BAYAHUDIYA

1. Nebukadnezzar ya Yaƙi Arfakshad

1 Ana nan a shekara ta sha biyu ta mulkin Nebukadnezzar wanda ya mallaki Assuriyawa a babban garin Nineba, a zamanin Arfakshad, shi ma ya mallaki Mediyawa daga babban birninsu, Ekbatana. 2 Shi ne sarkin da ya sake wa Ekbatana sabon garu na duwatsu, kowannensu mai tsayi kamu uku da tsawo, kamu shida da faɗi, garu ma ya kai tsawon kamu sabain, faɗi kamu hansin. 3 A ƙofofin garun sai ya gina hasumiyoyi masu tsawo kamu ɗari ɗari, da faɗi kamu sittin sittin gun harsashin ginin. 4 Ya yi musu ƙofofi masu tsawo kamu sabain sabain, da faɗi kamu arbain, arbain, domin karusansa na yaƙi su iya wucewa, sojojinsa ma su iya fita banga banga.

5 A zamanin ne Nebukadnezzar sarki ya yaƙi sarki Arfakshad a babban filin nan na yankin Ragau. 6 Sai dukan mutanensa waɗanda ke zaune kan tsaunuka da waɗanda ke zaune bakin kogin Yufiretis, da na Taigiris, da na Haidasafes, har da na karkara inda Ariyok ke mulkin Elamawa, kabilai da dama suka hada ƙarfi domin su yaƙi Kaldiyawa.

7 Saan nan Nebukadnezzar, Sarkin Assuriyawa, ya aika wa dukan waɗanda ke zaune a Farisa can gabas, da waɗanda ke zaune a yamma, kamar su Kilikiya, da Dimashƙu, da ƙasar Lebanon da kewayenta, da dai dukan waɗanda ke zaune a ga6ar teku, 8 da mutanen da ke zaune a yankunan Karmel, da Gileyad, da na arewacin Galili, da na karkaran nan mai faɗi ta Asdaralona, 9 da duk waɗanda ke zaune a ƙasar Samariya da ƙauyukanta, da yammacin Urdun, har zuwa Urushalima, da Betanya, da Kalosa, da Kadesh, da wajen Kogin Masar, da wajen Tafanes, da Ramases, da dukan ƙasar Goshen, 10 har gaba da Tanis da Memfis, da dukan mazaunan Masar har kan iyakar Habasha.

11 Amma dukan mazaunan wuraren nan, sai suka raina umarnin Nebukadnezzar, Sarkin Assuriyawa, suka ƙi taya shi yaƙi, gama ba su jin tsoronsa, amma sun dauke shi kamar maƙiyi wanda ba mai goyon bayansa, sai suka kori manzannin sarki hannu wofi, har kuma da kunya. 12 Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da dukan waɗannan sassa. Ya rantse, cewa zai yi murabus, in bai ɗau fansa a kan Kilikiya, da Dimashƙu, da Suriya ba, ya kuma yanka dukan mazaunan Mowab, dal mutanen Ammon, da na dukan Yahudiya, da kowa da kowa na Masar, har an kai gabar tekunan nan biyu.

13 A shekara ta sha bakwai, sai ya auka wa Arfakshad da yaƙi, ya kore shi fata fata, ya hallaka dukan sojojin Arfakshad kaf, dukansu na dawakan da na karusan. 14 Ta haka ya mallaki biranen Arfakshad, ya gangaro Elbatana, ya ci hasumiyoyinta, ya mai da kasuwoyinta ganima, kyanta kuma ya dushe. 15 Ya kama Arfakshad a duwatsun nan na Ragau, ya kashe shi da masu farauta, ya hallaka shi kwata kwata, har kwanan gobe. 16 Saan nan suka koma gida, da shi da sojansa bila haddin, babbar ƙungiya ta mazan fama. A can ne shi da sojojinsa suka shakata, suka kuma yi bikin kwana ɗari da ashirin.

2. Shirin Yakin Kasashen Yamma

1 A shekara ta sha takwas, a rana ta ashirin da biyu ga watan farko, aka yi wata tattaunawa a fadar Sarkin Assuriyawa, Nebukadnezzar, kan yadda zai yi ramuwar gayya ga dukan sassan duniya, kamar dai yadda ya ce zai yi. 2 Sai ya kira jarumawansa da dai sauran ƙusoshin gari, ya bayyana musu asirtaccen nufinsa filla filla, ya hurta yadda zai hallaka dukan sassan nan gaba daya. 3 Sai aka zartar da hukuncin duk wanda bai bi umarnin Nebukadnezzar ba, za a hallaka shi. 4 Da ya gama bayyana nufinsa, shi Nebukadnezzar, Sarkin Assuriyawa, ya kirayi Halofanesa, babban jarumin dukan sojojinsa, wanda yake bayan Nebukadnezzar sai shi, ya ce masa, 5 Abin da Babban Sarki ya ce ke nan, wanda ke ubangijin dukan duniya. In za ka tafi bakin dāga, ka zaɓi dakaru na sojan ƙafa dubu dari da dubu ashirin, da sojan doki dubu goma sha biyu. 6 Ka tafi, ka auka wa ƙasashen yamma, tun da ya ke sun ƙi bin maganata. 7 Ka ce musu su yi shirin ba da kansu, gama ina zuwa a kansu, sojojina za su rufe ƙasar, har ba masaka tsinke, za su mai da wurin ganimarsu. 8 Waɗanda aka kashe za su cika kwaruruwansu, kowane kwazazzabo da kowane kogi za su cika da gawawwakinsu, har su ba jeji. 9 Zan kai su a bayin yaƙi, har zuwa bangon duniya.

10 Ka ƙwato mini dukan ƙasashensu. In sun ba da kansu da kansu, ka riƙe mini su, sai lokacin da na zo in hore su. 11 Amma dukan garuruwan da suka ƙi, kada ka ji tausayinsu, ka yanyanka su, ka mai da su ganima. 12 Gama na rantse da raina da sarautata, duk abin da na hurta, hannuna zai zartar da shi. 13 Kai kuma, ka fa kula kada ka keta wani haddi nawa, ni da nake ubangijinka, amma ka bi umarnai yadda na dokace ka da su, kada dai ka daɗe.

14 Sai Halofanesa ya zabura daga gaban ubangijinsa, ya kira dukan jarurnawansa, da shugabannin yaƙi, da manyan sojojin Assuriyawa. 15 Ya kintsa sojoji sashi sashi, kamar dai yadda ubangijinsa ya sa masa a baka, su sojan ƙafa dubu ɗari da ashirin, tare da sojoji mahaya, su dubu goma sha biyu, 16 sai kuwa ya shirya su sashi sashi, yadda za su yaƙi kowane irin abokin gāba. 17 Ya ɗibi raƙuma, da jakai, da alfadarai da yawa don hawa, da kuma tumaki, da bijimai, da awaki, ga su nan tasasa don guzuri, 18 da kuma isasshen abinci saboda kowane dakari, da isassun zinariya da azurfa daga fadar sarki.

19 Sai Halofanesa ya tasa ƙeyar sojojin, suka fita daga gaban sarki Nebukadnezzar, suka rufe ƙasashen yamma da karusansu, da mahayansu, da sojojin ƙafa. 20 Har ma yan sari-ka-noƙe suka bi su a baya, suka rufe ƙasa kamar fāri, taron har ya fi gaban ƙidaya dai.

Halofanesa ya ci Kasashen Yamma

21 Suka rankaya daga Nineba zuwa karkarar Bakataleta tafiya kwana uku, daga Bakataleta sai suka kai kusa da tsaunukan da ke arewacin Kilikiya. 22 Daga can ne sai Halofanesa ya kwashe dukan sojojinsa, sojan ƙafa, da sojan doki, da karusan, ya dikaka cikin tsaunukan, 23 ya rushe yankunan Fut da Lud, ya washe dukan Rasisawa da Ismailawa waɗanda ke zaune a gefen hamada, kudancin ƙasar Kaldiya.

24 Saan nan ya bi ta Kogin Yufiretis, ya haye ta ƙasan nan da ke tsakanin koguna biyu, ya hallaka dukan biranen da ke gefen gulbin Abarona, sai da ya kai bakin teku tukuna. 25 Ya kwace ƙasar Kilikiya, ya kuma kashe duk waɗanda suka nuna taurinkai, har ya shiga kudancin kan iyakar Yafet, ya doshi ƙasar Arabiya haiƙan. 26 Ya yi wa dukan Madayanawa zobe, ya ƙone alfarwansu, ya washe garkunan tumakinsu. 27 Saan nan ya gangara zuwa karkarar Dimashƙu a lokacin yankan alkama, ya ƙone dukan gonakinsu, ya washe garkunansu na tumaki, da na awaki, da na shanu, ya mai da biranensu ganima, ya ɓata karkararsu, ya kuma kashe dukan samari ganiyar ƙarfi da kaifin takobi. 28 Don haka sai duk mutanen da ke zaune a bakin gaɓar teku suka firgita saboda shi, na Sidon da na Taya, da waɗanda ke Sur, da Okina, da mazaunan Yamaniya. Har mazaunan Azotus da Askelon ma suka ji tsoronsa matuƙar gaske.

3

1 Don haka, sai mutanen garuruwan nan suka aika da saƙon neman sullm, suka ce, 2 Ai, tun da ya ke mu bayin Nebukadnezzar ne, babban sarki, muna rusuna a gabanka. Duk abin da kake son yi da mu, ai, ba mai ce maka aa. 3 Ka duba, gine‑ginenmu, da dukan ƙasarmu, da dukan gandayen alkamarmu, da garkunanmu na tumaki da na shanu, da duk abin da ke cikin zangonmu, ga su nan a gabanka, ka yi duk abin da ka ga dama da su. 4 Biranenmu da mazaunansu sun zama bayinka. Ka zo, ka yi musu duk abin da ya gamshe ka.

5 Bayan da aka gaya wa Halofanesa wannan duka, 6 sai ya gangara gaɓar teku da sojojinsa, ya sa runduna a kowane birni, ya zaɓi sojoji sababbin shiga daga cikin biranen. 7 Mutanen waɗannan birane da dukan jamaar ƙauyukansu, sai suka marabce shi da nannaɗa furanni, da rawa, da buga tambura. 8 Duk da haka sai ya Ialata dukan shirayin gumakansu, ya kuma kakkarye jigunan tsafinsu sarai, gama ya sami iznin warwatsar da dukan yan allolin da ke a ƙasar, domin dukan alumman ƙasar su bauta wa Nebukadnezzar, shi kadai. An ce duk kabilai su riƙa kiran sunansa da bakinsu, sai ka ce wani ɗan allah ne. 9 Saan nan Halofanesa ya gabato ƙauyen AsdaraIona, kusa da Dotan, ya zo gaban babban tsaunin nan na Yahudiya. 10 A nan sai ya yi sansani a tsakanin Geba da Sakatafolis, ya yi zaman wata guda cir, domin ya kintsa dukan kayan da sojansa za su bukata.

4. Yahudawa suna Shirin Tsaro

1 A lokacin, ashe, dukan Israilawa da ke zaune a Yahudiya sun ji abin da Halofanesa, babban jarumin sarki Nebukadnezzar ya yi wa sauran alummai, yadda ya washe masujadansu, ya kuma rurrushe su. 2 Don haka, da suka ji ya matso garinsu, duk sai suka tsunke da shi, suka tsorata kan abin da zai auka wa Urushalima da Haikalin Ubangiji Allahnsu. 3 Gama ba su daɗe da dawowa daga bauta ba, suka sami hallara a gu guda a ƙasar Yahudiya, kwanan nan ne kuwa aka tsabtace kayayyaƙi masu tsarki, da bagade, da Haikali daga ƙazantarwar da aka yi musu.

4 Sai mutanen Urushalima suka yi aike a dukan gundumomin Samariya, da na Kona, da na Bet‑horon, da na Balmayin, da na Yariko, da na Koba, da na Aisora, bar da kwarin Salem. 5 Sai mutanen biranen nan suka sa masu tsaro bisa ƙololuwar dukan tsaunuka masu tsawo, suka kuma yi gineginen tsare ƙauyuka, suka ajiye abinsu na shirin yaƙi, tun da ya ke gonakin ba su daɗe da girbi ba.

6 Yowakima, babban firist wanda ke Urushalima a zamanin, ya rubuto wa mutanen da ke zaune a Betuliya da Betamatsayima, da ke fuskantar Asdaralona da ke harmun riga da Dotan, 7 ya umarce su su tare duk mashigai na tsaunuka, tun da ya ke ƙofofin Yahudiya ne, za a ma sami sauƙin dakatar da mai shirin shiga, gama ƙofar shiga ƙaramar gaske ce, mutum biyu kawai ke iya kurdawa su, wuce da ƙyar. 8 Sai Israilawa suka yi duk abin da Yowakima babban firist da mashawartan dattawa suka umarta.

Yahudawa suna Addua

9 Dukan Israilawa suka yi kuka mai zafi a gaban Ubangiji suka kuma kasƙantar da kansu. 10 Su da matansu, da yayansu, da shanunsu, da kowane baƙo da ɗan ƙodago, da bawa, duk suka yi damara da tsummoki. 11 Sai dukan mata da maza, Israilawa, da yayansu da ke zaune a Urushalima, suka rusuna a gaban Haikalin, suka yi hurwa da toka, suka kuma nuna tsummokinsu a gaban Ubangiji. 12 Har ma zobe suka yi wa bagaden da tsummoki, suka yi roƙo gaba daya, suna yin addua da sahihiyar zuciya ga Allahn Israilawa, kada ya raba su da yayansu ko matansu, kada ma a hallaka biranen da suka gāda tun kakanni da iyaye, kada kuma ama su keta haddin Haikalin, su yi masa baa.

13 Ubangiji kuwa ya ji roƙe‑roƙensu, ya ga wuyar da suke sha, gama mutanen sun yi azumi kwana da kwanaki, tun daga kan iyakar Yahudiya bar ya zuwa Haikalin Ubangiji Mai Iko Dukka a Urushalima. 14 Da Yowakima, babban firist, da sauran firistoci waɗanda ke hidimar Ubangiji dai, sai suka yi damara da tsummoki, suka dinga miƙa hadayar ƙonawa ta kowace rana da hadayun alkawari da na yardar rai saboda mutane. 15 Har da toka a kan rawunansu, suka riƙa daga muryar ga Ubangiji, don ya duba jamaar Israilawa da idon rahama.

5. Jawabin Halofanesa

1 A lokacin da Halofanesa, jarumin sojojin Assuriyawa ya ji, wai mutanen Israilawa sun shirya yaƙi, sun kuma rufe dukan mashigai na tsaunuka, sun yi gine‑ginen tsaro bisa ƙololuwarsu, sun tare hanyoyin karkara ma da gumagumai, 2 sai ya husata kwarai. Har ya kirayi dukan yayan sarakunan Mowab gaba ɗaya, da jarumawan Ammonawa, da dai dukan hakiman bakin teku, 3 ya ce musu, Ku gaya mini mana, ya ku Kananiyawa, waɗanne mutane ne ke zaune a garin can na kan tsauni? Waɗanne garuruwa ne suke zaune ciki? Sojojinsu sun kai dubu nawa? A kan me suka yi haɗin gwiwa? Wanene sarkinsu wanda ke musu jagora zuwa bakin dāgā? 4 Me ya sa a cikin dukan mutanen yamma nan, sai su kadai ne suka ƙi zuwa taryata?

Jawabin Akiyora

5 Saan nan Akiyora, shugaban dukan Ammonawa, ya ce masa, Bari ubangijina ya saurari jawabi daga bakin bawansa, ni kuma zan gaya maka gaskiya a kan mutanen nan da ke zaune a gundumar duwatsun da ke kurkusan nan. Ba ƙarya bawanka zai sheƙa maka ba.

6 Waɗannan mutane zuriyar Kaldiyawa ne. 7 Sun taɓa zama ƙasan nan ta tsakanin koguna biyu, saboda ba su son bauta wa yan allolin nan na kakanninsu Kaldiyawa. 8 Tun da ba su bi tsofaffin hanyoyin nan na kaka da kakanni ba, Allah na Sama kaɗai kuwa suka yi wa bauta, wato Allahn da aka sanar musu, don haka ne ma Kaldiyawa suka kore su daga gaban yan allolin nan nasu, su kuwa suka gudu zuwa ƙasan nan ta tsakanin koguna biyu, sun kuma daɗe can. 9 Saan nan Allahnsu ya umarce su su bar ƙasar da suke zaune a ciki dā, su tafi su zauna a ƙasar Kanana. A can suka zauna, suka kuwa arzuta ƙwarai da gaske, ga dai zinariya da azurfa da kuma garkunan shanu tasasa. 10 Da yunwa ta auka wa ƙasar Kanana, sai suka gangara zuwa Masar, suka zauna can, suka daɗe suna ta garƙar abinci. A can ne ma suka zama babbar alumma, suka yi yawan gaske wanda ya fi gaban ƙirga. 11 Sai Sarkin Masar ya fara gasa musu azaba, har ya mai da su bayi masu aikace‑aikacen yin tubali, ya ƙasƙantar da su, ya dai mai da su jakai. 12 Sai suka yi kuka ga Allahnsu, ya kuwa kwararo wa dukan ƙasar Masar annobai iri in, waɗanda ba maganinsu, har da Masarawa suka yiwo musu korar kare daga ƙasarsu tukuna. 13 Har Allah ya busar da Bahar Maliya dominsu, suka haye. 14 Ya bi da su ta hanyar Sinai da Kadesh‑Bameya, suka wartaki dukan mazaunan jejin nan, suka maye wurin. 15 Suka zauna a ƙasar Amoriyawa, saboda ƙarfinsu sai suka hallaka dukan mazaunan Heshbon. Da suka haye Kogin Urdun, sai suka karɓe duk kasashen nan na kan tuddai. 16 Har ma suka kori Kananiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Shekemiyawa, da dukan Gergisiyawa fata fata, suka gaje tsaunukan nan, suka kuma daɗe zaune a wurin.

17 Da ya ke ba su saɓa wa Allahnsu ba dai, sai suka yi ta arzuta, gama Allahn da ba ya yin naam da saɓo yana tare da su. 18 Amma da dai suka bauɗe daga hanyar da ya zaɓar musu, sai aka yi ta cinsu a gun yaƙi, har ma aka yi ta kama waɗansu, ana kai su bakin kasashe, sun zama bayin yaƙi, aka rurrushe Haikalin Allahnsu, abokan gābansu suka kame biranensu. 19 Amma yanzu sun juyo a gun Allahnsu, sun daddawo daga wuraren da aka watsar da su, sun mamaye Urushalima, inda Haikalinsu yake, sun zauna a ƙasar tuddai, tun da ya ke ba kowa a ciki.

20 Saboda haka, yanzu, ya maigiɗana, ubangijina, in an sami wani kuskure gun mutanen nan, in kuma mun tabbata sun saɓi Allahnsu, sai mu tafi, mu ci su. 11 Amma in ba mugun aiki a kabilarsu, sai ubangijina ya ƙyale su, tun da ya ke Allah Ubangijinsu zai kāre su, zai ma kiyaye su, mu kuwa mu kunyata a idanun dukan duniya.

22 Da Akiyora ya gama faɗar haka, sai dukan mutanen da ke zaune a gefen alfarwai suka fara gunaguni. Babban jarumin nan, Halofanesa, da dai dukan mutanen bakin teku da Mowabawa, sai suka ƙudura cewa, Ai, sai a yi gunduwa gunduwa da shi, 23 gama sun ce, Mu ba za mu ji tsoron Israilawa ba, ai, mutane ne yan tawaye, ba su ma kuwa da ƙarfi gun yaƙi. Don haka ma auka musu, ya ubangiji Halofanesa, ai, wannan babbar ƙungiyar mayaƙa taka za ta hallaka su.

6. Halofanesa ya Ba da Amsa

1 Da mutane na waje suka gama hargowarsu, sai Halofanesa shugaban sojojin Assuriyawa, ya ce wa Akiyora, da dukan Mowabawa, da sojojin haya na Ammonawa , 2 Kai wanene, Akiyora, da za ka yi mana annabci yau, cewa kada mu yi yaƙi da Israilawa, domin wai Allahnsu zai kāre su? Wanene Allah banda Nebukadnezzar, Babban Sarki? Ai, aikawa zai yi da mayaƙansa ya shafe su sarai daga fuskar ƙasa ma. Allah nasu kuwa ba zai agaje su ba ko kaɗan. 3 Mu bayin sarki, mu ne za mu hallaka su kamar dai wuta da saɓi. Ai, ba su ma iya shanye harin sojamnu na dawakai. 4 Za mu ƙone garinsu ƙurmus, jininsu zai shanye kan duwatsunsu, gonakinsu kuma su cika da gawawwaki birjit. Wane su da mu? Hallaka su za mu yi kakat. Haka ne Sarkin Duniya, Nebukadnezzar, ya ce. Ai, ya yi hurci, ko ɗaya kuwa ba zai faɗi a ƙasa banza ba. 5 Amma kai kuwa Akiyora, Baammonen haya, wa ya gaya maka wannan maganar banza haka? Ba za ka ƙara ganin fuskata ba, sai ran da na ɗauko fansa a kan kabilan nan wadda ta fito daga Masar. 6 Da na dawo daga yaƙi, takuban sojana da masunsu za su soki kuyaɓunka, za ka tarar da waɗanda suka mutu lokacin yaƙin. 7 Yanzu bayina za su kama ka, su kai ka a ɗaya daga cikin ƙauyukan duwatsun, 8 ba za ka mutu ba, sai an haɗa ku tare, kai da Israilawa, a hallaka ku baki daya. 9 In kuwa ka tabbata a ranka, ba su kamuwa, to, sai ka sa ranka a inuwa. Ni dai na yi magana, ba ko guda daga cikin kalmomina da ba za ta cika ba kuwa.

An Kai Akiyora Betuliya

10 Saan nan Halofanesa ya umarci bayinsa, waɗanda ke jiran a ce musu, Ku yi, su kama Akiyora, su tafi da shi Betuliya, su danƙa shi a hannun Israilawa. 11 Sai bayin suka cafe shi, suka yi waje da shi daga zangonsu, sai suka danƙi hanyar karkara ɗoɗar, suka nufi tsaunuka, sai da suka kai maɓuɓɓugar ruwan nan ta ƙarkashin Betuliya. 12 Da mutanen garin suka hango su tafe, sai suka kwashi makamansu, suka tafi gefen dutse, sai dukan gwanayen duffa suka hana su shigewa ta wurin jifarsu da duwatsu. 13 Duk da haka sai da Assuriyawan suka kai gindin tsaunin, suka ɗaure Akiyora tam, suka bar shi nan kwance a gindin tsaunin, suka koma gun ubangijinsu.

14 Da Israilawa suka fito daga birninsu, sai suka tarar da Akiyora, suka kwance shi, suka kai shi Betuliya, suka gabatar da shi a gaban ƙusoshin garinsu, 15 waɗanda a zamanin nan su ne Azariya ɗan Mika, na kabilan nan ta Saminu, da Kabarisa ɗan Gotaniyal, da Karmisa ɗan Malkiyal. 16 Sai aka kira dukan dattawan garin. Dukan samari da mata kuma suka gaggauto zuwa gun taruwar, suka tsai da Akiyora a tsakiyar dukan jamaarsu, saan nan Azariya ya tambaye shi ainihin abin da ya faru. 16 Akiyora ya amsa, ya gaya musu abin da aka guɗanar a shawarar Halofanesa, da dai dukan abubuwan da shi Akiyora ya fada game da Israilawa a gaban jarumawan Assuriyawa, da dukan cika baki da Halofanesa ya yi, ya hurza a kan Israilawa.

18 Sai mutane suka rusuna, suka yi wa Allah sujada, suka roƙe shi, suka ce, 19 Ya Ubangiji Allah na Sama, ka dubi barancinsu fa! Ka kuma dubi ƙasƙantar da kai na jamaarmu. Ka dube mu tsarkakanka ran nan da idon rahama. 20 Saan nan suka taazanta Akiyora, suka kuma yabe shi matuƙa. 21 Sai Azariya ya ɗauke shi daga cikin taron, ya kai shi nasa gida don su shaƙata tare da dattawa. A dukan daren nan, sai suka yi ta kira Allahn Bani Israila domin ya taimaka.

7. An Kewaye Betuliya da Yaƙi

1 Kashegari sai Halofanesa ya umarci dukan sojojinsa, da dai dukan waɗanda suka zo don haɗin gwiwa, su tashi, su kai wa Betuliya hari, su kame mashigai tsakanin tsaunukan, su yaƙi Israilawa. 2 Sai dukan jarumawansu suka tashi ran nan, askarawansu duka duka dubu ɗari da dubu sabain ne na sojan ƙafa, da dubu goma sha biyu na sojan doki, tare da dawakan kaya da masu kora su, taro ne dai tasasa, ga shi nan. 3 Sai suka yi zango a kwarin nan na Betuliya, a gefen maɓuɓɓugar ruwa, suka mamaye wurin, har da suka game da Dotan har zuwa Balbayima, daga Betuliya har zuwa Kayamona, wadda ke kusa da Asdaralona.

4 Da Israilawa suka hango babban taron, sai suka tsunke da shi, saan nan kowannensu ya ce wa maƙwabcinsa, Ai, waɗannan mutane, yanzu za su lashe dukan fuskar ƙasar, ko tudu ko kwari, duk ba za su ɗauke su ba. 5 Saan nan kowa ya saɓi makaminsa, suka hura wutar ba da alama a hasumiyoyinsu, sai suka kwana suna tsaro.

6 Kashegari sai Halofanesa ya dikako sojansa na doki zuwa gun Israilawan da ke a Betuliya, 7 ya shirya yadda zai ci birnin, sai ya je rijiyoyin da mutanen garin ke shan ruwa, ya sa sojansa tsaro a gun, ya dawo gun babbar rundunar soja.

8 Saan nan dukan sarakunan Edomawa da na Mowabawa da na gaɓar teku suka ce masa, 9 Bari ubangijinmu ya saurari jawabin nan, don kada a ci sojojinsa. 10 Gama mutanen nan, wato Israilawa, ba ga māsu suke dogara ba, amma ga tsaunukansu inda suke zaune, tun da ya ke duwatsunsu ba su hawu a daɗi. 11 Saboda haka, ubangijina, kada ka yi yaƙi da su gaba da gaba, sojanka ko gudu ba zai salwanta ba. 12 Ka yi zamanka a zangonku, kai da dukan sojanka, ku sa barorinka dai kawai su tsare maɓuɓɓugar ruwa wadda ke fitowa daga gindin dutse, 13 gama can ne dukan mutanen Betuliya ke shan ruwansu. Don haka ƙishi ma kawai ne zai hallaka su, su ba da birninsu don kansu. Mu da sauran jamaarmu ma hau tuddai na kurkusa, mu yi tsaro, mu hana kowa barin garin. 14 Su da matansu da yayansu za su galabaita da yunwa. Kafin ma mu fāɗa musu da yaƙi, za su suma a garin. 15 Ta haka ne za ka saka musu da mugunta, duk sun yi maka tawaye, ba su karɓe ka da salama ba, sai sun gwammaci kiɗi a karatu.

16 Sai Halofanesa ya yi naam da waɗannan maganganu da dukan bayinsa suka gaya masa, ya umarci a yi abin da suka ce. 17 Daganan sai sojojin Mowabawa suka matsa gaba, tare da Assuriyawa dubu biyar, suka sauka a kwarin, suka gāje mashayar ruwan Israilawa. 18 Saan nan Edomawa da Ammonawa su kuma suka yi nasu zango hannun riga da Dotan a kan tsauni, suka aika da waɗansu daga cikin jamaarsu zuwa kudu da gabas, wajen Akaraba, wadda take kusa da Kusai, gab da gulbin Makamura. Sauran sojojin Assuriyawa, suka yi sansani a karkara, suka rufe fuskar dukan ƙasar, su da tantinsu, da kayansu masu yawan gaske, suka zama kasaitaccen taro.

19 Sai Israilawa suka yi roƙo ga Ubangiji Allahnsu, gama sun karaya, tun da ya ke maƙiyansu sun yi musu zobe, ba wata hanya da za su bi su sulale. 20 Sai dukan Assuriyawa da sojan dokinsu, da karusansu, da sojan ƙafa, suka hana su fita koina har kwana talatin da huɗu, sai da dukan randunan ruwansu suka ƙare ƙarƙaf tukuna. 21 Duk ruwan da suka tara ya ƙare, har suka riƙa yini da ƙishi, gama wanda kowa zai sha aunanne ne. 22 Yayansu suka karaya, matansu da samari suka fara suma saboda tsananin kishi, suka soma kwantawa a hanyar birni da kusa da ƙofofin gari, ba su ma da wani sauran ƙarfi.

23 Saan nan dukan mutane, samari, da mata, da yaya, suka taru a gaban Azariya da sarakunan birnin, suka yi kuka da kakkausar murya, suka ce wa dukan dattawa, 24 Ai, Allah ne zai sharaanta tsakaninmu da ku, Allah ya isa kuma! Gama kun cuce mu tun da kuka ƙi sulhuntawa da Assuriyawa. 25 Gama yanzu ba mu da mataimaki ko guda, Allah ma ya danƙa mu a hannunsu, ya ƙwala mu da ƙasa a gabansu ta ƙishirwa da dai matuƙar rashin ƙarfi. 26 Ku kira su yanzu, ku danƙa wa Halofanesa dukan birnin, da shi da dukan jarumawansa, su mai da mu ganima. 27 Ai, gara su kama mu, su maishe mu bayi, in an yi haka za mu rayu, ba za mu ga mutuwar yayanmu ba ƙiri ƙiri, ko ganin matanmu da yaransu suna numfashin ƙarshe na barin duniya . 28 Mun rantse da Allah na sama da ƙasa, Ubangijin kakanninmu, wanda ya hore mu gwargwadon laifofinmu da na kakanninmu, ku yi abubuwan da muka ce a wannan karo!

29 Saan nan dukan taron ya barke da kuka, suka kira ga Ubangiji Allah da babbar murya. 30 Sai Azariya ya ce musu, Ku ƙarfafa, yanuwana! Mu dai ɗaure har kwana biyar nan gaba, tukuna, zuwa wannan lokaci Ubangiji Allahnmu zai kwararo mana jinƙansa, gama ba zai yarda a hallaka mu kwatakwata ba. 31 Amma in kwanakin nan sun wuce, ba mu ga wani taimako ya zo mana ba, sai mu yi abin da kuka ce. 32 Saan nan ya sallami mutanen, ya kuwa tafi inda aka nuna masa, suka hau garu da hasumiyoyin birninsu. Da mata da yayansu, sai ya ce su tafi gida. Mutanen garin kuwa suka sha wuya ƙwarai.

8 Bayahudiya

1 A zamanin, wata mace mai suna Bayahudiya ta ji labarin waɗannan abubuwa duka, ita yar Merari ce, ɗan nan na Yusufu, ɗan Oziyel, ɗan Elkiya, ɗan Hananiya, ɗan Gidiyon, ɗan ƙafayim, ɗan Affitob, ɗan lliya, ɗan Hilkiya, ɗan Eliyab, ɗan Nataala, ɗan Salamiyel, ɗan Sarasadai, ɗan Saminu, ɗan Israila. 2 Manassa ne mijinta, wanda yake asalinsa ɗan kabilarta da danginta ne, ya mutu a lokacin yankan alkama. 3 Gama kamar yadda ya tsaya, yana shugabancin mutanen da ke ɗaurin dammuna a gona, sai zafin rana ya zauta shi, ya kwanta a gadonsa, ya mutu a birninsa na Betuliya. Suka rufe shi gab da iyayensa a filin nan na tsakanin Dotan da Balamon. 4 Bayahudiya ta yi zaman gwaurancinta a gida na shekara uku da wata hudu. 5 Sai ta kafa wa kanta alfarwar a ƙololuwar ɗakinta, ta sa tsummokinta na yin takaba. 6 Ta yi ta yin azumi a lokacin takabarta, sai dai ranar Jummaa da Asabar ne kawai ba ta yi, kafin wata ya tsaya kuma da ranar da wata ya tsaya, da ranakun bukukuwa da na jin daɗi gun Israilawa. 7 Ita kyakkyawar ya ce, fuskan nan, sai ka ce ta aljana. Mijinta, Manassa, ya bar mata zinariya da azurfa, da bayi mata da maza, da shanu da gonaki, tana kuma kula da su duka. 8 Ba wanda ya taɓa cewa ta yi abin Allah wadai, gama tana da tsoron Allah matuƙa.

Jawabinta ga Dattawa

9 Da Bayahudiya ta ji muguwar maganar da jamaa suka yi game da sarakuna a kan wahalar da suke sha ta wuyar ruwa, da dukan abin da Azariya ya ce musu, da yadda ya yi alkawarin yi, cewa a ba Assuriyawa garin bayan kwana biyar, 10 sai ta aiki baiwarta, wadda ke kula da duk abin da Bayahudiya ta mallaka, ta kira Azariya, da Kabaris, da Karmisa, dattawan birnin. 11 Suka zo gunta kuwa saan nan ta ce musu, Ku saurare ni, ya ku sarakunan jamaar Betuliya. Abin da kuka gaya wa jamaa a yau bai kamata ba ko kaɗan. Kun faɗa, har kuma kun yi rantsuwa a tsakaninku da Allah, kuna alkawarta za ku ba maƙiyanku birninku, har kuka ce sai kuwa in Ubangiji ya juyo, ya yi muku taimako a tsakanin kwana biyar. 12 Ku wanene da za ku jarraba Allah a lokacin nan, har da kuke mai da kanku kamar Allah? 13 Kuna gwada Ubangiji Allah ke nan. Ba za ku fahimci kome ba din din din? 14 Ba ku iya sanin zurfin zuciyar ɗan adam, ba ku ma sanin abin da mutum ke tunani. Ta yaya za ku iya sanin nufin Allah, wanda ya halicci dukan abu, ku san tunaninsa kuwa, ku gane abin da ya yi nufi?

Ko kadan, yanuwana, kada ma ku husatar da Ubangiji Allalmmu. 15 Gama in bai yi niyyar taimakonmu nan da kwana biyar ba, yana da ikon kāre mu duk a lokacin da ya ga dama, yana ma da ikon hallaka mu a idanun maƙiya namu in ya so yin hakanan. 16 Kada ku yi ƙoƙarin tilasta wa nufin Ubangiji Allalmmu,

Gama Allah ba mutum ba ne da za a yi ciniki da shi,
      Ko kuma ɗan adam da za a yi masa kurari.

17 Saboda haka, da ya ke kuna jiran ya fanshe ku, bari mu roƙe shi ya taimake mu, zai ji roƙonmu in ya so. 18 Gama a cikin alummarmu ta yanzu ba kabila, ko dangi, ko gari, wanda ke bauta wa yan allolin da hannun yan adam ya siffata, kamar yadda kakanninmu suka yi a zamanin dā. 19 Ai, saboda mugun abin da kakanninmu suka yi ne, aka karkashe su, aka mai da su ganima, suka sha wulakanci tsantsa a gun magabtanmu. 20 Amma, ai, mu ba mu yarda da wani allah dabam ba, banda shi ɗin nan. Saboda haka ko muna sa rai ba zai raina ƙurarmu ba, ko ta sauran alummarmu. 21 Gama in an kama mu, za a kama dukan Yahudiya ma, Haikalinmu mai tsarki kuma za a mai da shi ganima. AIlah kuwa zai saka mana daidai wa daida saboda keta haddin Haikalin da muka bari aka yi. 22 A kan yankan yanuwanmu da kama bayin yaƙi daga cikinmu, da mai da garinmu kufai—duk waɗannan zai dora mana a ka a duk wuraren da za mu yi bauta gun sauran alumma. Za a ci mana mutunci a idanun waɗanda suka kama mu. 23 Gama bautarmu ba za ta kawo mana wani alheri ba, amma Ubangiji Allah zai mai da ita cin mutunci.

24 Saboda haka yanzu, yanuwana, bari mu nuna wa yanuwanmu hanya tagari, gama su ma a gunmu ne suka dogara, Haikali mai tsarki, da Wuri Mafi Tsarki, da bagade, ai, duk hannumnu suke. 25 Ba tare da ɓata wani lokaci ba, bari mu gode wa Ubangiji Allalmmu, wanda yake gwada mu kamar dai yadda ya yi da kakanninmu. 26 Ku fa tuna, abin da ya yi wa kakanmu Ibrahim, da yadda ya gwada Ishaku, da kuma abin da ya faru da Yakubu a arewacin ƙasan nan, ta tsakanin koguna biyu, a loton da yake kiwon garken tumakin nan na Laban, kawunsa. 27 Gama bai gasa mana azaba ba, kamar yadda ya gasa musu, yana binciken zukatansu, bai ma nemi yin sakayya a kanmu ba, amma Ubangiji ya i wa waɗanda suke kusa da shi domin ya gyara halinsu.

Shawarwarin Dattawa da Bayahudiya

28 Saan nan Azariya ya amsa mata cewa, Dukan abin da kika fada, ai, wannan zahiri ne, ba rna wanda zai iya yi miki gardama a kai ko kaɗan. 19 Ai, ba yau kadɗai ba ne kika nuna hikimarki, amma tun farkon ƙuruciyarki dukan jamaa sun fara gane fahiminki, gama halin zuciyarki na gaskiya ne. 20 Amma mutane sun ƙishirta ƙwarai, sun kuma tilasta mana mu yi abin da muka alkawarta, suka sa mu muka yi rantsuwa wadda ba mu iya karyawa. 21 Don haka ki yi mana addua, tun da ya ke ke macen kirki ce, domin Ubangiji ya aiko mana da ruwan sama, mu cika rijiyoyinmu yadda ba za mu ƙara suma don ƙishirwa ba.

32 Sai Bayahudiya ta ce musu, Ku saurare ni. Zan yi wani abu wanda zai shafi dukan alummarmu, har kan tsararraki masu zuwa nan gaba. 33 Ku tsaitsaya a ƙofar gari yau da dad dare, ni zan fita tare da baiwata. A yan kwanakin da kuka alkawarta hannanta birninku ga maƙiyanmu, Ubangiji zai fanshi Israilawa ta hannuna. 34 Sai dai kada ku yi ƙokarin binciken nufina, gama ba zan faɗa muku ba, sai a lokacin da na gama tukuna.

35 Azariya da sarakuna kuwa suka ce mata, Ki sauka lafiya, Ubangiji kuma ya shirya ki domin ki ɗauko mana fansa a kan makiyanmu. 36 Saan nan dattawa suka fito daga gidanta, suka koma wurin aikinsu.

9. Adduar Bayahudiya

1 Saan nan Bayahudiya ta durkusa, ta yi hurwa da toka, ta yaye mayafin da ke bisa tsummokin da ta daura. A lokacin ne da ake ƙona turaren magariba a ɗakin sujada a Urushalima, Bayahudiya ta yi kuka ga Allah da babbar murya, ta ce, 2 Ya Ubangiji Allah na kakana Saminu, kai ne ka ba Saminu takobi don ya yi ramuwa kan baƙin da suka ɓata budurcin Dinatu, suka birkice mata buje don su kunyata ta, suka ɓata ta, ko da ya ke kai ne ka ce kada a yi haka, amma duk da haka, suka yi. 3 Saboda haka ka bayar da sarakunansu, aka yanyanka, bar gadajen da suka aikata abin kunya a kai suka jiƙe da jininsu. Kai ne ka kashe bayi tare da sarakuna, har ko suka fāɗi a bisa junansu. 4 Kai ne ka ba da matansu su zama ganima, yayansu kuma bayin yaƙi, dukan ganimar dukiya kuma, aka raba ta a tsakanin ƙaunatattunka, masu kishinka, masu ƙin saɓon da aka yi wa yaruwarsu, waɗanda suka nemi taimakonka.

5 Ya Allah, Allahna, ni ma ka saurare ni mana, da ya ke ni gwauruwa ce. Gama kai ne ka yi waɗannan abubuwa duk, da mafarinsu da Rarshensu. Kai ne ka ƙaddara abubuwan da ke akwai yanzu, har ma da masu zuwa nan gaba. 6 I, ai, duk abubuwan nan da ka nufa sun auku yadda ka nufa. 7 Ai, abubuwan da ka ƙaddara su ne suke gabatar da kansu, suke cewa, Ka duba, ai, ga mu nan gun. Gama kai mai gama aiki ne tun bai zo ba, duk ka san ƙaddararka sarai, ba sai wani ya sa maka a baka ba.

7 Ai, ga shi ma, Assuriyawa, sai ƙara haɓaka suke yi, suna harbin iska don ƙarfi saboda dawakansu da mahayansu, suna taƙama da sojansu na ƙafa, sun amince da garkuwoyinsu da māsunsu, a kan bakansu da majajjawansu, amma sun mance

8 Kai ne ke Ubangiji wanda ke ragargaje yaƙi,
      Ai, sunanka Ubangiji.

Ka ɓarke ƙarfinsu ta ikonka, ka ƙaskanta ikonsu da fushinka, gama sun yi nufin lalata wurinka mafi tsarkin nan, su kuma ɓata Haikalin nan mai tsananin ɗaukaka inda zatinka yake, wai har ma suna son sare zankayen da ke kusurwoyin bagadenka da takobi. 9 Ka dubi alfarman nan tasu fa, ka kwararo musu da fushinka bisa kansu. Amma ni da nake gwauruwan nan, ka ba ni ƙarfin da zan yi abin da na nufa. 10 Ta daɗin bakina ka sare bawa da sarki, bar su fāɗi a bisa junansu, ka karya alfarmarsu ta hannun mace.

11 Gama ikonka ba da yawan mutane ba ne, haka ma ƙarfinka ba sai a nuna kaurin cinya ba, gama kai Allah ne na ƙasƙantattu, kai mataimakin wadanda aka matsa wa ne, matokarar musakai, makiyayin gajiyayyu, fatar marasa fata.

12 Ka saurare ni, wayyo Allah, ka saurare ni! Allah na kakana, Allahn da Israilawa suka gāda, Ubangijin sama da ƙasa, Mahaliccin ruwaye, kai ne sarkin dukan halittarka, ka ji adduata mana! 13 Ka sa daɗin bakina ya raunata su, ya kai su mahalaka, tun da suka gina ramin mugunta, a game da yarjejeniyarka, har ma a game da ginin nan naka tsarkakakke, da tsaunin nan kuma na Sihiyona, da dai gidajen nan ma na yayanka. 14 Ka sa dukan alummarka da dukan kabilanta su tabbatar da cewa kai ne Allah, Allah na dukan iko da ƙarfi, saan nan kuma ba wani wanda ke kiyaye jamaar Israilawa, sai kai kaɗai.

10. Bayahudiya ta Tafi

1 Da Bayahudiya ta gama kukanta ga Allahn Israilawa, da adduar da ta yi, 2 sai ta tashi daga inda ta gurfana, ta kira baiwarta, suka shiga gidan da take zama a ranar Asabar da ranakun idi, 3 sai ta kwance tsummokin da ta ɗaura, da kayan nan na takabarta, ta yi wanka, ta shafe jikinta tsaf da mai mai ƙanshin gaske, ta tsefe gashin kanta, ta kitse gashin kanta da zaren alharini, ta sa kayanta na ado waɗanda takan sa a lokacin da mijinta, Manassa, ke da rai. 4 Ta sa takalmanta na taka tsara, ta sa mundayenta da zobbanta, ta sa yan kunnenta da dukan kayan adonta, ta dai tsabtace jikinta tsaf, domin ta ɗauke hankalin dukan mazan da za su gan ta.

5 Ta ɗora wa baiwarta kwalabar barasa da ɗan tulun man zaitun, ta cika yar jakarta da soyayyen riɗi, da waina, da burodi, da cuku, ta dai lulluɓe dukan kayan, ta ɗora wa baiwar.

6 Sai suka fita ƙofar garin Betuliya, suka tarar da Azariya tsaye da sauran dattawan garin, wato Kabaris da Karmisa. 7 Da dai suka yi arba da ita, suka ga yadda fuskarta da tufafinta suke ɗaukar ido, sai ta sheƙe su saboda kyanta, har suka ce mata, 8 Da ma dai Allahn kakanninmu ya yi miki alheri, ya i miki da nufinki, domin mutanen Israilawa su bunƙasa, a kuma ɗaukaka garin nan na Urushalima.

Sai ta bauta wa Allah. 9 Saan nan ta ce musu, Ku umarta a buɗe mini ƙofar garin wadda ke kulle, ni kuwa zan tafi in cika abubuwan nan da muka yi magana a kai, ni da ku. Sai suka umarci waɗansu samari su buɗe mata ƙofar, kamar dai yadda ta roƙa. 10 Da suka gama yin haka, Bayahudiya ta fita, da ita da baiwarta, sai mazan garin suka yi ta kallonta tana gangarawa, sai da ta ɓace wa ganinsu.

An Kama Bayahudiya

11 Bayahudiya da baiwarta suka miƙe ɗodar, suka bi ta kwarin, sai rundunar sojan Assuriyawa suka yi kaciɓis da ita, 12 suka kama ta, suka ce mata, To, ke yar wace kabila ce, daga ina kuma kika fito yanzu, ina za ki?

Sai ta kada baki, ta ce, Ni yar Ibraniyawa ce, amma yanzu gudu nake yi daga gunsu, gama ba da daɗewa ba za a ba ku su, ku hallaka su. 13 Yanzu gun babban shugaban Assuriyawa Halofanesa, za ni, don in gaya masa ainihin gaskiya, zan ma nuna masa hanyar da zai bi domin kamo dukan gundumomin tsaunukan nan, ba tare da sojansa ko ɗaya ya salwanta ba, a kama ko a yanke.

14 Da mutanen suka ji ta faɗi haka, suka dubi fuskarta─ai, kyanta har ya wuce wuri─sai suka ce mata, 15 Ai, kuwa kin gwada arziki da kika yi hanzari nan gun ubangijinmu. Maza maza ki tafi tantinsa, bari ma waɗansunmu su taka miki su kai ki gunsa. 16 In an kai ki gabansa, kada ma ki ji tsoron korne, amma ki maimaita masa abin nan dai da kika ce ɗazu, zai kuwa yi miki alheri. 17 Sai suka zaɓi mutum ɗari daga cikinsu, suka raka ta, ita da baiwarta, suka kai su har tantin Halofanesa.

18 Sai aka yi ta taruwa a sansani duka, gama duk an bi wuri wuri an farfaɗi isowarta. Sai maza suka zo duk, suka kewaye ta a loton da aka tafi a faɗa wa Halofanesa zuwanta. 19 Suka fa yi ta mamakin kyanta, suna shaawar Israilawa saboda ita, har kowa ya ce wa maƙwabcinsa, Haba, wa ke iya raina alumman nan mai kyawawan mata irin waɗannan haka? Ai, don haka kada mu bar ko dayansu da rai, gama in mun ƙyale su haka, za su jawo hankalin dukan duniya ma.

Bayahudiya ta Shiga gun Halofanesa

20 Saan nan matsaran Halofanesa da dukan bayinsa suka fito, suka marabce ta a zauren tanti. 21 Halofanesa na kwance, yana hutawa a ƙarƙashin laima tasa mai launin jar garura, wadda aka saka da zinariya, da safifa, da dajiyar duwatsu masu daraja. 22 Da suka ba shi labarinta, ya zabura sai zauren tantin, bayinsa suna riƙe masa fitilun zinariya. 23 Da Bayahudiya ta zo gaban Halofanesa da bayinsa, sai duk suka yi mamakin irin kyan fuskarta. Ta durƙusa, sai bayinsa suka miƙar da ita tsaye.

11

1 Saan nan Halofanesa ya ce mata, Kada ki damu, uwargida, kada ki karaya ko kaɗan, gama ni ban taɓa wulakanta duk mai son yi wa Nebukadnezzar hidima ba, da ya ke sarkin dukan duniya ne shi. 2 Ai, koyanzu ma, da mutanenki da ke zaune kan tsaunukan nan ba su tone ni ba, ba zan fara ɗaga musu ƙwala ba, amma duk su ne suka ja wannan da kansu. 3 To, yanzu ki gaya mini dalilin da ya sa kika baro su, kika zo nan gunmu, tun da ya ke kin kawo matsera. Sa ranki a inuwa, ba abin da zai taɓa ki, daga daren yau har zuwa gaba. 4 Ba wanda zai yi miki wani lahani, amma za a yi miki goma sha tara ta arziki, kamar dai yadda ake yi wa dukan bayin ubangijina sarki Nebukadnezzar.

5 Bayahudiya ta ce masa, Ka yarda da abin da baiwarka za ta gaya maka, bari baiwarka ta yi magana a gabanka, ba ruɗin ubangijina zan yi ba da maraicen nan. 6 In ma ka bi abin da zan gaya maka, Ialle kuwa Allah zai aikata alajabi ta kanka, ba ma za ka kasa ci ma burinka ba. 7 Ai, sarkin dukan duniya, Nebukadnezzar, na zaune dafaan a kan gadon mulki, yana kuma riƙe da ragamar mulki kankan, shi ne ya aiko ka ka shugabanci kowane mai rai, haka ma dabbobin dawa, da na gida, da tsuntsayen sama dai, duk waɗanda za su wanzu a ƙarƙashin jagorancin Nebukadnezzar da dukan gidansa. 8 Gama mun ji labarin gwanintarka da hazikancinka duka, an ma sanar da dukan duniya, cewa a dukan ƙasar, Halofanesa, ba mutumin kirki irinka, mai ɗumbun sani, mai iya shirin yaƙi, ga faɗa kamar zuma.

9 Yanzu mun ji jawabin da Akiyora ya yi a mashawartarku. Saad da mutanen Betuliya sun bar shi da rai, ya kuma sanar musu duk abin da ya gaya maka. 11 Saboda haka, ya ubangijina, maigidana, don Allah, kada ka raina duk abin da ya ce, amma ka riƙe abin a zuci, gama gaskiya ne. Ba za a hori alummarmu ba, ai, ba ma za a nufe su da takobi ba, sai dai in sun yi wa Allahnsu zunubi. 10 Amma yanzu, kada a ci ubangijina, murnarsa ta koma ciki, garna yanzu zunubi ya ɗauke musu hankali, sun sa Allah ya husata ta saɓonsu. Za a kashe su, 11 gama abincinsu ya ƙare, ruwan shansu ma yanzu sauran na ɗora rai, sun yi shirin yanka dabbobinsu, su kuma ci dukan abin da Allah ya hana su su ci. 12 Sun yi shawarar auka wa hatsin tumun fari, da barasa, da mai waɗanda suka keɓe wa firist da ke yin hidima a gaban Allahnmu can Urushalima, ko da ya ke haram ne ga mutanen, su tattaɓa waɗannan abubuwa da hannuwansu. 13 Sun aika da mutane zuwa Urushatima, gama waɗanda ke zaune a can sun taɓa cin keɓaɓɓen abinci, su ma. Mutanen Betuliya suna jiran a ba su izni daga dattawan Urushalima tukuna. 14 Da iznin ya iso, za su auka wa abincin nan da nan. A ranan nan ne kuwa za a bangaza su a hannunka, ka hallaka su.

16 Don haka ne ma, da ni baiwarka na ji dukan wannan magana, sai na gudu daga gunsu, Allah ne ya kawo ni, ya haɗa ni da kai, domin ni da kai mu yi waɗansu abubuwa da za su ba dukan duniya mamaki, iyakar dai dukan wanda zai ji abin nan da aka yi. 17 Gama baiwarka mai ibada ce, tana yi wa Allah na Sama hidima dare da rana. Don haka, haba ubangijina, ai, gunka ne zan zauna, amma kowane dare sai baiwarka ta gangara kwari, ta riƙa roƙon Allah. Shi ne zai gaya mini in sun yi zunubin nan nasu. 18 Saan nan in dawo, in gaya maka, ka fita, kai da dukan jarumawanka. Ai, ba za su iya karawa da kai ba. 19 Saan nan zan bi da kai ta tsakiyar Yahudiya, sai mun gama da Urushalima tukuna, in kafa maka gadon sarauta a tsakiyarta, sai ka bi da su kamar dai tumakin da ba su da makiyayi, ba kuwa karen da zai buɗe baki, ya yi maka gumani. Gama an sanar mini da haka ta sanina na abin da zai je, ya zo ne, aka faɗakar da ni, don haka aka turo ni in zo in gaya maka.

20 Sai kalaminta ya shere Halofanesa duk da bayinsa, har suka yi mamakin hikimarta, suka ce, 21 Kai, wannan ya, ai, ba irinta daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ga dai kyan fuska da kuma tsabar hikima ta magana!

22 Sai Halofanesa ya ce mata, Amma dai mun gode wa Allah da ya turo mana ke daga mutanenki, domin ki ƙarfafa mu mu hallaka waɗanda suka toni ubangijina. 23 Ba kyan fuska kawai ke gare ki ba, amma kina da hikimar magana ma, bugu da ƙarfi, in dai kika aikata abin da kika ce, to, Allalinki zai zama Allahna, za ki kuma zauna a gidan Nebukadnezzar, ki sanu a dukan duniya.

12

Saan nan ya umarce su su kai ta inda aka ajiye akusansa na zinariya, ya ce kuma su shirya mata gara ta abinci mai daɗi irin nasa, su kuma ba ta irin giyarsa, ta ci ta sha. 2 Amma Bayahudiya ta ce, Ai, ba na cinsa ko kaɗan, don ba na so in keta haddi, amma abin da na kawo ya ishe ni, in ci in sha.

3 Sai Halofanesa ya ce mata, In naki ya ƙare fa, ina za mu je mu samo miki irinsa? Gama ba ko guda daga cikin mutanenki a nan garin.

4 Bayahudiya ta ce, Allah ya ja zamaninka, ya ubangijina, ai, baiwarka ba za ta ƙarar da abin da ke hannunta ba kafin Ubangiji ya cika abubuwan da ya nufa aikatawa ta hannunta.

5 Saan nan bayin Halofanesa suka kawo ta a cikin tantinsa, ta yi ta sharar barcinta, sai da tsakar dare ta yi. Wajen asubar fari sai ta tashi, 6 ta aika gun Halofanesa, ta ce, Bari yanzu ubangijina ya umarta a bar baiwarsa ta fita ta yi addua.

7 Sai Halofanesa ya umarci matsaransa kada su hana ta fita. Ta yi ta zamanta a sansam bar kwana uku, a kowane dare sai ta gangara kwarin nan na Betuliya, tana yin wanka a maɓuɓɓugar ruwa ta kwarin da sansanin yake. 8 Da ta fito daga maɓuɓɓugar kwarin sai ta yi addua ga Ubangiji Allahn Israilawa yadda zai craga alummarsa. 9 Sai ta yi kwalliya, ta dawo, ta shiga tantin, ta zauna can, sai an kawo mata abincinta na magariba.

Liyafar Halofanesa

10 A rana ta huɗu sai Halofanesa ya shirya wata ƙasaitacciyar liyafa saboda bayinsa kawai, bai ma gayyaci ko ɗaya daga cikin jarumawansa ba. 11 Sai ya ce wa Bagauda dandaƙaƙƙcen nan wanda ke da iko a bisa dukan mallakarsa, Je ka yanzu, ka rarraso Baibraniyan nan ta zo nan, mu ci mu sha tare. 12 Ai, abin kunya ne in irin wannan mace tana nan, ba mu kuma more ta ba, gama in ba mu ruɗe ta ba, za a yi mana dariya.

13 Sai Bagauda ya fita daga gaban Halofanesa, ya tarye ta, ya ce mata, Wannan kyakkyawar baiwa, don Allah, ki zo gun ubangijina. Ai, za a girmama ki, ki zo, ki ci ki sha, ki yi murna tare da mu. Ai, a yau ɗin nan za a mai da ke kamar ɗaya daga cikin yan matan nan na Assuriyawa waɗanda ke yin hidima gaban Nebukadnezzar a gidansa.

14 Sai Bayahudiya ta ce, Wace ni in ƙi abin da ubangijina ya ce? Ai, ni duk abin da yake faranta masa rai, shi ne zan yi, da hanzari kuwa. Abin kuwa zai faranta mini rai har ran da na mutu.

15 Sai ta miƙe tsaye, ta yi dai wani tsatsetsen ado, irin na taka tsara, sai baiwarta ta shiga gabanta, ta shimfiɗa mata waɗansu dardumu da Bagauda ya ba ta don ta yi amfani da su kowace rana, ta riƙa kwantawa a kai lokacin da take cin abinci. 16 Sai Bayahudiya ta zo, ta kwanta. Saan nan zuciyar Halofanesa ta kaɗa, ransa ya biya, ya yi ta tsima, yana begen ya kwana da ita, gama dā ma jira yake kawai ya ruɗe ta tun ma a ranar da ya fara ganinta. Ai, ya so yin haka. 17 Sai Halofanesa ya ce mata, To, ki sha mana, ki kuma yi farin ciki da mu nan!

18 Bayahudiya ta ce, Ai, yanzu kuwa, ya ubangijina, gama tun da aka haife ni ban taɓa yin farin ciki kamar yau ba. 19 Saan nan ta ɗauki abincin nan da baiwarta ta shirya mata, ta ci ta sha. 20 Sai Halofanesa ya ji daɗinta kwarai da gaske, ya sha giya, ya yi tatil, irin ma wadda bai taɓa sha ba, tun da aka haife shi.

13

1 Da yamma ta yi, sai bayinsa suka fita nan da nan. Saan nan Bagauda ya rufe ƙofar tantin daga waje, ya kori sauran bayi daga gaban maigida nasu, suka tafi, suka kwanta, kowa ya rungume tabarma, gama sun gaji, da ya ke an daɗe ana kwaɗar gara da giyar liyafar. 2 Sai aka bar Bayahudiya ita kaɗai a tantin, da Halofanesa kwance bisa kan gadonsa gototo, gama ya sha ya bugu. 3 Amma a loton, Bayahudiya ta gaya wa baiwarta ta jira a bakin ƙofa, bar ta fita waje, kamar dai yadda ta saba yi kowace rana, gama ta ce za ta fita ta yi addua. Haka kuma ta gaya wa Bagauda shi ma.

An Fille Kan Halofanesa

4 Sai kowa ya fita waje, ba sauran kowa, babba ko yaro, ba dai kowa a ɗakin kwana. Saan nan Bayahudiya ta tsaya gefen gadonsa, ta ce a zuciyarta, Ya Ubangiji Allah na dukan iko, a yanzu hakanan ka dubi aikin hannuwana ta yadda za a ɗaukaka Urushalima. 5 Gama yanzu ne lokacin da za ka taimaki magadanka, ni dai ka idar mini da nufina in hallaka maƙiyanmu da suka taso mana.

6 Sai ta tafi gun turken gadon kwanciyar a bisa kan Halofanesa, ta zare takobinsa da ya rataye a can. 7 Ta matso kusa da gadonsa, ta ja tukkun nan nasa, ta ce, Ka ba ni ƙarfi a wannan loto, ya Ubangiji Allah na Israilawa! 8 Sai ta yi ta dafka wa wuyansa sara har sau biyu da dukan ƙarfinta, har da ta fille masa wuya. 9 Saan nan ta mirgine gawar ƙasa daga kan gadon, ta kuma hargitsar da laiman nan tasa. Da aka ɗan jima kaɗdan, sai ta fita waje, ta miƙa wa baiwarta kan Halofanesa. 10 Ita kuwa ta jefa kan a burgamin nan na abincinta. Saan nan sai su biyu suka fita waje gaba ɗaya, kamar dai yadda suka saba tafiya gun yin adduan nan.

An Koma Betuliya

Sai suka bi ta sansanin, suka kukkurɗa ta kwarin nan, suka haye tsauni, suka nufi Betuliya, har suka kai ƙofofin garin.

11 Sai Bayahudiya ta kirayi matsaran garin tun daga nesa da ƙofar garin, ta ce, Kai, ku buɗe, ku buɗe ƙofar mana! Allah, Allahn nan namu, wanda ke tare da mu bar yanzu, yana nan yana nuna ikonsa a Israila da ƙarfin nan nasa a kan maƙiyanmu, kamar dai yadda ya gama yi ɗazun nan.

12 Da mutanen garin suka ji muryarta, sai suka hanzarta, suka isa ƙofar garin, suka kira dattawan birnin. 13 Duk suka garzayo a guje, babba da yaro, gama ba su gaskata ta dawo lami lafiya ba. Sai suka buɗe mata ƙofa, ta shiga, suka kuma kunna fitila don su ga haske, suka kewaye su, ita da baiwan nan tata.

14 Saan nan ta yi musu magana da kakkausar murya, ta ce, Ku yabi Ubangiji, ku yabe shi kwarai! Ku yabi Allah, wanda bai janye jinƙan nan nasa daga gidan Israila ba, amma ya hallaka maƙiyanmu ta hannuna ɗazu dazun nan ma kuwa. 15 Saan nan ta zaro kan daga cikin burgamin, ta nunnuna musu, ta ce musu kuma, Kai, duk ku duba, ga kan Halofanesan nan, babban jarumin sojan Assuriyawan nan, ga kuma laiman nan wadda yake yin rigingine a ƙarƙashinta in ya sha ya yi tatil. Ubangiji ya kashe shi ta hannun mace. 16 Na rantse da Ubangiji mai rai wanda ya raka ni, ya kuma kiyaye ni a inda na je ɗin nan. Shi ne mai shaidata. Fuskata ce ma ta ruɗi Halofanesa, har ta kai shi ga mahalaka, amma duk da haka bai ma sami damar kwana da ni ba, don kada ya lalata ni.

17 Sai mamaki ya rufe dukan mutane, suka gurfana, suka bauta wa Allah. Saan nan suka ce ga baki daya,

Albarka ta tabbata ga Allahn nan namu,
      Wanda ya kasƙanta maƙiyan mutanensa yau yau ɗin nan.
18 Sai Azariya ya ce mata,
Ke wannan ya, Allah Madaukaki ya sa miki albarka
      Fiye da kowaɗanne mata a nan duniya.
Yabo kuma ga Ubangiji Allah wanda ya halicci sama da ƙasa,
      Ya kuma bi da ke har kika sare kan shugaban maƙiyanmu.
19 Ai, mutane ma ba za su mance da wannan babban aiki naki mai kawo sa zuciya  ba,
      A duk lokacin da za su ba da labarin ikon Allah.
20 Allah ya sa a girmama ki kullayaumin,
      Saboda aikin da kika yi,
A kuma sa miki albarka a kai a kai,
      Gama kin sai da ranki a lokacin da ake ƙasƙanta alummarmu,
Kin kāre mu daga masifa,
      Kin kuma yi tafiya ba karkacewa a gaban Allahnmu.

Sai dukan mutane suka ce, Amin, amin.

14. Nasihar Bayahudiya

1 Saan nan Bayahudiya ta ce musu, Ku saurara dai, yanuwana, ku ɗauki kan nan, ku rataye shi a kan zankayen nan ta katangarku. 2 Kāna da gari ya waye, rana ta fito, bari kowane jarumi ya ɗauki makamansa, ya fita, ya tsaya, ya sa shugaba a kowane sashi, ku shirya dai kamar za ku tafi karkara ku kai wa Assuriyawa hari, sai dai kada ku tafi. 3 Saan nan Assuriyawan za su kwaso makamansu su shiga tantuna, su ta da shugaban sojansu, nan da nan kuwa za su kutsa kai a tantin Halofanesa, ba kuwa za su tarar da shi ba. Saan nan tsoro zai rufe su, har ma su ce muku, ku zo mu je. 4 Da ku da dukan waɗanda ke zaune a kan iyakar Israila za ku bi su kuna fallewa kamar rama. 5 Amma kafin ku aikata haka, ku kawo mini Akiyora Baamnoniye tukuna, domin ya gani, ya kuma sansance kan nan na Halofanesa ne wanda ya raina gidan Israila, har ya aiko shi Akiyora gunmu, wai don ya mutu tare da

Akiyora ya Ga Alamarin

6 Sai suka kira Akiyora daga gidan Azariya. Da dai ya fito, sai ya hango kan Halofanesa a hannun ɗaya daga mutane cikin taron, sai ya fāɗi rigingine don tsananin mamaki. 7 Da suka miƙar da shi tsaye kuma, sai ya fāɗa kan ƙafafun Bayahudiya, ya durƙusa a gabanta, ya ce mata, Mai albarka ce ke a kowane gida na Yahudiya! A kowace alumma duk wanda ya ji sunanki zai yi mamaki. 8 Yanzu sai ki gaya mini abubuwan da kika yi a yan kwanakin nan.

Sai Bayahudiya ta bayyana masa duk abin da ta yi dalla dalla a gaban dukan jamaa, tun daga ranar da ta bar gida, har zuwa wannan lokaci da take magana da su. 9 Da ta gama bayani, sai mutane suka yi wata irin gunza, suna kakabin murna a birninsu.

10 Da Akiyora ya ga dukan abubuwan da Allah na Israilawa ya yi, sai ya gaskata sosai ga Allah, nan take kuma aka yi masa kaciya, ya zama Baisraile, haka yake har kwanan gobe.

Assuriyawa sun Razana

11 Da asubar fari ta keto, sai suka rataye kan Halofanesa a kan katanga, kowane jarumi kuma ya saɓi makamansa, suka fita ƙungiya ƙungiya zuwa gefen kan tsaunukan. 12 Da Assuriyawa suka hango su, sai suka aiko da saƙo zuwa ga shugabanninsu, sai shugabannin ɗin suka isa gun shugaba, da waɗanda ke bisansu, da dai dukan shugabanninsu. 13 Sai suka tafi tantin Halofanesa, suka ce wa bawan da ke kula da alamuran gidan Halofanesa, Ka tasar mana da maigidanmu, gama bayin nan sun tasar mana, har sun auka mana da yaƙi, domin a hallaka su kwatakwata. 14 Sai Bagauda ya tafi, ya ƙwanƙwasa ƙofar tantin, gama ya tsammaci suna kwance, da Halofanesa da Bayahudiyan nan. 15 Amma tun da ya ke bai ji kowa ba, sai ya buɗe ƙofar dakin kwanan, ya kutsa kai ciki, ya kuwa tarar da shi kwance a ƙasa matacce, ga shi kuma, an fille kan, sai gangar jiki a tsibe. 16 Sai ya tashi kwance kwance, ya fasa makoki, ya kuma kyakkece tufafinsa. 17 Ya kuma zabura zuwa tantin da Bayahudiya ke zama. Da bai same ta a gun ba, sai ya yiwo waje da gudu, ya yi wa mutanen magana da kakkausar murya, ya ce, 18 Ai ku, bayin nan sun yi mana zamba cikin aminci! Wata mace, Baibraniya, ta keta haddin gidan sarki Nebukadnezzar. Ku duba, yanzu ga gawar Halofanesa nan shinƙinƙin a ƙasa, an ma fille masa kai!

19 Da shugabannin sojan Assuriyawa suka ji haka, sai suka yayyage taguwoyinsu, suka razana ƙwarai, suka cika sansani nasu da koke‑koke.

15

1 Da mutane a sansani suka ji abin da ya faru, sai suka yi mamaki matuƙar gaske. 2 Sai tsoro da razana suka rufe su, don haka har ba wanda ya tsaya jiran wani, amma kowannensu ya bazama zuwa kwari da tsauni. 3 Sojan Assuriyawa da aka ajiye a kewayen Betuliya su ma suka gudu suka tsere. Saan nan Israilawa, kowannensu da ke aikin soja, ya wanke hannu, ya auka wa Assuriyawa.

An Fafari Assuriyawa

4 Sai Azariya ya baza maaika, waɗdansu zuwa Betomasayim, waɗansu zuwa Koba, da Kona, da dukan gundumar Israilawa, su sanar da kowa abubuwan da suka faru, a fito a auka wa maƙiya domin a hallaka su. 5 Da fa Israilawa suka ji abin nema ya samu, duk gaba ɗaya sai suka yiwo kukan kura, suka auka wa abokan gaba, suka rarrake su, har da suka kai su Koba. Na Urushalima da na kan tsaunukan nan duk, sai da suka gama a gun, gama an sanar musu da abin da ya faru a sansanin maƙiyansu. Da waɗanda ke Gileyad da na Galili, duk dai suka taru, suka yi wa Assuriyawan mugun kisan gaske, har bayan birnin Dimashƙu da kan iyakarta. 6 Sauran mutanen Betuliya suka auka wa tantunan Assuriyawa, suka mai da su ganima, suka kuwa arzuta ƙwarai da gaske. 7 Israilawan da suka dawo daga yaƙin, suka gāje sauran abin da ya ragu, har aka ciccika ƙauyuka, da birane na tsaunuka, da karkara da ganima isasshiya, gama dukiya dai, ga ta nan koina a jibge.

8 Saan nan Yowakima, babban firist, da sauran ƙusoshin Israilawa da ke zaune a Urushalima, suka zo su shaida manyan abubuwan da Ubangiji ya yi wa Israilawa su ga Bayahudiya, su kuma gaishe ta. 9 Da suka gan ta, sai suka sa mata albarka ga baki daya suka ce,

Ai, ke ce ɗaukakar Urushalima,
      Ke ce ma darajar Israilawa,
Abin fariya ga alummarmu!
10 Kin aikata abubuwan nan da hannunki,
      Kin yi wa Israilawa babban alheri.
Allah ma ya yi naam da hakanan.
      Ubangiji Mai Iko Dukka ya sa miki albarka har abada!

Sai dukan mutane suka ce, Amin, amin dai!

11 Dukan mutane suka yi ta kwasar ganima har kwana talatin. Sai suka ba Bayahudiya tantin Halofanesa, da dukan akusansa na zinariya, da gadajensa, da tasoshinsa, da dai dukan kayan da ke ɗakinsa, sai ta kwashe su kaf, ta dankara wa alfadaranta, ta tafi da su.

12 Saan nan dukan Israilawa mata suka taru domin su gan ta, su kuma sa mata albarka, har waɗansunsu ma suka yi mata rawa da waƙa. Sai Bayahudiya ta ɗauki waɗansu rassa, ta ba matan nan da ke tare da ita, 13 sai kowaccensu ta yi wa kanta rawani da ganyen zaitun, da ita da waɗanda ke tare da ita. Ta kuma shugabanci rawar, tana gaban dukan matan. Israilawa maza na binsu a baya, riƙe da makamansu, suna rataye da furanni, suna rawa, suna sheƙa waƙa.

Waƙar Bayahudiya

14 Saan nan Bayahudiya ta fara yin godiya ga Allah a gaban dukan Israilawa. Dukan mutanen ma gaba ɗaya da babbar murya sai suka yi waƙar yabon Allah tare da ita. Ga abin da Bayahudiya ta fada.

ɓ16

1 Ku soma yi wa Allahna waƙa da tambura,
      Ku yi wa Ubangijina yabo da kuge.
Ku raira masa sabuwar waƙa mana,
      Ku ɗaukaka shi, ku kuma kira bisa sunansa.
2 Gama Allah shi ne Ubangiji, maganin yaƙe-yaƙe,
      Ya ma kafa mazauninsa a tsakiyar jamaarsa,
      Ya kuɓutar da ni daga hannun masu wawarata.

3 Gama Sarkin Assuriyawa daga tsaunukan arewa ya gangaro,
      Ya kawo mutanensa masu ɗumbun yawa.
Babban taronsu suka shaƙe kwari,
      Sojansu na dawakai suka mamaye tsaunuka.
4 Gama ya yi kurari, cewa zai ƙone dukan gundumar ƙasata,
      Ya kashe samarina da sara da takobi,
Sai ya dauki yayana, ya ƙwala da ƙasa,
      Ya kama yarana, ya mai da su bayi
      Ya kwashi yan matana, ya mai da su ganima.

5 Amma Ubangiii Mai Iko Dukka ya cukwikwiye su gu ɗaya,
      Ya ƙasƙantar da su ta hannun ya mace.
Gama mai ƙarfin nan nasu ba a cukwikwiye shi ta hannuwan samari ba.
      Ai, ƙattin nan ba su kwala shi da ƙasa ba,
      Ko manyan jarumawa ma ba su auka masa ba.
Amma Bayahudiyan nan, yar wajen Merari ce,
      Ta i masa ta wurin yawan kyan fuskarta.
Gama ta tuɓe tufafinta na takaba,
      Domin ta ɗaukaka dannannun Israilawan nan dai.
Ta shafe fuskartafayau da mai,
      8 Ta kitse gashin kanta da zaren alharini,
Ta yi ado da tufatin yauƙi domin ta burma shi.
      9 Takalmanta sun ɗauke idonsa,
Kyanta ya sheƙe shi sarai,
      Takobi kuwa ya fille masa kai.

10 Sai mulanen Farisa suka yi ta tsalle,
      Suna faɗar ƙarfin halinta,
      Mediyawa suka riƙe bakinsu a kan mazakutar da ta yi.
11 Saan nan dannannun mutanena suka ɗau ihu,
      Abokan gāba kuwa suka firgita.
Kumamaina suka yi gaza,
      Abokan gāba kuwa suka durƙusa.
Mutanena suka daka tsawa,
      Abokan gāba kuwa suka ranta cikin na kare.
12 Yayan bayi mata ne ma suka sassoke su,
      Yayan tawaye suka rarraunata su,
      Aka hallaka su a gaban sojan Ubangijina.

13 Ai, dole in raira wa Allahna sabuwar waƙa.
      Ya Ubangiji, ai, kai mai girma ne da ɗaukaka,
      Mai tsananin iko, ba mai iya karawa da kai.
14 Ka sa dukan halittunka su yi maka hidima,
      Gama magana kawai ka yi, sai suka wanzu.
Kai ne ka aiko da nurnfashinka, ka halitta su kuwa,
      Ai, ba mai iya yin jayayya da kalmarka.
15 Gama ko da aka jijige gindin tsaunuka da zurfin tekuna,
      Ko da duk duwatsu sun narke a  gabanka, sai ka ce ƙankara,
      Ga masu tsoronka za ka nuna jinƙai.

16 Gama kowace irin hadaya mai ƙanshi ƙaramar aba ce,
      Haka ma hadayun ƙonawa masu kitse,
      Amma duk mai tsoron Ubangiji, shi ne mai girma har abada.
17 Kaiton alumman da suka auka wa mutanena!
      Ubangiji Mai Iko Dukka ne, zai saka musu a ranar sharia.
Wuta da tsutsotsi ne zai sa su cinye su,
      Za su yi ta ƙuna a cikin azaba har abada.

An Yi wa Allah Godiya a Urushalima

18 Da jamaa suka iso Urushalima, sai suka bauta wa Allah. Nan da nan da aka tsarkake mutanen, sai suka miƙa hadayun ƙonawa, da na sa kai, da dai waɗansu sauran kyautai. 19 Sai Bayahudiyan nan ta sadaukar da dukan kayan da aka kwaso a gidan Halofanesa, waɗanda jamaa suka ba ta, da laimar da ta ɗauko a gaban gadonsa, duk dai ta haɗa, ta bayar hadaya ga Ubangiji. 20 Sai mutane suka yi ta biki a gaban wurin nan tsattsarka a Urushalima har watanni uku. Bayahudiya kuma tana nan gunsu.

Shaharar Bayahudiya

21 Bayan haka, sai kowa ya korna gidan iyayensa. Bayahudiya kuma, sai ta koma Betuliya, ta je ta zauna a gidansu. A zamaninta aka ɗaukaka ta kuwa ƙwarai da gaske a koina. 22 Mutane da dama suka yi burin su aure ta, amma sai ta yi zaman gwauranci bayan mijinta Manassa ya mutu, an rufe shi kusa da danginsa. 23 Sai ta yi ta tsufa a gidan mijinta na dā, har da ta yi shekara ɗari da biyar. Ta mutu kuma a garin Betuliya, suka rufe ta a kogon nan na mijinta Manassa. 24 Israilawa kuwa suka yi mata makoki na kwana bakwai. Ba ta mutu ba sai da ta rarrabar da kayan da ta mallaka, ta ba dangin mijinta Manassa da nata dangi kuma, har ma ta yanta baiwarta.

25 Ba wanda ya taɓa kawo Israilawa wani hari a zamanin Bayahudiya, har ma bayan mutuwarta da daɗewar gaske.

*      *      *      *      *
*      *      *
*