Ephesians

WASIƘAR BULUS ZUWA GA
Afisawa

1

Gaisuwa

1Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.

2Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Albarku na Ruhu a cikin Almasihu

3Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu, 4domin kuwa ya zaɓe mu a cikin Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa. 5Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri, 6domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa. 7Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah, 8wanda ya falala mana. Da matuƙar hikima da basira 9ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu. 10Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.

11A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi, 12domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa. 13A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa'ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta. 14Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.

Addu'a don Hikima da Sani

15Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka, 16ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa'ad da nake yi muku addu'a, 17da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah, 18a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka, 19da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa, 20wanda ya zartar ga Almasihu sa'ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya, 21a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma. 22Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka. 23Ikilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.

2

Daga Mutuwa zuwa Rai

1Ku kuma zai raya ku sa'ad da kuke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku, 2waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu. 3Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam. 4Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana, 5ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku), 6a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya. 7Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu. 8Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah, 9ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya. 10Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

Zama Ɗaya da Almasihu

11Saboda haka, ku tuna dā ku al'ummai ne bisa ɗabi'a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). 12Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama'ar Isra'ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya. 13Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu. 14Domin Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya mai da Yahudawa da al'ummai ɗaya, wato ya rushe katangar nan da ta raba su a kan gāba. 15Har ya soke Shari'ar nan mai umarni da dokoki, ta wurin ba da jikinsa, domin ta gare shi yă halicci sabon mutum guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă kawo salama, 16yă kuma sulhunta su duka biyu ga Allah, su zama jiki ɗaya ta wurin gicciye, ta haka yă kashe gābar. 17Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. 18Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda. 19Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan 'yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma, 20waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin, 21dukan wanda aka haɗa tsarin ginin a cikinsa, yana kuma tashi ya zama haikali tsattsarka na Ubangiji. 22A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.

3

Hidimar Bulus ga Al'ummai

1Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai, 2in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku, 3wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice. 4A yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata saboda asirin Almasihu, 5wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu, 6wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.

7An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa. 8Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa, 9in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa. 10An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masa iko a samaniya, ta hanyar Ikilisiya. 11Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 12A cikinsa muke da gabagaɗin isa ga Allah, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu a gare shi. 13Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

A San Ƙaunar Almasihu

14Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban, 15shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna, 16ina addu'a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa, 17har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku, 18har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta, 19ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.

20Ɗaukaka tă tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu. 21Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a cikin Ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai har abada abadin. Amin.

4

Ɗayantuwar Ruhu

1Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku, 2da matuƙar tawali'u, da salihanci, da haƙuri, kuna jure wa juna saboda ƙauna. 3Da ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar da Ruhu yake zartarwa, kuna a haɗe a cikin salama. 4Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan. 5Ubangiji guda ne, bangaskiya guda, da kuma baftisma guda. 6Allah ɗaya ne, Ubanmu duka, wanda yake bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma. 7Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu. 8Saboda haka, Nassi ya ce, “Sa'ad da ya hau Sama ya bi da rundunar kamammu, Ya kuma yi wa 'yan adam baye-baye.”

9(Wato, da aka ce “Ya hau” ɗin, me aka fahimta, in ba cewa dā ya sauka a can ƙasa ba? 10Shi wanda ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau a can birbishin dukkan sammai, domin ya cika kome.) 11Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa, 12domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikilisiya, domin a inganta jikin Almasihu, 13har mu duka mu riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu. 14An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu. 15A maimakon haka, sai mu faɗi gaskiya game da ƙauna, muna girma a cikinsa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da yake shugabanmu. 16Domin ta gare shi ne dukkan jiki yake a game, yake kuma a haɗe, ta wurin gudunmawar kowace gaɓa, ta wurin kuma aikin kowace gaɓa daidai jikin yake ƙara girma, yana kuma ingantuwa da halin ƙauna.

Sabon Rai a cikin Almasihu

17To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku sāke yin zama irin na al'ummai, masu azancin banza da wofi. 18Duhun zuciya yake a gare su, bare suke ga rai wanda Allah yake bayarwa, sabili da jahilcin da yake a gare su, saboda taurin kansu. 19Zuciyarsu ta yi kanta, sun dulmiya a cikin fajirci, sun ɗokanta ido a rufe ga yin kowane irin aikin lalata. 20Ba haka kuka koyi al'amarin Almasihu ba, 21in da a ce kun saurare shi, an kuma koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta Yesu take. 22Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha'awoyinsa na yaudara, 23ku kuma sabunta ra'ayin hankalinku, 24ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.

25Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne. 26In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana, 27kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa. 28Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba matalauta. 29Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta. 30Ku kuma kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa. 31Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta. 32Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.

5

Ku Yi Zaman Haske

1Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun 'ya'yansa ne. 2Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.

3Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba. 4Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah. 5Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah. 6Kada wani ya hilace ku da maganar wofi, gama sabili da waɗannan zunubai ne fushin Allah yake aukawa a kan kangararru. 7Saboda haka, kada ku yi cuɗanya da su, 8domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske, 9domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya. 10Ku dai tabbata abin zai gamshi Ubangiji. 11Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su. 12Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da suke yi a asirce. 13Duk abin da aka kawo a gaban haske a san ainihinsa, gama duk abin da aka san ainihinsa ya haskaka. 14Saboda haka aka ce, “Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu. Almasihu kuwa zai haskaka ka.”

15Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. 16Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne. 17Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji. 18Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha'a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu, 19kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku. 20Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.

Maza da Mata

21Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu. 22Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa. 23Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu ke shugaban Ikilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin. 24Kamar yadda Ikilisiya take bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali. 25Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikilisiya, har ya ba da kansa dominta, 26domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma, 27domin shi kansa yă ba kansa Ikilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu. 28Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan. 29Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu yake yi wa Ikilisiya, 30domin mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31“Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.” 32Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikilisiya. 33Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta yi wa mijinta ladabi.

6

Biyayya da Ƙauna

1Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai. 2Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3don al'amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.” 4Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.

5Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu ku ke yi wa ke nan, 6ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya, 7kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba. 8Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi. 9Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.

Makaman Allah Duka

10A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa. 11Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis. 12Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu. 13Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage. 14Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku, 15shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita. 17Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah, 18a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a. 19Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara, 20wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu'a, duk sa'ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.

Gaisuwa

21A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan'uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome. 22Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya.

23Salamar Allah Uba da ta Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata ga 'yan'uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya. 24Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.