Deuteronomy
1Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab. 2Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir. 3A shekara ta arba'in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra'ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu. 4A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai. 5A hayin Urdun, cikin ƙasar Mowab, Musa ya yi niyya ya fassara waɗannan dokoki. Ya ce, 6“Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, “‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa. 7Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan'aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis. 8Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.”
(Fit 18.13-27)
9“A wancan lokaci ne na yi magana, na ce, “‘Ba zan iya ɗaukar nawayarku ba, 10gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama. 11Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku! 12Ƙaƙa ni kaɗai zan iya ɗaukar nawayarku da wahalarku da kuma faɗace-faɗacenku? 13Ku zaɓi masu hikima, da masu ganewa daga cikin kabilanku, waɗanda suka saba da zaman jama'a, ni kuwa in sa su zama shugabanninku!” 14Kuka amsa mini, kuka ce, “‘I, daidai ne kuwa mu bi shawarar nan da ka kawo mana.” 15Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma'amala da jama'a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.
16“A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, “‘Ku yi adalci cikin shari'a tsakanin 'yan'uwanku, tsakanin mutum da ɗan'uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi. 17Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.” 18A wancan lokaci na umarce ku da dukan abin da ya kamata ku yi.”
(L. Ƙid 13.1-33)
19“Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya. 20Sa'an nan na faɗa muku cewa, “‘Kun iso ƙasar tuddai ta Amoriyawa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu. 21Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.”
22“Sa'an nan sai dukanku kuka zo wurina, kuka ce, “‘Bari mu aika da mutane, su je su leƙo mana asirin ƙasar tukuna, domin su shawarce mu ta hanyar da za mu bi, da kuma irin biranen da za mu shiga.”
23“Na ga al'amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila. 24Mutanen kuwa suka kama hanya, suka tafi tuddai, suka kuma isa kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar. 25Da hannunsu suka ɗebo daga cikin amfanin ƙasar, suka gangaro mana da shi. Suka kuma faɗa mana cewa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu, mai kyau ce.
26“Amma kuka ƙi ku haura, kuka ƙi bin umarnin Ubangiji Allahnku. 27Sai kuka yi ta gunaguni cikin alfarwanku, kuna cewa, “‘Ai, saboda Ubangiji ya ƙi mu, shi ya sa ya fisshe mu daga ƙasar Masar, don ya bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallaka mu. 28Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.”
29“Sai na ce muku, “‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita. 30Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku. 31Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.” 32Amma ko da yake ya yi muku haka duk da haka ba ku dogara ga Ubangiji Allahnku ba. 33Shi wanda ya bishe ku, ya nuna muku inda za ku yi zango. Da dare yakan nuna muku hanya da wuta, da rana kuma yakan bi da ku da girgije.”
(L. Ƙid 14.20-35)
34“Ubangiji kuwa ya ji maganganunku, sai ya yi fushi, ya rantse, ya ce, 35“‘Daga cikin mutanen wannan muguwar tsara ba wanda zai ga ƙasan nan mai albarka wadda na rantse zan ba kakanninku, 36sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da 'ya'yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.” 37Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, “‘Har kai ma ba za ka shiga ba. 38Baranka, Joshuwa ɗan Nun, shi ne zai shiga. Sai ka ƙarfafa masa zuciya gama shi ne zai bi da Isra'ilawa, har su amshi ƙasar, su gāje ta.”
39“Sa'an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, “‘Amma 'ya'yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta. 40Amma ku, sai ku koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya.”
(L. Ƙid 14.39-45)
41“Sa'an nan kuka amsa mini, kuka ce, “‘Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi. Za mu tafi mu yi yaƙi bisa ga faɗar Ubangiji Allahnmu.” Sai kowannenku ya yi ɗamara ya ɗauki makaman yaƙinsa, kuka yi tsammani abu mai sauƙi ne ku shiga ƙasar tuddai.
42“Amma Ubangiji ya ce mini in faɗa muku, kada ku tafi kada kuma ku yi yaƙi, gama ba ya tare da ku. Maƙiyanku za su kore ku. 43Haka kuwa na faɗa muku, amma ba ku kasa kunne ba, kuka ƙi yin biyayya da umarnin Ubangiji. Sai kuka yi izgili, kuka hau cikin ƙasar tuddai. 44Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma. 45Sai kuka koma, kuka yi kuka ga Ubangiji, amma Ubangiji bai ji kukanku ba, bai kuma kula da ku ba. 46Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”
1“Muka koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya kamar yadda Ubangiji ya faɗa mini. Muka daɗe muna ta gewaya ƙasar tuddai ta Seyir.
2“Sai Ubangiji ya ce mini. 3“‘Ai, kun daɗe kuna ta gewaya waɗannan tuddai. Ku juya, ku nufi arewa. 4Ka umarci jama'a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali, 5kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir. 6Za ku sayi abincin da za ku ci, da ruwan da za ku sha a wurinsu. 7Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.”
8“Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda sike zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.
9“Sai Ubangiji ya ce mini, “‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.”
10(Emawa manya ne, masu yawa, dogaye ne kuma kamar Anakawa. Su ne suke zaune a ƙasar a dā. 11Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa. 12Hakanan kuma a dā Horiyawa ne suke zaune a ƙasar Seyir, amma mutanen zuriyar Isuwa suka zo, suka kore su, suka karkashe su, suka zauna a wurin, daidai kamar yadda Isra'ilawa suka yi da ƙasar mallakarsu, wadda Ubangiji ya ba su.)
13“‘Yanzu, ku tashi ku haye rafin Zered da kanku.” Sai kuwa muka haye. 14Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu. 15Hakika kuwa ikon Ubangiji ya buge su har suka hallaka ƙaƙaf.
16“Sa'ad da dukan waɗanda suka isa yaƙi suka mutu, 17sai Ubangiji ya yi mini magana, ya ce, 18“‘Yau za ku ratsa kan iyakar ƙasar Mowab a Ar. 19Sa'ad da ku kuka zo kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su, gama ba zan ba ku abin mallaka daga yankin ƙasar Ammonawa ba, domin na ba da ita ta zama mallaka ga zuriya Lutu.”
20(Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta. 21Manyan mutane masu yawa dogaye ne kuma kamar Anakawa, amma Ubangiji ya hallakar da su a gabansu, suka kore su, suka zauna a wurinsu, 22daidai kamar yadda Ubangiji ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a Seyir, sa'ad da ya hallakar da Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su suka zauna a wurinsu har wa yau. 23Hakanan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)
24“Ubangiji ya ce, “‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba'amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi. 25A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.”
(L. Ƙid 21.21-30)
26“Sa'an nan na aiki manzanni daga jejin Kedemot zuwa Sihon, Sarkin Heshbon, ina neman zaman lafiya, na ce, 27“‘Ka yardar mini in bi ta cikin ƙasarka. Zan bi ta kan babbar hanya sosai, ba zan ratse dama ko hagu ba. 28Zan sayi abincin da zan ci, da ruwan da zan sha a wurinku. 29Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.”
30“Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau.
31“Sai Ubangiji ya ce mini, “‘Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa a gare ku. Ku fara fāɗa wa ƙasarsa da yaƙi don ku mallake ta.” 32Sai Sihon da mutanensa suka fita su gabza yaƙi da mu a Yahaza. 33Ubangiji Allahnmu ya bashe shi a hannunmu, muka ci nasara a kansa, da 'ya'yansa, da dukan mutanensa. 34Muka ci dukan garuruwansa, muka hallaka kowane gari, da mata, da maza, da yara, ko ɗaya bai ragu ba. 35Sai dabbobi ne kaɗai da dukiyar garuruwan da muka ci, su ne muka kwashe ganima. 36Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu. 37Amma ba ku kusaci ƙasar Ammonawa ba, wato ƙasar da take a kwarin kogin Yabbok, da garuruwan ƙasar tuddai, da wuraren da Ubangiji Allahnmu ya hana mu.”
(L. Ƙid 21.31-35)
1“Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama'arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai. 2Sai Ubangiji ya ce mini, “‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama'arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.”
3“Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama'arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai. 4Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan. 5Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu. 6Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara. 7Amma muka riƙe dabbobi da dukiyar da muka kwaso daga garuruwan, ganima.
8“A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.” 9(Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.) 10“Wato dukan garuruwa na ƙasar tudu, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Bashan har zuwa Salka da Edirai, garuruwa na mulkin Og ke nan cikin ƙasar Bashan.”
11(Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)
(L. Ƙid 32.1-42)
12“Sa'ad da muka mallaki ƙasar a wannan lokaci, sai na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, da rabin ƙasar tuddai ta Gileyad tare da garuruwanta. 13Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.”
(Duk dai yankin ƙasar nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.” 14(Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)
15“Na ba Makir Gileyad. 16Na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar da ta tashi daga Gileyad har zuwa kwarin Arnon, tsakiyar kwarin shi ne iyakar har zuwa kwarin kogin Yabbok wanda ya yi iyaka da Ammonawa. 17Na kuma ba su Araba, Urdun shi ne iyaka daga Kinneret, har zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.
18“A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, “‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban 'yan'uwanku, Isra'ilawa. 19Amma matanku, da 'ya'yanku, da dabbobinku, na sani kuna da dabbobi da yawa, su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku, 20har lokacin da Ubangiji ya zaunar da 'yan'uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa'an nan kowa zai koma ga mallakarsa.”
21“A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, “‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Hakanan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu. 22Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.”
23“Sa'an nan kuma na roƙi Ubangiji, na ce, 24“‘Ya Ubangiji Allah, kai ne ka fara nuna wa baranka ɗaukakarka da ikonka. Ba wani Allah a Sama ko a duniya da zai aikata ayyuka na banmamaki irin naka. 25Ka yarje mini, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun, ƙasar nan mai kyau ta tuddai, da Lebanon.”
26“Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, “‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al'amari. 27Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba. 28Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama'ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.”
29“Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”
1“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku yake ba ku. 2Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su. 3Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba'al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba'al-feyor. 4Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.
5“Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta. 6Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al'ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa'ad da al'ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “‘Ba shakka, wannan babbar al'umma tana da hikima da ganewa.”
7“Gama babu wata babbar al'umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa'ad da muka kira gare shi. 8Ko kuwa, da akwai wata babbar al'umma wadda take da dokoki da farillai na adalci kamar waɗannan dokoki da na sa a gabanku yau?”
9“Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su, 10da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, “‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.”
11“Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutsen sa'ad da dutsen yake cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma girgije baƙi ƙirin yana rufe da dutsen. 12Ubangiji kuwa ya yi magana da ku ta tsakiyar wuta. Kuka ji hurcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji. 13Shi ne ya hurta muku shari'ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu. 14Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”
15“Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta. 16Don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji, 17ko siffar dabbar da take a duniya, ko siffar tsuntsun da yake tashi a sararin sama, 18ko siffar kowane abu mai jan ciki bisa ƙasa, ko siffar kifin da yake cikin ruwa ƙarƙashin ƙasa. 19Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai. 20Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama'arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau. 21Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasar nan wadda yake ba ku abar gādo ba. 22Gama a nan ƙasar zan mutu, ba zan haye Urdun ba, amma ku za ku haye, ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa. 23Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku. 24Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.
25“Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi, 26to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf. 27Ubangiji zai warwatsa ku cikin al'ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al'ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku. 28Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana. 29Amma idan kun nemi Ubangiji Allahnku a can inda kuke, za ku same shi muddin kun neme shi da zuciya ɗaya, da dukan ranku. 30Sa'ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya. 31Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.
32“Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa? 33Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu? 34Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka? 35An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma. 36Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar. 37Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma. 38Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau. 39Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma. 40Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”
41Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun, 42domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa. 43Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.
44Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra'ilawa, 45su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar, 46a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar. 47Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun. 48Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon, 49da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.
(Fit 20.1-17)
1Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai. 2Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb. 3Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau. 4Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta. 5Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba. “Ubangiji ya ce, 6“‘Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar daga gidan bauta.
7“‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni.
8“‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa. 9Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni. 10Amma nakan nuna ƙauna ga dubbai waɗanda suke ƙaunata, suna kiyaye umarnaina.
11“‘Kada ka rantse da sunan Ubangiji Allahnka a kan ƙarya, gama Ubangiji ba zai kuɓutar da wanda yake rantsewa da sunansa a kan ƙarya ba.
12“‘Ka kiyaye ranar Asabar, ka riƙe ta da tsarki yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka. 13Kwana shida za ka yi aikinka duka. 14Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka. 15Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.
16“‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
17“‘Kada ka yi kisankai.
18“‘Kada ka yi zina.
19“‘Kada ka yi sata.
20“‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka.
21“‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.”
22“Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”
(Fit 20.18-21)
23“Sa'ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina, 24suka ce, “‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu. 25Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu. 26Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu? 27Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.”
28“Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, “‘Na ji maganar da jama'ar nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne. 29Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada. 30Tafi, ka faɗa musu su koma cikin alfarwansu. 31Amma kai ka tsaya nan a wurina don in faɗa maka dukan umarnai, da dokoki, da farillai, waɗanda za ka koya musu su kiyaye a ƙasar da nake ba su, su mallake ta.”
32“Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu. 33Sai ku bi hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku don ku rayu, ku zauna lafiya, ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.”
1“Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta, 2don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai. 3Don haka, ku ji, ya Isra'ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku.
4“Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku. 6Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku. 7Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi. 8Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama. 9Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”
10“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba, 11da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, 12to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. 13Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa. 14Kada ku bi waɗansu alloli na al'umman da suke kewaye da ku, 15gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.
16“Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha. 17Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su. 18Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku. 19Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta.
20“Idan nan gaba 'ya'yanku suka tambaye ku ma'anar maganarsa, da dokoki, da farillai, waɗanda Ubangiji Allahnmu ya umarce ku da su, 21sai ku amsa wa 'ya'yanku, ku ce, “‘Dā mu bayin Fir'auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko. 22A idonmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da mu'ujizai gāba da Masarawa, da Fir'auna, da dukan gidansa. 23Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu. 24Ubangiji kuwa ya umarce mu mu kiyaye dukan waɗannan umarnai, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu domin amfanin kanmu kullum, domin kuma mu wanzu kamar yadda muke a yau. 25Idan mun lura, muka kiyaye waɗannan umarnai, muka aikata su kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, zai zama adalci a gare mu.”
(Fit 34.11-16)
1“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi. 2Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai. 3Kada ku yi aurayya da su. Kada ku aurar wa ɗansu da 'yarku, kada kuma ku auro wa ɗanku 'yarsu. 4Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri. 5Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al'amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu. 6Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa.
7“Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al'ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al'ummai. 8Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar. 9Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa. 10Amma a fili Ubangiji yakan yi ramuwa a kan maƙiyansa, yakan hallaka su. Ba zai yi jinkirin yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili. 11Saboda haka, sai ku kiyaye umarnai, da dokoki, da farillai ku aikata su, wato waɗanda nake umartarku da su yau.”
(L. Fir 26.3-13; M. Sh 28.1-14)
12“Idan za ku saurari waɗannan farillai, ku kiyaye su, sai Ubangiji Allahnku ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku, ya kuma ƙaunace ku. 13Ubangiji zai ƙaunace ku, ya sa muku albarka, ya riɓaɓɓanya ku. Zai sa wa 'ya'yanku albarka, ya yalwata amfanin gonarku, da hatsinku, da inabinku, da manku, da garken shanunku, da 'yan ƙananan garkenku a ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku. 14Za ku fi kowace al'umma samun albarka. Ba za a iske mutum ko mace marar haihuwa a cikinku ba, ko a cikin garkenku. 15Ubangiji zai kiyaye ku daga dukan cuce-cuce. Ba zai wahalshe ku da mugayen cuce-cuce na Masar ba, waɗanda kuka sani, amma zai wahalar da duk maƙiyanku da waɗannan mugayen cuce-cuce. 16Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.
17“Ya yiwu ku ce a zuciyarku, “‘Waɗannan al'ummai sun fi mu yawa, ta ƙaƙa za mu iya ƙorarsu?” 18Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya yi da Fir'auna da dukan Masarawa. 19Ku tuna kuma da wahalar da kuka gani da idonku, da alamu, da mu'ujizai, da dantse mai iko mai ƙarfi wanda Ubangiji Allahnku ya fito da ku. Hakanan kuma Ubangiji Allahnku zai yi da dukan al'umman nan da kuke jin tsoronsu. 20Banda wannan kuma Ubangiji Allahnku zai aiko da zirnako a cikinsu su hallaka sauran da suka ragu, suka ɓuya. 21Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana. 22Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al'ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku. 23Ubangiji Allahnku zai bashe su a gare ku, zai firgitar da su har ya hallakar da su. 24Zai ba da sarkunansu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Ba wanda zai iya tasar muku har kun ƙare su. 25Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu. 26Kada ku kawo abin ƙyama a gidajenku don kada ku zama abin ƙyama kamarsa. Lalle sai ku ƙi shi, ku ji ƙyamarsa, gama haramtacce ne.”
1“Sai ku lura, ku aikata dukan umarnan da na umarce ku da su don ku rayu, ku riɓaɓɓanya, ku shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku. 2Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu. 3Ya koya muku tawali'u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji. 4A shekarun nan arba'in tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba. 5Kun san wannan a zuciyarku, wato kamar yadda mutum yakan yi wa ɗansa tarbiyya, haka kuma Ubangiji Allahnku yake yi muku tarbiyya. 6Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa. 7Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu. 8Ƙasa mai alkama, da sha'ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma. 9Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta. 10Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”
11“Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau. 12Sa'ad da kuka ci kuka ƙoshi, kuka gina kyawawan gidaje, kuka zauna ciki, 13garkunanku na shanu da tumaki suka riɓaɓɓanya, azurfarku, da zinariyarku suka ƙaru, sa'ad da dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, 14to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta. 15Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. 16Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali'u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya. 17Kada ku ce a zuciya, “‘Ai, ikona da ƙarfin hannuwana ne suka kawo mini wannan wadata.” 18Sai ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne ya ba ku ikon samun wadata domin ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku kamar yadda yake a yau. 19Idan kun manta da Ubangiji Allahnku, kuka bi gumaka, kuka bauta musu, kuka yi musu sujada, to, yau ina faɗakar da ku, cewa lalle za ku hallaka 20kamar al'umman da Ubangiji ya hallakar a gabanku. Haka za ku hallaka domin ba ku kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku ba.”
1“Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu. 2Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, “‘Wane ne zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?” 3Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.
4“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, “‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.” Gama saboda muguntar al'umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku. 5Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 6Sai ku sani fa, ba saboda adalcinku ne Ubangiji Allahnku yake ba ku kyakkyawar ƙasar nan don ku mallake ta ba, gama ku jama'a ce mai taurinkai.”
(Fit 31.18ū32.35)
7“Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji. 8A Horeb kuka tsokani Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi fushi, har yana so ya hallaka ku. 9Sa'ad da na hau kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, wato allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutsen dare arba'in da yini arba'in ban ci ba, ban sha ba. 10Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron. 11Bayan dare arba'in da yini arba'in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, wato alluna na alkawarin.
12“Sa'an nan ya ce mini, “‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama'arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.”
13“Ubangiji kuma ya ce mini, “‘Na ga mutanen nan suna da taurinkai. 14Bari in hallaka su, in shafe sunansu daga duniya, sa'an nan in maishe ka wata al'umma wadda ta fi su iko da kuma yawa.”
15“Sai na juya, na gangaro daga dutsen da allunan nan biyu na alkawari a hannuwana, dutsen kuma na cin wuta. 16Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi. 17Sai na ɗauki allunan nan biyu, na jefar da su ƙasa da hannuna, na farfashe su a idonku. 18Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi. 19Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu'ata a wannan lokaci. 20Ubangiji kuma ya husata da Haruna, har ya so ya kashe shi, amma na yi roƙo dominsa a lokacin. 21Sa'an nan na ɗauki abin zunubin nan, wato siffar maraƙin da kuka yi, na ƙone, na farfashe, na niƙe shi lilis, ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da garin a rafi wanda yake gangarowa daga dutsen.
22“Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata'awa. 23Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, “‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,” sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba. 24Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne.
25“Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku. 26Na roƙi Ubangiji, na ce, “‘Ya Ubangiji Allah, kada ka hallaka jama'arka, abar gādonka wadda ka fanshe ta ta wurin girmanka, waɗanda kuma ka fito da su daga Masar da ikon dantsenka. 27Ka tuna da bayinka, su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kada ka kula da taurinkan jama'ar nan, ko muguntarsu, ko zunubansu 28Don kada mutanen ƙasar da ka fito da mu su ce, “Ai, saboda Ubangiji ya kāsa ya kai su ƙasar da ya alkawarta musu, saboda kuma ba ya ƙaunarsu, shi ya sa ya fito da su don ya kashe su a jeji.” 29Amma su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fito da su da ikonka mai girma da dantsenka mai iko.”
(Fit 34.1-10)
1“A lokacin nan kuwa Ubangiji ya ce mini, “‘Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka hau zuwa wurina a bisa dutsen, ka kuma yi akwati na itace. 2Ni kuma zan rubuta a allunan maganar da take kan alluna na farko waɗanda ka farfashe. Za ka ajiye su cikin akwatin.”
3“Sai na yi akwati da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko. Sai na hau dutsen da alluna biyu a hannuna. 4Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su. 5Na sauko daga dutsen, na ajiye allunan cikin akwatin da na yi, a nan suke kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
6(Isra'ilawa suka kama tafiya daga rijiyoyin Bene-ya'akan suka zo Mosera. Nan ne Haruna ya rasu, aka binne shi. Sai ɗansa Ele'azara, ya gāje shi a matsayinsa na firist. 7Daga nan suka tafi Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa. 8A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau. 9Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da 'yan'uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)
10“Na sāke yin dare arba'in da yini arba'in a kan dutsen kamar dā. Ubangiji kuwa ya amsa addu'ata a lokacin kuma, ya janye hallaka ku. 11Sai Ubangiji ya ce mini, “‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama'ar nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”
12“Yanzu fa, ya Isra'ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku. 13Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku. 14Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne. 15Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al'umma, kamar yadda yake a yau. 16Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai. 17Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci. 18Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari'a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura. 19Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. 20Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa. 21Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al'amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku. 22Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”
1“Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku kiyaye faɗarsa, da dokokinsa da farillansa, da umarnansa kullum. 2Yau fa ku sani ba da 'ya'yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa, 3da alamunsa, da ayyukan da ya yi a kan Fir'auna Sarkin Masar, da dukan ƙasar, 4da irin abin da ya yi wa sojojin Masar, da dawakansu, da karusansu, da yadda ya sa ruwan Bahar Maliya ya haɗiye su, a sa'ad da suke bin sawunku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf, 5da abin da ya yi muku a jeji kafin ku iso wannan wuri, 6da abin da ya yi wa Datan, da Abiram, 'ya'yan Eliyab, ɗan Ra'ubainu, yadda ƙasa ta buɗe a tsakiyar Isra'ilawa ta haɗiye su da dukan 'ya'yansu, da alfarwansu, da dukan abu mai rai da yake tare da su. 7Amma idanunku sun ga manyan ayyukan nan da Ubangiji ya aikata.”
8“Don haka fa, sai ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar da za ku mallaka, 9domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku da zuriyarsu, ƙasar da take da yalwar abinci. 10Gama ƙasar da za ku shiga garin ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar take ba inda kuka fito, inda kukan shuka iri sa'an nan ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu. 11Amma ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwaruruka wadda ruwan sama yake shayar da ita. 12Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku yake lura da ita, Ubangiji Allahnku yana dubanta kullum, tun daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.
13“Idan kun yi biyayya da umarnansa waɗanda ya umarce ku da su yau, kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kun bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku, 14zai shayar da ƙasarku da ruwa a kan kari, da ruwan bazara da na kaka. Za ku tattara sabon hatsinku da sabon ruwan inabinku, da manku. 15Zai sa ciyawa ta tsiro a saurukanku domin dabbobinku. Za ku ci ku ƙoshi. 16Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada, 17don kada Ubangiji ya yi fushi da ku, ya rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.
18“Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku. 19Za ku koya wa 'ya'yanku su, ku yi ta haddace su, sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi. 20Za ku rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da bisa ƙofofinku, 21don kwanakinku da kwanakin 'ya'yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su muddin samaniya tana bisa duniya.
22“Idan dai za ku lura, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda nake umartarku ku kiyaye, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a dukan hanyoyinsa, ku manne masa, 23sa'an nan Ubangiji zai kori al'umman nan duka a gabanku. Za ku kori al'umman da suka fi ku yawa da ƙarfi. 24Duk inda tafin ƙafarku ya taka kuma zai zama naku. Iyakarku za ta kama daga jeji zuwa Lebanon da kuma daga Kogin Yufiretis zuwa Bahar Rum. 25Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku.
26“Ga shi, yau, na sa albarka da la'ana a gabanku. 27Za ku sami albarka idan kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau. 28Za ku zama la'anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau, har ku bi waɗansu alloli waɗanda ba ku san su ba. 29Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la'anar kuma a Dutsen Ebal. 30Duka biyunsu suna hayin Urdun ne, yamma da hanya a ƙasar Kan'aniyawa, mazaunan Araba, kusa da Gilgal, wajen itacen oak na More. 31Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa'ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki, 32sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”
1“Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya. 2Sai ku hallaka dukan wuraren da al'umman da za ku kora sukan bauta wa gumakansu, a bisa duwatsu masu tsawo, da bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhu. 3Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al'amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.
4“Ba haka za ku yi wa Ubangiji Allahnku ba. 5Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa. 6A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, da 'ya'yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. 7A nan, wato a gaban Ubangiji Allahnku, za ku ci, ku yi murna, ku da iyalanku, a kan dukan abin da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka da shi.
8“Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama. 9Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna. 10Amma sa'ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, sa'ad da kuma ya ba ku hutawa daga maƙiyanku waɗanda suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya, 11sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa. 12Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku. 13Ku lura, kada ku miƙa hadayunku na ƙonawa ko'ina, 14amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.
15“Amma kwā iya yanka nama ku ci a garuruwanku duk lokacin da ranku yake so, bisa ga albarkar da Ubangiji yake sa muku. Mai tsarki da marar tsarki za su ci abin da aka yanka kamar barewa da mariri. 16Amma ba za ku ci jinin ba, sai ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. 17Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta 'ya'yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa. 18Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi. 19Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.
20“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta muku, sa'an nan ku ce, “‘Ina so in ci nama,” saboda kuna jin ƙawar nama, to, kuna iya cin nama yadda kuke so. 21Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunsansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku. 22Kamar yadda akan ci barewa ko mariri haka za ku ci. Marar tsarki da mai tsarki za su iya cin naman. 23Sai dai ku lura, kada ku ci jinin, gama jinin shi ne rai, kada ku ci ran tare da naman. 24Kada ku ci jinin, sai ku zubar a ƙasa kamar ruwa. 25Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji. 26Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa. 27Sai ku miƙa nama da jinin hadayunku na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji Allahnku. Za ku zuba jinin sadakokinku a bisa bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku ci naman. 28Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”
29“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kawar muku da al'umman nan waɗanda za ku shiga ƙasarsu don ku kore su, sa'ad da kuka kore su, kun zauna a ƙasarsu, 30to, sai ku lura, kada ku jarabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku! Kada ku tambayi labarin kome na gumakansu, ku ce, “‘Ƙaƙa waɗannan al'ummai suka bauta wa gumakansu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.” 31Kada ku yi wa Ubangiji Allahnku haka, gama sun yi wa gumakansu dukan abar ƙyamar da Ubangiji yake ƙi, har sun ƙona wa gumakansu 'ya'yansu mata da maza.
32“Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.
1“Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu'ujiza, 2idan alamar ko mu'ujizar ta auku, idan kuma ya ce, “‘Bari mu bi gumaka, mu bauta musu,” gumakan da ba ku san su ba, 3kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku. 4Sai ku bi Ubangiji Allahnku, ku yi tsoronsa, ku kiyaye umarnansa, ku kasa kunne ga muryarsa, shi ne za ku bauta masa, ku manne masa kuma. 5Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
6“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, “‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,” 7wato gumakan al'umman da suke kewaye da ku, ko suna kusa da ku, ko suna nesa da ku, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, 8kada ku yarda, kada ku saurare shi. Kada kuma ku ji tausayinsa, kada ku haƙura da shi ko ku ɓoye shi. 9Hannunku ne zai fara jifansa, sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi, har ya mutu. 10Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta. 11Da hakanan dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro, har da ba za su ƙara aikata mugun abu irin wannan a cikinku ba. 12-13“Idan kuka ji akwai 'yan ashararu a wani gari wanda Ubangiji Allahnku ya ba ku ku zauna a ciki, sun fito daga cikinku, suka rikitar da mazaunan garin suna cewa, “‘Ku zo mu bauta wa gumaka,” waɗanda ba ku san su ba, 14to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. Idan hakika gaskiya ne, mugun abu haka ya faru a cikinku, 15sai ku karkashe dukan mazaunan garin da takobi, ku kuma karkashe dabbobin da suke cikinsa. Za ku hallaka garin ƙaƙaf. 16Ku tattara dukan ganimar garin a dandali, ku ƙone garin da dukan ganimar, hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji Allahnku. Garin zai zama kufai har abada, ba za a ƙara gina shi ba. 17Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku, 18in dai za ku yi wa Ubangiji Allahnku biyayya, ku kiyaye dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, ku kuma ku aikata abin da yake daidai ga Ubangiji Allahnku.”
1“Ku 'ya'ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu. 2Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”
(L. Fir 11.1-47)
3“Kada ku ci abin da yake haram. 4Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya, 5da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse. 6Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa. 7Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku. 8Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu.
9“Daga dukan irin abin da yake zaune a ruwa za ku iya cin duk abin da yake da ƙege da ɓamɓaroki. 10Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku.
11“Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye. 12Amma waɗannan tsuntsaye ne ba za ku ci ba, mikiya, da gaggafa, da ungulun kwakwa, 13da duki, da buga zabi, da kowace irin shirwa, 14da kowane irin hankaka, 15da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho, 16da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi, 17da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo, 18da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.
19“Dukan 'yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su. 20Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.
21“Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”
22“Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara. 23Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada. 24Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa'ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka, 25to, sai ku sayar da zakar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, 26ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.
27“Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku. 28A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku. 29Sa'an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”
1“A ƙarshen kowace shekara bakwai dole ku yafe dukan basusuwan da kuke bi. 2Ga yadda za ku yafe. Sai kowane mai bin bashi ya yafe wa maƙwabcinsa, kada ya karɓi kome a hannun maƙwabcinsa ko ɗan'uwansa, gama an yi shelar yafewa ta Ubangiji. 3Kana iya matsa wa baƙo ya biya ka, amma sai ka yafe wa danginka bashin da kake binsa.
4“Ba za a sami matalauci a cikinku ba, da yake Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, ku mallaka, 5muddin kun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye wannan umarni da na umarce ku da shi yau. 6Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka kamar yadda ya alkawarta. Za ku ba al'ummai da yawa rance, amma ba za ku bukaci rance don kanku ba. Za ku mallaki al'ummai da yawa, amma su ba za su mallake ku ba.
7“Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci. 8Amma ku ba shi hannu sake, ku ranta masa abin da yake so gwargwadon bukatarsa. 9Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, “‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,” har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. 10Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi. 11Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga 'yan'uwanku, da mabukaci, da matalauci.”
(Fit 21.1-11)
12“Idan aka sayar muku da Ba'ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku 'yantar da shi. 13Idan kuma kun 'yantar da shi, kada ku bar shi ya tafi hannu wofi. 14Sai ku ba shi hannu sake daga cikin tumakinku, da awakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Ku ba shi kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka. 15Ku tuna dā ku bayi ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnku ya 'yantar da ku, domin haka nake ba ku wannan umarni yau.
16“Amma idan ya ce muku, “‘Ba na so in rabu da ku,” saboda yana ƙaunarku da iyalinku, tun da yake yana jin daɗin zama tare da ku, 17to, sai ku ɗauki basilla ku huda kunnensa har ƙyauren ƙofa, zai zama bawanku har abada. Haka kuma za ku yi da baiwarku. 18Sa'ad da kuka 'yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin dukan abin da kuke yi.”
19“Sai ku keɓe wa Ubangiji Allahnku dukan 'yan fari maza waɗanda aka haifa muku daga cikin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. Kada ku yi aiki da ɗan farin shanunku, kada kuma ku sausayi ɗan farin tunkiyarku. 20Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa. 21Idan yana da wani lahani kamar gurguntaka ko makanta, ko kowane irin mugun lahani, to, kada ku miƙa shi hadaya ga Ubangiji Allahnku. 22Sai ku ci shi a gida. Mai tsarki da marar tsarki a cikinku za su iya ci, kamar barewa ko mariri. 23Sai dai kada ku ci jinin, amma ku zubar a ƙasa kamar ruwa.”
(Fit 12.1-20; L. Fir 23.5-8)
1“Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare. 2Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa. 3Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku. 4Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.
5“Kada ku miƙa hadayar ƙetarewa a kowane garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 6Amma ku miƙa ta a wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. Nan za ku miƙa hadayar ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, daidai da lokacin da kuka fito daga Masar. 7Sai ku dafa shi, ku ci a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Da safe sai ku koma alfarwanku. 8Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.
(Fit 23.16; L. Fir 23.15-21)
9“Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da yake tsaye. 10Sa'an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku. 11Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da yake zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku. 12Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.
(Fit 23.16; L. Fir 23.34-43)
13“Za ku yi Idin Bukkoki kwana bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku, da wurin matsewar ruwan inabinku. 14Sai ku yi murna a cikin idin, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku. 15Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna.
16“Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi. 17Kowane mutum zai kawo irin abin da ya iya, gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa masa.”
18“Sai ku naɗa alƙalai da shugabanni domin garuruwanku waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku bisa ga kabilanku. Sai su yi wa jama'a shari'a da adalci. 19Kada ku ɓata shari'a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali. 20Adalci ne kaɗai za ku sa gaba domin ku rayu, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
21“Kada ku dasa kowane irin itace na tsafi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku, wanda za ku gina. 22Kada kuma ku kafa al'amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”
1“Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya da sa ko da tunkiya da take da lahani ko naƙasa, gama wannan abar ƙyama ce ga Ubangiji Allahnku.
2“Idan aka sami wata, ko wani, daga cikin wani gari da Ubangiji Allahnku yake ba ku, yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku, yana karya alkawarinsa, 3har ya je, ya bauta wa gumaka, ya yi musu sujada, ko rana, ko wata, ko ɗaya daga cikin rundunar sama, ya yi abin da na hana, 4idan aka faɗa muku, ko kuwa kun ji labarinsa sai ku yi cikakken bincike. Idan gaskiya ce, aka kuma tabbata an yi wannan mugun abu cikin Isra'ilawa, 5to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. 6Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku za a kashe shi, amma ba za a kashe mutum a kan shaidar mutum ɗaya ba. 7Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.
8“Idan aka kawo muku shari'a mai wuyar yankewa a ɗakin shari'arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari'a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa. 9Za ku kai maganar wurin Lawiyawan da suke firistoci, ko kuma a wurin alƙalin da yake aiki a lokacin. Za ku tambaye su, za su faɗa muku yadda za a yanke shari'a. 10Sai ku yanke shari'ar yadda suka faɗa muku daga wurin da Ubangiji ya zaɓa. Ku lura fa, ku yi yadda suka faɗa muku. 11Dole ne ku yi yadda suka koya muku, da yadda suka yanke shari'ar. Kada ku kauce dama ko hagu daga maganar da suka faɗa muku. 12Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra'ilawa. 13Sa'an nan duk jama'a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”
14“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku don ku mallake ta, ku zauna a ciki, sa'an nan ku yi tunanin naɗa wa kanku sarki, kamar al'umman da suke kewaye da ku, 15to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba. 16Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, “‘Kada ku sāke komawa can.” 17Kada kuma ya auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace. Kada kuma ya tattara wa kansa kuɗi da yawa. 18Sa'ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci. 19Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai, 20don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi 'yan'uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu, don shi da 'ya'yansa su daɗe, suna mulki a Isra'ila.”
1“Lawiyawa da firistoci, wato dukan kabilar Lawi, ba su da rabo ko gādo tare da mutanen Isra'ila. Hadayun Ubangiji da dukan abin da ake kawo masa, su ne za su zama abincinsu. 2Ba za su sami gādo tare da 'yan'uwansu ba, Ubangiji ne gādonsu kamar yadda ya alkawarta musu.
3“To, ga rabon da jama'a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin. 4Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya. 5Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da 'ya'yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada.
6“Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra'ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa. 7Idan ya zo, sai ya yi aiki saboda sunan Ubangiji Allahnku kamar sauran 'yan'uwansa Lawiyawa waɗanda suke aiki a gaban Ubangiji a can. 8Zai sami rabon abincinsa daidai da saura, har da abin da yake na kakanninsa wanda ya sayar.”
9“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku shiga kwaikwayon ayyuka na banƙyama na waɗannan al'ummai. 10Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa 'yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri, 11ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha'ani da matattu. 12Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al'ummai a gabanku. 13Sai ku zama marasa aibu a gaban Ubangiji Allahnku.
14“Gama waɗannan al'ummai da za ku kora suna kasa kunne ga masu maita da masu duba, amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.
15“Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama'arku, sai ku saurare shi.
16“Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Ubangiji Allahnku a Horeb, a ranar taron, gama kun ce, “‘Kada ka bar mu mu ƙara jin muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don kada mu mutu,” 17Ubangiji kuwa ya ce mini, “‘Abin da suka faɗa daidai ne. 18Zan tayar musu da wani annabi kamarka daga cikin 'yan'uwansu. Zan sa magana a bakinsa, zai faɗa musu duk abin da na umarce shi. 19Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi. 20Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.”
21“Ya yiwu ku ce a zuciyarku, “‘Ƙaƙa za mu san maganar da Ubangiji bai faɗa ba?” 22Sa'ad da annabi ya yi magana da sunan Ubangiji, idan abin da ya faɗa bai faru ba, bai zama gaskiya ba, to, wannan magana ba Ubangiji ne ya faɗa ba. Wannan annabi ya yi izgili ne kawai, kada ku ji tsoronsa.”
(L. Ƙid 35.9-28; Josh 20.1-9)
1“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya hallaka al'ummai waɗanda zai ba ku ƙasarsu, sa'ad da kuka kore su, kuka zauna cikin garuruwansu da gidajensu, 2sai ku keɓe garuruwa uku a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka. 3Sai ku shirya hanyoyi, ku kuma raba yankin ƙasa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku ku mallaka kashi uku, domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can. 4Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā, 5misali, idan mutum ya tafi jeji, shi da abokinsa don su saro itace. Da ya ɗaga gatari don ya sari itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar, ya sari abokinsa har ya mutu. Irin wannan mai kisankai zai gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen don ya tsira, 6don kada mai bin hakkin jini ya bi shi da zafin fushinsa, ya cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā. 7Domin haka na umarce ku, ku keɓe wa kanku garuruwa uku.
8“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta wa kakanninku, har ya ba ku dukan ƙasar da ya alkawarta zai ba kakanninku, 9in dai kun lura, kun kiyaye umarnin da nake umartarku da shi yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa kullum, sa'an nan sai ku ƙara garuruwa uku a kan waɗannan uku ɗin kuma, 10don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku.
11“Amma idan wani mutum yana ƙin wani ya kuwa tafi ya yi fakonsa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, sa'an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin garuruwan nan, 12sai dattawan garinsu su aiko, a kamo shi daga can, sa'an nan su bashe shi ga mai bin hakkin jini don a kashe shi. 13Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra'ila, don ku sami zaman lafiya.
14“A cikin gādon da za ku samu a ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku ku mallaka, kada ku ci iyakar maƙwabcinku, wanda kakan kakanni suka riga suka kafa.”
15“Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum. 16Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani, 17sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin. 18Sai alƙalan su yi bincike sosai. Idan ɗan sharrin ya ba da shaidar zur a kan ɗaya mutumin, 19to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. 20Sauranku za su ji, su ji tsoro, ba za a ƙara aikata irin wannan mugunta ba. 21Kada ku ji tausayi, zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.”
1“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku. 2Sa'ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist ya zo gaba, ya yi magana da jama'a, 3ya ce musu, “‘Ku ji, ya ku Isra'ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su. 4Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, zai yaƙi magabtanku dominku, ya ba ku nasara.”
5“Sa'an nan shugabanni za su yi magana da jama'a, su ce, “‘Ko akwai wani mutum a nan wanda ya gina gidan da bai buɗe shi ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya yi bikin buɗewar. 6Ko akwai wani mutum wanda ya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani wani dabam ya ci amfaninta. 7Ko akwai wani mutum wanda yake tashin yarinya, amma bai aure ta ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani ya aure ta.”
8“Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama'a magana, su ce, “‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran 'yan'uwansa kuma su karai.” 9Sa'ad da shugabannin yaƙi suka daina yi wa jama'a jawabi, sai a zaɓi jarumawan sojoji don su shugabanci mutane.
10“Sa'ad da kuka kusaci gari don ku yi yaƙi, sai ku fara neman garin da salama. 11In ya yarda da salamar, har ya buɗe muku ƙofofinsa, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su bauta muku. 12Amma idan ya ƙi yin salama da ku, amma ya yi yaƙi da ku, sai ku kewaye shi da yaƙi. 13Idan Ubangiji Allahnku ya bashe shi a hannunku, sai ku karkashe dukan mazaje da takobi. 14Amma mata, da yara, da dabbobi, da dukan abin da yake cikin garin, da dukan ganimarsa, sai ku kwashe su ganima, ku mori ganimar magabtanku, wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku. 15Haka za ku yi da dukan garuruwan da suke nesa da ku, wato garuruwan da ba na al'umman da suke kusa da ku ba.
16“Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo. 17Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku, 18don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.
19“Sa'ad da kuka kewaye gari da yaƙi, kuka daɗe kuna yaƙi da shi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari har ku lalata su, gama za ku ci amfaninsu. Kada ku sassare su, gama itatuwan da suke cikin saura ba mutane ba ne, da za ku kewaye su da yaƙi. 20Sai dai itatuwan da kuka sani ba su ba da 'ya'ya, su ne za ku sassare, ku yi kagara da su saboda garin da kuke yaƙi da shi har ku ci garin.”
1“Idan aka iske gawar mutum wanda wani ya kashe a fili a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka, ba a kuwa san wanda ya kashe shi ba, 2sai dattawanku da alƙalanku su fito su auna nisan wurin daga gawar zuwa garuruwan da suke kewaye da gawar. 3Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba. 4Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar. 5Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci. 6Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin. 7Sa'an nan su ce, “‘Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba. 8Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.” 9Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”
10“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, Ubangiji Allahnku kuwa ya bashe su a hannunku, kun kuwa kama su bayi, 11in a cikinsu ka ga wata kyakkyawar mace wadda ka yi sha'awarta, to, ka iya aurenta. 12Sai ka kawo ta gidanka, ta aske kanta, ta yanke farcenta, 13ta tuɓe tufafin bauta. Sa'an nan sai ta zauna a gida tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta har wata ɗaya cif. Bayan haka ka iya shiga wurinta, ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka. 14In ka ji ba ka bukatarta, sai ka sake ta ta tafi inda take so, amma kada ka sayar da ita, kada kuma ka wahalshe ta, tun da yake ka riga ka ƙasƙantar da ita.”
15“Idan mutum yana da mata biyu, amma ya fi ƙaunar ɗayar, idan kuwa dukansu biyu, wato mowar da borar, suka haifi 'ya'ya, idan bora ce ta haifi ɗan fari, 16to, a ranar da zai yi wa 'ya'yansa wasiyya a kan gādon da zai bar musu, kada ya sa ɗan mowa ya zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan borar wanda shi ne ɗan farin, 17Amma sai ya yarda ya ba ɗan farin, wato ɗan borar, za a ba shi riɓi biyu na dukan abin da yake da shi gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.”
18“Idan mutum yana da gagararren ɗa wanda ba ya jin maganar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa, sun kuma hore shi, duk da haka bai ji ba, 19sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su kama shi, su kawo shi wurin dattawan garin a dandalin ƙofar gari. 20Sai su faɗa wa dattawan garinsu, su ce, “‘Wannan ɗanmu ne, gagararre, ba ya yi mana biyayya. Shi mai zari ne, mashayi!” 21Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”
22“Idan mutum ya yi laifin da ya isa mutuwa, aka rataye shi a itace har ya mutu, 23kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”
1“Idan kun ga ɓataccen san wani, ko tunkiyarsa, to, kada ku ƙyale shi, amma lalle sai ku komar da shi ga mai shi. 2Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa'an nan ku ba shi. 3Hakanan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su.
4“Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.
5“Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata. Duk mai yin haka, abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
6“Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da 'ya'yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa 'ya'yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan. 7Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe 'ya'yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.
8“Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.
9“Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku don kada abin da kuka shuka da amfanin gonar inabinku su zama haramiyarku.
10“Kada ku haɗa sa da jaki su yi huɗa tare.
11“Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.
12“Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.
13“Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa'an nan ya ƙi ta, 14yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, “‘Na auri wannan mata, amma sa'ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,” 15sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin. 16Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, “‘Na ba wannan mutum 'yata aure, amma ya ƙi ta. 17Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske 'yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin 'yata.” Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan. 18Sai dattawan garin su kama mutumin su yi masa bulala, 19su ci shi tara shekel ɗari na azurfa, su ba mahaifin yarinyar, gama a fili mutumin ya ɓata sunan budurwar cikin Isra'ila. Za ta zama matarsa, ba shi da iko ya sake ta muddin ransa.
20“Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba, 21sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
22“Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra'ila.
23“Idan a cikin gari wani ya iske budurwar da ake tashinta, ya kwana da ita, 24sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
25“Amma idan a saura wani ya fāɗa wa yarinyar da ake tashinta, har ya kwana da ita ƙarfi da yaji, sai a kashe wannan mutum. 26Amma ita yarinyar ba za a yi mata kome ba, domin ba ta yi laifin da ya isa mutuwa ba, gama wannan shari'a daidai take da ta mutumin da ya faɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi. 27Gama sa'ad da ya same ta a saura, ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta.
28“Idan wani ya iske yarinyar da ba a tashinta, ya kama ta, ya kwana da ita, aka kuwa same su, 29to, sai wanda ya kwana da ita ya ba mahaifinta shekel hamsin na azurfa, ita kuwa za ta zama matarsa, gama ya ci mutuncinta. Ba zai sake ta ba muddin ransa.
30“Kada mutum ya auri matar mahaifinsa, kada kuma ya kware fatarinta, gama na mahaifinsa ne.”
1“Duk wanda aka dandaƙe ko wanda aka yanke gabansa ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
2“Shege ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.
3“Kada Ba'ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama'ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba, 4domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku. 5Amma Ubangiji Allahnku ya ƙi saurarar Bal'amu, sai Ubangiji ya juyar da la'anar ta zama muku albarka saboda Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku. 6Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata.
7“Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa. 8'Ya'yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama'ar Ubangiji.”
9“Sa'ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu. 10Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin. 11Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa'ad da rana ta faɗi.
12“Za ku keɓe wani wuri a bayan sansani inda za ku riƙa zagayawa. 13Sai ku ɗauki abin tona ƙasa tare da makamanku. Lokacin da za ku zagaya garin yin najasa, sai ku tsuguna ku tona rami da abin tona ƙasa sa'an nan ku rufe najasar da kuka yi. 14Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”
15“Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa. 16Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi.
17“Kada Isra'ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini. 18Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa'adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
19“Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa. 20Kun iya ba baƙo rance da ruwa, amma kada ku ba danginku rance da ruwa don Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan abin da za ku yi a ƙasar da kuke shiga, ku kuma mallake ta.
21“Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba. 22Idan kun nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba. 23Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi wanda kuka alkawarta.
24“Sa'ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin 'ya'yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku. 25Sa'ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”
1“Idan mutum ya sami wata mata ya aura, amma idan ba ta gamshe shi ba saboda ya iske wani abu marar kyau game da ita, har ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, 2ta kuwa fita gidansa, idan ta je ta auri wani mutum dabam, 3idan shi kuma ya ƙi ta, ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, ko kuma idan ya mutu ne, 4to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.
5“Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”
6“Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne.
7“Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba'isra'ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.
8“Game da ciwon kuturta, sai ku lura ku bi daidai da yadda firistoci na Lawiyawa suka umarce ku, ku yi. Sai ku kiyaye, ku aikata yadda na umarce su. 9Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Maryamu a lokacin da kuka fito daga Masar.
10“Idan kun ba maƙwabcinku rance na kowane iri, kada ku shiga gidansa don ku ɗauki jingina. 11Sai ku tsaya a waje, mutumin da kuka ba shi rancen zai kawo muku jinginar. 12Amma kada ku yarda abin da aka jinginar ya kwana a wurinku idan mutumin matalauci ne. 13Sai ku mayar masa da shi a faɗuwar rana domin ya yi barci yafe da rigarsa ya gode muku. Yin haka zai zama muku adalci a wurin Ubangiji Allahnku.
14“Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku. 15Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku.
16“Kada a kashe ubanni maimakon 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.
17“Kada ku karkatar da shari'ar baƙo ko maraya. Kada kuma ku karɓi mayafin matar da mijinta ya rasu abin jingina. 18Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku ya fanshe ku daga can, saboda haka ina umartarku ku yi wannan.
19“Idan kun manta da wani dami a gona lokacin girbin amfanin gona, kada ku koma ku ɗauko. Ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan aikin hannuwanku. 20Sa'ad da kuka kakkaɓe 'ya'yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske. 21Sa'ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske. 22Sai ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, don haka nake umartarku ku yi wannan.”
1“Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin, 2idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi. 3Za a iya yi masa bulala arba'in, amma kada ta fi haka, don kada a ci gaba da bugunsa fiye da haka, har ya zama rainanne a idonku.
4“Kada ku yi wa takarkari takunkumi sa'ad da yake tattaka hatsinku.”
5“Idan 'yan'uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan'uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi. 6Ɗan farin da za ta haifa, zai zama magajin marigayin don kada a manta da sunansa cikin Isra'ila. 7Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, “‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.” 8Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, “‘Ba na so in aure ta,” 9sai matar ɗan'uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, “‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan'uwansa.” 10Za a kira sunan gidansa cikin Isra'ila, “‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.”
11“Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta, 12sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi.
13“Kada ku riƙe ma'aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami. 14Kada kuma ku ajiye mudu iri biyu a gidanku, wato babba da ƙarami. 15Sai ku kasance da ma'aunin nauyi da mudu masu kyau don ku daɗe a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 16Gama duk wanda yake aikata irin waɗannan abubuwa, da dukan marasa gaskiya, abin ƙyama ne su ga Ubangiji Allahnku.”
17“Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar. 18Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba. 19Domin haka sa'ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”
1“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta, 2to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. 3Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, “‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.”
4“Sa'an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku. 5Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, “‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa. 6Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu. 7Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana. 8Sai Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantsensa mai ƙarfi, mai iko, tare da bantsoro, da alamu, da mu'ujizai. 9Ubangiji ya kawo mu nan, ya ba mu ƙasar nan, ƙasar da take mai yalwar abinci. 10Ga shi, yanzu mun kawo nunan fari na amfanin ƙasar, da kai, ya Ubangiji, ka ba mu.” “Sai ku ajiye shi a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi sujada a gaban Ubangiji Allahnku. 11Ku yi murna kuma, ku da Lawiyawa, da baƙin da suke zaune tare da ku, saboda dukan alherin da Ubangiji Allah ya yi muku, ku da gidanku.
12“Sa'ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku. 13Sa'an nan za ku ce a gaban Ubangiji Allahnku, “‘Na fitar da tsattsarkan kashi daga cikin gidana na ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu bisa ga umarnin da ka yi mini. Ban karya wani umarninka ba, ban kuwa manta da su ba. 14Ban ci kome daga cikin zakar sa'ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa'ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni. 15Ka duba ƙasa daga Sama, daga wurin zamanka mai tsarki, ka sa wa jama'arka, Isra'ila, albarka duk da ƙasar da ka ba mu, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda ka rantse wa kakanninmu.”
16“Yau Ubangiji Allahnku yana umartarku ku kiyaye waɗannan dokoki da farillai. Sai ku lura ku aikata su da dukan zuciyarku da dukan ranku. 17Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya. 18Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama'arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa. 19Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”
1Musa da dattawan Isra'ila suka umarci jama'a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau. 2Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa. 3Sai ku rubuta kalmomin wannan shari'a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku. 4Sa'ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa. 5Can za ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a taɓa sassaƙa su da baƙin ƙarfe ba. 6Sai ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a sassaƙa ba. A bisa wannan bagade za ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. 7Za ku kuma miƙa hadayu na salama ku ci a wurin, ku yi ta murna a gaban Ubangiji Allahnku. 8Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.”
9Sai Musa da Lawiyawan da suke firistoci, suka ce wa Isra'ilawa, “Ku ji. Yau kun zama jama'ar Ubangiji Allahnku. 10Sai ku saurari muryar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa, da dokokinsa waɗanda muke umartarku da su yau.”
11A wannan rana kuma Musa ya umarci jama'a, ya ce, 12“Sa'ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama'a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu. 13Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la'anta, wato kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali. 14Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa:
15“‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
16“‘La'ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
17“‘La'ananne ne wanda ya ci iyakar maƙwabcinsa.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
18“‘La'ananne ne wanda ya karkatar da makaho daga hanya.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
19“‘La'ananne ne wanda ya yi wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa ta gaske shari'a ta rashin gaskiya.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
20“‘La'ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
21“‘La'ananne ne wanda ya kwana da dabba.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
22“‘La'ananne ne wanda ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
23“‘La'ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
24“‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
25“‘La'ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
26“‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.” “Sai dukan jama'a su amsa, “‘Amin, Amin!”
(L. Fir 26.3-13; M. Sh 7.12-24)
1“Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'umma. 2Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.
3“Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.
4“'Ya'yanku za su zama masu albarka, hakanan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku.
5“Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.
6“Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.
7“Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
8“Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.
9“Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama'arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa. 10Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku. 11Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da 'ya'ya, da 'ya'yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku. 12Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al'ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba. 13Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su, 14idan kuma ba ku kauce zuwa dama ko hagu daga maganar da na umarce ku da ita yau ba, wato don ku bi waɗansu gumaka, ku bauta musu.”
(L. Fir 26.14-46)
15“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku.
16“La'anannu za ku zama a gari da karkara.
17“La'anannu ne kwandunanku da makwaɓan ƙullunku.
18“La'anannu ne 'ya'yanku, da amfanin gonakinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da na awakinku.
19“Da la'ana za ku shiga, da la'ana kuma za ku fita.
20“Ubangiji zai aiko muku da la'ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni. 21Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 22Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace. 23Samaniya da yake bisa kanku za ta zama tagulla, ƙasar kuma da kuke a bisa kanta ta zama baƙin ƙarfe. 24Ubangiji zai mai da ruwan sama na ƙasarku gāri da ƙura, zai zubo muku da shi daga sama har ku hallaka.
25“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya. 26Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su. 27Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba. 28Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali. 29Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.
30“Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin. 31Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku. 32A idonku za a ba da 'ya'yanku mata da maza ga wata al'umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome. 33Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum. 34Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata. 35Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.
36“Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu. 37Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.
38“Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye. 39Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi. 40Za ku sami itatuwan zaitun ko'ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama 'ya'yan za su kakkaɓe. 41Za ku haifi 'ya'ya mata da maza, amma ba za su zama naku ba, gama za a kai su bauta. 42Ƙwari za su cinye dukan itatuwanku da dukan amfanin ƙasarku.
43“Baƙin da suke tare da ku za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya baya. 44Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45“Dukan waɗannan la'anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba. 46Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada. 47Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace, 48domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku. 49Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba, 50al'umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara. 51Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku. 52Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 53Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi. 54Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu, 55domin kada ya ba wani daga cikinsu naman 'ya'yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku. 56Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da 'yarta. 57A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da 'ya'yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
58“Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafin ba, domin ku ji tsoron sunana nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku, 59to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa. 60Sai ya sāke kawo muku cuce-cuce irin na Masar, waɗanda kuka ji tsoronsu, za su kuwa manne muku. 61Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka. 62Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama 'yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba. 63Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, hakanan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.
64“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba. 65Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al'ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. 66Kullum ranku zai kasance da damuwa, za ku zauna da tsoro dare da rana, kuna tsoron abin da zai sami ranku. 67Da safe za ku ce, “‘Da ma maraice ne.” Da maraice kuma za ku ce, “‘Da ma safiya ce,” saboda tsoron da yake a zuciyarku, da abubuwan da idanunku suke gani. 68Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.”
1Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra'ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb.
2Sai Musa ya kira dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir'auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar. 3Idanunku sun ga manyan wahalai, da alamu, da mu'ujizai masu girma. 4Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba. 5Shekara arba'in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba. 6Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku. 7Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su. 8Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda. 9Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.
10“Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra'ila, 11da 'ya'yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa. 12Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau. 13Don ya mai da ku jama'arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. 14Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba, 15amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu.
16“Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al'ummai muka wuce. 17Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya. 18Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci. 19Idan wani mutum ya ji zantuttukan la'anar nan sa'an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, “‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,” wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya. 20Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la'anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya. 21Ubangiji zai ware mutumin nan daga dukan kabilan Isra'ila, don ya hukunta shi bisa ga dukan la'anar da aka rubuta a wannan littafin dokoki.
22“Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato 'ya'yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata. 23Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa. 24Dukan al'ummai za su ce, “‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya sa ya yi fushi mai tsanani haka?” 25Sa'an nan jama'a za su ce, “‘Saboda sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, wato alkawarin da ya yi da su sa'ad da ya fisshe su daga ƙasar Masar. 26Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba. 27Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la'anar da aka rubuta a wannan littafin. 28Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.”
29“Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da 'ya'yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.”
1“Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku, 2kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau, 3sa'an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al'ummai inda ya warwatsa ku. 4Idan korarrunku suna can ƙurewar duniya, Ubangiji Allahnku zai tattaro ku daga can, ya dawo da ku. 5Ubangiji Allahnku kuma zai komo da ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, za ku mallake ta. Ubangiji zai arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku fiye da kakanninku. 6Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta 'ya'yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu. 7Ubangiji Allahnku kuwa zai ɗora wa magabtanku da maƙiyanku waɗanda suka tsananta muku waɗannan la'ana. 8Sa'an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau. 9Ubangiji Allahnku zai arzuta dukan aikin hannuwanku ƙwarai, ya kuma arzutar da 'ya'yanku da 'ya'yan shanu, da amfanin gona, gama Ubangiji zai ji daɗi ya arzuta ku kuma yadda ya ji daɗin kakanninku, 10idan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa da dokokinsa waɗanda suke rubuce a littafin dokokin nan, idan kuma kun juyo wurin Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.
11“Gama wannan umarni da na yi muku yau, bai fi ƙarfinku ba, bai kuma yi nisa da ku ba. 12Ba cikin Sama yake ba, balle ku ce, “‘Wa zai hau zuwa sama, ya sauko mana da shi don mu ji, mu kiyaye?” 13Ba kuma a hayin teku yake ba, balle ku ce, “‘Wa zai haye mana wannan teku don ya kawo mana shi don mu ji, mu kiyaye?” 14Amma umarnin yana kurkusa da ku, yana cikin bakinku da zuciyarku don ku kiyaye shi.
15“Ga shi yau, na sa rai da nagarta a gabanku, da mutuwa da mugunta. 16Idan kuka kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, idan kuma kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna yin tafiya cikin tafarkunsa, kuna kiyaye umarnansa, da dokokinsa, da farillansa, to, za ku rayu, ku riɓaɓɓanya, Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. 17Amma idan zuciyarku ta kangare kun ƙi ku saurara, amma zuciyarku ta janye ku kun yi wa gumaka sujada, kuka bauta musu, 18to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba. 19Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la'ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku. 20Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi biyayya da maganarsa, ku manne masa, gama wannan shi ne ranku da tsawon kwanakinku, don ku zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya rantse zai ba kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
1Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra'ilawa magana. 2Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, “‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.” 3Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al'ummar da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 4Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa'ad da ya hallaka su. 5Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku. 6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”
7Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama'ar Isra'ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama'a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo. 8Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”
9Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra'ila. 10Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki, 11sa'ad da dukan Isra'ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu. 12Ku tara dukan jama'a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan, 13domin 'ya'yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”
14Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada. 15Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al'amudin girgije. Al'amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.
16Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su. 17A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, “‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.” 18Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.
19“Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra'ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙar nan ta zama shaida a gare ni game da Isra'ilawa. 20Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina. 21Sa'ad da yawan masifun nan da wahalar nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”
22Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama'ar Isra'ila.
23Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama'ar Isra'ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”
24Sa'ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin, 25sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce, 26“Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku, 27gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata. 28Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu. 29Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”
30Sa'an nan Musa ya hurta kalmomin wannan waƙa a kunnen dukan taron jama'ar Isra'ila har ƙarshensu.
1“Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana, Bari duniya ta ji maganar bakina.
2Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, Maganata ta faɗo kamar raɓa, Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa, Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
3Gama zan yi shelar sunan Ubangiji, In yabi girman Allahnmu!
4“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5Sun aikata mugunta a gabansa, Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, Su muguwar tsara ce, karkatacciya,
6Haka za ku sāka wa Ubangiji, Ya ku wawaye, mutane marasa hikima? Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba, Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku>
7“Ku fa tuna da kwanakin dā, Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki, Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku, Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,
8Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu, Sa'ad da ya raba 'yan adam, Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.
9Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa, Yakubu shi ne rabon gādonsa.
10“Ya same shi daga cikin hamada, A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya kewaye shi, ya lura da shi, Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.
11Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta, Tana rufe da 'yan tsakinta, Ta buɗe fikafikanta, ta kama su, Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.
12Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi, Ba wani baƙon allah tare da shi.
13“Ya sa shi ya hau kan tuddai, Ya ci amfanin ƙasa, Ya sa shi ya sha zuma daga dutse, Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.
14Ya sami kindirmo daga shanu, Da madara daga garken tumaki da na awaki, Da kitse daga 'yan raguna, da raguna, Da bijimai, da bunsurai daga Bashan, Da alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.
15“Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska, Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul. Ya rabu da Allahn da ya yi shi, Ya raina Dutsen Cetonsa.
16Suka sa shi kishi, saboda gumaka, Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.
17Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba, Ga gumakan da ba su sani ba, Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya, Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
18Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku, Kun manta da Allahn da ya ba ku rai.
19“Ubangiji ya gani, ya raina su, Saboda tsokanar da 'ya'yansa mata da maza suka yi masa.
20Ya ce, “‘Zan ɓoye musu fuskata, Zan ga yadda ƙarshensu zai zama. Gama su muguwar tsara ce, 'Ya'ya ne marasa aminci.
21Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba, Suka tsokani fushina da gumakansu, Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba. Zan tsokane su da wawanyar al'umma.
22Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu.
23“‘Zan tula musu masifu, Zan ƙare kibauna a kansu,
24Za su lalace saboda yunwa, Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su. Zan aika da haƙoran namomi a kansu, Da dafin abubuwa masu jan ciki.
25Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, A cikin ɗakuna kuma tsoro, Zai hallaka saurayi da budurwa, Da mai shan mama da mai furfura.
26Na ce, “Zan watsar da su, In sa a manta da su cikin mutane.”
27Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi, Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara. Ai, ni ne na yi wannan.”
28“Gama su al'umma ce wadda ba ta yin shawara, Ba su da ganewa.
29Da suna da hikima, da sun gane wannan, Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!
30Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu, Mutum biyu kuma su kori zambar goma, Sai dai Dutsensu ya sayar da su, Ubangiji kuma ya bashe su>
31Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, Ko abokan gabanmu ma sun san haka.
32Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma ne Da gonakin Gwamrata. 'Ya'yan inabinsu dafi ne, Nonnansu masu ɗaci ne.
33Ruwan inabinsu dafin macizai ne. Da mugun dafin kumurci.
34“Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba, A ƙulle kuma a taskokina>
35Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne, A lokacin ƙafarsu za ta zame, Gama ranar masifarsu ta kusa, Hallakarsu za ta zo da sauri.
36Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa, Zai ji ƙan bayinsa, Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa, Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.
37Sa'an nan zai ce, “‘Ina gumakansu, Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,
38Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu, Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha? Bari su tashi su taimake ku, Bari su zama mafaka!
39“‘Ku duba fa, ni ne shi, Ba wani Allah, banda ni, Nakan kashe, in rayar, Nakan sa rauni, nakan kuma warkar, Ba wanda zai cece su daga hannuna.
40Na ɗaga hannuna sama, Na rantse da madawwamin raina,
41Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya, Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci, Zan ɗauki fansa a kan magabtana Zan sāka wa maƙiyana.
42Zan sa kibauna su bugu da jini, Takobina zai ci nama, Da jinin kisassu da na kamammu, Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.”
43“Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa, Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu, Zai ɗauki fansa a kan magabtansa, Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”
44Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama'a.
45Sa'ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra'ila, 46ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai. 47Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”
48A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa, 49“Ka hau duwatsun Abarim, wato Dutsen Nebo wanda yake a ƙasar Mowab, daura da Yariko, ka duba ƙasar Kan'ana wadda zan ba Isra'ilawa su mallaka. 50Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan'uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya. 51Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba. 52Za ka ga ƙasar da nake ba jama'ar Isra'ila, amma ba za ka shiga cikinta ba.”
1Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra'ilawa kafin ya rasu. 2Ya ce, “Ubangiji ya taho daga Sina'i, Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka, Ya taho tare da dubban tsarkakansa, Da harshen wuta a damansa.
3Hakika, yana ƙaunar jama'arsa, Dukan tsarkaka suna a ikonka, Suna biye da kai, Suna karɓar umarninka.
4Musa ya ba mu dokoki, Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu.
5Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun, Sa'ad da shugabanni suka taru, Dukan kabilan Isra'ila suka taru.
6“Allah ya sa Ra'ubainu ya rayu, kada ya mutu, Kada mutanensa su zama kaɗan.”
7A kan Yahuza ya ce, “Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji, Ka kawo shi wurin jama'arsa. Ka yi yaƙi da ikonka dominsu, Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”
8A kan Lawi ya ce, “Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka, Shi wanda ka jarraba a Masaha, Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba,
9Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, “‘Ban kula da ku ba.” Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne. Ya kuma ƙyale 'ya'yansa, Domin sun kiyaye maganarka, Sun riƙe alkawarinka.
10Suna koya wa Yakubu farillanka, Suna koya wa Isra'ila dokokinka. Suna ƙona turare a gabanka, Suna ƙona hadaya ta ƙonawa a bagadenka.
11Ya Ubangiji ka inganta jaruntakarsu, Ka karɓi aikin hannuwansu, Ka murƙushe ƙarfin abokan gābansu, Da waɗanda suke ƙinsu don kada su ƙara tashi.”
12A kan Biliyaminu, ya ce, “Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne, Yana zaune lafiya kusa da shi, Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini, Yana zaune a kan kafaɗunsa.”
13A kan Yusufu, ya ce, “Ubangiji ya sa wa ƙasarsa albarka, Da kyawawan kyautai daga sama, da raɓa, Da ruwan da yake a ƙasa,
14Da kyawawan kyautan da rana yake bayarwa, Da kyawawan kyautan da watanni suke bayarwa,
15Da abubuwa mafi kyau na duwatsun dā, Da kyawawan kyautai na madawwaman tuddai.
16Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, Da alherin wanda yake zaune a jeji. Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu, A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin 'yan'uwansa.
17Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take, Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke, Da su yake tunkwiyin mutane, Zai tura su zuwa ƙurewar duniya, Haka fa rundunan Ifraimu za su zama, Haka kuma dubban Manassa za su zama.”
18A kan Zabaluna ya ce, “Ka yi murna da tafiye-tafiyenka, ya Zabaluna, Kai kuma Issaka, cikin alfarwanka.
19Za su kira mutane zuwa dutse, Can za su miƙa hadayu masu dacewa, Gama za su ɗebo wadatar tekuna, Da ɓoyayyun dukiyar yashi.”
20A kan Gad, ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad, Gad yana sanɗa kamar zaki, Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai.
21Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau, Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba. Ya zo wurin shugabannin mutane, Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji, Ya kiyaye farillansa.”
22A kan Dan, ya ce, “Dan ɗan zaki ne, Mai tsalle daga Bashan.”
23A kan Naftali, ya ce, “Ya Naftali, ƙosasshe kake da alheri, Cike kake da albarkar Ubangiji. Sai ka mallaki tafki da wajen kudu.”
24A kan Ashiru, ya ce, “Ashiru mai albarka ne fiye da sauran 'yan'uwansa, Bari ya zama abin ƙauna ga 'yan'uwansa, Ya kuma tsoma ƙafarsa cikin mai.
25Kurfanka na baƙin ƙarfe ne da tagulla, Ƙarfinka ba zai rabu da kai ba muddin ranka.”
26“Babu wani kamar Allahn Yeshurun, Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka, Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa.
27Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka, Madawwaman damatsansa suna tallafarka, Yana kore maka maƙiyanka, Ya ce, “‘Ka hallaka su!”
28Da haka Isra'ila yana zaune lafiya, Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗai A ƙasa mai hatsi da ruwan inabi, Wurin da raɓa yake zubowa daga sama.
29Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”
1Sai Musa ya tashi daga filayen Mowab zuwa Dutsen Nebo, a ƙwanƙolin Fisga wanda yake daura da Yariko. Sai Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, tun daga Gileyad har zuwa Dan, 2da dukan Naftali, da ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, da dukan ƙasar Yahuza har zuwa Bahar Rum, 3da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar. 4Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”
5Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa. 6Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau. 7Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba. 8Isra'ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana talatin. Sa'an nan kwanakin kuka da makoki domin Musa suka ƙare.
9Joshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra'ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa.
10Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra'ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska. 11Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa. 12Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra'ilawa.