun sarki Dawuda, sai ya aika zuwa wurin firistoci, wato Zadok da Abiyata, a faɗa musu su tambayi dattawan Yahuza abin da ya sa suka zama na ƙarshe a kan komar da sarki a gidansa. 12Ya ce, “Ai, ku 'yan'uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki? 13Ku ce wa Amasa, “‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.” 14Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.
15Sa'ad da sarki ya iso Urdun. Mutanen Yahuza suka tafi Gilgal suka taryi sarki, domin su hawo da shi Urdun. 16Shimai ɗan Gera kuma, mutumin Biliyaminu daga Bahurim, ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuza don ya taryi sarki Dawuda. 17Ya zo tare da mutum dubu (1,000) daga kabilar Biliyaminu. Ziba kuma, baran gidan Saul, ya zo a gaggauce a gaban sarki a Urdun tare da 'ya'yansa maza, su goma sha biyar, da barorinsa guda ashirin. 18Suka haye zuwa wancan hayi don su hawo da iyalin sarki, su kuma yi masa abin da zai ji daɗi. Sa'ad da sarki yake shirin hayewa, sai Shimai ɗan Gera ya zo ya fāɗi a gābansa. 19Ya ce wa sarki, “Ina roƙon ubangijina, sarki, in ka yarda kada ka riƙe baranka da laifi, kada ka tuna da laifin da baranka ya yi a ranar da ubangijina sarki yake gudu daga Urushalima. Kada sarki ya riƙe wannan a zuci. 20Gama na sani, ranka ya daɗe, na yi laifi, shi ya sa na zama na farko daga gidan Yusufu yau da na fito domin in taryi ubangijina sarki.”
21Abishai ɗan Zeruya kuwa ya ce, “Ya kamata a kashe Shimai gama ya zagi wanda Ubangiji ya zaɓa ya zama sarki.”
22Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan'uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra'ila yanzu, don haka ba Ba'isra'ilen da za a kashe a yau.” 23Sa'an nan ya ce wa Shimai, “Ina tabbatar maka, cewa, ba za a kashe ka ba.”
24Sa'an nan Mefiboshet jikan Saul ya gangara ya taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har zuwa ranar da ya komo da nasara Mefiboshet bai wanke ƙafafunsa ba, bai kuma yi gyaran fuska ba, bai ma wanke tufafinsa ba. 25Sa'ad da ya iso daga Urushalima don ya taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet?”
26Mefiboshet ya amsa ya ce, “Ya ubangijina, sarki, barana ya ruɗe ni, gama na ce masa ya yi wa jaki shimfiɗa don in hau in tafi wurin sarki, gama ka sani ni gurgu ne, ranka ya daɗe. 27Barana ya ɓata sunana a gaban ubangijina, sarki. Amma ranka ya daɗe, ya sarki, kai kamar mala'ikan Allah kake, sai ka yi abin da ya yi maka daidai. 28Gama dukan mutanen gidan kakana sun cancanci mutuwa a gabanka, ranka ya daɗe, amma ga shi, ka sa na zama ɗaya daga cikin waɗanda suke ci a teburinka. Ba ni da dalilin da zai sa in yi wa sarki wani kuka kuma.”
29Sai sarki ya ce masa, “Me ya kawo wannan magana a kan harkokinka? Ai, na riga na zartar, cewa, kai da Ziba za ku raba mallakar Saul.”
30Mefiboshet ya ce wa sarki, “A ma bar masa duka ya mallaka, ni dai tun da ubangijina, sarki, ya komo gida lafiya, to, alhamdu lillahi.”
31Barzillai Bagileyade kuma ya gangara daga Rogelim zuwa wurin sarki domin ya yi wa sarki rakiya zuwa hayin Urdun. 32Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa'ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne. 33Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka zo mu tafi tare zuwa Urushalima, ni kuwa zan riƙa biya maka bukata.”
34Amma Barzillai ya amsa, ya ce, “Shekaruna nawa suka ragu har da zan tafi Urushalima tare da sarki? 35A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe. 36Ban cancanci wannan irin babban lada ba. Zan dai yi maka 'yar rakiya zuwa hayin Urdun. 37Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”
38Sarki ya ce, “To, Kimham zai tafi tare da ni, zan kuwa yi masa abin da zai yi maka daɗi. Duk abin da kake so a gare ni, zan yi maka.” 39Sa'an nan dukan jama'a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.
40Sarki kuwa ya yi tafiya zuwa Gilgal. Kimham kuma ya tafi tare da shi. Mutanen Yahuza duka, da rabin mutanen Isra'ila suna tafe tare da sarki. 41Sai dukan mutanen Isra'ila suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Me ya sa mutanen Yahuza 'yan'uwanmu, suka sace ka, suka kawo sarki da iyalinsa a wannan hayin Urdun, tare da dukan mutanensa?”
42Dukan mutanen Yahuza suka amsa wa mutanen Isra'ila suka ce, “Domin sarki ɗan'uwanmu ne na kusa. Me ya sa kuke fushi a kan wannan al'amari? Me muka ci a jikin sarki, ko kun ji ya ba mu wani abu ne?”
43Isra'ilawa kuma suka amsa wa mutanen Yahuza, suka ce, “Muna da rabo goma a wurin sarki Dawuda fiye da ku, don me kuka raina mu? Ba mu ne muka fara maganar komowar sarki ba?” Amma maganar mutanen Yahuza ta fi ta mutanen Isra'ila zafi.
1Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.” 2Sai dukan Isra'ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.
3Da Dawuda ya koma gidansa a Urushalima, kwarakwaran nan nasa guda goma waɗanda ya bar su tsaron gida ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya yi ta lura da su, amma bai shiga wurinsu ba. Haka suka zauna a keɓe, suna zaune kamar gwauraye.
4Sa'an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mini mutanen Yahuza kafin kwana uku, kai kuma ka zo tare da su.” 5Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuza, amma ya makara, bai zo a lokacin da aka ƙayyade masa ba. 6Dawuda kuma ya ce wa Abishai, “Sheba ɗan Bikri fa, zai ba mu wuya fiye da Absalom, sai ka ɗauki mutanena, ka bi sawunsa, don kada ya ci garuruwa masu garu har ya tsere mana.” 7Sa'an nan mutanen Yowab, wato Keretiyawa da Feletiyawa, da dukan jarumawa, suka bi bayan Abishai. Suka fita daga Urushalima don su bi sawun Sheba, ɗan Bikri.
8Sa'ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi. 9Yowab ya ce wa Amasa, “Abokina kana lafiya?” Yowab kuma ya kama gemun Amasa da hannun dama don ya sumbace shi. 10Amma Amasa bai lura Yowab yana da takobi a hannunsa ba. Yowab kuwa ya kirɓa masa takobin a ciki sau ɗaya, sai hanjin Amasa ya zuba ƙasa, ya mutu. Sa'an nan Yowab da Abishai ɗan'uwansa suka bi sawun Sheba, ɗan Bikri. 11Sai ɗaya daga cikin samarin Yowab ya tsaya kusa da gawar Amasa ya ce, “Duk wanda yake son Yowab da duk wanda yake goyon bayan Dawuda, ya bi Yowab.” 12Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya. 13Sa'ad da aka kawar da ita daga kan hanya, dukan mutane kuwa suka bi Yowab domin su bi sawun Sheba ɗan Bikri.
14Sai Sheba ya bibiya kabilan Isra'ila, har ya kai Abel-bet-ma'aka. Dukan dangin Beri kuwa suka taru suka bi shi zuwa cikin garin. 15Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma'aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun. 16Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.” 17Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “I, ni ne.” Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.” Ya ce, “Ina sauraronki.”
18Ta ce, “A dā sukan ce, “‘A nemi shawara a Abel,” gama a can ake raba gardama. 19Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra'ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”
20Yowab ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Ba zan lalatar ko in hallakar da birninku ba. 21Ba haka ba ne, ni dai ina neman mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu, wanda ake ce da shi Sheba, ɗan Bikri. Shi ne ya tayar wa sarki Dawuda. Shi kaɗai za ku ba ni, ni kuwa zan janye daga garin.” Macen kuwa ta ce wa Yowab, “To, za a jefar maka kansa ta kan garu.” 22Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.
(2 Sam 8.15-18; 1 Tar 18.14-17)
23Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra'ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro. 24Adoniram shi ne shugaban aikin gandu, Yehoshafat, ɗan Ahilud, shi ne marubuci. 25Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci. 26Aira mutumin Yayir shi ne mashawarcin Dawuda.
1A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.” 2(Gibeyonawa dai ba mutanen Isra'ila ba ne, su Amoriyawan da suka ragu ne, waɗanda Isra'ilawa suka rantse musu, cewa, ba za su kashe su ba. Amma Saul, saboda kishin da yake yi domin mutanen Isra'ila da Yahuza, ya nema ya kashe su duk.) 3Dawuda kuwa ya kira Gibeyonawa ya ce musu, “Me zan yi muku, da me zan yi kafara, domin ku sa wa mutanen Ubangiji albarka?”
4Gibeyonawa suka amsa suka ce, “Ba zancen azurfa ko zinariya yake tsakaninmu da Saul ko da gidansa ba. Ba kuma wani mutum muke so mu kashe daga cikin Isra'ila ba.” Dawuda kuma ya tambaye su ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”
5Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya karkashe mu, ya yi niyyar hallakar da mu, don kada mu kasance tare da Isra'ilawa ko'ina a cikin karkararsu. 6Sai ka ba mu 'ya'yansa maza bakwai domin mu rataye su a gaban Ubangiji a Gibeya a kan dutsen Ubangiji.” Sarki kuwa ya ce, “To, zan bayar.”
7Amma sarki ya ware Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, saboda rantsuwar da take tsakaninsa da Jonatan, ɗan Saul. 8Sai sarki ya sa aka kamo masa Armoni da Mefiboshet, 'ya'yan Saul waɗanda Rizfa, 'yar Aiya, ta haifa masa, da 'ya'ya maza biyar na Adriyel, ɗan Barzillai, mutumin Abelmehola, waɗanda matarsa Merab 'yar Saul ta haifa masa. 9Sarki kuwa ya bai wa Gibeyonawa su. Sai suka rataye su a kan dutse a gaban Ubangiji. Su bakwai ɗin nan suka hallaka gaba ɗaya. An kashe su a farkon kakar sha'ir.
10Rizfa kuwa, 'yar Aiya, ta ɗauki algarara ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutsen. Ta zauna a wurin tun daga farkon kaka har zubar ruwan damuna da ya bugi gawawwakin. Ba ta bar tsuntsaye su sauka a kansu da rana ba, ko namomin jeji da dare.
11Sa'ad da aka sanar wa Dawuda abin da Rizfa, 'yar Aiya, ƙwarƙwarar Saul ta yi, 12Dawuda ya tafi ya kwaso ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan daga wurin mutanen Yabesh a Gileyad. (Gama suka sace su daga dandalin Bet-sheyan, a inda Filistiyawa suka rataye su, a ranar da suka kashe Saul a Gilbowa.) 13Daga can ne ya kwaso ƙasusuwan Saul da na Jonatan, suka kuma tattara ƙasusuwan waɗanda aka rataye. 14Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu'arsu a kan ƙasar.
15Ana nan sai Filistiyawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi. Dawuda kuwa ya gangara tare da jama'arsa, suka yi yaƙi da Filistiyawa. Dawuda kuwa ya gaji. 16Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda. 17Abishai ɗan Zeruya kuwa, ya kawo wa Dawuda gudunmawa. Ya faɗa wa Bafilisten, ya kashe shi. Jama'ar Dawuda kuwa suka sa ya yi musu alkawari ba zai ƙara binsu zuwa wurin yaƙi ba. Suka ce, “Kai ne begen Isra'ila, ba mu so mu rasa ka.”
(1 Tar 20.4-8)
18Bayan wannan kuma suka sāke yin yaƙi da Filistiyawa a Gab. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin gwarzayen.
19Suka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gab, sai Elhanan, ɗan Yayir, mutumin Baitalami, ya kashe ɗan'uwan Goliyat na Gat, wanda girman gorar māshinsa ta yi kama da dirkar masaƙa.
20An kuma yi wani yaƙi a Gat, inda aka sami wani ƙaton mutum wanda shi cindo ne, hannuwa da ƙafafu, wato yana da yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi kuma daga cikin zuriyar gwarzayen mutanen ne. 21Sa'ad da ya nuna wa Isra'ilawa raini, Jonatan ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya kashe shi.
22Waɗannan gwarzaye huɗu sun fito daga zuriyar gwarzayen Gat ne. Dawuda da mutanensa suka kashe su.
(Zabura ta 18)
1Wannan waƙa Dawuda ya raira wa Ubangiji sa'ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun Saul da dukan sauran abokan gābansa, ya ce,
2“Ubangiji ne mai cetona, Shi ne ƙaƙƙarfar kagarata.
3Allahna, shi ne kāriyata, Ina zaune lafiya tare da shi. Yana kāre ni kamar garkuwa, Yana tsare ni, ya kiyaye ni. Shi ne mai cetona.
4Na yi kira ga Ubangiji, Ya cece ni daga abokan gābana. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
5Gama raƙuman ruwa na mutuwa sun kewaye ni, Raƙuman ruwa na hallaka suna gangarawa ta kaina.
6Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi, Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
7A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji, Na yi kira ga Allah domin taimako. Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata, Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.
8“Sa'an nan duniya ta yi tangaɗi, ta girgiza, Harsashin sararin sama ya yi makyarkyata, ya raurawa, saboda fushin Allah.
9Hayaƙi ya fito daga kafafen hancinsa, Harshen wuta mai cinyewa da garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
10Ya jā sararin sama baya ya sauko, Da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
11Ya hau kerub, ya tashi sama, Ya yi tafiya ta fikafikan iska.
12Ya rufe kansa da duhu, Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,
13Garwashi mai ci daga tsawar walƙiya a gabansa.
14“Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama Aka kuma ji muryar Maɗaukaki.
15Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa, Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.
16An bayyana ƙarƙashin teku a fili, An tone tussan duniya, Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa, Ya yi musu ruri cikin fushi.
17Daga Sama Ubangiji ya miƙo ya ɗauke ni, Ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.
18Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina, Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!
19Sa'ad da nake cikin wahala sun auka mini, Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari, Ya cece ni domin yana jin daɗina.
21“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina, Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.
22Gama na kiyaye dokar Ubangiji, Ban yi wa Allahna tayarwa ba.
23Na kiyaye dukan dokokinsa, Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.
24Ya sani ni marar laifi ne, Na kiyaye kaina daga aikata mugunta.
25Domin haka ya sāka mini bisa ga adalcina, Gama ya sani ba ni da laifi.
26“Kai, ya Ubangiji, amintacce ne ga waɗanda suke da aminci, Nagari ne kuma ga waɗanda suke cikakku.
27Mai Tsarki ne kai ga waɗanda suke tsarkaka, Amma kana gāba da waɗanda suke mugaye.
28Kakan ceci masu tawali'u, Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.
29“Ya Ubangiji, kai ne haskena, Kana haskaka duhuna.
30Ka ba ni ƙarfi don in auka wa abokan gābana, Da iko domin in murƙushe tsaronsu.
31“Allahn nan cikakke ne ƙwarai, Maganarsa tabbatacciya ce! Kamar garkuwa yake Ga dukan masu neman kiyayewarsa.
32Ubangiji shi kaɗai ne Allah, Allah ne kaɗai madogararmu.
33Allahn nan shi ne mafaka, mai ƙarfi ne a gare ni, Ya sa hanyata ta zama lafiyayyiya.
34Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa, Ya kiyaye ni a kan duwatsu.
35Ya horar da ni domin yaƙi, Domin in iya tausa baka mafi ƙarfi.
36“Ya Ubangiji, ka kiyaye ni, ka cece ni, Taimakonka ya sa na zama babba.
37Ka hana a kama ni, Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.
38Na runtumi abokan gābana, na kuwa hallaka su, Ban tsaya ba sai da na kore su.
39Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba, Suna kwance warwar a ƙafafuna.
40Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi, Nasara kuma a kan abokan gābana.
41Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana, Na hallaka waɗanda suke ƙina.
42Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su, Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.
43Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura, Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.
44“Ka cece ni daga jama'ata mai tawaye, Ka sa in yi mulkin al'ummai, Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.
45Baƙi sun zo suna rusuna mini, Sa'ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.
46Zuciyarsu ta karai, Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.
47“Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa! Allah ne ƙaƙƙarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa!
48Ya ba ni nasara a kan abokan gabana, Ya sa mutane a ƙarƙashin mulkina,
49Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiya. Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan maƙiyana, Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali.
50Domin wannan zan yi yabonka cikin al'ummai, Zan raira yabbai gare ka.
51Allah ya ba sarkinsa manya manyan nasarori, Ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shi wanda ya zaɓa, Wato ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”
1Wannan ita ce maganar Dawuda ta ƙarshe. Dawuda ɗan Yesse, shi ne mutumin da Allah ya ɗaukaka, wanda Allah na Yakubu ya zaɓa ya zama sarki, wanda kuma ya shirya waƙoƙin Isra'ila. Dawuda ya ce,
2“Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina, Saƙonsa yana kan leɓunana.
3Allah na Isra'ila ya yi magana, Matsaron Isra'ila ya ce mini, “‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci, Wanda yake mulki da tsoron Allah,
4Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir, Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.”
5“Haka Allah zai sa wa zuriyata albarka, Gama ya yi mini madawwamin alkawari, Duka kuwa a shirye yake, zai kuwa kiyaye. Abin da nake bukata ke nan, Wannan ne nasarata, Na tabbata kuwa Allah zai kammala shi.
6Amma marasa Allah suna kama da ƙayayuwan da aka zubar,
7Amma wanda zai taɓa su, sai da wani ƙarfe ko da māshi, Za a ƙone su ƙurmus.”
(1 Tar 11.10-47)
8Ga sunayen jarumawan Dawuda, Yosheb-basshebet, daga Takemon, shi ne ɗaya daga cikin shugabanni uku. Ya girgiza māshinsa, ya kashe mutum ɗari takwas baki ɗaya.
9Wanda yake biye da shi a cikin su uku ɗin shi ne Ele'azara, ɗan Dodo, ɗan Ahowa. Yana tare da Dawuda sa'ad da suka raina Filistiyawan da suka taru don yaƙi. Mutanen Isra'ila kuwa suka jā baya, 10shi kuwa ya tsaya, ya yi ta yaƙi da Filistiyawa, har hannunsa ya ƙage, har bai iya ɓanɓaruwa daga takobinsa ba. Ubangiji ya ba da babbar nasara a wannan rana. Bayan an gama sai Isra'ilawa suka koma wurin Ele'azara don su kwashi ganima kawai.
11Biye da Ele'azara kuma, sai Shamma, ɗan Agi, daga Harod. Filistiyawa suka taru a Lihai, inda akwai wata gonar wake. Isra'ilawa kuwa suka guji wa Filistiyawa. 12Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta. Ya kuma kashe Filistiyawa. Ubangiji ya ba da babbar nasara.
13Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa. 14Dawuda yana cikin kagara, ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuwa tana a Baitalami. 15Dawuda ya ji marmari, ya ce, “Kai, da ma wani zai ba ni ruwan rijiyar ƙofar garin Baitalami in sha!” 16Shahararrun jarumawan nan uku kuwa suka sheƙa a guje, suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka tafi, suka ɗebo ruwa daga rijiyar ƙofar garin Baitalami, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda bai sha ba, ya zuba shi hadaya a gaban Ubangiji. 17Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji, ka tsare ni daga shan jinin mutanen da suka sadaukar da ransu.” Saboda haka bai sha ruwan ba. Abubuwan da jarumawan nan uku suka yi ke nan.
18Abishai, ɗan'uwan Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban jarumawan nan talatin. Sa'ad da ya girgiza mashinsa, sai da ya kashe mutum ɗari uku. Da haka ya samar wa kansa sūna tare da mutanen nan uku. 19Shi ya fi shahara daga cikin su talatin ɗin, don haka ya zama shugabansu, amma bai kai su uku ɗin can ba.
20Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo. 21Ya kuma kashe wani Bamasare mai cika fuska. Bamasaren yana da māshi a hannunsa, amma Benaiya ya tafi wurinsa da sanda, ya fizge mashin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da māshin. 22Abubuwan da Benaiya, ɗan Yehoyada ya yi ke nan. Da haka ya samar wa kansa suna tare da jarumawan nan talatin. 23Ya shahara cikin jarumawan nan talatin, amma bai kai su uku ɗin can ba. Dawuda kuwa ya maishe shi ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
(1 Tar 21.1-27)
1Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa. Ya kuwa zuga Dawuda a kansu, ya ce, “Tafi ka ƙidaya jama'ar Isra'ila da ta Yahuza.” 2Sai sarki ya ce wa Yowab da shugabannin sojojin su tafi cikin dukan kabilan Isra'ila, tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, su ƙidaya mutanen don ya san yawansu.
3Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mutanenka su ƙaru har sau ɗari fiye da yadda suke, har ubangijina sarki ya gani da idonsa, amma me ya sa sarki yake so ya yi wannan abu?” 4Amma maganar sarki ta rinjayi ta Yowab da ta sauran shugabannin sojojin. Yowab kuwa da sauran shugabannin sojojin suka tashi daga gaban sarki suka tafi su ƙidaya mutanen Isra'ila.
5Suka haye Urdun suka fara daga Arower, da garin da yake tsakiyar kwarin zuwa Gada, har zuwa Yazar. 6Sa'an nan suka zo Gileyad da Kadesh cikin ƙasar Hittiyawa, daga nan suka tafi Dan-ja'an. Daga Dan-ja'an kuma suka ratsa zuwa Sidon. 7Suka tafi kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa, da na Ƙan'aniyawa. Daga can suka tafi ƙasar kudu ta Yahuza a Biyer-sheba. 8Da suka gama ratsa dukan ƙasar, sai suka komo Urushalima bayan wata tara da kwana ashirin. 9Yowab kuwa ya ba sarki yawan jimillar mutanen da aka samu. A Isra'ila an sami mutanen da suka isa yin yaƙi, su dubu ɗari takwas (800,000). A Yahuza kuwa an sami mutum dubu ɗari biyar (500,000).
10Bayan da Dawuda ya ƙidaya mutane, sai lamirinsa ya kā da shi, ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka gafarta mini, gama na yi wauta.”
11Da Dawuda ya tashi da safe, sai Ubangiji ya yi magana da annabi Gad, wato annabin da yake tare da Dawuda, ya ce, 12“Tafi ka faɗa wa Dawuda na ba shi abu uku don ya zaɓi ɗaya wanda za a yi masa daga cikinsu.”
13Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”
14Dawuda kuwa ya ce, “Na shiga uku, gara in faɗa a ikon Ubangiji, gama shi mai rahama ne, da in faɗa a ikon mutum.” 15Ubangiji kuwa ya aika da annoba a kan Isra'ila tun da safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade. Mutum dubu saba'in (70,000) suka mutu daga Dan zuwa Biyer-sheba. 16Sa'ad da mala'ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima don ya hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala'ikan da yake hallakar da mutanen, “Ya isa, ka janye hannunka.” Mala'ikan ya tsaya kusa da masussukar Arauna Bayebuse.
17Da Dawuda ya ga mala'ika wanda yake hallakar da mutanen, sai ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi, na aikata mugunta, amma me waɗannan tumaki suka yi? Ina roƙonka, ka hukunta ni da gidan ubana.”
18A ran nan Gad ya koma wurin Dawuda ya ce masa, “Ka haura ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.” 19Dawuda kuwa ya haura bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Gad.
20Da Arauna ya waiga, ya ga sarki da fādawansa suna zuwa wurinsa, sai ya tafi ya tarye su. Ya tafi ya rusuna a gaban sarki har ƙasa, 21ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, me ya kawo ka?” Sai Dawuda ya ce, “Don in sayi masussukarka ne domin in gina wa Ubangiji bagade, domin a kawar wa mutanen da annobar.”
22Arauna kuwa ya ce wa Dawuda, “Bari ubangijina, sarki, ya karɓa, ya yi abin da yake so. Ga shanun nan domin hadayar ƙonawa, ga kuma itacen sussuka da karkiya domin itacen hadayar.”
23Dukan waɗannan Arauna ya ba sarki. Ya kuma ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya karɓa.”
24Amma sarki ya ce wa Arauna, “A'a, saye zan yi daga gare ka da tamani. Ba zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da abin da ban yi wahalarsa ba.” Dawuda ya sayi masussukar da shanu a bakin shekel hamsin na azurfa. 25Sa'an nan ya gina wa Ubangiji bagade a wurin. Ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama. Sa'an nan Ubangiji ya amsa masa addu'o'i saboda ƙasar. Aka kawar wa Isra'ila da annobar.