LITTAFIN BARUK

1. Baruk da Yahudawa a Babila

1 Waɗannan ne jawaban littafin Baruk ɗan Neriya, ɗan Maaseya, ɗan Zadakiya, ɗan Hasadiya, ɗan Hilkiya 2 da ya rubuto a Babila, a shekara ta biyar, bakwai ga wata, a lokacin da Kaldiyawa suka ci Urushalima, suka ƙone garin ƙurmus da wuta. 3 Sai Baruk ya karanta kalmomin wannan littafi a kunnen Yekoniya, cran Yehoyakim, Sarkin Yahudiya, a kunnuwan duk waɗanda suka zo sauraron littafin da za a karanta kuma, 4 har da fādawa cikinsu, da yayan sarakuna, da dattawa, da dukan jamaa, babba da ƙaramia taƙaice dai, dukan waɗanda ke zaune a Babila a bakin kogin Sudi.

5 Saan nan suka yi kuka, suka yi azumi da addua a gaban Ubangiji, 6 suka kuma tara waɗansu yan kuɗi, kowa ya ba da abin da zai iya. 7 Aka tara, aka aika Urushalima, ga Yehoyaƙirn firist, ɗan Hilkiya, ɗan Shallum, da firistoci, da dukan mutanen da aka samu tare da shi a Urushalima. 8 A wannan lokaci ne kuma Baruk ya karɓo kwanonin da aka ɗauka daga Haikalin Ubangiji, ya mai da su ƙasar Yahudiya a ranar goma ga watan Siban. Waɗannan kwanonin azurfa Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahudiya ne, ya yi su 9 bayan da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kama Yekoniya, da hakimai, da gwanayen aiki, da fādawa, da talakawa ma, na Urushalima, ya kai su Babila.

10 Sai Yahudawan Babila suka ce a wasiƙarsu, Ga kuɗi mun aika muku, ku sayi hadayar ƙonawa, da hadayar laifi, da turaren ƙonawa, ku kuma shirya hatsin miƙaya, ku miƙa a kan bagaden Ubangiji Allalmmu, 11 sai ku yi addua saboda ran Nebukadnezzar Sarkin Babila, da kuma ran Belshazzar ɗansa, domin ranakunsu su zama kamar ranakun sama da ke bisa duniya. 12 Ubangiji kuma ya ba mu ƙarfi, ya haskaka idanunmu domin mu zauna karƙashin inuwar Nebukadnezzar Sarkin Babila, da kuma ta Belshazzar ɗansa, mu bauta musu kwanaki masu yawa, mu sami alheri daga gare su.

13 Sai kuma ku yi mana addua ga Ubangiji Allahnmu, gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, har kuma yau fushin Allah da harzukarsa ba su rabu da mu ba. 14 Ku karanta wannan naɗaɗɗiyar takarda wadda muka aiko muku, a ɗakin sujada a ranar Idin Bukkoki, da kuma a taruwar da ake yi a kwanakin idin nan.

Hurcin Zunubai

15 Adalci na Ubangiji Allahnmu ne, amma jin kunya a fuska a wannan rana ya kamace mu, mu mutanen Yahudiya da waɗanda ke zaune a Urushalima, 16 sarakunamnu da fādawanmu, da firistocinmu, da annabawanmu, da kuma kakanninmu, 17 Gama mun yi zunubi gaban Ubangiji, 18 mun keta maganarsa, ba mu ma yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu, domin mu bi dokokin da ya sa a gabanmu ba. 19 Tun daga ranar da Ubangiji ya fito da kakanninmu daga ƙasar Masar har zuwa yau, ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba, mun ma yi watsi da sauraron muryarsa. 20 Har ila yau sai rashin saa ya dame mu, laana ta faɗo mana wadda Ubangiji ya yarda da ita ta wurin bawansa Musa, a ranar da ya fito da kakanninmu daga Masar, don ya ba mu ƙasar da ke malata da yawan albarka. 21 Ba mu bi muryar Ubangiji Allahnmu ba, wadda dukan annabawan da ya aiko suka bayyana mana, 22 amma kowannenmu, don taurinkai, sai ya bi tasa hanya, muka bauta wa yan alloli, muka yi mugun abu a gaban Ubangiji Allahnmu.

2.

1 Sai Ubangiji ya cika maganarsa, wadda a zamanin dā ta yi gāba da mu da alƙalanmu waɗanda ke sharaanta Israilawa, ta yi dai gāba da sarakunanmu, da fādawanmu, da mutanen Yahudiya. 2 Ba inda aka yi mugun balai duk duniya kamar Urushalima, kamar yadda aka sanar a Attaura, cewa 3 waninmu zai ci naman ɗansa, waninmu kuma zai ci naman yarsa. 4 Sai Allah ya mai da mu tatakawan dukan mulkokin da ke kewaye da mu, mu zama abin zargi, abin gudu ga dukan mutanen da ke kewaye da mu, inda Ubangiji ya hargitsa mu. 5 Aka dankwafe mu, ba a ɗaga mu ba, gama mun yi zunubi a gaban Ubangiji Allahnmu, tun da ba mu saurari muryarsa ba.

6 Adalci na Ubangiji Allahnmu ne, amma jin kunya a fuska ya kamace mu, mu da kakanninmu, kamar yadda yake a yau. 7 Dukan balain da Ubangiji ya firgita mu da shi, ya sha kanmu. 8 Duk da haka ba mu nemi Ubangiji ba, da za mu dawo gare shi, kowannewnu sai ya riƙa bin nufin muguwar zuciyarsa. 9 Ubangiji ya riƙe waɗannan annobai sai da kaida ta cika, kana ya angazo mana su, gama Ubangiji mai adalci ne a dukan abin da ya umarce mu mu. 10 Ba mu bi muryarsa ba, domin mu bi dokokin Ubangiji, waɗanda ya sa a gabanmu.

Adduar Neman Tsira

11 Yanzu, ya Ubangiji Allah na Israilawa, wanda ka fito da alummarka daga Masar da dantse mai ƙarfi, da alajabai, da babban iko, ka ma yi wa kanka babban suna kamar wanda kake da shi a yau. 12 Mun yi zunubi, mun Yi rashin adalci, mun saka maka, ya Ubangiji Allahnmu, a wajen dukan dokokinka. 13 Ka kawar da fushinka daga wajenmu, don mu kaɗan ne muka ragu, a tsakanin arna, inda ka yi ɗaya ɗaya da mu. 14 Ka saurara, ya Ubangiji, ga adduarmu da roƙonmu, saboda sunanka ka fanshe mu, ka nuna mana alheri a idanun waɗanda suka mai da mu bayi, 15 domin dukan duniya ta sani, kai ne Ubangiji Allalmmu, gama Israila da zuriyarsa, ana kiransu da sunanka, 16 Ya Ubangiji, ka dubo mu daga wurin zamanka mai tsarki, ka kuma yi juyayinmu. Ka kasa kunne gare mu, ya Ubangiji, ka saurare mu. 17 Ka buɗe idanunka, ka duba, domin ba matattu, waɗanda ke a lahira, waɗanda ba su numfashi, da za su girmama ka, ya Ubangiji, su yabi adalcinka, 18 Amma ruhun wanda ke baƙin ciki matuƙa, wanda ke yawace‑yawace da kai a sunkuye, yana fama da ciwo, yana dindimi kuma, yana ma jin yunwa, shi ne wanda zai girmama ka, ya yabi adalcinka, ya Ubangiji.

19 Ba saboda aikin adalcin kakanninmu da na sarakunamnu ne muke roƙon tausayi gare ka ba, ya Ubangiji Allalmmu. 20 Aa, amma ka nuna fushinka da haushinka a gare mu, kamar dai yadda ka alkawarta yi ta wurin bayinka annabawa a lokacin da ka ce, Haka ni Ubangiji na ce. 21 Ku yarda ku yi aikin da Sarkin Babila zai ba ku, saan nan ne za ku zauna a ƙasar da na ba kakanninku. 22 Amma in ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji ba, ba ku bauta wa Sarkin Babila ba, 23 zan hana ku jin daɗi, in kawo muku baƙin ciki, ba za a yi bikin aure a garuruwan Yahudiya da Urushalima ba, za a ma wofinta garin duka, a mai da shi kufai. 24 Amma ba mu yi biyayya da muryarka, cewa mu yi wa Sarkin Babila hidima ba, ka kuwa cika maganarka wadda ka faɗa ta bakin annabawa cewa, za a tono kasusuwan sarakunanmu da na kakanninmu. 25 Yanzu, ga shi, an tonso su, an jefa su a zafin rana da jaurar dare, jamaarka ma suka halaka da babban baƙin ciki ta yunwa, da kaifin takobi da kora. 26 Ɗakin kuma da ake kira da sunanka, ka mayar da shi kamar yadda yake a yau, saboda muguntar mulkin Israilawa da mulkin Yahudawa.

An Tuna da Alkawaran Allah

27 Duk da haka ka ɗan hore mu, ya Ubangiji Allalmmu, da dukan dauriya da kuma dukan tausayinka, 28 kamar yadda ka alkawarta ta bakin bawanka Musa, lokacin da ka umarce shi ya rubuta Attaura a gaban Israilawa, ka ce, 29 In ba ku yi biyayya da muryata ba, wannan babban taron jamaa zai komo ɗan hikan a tsakanin arnan da zan hargitsa ku cikinsu. 30 Amma na sani, ba za ku saurare ni ba, gama mutane ne da ba ku jin dawo nan. Amma a ƙasar da za a kai ku bauta za ku komo cikin hankalinku, 31 za ku sani kuma, ni ne Ubangiji Allahnku. A can zan ba ku tunani da kunnuwan sauraro, 32 za ku yabi sunana a ƙasar da aka kai ku bauta, za ku tuna da sunana, 33 za ku juya wa taurinkanku da ƙetarku baya, don za ku tuna da abin da ya sami kakanninku da suka yi zunubi a gaban Ubangiji. 34 Saan nan zan mai da ku ƙasar da na rantse zan ba kakanninku, Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, su mallake ta. Zan riɓaɓɓanya ku, ba ma za ku ragu ba. 35 Zan kuma yi madawwamiyar yarjejeniya tare da ku, domin in zama Allahnku, sai kuma ku zama mutanena. Ba zan ƙara fitar da alummata Israilwa daga ƙasar da na ba ku ba.

3.

1 Ya Ubangiji Mai Iko Dukka AlIahn Israilawa, rayuka masu damuwa waɗanda ke da gajiya suna kuka zuwa gare ka. 3 Ka saurara, ya Ubangiji, ka yi jinƙai, gama mun yi zunubi a gabanka. 3 Ka dawwama har abada, mu kuwa ba mu iya ɗorewa har abada. 4 Ya Ubangiji mai iko, Allahn Israilawa ka ji adduoin Israilawa waɗanda suka yi kaɗan, jikokin waɗanda suka yi laifi a gabanka, waɗanda ba su saurari muryar Ubangiji Allahnsu ba, don haka sai balai ya rarume su. 5 Kada ka tuna da shaidancin kakanninmu, amma ka tuna da ikonka da sunanka a wannan lokaci. 6 Ai, kai ne Ubangiji Allahnmu, za mu yabe ka, ya Ubangiji. 7 Gama ka sa tsoronka a zukatanmu domin mu yi kira ga sunanka, mu yabe ka lokacin baƙuncinmu a wata ƙasa, gama mun kori dukan shaiɗancin kakanninmu waɗanda suka saɓa maka, daga gindin zukatanmu. 8 Ga mu nan yau, a bakuwar ƙasa, inda ka yi ɗaya ɗaya da mu, mun zama abin zargi, laanannu, an kuma hukunta mu saboda dukan shaiɗancin kakanninmu waɗanda suka yi wa Ubangiji Allahmu tawaye.

Hikima ta Sanarwa da Israilawa Kanta
9 Ku ji kaidodin rai, ya ku Israilawa,
      Ku saurara, domin ku koyi basira.
10 Don me, ku Israilawa, kuke zaune a ƙasar magabtanku,
      Kuka girma, har kuka tsufa a ƙasar waje,
11 Kuka ƙazantu ta wurin zama da waɗanda ke matattu,
      Aka kuma ƙidaya ku cikin waɗanda ke mallakar mulkin kurwa?
      12 Kun saki tushen hikima.
13 Da kun yi tafiya a hanyar Allah,
      Da kun zauna da salama har abada.
14 Ku nemi inda basira take,
      Da inda ƙarfi yake,
      Da inda ganewa take,
Domin ku farga nan da nan,
      Ku gane inda tsawon rai yake,
Da inda haske yake ga idanu,
      Da inda salama take.

15 Wa ke iya gane tukubar hikima?
      Wa ma ke iya shiga maajinta?
16 Ina sarakunan arna suke,
      Da mafarauta waɗanda suka mallaki dabbobin duniya,
17 Waɗanda ke gadarsu da tsuntsayen jeji?
      Suka tara wa kansu azurfa da zinariya,
Abubuwan da mutane suka fi yin naam da su,
      Amma duk da haka neman ƙari suka yi ta yi kullum.
18 Suna aiki a kan samun azurfa da kular gaske,
      Ba sauran alamar aikinsu.
19 Ai, sarakunan nan sun halaka,
      An aika da su zuwa mulkin kurwa,
      Waɗansu kuma sun gaje su.

20 Jikokinsu sun ga hasken duniya a lokacin da aka haife su,
      Amma ba su koyi hanyar ilimi ba.
21 Ba su ma gane tafarkinsa ba,
      Balle su rungume shi hannu biyu biyu,
      Yayansu ma sun bauɗe wa hanyarsa kwarai da gaske.
22 Ba a ji labarin ilimi a kasar Kanana ba,
      Ba a ma taɓa ganinsa a ƙasar Teman ba,
23 Yayan Hajara ma, waɗanda suka baraci basira a duniya,
      Da manyanyan kasuwa na Madayana da Teman,
Har da masu ƙaga karin magana da masu neman ganewa,
      Duk ba su gane kan hikima ba,
      Ko ma tuna hanyoyinta, ba su yi ba.
24 Haba Israilawa, ai, halittar Allah da girma take,
      Sashin da ya mallaka da makeken fāɗri yake,
25 Fankacece ne, ba shi da maƙara,
      Mai tsawo ne, ba ya ma kimantuwa don yawa.
26 A cikin halitta aka haifi ƙattin nan, jarumawan farko,
      Dogaye ne ƙwarai, gwanayen yaƙi.
27 Allah bai zaɓe su ba,
      Balle ya ba su ilimi.
28 Sai suka halaka, don ba su da basira,
      Suka halaka ta barancinsu.
29 Wanene ya hau sama, ya sauko da hikima,
      Ya keto gizagizai da ita?
30 Wanene ya haye teku, ya nemo ta,
      Ko da zinariya ne ya sawo ta?
31 Amma wanda ya san ɗakwacin abu ya san ta,
      Ya san ta da ganewarsa.

32 Shi ne wanda ya halicci sama da ƙasa har abada,
      Ya cika su da halitta masu ƙafa hurhuɗu.
33 Shi ne wanda ke aika da haske, ya kuwa tafi nan da nan,
      Da ya kira shi, sai ya yi biyayya da rawar jiki.
34 Taurari suna haskakawa, farin ciki suke kuma.
      35 Da ya kira su, sai su ce, Ga mu nan!
      Suna haskensu da farin ciki ga wanda ya halicce su.
36 Shi ne Allahnmu,
      Ba ma wani allahn da za a gwada da shi!
37 Ya nemi dukan hanyar ilimi,
      Ya ba Yakubu bawansa ita,
      Wato Israila, wanda yake ƙauna matuƙa.

38 Daga baya ne, hikima ta bayyana a duniya,
      Ta yi ta maamala da yan adam.

4.

1 Hikiman nan tana ƙunshe littafin dokokin Allah,
      Wato shariarsa, wadda za ta ɗore har abada.
Duk waɗanda suka dafkake ta za su rayu,
      Amma waɗanda suka yi watsi da ita za su halaka.
2 Ku dawo da baya, jamaar Yakubu, ku riƙe ta kankan,
      Ku bi ɗan mafarin haskenta, za ta kai ku aljannarta.
3 Kada ku ba wani darajarku,
      Kada ma ku ba wani kincakiri faidarku.
4 Masu albarka ne mu Israilawa,
      Gama mun san abubuwan da ke faranta wa Allah rai.

Urushalima tana Kuka, tana Taazanta Yayanta
5 Ku ƙarfafa, jamaata,
      Israilawa, ku tuna!
6 Ai, ba a sayar da ku gun arna don a hallaka ku ba,
      Amma domin haushin da kuka ba Allah,
      Aka danƙa ku a hannun abokan gāba.
7 Gama kun saɓa wa wanda ya halicce ku,
      Dā kuka riƙa yi wa aljannu hadaya, ba Allah ba.
8 Kun mance da Allah madawwami, wanda ya rene ku,
      Kun saɓa wa Urushalima, wadda ta ba ku mama.
9 Ai, ko Urushalima, da ta ga tsananin fushin Allah yana zuwa gare ku,
      Sai ta faɗa muku wannan.

Ku saurara, ku maƙwabtan Sihiyona,
      Allah ya kawo mini babban baƙin ciki.
10 Gama da idona na ga an kama yayana mata da maza,
      Haka Madawwamin ya ƙaddara musu.
11 Na ba su maman farin ciki,
      Amma na aike su da kuka da baƙin ciki.
12 Kada wani ya raina ni saboda ni gwauruwa ce,
      Yawancin yayana sun yi mini nisa,
Don an yi watsi da ni saboda zunuban yayana,
      Domin sun bauɗe wa shariar Allah.
13 Ba su koyi kaidodinsa ba,
      Ko tafiya bisa ga dokokinsa,
      Ba su kuma yarda adalcin Allah ya kahu da gindinsa a zukatansu ba.
14 Maƙwabtan Sihiyona, ku iso,
      Ku tuna yadda aka mai da yayana mata da maza bayin yaƙi.
      Haka Madawwami ya ƙaddara musu su yi.
15 Gama ya bangazo musu waɗansu abokan gāba daga nesa,
      Kabila mai baranci, mai yare dabam,
Waɗanda ba su girmama dattijo,
      Balle suji tausayin yaro.
16 Sun kwashe mini, ni gwauruwa,
      Yayana maza na gaban goshi,
      Sun ma sa ni kuka a kan yayana mata, a kaɗaice.
17 Amma, yayana, ta yaya zan iya taimakonku?
      18 Gama wanda ya ɗora muku balain nan,
      Shi ne ma zai cece ku daga hannun maƙiyanku.
19 Ku tafi, yayana, ku tafi,
      Gama an bar ni ba makoma.
20 Na tuɓe tufafin salama,
      Na zuba tsummoki don roƙon gafarar zunubaina,
      Zan yi kuka ga Madawwami dukan kwanakin raina.

21 Ku ƙarfafa, ku yayana, ku yi kuka ga Allah,
      Zai kare ku daga zalunci a hannun abokan gābanku.
22 Gama na ɗora begena ga Madawwami domin ya cece ku,
      Farin ciki ya zo mini daga Mai Tsarkin nan, saboda jinƙai
      Wanda zai zo muku da sauri daga Madawwamin Mai Cetonku.
23 Gama na aike ku tare da kuka da baƙin ciki,
      Amma Allah zai dawo mini da ku da murna
      Da farin ciki na har abada.
24 Kamar yadda maƙwabtan Sihiyona suka ga yadda aka kama ku, ku zama bayin yaƙi,
      Haka ne za su ga fansarku ta zo daga wurin Allahnku,
      Wadda za ta zo muku da ɗaukaka da bangirma na Madawwami.

25 Yayana, ku karɓi fushin Allah da haƙuri,
      Wanda ya auko muku.
Magabtanku sun ci yar nasara a kanku,
      Amma nan gaba kaɗan za ku zuba ido, ku ga hallakarsu,
      Yadda za ku kā da su, ku tāke.
26 Majidadina sun yi tafiya ta hanya mai kwazazzabai,
      Magabta sun kwashe su, sai ka ce garken tumaki.
27 Ku ƙarfafa, ku yayana, ku yi kuka ga Allah,
      Shi wanda ya ɗora muku matsalar, zai tuna da ku.
28 Gama kamar yadda dā nufinku ne ku bauɗe wa Allah,
      Yanzu ku nemi alherinsa da niyya mai ninki goma.
29 Shi wanda ya kawo muku balain nan
      Zai fanshe ku, ya kawo muku madawwamin farin ciki.

An Agaji Urushalima
30 Ki ƙarfafa, ya ke Urushalima,
      Gama wanda ya raɗa miki sunan nan zai agaje ki.
31 Tasu ta ƙare, waɗanda suka yi miki lahani,
      Suka ma yi wa masifarki dariya.
32 Tasu ta ƙare, garuruwan da suka mai da yayanki bayi,
      Tasa ta ƙare, garin da ya riƙi yayanki.
33 Gama yadda garin nan ya yi farin cikin masifarki, da murna da kangonki,
      Haka ne zai yi baƙin ciki da nasa kango.
34 Za a tsame masa gaggan daga cikin jamaarsa,
      Fankamarsa za ta koma abin tausayi.
35 Gama Madawwaini zai aiko masa da wuta,
      Ta yi ta ci kwana da kwanaki,
      Zai zama matattarar aIjannu har zuwa wani lokaci.

36 Ki duba gabas da ke, ya Urushalima,
      Ki ga farin cikin da ke zuwa miki daga wurin Allah.
37 Ki duba, ki ga yayanki suna zuwa,
      Waɗanda kika aike da su da.
Ga su nan tafe, tattare daga gabas da yamma,
      Bisa ga umarnin Mai Tsarkin nan,
      Suna yin farin ciki da ɗaukakar Allah.

5.

1 Ki tuɓe tufafinki na baƙin ciki da zaluncin da aka yi miki, ya Urushalima,
      Ki sa kayan dawwama na ɗaukakar Allah da ke zuwa miki.
2 Ki sa tufafin adalci wanda ke daga wurin Allah,
      Ki naɗe kanki da rawanin ɗaukaka ta Madawwamin.
      3 Gama Allah zai nuna wa dukan duniya haskenki.
4 Allah zai raɗa miki madawwamin suna, wato
      Adalci Mai Salama da Ibadar Allah Maɗaukaki.

5 Ki tashi, Urushalima, ki hau tsaunuka,
      Ki kuma duba wayen gabas.
Ki ga yayanki sun taru daga gabas da yamma,
      Bisa ga umarnin Mai Tsarkin nan,
      Suna murna domin Allah ya tuna da su.
6 Gama sun rabu da ke,
      Suna tafiya da ƙafa,
      Magabtansu sun tasa ƙyeyarsu gaba,
Amma Allah zai dawo miki da su,
      A goye su da ɗaukaka, kamar yayan sarki.
7 Gama Allah ya umarci a baje kowane dutse da madawwamin tudu,
      A cika kowane kwari har baka,
      Domin Irsrailawa su bi, su haye lafiya, bisa ga ɗaukakar Allah.
8 Kurmi da kowane irin itace mai ƙanshin fure
      Sun inuwantar da Israilawa, bisa ga dokar Allah.
9 Gama Allah zai shugabanci Israilawa da murna,
      Ta wurin hasken ɗaukakarsa
      Tare da jinƙai da adalcin da suka zo daga gunsa.

6. Wasiƙar Irmiya

1 Ga fassarar wasiƙar da Irmiya ya aika wa bayin yaƙi waɗanda za a kwashe zuwa Babila, in ji Sarkin Babila. Ya yi musu gargaɗi kamar yadda Allah ya umarce shi.

Saboda zunuban da kuka yi a gaban Allah, Nebukadnezzar Sarkin Babila zai kwashe ku ku yi zaman talala. 2 In kun kai Babila, za ku yi yan shekaru a can, za ku ma daɗe, har tsara bakwai, amma bayan haka, zan kutto da ku da salama daga can. 3 To, a Babila za ku ga yan gumaka waɗanda aka yi da azurfa, da zinariya, da kuma itace, mutane suna ɗauka a kafada, har suna firgita arna. 4 Ku yi laakari, kada ku ma ku kwaikwayi abin da ama suke yi. Kada ma ku ji tsoro 5 lokacin da kuka ga taro gaban gumakan da bayansu, ana yi musu sujada, amma ku ce a zukatanku, Ya Ubangiji, dole ne mu yi maka sujada. 6 Gama malaikana yana tare da ku, yana kare rayukanku.

7 Gama masassaƙi yana koɗa bakunan gumakan, yana dalaye su da zinariya, yana kuma sa musu azurfa, amma ruba kawai suke, ba su iya yin magana. 8 Yana ɗaukar zinariya, yana yi wa kawunan gumakan rawani, sai ka ce yarinya mai yawan son kayan ado. 9 Wani lokaci sai sarakunan tsafi su zaro zinariya da azurfa a asirce, su biya wa kansu bukata, 10 har ma su bai wa karuwai yan kuɗi a kan benayen ɗakin gumaka. Suna sa wa gumakan nan na azurfa, da na zinariya, da na itace tufafi, kamar mutane. 11 Amma ko da ya ke an tufar da gumakan nan da zannuwa masu daraja, ba su iya tsare kansu daga gara ko tsatso. 12 Suna kuma bukatar a riƙa shafe fuskokinsu don ƙura mai yawa da ke sauka bisa kansu a ɗakin. 13 Kowannensu yana ɗaukar sandan girma kamar alƙalin yan adam, ko da ya ke ba ya iya hallaka wani wanda ya saɓa masa. 14 Kowarmensu yana riƙe da da takobi a hannunsa na dama da kuma gatari, amma ba ya iya ceton kansa lokacin yaƙi, ko daga hannun ɓarayi. Haka ya bayyana ba alloh suke ba, kada ku ji tsoronsu.

15 Kamar yadda akushin mutum ke rasa amfani in ya rabu biyu, haka ne gumaka nasu suke a lokacin da aka zaunar da su a gidajen da aka yi musu. 16 An cika musu idanu da ƙurar da ƙafafun masu shiga da fita ke tayarwa. 17 Kamar yadda ake rufe ƙofar kurkuku ga wanda ya keta haddin sarki, har ma a hukunta masa mutuwa, haka sarkin tsafi ke rufe ɗakin gumaka da ƙyaure, da sakatu, da makullai, don kada ɓarayi su ƙware su. 18 Suna kunna fitilu, iri waɗanda su ma ba su da su, ko da ya ke gumaka nasu ba su ganin fitilun. 19 Kamar ma dirkokin ɗakin suke, gara daga ƙasa ta rarake su duk da tufafinsu, don ba su san ciwon jikinsu ba. 20 Fuskokinsu sun duhunta da hayaƙi daga haikalin. 21 Jemagu, da tsattsewa, da sauran tsuntsaye suna sauka a jikinsu da kansu, haka ma kyanwoyi. 22 Ta haka ku tabbata ba alloli ba ne, kada ku ji tsoronsu.

23 Ko da aka yi musu adon zinariya, ba za su yi haske ba, sai in wani ya goge tsatsar. Ko lokacin da aka sassaƙa su ma, ba su ji kome ba. 24 Ana sayen su da tsadu, amma ba su yin ko numfashi. 25 Kamar yadda ba su da ƙafafu, mutane na ɗaukarsu a kafada, ta haka suke sa mutane su raina su. Waɗanda ke bauta musu ma suna shan kunya, gama sau da yawa gumakan sun fāɗi ƙasa, ba su iya tashi da kansu ba. 26 In wani ya tashe su, ba su iya motsi da kansu, ko sun ɓingire ma, ba su iya jirkitawa. Ana ba su abinci, amma matacce na iya cin abinci? 27 Abin da ake miƙa musu hadaya, sai sarakunan tsafi su sayar, su haye da kuɗin. Haka ma matansu ke ƙyafe: naman, su yi ta kansu da shi, amma ba su taimakon matalauta da gajiyayyu ko kaɗan. Har mace mai haila ko mai naƙuda, na iya taɓa hadayar. 28 Ai, duk waɗannan abubuwa sun tabbata su ba alloli ba ne, kada ku ji tsoronsu.

29 Ta yaya ma ake kiransu alloli? Ai, mata ne ke mika wa gumakan nan na azurfa, da zinariya, da itace, abinci. 30 Saan nan a haikalansu sarakunan tsafi sukan tsuguna waje ɗaya da tufafi yagaggu, su aske kansu da gyammansu, su kuma bar kansu ƙwal a buɗe, 31 suna hargowa a gaban gumaka nasu kamar yadda waɗansu ke yi wa matacce makoki. 32 Sarakunan tsafi sukan tuɓe tufalin gumakan, su sa wa matansu da yayansu. 33 Ko an saɓa wa gumakan nan ma, ko an yi musu alheri, ba su iya ramawa, ba su iya naɗa sarki ko su tuɓe shi. 34 Haka kuma, ba su iya ba da dukiya ko tsabar kuɗi. In wani ya yi musu alkawari bai ma cika ba, ba za su iya ci masa diddige ba. 35 Ba su iya fansar mutum daga mutuwa, ba su ma iya ƙwatar kumama daga hannun Kaƙƙarfa ba. 36 Ba su iya buɗe wa makaho ido ba, ba su iya yi wa mai shan wuya taaziyya ba. 37 Ba su iya jin tausayin gwauruwa, ba su ma iya yi wa maraya alheri. 38 Waɗannan gumaka da aka yi da itace, aka kuma dalaye da zinariya da azurfa, kamar ɓalgacen duwatsu suke daga babban dutse. Waɗanda kuma suka dakata musu za su sha kunya. 39 Don me ma wani zai tsammaci su alloli ne, har a kira su haka?

40 Bayan haka, har Kaldiyawa ma sun rama su, gama da sun ga kurma, sai su kai shi gun allahnsu mai suna Bel domin Bel ya sa wanda ba ya iya magana, wai ya maganta. Amma Bel ɗin ya fi kurman kuruncewa. 41 Duk da haka, mutanen nan ba su iya ganewa da wannan, su watsar da gumakan, gama mutanen, jahilci ya yi musu kanta. 42 Matan kuma sai su yi damara da waɗansu igiyoyi, su zauna a gefen karauka, suna ƙona ƙaiƙayi, wai turaren ƙonawa. 43 Da wani matafiyi ya ja ɗaya daga cikinsu, ya kwana da ita, ita kuma ta sami mijin aure ke nan, ta raina maƙwabciyarta, domin ba wanda ya yi shaawarta, ba a kuma ture igiyoyinta waje ɗaya ba. 44 Duk abin da ake yi da gumakan nan ruɗi ne. Don me wani zai tsammaci su alloli ne, har a kira su haka?

45 Masassaƙa da maƙeran zinariya ne suka yi su, ba wani abu za su zama ba, sai abin da gwanaye suka mai da su. 46 Mutanen da suka yi su ma, ba su cika daɗewa ba. Ta ƙaƙa abubuwan da suka yi za su zama alloli? 47 Ƙarya da abin zargi kawai suka bar wa yan baya. 48 Da yaƙi ko balai ya auko musu, sai sarakunan tsafi su yi taron gaggawa na Ina za su kawar da jiki, su da gumaka nasu? 49 Ta ƙaƙa wani zai kasa ganewa, cewa waɗannan ba alloli ba ne, tun da ba su iya kare kansu a lokacin yaƙi ko balai ba? 50 Ai, tun da ya ke da itace aka yi su, aka dalaye su da zinariya da azurfa, daga baya za a gane irin ruɗin da aka yi. Dukan kabilai da sarakunan duniya za su sani ba alloli ba ne, amma aikin hannuwan mutane ne, ba su da ikon Allah a cikinsu.

51 Don haka, wa zai kasa sanin su ba alloli ba ne? 52 Gama ba su iya zaɓar wa ƙasa sarki, ko aiko da ruwan sama don rayuwar jamaa ba. 53 Ba su ma iya sharaanta matsala in wani ya saɓi wani, ko ceton wanda aka ƙwara ba. Kamar hankaki suke a tsakanin sama da ƙasa. 54 Lokacin da gobara ta kama ɗakin allolin itace waɗanda aka dalaye da zinariya ko azurfa, sai sarkin tsafinsu ya dafa kunne, ya ranta ciki na kare, armna yan allolin su yi ta cin wutar kamar dirkoki, sai sun ƙone kurmus. 55 Banda haka ma, ba su iya yin tsayayya da wani sarki ko magabci ba. 56 Don haka, wa zai yarda ko ya tsammaci su yan alloli ne?

Allolin da aka yi da itace, aka dalaye su da azurfa da zinariya, ba su iya kāre kansu daga ƙattin ɓarayi ko yan fashi ba, 57 waɗanda suke tuɓe zinariya, da azurfa, da kuma zannuwan da aka sa musu, su tafi da ganima, amma gumakan ba su iya taimakon kansu. 58 Ai, gara zama sarkin da ke nuna bijinta, ko tarkacen ɗaki waɗanda ke biya wa mai su bukata, da zama waɗannan allolin ƙarya. Gara ma ƙyauren kofa, wanda ke tsare lafiyar masu gida, da waɗannan allolin ƙarya. Gara ma ginshikin itace a fādar sarki, da allolin nan. 58 Gama rana, da wata, da taurari suna haskakawa, suna kuma da biyayya lokacin da aka aiko su su yi hidima. 59 Haka ma walƙiya take. Lokacin da ta yi walai, ana ganinta koina. Iska ma tana hurawa a kowace ƙasa. 60 Gizagizai kuma, lokacin da Allah ya umarce su, sai su tafi dukan ƙasashen duniya. Ai, bin dokar Allah suka yi. Da aka aiko wuta daga sama ma ta lashe duwatsu da itatuwa, ai, ta aikata. 62 Amma gumakan nan ba su kai kyan duk waɗannan abubuwa da ikonsu ba ko kaɗan. 63 Don haka bai kamata wani ya tsammaci su alloli ne ba, ko ya kira su alloli, don ba su iya yanke sharia, ko su yi wa jamaa wani alheri ba. 64 Tun da ya ke kun sani ba alloli ba ne, to, kada ku ji tsoronsu.

65 Gama ba su iya sa wa sarki albarka ko laana. 66 Ba su iya nuna wa alummai ayoyi a samaniya, ko yin haske kamar na rana ko na wata. 67 Namomin jeji ma sun fi su nesa ba kusa ba, gama suna ranta ciki na kare in sun ga hatsari. 68 Don haka mu dai mun tabbata su ba alloli ba ne ko kaɗan, kada ma ku ji tsoronsu. 69 Kamar burtun da aka yi wa biri, haka allolin itacensu suke, waɗanda aka dalaye su da zinariya da azurfa. 70 Ai, allolin nan nasu na itace da aka dalaye da zinariya da azurfa, kamar sarƙaƙƙiya suke a gona, inda kowane tsuntsu ke sauka, kamar ma mushen da aka yar suke. 71 Zannuwansu masu daraja da ke ruɓewa su za su sanar muku ba alloli ba ne. Daga ƙarshe ma hallaka su za a yi ɗungum, su zama abin zargi a ƙasar. 72 Gara adalin da ba shi da gumaka, gama zai yi nesa da abin zargi.

*      *      *      *      *
*      *      *
*