Ecclesiastes
1Maganar Mai Wa'azi ɗan Dawuda, Sarkin Urushalima.
2Banza a banza ne, in ji Mai Hadishi, Banza a banza ne, dukan kome banza ne.
3Wace riba ce mutum zai samu daga cikin aikinsa, Da yake yi a duniya>
4Zamani yakan wuce, wani zamani kuma ya zo, Amma abadan duniya tana nan yadda take.
5Rana takan fito, takan kuma faɗi, Sa'an nan ta gaggauta zuwa wurin fitowarta.
6Iska takan hura zuwa kudu, ta kuma hura zuwa arewa, Ta yi ta kewayawa, har ta koma inda ta fito.
7Kowane kogi yakan gangara zuwa teku, Amma har yanzu teku ba ta cika ba. Ruwan yakan koma mafarin kogin, Ya sāke gangarawa kuma.
8Kowane abu yana sa gajiya, Gajiyar kuwa ta fi gaban magana. Idanunmu ba sā ƙoshi da gani, Haka kuma kunnuwanmu ba sā ƙoshi da ji.
9Abin da ya faru a dā, shi zai sāke faruwa, Abin da aka yi a dā, shi za a sāke yi. A duniya duka ba wani abu da yake sabo.
10Da akwai wani abu da za a ce, “Duba, wannan sabon abu ne?” Abin yana nan tuntuni kafin zamaninmu.
11Ba wanda yake iya tunawa da abin da ya faru a dā, Da abin da zai faru nan gaba. Ba wanda zai iya tunawa da abin da zai faru A tsakanin wannan lokaci da wancan.
12Ni Mai Hadishi sarki ne, na sarauci Isra'ilawa a Urushalima. 13Na ɗauri aniya in jarraba, in bincika dukan abubuwan da ake yi a duniyar nan. Allah ya ƙaddara mana abu mai wuya. 14Na ga dukan abin da ake yi a duniya, duk aikin banza ne da ɓata lokaci kawai. 15Ba za a iya miƙar da abin da ya tanƙware ba, ba kuma za a iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16Na ce wa kaina, “Na zama babban mutum, na fi duk wanda ya taɓa mulkin Urushalima hikima. Hakika na san hikima da ilimi.” 17Na ɗaura aniya in san bambancin da yake tsakanin ilimi da wauta, da a tsakanin hikima da gāɓanci. Amma na gane harbin iska nake yi kawai. 18Gwargwadon hikimarka gwargwadon damuwarka, gwargwadon ƙarin iliminka gwargwadon jin haushinka.
1Na sa rai in ji wa kaina daɗi, in kuma san yadda farin ciki yake. Sai na tarar wannan ma aikin banza ne. 2Na kuma gane dariya wauta ce, nishaɗi kuma ba shi da wani amfani. 3Muradina shi ne in san hikima in nemi yadda zan ji wa raina daɗi da ruwan inabi, in sa kaina ga aikata wawanci. Bisa ga tsammanina mai yiwuwa ne wannan shi ne abu mafi kyau da mutane za su yi a duniya, a 'yan kwanakinsu.
4Na kammala manyan abubuwa. Na gina wa kaina gidaje, na yi gonakin inabi. 5Na kuma yi wa kaina lambuna da gonakin itatuwa, ba irin itatuwa masu 'ya'ya da ba su a ciki. 6Na yi tafkuna na yi wa itatuwana banruwa. 7Na sayo bayi mata da maza, an kuma haifa mini cucanawa a gidana. Ina kuma da manyan garkunan shanu, da na tumaki, da na awaki fiye da dukan wanda ya taɓa zama a Urushalima. 8Na tara wa kaina azurfa, da zinariya, daga baitulmalin ƙasashen da nake mulki. Mawaƙa mata da maza suna raira mini waƙa, ina da dukan irin matan da kowane namiji zai so.
9I, na ƙasaita fiye da dukan waɗanda suka riga ni zama a Urushalima. Hikimata kuma ba ta taɓa a rabuwa da ni ba. 10Duk abin da nake so, na samu, ban taɓa hana wa kaina kowane irin nishaɗin da nake so ba. Ina fāriya da kowane irin abin da na aikata. Wannan shi ne ladana na dukan aikina. 11Na yi tunani a kan dukan abin da na aikata, da irin wahalar da na sha lokacin da nake yin aikin, sai na gane ba shi da wata ma'ana, na zama kamar mai harbin iska, ba shi da wani amfani. 12Bayan wannan duka, abin da sarki zai iya yi kaɗai, shi ne abin da sarakunan da suka riga shi suka yi. Sai na fara tunani a kan abin da ake nufi da hikima, ko rashin kula, ko wauta. 13To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu. 14Mai hikima ya san inda ya nufa, amma wawa ba zai iya sani ba. Na kuma sani makomarsu guda ce. 15A zuciyata na ce, “Abin da yakan sami wawa shi ne kuma zai same ni. To, wace riba na ci ke nan saboda hikimar da nake da ita?” Na kuma ce a zuciyata, “Wannan ma aikin banza ne.” 16Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba, nan gaba za a manta da dukansu. Yadda mai hikima yake mutuwa haka ma wawa yake mutuwa. 17Saboda haka rai ba wani abu ba ne a gare ni, domin dukan abin da yake cikinsa bai kawo mini kome ba sai wahala. Duka banza ne, ba abin da nake yi sai harbin iska kawai.
18Daga cikin dukan abin da na samu kan aikin da na yi, ba su da wata ma'ana a gare ni, gama na sani zan bar wa magājina ne. 19Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne. 20Na yi baƙin ciki a kan dukan wahalar aikin da na yi a duniya. 21Kai ne ka yi aiki da dukan hikimarka, da iliminka, da gwanintarka, amma kuma tilas ka bar shi duka ga wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma bai amfana kome ba, mugun abu ne. 22Me mutum zai samu daga cikin aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin? 23Dukan abin da yake yi a kwanakinsa, ba abin da ya jawo masa, sai damuwa da ɓacin zuciya. Da dare ma ba ya iya hutawa. Wannan kuma aikin banza ne duka.
24Ba abin da ya fi wa mutum kyau fiye da ya ci, ya sha, ya saki jiki, ya ci moriyar aikinsa. Na gane wannan ma daga wurin Allah ne. 25Ƙaƙa za ka sami abin da za ka ci, ko ka ji daɗin zamanka in ba tare da shi ba? 26Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.
1Dukan abin da yake faruwa a duniyar nan yakan faru ne a cikin lokacin da Allah ya so.
2Shi yake sa lokacin haihuwa, da lokacin mutuwa, Da lokacin dashe, da lokacin tumɓuke abin da aka dasa,
3Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa, Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.
4Shi ne kuma yake sa lokacin yin kuka, da lokacin yin dariya, Da lokacin yin makoki, da lokacin yin murna,
5Da lokacin warwatsa duwatsu, da lokacin tattarawa, Da lokacin rungumewa, da lokacin da ba a yi.
6Shi ne kuma yake sa lokacin nema, da lokacin rashi, Da lokacin adanawa, da lokacin zubarwa,
7Da lokacin ketawa, da lokacin gyarawa, Da lokacin yin shiru, da lokacin magana.
8Shi ne kuma yake sa lokacin ƙauna, da lokacin ƙiyayya, Da lokacin yaƙi, da lokacin salama.
9Wace riba mutum zai ci a kan dukan aikinsa? 10Na san hukuncin da Allah ya ɗora mana mu yi ta fama da shi. 11Shi ya sa wa kowane abu lokacinsa. Shi ne kuma ya sa mana buri mu san abin da yake nan gaba, amma fa bai ba mu cikakken sanin ayyukan da yake yi ba, tun daga farko har zuwa ƙarshe. 12Na gane iyakar abin da mutum zai yi, shi ne ya yi farin ciki, ya yi abin kirki tun yana da rai. 13Dukanmu mu ci, mu sha, mu yi murna da abin da muka yi aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.
14Na sani dukan abin da Allah ya yi zai dawwama, ba abin da za a ƙara, ko a rage. Allah ya yi haka kuwa domin mutane su zama masu tsoronsa. 15Dukan abin da ya faru, ya riga ya faru a dā. Allah ya sa abin da ya faru ya yi ta faruwa. Allah yana hukunta abin da ya riga ya faru.
16Banda wannan kuma, na gane a duniyar nan mugunta ta gāje matsayin adalci da na abin da yake daidai. 17Sai na ce a zuciyata, “Da adali, da mugu, Allah zai shara'anta su, domin an ƙayyade lokaci na yin kowane abu da na yin kowane aiki.” 18Na dai ce Allah yana jarraba mutum ne domin ya nuna masa bai ɗara dabba ba. 19Gama makomar 'yan adam da ta dabbobi ɗaya ce, yadda ɗayan yake mutuwa haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne. Mutum bai fi dabba ba, gama rai ba shi da wata ma'ana ga kowannensu. 20Dukansu wuri ɗaya za su tafi, gama dukansu biyu daga turɓaya suka fito, dukansu biyu kuma za su koma cikinta. 21Wa zai iya tabbatarwa, cewa ruhun mutum zai tafi sama, ruhun dabba kuwa zai tafi ƙasa? 22Na gane abin da ya fi wa mutum, shi ne ya more wahalar aikinsa, gama ba wani abu da zai iya yi. Ba wata hanya da zai san abin da zai faru bayan mutuwarsa.
1Sa'an nan na sāke dubawa a kan rashin adalcin da yake ci gaba a duniyar nan. Waɗanda ake zalunta suna kuka, ba kuwa wanda zai taimake su, domin waɗanda suke zaluntarsu suke da iko. 2Ina ƙyashin waɗanda suka mutu, gama sun fi waɗanda suke da rai yanzu jin daɗi. 3Amma wanda ya fi su jin daɗi duka, shi ne wanda bai taɓa rayuwa ba, balle ya ga rashin adalcin da yake ta ci gaba a duniyar nan.
4Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai. 5Za su ce, “Wawa ne zai ƙi yin aiki, ya zauna har yunwa ta kashe shi.” 6Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai, da tafin hannu biyu cike da tashin hankali, harbin iska ne kawai.
7Na kuma ga wani abu a zaman mutum, wanda bai amfana kome ba, 8mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.
9Biyu sun fi ɗaya, gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu. 10Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya faɗi yana shi kaɗai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi. 11Idan mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna, amma ƙaƙa mutum ɗaya zai ji ɗumi? 12Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa. 13-14Mutum yana iya tashi daga matsayin talauci ya zama sarki a ƙasarsa, ko ya fita daga kurkuku ya hau gadon sarauta. Amma lokacin da sarki ya tsufa, idan wautarsa ta hana shi karɓar shawara, bai fi saurayin ɗin da yake talaka mai basira ba. 15Na yi tunani a kan dukan mutanen da suke zaune a duniyar nan, sai na gane a cikinsu akwai saurayin da zai maye matsayin sarkin. 16Mutanen da sarki yake mallaka suna da yawan gaske. Amma bayan ba shi ba wanda zai gode masa saboda ayyukan da ya yi. Hakika wannan ma aikin banza ne, harbin iska kawai.
1Ka yi hankali lokacin da kake shiga Haikali. Gara ka tafi can da niyyar koyon wani abu, da ka miƙa hadaya kamar waɗansu wawaye da ba su san halal da haram ba. 2Yi tunani kafin ka yi magana, kada ka yi wa Allah wa'adi na gaggawa. Allah yana Sama kai kuwa kana duniya. Don haka kada ka faɗa fiye da abin da ya kamata. 3Yawan damuwarka yana iya sa ka yi mafarkai. Yawan maganarka kuma yana iya sa ka ka yi maganar wauta. 4Sa'ad da ka yi wa'adi ga Allah, yi hanzari ka cika, gama wawa ba shi da wani amfani a gare shi. Sai ka cika wa'adin da ka yi! 5Gara kada ka yi wa'adi, da ka yi wa'adi, amma ba ka cika ba. 6Kada ka bar maganar bakinka ta kai ka ga yin zunubi, har ka ce wa manzon Allah, ba haka kake nufi ba. Don me za ka sa Allah ya yi fushi da kai, har ya hallakar da abin da ka yi wahalarsa? 7Yawan mafarkanka, da dukan ayyukanka, da yawan maganganunka duk banza ne, duk da haka ya fi maka amfani ka yi tsoron Allah.
8Idan ka ga hukuma na zaluntar talakawa, ba ta yi musu adalci, ba ta kiyaye hakkinsu, kada ka yi mamaki. Kowane shugaba yana da shugaban da yake goyon bayansa. Dukansu biyu suna da goyon bayan manyan shugabanni.
9Abin da ƙasa take bukata, shi ne sarkin da yake kulawa da aikin gona.
10Idan kana ƙaunar kuɗi, daɗi ba zai ishe ka ba, wanda kuma yake ƙaunar dukiya, ba zai ƙoshi da riba ba, wannan kuma aikin banza ne. 11Gwargwadon dukiyarka gwargwadon mutanen da za ka ciyar, ribarka kaɗai ita ce sanin kana da dukiya. 12Ma'aikaci, ko yana da isasshen abinci, ko ba shi da isasshe, duk da haka yakan ji daɗin barcinsa da dare. Amma mawadaci yakan kwana bai rintsa ba, saboda yawan tunani.
13Wani mugun abu da na gani a duniyar nan, shi ne mutane sun ajiye kuɗi domin lokacin da za su bukace su. 14Amma sukan lalace saboda muguwar ma'amala, har ba abin da ya ragu da za su bar wa 'ya'yansu gado. 15Mukan bar duniyar nan kamar yadda muka shigo ta, ba mu da kome. Dukan ayyukanmu, ba abin da za mu ɗauka mu tafi da shi. 16Wannan mugun abu ne, mukan tafi kamar yadda muka zo. Mukan yi aiki, muna ƙoƙari mu kama iska, me muka samu ke nan? 17Mun yi zamanmu a duhu, da baƙin ciki, da damuwa, da fushi, da cuta.
18Ga abin da na gani yana da kyau, ya kuma dace, shi ne kurum mutum ya ci, ya sha, ya ji daɗin aikin da ya yi a 'yan kwanakin rai da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum. 19Duk wanda Allah ya ba wadata da dukiya ya kuma bar shi ya ci moriyarsu, sai ya yi godiya ya ci moriyar aikin da ya yi, wannan kyauta ce ta Allah. 20Tun da yake Allah ya yarje masa, ya zauna da farin ciki, ba ya cika damuwa saboda rashin tsawon kwanaki.
1Na kuma lura, a duniyar nan an yi wa ɗan adam rashin adalci ƙwarai. 2Allah yakan ba wani mutum dukiya, da daraja, da wadata, i, da kowane abu da yake bukata. Amma bai ba shi iko ya more su ba. A maimakonsa wani baƙo ne zai more su. Wannan aikin banza ne ba kuwa daidai ba ne. 3Mai yiwuwa ne mutum ya haifi 'ya'ya ɗari ya kuma yi tsawon rai, amma kome tsawon ransa ba wani abu ba ne idan ba shi da farin ciki, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba. Sai na ce, gara jaririn da aka haifa matacce da shi. 4Haihuwar ba ta amfane shi kome ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.
7Dukan wahalar da ɗan adam yake yi ta samun abinci ce, amma duk da haka bai taɓa ƙoshi ba. 8Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce kuma matalaucin da ya iya zama da mutane zai samu? 9Abin da ya zo hannu ya fi dogon buri gama dogon buri aikin banza ne, harbon iska kawai.
10Kowane abu da ya kasance, an riga an ba shi suna, yadda aka yi mutum haka zai zama. Ba kuwa zai iya gardama da abin da ya fi ƙarfinsa ba. 11Yawan magana yakan ɓata al'amari. Wane amfani zai yi wa mutum? 12Wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a 'yan kwanakinsa marasa amfani? Sukan wuce kamar inuwa. Wa kuma zai iya faɗa wa mutum abin da zai faru a duniya bayan rasuwarsa>
1Kyakkyawan suna ya fi man ƙanshi tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwa.
2Gara a tafi gidan da ake makoki Da a tafi gidan da ake biki, Gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane Ya kamata duk mai rai ya riƙe wannan a zuciyarsa, Mutuwa tana jiran kowa.
3Baƙin ciki ya fi dariya, Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
4Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa, Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.
5Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima, Da ya ji wawaye suna yabonsa.
6Dariyar wawa kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya ce. Wannan ma aikin banza ne.
7Hakika zalunci yakan sa mai hikima ya zama wawa, Karɓar rashawa kuma yakan lalata hali.
8Gara ƙarshen abu da farkonsa. Mai haƙuri kuma ya fi mai girmankai.
9Ka kame fushinka, Gama wawa ne yake cike da fushi.
10Kada ka yi tambaya, cewa me ya sa zamanan dā suka fi na yanzu? Gama wannan tambaya ba ta hikima ba ce.
11Ya kamata kowane mutum ya zama mai hikima, Gama tana da kyau kamar cin gādo.
12Hikima mafaka ce, takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita, ita ce amfanin ilimi.
13Ka yi tunanin aikin Allah, Wa ya isa ya miƙe abin da ya tanƙware>
14In kana jin daɗi, ka yi murna, In kuma wahala kake sha, ka tuna, Allah ne ya yi duka biyunsa, Don kada mutum ya san abin da zai faru a nan gaba.
15A kwanakina marasa amfani na ga kowane irin abu. Adali ba safai yakan yi tsawon rai ba, mugu kuwa yakan yi tsawon rai a mugayen ayyukansa. 16Kada ka cika yin adalci, kada kuma ka cika yin hikima, gama don me za ka kashe kanka? 17Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, gama don me za ka mutu tun kwanakinka ba su cika ba? 18Idan ka riƙe wannan zai amfane ka. Kada ka bar wancan, gama shi wanda yake tsoron Allah zai yi amfani da su.
19Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.
20Ba wani mutum a duniyar nan wanda yake aikata abin da yake daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.
21Kada ka kula da kowane abu da mutane suke faɗa, mai yiwuwa ne ka ji baranka yana zaginka. 22Kai kanka ka sani sau da yawa kakan zagi waɗansu mutane.
23Na yi amfani da hikimata don in jarraba wannan duka, domin na ɗaura aniya in zama mai hikima, amma abin ya fi ƙarfina. 24Wane ne zai iya sanin gaibi? Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa. 25Amma na duƙufa neman ilimi, ina ta yin nazari, ina nema in san hikima da amsoshin tambayoyina, in kuma san mugunta da wautar dakikanci.
26Sai na iske wani abu da ya fi mutuwa ɗaci, wato mace wadda ƙaunar da take yi maka za ta kama ka kamar tarko, kamar kuma raga. Rungumewar da za ta yi maka za ta ɗaure ka kamar sarƙa. Wanda Allah yake jin daɗinsa zai tsere mata, amma za ta kama mai zunubi. 27Haka ne, in ji Mai Hadishi, da kaɗan da kaɗan na gane wannan sa'ad da nake neman amsa. 28Amsar da nake nema ban samu ba. Na sami mutum ɗaya mai hikima, wato a cikin mutum dubu, amma daga cikin mata ban sami ko ɗaya ba. 29Wannan ne kaɗai abin da na gane, tsaf Allah ya yi mu, amma mu muka rikitar da kanmu.
1Mutum mai hikima ne kaɗai ya san ainihin ma'anar yadda abubuwa suke. Hikima takan sa shi fara'a, da sakin fuska.
2Ka kiyaye umarnin sarki saboda alkawarin da ka ɗauka. 3Sarki yana iya yin kowane abu da ya ga dama, don haka ka guje wa wurin da yake, kada ka zauna a wuri mai hatsari haka. 4Da iko sarki yake aiki, don haka ba mai iya ce masa, “Don me?”
5Muddin ka kiyaye umarnin sarki gidanka lafiya, mai hikima yakan yi abu, ya kuma san lokacin yi da hanyar da ta dace da yinsa. 6Akwai lokacin da ya dace, da hanyar da ta dace na yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa. 7Ko ɗaya daga cikinmu ba wanda ya san abin da zai faru, wane ne zai faɗa mana? 8Ba wanda zai iya hana kansa mutuwa, ko ya dakatar da ranar mutuwarsa. Idan yaƙi ya zo ba makawa, ba yadda za mu yi mu zurare.
9Na ga wannan duka a sa'ad da nake tunani a kan abubuwan da ake yi a duniyar nan, duniyar da waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu. 10Hakika na ga an kai mugaye an binne, amma a birnin nan inda suka aikata wannan mugun abu, mutane suna yabonsu, amma sun kuma manta da su. Wannan kuma aikin banza ne.
11Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan. 12Ko da yake mugun mutum ya aikata laifofi sau ɗari, amma kuwa ya rayu, duk da haka na sani idan kana tsoron Allah kome zai tafi daidai. 13Ga mugaye ba zai tafi daidai ba, kamar inuwa ransu yake. Za su yi mutuwar ƙuruciya domin ba su da tsoron Allah. 14Dubi aikin banza da yake faruwa a duniya. Wani lokaci adalai suke shan hukuncin da za a yi wa mugaye, mugaye kuwa su karɓi sakayyar da za a ba adalai. Na ce wannan ma aikin banza ne.
15Abin da na ce, shi ne mutum ya ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne ya ci, ya sha, ya ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakinsa wanda Allah ya ba shi a wannan duniya.
16A duk lokacin da nake ƙoƙari in zama mai hikima, in san abin da yake faruwa a duniya, sai na gane, ko da a ce mutum ba zai yi barci ba dare da rana, 17sam, ba zai taɓa fahimtar abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.
1Na daɗe ina tunani ƙwarai a kan wannan abu duka, yadda Allah yake sarrafa ayyukan masu hikima da na adalai, har da ƙaunarsu da ƙiyayyarsu. Ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba. 2Ba wani bambanci. Makoma ɗaya ce, ta adali da ta mugu, da ta mutumin kirki da ta marar kirki, da ta tsattsarka da ta marar tsarki, da ta masu yin sujada da ta marasa yi. Mutumin kirki bai fi mai zunubi ba. Wanda ya yi rantsuwa bai fi wanda bai yi ba. 3Duk makomarsu ɗaya ce, wannan ita ce ɓarnar da take faruwa a duniya. Muddin mutane suna da rai tunaninsu cike yake da mugunta da rashin hankali. Bayan haka sukan mutu. 4Amma dukan wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki. 5Hakika rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da wani sauran lada nan gaba, an manta da su ke nan sam. 6Ƙaunarsu, da ƙiyayyarsu, da kishinsu sun mutu tare da su. Ba za su ƙara yin wani abu da ake yi a duniya ba.
7Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. 8Ka yi farin ciki da fara'a kullum. 9Ka yi nishaɗi da matar da kake ƙauna, dukan kwanakin ranka na banza waɗanda Allah ya ba ka a wannan duniya, ka more kowace rana, wannan ne kaɗai rabonka na wahalar aikinka a duniya. 10Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.
11Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyar nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa'a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu. 12Gama mutum bai san lokacinsa ba, kamar kifayen da akan kama da taru, kamar kuma tsuntsayen da akan kama da tarko, hakanan mugun lokaci yakan auko wa 'yan adam farat ɗaya.
13A duniyar nan na ga wani babban al'amari game da hikima. 14Dā akwai wani ɗan ƙaramin gari, mutane kuma suke ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani. 15Akwai wani matalauci, mai hikima, a garin, sai ya ceci garin ta wurin hikimarsa. Duk da haka ba wanda ya tuna da wannan matalauci. 16Na ce hikima ta fi ƙarfe ƙarfi, ko da yake an raina hikimar matalauci da maganarsa. 17Gara a kasa kunne ga tattausar maganar mai hikima, da a kasa kunne ga hargagin mai mulki a tsakanin wawaye. 18Hikima ta fi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan yi ɓarna mai yawa.
1Matattun ƙudaje sukan sa man ƙanshi ya yi wari, hakanan wauta kaɗan takan ɓata hikima da daraja.
2Zuciyar mai hikima takan kai shi ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan kai shi ga yin mugun abu. 3Ko lokacin da wawa yake tafiya a hanya, yakan nuna ba shi da hankali, yakan kuma bayyana wa kowa shi wawa ne.
4Idan mai mulki ya husata da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
5Akwai mugunta wadda na gani a duniya, wato kuskuren da masu mulki suke yi. 6Ana ba wawaye manyan matsayi, attajirai kuwa ana ƙasƙantar da su. 7Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, shugabanni kuwa suna tafiya a ƙasa kamar bayi.
8Wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki. Wanda kuma ya rushe katanga, shi maciji zai sara. 9Wanda yake farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni. Wanda kuma yake faskare itace yana cikin hatsarinsu. 10Idan gatari ya dakushe ba a wasa shi ba, dole ne a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma hikima takan taimake shi ya ci nasara. 11Idan maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi kuma, ba shi da wani amfani. 12Maganar mai hikima alheri ce, amma maganganun wawa za su hallaka shi. 13Farkon maganganunsa wauta ne, ƙarshensu kuma mugunta ne da hauka. 14Wawa ya cika yawan surutu. Wa ya san abin da zai faru nan gaba? Wa zai iya faɗa masa abin da zai raru bayan rasuwarsa>
15Wahalar wawa takan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.
16Kaitonki, ya ƙasa wadda sarkinki yaro ne, shugabanninki kuma suna ta shagalinsu tun da safe. 17Mai farin ciki ce, ke ƙasar da sarkinki mai dattako ne, shugabanninki kuma suka ci a kan kari don su sami ƙarfi, ba domin su bugu ba.
18Saboda lalaci ɗaki yakan yi yoyo, sai tsaiko ya lotsa.
19Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma ba za ka sami ko ɗaya ba, sai idan kana da kuɗi.
20Kada ka zagi sarki ko a cikin zuciyarka, kada kuma ka zagi mawadaci a cikin ɗakin kwananka, gama tsuntsu zai kai maganarka, wani taliki mai fikafikai zai tone asirinka.
1Ka jefa kyautarka a baya, ka tsince ta a gaba. 2Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.
3Idan gizagizai sun cika da ruwa sukan sheƙar da shi ƙasa. A inda itace ya faɗi, a nan zai kwanta, ko wajen kudu ko arewa. 4Wanda yake la'akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la'akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba. 5Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri suke girma a mahaifar uwarsa, hakanan kuma ba ka san aikin Allah ba, wato wanda ya yi abu duka. 6Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
7Haske yana da daɗi, abu mai kyau kuma idanu su dubi hasken rana. 8Idan mutum ya rayu har shekaru da yawa, bari ya yi murna a cikinsu duka. Sai dai kuma ya tuna da kwanakin duhu, gama sun fi yawa. Duk abin da ya faru banza ne.
9Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha'awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al'amuran nan duka Allah zai shara'anta ka.
10Kada ka bar kome ya dame ka, ko ya yi maka zafi a rai, gama ƙuruciya da samartaka ba za su dawwama ba.
1Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin samartakarka kafin mugayen kwanaki da shekaru su zo, da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu.” 2Wato lokacin da rana, da haske, da wata, da taurari za su duhunta, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙar da ruwa. 3A lokacin nan hannuwanka da suke kāre ka, za su yi makyarkyata, ƙafafunka za su rasa ƙarfi. Haƙora kaɗan za su ragu a bakinka. Idanunka za su duhunta. 4Bakinka a rufe yake, haƙora ba su tauna abinci. Muryar tsuntsu za ta farkar da kai. Ba za ka iya jin muryar mawaƙa ba. 5Sa'an nan za ka ji tsoron hawan tudu, tafiya kuma za ta yi maka wuya. Gashin kanka zai furfurce. Za ka ja jikinka. Ba sauran sha'awar mace. Daganan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna. 6Hakika, ka tuna da Mahaliccinka kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe, ko tulu ya fashe a bakin rijiya, ko igiya ta tsinke a bakin tafki, 7sa'an nan turɓaya ta koma ƙasa kamar a dā, ruhu kuma ya koma wurin Allah wanda ya ba da shi.
8Banza a banza, duk banza ne, in ji Mai Hadishi. Duk a banza ne.
9Saboda hikimar Mai Hadishi ya koya wa mutane ilimi. Ya auna, ya bincika, ya tsara karin magana da lura sosai. 10Ya nemi kalmomi, ya rubuta su daidai. 11Kalmomin mutane masu hikima kamar sanduna suke da makiyaya suke amfani da su, su bi da tumaki.
12Ya ɗana, ka yi hankali, kada ka zarce waɗannan, gama wallafa littattafai ba shi da iyaka, yawan karatu kuma gajiyar da kai ne!
13Bayan wannan duka, makasudin maganar shi ne, ka yi tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum. 14Allah zai shara'anta kowane irin aiki, ko a ɓoye aka yi shi, ko nagari ne, ko mugu.