Amos

1

Horon Allah a kan Maƙwabtan Isra'ila

1Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya ke sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa ke sarautar Isra'ila.

2Amos ya ce, “Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona, Muryarsa za ta yi tsawa daga Urushalima. Da jin wannan, sai wuraren kiwo za su bushe, Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da ke kore zai yi yaushi.”

Suriya

3Ubangiji ya ce, “Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun zalunci mutanen Gileyad da zalunci mai tsanani.

4Don haka zan aukar da wuta a kan fādar Sarkin Suriya. Za ta ƙone kagarar Ben-hadad, sarki.

5Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofin birnin Dimashƙu, In kawar da masu sarautar Bet-eden da na kwarin Awen. Za a kwashe mutanen Suriya ganima zuwa ƙasar Kir.”

Filistiya

6Ubangiji ya ce, “Mutanen Gaza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe al'umma duka, sun sayar wa mutanen Edom.

7Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Gaza ta ƙone kagarar birnin.

8Zan kawar da masu sarautar biranen Ashdod da Ashkelon, Zan karɓe sandan mulkin Ekron. Sauran Filistiyawa da suka ragu kuma, Za su mutu duka.”

Taya

9Ubangiji ya ce, “Mutanen Taya sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe mutanen sun kai ƙasar Edom. Suka karya yarjejeniyar abuta wadda suka yi.

10Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Taya, Ta ƙone kagarar birnin.”

Edom

11Ubangiji ya ce, “Mutanen Edom sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun farauci 'yan'uwansu, Isra'ilawa, Suka ƙi su nuna musu jinƙai. Ba su yarda su huce daga fushinsu ba.

12Saboda haka zan aukar da wuta a kan Teman, Ta ƙone kagarar Bozara.”

Ammon

13Ubangiji ya ce, “Mutanen Ammon sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don haɗamarsu ta ƙasa, Suka tsaga mata masu ciki a Gileyad.

14Saboda haka zan aukar da wuta a kan garun Rabba, Ta ƙone kagarar birnin. Za a yi kururuwa a ranar yaƙi, Faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.

15Sarkinsu da manyan mutanensu za a kai su wata ƙasa dabam.”

2

Mowab

1Ubangiji ya ce, “Mutanen Mowab sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun ƙone ƙasusuwan Sarkin Edom Don su yi toka da su.

2Zan aukar da wuta a ƙasar Mowab, Ta ƙone kagarar Keriyot. Jama'ar Mowab za su mutu a hargitsin yaƙi, Sa'ad da sojoji ke sowa, ana busa ƙahoni.

3Zan kashe Sarkin Mowab da shugabannin ƙasar.”

Yahuza

4Ubangiji ya ce, “Mutanen Yahuza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun raina koyarwata sun ƙi bin umarnaina. Allolinsu na ƙarya waɗanda kakanninsu suka bauta wa, Sun sa su su ratse daga hanya.

5Saboda haka zan aukar da wuta a kan Yahuza Ta ƙone kagarar Urushalima.”

Allah ya Hukunta Isra'ila

6Ubangiji ya ce, “Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun sayar da salihai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta Waɗanda bashinsu bai kai ko kuɗin bi-shanu ba.

7Sun tattake marasa ƙarfi da kāsassu, Suna tunkuɗe matalauta su wuce. Tsofaffi da samari sukan tafi wurin karuwan Haikali. Ta haka suke ɓata sunana mai tsarki.

8A duk wuraren sujadarsu sukan kwanta A bisa tufafin da suka karɓe jingina. A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sha ruwan inabi Da suka karɓo daga wurin waɗanda suke bi bashi.

9“Amma ga shi, saboda ku na hallakar da Amoriyawa, Dogayen mutanen nan masu kama da itatuwan al'ul, Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak, Na hallaka su ƙaƙaf.

10Na fito da ku, wato jama'ata daga Masar. Na bi da ku cikin jeji shekara arba'in, Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa ta zama taku.

11Na zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yanku su zama annabawa, Waɗansu kuma daga cikin samarinku su zama keɓaɓɓu. Ko ba haka ba ne, ya ku Isra'ilawa? Ni, Ubangiji, na yi magana.

12Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwan inabi, Kuka kuma umarci annabawa kada su isar da saƙona.

13Zan danƙare ku a inda kuke Kamar yadda ake danƙare amalanke da kayan tsaba.

14Ko masu saurin gudu ma ba za su tsere ba, Ƙarfafa za su zama kumamai, Sojoji kuma ba za su iya ceton kansu ba.

15'Yan baka ba za su iya ɗagewa ba. Masu saurin gudu ba za su tsira ba. Mahayan dawakai kuma ba za su tsere da rayukansu ba.

16Ko sojojin da suka fi jaruntaka duka ma, Za su gudu tsirara a ran nan.” Ubangiji ne ya faɗa.

3

Aikin Annabi

1Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.

2Daga cikin dukan al'umman da nake ƙauna a duniya, Ku kaɗai ne na sani, Nake kuma kulawa da ku, Don haka zan hukunta ku saboda zunubanku.”

3Zai yiwu a ce mutum biyu za su yi tafiya tare, Amma su rasa shirya magana>

4Zai yiwu zaki ya yi ruri a jeji Ba tare da ya kama nama ba? Zai yiwu sagarin zaki ya yi gurnani a kogonsa In bai kama wani abu ba>

5Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasa In ba a kafa masa tarko ba? Zai yiwu tarko ya zargu In bai kama wani abu ne ba>

6Zai yiwu mutane su rasa firgita, Idan aka busa ƙahon yaƙi a birni? Zai yiwu wata babbar masifa ta auko wa birni Ba da yardar Ubangiji ba>

7Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.

8Zaki ya yi ruri! Wa ba zai ji tsoro ba? Sa'ad da Ubangiji ya yi magana! Wa zai ƙi yin shelar maganarsa>

Faɗuwar Samariya

9Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”

10Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.

11“Saboda haka abokan gaba za su kewaye ƙasarsu, Su hallakar da kagaransu, Su washe gidajen nan nasu masu daraja.”

12Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci ƙafafu biyu Ko kunne ɗaya na tunkiya daga bakin zaki, Hakanan kuma kima daga cikin mutanen Samariya Waɗanda ke zaman jin daɗi za su tsira.

13Ku saurara yanzu, Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,” In ji Ubangiji, Maɗaukaki.

14“Ran da na hukunta mutanen Isra'ila saboda zunubansu, Zan hallakar da bagadan Betel. Za a kakkarya zankayen bagaden, Su fāɗi ƙasa.

15Zan murmushe gidajensu na rani da na damuna. Zan hallakar da gidajen da aka ƙawata da hauren giwa, Kowane babban gida kuwa za a rushe shi.”

4

1Ku kasa kunne ga wannan, ya ku matan Samariya, Ku da kuka yi ƙiba kamar turkakkun shanu, Ku da kuke wulakanta kasassu, Kuna yi wa matalauta danniya, Kukan umarci mazajenku, Ku ce, “Kawo mini abin sha!”

2Da ya ke Ubangiji Mai Tsarki ne Ya riga ya yi alkawari, Ya ce, “Hakika kwanaki za su zo Da za a jawo ku da ƙugiyoyi, Kowannenku zai zama kamar kifi a ƙugiya.

3Za a kwashe ku, a fitar da ku Ta inda garu ya tsage na mafi kusa duka, a jefar.”

Isra'ila Sun Kāsa Koyo

4Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri, Ku yi ta zunubi! Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi! Ku yi ta kawo dabbobi sadaka kowace safiya. A kowace rana ta uku Ku yi ta ba da zaka.

5Ku miƙa abincinku hadaya ta godiya. Ku yi ta yin fariya da hadayarku ta yardar rai! Gama irin abin da kuke jin daɗin yi ke nan.”

6Ubangiji ya ce, “Ai, ni ne, na sa a yi yunwa a biranenku. Shi ya sa ba ku da abinci. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.

7Na hana wa shuke-shukenku ruwa A lokacin da suka fi bukata. Na sa a yi ruwa a wani birni, A wani birni kuwa na hana, Wata gonar ta sami ruwan sama, Amma wadda ba ta samu ba ta bushe.

8Ƙishirwa ta sa jama'a su tafke har birane biyu ko uku Suka tafi neman ruwa a birnin da suke maƙwabtaka da shi, A nan ma ba su sami isasshen ruwan sha ba, Duk da haka ba ku komo wurina ba.

9“Na sa darɓa, da domana Su lalatar da amfanin gonakinku. Fāra kuma ta cinye lambunanku Da gonakin inabinku, da itatuwan ɓaurenku, Da na zaitun ɗinku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.

10“Na aukar muku da annoba irin wadda na aukar wa Masar. Na karkashe samarinku a wurin yaƙi, Na kwashe dawakanku. Na cika hancinku da ɗoyin sansaninku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.

11“Na hallakar da waɗansunku Kamar yadda na hallakar da Saduma da Gwamrata. Kamar sanda kuke, wanda aka fizge daga wuta. Duk da haka ba ku komo wurina ba.

12Saboda haka, jama'ar Isra'ila, Ga abin da zan yi muku, Zan kuwa yi shi duk, Sai ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji.”

13Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!

Kira Zuwa Tuba

5

1Ku kasa kunne, ku jama'ar Isra'ila, ga waƙar makoki da zan yi a kanku.

2Isra'ila ta fāɗi, Ba kuwa za ta ƙara tashi ba. Tana fa kwance a ƙasa, Ba wanda zai tashe ta.

3Ubangiji ya ce, “Wani birnin Isra'ila ya aika da soja dubu, Ɗari ne kaɗai suka komo, Wani birni kuma ya aika da soja ɗari ne, Amma goma kaɗai suka komo.”

4Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Ku zo gare ni, za ku tsira.

5Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba. Kada ku yi ƙoƙarin nemana a Betel, Gama Betel lalacewa za ta yi. Kada ku tafi Gilgal, Gama an ƙaddara wa jama'arta su yi ƙaura.”

6Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira. Idan kuwa kun ƙi, Shi zai babbaka jama'ar Yusufu Kamar yadda a kan babbaka da wuta. Wuta za ta ƙone jama'ar Betel, Ba kuwa mai kashe wutar.

7Abin tausayi ne ku da kuke ɓata shari'a, Kuna hana wa mutane hakkinsu.

8Ubangiji ne ya yi taurarin Kaza da 'ya'yanta Da mai farauta da kare. Ya mai da duhu haske, Rana kuwa dare. Shi ya kirawo ruwan teku ya bayyana, Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa. Sunansa Ubangiji ne.

9Ya kawo halaka a kan ƙarfafa, Da a kan birane masu garu.

10Kun ƙi wanda ya tsaya a kan adalci, Da mai faɗar ainihin gaskiya a gaban shari'a.

11Kun matsa wa talakawa lamba, Kun ƙwace musu abincinsu. Saboda haka kyawawan gidajen nan da kun gina da dutse, Ba za ku zauna a cikinsu ba, Ba kuwa za ku sha ruwan inabin nan Daga kyawawan gonakin inabinku ba.

12Na san irin zunuban da kuke yi, Da mugayen laifofin da kuka aikata. Kuna wulakanta mutanen kirki, Kuna cin hanci, Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar adalci a majalisa.

13Ashe, ba abin mamaki ba ne, Da masu hankali suka kame bakinsu A waɗannan kwanaki na mugunta.

14Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, ba mugunta ba, Domin ku tsira. Sa'an nan ne Ubangiji Allah Maɗaukaki Zai kasance tare da ku sosai, Kamar yadda kuka ɗauka!

15Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta, Ku yi adalci cikin majalisar alƙalanku! Watakila Ubangiji Allah Mai Runduna Zai yi wa sauran da suka ragu na wannan al'umma alheri.

16Haka Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Za a yi kuka, a yi kururuwa a titunan birninku saboda azaba. Daga ƙauyuka za a kirawo mutane Su zo su yi makokin. Waɗanda suka mutu, tare da masu makoki da aka ijarar da su.

17Za a yi kuka ko'ina cikin dukan gonakin inabinku Gama zan zo in yi muku horo.”

18Taku ta ƙare, ku da kuke marmarin zuwan ranan nan ta Ubangiji! Wane amfani wannan rana za ta yi muku? Rana ta baƙin ciki ce, Ba ta murna ba.

19Zai zama kamar wanda ya tsere wa zaki Ya fāɗa a bakin beyar! Ko kuwa kamar wanda ya komo gida, Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.

20Ranar Ubangiji za ta kawo baƙin ciki, Ba murna ba. Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.

21Ubangiji ya ce, “Na ƙi bukukuwanku na addini. Ina ƙyamarsu!

22Sa'ad da kuka kawo mini hadayun ƙonawa Da hadayunku na tsaba, ba zan karɓa ba. Ba kuma zan karɓi turkakkun dabbobinku Waɗanda kuka miƙa mini hadayun godiya ba.

23Ku yi shiru da yawan hargowar waƙoƙinku. Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku da bushe-bushenku.

24Sai ku sa adalci da nagarta su gudano a yalwace Kamar kogin da ba ya ƙafewa.

25“Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu, 26duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku. 27Ni kuwa zan sa ku yi ƙaura zuwa wata ƙasa gaba da Dimashƙu.” Ubangiji, Allah Mai Runduna, shi ne ya faɗa.

Halakar Isra'ila

6

1Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, Da ku da kuke tsammani kuna zaman lafiya a Samariya, Ku da kuke manyan mutane Na wannan babbar al'umma ta Isra'ila, Waɗanda jama'a ke zuwa a gare su neman taimako!

2Ku je ku duba a birnin Kalne. Sa'an nan ku zarce zuwa babban birnin Hamat, Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa. Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne? Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi naku>

3Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan rana ta masifa, Amma ga shi, goyon bayan hargitsi kuke ta yi, Ta wurin ayyukanku.

4Taku ta ƙare, ku da kuke kwance kan gadajen hauren giwa, Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayen kujerunku, Ku ci naman maraƙi da na rago.

5Kukan so ku tsara waƙoƙi kamar yadda Dawuda ya yi, Ku raira su da garayu.

6Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi, Ku shafe jiki da mai mafi kyau, Amma ba ku yin makoki saboda lalacewar Isra'ila.

7Don haka, ku ne na fari da za a sa su yi ƙaura Bukukuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

8Ubangiji kansa ne ya rantse. Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Ba na son girmankai na jama'ar Isra'ila. Ba na son fādodinsu. Zan ba da birnin da dukan abin da ke cikinsa ga abokan gābansu.”

9Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu. 10Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga kowanene da ke ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.” 11Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.

12Dawakai sukan yi sukuwa a duwatsu? Ana huɗan teku da garmar shanu? Duk da haka kuka mai da adalci dafi, Kuka mai da nagarta, mugunta.

13Kuna fariyar cin garin Lodebar, wato wofi, da yaƙi. Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ci Karnayim, wato ƙaho biyu, da yaƙi.”

14Ubangiji Allah Mai Runduna kansa, ya amsa ya ce, “Zan aiko da wata al'umma ta yi gāba da ku, ya Isra'ilawa. Za ta matse muku Tun daga mashigin Hamat wajen arewa, Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”

Wahayi uku na Halaka

7

Wahayin Fāra

1A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, sai na ga ya yi cincirindon fara nan da nan bayan da aka ƙarasa yankan rabon ingiricin da ke na sarki, ciyawar kuma ta soma tohuwa.

2A wahayin, na ga fara ta cinye kowane ɗanyen ganye a ƙasar. Sai na ce, “Ka gafarta wa jama'arka, ya Ubangiji! Ƙaƙa za su tsira? Ga su 'yan kima ne, marasa ƙarfi.”

3Ubangiji kuwa ya dakatar da nufinsa, Ya ce, “Abin da ka gani, ba zai faru ba.”

Wahayin Wuta

4A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, na gan shi yana shirin hukunta jama'arsa da wuta. Wutar ta ƙone babbar teku, har ma ta fara ƙone ƙasar. 5Sa'an nan na ce, “Ya Ubangiji, in nufinka ne ka bari! Ƙaƙa jama'arka za su tsira? Ga su 'yan kima ne, marasa ƙarfi.”

6Ubangiji kuwa ya dakatar da nufinsa, ya ce, “Wannan me ba zai faru ba.”

Wahayin Ma'auni

7Ubangiji kuma ya nuna mini wani wahayi. A wahayin sai na gan shi, yana tsaye kusa da bangon da ake ginawa. Yana riƙe da igiyar awon gini.

8Ya tambaye ni, ya ce, “Amos, me ka gani?” Sai na ce, “Igiyar awon gini na gani.” Ya kuma ce, “Duba, da wannan zan nuna yadda jama'ata sun zama kamar bangon da ya karkace. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.

9Zan hallakar da wuraren sujada na zuriyar Ishaku. Za a hallakar da tsarkakan wurare na Isra'ila. Zan fāɗa wa zuriyar sarki Yerobowam da yaƙi.”

Amos da Amaziya

10Amaziya, firist, na Betel kuwa, ya tafi ya faɗa wa Yerobowam Sarkin Isra'ila, ya ce, “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a cikin jama'ar Isra'ila. Maganganunsa za su hallakar da ƙasar. 11Abin da ya faɗa ke nan, “‘Za a kashe Yerobowam a bakin dāga, a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.”

12Amaziya kuwa ya ce wa Amos, “Kai maƙaryaci ne na ainihi! Koma ƙasar Yahuza ka nemi abin zaman gari, ka yi ta annabcinka a can. 13Amma a nan Betel kada ka ƙara yin annabci. Nan wurin yin sujada na sarki ne, haikali ne na al'umma.”

14Sai Amos ya amsa ya ce, “Ni ba annabi ba ne. Wannan ba aikina ba ne. Ni makiyayi ne, mai kuma lura da itatuwan ɓaure. 15Amma Ubangiji ya raba ni da aikina na kiwo, ya umarce ni in tafi in yi magana da jama'arsa, wato Isra'ila. 16Domin haka, sai ka kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce. Saboda ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama'ar Isra'ila, kada kuwa in yi wa zuriyar Ishaku ɓaɓatu, 17to, ga abin da Ubangiji ya ce maka, ya kai Amaziya, “‘Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe 'ya'yanka a cikin yaƙi. Za a rarraba wa waɗansu ƙasarka, kai kanka kuwa za ka mutu a ƙasar arna. Za a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.”

8

Wahayi na Huɗu, Kwandon Ɓaure na Ci

1Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci. 2Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?” Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.” Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba. 3Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”

An kai Ƙarshen Isra'ila

4Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.

5Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosa keɓaɓɓun kwanakin nan su wuce, Mu sami damar yin kasuwancinmu. Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne? Ko mā sami damar kai hatsinmu kasuwa, Mu sayar musu da tsada, Mu yi awo da ma'aunin zalunci, Mu daidaita ma'auni yadda za mu cuci mai saya>

6Za mu sayi matalauci da azurfa ya zama bawa, Mai fatara kuma da takalma bi-shanu. Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi, Mu ci riba mai yawa.”

7Ubangiji Allahn Isra'ila ya riga ya rantse, Ya ce, “Ba zan manta da mugayen ayyukanku ba.

8Shi ya sa ƙasar za ta girgiza, Duk wanda ke cikinta zai yi baƙin ciki. Ƙasa duka za ta girgiza. Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.

9A wannan lokaci rana za ta fāɗi da tsakar rana, Duniya ta duhunta da rana kata. Ni, Ubangiji ne na faɗa.

10Zan mai da bukukuwanku makoki, In sa waƙoƙinku na murna su zama na makoki. Zan sa muku tufafin makoki, In sa ku aske kanku. Za ku yi makoki kamar iyayen da suka rasa tilon ɗansu. Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.

11“Lokaci yana zuwa da zan aiko da yunwa a ƙasar. Mutane za su ji yunwa, Ba ta abinci ba, Za su ji ƙishi, Ba na ruwa ba. Za su ji yunwar rashin samun saƙo daga wurin Ubangiji. Ni Ubangiji ne, na faɗa.

12Mutane za su raunana, su riƙa kai da kawowa, Daga gabas zuwa yamma, daga kuma kudu zuwa arewa. Za su dudduba ko'ina suna neman saƙo daga Ubangiji, Ba kuwa za su samu ba.

13A ranan nan kyawawan 'yan mata da samari Za su faɗi saboda ƙishirwa.

14Waɗanda suka yi rantsuwa da gumakan Samariya, Waɗanda suka ce, “‘Na rantse da gunkin Dan, Da ran gunkin Biyer-sheba,” Irin waɗannan mutane za su fāɗi, Ba za su ƙara tashi ba.”

9

Ba a Kauce wa Hukuncin Allah

1Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce, “Bugi ginshiƙan Haikali don shirayi duka ya girgiza. Farfasa su, su fāɗi a kan mutane! Sauran mutane kuwa, Zan kashe su a wurin yaƙi. Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.

2Ko da za su nutsa zuwa lahira, Zan kama su. Ko sun hau Sama, Zan turo su.

3Ko da za su hau su ɓuya a bisa ƙwanƙolin Dutsen Karmel, Zan neme su in cafko su. Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashin teku, Sai in sa dodon ruwa ya yayyage su.

4Idan kuwa abokan gābansu ne suka kama su, In umarce su su hallaka su da takobi, Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”

5Ubangiji Allah Mai Runduna Ya taɓi duniya, ta girgiza. Duk waɗanda ke zaune cikinta Suna baƙin ciki. Duniya duka takan hau Ta kuma gangara kamar ruwan Kogin Nilu.

6Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama, Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya. Ya sa ruwan teku ya zo, Ya kwarara shi a bisa duniya. Sunansa Ubangiji ne!

7Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ina yi da ku daidai yadda nake yi da Habashawa. Na fito da Filistiyawa daga Kaftor, Suriyawa kuwa daga Kir, Daidai yadda na fito da ku daga Masar.

8Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka su daga duniya, Amma ba zan hallaka dukan jama'ar Yakubu ba.

9“Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ila Da matankaɗi kamar hatsi. Zan rairaye su daga cikin sauran al'umma, Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba za ta salwanta ba.

10Masu zunubi daga cikin jama'ata za su mutu a yaƙi, Wato dukansu da ke cewa, “‘Allah ba zai bar wata masifa ta kusace mu ba!”

Ceton da Za a Yi wa Isra'ila Nan Gaba

11“Wata rana zan sāke tayar da birnin Dawuda Tankar yadda akan ta da gidan da ya rushe. Zan gyara garunsa, in sāke mai da shi. Zan sāke gina shi in mai da shi kamar yadda yake tun dā.

12Ta haka jama'ar Isra'ila za ta ci nasara bisa sauran ƙasar Edom wadda ta ragu, Da bisa dukan al'umman da a dā su nawa ne,” In ji Ubangiji, wanda zai sa al'amarin ya auku.

13Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa, Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan da nan, Matsewar ruwan inabi kuma Za ta bi bayan shuka nan da nan. Duwatsu za su zubo da ruwan inabi mai zaƙi, Tuddai kuma su gudano da shi.

14Zan komo da mutanena ƙasarsu, Za su giggina biranensu da suka rurrushe, Su zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi, su sha ruwan inabin. Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.

15Zan dasa su a ƙasar da na ba su, Ba kuwa za a ƙara tumɓuke su ba.” Ubangiji Allahnku ne ya faɗa.