Daniel
1A shekara ta uku ta mulkin Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo Urushalima ya kewaye ta da yaƙi. 2Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.
3Sa'an nan Sarkin Babila ya umarci sarkin fādarsa, Ashfenaz, ya zaɓo masa waɗansu samari daga cikin Yahudawa, waɗanda ke daga gidan sarauta, da kuma daga gidan manya, 4su kasance samari ne kyawawa, waɗanda ba su da wata naƙasa, masu fasaha cikin kowane abu, masu fahimta, da masu saurin ganewa, waɗanda suke da halin iya hidima a fādar sarki. Nebukadnezzar ya umarci Ashfenaz ya koya musu littattafan Kaldiyawa da harshen Kaldiyawa. 5Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima. 6A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza. 7Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.
8Daniyel kuwa ya ƙudura a ransa, ba zai ƙazantar da kansa da cin abinci iri na sarki da shan ruwan inabinsa ba, don haka ya roƙi sarkin fāda, kada ya ba shi wannan abinci da zai ƙazantar da shi. 9Allah kuwa ya sa Daniyel ya sami farin jini da soyayya a wurin sarkin fāda. 10Sa'an nan sarkin fāda ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoro kada shugaban sarki wanda ya umarta a riƙa ba ku wannan abinci da ruwan inabi ya ga jikinku ba su yi kyau kamar na samarin tsaranku ba, ta haka za ku sa in shiga uku a wurin sarki.”
11Sai Daniyel ya ce wa baran da sarkin fāda ya sa ya lura da su Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, 12“Ka jarraba barorinku har kwana goma. A riƙa ba mu kayan lambu mu ci, a kuma riƙa ba mu baƙin ruwa mu sha. 13Sa'an nan ka duba fuskokinmu da na samari waɗanda ke cin abinci irin na sarki. Ka yi da barorinku gwargwadon yadda ka gan mu.”
14Ya yarda da abin da Daniyel ya ce, ya kuwa jarraba su har kwana goma ɗin. 15A ƙarshen kwana goma ɗin, sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da ke cin abinci irin na sarki. 16Don haka baran ya janye shirin ba su abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.
17Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.
18Sa'ad da lokacin da sarki ya ƙayyade ya ƙare, sarkin fāda ya gabatar da su a gaban Nebukadnezzar. 19Da sarki ya yi magana da su, sai ya tarar a cikinsu duka, ba wani kamar Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya. Don haka aka maishe su 'yan majalisar sarki. 20A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda ke cikin mulkinsa har sau goma. 21Daniyel kuwa ya ci gaba har shekarar farko ta sarki Sairus.
1Nebukadnezzar ya yi mafarki a shekara ta biyu ta sarautarsa, ya kuwa damu ƙwarai har barci ya gagare shi. 2Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki. 3Sarki kuwa ya ce musu, “Na yi mafarki, na kuwa matsu ƙwarai in san mafarkin.”
4Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.”
5Sai sarki ya amsa wa Kaldiyawa, ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini da mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa gunduwa, a mai da gidajenku juji. 6Amma idan kun tuna mini mafarkin, duk da fassararsa, to, zan ba ku lada, da kyautai, da girma mai yawa. Don haka sai ku faɗa mini mafarkin, duk da fassararsa.”
7Suka amsa, suka ce, “Bari sarki ya faɗa wa barorinsa mafarkin, mu kuwa za mu yi maka fassararsa.”
8Sarki kuwa ya amsa ya ce, “Na sani kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin kun ga na manta da abin. 9Idan ba ku tuno mini da mafarkin ba, hukuncin kisa ne ke jiranku. Kun haɗa kai don ku yi mini maganganun ƙarya na wofi har lokaci ya wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”
10Sa'an nan Kaldiyawa suka amsa wa sarki, suka ce, “Ba wani mahaluki a duniya wanda zai iya biyan wannan bukata ta sarki, gama ba wani sarki wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya a wurin mai sihiri, ko mai dabo, ko Bakaldiye. 11Abin nan da sarki ke so a yi masa yana da wuya, ba wanda zai iya biya wa sarki wannan bukata, sai dai ko alloli waɗanda ba su zama tare da 'yan adam.”
12Saboda haka sarki ya husata ƙwarai, ya umarta a karkashe duk masu hikima na Babila. 13Sai doka ta fita cewa a karkashe masu hikima. Aka nemi Daniyel da abokansa don a kashe su.
14Daniyel kuwa ya amsa wa Ariyok, shugaban dogaran sarki, a hankali da hikima, sa'ad da Ariyok ya fita don ya karkashe masu hikima na Babila. 15Daniyel ya ce wa Ariyok shugaban dogaran sarki, “Me ya sa ake gaggauta dokar sarki haka?” Sai Ariyok ya bayyana wa Daniyel yadda al'amarin yake.
16Sa'an nan Daniyel ya shiga wurin sarki, ya roƙe shi ya ba shi lokaci domin ya yi masa fassarar. 17Sai Daniyel ya tafi gidansa, ya sanar wa abokansa, wato su Hananiya, da Mishayel, da Azariya da al'amarin. 18Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila. 19Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daganan Daniyel ya yabi Allah na Sama.
20Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin, Wanda hikima da iko nasa ne.
21Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,
22Yana bayyana zurfafan abubuwa masu wuyar ganewa, Ya san abin da ke cikin duhu. Haske kuma yana zaune tare da shi.
23A gare ka nake ba da godiya da yabo, ya Allah na kakannina, Gama ka ba ni hikima da iko, Har ka sanar mini da abin da muka roƙe ka, Ka sanar mana da matsalar da ta dami sarki.”
24Sa'an nan Daniyel ya tafi wurin Ariyok wanda sarki ya sa ya karkashe masu hikima na Babila, ya ce masa, “Kada ka karkashe masu hikima na Babila, ka kai ni gaban sarki, ni kuwa zan yi wa sarki fassarar.”
25Nan da nan kuwa Ariyok ya kai Daniyel gaban sarki, ya ce masa, “Na sami wani daga cikin kamammun ƙasar Yahuza wanda zai iya sanar wa sarki da fassarar.”
26Sarki kuwa ya ce wa Daniyel, mai suna Belteshazzar, “Ka iya faɗa mini mafarkin duk da fassararsa?”
27Daniyel ya amsa wa sarki, ya ce, “Ba masu hikima, ko masu dabo, ko masu sihiri, ko masu duba, da za su iya su warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi. 28Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.
29“Ya maigirma, sa'ad da kake kwance a gadonka sai tunanin abin da zai faru nan gaba ya zo maka. Shi kuma wanda ke bayyana asirai ya sanar da kai abin da zai faru nan gaba. 30Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka.
31“Ya sarki, ka ga wani babban mutum-mutum mai walƙiya, mai bantsoro, yana tsaye a gabanka. 32An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla. 33Da baƙin ƙarfe aka yi sharaɓansa, an yi ƙafafunsa da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu. 34Sa'ad da kake cikin dubawa, sai aka gutsuro wani dutse ba da hannun mutum ba, aka bugi ƙafafunsa na baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, aka ragargaza shi. 35Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.
36“Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu faɗa wa sarki fassararsa. 37Ya sarki, kai ne sarkin sarakuna wanda Allah na Sama ya ba ka sarauta, da iko, da ƙarfi, da daraja. 38A hannunka kuma ya ba da dukan wurare inda 'yan adam, da dabbobi, da tsuntsaye suke zama. Ya sa ka ka mallake su duka. Kai ne kan zinariyan nan na mutum-mutumin. 39A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya. 40Za a kuma yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar baƙin ƙarfe. Da ya ke baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, hakanan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki. 41Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin ƙarfe da ke gauraye da yumɓu. 42Kamar yadda yatsotsin ƙafafun rabi baƙin ƙarfe, rabi kuma yumɓu ne, hakanan mulkin zai kasance, rabi da ƙarfi, rabi kuma da gautsi. 43Kamar yadda ka ga baƙin ƙarfen ya gauraya da yumɓun, hakanan mulkokin za su gauraye da juna ta wurin aurayya, amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa. 44A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada. 45Kamar yadda ka ga an gutsuro dutse ba da hannun ɗan adam ba, ya kuwa ragargaje baƙin ƙarfen, da tagullar, da yumɓun, da azurfar, da zinariyar, Allah Maɗaukaki ya sanar wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin tabbatacce ne, fassarar kuma gaskiya ce.”
46Sarki Nebukadnezzar kuwa ya fāɗi a gaban Daniyel, ya gaishe shi, sa'an nan ya umarta a miƙa hadaya, da hadaya ta turare ga Daniyel. 47Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” 48Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda ke Babila. 49Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.
1Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda ke a lardin Babila. 2Sa'an nan ya aika a kirawo su hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna, su zo, su halarci bikin keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. 3Sai hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna suka taru don keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Suka kuma tsaya a gaban gunkin. 4Mai shela ya ta da murya da ƙarfi, ya ce, “An umarce ku, ya ku jama'a, da al'ummai, da harsuna mabambanta, 5cewa sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi, ku yi sujada ga gunkin zinariyan nan da sarki Nebukadnezzar ya kafa. 6Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.” 7Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.
8A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa. 9Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ranka ya daɗe. 10Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya. 11Duk wanda bai faɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta. 12Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”
13Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki. 14Nebukadnezzar ya ce musu, “Ko gaskiya ne, wai kai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego ba ku bauta wa allolina ba, ba ku kuma yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa ba? 15Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga kowanene allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
16Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari. 17Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki. 18Ko ma bai cece mu ba, ka sani fa ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka, ko kuma mu yi wa gunkin zinariya da ka kafa sujada ba.”
19Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā. 20Sa'an nan ya umarci waɗansu ƙarfafan mutane daga cikin sojojinsa su ɗaure Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, su jefa su a tanderun gagarumar wuta. 21Sai aka ɗaure su suna saye da rigunansu da wandunansu, da hulunansu, da sauran tufafinsu, aka jefa su a tanderun gagarumar wuta. 22Tsananin umarnin sarki ya sa aka haɓaka wutar, sai harshen wutar ya kashe waɗanda suka jefa su Shadrak, da Meshak, da Abed-nego cikin wutar. 23Sa'an nan mutanen nan uku, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka faɗi a tanderun gagarumar wuta a ɗaure.
[Ga ƙari a Littafin Daniyel a sura ta 3 tsakanin aya ta 23 da 24]
1 Da aka watsa samarin cikin tanderu mai gagarumar wuta, sai suka yi ta rawa a tsakiyar wutar, har suka raira waƙar yabon Allah, suna girmama Ubangiji. 2 Sai Azariya ya tashi tsaye, ya yi wannan addua a tsakiyar wuta. Ga abin da va ce:
3 Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji,
Allah na kakanninmu,
Ka ma cancanci yabo,
I, sunanka kuma ɗaukakakke ne har abada.
4 Gama kai mai adalci ne a dukan abubuwan da ka yi,
Dukan ayyukanka suna da gaskiya.
Hanyoyinka kuma ba su da aibu,
Ai, dukan shariunka na zahiri ne.
5 Shariar da ka yi mana, ai, duk ta gaskiya ce,
Haka ma wadda ka yi wa Urushalima,
Wato tsarkakakken birnin nan na kakanninmu.
Bisa ga gaskiya da adalci ne ka auko duk wannan abu a
kanmu saboda zunubanmu.
6 Ai, ta zunubanmu da ƙin manufa ne muka bauɗe maka,
Mun yi saɓo a kowane abu.
Ba mu yi biyayya da dokokinka ba,
7 Ba mu bi su ba, ko mu kiyaye abin da suka ce,
Wanda ka umarce mu mu zauna lami lafiya.
8 Don haka duk abin da ka jibgo mana
Da wanda duk ka yi mana,
Ai, da adalci da gaskiya ne ka yi.
9 Ka ba da mu a hannun magabtan da ba su san abin da ya kamata ba,
Ranmu, ko kaɗan, bai kwanta da su ba.
Ka danƙa mu a hannun mugun sarki,
Duk duniyan nan, ba wanda ya kai shi ƙeta.
10 Yanzu ba mu iya ko buɗe bakinmu,
Kunya da ƙasƙanci sun auka wa bayinka, masu yi
maka bauta.
11 Don darajar sunan nan naka,
Kada ka ba da mu kwatakwata,
Kada ma ka zare yarjejeniyarka.
12 Kada ma ka janye jinƙanka daga gunmu,
Saboda Ibrahim ƙaunataccenka,
Da kuma Ishaku bawanka,
Da mai tsarkin nan naka, Israila,
13 Waɗanda ka yi alkawari ta kansu, cewa
Jikokinsu za su yi yawan gaske kamar taurarin sama,
Har su yi yawan rairayin da ke bakin teku.
14 Gama mu yanzu, ya Ubangiji, mun fi sauran alumma salwanta,
An ma yi mana ƙasƙanci kwanan nan a dukan duniya
Saboda zunubanmu ne kuwa.
15 A wannan lokaci ma ba mu da sarki, ko annabi, ko shugaba,
Ba hadayar ƙonawa, ko wata irin hadaya, ko sadaka, ko
turaren ƙonawa,
Ba gun da za a miƙa hadaya a gabanka, ko neman
jinƙai.
16 Duk da haka, don muna da karyayiyyar zuciya da ruhun tuba,
Ai ka karɓe mu.
17 Kamar dai yadda ka karɓi hadayun ƙonawa na raguna da na bijimai,
Da kuma na yayan raguna masu kiɓa dubbai bisa
dubbai,
Haka ma ka karɓi hadayarmu ta yau,
Domin muna binka sau da ƙafa.
Gama duk wanda ya dogara gare ka,
Ko kadan ba zai kunyata ba.
18 Yanzu mun bi ka da dukan zuciya,
Kanmu ƙasa, hannumnu baya, muna neman fuskarka.
19 Kada ka sa mu mu kunyata,
Amma ka rufa mana asiri ta haƙurinka,
Da kuma yawan jinƙanka.
20 Ka fanshe mu ta ayyukanka na alajabi,
Ka kuma sa a ɗaukaka sunanka, ya Ubangiji.
21 Ka sa duk waɗanda suka nufi su yi wa bayinka lahani, su kunyata,
Ka sa a ƙasƙanta su a hana su dukan iko da
mulki,
Ka kuma buge musu gwiwoyi.
22 Ka sa su sani kai ne Ubangiji, Allah Makadaici,
Wanda dukan duniya ke ɗaukakawa.
23 Lokacin da Azariya ke yin adduan nan, bayin sarkin da suka angaza su a wutar, ba su daina zuba wa wutar farar wuta, da baƙin mai, da yayi, da faskare ba. 24 Sai harshen wutar ya hau daga tanderu, har kamu arbain da tara. 25 Ta haɓaka, ta lashe Kaldiyawa waɗanda ke kewaye gagarumar wutar. 26 Amma wani malaikan Ubangiji ya gangara cikin tanderun tare da Azariya da abokansa, ya kori wuta daga tanderun. 27 Sai ya mai da tsakiyar tanderun kamar iska mai sanyi, ya zama har wutar ba ta taɓa su ba ko kaɗan, ba ta yi musu lahani ko wahala ba. 28 Saan nan su uku, da murya ɗaya, sai suka raira waƙa ga Allah, suka girmama shi, suka yabe shi a tsakiyar tanderun. Ga abin da suka ce:
29 Yabo ya tabbata gare ka, Ya Ubangiji Allah na kakanninmu,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
30 Yabo ya tabbata a gare ka, Sunanka mai tsarki yana da daraja,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
31 Yabo ya tabbata gare ka a Haikalin ɗaukakarka mai tsarki,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
32 Yabo ya tabbata gare ka, a bisa kursiyinka,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
33 Yabo ya tabbata gare ka, Wanda ke zaune a bisa kerubobi,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo ya tabbata gare ka, Mai duba zurfin duniya,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
34 Yabo ya tabbata gare ka a sararin sama,
A yabe ka, a girmama ka har abada.
35 Ku yabi Ubangiji, ku ayyukan Ubangiji duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
36 Ku yabi Ubangiji, ku malaikun Ubangiji duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
37 Ku yabi Ubangiji, ku sammai da birbishin ƙasa,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
38 Ku yabi Ubangiji, ku ruwaye birbishin duniya,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
39 Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin Allah,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
40 Ku yabi Ubangiji, ku rana da wata masu haske,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
41 Ku yabi Ubangiji, ku taurarin sama duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
42 Ku yabi Ubangiji, ku tsattsafi da raɓa duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
43 Ku yabi Ubangiji, ku iska da hadiri duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
44 Ku yabi Ubangiji, ku gumi da wuta duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
45 (Ku yabi Ubangiji, ku rani da damuna duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
46 Ku yabi Ubangiii, ku raɓa da ruwan sama duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.)
47 Ku yabi Ubangiji, ku jaura da sanyi duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
48 Ku yabi Ubangiji, ku ƙankara da dusan ƙanƙara duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
49 Ku yabi Ubangiji, ku dare da rana duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
50 Ku yabi Ubangiji, ku haske da duhu duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
51 Ku yabi Ubangiji, ku walkiya da girgije duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
52 Ku yabi Ubangiii, ku duniya duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
53 Ku yabi Ubangiji, ku duwatsu da tuddai duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
54 Ku yabi Ubangiii, ku mabunƙusa ƙasa duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
55 Ku yabi Ubangiji, ku maɓuɓɓugan ruwa duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
56 Ku yabi Ubangiii, ku tekuna da koguna duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
57 Ku yabi Ubangiji, ku kifaye manya da ƙanana,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
58 Ku yabi Ubangiji, ku tsuntsayen sama duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
59 Ku yabi Ubangiii, ku dabbobin duniya duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
60 Ku yabi Ubangiji, ku yan adam duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
61 Ku yabi Ubangiii, ku Israilawa duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
62 Ku yabi Ubangiji, firistocin Ubangiji duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
63 Ku yabi Ubangiji, ku bayin Ubangiji duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
64 Ku yabi Ubangiji, ku masu halin adalci duka,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
65 Ku yabi Ubangiji, ku tsarkaka masu sanyin hali
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
66 Ku yabi Ubangiji, Hananiya, da Azariya, da Mishayel,
Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
Gama ya ƙwato mu daga lahira,
Ya fanshe mu daga mutuwa,
Ya kuɓutar da mu daga gagarumin tanderu duk da
azabarta.
67 Ku yi wa Ubangiji godiya, gama shi mai alheri ne,
Jinƙansa ma yana ɗorewa har abada,
68 Ku yabi Allah da ke bisa alloli duka,
Ku yabe shi, ku yi masa godiya,
Gama jinƙansa yana ɗorewa har abada abadin.
24Sarki Nebukadnezzar kuwa ya zabura ya miƙe tsaye, cike da mamaki. Ya ce wa manyan fādawansa, “Ashe, ba mutum uku ne muka jefa a wuta ba?” Su kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ba shakka, haka yake, ranka ya daɗe.”
25Sarki ya ce, “Amma ina ganin mutum huɗu a sake, suna tafiya a tsakiyar wuta, ba kuma abin da ya same su, kamannin na huɗun kuwa kamar na ɗan alloli.”
26Nebukadnezzar fa ya matso kusa da ƙofar tanderun gagarumar wuta, ya ce, “Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, bayin Allah Maɗaukaki, ku fito, ku zo nan!” Sai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka fita daga cikin wutar. 27Sa'an nan su hakimai, da wakilai, da muƙaddasai, da manyan 'yan majalisa suka taru, suka ga lalle wutar ba ta yi wa jikunan mutanen nan lahani ba, gashin kawunansu bai ƙuna ba, tufafinsu ba su ci wuta ba, ko warin wuta babu a jikinsu.
28Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai. 29Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, “‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.”
30Sa'an nan sarki ya ƙara wa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego girma a lardin Babila.
1“Daga sarki Nebukadnezzar zuwa ga dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta waɗanda ke zaune a duniya duka. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! 2Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.
3“Alamunsa da girma suke! Al'ajabansa da bantsoro suke! Sarautarsa ta har abada ce, Mulkinsa kuma daga zamani zuwa zamani ne.
4“Ni, Nebukadnezzar ina cikin gidana, ina nishaɗi a fādata. 5Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni. 6Don haka na umarta a kirawo mini dukan masu hikima na Babila don su yi mini fassarar mafarkin. 7Sai masu sihiri, da masu dabo, da Kaldiyawa, da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya yi mini fassararsa ba. 8Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce, 9“‘Ya Belteshazzar shugaban masu sihiri, tun da ya ke na san ruhun alloli tsarkaka yana a cikinka, ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga mafarkin da na yi, sai ka faɗa mini fassararsa.
10“‘Wahayin da na gani ke nan sa'ad da nake kwance a gadona. Na ga wani itace mai tsayi ƙwarai a tsakiyar duniya.
11Itacen ya yi girma, ya ƙasaita, Ƙwanƙolinsa ya kai har sama, Ana iya ganinsa ko'ina a duniya.
12Yana da ganyaye masu kyau Da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.
13“‘A cikin wahayin da na gani sa'ad da nake kwance a gado, sai ga wani mai tsaro, tsattsarka, ya sauko daga sama. 14Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.
15Amma a bar kututturen da saiwoyinsa a ƙasa Ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. A bar shi can cikin ɗanyar ciyawar saura, Ya jiƙe da raɓa, Ya yi ta cin ciyawa tare da namomin jeji.
16A raba shi da hankali irin na mutane, A ba shi irin na dabba. Zai zauna a wannan hali har shekara bakwai.
17Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki ke sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.”
18“‘Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.”
19Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka. 20Itacen nan da ka gani wanda ya yi girma, ya ƙasaita, ƙwanƙolinsa ya kai sama, har ana iya ganinsa daga ko'ina a duniya, 21yana da ganyaye masu kyau da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci, namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, tsuntsaye kuma suka zauna a rassansa, 22kai ne wannan itace, ya sarki. Ka yi girma, ka ƙasaita. Girmanka ya kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko'ina a duniya. 23Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.
24“Ga ma'anarsa, ya sarki, wannan ƙaddara ce wadda Maɗaukaki zai aukar wa shugabana sarki da ita. 25Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne ke sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama. 26Kamar yadda aka umarta a bar kututturen itacen da saiwoyinsa, hakanan za a tabbatar maka da sarautarka sa'ad da ka gane Mai Sama ne ke mulki. 27Saboda haka, ya sarki, sai ka karɓi shawarata, ka daina zunubanka, ka yi adalci. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulakantawa, watakila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”
28Wannan duka kuwa ya sami sarki Nebukadnezzar. 29Bayan wata goma sha biyu, sa'ad da yake yawatawa a kan benen fādar Babila, 30sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”
31Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta. 32Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne ke sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”
33Nan take sai abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar ya tabbata. Aka kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, akaifunsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
34“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.
35Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, “‘Me kake yi?”
36“A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. 'Yan majalisata da fādawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā. 37Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”
1Sarki Belshazzar ya yi wa dubban manyan mutanensa liyafa, ya kuwa sha ruwan inabi a gabansu. 2Da Belshazzar ya kurɓa ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezzar ubansa ya kwaso daga Haikali a Urushalima, domin sarki, da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa su sha ruwan inabi da su. 3Sai suka kawo tasoshin zinariya da na azurfa waɗanda aka kwaso daga cikin Haikali, wato Haikalin Allah a Urushalima. Sai sarki da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa, suka yi ta sha da su. 4Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse.
5Nan da nan sai yatsotsin hannun mutum suka bayyana, suka yi rubutu a kan shafen bangon fādar sarkin, wanda ke daura da fitila. Sarki kuwa yana ganin hannun sa'ad da hannun yake rubutu. 6Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna. 7Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” 8Sai dukan masu hikima na sarki suka shigo, amma ba wanda ya iya karanta rubutun balle ya faɗa wa sarki ma'anarsa. 9Belshazzar sarki fa ya firgita ƙwarai, fuskarsa ta turɓune, fādawansa duk suka ruɗe.
10Da sarauniya ta ji maganganun sarki da na manyan fādawansa, sai ta shiga babban ɗakin da ake liyafar, ta ce, “Ran sarki, ya daɗe! Kada ka firgita, kada kuma fuskarka ta turɓune. 11Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba. 12Yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.”
13Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda ubana ya kawo daga Yahuza? 14Na ji labari, cewa kana da ruhun alloli tsarkaka, da fahimi, da ganewa, da mafificiyar hikima. 15Yanzun nan aka kawo mini masu hikima, da masu dabo don su karanta wannan rubutu, su kuma bayyana mini ma'anarsa, amma sun kāsa faɗar ma'anar rubutun. 16Amma na ji ka iya fassara, ka kuma iya warware al'amura masu wuya. Idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya bayyana mini ma'anarsa, to, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin mulkin ƙasar.”
17Daniyel kuwa ya amsa, ya ce wa sarki, “Riƙe kyautarka, ka ba wani duk da haka zan karanta wa sarki rubutun, in kuma bayyana masa ma'anarsa.
18“Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba. 19Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani. 20Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. 21Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne ke sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
22“Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba. 23Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
24“Domin haka Allah ya aiko da wannan hannu da ya yi rubutun nan. 25Wannan shi ne rubutun da aka yi, MENE, MENE, TEKEL, da UPHARSIN. 26Ma'anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare. 27Ma'anar TEKEL ita ce an auna ka a ma'auni, aka tarar ka kāsa. 28Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”
29Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.
30A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa. 31Dariyus kuwa Bamediye ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.
1Dariyus ya ga ya yi kyau ya naɗa muƙaddas guda ɗari da ashirin a dukan mulkinsa. 2Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome. 3Sai Daniyel ya shahara fiye da sauran shugabannin, da su muƙaddasan, domin yana da nagarin ruhu a cikinsa. Sarki kuwa ya shirya ya gabatar da shi kan dukan mulkin. 4Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci. 5Sai mutanen nan suka ce, “Ba za mu sami Daniyel da laifin da za mu kama shi da shi ba, sai dai ko mu neme shi da laifi wajen dokokin Allahnsa.”
6Sa'an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe! 7Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da 'yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki. 8Yanzu, ya sarki, sai ka tabbatar da dokar, ka sa hannu, don kada a sāke ta, gama dokar Mediya da Farisa ba a soke ta.” 9Sai sarki Dariyus ya sa hannu a dokar.
10Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda ke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.
11Sai mutanen nan suka tafi, suka iske Daniyel yana kai koke-kokensa da roƙonsa ga Allahnsa. 12Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?” Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.”
13Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”
14Sa'ad da sarki ya ji wannan magana, sai ransa ya ɓaci ƙwarai, sai ya shiga tunani ta yadda zai yi ya kuɓutar da Daniyel. Ya yi ta fama har faɗuwar rana yadda zai yi ya kuɓutar da shi. 15Sai waɗannan mutane suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ka sani fa ya sarki, doka ce ta Mediya da Farisa, cewa ba dama a soke doka ko umarni wanda sarki ya kafa.”
16Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.” 17Sai aka kawo dutse aka rufe bakin kogon, sarki kuwa ya hatimce shi da hatiminsa, da hatimin fādawansa, don kada a sāke kome game da Daniyel. 18Sarki ya koma fādarsa, ya kwana yana azumi, bai ci abinci ba, ya kuma kāsa yin barci.
19Gari na wayewa, sai sarki ya tashi, ya tafi da gaggawa wurin kogon zakoki. 20Da ya zo kusa da kogon da Daniyel yake, sai ya ta da murya ya yi kira da damuwa, ya ce wa Daniyel, “Ya Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta masa kullum, yana da ikon cetonka daga zakoki?”
21Sai Daniyel ya ce wa sarki, “Ran sarki ya daɗe! 22Allahna ya aiko mala'ikansa ya rufe bakunan zakoki, ba su iya yi mini lahani ba, domin ban yi wa Allah laifi ba, ban kuma yi maka ba.”
23Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa. 24Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.
25Dariyus sarki kuwa ya rubuta wa dukan jama'a da al'ummai, waɗanda ke zaune a duniya duka, ya ce, “Salama ta yalwata a gare ku. 26Ina umartar mutanen da ke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel, Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami, Sarautarsa ba ta tuɓuwa, Mulkinsa kuma madawwami ne.
27Yakan yi ceto, yakan kuma kuɓutar, Yana aikata alamu da mu'ujizai a sama da duniya. Shi ne wanda ya ceci Daniyel daga bakin zakoki.”
28Daniyel kuwa ya bunƙasa a zamanin mulkin Dariyus da na Sairus mutumin Farisa.
1A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa'ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa. 2Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku. 3Sai manyan dabbobi huɗu iri dabam dabam suka fito daga cikin tekun. 4Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.
5“Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, “‘Tashi ki cika cikinki da nama.”
6“Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.
7“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma. 8Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”
9“Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa. Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara, Gashin kansa kamar uku ne tsantsa, Kursiyinsa harshen wuta ne, Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne.
10Kogin wuta yana gudu daga gabansa. Dubun dubbai suna ta yi masa hidima, Dubu goma sau dubu goma suka tsaya a gabansa, Aka kafa shari'a, aka buɗe littattafai.
11“Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon ke hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone. 12Sauran dabbobi kuwa aka karɓe mulkinsu, amma aka bar su da rai har wani ƙayyadadden lokaci.
13“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.
14Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”
15“Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni. 16Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda ke tsaye a wurin, na tambaye shi ma'anar waɗannan abubuwa duka. Sai ya bayyana mini, ya kuma ganar da ni ma'anar waɗannan abubuwa. 17Waɗannan manyan dabbobi guda huɗu, sarakuna ne huɗu waɗanda za su taso a duniya. 18Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.
19“Sai na nemi in san ainihin ma'anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. 20Na kuma so in san ma'anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda da ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.
21“Ina dubawa ke nan sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka har ya rinjaye su, 22sai da Tun Fil Azal ya zo ya yanke shari'a, aka ba tsarkaka na Maɗaukaki gaskiya. Da lokaci ya yi aka ba tsarkaka mulkin.
23“Ga abin da ya ce, “‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta. 24Ƙahonin nan goma kuwa, sarakuna goma ne waɗanda za su taso daga cikin mulkin. Sa'an nan wani sarki zai taso a bayansu wanda zai bambanta da sauran da suka fara tasowa, zai kā da sarakuna uku. 25Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari'a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi. 26Amma majalisa za ta zauna ta yanke shari'a, za a karɓe mulkinsa, a hallaka shi har abada. 27Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.”
28“Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al'amarin duka a zuciyata.”
1A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari. 2A wahayin sai na gani ina a bakin kogin Ulai a Shushan, masarautar lardin Elam. 3Da na ta da idanuna, sai na ga rago a tsaye a gāɓar kogin. Yana da ƙaho biyu dogaye, amma ɗaya ya ɗara ɗaya tsawo. Wanda ya ɗara tsawon shi ne ya tsiro daga baya. 4Na ga ragon ya kai karo wajen yamma da wajen kudu, da wajen arewa. Ba wata dabbar da ta iya karawa da shi, ba wanda kuma zai iya kuɓuta daga ikonsa, ya yi yadda ya ga dama, ya ɗaukaka kansa.
5Sa'ad da nake cikin tunani, sai ga bunsuru ya ɓullo daga wajen yamma, ya ratsa dukan duniya, ba ya ko taɓa ƙasa. Akwai ƙaho na gaske a tsakanin idanunsa. 6Sai ya zo wurin ragon, mai ƙahoni biyu, wanda na gani a tsaye a gāɓar kogi. Bunsurun kuwa ya tasar masa da fushi mai zafi. 7Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, sai ya gabza wa ragon karo. Ya kakkarya ƙahonin nan nasa biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, ba ya iya kare kansa daga bunsurun. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun. 8Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.
9Wani ƙarami ƙaho kuma ya tsiro daga cikin ɗayansu, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai. Ya nuna ikonsa wajen gabas, da wajen kudu, da wajen ƙasa mai albarka. 10Ya ƙasaita, har ya kai cikin rundunar sama. Ya jawo waɗansu taurari zuwa ƙasa, ya tattake su. 11Ya ɗaukaka kansa, har ya mai da kansa daidai da shugaban runduna. Ya hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga Sarkin sarakuna, ya kuma rushe masa wuri mai tsarki. 12Saboda zunubi sai aka ba da runduna duk da hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara.
13Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da ke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da ke lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”
14Ya ce mini, “Sai an yi kwana dubu biyu da ɗari uku, sa'an nan za a mai da wuri mai tsarki daidai da yadda yake a dā.”
15Sa'ad da ni Daniyel, na ga wahayin, ina so in gane, sai ga wani kamar mutum ya tsaya a gabana. 16Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra'ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.” 17Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki. Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”
18Sa'ad da yake magana da ni, sai barci mai nauyi ya kwashe ni da nake kwance rubda ciki, amma sai ya taɓa ni, ya tashe ni tsaye. 19Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe.
20“Ragon nan mai ƙaho biyu da ka gani, sarakunan Mediya ne da na Farisa. 21Bunsurun kuwa Sarkin Hellas ne. Babban ƙahon nan da ke tsakanin idanunsa shi ne sarki na farko. 22Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al'ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba.
23“A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito. 24Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi. 25Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba. 26Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”
27Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.
1A shekara ta fari ta sarautar Dariyus ɗan Ahazurus Bamediye wanda ya ci sarautar Kaldiyawa, 2a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.
3Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka. 4Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba. Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda ke kiyaye dokokinka.
5“Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka. 6Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa. 7Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda ke kusa da waɗanda ke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka. 8Ya Ubangiji kunya ta rufe mu, mu da sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, saboda mun yi maka zunubi. 9Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa. 10Ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ta wurin kiyaye dokokinsa ba, waɗanda ya ba mu ta hannun bayinsa annabawa. 11Dukan Isra'ilawa sun karya dokokinka, sun kauce, sun ƙi bin maganarka. La'ana da rantsuwa waɗanda ke a rubuce cikin dokokin Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi. 12Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba. 13Kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, haka wannan bala'i ya auko a kanmu, duk a haka ba mu nemi jinƙan Ubangiji Allahnmu ba, ba mu daina aikata muguntarmu ba, ba mu lizimci gaskiyarka ba. 14Domin haka Ubangiji ya shirya bala'i, ya kuma aukar mana da shi, gama Ubangiji Allahnmu mai adalci ne cikin dukan abin da ya aikata, amma mu ba mu bi maganarsa ba.
15“Ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama'arka daga ƙasar Masar da iko mai girma, da haka ka bayyana ikonka kamar yadda yake a yau, amma mun yi zunubi, mun aikata mugunta. 16Ya Ubangiji, saboda dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hasalarka da ka yi da birninka Urushalima, tsattsarkan tudunka. Gama saboda zunubanmu da muguntar kakanninmu, Urushalima da jama'arka sun zama abin ba'a ga waɗanda ke kewaye da mu. 17Yanzu ya Allahnmu, ka ji addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Sabili da sunanka da idon rahama ka dubi tsattsarkan wurinka wanda ya zama kango. 18Ya Allahna, ka karkato kunnenka ka ji, ka buɗe idanunka ka ga yadda mu da birnin da ake kira da sunanka muka lalace. Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roƙe-roƙenmu ba, amma saboda yawan jinƙanka. 19Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”
20Sa'ad da nake ta addu'a, ina faɗar zunubina, da na jama'ata Isra'ila, ina kawo roƙe-roƙena wurin Ubangiji Allahna saboda tsattsarkan tudun Allahna. 21Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice. 22Ya zo, ya ce mini, “Ya Daniyel, na zo ne don in ba ka hikima da ganewa. 23A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.
24“An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali. 25Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara. 26Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Naɗaɗɗe, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara. 27Wannan shugaba zai yi alkawari mai ƙarfi na shekara bakwai da mutane da yawa. Amma bayan shekara uku da rabi za a hana a yi sadaka da hadaya. Abin ƙyama zai kasance a ƙwanƙolin Haikali, har lokacin da ƙaddara za ta auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”
1A shekara ta uku ta sarautar Sairus Sarkin Farisa, sai aka aiko da saƙo wurin Daniyel, wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar. Saƙon kuwa gaskiya ne, ya shafi zancen yaƙi, Daniyel kuwa ya fahimci saƙon.
2A waɗannan kwanaki, ni Daniyel, ina fama da baƙin ciki har mako uku. 3A makon nan uku ban ci wani abincin kirki ba, balle nama ko shan ruwan inabi, ban kuma shafa mai ba.
4A rana ta ashirin da huɗu ga watan fari, ina tsaye a gāɓar babban kogin Taigiris. 5Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa. 6Jikinsa kamar lu'ulu'u yake, fuskarsa kamar walƙiya, idanunsa kuma kamar harshen wuta, hannunwansa da ƙafafunsa kuwa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kamar ta babban taron jama'a.
7Ni kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da ke tare da ni ba su ga wahayin ba, sai dai babbar razana ta auko musu, har suka gudu, suka ɓuya. 8Aka bar ni, ni kaɗai, na ga wannan babban wahayi, ni kuwa ba ni da sauran ƙarfi. Fuskata ta sauya, ta turɓune, ba ni da sauran ƙarfi. 9Sa'an nan na ji muryarsa, da jin muryarsa, sai na faɗi rubda ciki, barci mai nauyi ya kwashe ni.
10Sai hannu ya taɓa ni, ya tashe ni, sa'an nan hannuwana da gwiwoyina suna ta kaɗuwa. 11Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.
12Sai ya ce mini, “Kada ka ji tsoro, Daniyel, gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu'arka, amsar addu'arka ce ta kawo ni. 13Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa. 14Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”
15Sa'ad da ya faɗa mini wannan magana, na sunkuyar da kaina ƙasa, na yi shiru, ba magana. 16Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda ke tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi. 17Ƙaƙa zan iya magana da kai, ya shugabana? Yanzu ba ni da sauran ƙarfi, ba ni kuma da sauran numfashi.”
18Mai kamannin mutum ɗin nan kuma ya sake taɓa ni, ya kuma ƙarfafa ni. 19Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”
20Shi kuwa ya ce, “Ka san dalilin zuwana wurinka? Yanzu zan koma in yi yaƙi da shugaban Farisa, sa'ad da na murƙushe shi, shugaban Hellas zai taso. 21Zan faɗa maka abin da ke rubuce a littafin gaskiya. Ba wanda zai taimake ni yaƙi da waɗannan, sai dai Mika'ilu shugabanka.
1“A shekara ta fari ta sarautar Dariyus Bamediye, na tashi na tabbatar da shi, na kuma ƙarfafa shi.”
2“Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa'ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.
3“Sa'an nan wani sarki babba zai taso wanda zai yi mulki da babban iko yadda ya ga dama. 4Sa'ad da ya ƙasaita mulkinsa zai faɗi, a rarraba shi kashi huɗu a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, amma ba za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki mulkinsa saboda waɗansu.
5“Sarkin kudu zai yi ƙarfi, amma ɗaya daga cikin jarumawansa zai ƙasaita fiye da shi, mulkinsa kuma zai zama babba. 6Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da 'yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta. 7Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi. 8Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba. 9Bayan wannan sarkin arewa zai kai wa sarkin kudu yaƙi, amma tilas zai janye, ya koma ƙasarsa.
10“'Ya'yansa maza za su tara babbar rundunar yaƙi. Ɗayansu zai mamaye kamar rigyawa, har ya kai kagara wurin da abokan gāba suke. 11Sarkin kudu zai husata ya kai wa sarkin arewa yaƙi, za a ba da rundunar sojojin sarkin arewa a hannunsa. 12Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce. 13Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.
14“A waɗannan kwanaki mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin kudu. Amma waɗansu 'yan kama-karya za su taso daga jama'arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattaka su. 15Sa'an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin garun birni don ya ci birnin da yaƙi. Sojojin kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansa ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa. 16Amma wanda ya kawo masa yaƙin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai tsaya a ƙasa mai albarka, ya mallake ta duka. 17Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da 'yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gābansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba. 18Daganan zai yunƙura zuwa ƙasashen gaɓar teku, ya ci da yawa daga cikinsu, amma wani jarumi zai kawo ƙarshen fāɗin ransa. Zai sa fāɗin ransa ya koma masa. 19Sa'an nan zai juya, ya nufi kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe, ya fāɗi, ba za a ƙara ganinsa ba.”
20“Wani sarki zai ɗauki matsayinsa, zai aiki mai karɓar haraji cikin daularsa, amma ba da daɗewa ba za a kashe shi, ba cikin hargitsin yaƙi ba.
21“Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba. 22Zai shafe rundunonin sojoji har da rantsattsen shugaba. 23Daga lokacin da aka ƙulla yarjejeniya da shi, zai yi munafunci. Zai sami iko ta wurin goyon bayan mutane kima. 24Ba zato ba tsammani zai kai wa lardi mafi arziki hari. Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba wa mabiyansa kwason yaƙi, da ganima, da dukiya. Zai kuma yi shiri ya kai wa kagara hari amma domin ɗan lokaci ne kawai.
25“Zai iza kansa ya yi ƙarfin hali ya kai wa sarkin kudu yaƙi da babbar rundunar soja. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya. 26Waɗanda ke na jikinsa, su ne za su zama sanadin faɗuwarsa. Za a kashe rundunar sojojinsa, a shafe su duk. 27Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.
28“Sarkin arewa zai koma gida da dukiya mai ɗumbun yawa. Zuciyarsa za ta yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai yi yadda ya ga dama sa'an nan ya koma ƙasarsa.
29“A ƙayyadadden lokaci kuma zai koma kudu, amma a wannan karo abin ba zai zama kamar dā ba, 30gama jiragen ruwa na Kittim za su tasar masa, shi kuwa zai ji tsoro, ya janye. “Zai koma ya huce fushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai kula da waɗanda suka yi banza da tsattsarkan alkawarin. 31Sojojinsa za su ɓata tsattsarkan wuri da kagararsa. Za su kuma hana yin hadayu na yau da kullum, su kafa abin banƙyama da ke lalatarwa. 32Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu. 33Waɗansu daga cikin mutane waɗanda ke da hikima, za su wayar da kan mutane da yawa. Amma duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta. 34Sa'ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci. 35Waɗanda suke da hikima, za a kashe su, don a tsabtace su, a tsarkake su, su yi tsab tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.
36“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka kaddara zai cika. 37Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba, ko begen da mata ke yi. Ba kuwa zai kula da kowane irin gunki ba, domin zai aza kansa ya fi su duka. 38A maimakon haka zai girmama gunkin kagarai, gunkin da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tamani. 39Zai tasar wa kagara mafi ƙarfi da taimakon baƙon gunki. Waɗanda suka yarda da shi, zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.
40“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce. 41Zai shiga kyakkyawar ƙasa ya kashe dubban mutane. Amma ƙasar Edom, da ta Mowab, da yawancin ƙasar Ammonawa za su kuɓuta daga hannunsa. 42Zai kai wa waɗansu ƙasashe yaƙi, ƙasar Masar kuwa ba za ta kuɓuta ba. 43Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tamani na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Habasha da yaƙi. 44Labarin da zai zo masa daga gabas da arewa zai firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, ya karkashe mutane da yawa, ya shafe su. 45Zai kafa manyan alfarwai na sarauta a tsakanin teku da tsattsarkan dutse. Amma zai mutu ba kuwa wanda zai taimake shi.”
1“A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda ke lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi. 2Waɗanda suka rasu za su tashi, waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci. 3Waɗanda ke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.
4“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”
5Sa'an nan ni Daniyel na duba, sai ga waɗansu biyu a tsaye, ɗaya a wannan gāɓa ɗayan kuma a waccan gāɓar kogin. 6Dayansu ya ce wa mutumin da ke sāye da rigar lilin, wanda ke tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”
7Sai mutumin da ke sāye da rigar lilin ɗin, wanda ke tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”
8Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, menene ƙarshen waɗannan abubuwa?”
9Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci. 10Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.
11“Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda ke lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa'in. 12Masu farin ciki ne waɗanda suka daure, har suka kai ƙarshen kwana dubu da ɗari uku da talatin da biyar.
13“Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.”
1 A zamanin da, an yi wani mutum da ya zauna a Babila mai suna Yowakim. 2 Ya auri wata mace mai suna Suzana, yar Hilkiya, wata kyakkyawa ce mai tsoron Ubangiji. 3 Iyayenta adalai ne, sun kuma reni yarsu bisa ga Attaura ta Musa. 4 Yowakim mai wadata ne ƙwarai, yana da wani kyakkyawan lambu kusa da gidansa, Yahudawa sukan ziyarce shi a kai a kai, don duk ya fi su martaba.
5 A shekaran nan aka zaɓi mutum biyu su zama alƙalai. A kansu ne ma Ubangiji ya ce, Daga Babila ne shaicranci ya zo, daga dattawan da aka naɗa alkalai, waɗanda ya kamata su shugabanci jamaa. 6 Duk masu son kai ƙara suna zuwa gun mutanen nan. Su alkalan kuma suna zuwa gidan Yowakim a kai a kai. 7 Kowace rana, da maziyarta suka ba da baya da rana, sai Suzana ta tafi yawon miƙe ƙafa a lambun mijinta. 8 Dattawan nan biyu sun saba ganinta kowace rana, tana tafiyar lambun, tana yawace‑yawacenta. Ai, fa sai suka fara shaawar kyanta. 9 Sun tayar da lamirinsu, sun ƙi ko duba sama, ko tuna da dokokin adalci. 10 Su duka biyu suna ƙyashinta, amma ba su gaya wa juna suna sonta ba, 11 gama suna jin kunyar gaya wa juna yadda kowannensu ke so ya kwana da ita. 12 Har ma sun ƙagauta, kowace rana, sai zuba mata ido suke yi.
13 Wata rana sai suka ce wa junansu, Kai, mu tafi gida mana, ai, an gama abinci. Da suka fita waje, sai suka rabu da juna. 14 Amma kowannensu ya koma gidan su Suzana, duk sai suka sāke haɗuwa. Suka ce wa juna, Me ya sa haka? Sai suka magantu kan shaawarsu. Saan nan sai suka shawarta lokacin da za su iya samunta, ita kadai.
15 Wata rana, lokacin da suke zaman tsammani, sai ta shiga lambun kamar yadda ta saba yi da yan mata biyu kawai, tana shirin wanka cikin lambu, don ana jiɓi. 16 Ba kowa ke wurin sai dattawan nan biyu, waɗanda suka ɓoye, suna leƙenta. 17 Sai ta ce wa yan matanta, Ku miƙo mini sabulu da man shafawa, ku kuma rufe ƙofofin lambun don in yi wanka. 18 Suka yi kamar yadda ta ce, suka rufe ƙofofin, suka fita ta ƙofar gida domin su kawo abubuwan da aka umarce su, ba su ma ga dattawan nan ba, don sun ɓoye a ciki.
19 Da yan matan suka fita waje, sai dattawan nan biyu suka ruga gunta, suka ce, 20 Ke, ki duba, an rufe ƙofofin lambun dai, ba wanda zai ganmu. To, muna shaawarki, ki yardar mana, ki sam mana ma taɓa. 21 In kika ƙi, za mu dafa miki, mu ce wani saurayi ya yi lalata da ke, har mu ce don haka ne ma kika koro yan matanki waje.
22 Sai Suzana ta yi ajiyar zuciya ƙwarai, ta ce, Kun kewaye ni ta koina. In kuwa na yi wannan abu, mutuwa zan yi, in ban yi ba kuma, ba zan iya kuɓuce muku ba. 23 Ba zan yi abin ba, gara ku yi mini ɗaukakakkiyar da kuka ce, da in yi zunubi a gaban Ubangiji. 24 Saan nan Suzana ta fasa ƙara da kakkausar murya, sai dattawan nan biyu suka yi mata ihu. 25 Har ma gudansu ya ruga, ya buɗe ƙofar lambun. 26 A lokacin da bayi maza na gida suka ji kururuwa cikin lambun, sai suka yiwo dandazo ƙofar gida, su ga abin da ya same ta. 27 Da dattawan nan suka gaya wa bayin ƙagen, sai bayin suka ji kunyar gaske, don abin kunya irin wannan bai taɓa faɗa wa Suzana haka ba.
28 Kashegari da jamaa suka taru a gidan mijinta, wato Yowakim, sai dattawan nan biyu suka zo, don tsananin ƙeta suna so su sa a kashe Suzana. 29 Suka ce wa jamaa, Ku kira mana Suzana, yar Hilkiya, matar Yowakim. 30 Aka aika wa Suzana. 31 Sai ta zo, har ma da iyayenta da yayanta da dai dukan danginta. 32 Suzana ya ce mai kyan diri, ga kyau, sai ka ce aIjana. 33 Tana da lulluɓi, sai shaiɗanun nan suka ce a kware lulluɓin domin su ƙara kallon kyanta a tsanaki. 34 Amma da iyayenta, da dai duk sauran dangi, kowa ya gan ta, sai ta fashe da kuka.
34 Daganan dattawan nan biyu suka tsaya a tsakiyar jamaa, suka tsira wa Suzana hannu. 35 Da ta fara kuka, sai ta ɗaga kai sama, gama ta amince da Ubangiji da dukan zuciyarta. 36 Sai manyan gwazar suka ce, Muna yawo cikin lambu mu kaɗai, sai matan nan ta shigo lambun da yan mata guda biyu, ta rufe ƙofofin lambun, saan nan ta kori yan mata biyu ɗin. 37 Nan da nan sai wani saurayi, da ke ɓoye a lambun, ya je gunta, suka yi lalata. 38 Mu kuwa muna laɓe a kusurwar dami, da muka ga wanhan mugun abu, sai muka ruga don mu hana su. 39 Muka tarar sun ƙulle, amma ba dama mu taɓa namijin, don ya fi ƙarfinmu, sai ya buɗe ƙofa ɓagas, ya shara da gudu. 40 Sai muka riƙe ta, muka ce ta gaya mana sunan saurayin. 40 Amma ta ƙi. Abin da muka shaida ke nan. Sai taron ya gaskata, domin su dattawan jamaa ne, alƙalai kuma. Suka hukunta mata mutuwa.
42 Sai Suzana ta yi kururuwa da ƙarfi, ta ce, Ya Allah Madawwami, wanda ka san abin da ke ɓoye, ka san dukan abubuwa kafin ma su faru, 43 ka sani dai mutanen nan ƙage ne kawai suka yi mini. Ga shi, an hukunta mini mutuwa! Duk da haka ban yi ko ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙaga mini ba!
44 Sai Ubangiji ya ji roƙonta. 45 Ana tafiya da ita ke nan inda za a kashe ta, sai Allah ya iza tsattsarkan ruhu na wani saurayi mai suna Daniyel. 46 Ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce, Ba ruwana da jinin macen nan mai adalci.
47 Sai dukan jamaa suka waige shi, suka ce, Me kake cewa haka?
48 Da ya tsaya a tsakiyarsu, sai ya ce, Ashe, ku mutanen nan na Israila wawaye ne haka? Kun hukunta wa yar Israila mutuwa kawai, ba tare da binciken gaskiyar abin ba? 49 Ku dai koma fadar! Ai, mutanen nan ƙagen ƙarya ne suka yi mata kawai.
50 Sai dukan mutane suka dawo da gaggawa. Dattawan kuma suka ce masa, Zo, ka zauna nan a gabanmu, ka gaya mana gaskiya. Ai, kai ne ka yanke wa ƙasa cibiya!
51 Amma Daniyel ya ce wa taron, Ku raba alƙalan nan nesa da juna, zan jarraba su in gani.
52 Da aka raba su da juna, sai ya kirawo ɗayansu, ya ce masa, Kai, tsohon dattijon burgu, zunubanka sun tonu, waɗanda ka taɓa yi duka. 53 Kana yin shariar sonkai, kana hukunta adalai, ka ƙyale shaiɗanu, ko da ya ke Ubangiji ya ce, Kada ka hukunta adali marar aibu. 54 To yanzu, in dai ka tabbata ka gan ta, gaya mini gaskiya, ƙarƙashin wane itace ne ka ga sun ƙulle?
Ya amsa, ya ce, A ƙarƙashin itacen kargo.
55 Sai Daniyel ya ce, To madalla! Bakinka ya yanka wuyanka, gama malaikan Allah ya karɓo hukuncinka daga gun Allah, yanzu zai datsa ka biyu.
56 Saan nan ya kawar da wannan waje ɗaya, ya umarci a kawo gudan. Ya ce wa gudan, Kai jikan Kanana ne, ba na Yahuza ba, kyau ya ruɗa ka, shaawa kuma ta cika zuciyarka. 57 Ai, haka ne ma kuke ta yi da yan matan mulkin Israila, dole ne kuwa suke yarda da ku, don suna jin tsoronku. Amma yarinyan nan ta mulkin Yahudiya ba ta yarda da saɓonku ba ko kaƙan. 58 Yanzu, sai ka gaya mini, ƙarƙashin wane itace ne ka ga sun ƙulle?
Ya amsa shi ma, ya ce, A ƙarƙashin wani itacen maje ne.
59 Sai Daniyel ya ce masa, Naam! Kai ma ka sheƙa karyar, bakinka ya yanka wuyanka, gama malaikan Allah yana jiranka da takobi, zai raba ka biyu, ya hallaka dukanku biyu.
60 Dukan taron ya yi wata irin gunza gaba ɗaya, ya yabi Allah wanda ke fansar waɗanda suke sa rai a gare shi. 61 Suka wanke hannu, suka auka wa dattawan nan biyu, gama Daniyel ya ƙure ƙaryar ƙagensu. Sai aka yi musu horon da suka yi niyyar yi wa Suzana 62 bisa ga shariar Musa, aka kashe su. Ta haka aka fanshi jinin adala ran nan.
63 Sai Hilkiya da matarsa suka yabi Allah a kan yarsu Suzana, haka Yowakim mijinta, da dukan danginta suka yi, da ya ke ba a same ta da abin kunya ba. 64 Tun daga ran nan ne Daniyel ya yi babban suna a cikin jamaa.
1 A lokacin da sarki Asatiyagas ya mutu, sai Sairus mutumin Farisa, ya hau gadon mulkin. 2 Daniyel kuwa abokin sarki ne. Sarkin kuwa ba shi da wani ingantaccen aboki kamar Daniyel. 3 A zamanin Babilawa suna da wani gunkin da suke kira Bel, kowace rana suna ba Bel garwar gari goma sha biyu, da tumaki arbain, da dasar giya hamsin. 4 Sarkin ya yi naam da Bel, har yana yi masa sujada a kowace rana. Amma Daniyel yana bauta wa Allahnsa mai gaskiya. 5 Sai sarkin ya ce wa Daniyel, Don me ba ka bauta wa Bel ba?
Daniyel ya ce, Domin ban yi naam da gumakan da yan adam suka yi ba, sai dai Allah rayayye kaɗai, wanda ya halicci sama da ƙasa, yana kuma da iko bisa kowane mutum.
6 Sarkin ya ce masa, Ba ka ɗauki Bel shi ne allah rayayye ba? Ba ka ga abincin da yake dankara kowace rana ba, ga giya kuma?
7 Sai Daniyel ya yi dariya, ya kuma ce, Kada ka ruɗi kanka, ya sarki, gama wannan yumɓu ne kawai aka dalaye da jan ƙarfe. Ai, ba ya ma iya ci ko shan wani abu.
8 Sai sarkin ya husata, ya kira firistocinsa, ya ce musu, In ba ku gaya mini wanda ke cin kayan nan ba, to, za ku baƙunci lahira. 9 Amma in kun nuna mini yadda Bel ke cinye su, zan kashe Daniyel, gama ya saɓi Bel.
Sai Daniyel ya ce wa sarkin, A yi abin da ka umarta mana.
10 Akwai firistoci har sabain na Bel, banda matansu da yayansu.
Sai Sarki ya tafi da Daniyel har haikalin Bel. 11 Firistoci na Bel suka ce, Duba, yanzu za mu fita waje. Kai da kanka, ya sarki, kai ne za ka haɗa abincin, ka kuma ajiye giyar. Saan nan ka rufe ƙofar, ka hatimce ta da hatiminka. 12 Gobe in ka dawo da safe, har in ba ka tarar Bel ya naɗe su ba, mun yarda mu mutu, ko kuma Daniyel ya mutu, wanda yake māka mana ƙarya. 13 Ba ruwansu, gama a ƙarkashin teburin sun yi rami ta inda suke shiga kullum, suna cinye dukan abincin nan. 14 Da suka fita waje, sai sarkin ya shirya wa Bel abincin. Saan nan Daniyel ya umarci bayi su kawo toka su barbaɗa ta cikin dukan haikali a idon sarki, shi kaɗai. Saan nan suka fita waje, suka rufe ƙofar, suka sa hatimin sarki, suka kawar da jiki. 15 Da dare ya tsala, sai firistoci suka fito, su da matansu, da yayansu kamar dai yadda suka saba yi, suka cinye dukan abincin suka shanye giyar.
16 Da sassafe sai sarki ya taso, ya zo, da shi da Daniyel. 17 Sarki ya ce, An huje hatimin, Daniyel?
Daniyel ya ce, Aa, ranka ya daɗe.
18 Da dai aka buɗe ƙofar, Sarki ya duba teburin, sai ya yi kira da ƙarfi, ya ce, Ai, mai girma kake, ya Bel, ba ka ruɗin kowa, aa, ko kaɗan.
19 Sai Daniyel ya yi dariya, ya hana sarki shiga, ya ce masa, Dubi daɓen ɗakin, ka kula, sawun suwanene nan?
20 Sarki ya ce, Ni dai na ga sawun maza, da na mata, da yayansu. 21 Sai sarkin ya husata, ya matsa wa firistoci, da matansu, da yayansu, sai da suka nuna masa ɓoyayyiyar ƙofar da suka saba bi, suna cinye dukan abin da ke kan teburin. 22 Sai sarki ya sa aka kashe su, kana kuma ya ba Daniyel Bel ɗin, Daniyel kuwa ya lalata Bel duk da haikalinsa.
23 Akwai ma wani gawurtaccen maciji da Babilawa suka yi naam da shi. 21 Sarki ya ce wa Daniyel, Ba ka iya shakkar wannan allah ne rayayye, don haka ka bauta masa mana.
25 Daniyel ya ce, Zan bauta wa Ubangiji Allahna, gama shi ne Allah rayayye. 26 In kai dai, sarki, za ka ba ni dama, zan yanka macijin nan, ba tare da takobi ko kuma kulki ba.
Sarkin ya ce, Na ba ka iznin.
27 Sai Daniyel ya ɗauki baƙin mai, da kitse, da gashi, ya dafa su tare, ya yi waina, wadda ya ciyar da macijin da ita. Macijin ya ci wainar, har cikinsa ya fashe. Daniyel ya ce, Kai jamaa, dubi abin da kuke ta bauta wa!
28 Da Babilawa suka ji haka fa, sai suka ji haushi kwarai, suka kuma yi shirin kashe sarkin, suka ce, Ai, sarkin nan namu ya zama Bayahude, ya yi kacakaca da Bel, ya kuma kashe macijin, ya yanyanka sarkin tsafinsa. 29 Da suka isa gun sarkin, sai suka ce masa, Ka hannanta mana Damyel, ko kuwa mu kashe ka, kai da dukan iyalin gidanka. 30 Sarki fa, da ya ga sun matsa masa, sai ya hannanta musu Daniyel tilas. 31 Sai suka jefa Daniyel a ramin zakoki, har ya kwana shida a can ciki. 32 Akwai zakoki bakwai a ramin nan nasu. Abincin zakokin kuwa, shi ne kowace rana a ba su mushen mutum biyu da tumaki biyu, amma yanzu an hana musu, domin su cinye Daniyel.
33 A lokacin, annabi Habakuk yana Yahudiya. Sai ya ɗunɗuma abinci, ya gutsuttsura gurasa a kwanon, ya ɗauka, zai kai wa yan girbi a gona. 34 Amma wani mala ikan Ubangiji ya ce wa Habakuk, Wannan gara da ka shirya, ai, sai ka kai ta Babila, ka ba Daniyel, wanda yake zaune a ramin zakoki.
35 Habakuk ya ce, Malam, ai, ni ban taɓa zuwa Babila ba, ban kuma san ramin ba. 36 Saan nan malaikan ya suri Habakuk ta gashin kansa, ya ɗauke shi sama, ya saka a garin Babila, gab da ramin, da hucin iska mai karfi.
37 Sai Habakuk ya yi kira, ya ce, Daniyel, Daniyel! Ci abincin nan da Allah ya aiko maka!
38 Daniyel ya ce, Kai ne ka tuna da ni, ya Allah, ai, ba ka mancewa da waɗranda ke kaunarka. Sai Daniyel ya tashi, ya ci abinci. Nan da nan kuma malaikan Ubangijin ya mai da Habakuk gidansu.
40 A rana ta bakwai sai sarki ya zo domin ya yi wa Daniyel makoki. Da ya iso ramin, ya leƙa, sai ya yi arangama da Daniyel a zaune. 41 Sai sarkin ya yi kwakwazo, ya ce, Ai, kai mai girma ne, ya Ubangiji na Daniyel, ba ma wani kamarka. 42 Ya zaro Daniyel waje, ya zuba mutanen da suka yi shirin kashe Daniyel a ciki. Nan da nan kuwa zakokin suka dira musu a idon sarki.