2 Thessalonians

WASIƘAR BULUS TA BIYU ZUWA GA
Tasalonikawa

1

Gaisuwa

1Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.

2Alheri da salama na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Bayyanar Almasihu don Yin Hukunci

3Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi. 4Saboda haka, mu kanmu ma taƙama muke yi da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku a cikin yawan tsananin da kuke sha, da ƙuncin da kuke a ciki.

5Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suke cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa, 6domin kuwa Allah ya ga adalci ne, ya yi sakamakon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku, 7yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa, 8yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suke ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu. 9Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa, 10wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku. 11Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu'a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa, 12don a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu.

2

Sarkin Tawaye

1To, a game da komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma taruwarmu mu sadu da shi, muna roƙonku 'yan'uwa, 2kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ku kuwa hankalinku ya tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.

3Kada ku yarda kowa ya yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan. 4Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah. 5Ashe, ba ku tuna ba, nakan gaya muku haka tun muna tare? 6To, a yanzu dai kun san abin da yake tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa. 7Ko a yanzu ma tawayen nan, wanda ba shi fahimtuwa, an fara shi, amma farawar abin da zai faru, sai an ɗauke wanda yake hana shi tukuna. 8A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa. 9Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al'ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri, 10yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto. 11Saboda haka, Allah zai auko masu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya, 12don duk a hukunta waɗanda suke ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.

Ya Zaɓe ku ku Sami Ceto

13Ya ku 'yan'uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya. 14Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka'idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.

16To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa, 17yă ta'azantar da ku, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.

3

Addu'a Dominmu

1Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi mana addu'a, Maganar Ubangiji ta yi saurin yaɗuwa, ta sami ɗaukaka, kamar yadda ta samu a gare ku, 2a kuma cece mu daga fanɗararrun mutane, mugaye. Don ba duka ne suke da bangaskiya ba. 3Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan. 4Mun kuma amince da ku a game da Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi. 5Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.

Wajibi ne a Yi Aiki

6To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu. 7Ai, ku kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin sa'ad da muke a tare, ba mu nuna muku lalaci ba, 8ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku. 9Ba don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a'a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu. 10Ai, ko dā ma, sa'ad da muke a tare, mun yi muku wannan umarni, cewa duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci. 11Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin kome, masu shisshigi ne kurum. 12To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu. 13Amma ku 'yan'uwa, kada ku gaji da yin nagari.

14In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙar nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku yi cuɗanya da shi, don yă kunyata. 15Amma kada ku ɗauke shi a kan abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a kan shi ɗan'uwa ne.

Sa Albarka

16To, Ubangiji kansa, mai zartar da salama, yă ba ku salama a koyaushe a kowane hali. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.

17Ni Bulus, ni nake rubuto wannan Gaisuwa da hannuna. Ita ce kuwa shaidar kowace wasiƙata. Rubutun hannuna ke nan. 18Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku daka.