Esther

Esta

1

A Marfarkin Mordekai

1 A shekara ta biyu ta mulkin Ahazurus mai girma, a ranar farko ga watan nan Nisan, sai Mordekai, ɗan Ya'iru, ɗan Kish, na kabilan nan ta Biliyaminu, ya yi wani irm mafarki. 2 Mordekai Bayahude ne, a birnin nan na Shushan yake zaune, mutum ne mai martaba, yana zuwa majalisar sarki a kai a kai, 3 yana ma ɗaya daga cikin masu zaman talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kwaso daga Urushalima tare da Yekoniya, Sarkin Yahudiya.

4 Ga irin mafarkin da ya yi. Sai ya ji wata hayaniya, da hargitsi, da tsawa, da walƙiya, da wata irin ɗimuwa sun auka wa duniya. 5 Daganan sai waɗansu ƙattin macizai biyu suka fito, suna shirin yin faɗa da juna, suka kuma yi wata irin kuwwa. 6 Da suka yi kuwwan nan, sai kowace al'umma ta yi shirin yaƙi, domin su yaƙi al'ummar adalai. 7 Sai rana ta dushe, wahala da damuwa, ƙeta da babbar dimuwa, duk suka auko wa duniya. 8 Sai duk al'ummar adalai ta razana, ta ji tsoron abin da zai same ta, ta yi tsammani za a hallaka su, 9 sai suka yi kuka ga Allah. Saboda kukan nan nasu, sai wata 'yar maɓuɓɓuga ta malalo ruwa, har ta yi babban kogi, ta yi ambaliya da ruwa, 10 sai haske ya bayyana, rana ta fito, aka ɗaukaka ƙasƙantattu, su ma suka cinye masu izza.

11 A lokacin da Mordekai, wanda ya yi mafarkin nan, ya ga abin da Allah ke nufin yi, sai ya farka, ya kuma yi ta wuswasin abin a zuciyarsa, ya shiga gandun tunaninsa domin ya gane ma'anar mafarkin, har yamma ta yi.

An Tona Maƙarƙashiya

12 Mordekai ya zauna a fadar sarki tare da Bigtana da Taresa, dandaƙaƙƙun nan biyu waɗanda ke tsaron fadar. 13 Sai ya saurari hirarsu, ya kuma gane nufinsu, ya fahimci suna shirin auka wa Sarki Ahazurus, ya kuma fadakar da shi, game da nufinsu. 14 Sarki kuwa ya tuhumci dandaƙaƙƙun nan biyu, da suka yi hurci, sai aka kai su makasa. 15 Sai sarkin ya sa aka rubuta labarin al'amarin nan don tunawa. Mordekai ma sai da ya rubuta nasa labari. 16 Sarkin ya mai da Mordekai a cikin sarakunansa, har ya yi masa kyautai saboda aikin.

17 Amma Haman, ɗan wajen Hammedata, Ba'agagen nan, shi ɗan gaban goshin sarki ne ƙwarai, sai ya nufa cutar Mordekai da jama'arsa baki ɗaya, saboda dandaƙaƙƙun nan guda biyu na sarki da aka kashe.

1. Sarauniya Bashti ta Raina sarki Ahasurus

1 Ahasurus ya yi sarauta daga Hindu har zuwa Habasha, ya mallaki larduna dari da ashirin da bakwai. 2 A waɗannan kwanaki, sarki Ahasurus yake zaune a gadon sarautarsa a Shushan, masarauta.

3 A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya yi biki saboda sarakunansa, da barorinsa, da sarakunan yaƙin Farisa da Mediya, da manyan mutane, da hakiman larduna. 4 Sai ya nuna wadatar mulkinsa, da martabarsa, da darajarsa har kwanaki masu yawa, wato kwana ɗari da tamanin.

5 Bayan da waɗannan kwanaki sun cika, sai sarki ya yi wa manya da ƙanana waɗanda ke a Shushan, wato masarauta, biki, har na kwana bakwai a filin lambun fādar sarki. 6 Aka kewaye wurin da fararen labule da shunayya na Iallausan lilin, aka ɗaure da kirtani na Iallausan lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa da ginshiƙai na sassaƙaƙƙun duwatsu masu daraja. Akwai gadaje na zinariya da na azurfa a daɓen da aka yi da duwatsu masu daraja, masu launi iri iri. 7 Aka ba da sha a finjalai iri iri na zinariya. Aka shayar da su da ruwan inabi irin na sarauta a yalwace bisa ga wadatar sarki. 8 Aka yi ta sha bisa ga doka, ba wanda aka matsa masa, gama sarki ya umarci fadawansa su yi wa kowa yadda yake so.

9 Sarauniya Bashti kuma ta yi wa mata babban biki a fadar sarki Ahasurus.

10 A rana ta bakwai sa'ad da zuciyar sarki take murna saboda ruwan inabi, sai ya umarta bābāninsa guda bakwai, waɗanda ke yi masa hidima, wato Mehuman, da Bizta, da Harbona, da Bigta, da Abagta, da Zetar, da Karkas, 11 su kirawo sarauniya Bashti ta zo wurinsa da kambin sarauta, don ya nuna wa jama'a da shugabanni kyanta, gama ita kyakkyawa ce. 12 Amma sarauniya Bashti ta ƙi zuwa kamar yadda sarki ya umarci bābānin su faɗa mata. Wannan ya sa sarki ya husata ƙwarai.

13 Sarki kuwa ya nemi shawara ga masu hikima waɗanda suka ƙware zamani, gama sarki ya saba da yin haka ga waɗanda suka san doka da shari'a. 14 Su ne mutanen da ke kusa da shi, wato Karshena, da Shetar, da Admata, da Tarshish, da Meres, da Marsena, da Memukan. Su ne sarakuna bakwai na Farisa da Mediya, su ne masu zuwa wurin sarki, su ne kuma na fari a mulkin. 15 Sarki ya ce, "Bisa ga doka, me za a yi da sarauniya Bashti da ya ke ba ta yi biyayya da umarnin da na aika ta hannun bābāni ba?"

16 Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da sauran sarakai, ya ce, "Ba sarki ne kaɗai sarauniya Bashti ta yi wa laifi ba, amma har dukan sarakai, da sauran jama'a da ke dukan lardunan sarki Ahasurus. 17 Gama za a sanar wa dukan mata abin da sarauniya ta yi, gama abin da ta yi zai sa su raina mazansu, gama za su ce, 'Sarki Ahasurus ya umarta a kirawo masa sarauniya Bashti, amma ta ƙi.' 18 Yau ma matan Farisa da Mediya waɗanda suka ji abin da sarauniya ta yi, haka za su faɗa wa dukan hakimai. Wannan zai kawo raini da fushi mai yawa. 19 Idan sarki ya yarda, bari ya yi doka, a kuma rubuta ta cikin dokokin Farisa da Mediya don kada a sāke ta, cewa Bashti ba za ta ƙara zuwa wurin sarki Ahasurus ba. Bari sarki ya ba da matsayinta na sarauta ga wata wadda ta fi ta. 20 Sa'ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya."

21 Wannan shawara ta gamshi sarki da sauran sarakai, sarki ya yi kamar yadda Memukan ya shawarta. 22 Sai ya aika da takardu zuwa dukan lardunan sarki, kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da harshensu, domin kowane namiji ya zama shugaban gidansa, ya kuma zama mai faɗa a ji.

2. Esta ta Zama Sarauniya

1 Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta. 2 Sa'an nan barorin sarki waɗanda ke yi masa hidima suka ce masa, "Bari a samo wa sarki 'yan mata, budurwai, kyawawa. 3 Bari kuma sarki ya sa shugabanni a dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda ke lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa. 4 Bari sarki ya zaɓi budurwar da ta gamshe shi, ta zama sarauniya maimakon Bashti."

Sarki fa ya ji daɗin wannan shawara, ya kuwa yi haka din.

5 Akwai wani Bayahude a masarauta a Shushan, mai suna Mordekai ɗan Yayir, ɗan Shimai, ɗan Kish mutumin Biliyaminu. 6 An kamo shi a Urushalima tare 'yan zaman talala waɗanda aka kwashe tare da Yekoniya Sarkin Yahuza, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su zaman talala. 7 Mordekai ne ya goyi Hadassa, wato Esta, 'yar kawunsa, gama ita marainiya ce. Ita kuwa kyakkyawa ce. Sa'ad da iyayenta suka rasu, sai Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa.

8 Sa'ad da aka yi shelar dokar sarki, aka kuma tattara 'yan mata a masarauta a Shushan, a hannun Hegai, sai aka ɗauko Esta zuwa fādar sarki, aka sa ta a hannun Hegai wanda ke lura da mata. 9 Esta kuwa ta gamshi Hegai, ta kuma sami farin jini a wurinsa, sai nan da nan ya ba ta man shafawa, da rabon abincinta, da zaɓaɓɓun kuyangi guda bakwai daga fādar sarki. Ya kuma kai ta da kuyanginta a wuri mafi kyau na gidan matan kulle.

10 Esta ba ta riga ta bayyana asalin mutanenta, da danginta ba, gama Mordekai ya umarce ta kada ta yi. 11 Kowace rana Mordekai yakan zo shirayin gidan matan kulle don ya san yadda Esta take.

12 Sa'ad da lokacin kowace budurwa ya yi da za ta shiga wurin sarki Ahasurus, bayan da ta riga ta yi wata goma sha biyu na ka'idar yin kwalliyar mata, wato takan shafe jiki da man ƙanshi wata shida, ta kuma shafe jiki da turare da man shafawa wata shida, 13 sa'an nan budurwar za ta shiga wurin sarki, sai a ba ta dukan abin da take bukata ta ɗauko daga gidan matan kulle zuwa fadar sarki. 14 Takan tafi da yamma, ta koma gidan matan kulle na biyu da safe, a hannun Shawashgaz, bābā na sarki, wanda ke lura da kwarakwarai. Ba za ta ƙara zuwa wurin sarki ba, sai ko ta sami farin jini a wurin sarki sa'an nan a kirawo ta.

15 Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda ke lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta. 16 Sa'ad da aka kai Esta wurin sarki Ahasurus a fadarsa a wata na goma, wato watan Tebet, a shekara ta bakwai ta sarautarsa, 17 sai sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukan sauran matan. Ta kuwa sami alheri da farin jini a wurinsa fiye da sauran budurwan, saboda haka ya sa kambin sarauta a kanta. Ya naɗa ta sarauniya maimakon Bashti. 18 Sarki kuwa ya yi wa sarakunansa da barorinsa ƙasaitaccen biki saboda Esta. Ya kuma ba larduna hutu, ya ba da kyautai da yawa irin na sarauta.

Mordekai ya Ceci Ran Sarki

19 Sa'ad da aka tara budurwai a karo na biyu, Mordekai yana zaune a kofar sarki. 20 Har yanzu dai Esta ba ta bayyana asalin danginta da mutanenta ba, kamar yadda Mordekai ya umarce ta, gama Esta tana yi wa Mordekai biyayya kamar ta yi tun lokacin da yake renonta.

21 A kwanakin nan sa'ad da Mordekai ke zaune a ƙofar sarki, sai babani biyu na sarki, wato Bigtana da Teresh waɗanda ke tsaron ƙofar, suka yi fushi, har suka nema su kashe sarki Ahasurus. 22 Wannan maƙarƙashiya ta sanu ga Mordekai, shi kuwa ya faɗa wa sarauniya Esta. Esta kuma ta faɗa wa sarki da sunan Mordekai. 23 Sa'ad da aka bincika al'amarin aka tarar haka yake. Sai aka rataye mutum biyu ɗin a kan gumagumai. Aka kuma rubuta labarin a littafin tarihi a gaban sarki.

3. Maƙarƙashiyar Haman don ya Hallaka Yahudawa

1 Bayan waɗannan abubuwa, sai sarki Ahasurus ya gabatar da Haman ɗan Hammedata Ba'agage. Ya fifita shi bisa dukan sarakunan da ke tare da shi. 2 Dukan barorin sarki waɗanda ke a bakin ƙofar sarki suka rusuna suka yi wa Haman mubaya'a, gama sarki ya umarta a yi masa haka. Amma Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba. 3 Sai barorin sarki waɗanda ke a bakin ƙofar sarki suka ce wa Mordekai, "Me ya sa ka keta dokar sarki?" 4 Sa'ad da suka yi ta yi masa magana kowace rana, shi kuwa bai kasa kunne gare su ba, sai suka faɗa wa Haman, don su gani ko maganar Mordekai za ta tabbata, gama ya faɗa musu shi Bayahude ne. 5 Sa'ad da Haman ya ga Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba, sai ya husata. 6 Har ma ya ga a kashe Mordekai kaɗai, wannan bai isa ba. Da ya ke an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya nema ya hallaka dukan Yahudawa, wato kabilar Mordekai, waɗanda ke a dukan mulkin Ahasurus.

7 A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri'a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri'a ta fado a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.

8 Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, "Akwai waɗansu mutane da ke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su. 9 Idan ya gamshi sarki, bari a yi doka a hallaka su, ni kuwa zan ba waɗanda ke tafiyar da aikin sarki, talanti dubu goma (10,000) na azurfa, don su sa a baitulmalin sarki."

10 Sarki kuwa ya zare zobensa na hatimi daga hannunsa ya ba Haman Ba'agage, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa. 11 Sa'an nan ya ce masa, "Da kuɗin, da mutanen duk an ba ka, ka yi yadda ka ga dama da su."

12 Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama'a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki. 13 Aka ba 'yan‑kada‑ta‑kwana takardun zuwa dukan lardunan sarki don a hallaka Yahudawa, a karkashe, a ƙarasa su, ƙanana da manya, mata da maza, duk a rana ɗaya, wato ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, a kuma washe dukiyoyinsu.

B. Wasiƙar Ahazurus

1 Ga abin da wasiƙar ta ƙunsa, "Daga babban sarki, Ahazurus zuwa ga hakiman da ke mulkin lardunan nan ɗari da ashirin da bakwai waɗanda suke tun daga Hindu har zuwa Habasha, da sauran hakiman da ke ƙarƙashinsu, gaisuwa mai yawa gare ku.

2 "Ina sanar muku cewa, da na fara mulkin jama'a masu dama, na kuma riƙe ragamar mulkin dukan duniya, ba ni da nufin tsananin iko ya ɗauke mini hankali, amma so nake kullum in yi mulkina da rahama da sulhu, domin in daɗaɗa wa dukan talakawana rai, mutanen mulkina su ji daɗin zama a dukan gundumomina, domin in sa dukan mutane su more wa salama da suke ta bege tuntuni. 3 Da na shawarci mashawartana ta yadda za a ga cikowar burin yin haka, sai Haman, wanda ya fi dukanmu hikima da ibadar gaske, ga kuma biyayya, yake kuma wakilin dukan mulki, 4 ya ba ni shawara cewa, cikin dukan kabilan duniya akwai muguwar al'umma ɗaya, mai ƙin sauran al'ummai ta nata dokoki, tana keta haddin dokokin sarakuna, irin waɗannan mutane ba za su bari a kai ga zumuncin al'umman mulkinmu da muka ƙulla ba.

5 "Tun da ya ke mun gane kan waɗannan mutane na ta gāba da jama'a duka, suna ma bin ka'idodi dabam, ai, gāba da mu suke, suna yin laifofin da suka fi gaban magana, har da ƙyar mulki ya iya tsayawa da gindinsa, 6 kamar yadda Haman, wanda yake wakilin dukan mulki kuma, kamar ubanmu, ya rubuta wadansu wasiƙu a kansu, don haka mun umarta, cewa a haɗa su tare da matansu da 'ya'yansu, a hallaka su kwatakwata, kada a nuna musu wani tausayi ko jinƙai, a ranan nan ta sha huɗu ga watan goma sha biyu na wannan shekara. 7 Lokacin da mutanen nan waɗanda suka daɗe suna yin wannan irin ƙeta haka, suka baƙunci lahira a ranar tashin hankali, sa'an nan su ƙyale mu mu yi barkokinmu mu kaɗai, ba da sun dame mu ba nan gaba."

3

14 Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, su kasance a shirye don ranar.

15 Bisa ga umarnin sarki, sai 'yan-kada‑ta‑kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a Shushan, masarauta. Sarki da Haman kuwa suka zauna don su sha, amma birnin Shushan ya ruɗe.

4. Esta za ta yi ƙoko don Mutanenta

1 Da Mordekai ya ji dukan abin da aka yi, sai ya yage tufafinsa, sa'an nan ya sa rigar makoki, ya zuba toka a kā. Ya fita zuwa tsakiyar birni, yana ta rusa kuka da ƙarfi. 2 Ya tafi kusa da ƙofar sarki, gama ba a yarda wani ya shiga ƙofar sarki da rigar makoki ba. 3 A kowane lardi inda aka kai umarni da dokar sarki, Yahudawa suka yi babban baƙin ciki, da azumi, da kuka, da makoki. Waɗansu da yawa suka kwanta da rigunan makoki a cikin toka.

4 Sa'ad da kuyangin Esta da bābāninta suka tafi suka fada mata abin da Mordekai ke yi, sai sarauniya Esta ta damu kwarai, ta aika da riguna a sa wa Mordekai, ya tuɓe rigar makokinsa, amma Mordekai ya ƙi, bai yarda ba. 5 Sai Esta ta kirawo Hatak, ɗaya daga cikin bābānin sarki, wanda aka sa ya yi mata hidima, ta aike shi wurin Mordekai, don ya ji abin da ya faru, har ya sa yake yin haka. 6 Hatak kuwa ya tafi wurin Mordekai a dandalin birnin, a gaban ƙofar sarki. 7 Sai Mordekai ya faɗa masa dukan abin da ya faru da shi, da yawan kuɗin da Haman ya ce zai biya a sa a baitulmalin sarki don a hallaka Yalmdawa. 8 Mordekai kuma ya ba Hatak takardar dokar da aka yi a Shushan don a hallaka Yahudawa domin ya tafi ya nuna wa Esta ya sanar da ita, ya kuma umarce ta ta tafi wurin sarki don ta roƙi arziki ga sarki saboda mutanenta. 9 Sai Hatak ya tafi, ya faɗa wa Esta abin da Mordekai ya ce. " Esta kuma ta yi magana da Hatak sa'an nan ta aike shi da saƙo a wurin Mordekai cewa, 10 "Dukan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, ba tare da an kira shi ba, to, doka ɗaya ce ke kan mutum, wato kisa, ko mace ko namiji, sai dai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don ya rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba."

12 Hatak ya tafi ya faɗa wa Mordekai abin da Esta ta ce. Sai Mordekai ya ce masa ya je ya faɗa wa Esta haka, "Kada ki yi tsammani za ki tsira a fadar sarki fiye da sauran Yahudawa. 13 Gama idan kin yi shiru a irin wannan lokaci, to, taimako da ceto za su zo wa Yahudawa ta wata hanya dabam, amma ke da gidan iyayenki za ku halaka. Wa ya sani ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan maƙami?"

15 Sa'an nan Esta ta ce masa ya je ya faɗa wa Mordekai cewa, 16 "Ka tattara dukan Yahudawan da ke a Shushan, su yi azumi domina, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi hakanan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da ya ke ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan."

17 Sai Mordekai ya tafi ya yi abin da Esta ta umarce shi.

C. Addu'ar Mordekai

1 Mordekai ya yi daidai abin da Esta ta faɗa. Da ya tuna da dukan ayyukan mamaki na Ubangiji, sai ya yi addu'a, ya ce, 2 "Ya Ubangiji Allah, Sarki Mai Iko Dukka, ai, kowane abu yana bin ikonka. Ba wanda zai iya yin tsayayya da kai a cikin nufin nan naka na ceton Isra'ilawa. 3 Ai, kai ne ka halicci sama da ƙasa da duk abubuwan mamaki da ke a sama. 4 Kai ne Ubangijin abu duka. Ba wanda zai iya yi maka taurinkai a banza. 5 Ka san dukan kome. Ka sani, ya Ubangiji, ka sani ba wata tsiwa, ko rashin kunya, ko ɗaukakar banza da suka kai ni ga yin haka, wato da na ƙi sunkuya wa mai alfannan nan, Haman. 6 Da ma na iya sumbatar ƙafarsa domin Isra'ilawa su zauna lafiya. 7 Amma abin da na yi, na yi ne don kada in ɗaukaka mutum fiye da Allah. Ba ma zan sunkuya wa wani ba, sai dai kai, ya Ubangiji. Don haka, tun da na ƙi, ai, ba girmankai ba ne. 8 Yanzu, ya Ubangiji Allah, Sarki, Allah na Ibrahim, ka ceci mutanenka! Gama mutane suna neman halakarmu, suna shirin lalata mu, mu da muke mutanenka tuntuni. 9 Kada ka watsar da wannan mallaka taka, wadda ka sa ta zama taka a ƙasar Masar. 10 Ka ji roƙe‑roƙena, ka yi wa jama'arka jinƙai mai girma, ka mai da kukamnu ya zama dariya, domin mu yi ta yi wa sunanka waƙa, ya Ubangiji. Kada ka bari bakunan masu yabonka su halaka."

11 Dukan Isra'ilawa suka yi kuka da babbar muryar da dukan ƙarfinsu, gama sun ga mutuwa ƙiri ƙiri.

Addu'ar Esta

12 Sarauniya Esta kuma ta ii matuƙar tsoro, sai ta fake gaban Ubangiji, 13 ta tuɓe kayan adonta, ta sa na makoki. Maimakon ta barbaɗa ɗan goman nan yadda ta saba, sai ta yi ta hurwa da toka da kuma turɓaya. Ta hori jikinta sosai, maimakon kyan nan nata na dā, sai ta korna kamar ba a saye ta kobo ba, gashin kanta kuwa ba kitso.

14 Har ta roƙi Ubangiji Allahn Isra'ilawa ta ce, "Ya Ubangiji, Sarkinmu, kai kaɗai ne Allah. Ka zo, ka taimake ni mana, gama ni kaɗai ce, ba ni da wani mataimaki ko kaɗan, sai kai. 15 Ga shi, ina shirin kutsa kaina a cikin halaka. 16 Iyayena sun koya mini tun ƙuruciyata, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka zaɓi Isra'ilawa, su kaɗai daga cikin kabilai da yawa, su kaɗai ne kuma, ka zaɓa daga dukan 'yan'uwansu su zama abin mallakarka har abada, ka kuma yi musu alheri yadda ka alkawarta. 17 Amma mu mun yi zunubi a gabanka, ka kuwa hannanta mu ga abokan gabanmu, 18 domin mun girmama 'yan allolinsu. Ya Ubangiji, kai mai adalci ne. 19 Amma yanzu duk shan wuyar da muke yi ta bauta ba ta isa makamanmu ba, amma sun rantse da gumakansu, cewa 20 sai sun kashe ƙaddarar da ka hurta, su hallaka mu, mu da ke mallakarka, su rufe bakinmu. wanda ke yabonka, su lalata bagadenka da wunn ɗaukakan nan, wato masujadarka. 21 Ta haka sun nufi arna su buɗe baki, su yabi 'yan allolinsu da ba su da wata daraja, su kuma riƙa ɗaukaka sarkin da yake mutum mai mutuwa.

22 "Kada ka yar da sandanka, ya Ubangiji, ga wani daga cikin mutanen banzan nan. Kada ma ka bar mutane su yi na'am da faɗuwarmu. Amma ka sa mugun nufinsu ya koma musu, ka ma hori wanda ya yi wannan shiri, domin na baya su ji tsoro. 23 Ka tuna da mu, ya Ubangiji, ka nuna kanka a lokacin da muke shan wahala. Ni dai ina so ka ƙarfafa ni, ya Allah bisa alloli, Masaraucin masu sarauta. 24 Ka sa jawabina ya riƙa shiga kunnen zakin nan, ka sa shi, shi ma, ya ƙi jinin magabcin nan namu, domin magabcin nan da dukan magoya bayansa su halaka. 25 Mu dai, ka cece mu da ikon nan naka, ka zo ka taimake ni, gama ni kaɗai ce, ba ni da wani mataimaki kuma, sai kai, ya Ubangiji.

"Ai, ka dai san dukan abu. 26 Ka sani na ƙi jinin ɗaukakan nan ta arna, ma ƙyamar gadajen marasa kaciya da dai na kowane baƙo. 27 Ka sani ina cikin halin ƙaƙa naka yi, ina ma ƙyamar kambin matsayina na girma wanda ke bisa kaina in na shiga wurin mutane. Na ƙi jininsa, kamar tsumman haila yake a guna, ba na sa shi ma kuwa a ɗaki. 28 Ai, baiwarka ba ta taɓa cin abinci da Haman ba, ban taɓa halartar wani liyafar sarki ba, ban ma sha giyar da ake zuba wa gunki ba. 29 Ban taɓa yin wani ƙauli ba, tun ranar da aka kawo ni nan, har zuwa yau, sai a cikinka kaɗai, ya Ubangiji, Allah na Ibrahim. 30 Ya Allah, ai, ikonka ya zarce na kowa. Ka saurari muryar wadda ke shan wahala. Ka cece mu. daga hannun mugaye. Ka kuma sa in daina yin fargaba!"

D. Sarki ya Marabci Esta

1 A rana ta uku, lokacin da Esta ta gama yin addu'a, sai ta tuɓe tufatin nan nata na bakin ciki, ta sa kayanta na asin da asin, kyawawan nan. 2 A lokacin da ta fita, bayan ta ci ado ta yi tsab tsab, sai ta kira ga sunan Allah wanda ke kula da dukan mutane, yana cetonsu. Sa'an nan ta

kwashi bayi mata guda biyu. 3 Tana langaɓewa, sai ta jingina da ɗayar, 4 gudar kuwa ta riƙa binsu a baya, tana ɗaga tufafin uwargijiya tasu domin kada su share ƙasa. 5 Fuskarta ta fasu, ga ta nan dai, son kowa san kowa. Amma tana da ɗarɗar a zuci. 6 Ta yi ta wuce wannan ƙofa zuwa waccan, sai da ta kai har gaban sarki. Ta tarar da shi zaune a kan karagar mulkinsa, ya sha kayan nan nasu na sarakuna, suna ta sheƙin zinariya da na duwatsu masu daraja, gwanin kyan gani. 7 Sai ya daga kai, ya dube ta, yana wani toroƙo, yana yin waɗansu muzurai na fushi. Sai sarauniya ta durƙusa don tsoro, ta murtuke fuska, ta ƙara jingina da baiwarta. 8 Amma Allah ya juya zuciyar sarkin, duk ya sakwarkwace. Sai ya zabura, don ya gigice, ya tashi, ya rungume ta, har ta wartsake tukuna, yana ƙarfafa mata zuciya da kalami mai daɗi, yana cewa, 9 "Me ya same ki, Esta?" Ya ƙara da cewa, "Ai, ni dan'uwa ne a gare ki. Kada ki damu ko kaɗan, 10 ba wanda zai taɓa lafiyarki, talakawa kawai ne muka yi wa dokar kada su shigo. 11 Ki zo guna, mu shaƙata." 12 Da ya ɗaga sandansa na zinariya, sai ya maƙala mata shi a wuya, yana shafarta, yana cewa, "Ki yi magana, ya uwargida."

13 Sai ta amsa masa, ta ce, "Da na gan ka, cewa nake mala'ikan Allah ne, sai na gigice don tsoron ɗaukakarka. 14 Gama kana da fuskar bantsoro, ko da ya ke cike kake da alheri." 15 Da dai ta gama wannan magana, sai ta suma. 16 Ran sarki ya duhunta, da na dukan fadawansa, suka kuma yi iyakar ƙokarinsu su taimake ta ta wartsake sarai.

5. Esta ta Yi wa Sarki da Haman Liyafa

1 A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda. 2 Sa'ad da ya ga Esta tana tsaye a shirayin, sai ya miƙa mata sandan zinariya na sarauta, gama ta sami kwarjini a wurinsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan. 3 Sarki ya ce mata, "Menene, sarauniya Esta? Me kike so? Za a ba ki, ko rabin mulkina ma." 4 Sai Esta ta ce, "Idan sarki ya yarda, bari sarki ya zo tare da Haman yau wurin liyafa da na shirya wa sarki."

5 Sarki kuwa ya ce, "A zo da Haman maza, mu yi abin da Esta take so." Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya. 6 Sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya tambayi Esta, "Mecece bukatarki? Za a biya miki ko da rabin mulkina ne."

7 Sai Esta ta ce, "Bukatata, da roƙkona ke nan, 8 idan na sami tagomashi a wurin sarki, idan kuma sarki ya yarda ya biya bukatata da roƙona, to, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan yi musu, gobe kuwa zan yi abin da sarki ya fada."

Haman ya Yi Shirin Kashe Mordekai

9 Ran nan Haman ya fita da murna da farin ciki, amma da ya ga Mordekai a ƙofar sarki, Mordekai kuwa bai tashi ba, bai kuma yi rawar jiki a gabansa ba, sai ya husata ƙwarai. 10 Duk da haka Haman ya cije, ya tafi gida. Ya aika a kirawo abokansa da matarsa, Zeresh. 11 Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan 'ya'yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki. 12 Ya ƙara da cewa, "Har ma sarauniya Esta ma ba ta yarda kowa ya tafi tare da sarki wurin liyafar da ta shirya ba, sai ni. Gobe ma ta gayyace ni tare da sarki. 13 Duk da haka wannan bai yi mini daɗi ba, muddin Mordekai, Bayahuden nan, yana zaune a ƙofar sarki."

14 Matarsa, Zeresh kuwa, da abokansa duka suka ce, "Ka sa a shirya gungumen itace mai tsayi kamu hamsin, sa'an nan da safe ka faɗa wa sarki a rataye Mordekai a kai, sa'an nan ka tafi wurin liyafar tare da sarki da murna."

Haman kuwa ya ji daɗin wannan shawara, sai ya sa aka shirya gungumen itacen.

6. Haman ya Girmama Mordekai Tilas

1 A wannan dare kuwa sarki ya kasa yin barci, sai ya umarta a kawo littafin da aka rubuta al'amuran da ke faruwa don tunawa. Aka kuwa kawo, aka karanta wa sarki. 2 Sai aka tarar an rubuta yadda Mordekai ya gano maƙaƙashiyar Bigtana da Teresh, biyu daga cikin bābāni na sarki, masu tsaron ƙofa, waɗanda suka yi niyya su kashe sarki Ahasurus. 3 Sai sarki ya ce, "To, wace irin daraja ko girma aka ba Mordekai saboda wannan?"

Barorin sarki waɗanda ke yi masa hidima suka ce, "Ba a yi masa kome ba."

4 Sarki kuwa ya ce, "Wanene ke a shirayi?"

Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya. 5 Barorin sarki suka ce, "Ai, Haman ne ke tsaye a shirayi."

Sai sarki ya ce ya shigo.

6 Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, "Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?"

Haman ya yi tunani ya ce a ransa, "Wanene sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?"

7 Sai Haman ya ce wa sarki, "Abin da za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka ke nan. 8 Bari a kawo rigunan sarautar da sarki ya taɓa sawa, da dokin da sarki ya taɓa hawa, a kuma sa kambin sarauta a kansa. 9 Sa'an nan a ba ɗaya daga cikin manyan sarakunanka rigunan ya sa wa wanda kake so ka ɗaukaka, ya kuma hawar da shi kan dokin, sa'an nan ya zagaya da shi a dandalin birni, yana shelar a gabansa yana cewa, 'Haka za a yi wa wanda sarki ke so ya ɗaukaka.'"

10 Sai sarki ya ce wa Haman, "Yi maza, ka ɗauki rigunan da dokin, ka tafi wurin Mordekai, Bayahuden nan, wanda yakan zauna a ƙofar sarki ka yi masa kamar yadda ka faɗa. Kada ka kasa yin kome daga cikin abin da ka fada."

11 Haman kuwa ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sa wa Mordekai riguna, ya hawar da shi kan dokin, ya zagaya da shi a dandalin birnin, yana cewa, "Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka."

12 Sa'an nan Mordekai ya koma ƙofar sarki, Haman kuwa ya gaggauta zuwa gidansa, yana baƙin ciki, kunya ta rufe shi. 13 Da ya koma gida, sai ya faɗa wa Zeresh, matarsa, da dukan abokansa, duk abin da ya same shi. Sai mutanensa masu hikima da Zeresh, matarsa, suka ce masa, "Idan Mordekai, wanda ka fara faɗuwa a gabansa, in dai daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, amma hakika za ka fāɗi a gabansa."

14 Suna magana ke nan, sai bābānin sarki suka iso, suka tafi da Haman a gaggauce zuwa wurin liyafar da Esta ta shirya.

7. Haman ya Fāɗa Ramin da ya Haƙa

1 Sarki da Haman kuwa suka tafi wurin Esta, gun liyafa. 2 A rana ta biyu, sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, "Mecece bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Menene rokonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne."

3 Sai Esta ta ce, "Ya sarki, idan na sami tagomashi a wurinka, idan kuma sarki ya yarda, bukatata ita ce a bar ni da raina, roƙona kuma shi ne a bar mutanena. 4 Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa da mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba."

5 "Sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya Esta, "Wanene shi, ina yake, wanda zai yi karambanin yin wannan?"

6 Esta ta ce, "Haman ne, magabci, maƙiyi, mugu!"

Sai tsoro ya kama Haman a gaban sarki da sarauniya. 7 Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi. 8 Da sarki ya koma daga lambun fāda zuwa inda suke shan ruwan inabi, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfidar da Esta take zaune. Sai sarki ya ce, "Har ma zai ci mutuncin sarauniya a gabana, a giɗana?"

Da dai sarki ya faɗi haka, sai bābāni suka cafe Haman, 9 Sa'an nan Harbona, ɗaya daga cikin bābānin da ke yi wa sarki hidima ya ce, "Ga shi ma, Haman ya riga ya shirya gungumen itace a gidansa, mai tsayi kamu hamsin, inda zai rataye Mordekai wanda ya ceci sarki ta wurin maganarsa."

Sai sarki ya ce, "A rataye Haman a gungumen."

10 Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa'an nan sarki ya huce.

8. An Ba Yahudawa lzni kada su Miƙa Wuya

1 A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta. 2 Sa'an nan sarki ya dauki zobensa na hatimi, wanda ya karɓe a wurin Haman, ya ba Mordckai. Esta kuma ta ba Mordokai gidan Haman.

3 Sa'an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roke shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba'agage ya shirya wa Yahudawa. 4 Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya, 5 Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, "Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba'agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da ke cikin dukan lardunan sarki. 6 Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da halaka na mutanena da dangina?"

7 Sai sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya da Mordekai, Bayahude, "Ga shi, na riga na ba Esta gidan Haman, an kuma riga an rataye shi a bisa gungume domin ya so Ya taɓa Yahudawa. 8 Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba."

9 A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu. 10 An yi rubutu da sunan sarki Ahasurus, aka kuma hatimce shi da hatimin zoben sarki. Aka aika da wasiƙun ta hannun 'yan‑kada-ta‑kwana, waɗanda suka hau dawakai masu zafin gudu da akan mora a aikin sarki.

11 A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da ke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu. " Za a yi wannan a dukan lardunan sarki Ahasurus ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar.

E. Wasiƙar Sarki Ahazurus

Ga fassarar abin da wasiƙar ta ƙunsa, "Daga babban sarki, Ahazurus, zuwa ga ƙananan hakimai da ke mulkin lardunan nan ɗari da ashirin da bakwai, waɗanda suke tun daga Hindu zuwa Habasha, har zuwa sauran masu kula da sha'anoninmu, gaisuwa mai yawa da fatan alheri.

2 "Ina sanar muku cewa, mutane da dama, da ake ƙara girmamawa, sai ƙara iskanci suke ta yi. 3 Ba riƙa lahanta talakawanmu kawai suke yi ba, waɗanda ba su iya kome ba, sai yadda aka yi da su, amma sukan riƙa cizon, har ma hannun da ke ciyar da su. 4 Ba kasa godewa a kan alherin da 'yan adam ke yi musu kawai suke yi ba, amma sun cika ɓaranci da butulci, suna tsammani za su kuɓuta daga hukuncin Allah, wanda ke ganin dukan abu.

5 "Haka yakan faru, sau da yawa, wakilan da aka danƙa wa sha'anin mulki sukan ja hankalin sarakuna su kashe adalai, su kuma yi sauran ɓarna irin wadda ba a maganinta. 6 Duk wannan kuwa yakan faru domin ja'iran wakilan nan sun ruɗi sarakuna masu son aikata gaskiya. 7 Ana iya ganin wannan a fili a tarihin da muka ji na kaka da kakanninmu, amma za ku fi gane shi in kun duba irin ƙeta da wakiIan nan marasa cancanta suka yi a tsakaninku a zamanin yau. 8 Gama ya kamata nan gaba mu tafi da mulkinmu daidai wa daida don jin daɗin kowa da kowa, 9 ta duba sababbin halayen zamani, da yin shari'a ba da nuna bambanci ba.

10 "Ta haka ne Haman ɗan Hammedata, mutumin Makidoniya, wanda ba mutumin Farisa ba, ba ya ma nuna alheri kamar yadda muke yi, mun marabce shi, 11 muka riƙa shi hannu bibbiyu kamar dai yadda na yi da kowace al'umma, har ma muka ce, wai shi ne 'Dattijon Sarki' wanda kowa zai rusuna a gabansa, muka dai girmama shi ƙwarai da gaske, har ya zama wakilin dukan mulkin. 12 Amma shi kuwa, da ya ke bai cancanci riƙon ragamar mulkin ba, sai ya yi shirin ƙwace mana sarauta, ya kashe ni kuma. 13 Fiye da haka ma, sai ya shirya maƙarƙashiya iri iri don ya ruɗe ni in kashe Mordekai, wanda ke macecin nan namu, sarkin alheri, tare da Esta 'yar'uwan nan tamu marar aibu, da dai dukan sauran kabilan nan tasu baki ɗaya. 14 Ta haka ya nufi barinmu ba agaji, ya kuma sauya mulkin mutanen Farisa zuwa hannun Helenawa. 15 Amma sai muka gane cewa, ashe Yahudawa waɗanda wannan sarkin saɓo ya hukunta a hallaka su, ba mugaye ba ne, amma suna bin dokokin gaskiya. 16 Su kuma 'ya'yan Maɗaukaki ne, rayayyen nan da ya sa mu da kakanninmu muka yi sarauta lami lafiya.

17 "Don haka bai kamata ku aikata abin da wasiƙan nan ta Haman ɗan Hammedata ta umarta ba, 18 tun ma da ya ke aka rataye wanda ya rubuto a ƙofar garin Shushan da dukan iyalin gidansa, gama nan da nan ya sami horon da Allah, Sarkin dukan abu, ya ƙaddara masa.

19 "Ku kakkafa fassarar wasiƙan nan duk wurin da mutane ke taruwa, ku ba Yahudawa 'yancin bin nasu al'adu, 20 ku kuma kara da dukan wanda ke son auka musu a ranan nan da aka sa don a ci musu mutunci, wato ran goma sha uku ke nan ga watan goma sha biyu, wanda yake da suna Adar. 21 Gama Allah Mai Iko Dukka ne ya sauya ranan nan ta hallakarwa ta zama ranar farin ciki ga al'ummarsa da ya zaɓa. 22 Ku kuma, ya kamata ku girmama wannan rana tare da sauran ranakun idinku da murna mai yawa. 23 Daga yanzu har zuwa gaba, da ku da mutanenku na kirki na Farisa, ku riƙa tunawa da ranar da aka fanshe ku, aka kuwa hallaka abokan gabanku.

24 "Kowane birni da dai kowane lardin da bai bi wannan umarni ba, za a yi musu mugun kisa. Ba 'yan adam kaɗai ne za su yi nesa da wurin ba, amma har namomin jeji da tsuntsaye ma har abada."

8

1 Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, Yahudawa kuwa su yi shiri saboda wannan rana, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu. 14 Sai 'yan‑kada‑ta‑kwana suka hau dawakai masu zafin gudu waɗanda akan mora a aikin sarki, suka tafi da gaggawa don su iyar da dokar sarki. Aka yi shelar dokar a Shushan, masarauta.

15 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan. " Yahudawa suka sami haske, da farin ciki, da murna, da daraja. " A kowane lardi da birni inda maganar sarki da dokarsa suka kai, Yahudawa suka yi farin ciki da murna, suka yi biki, suka yi hutu. Mutane da yawa daga cikin mutanen ƙasar suka zama Yahudawa, gama tsoron Yahudawa ya kama su.

9 .Yahudawa sun Hallaka Maƙiyansu

1 A kan rana ta goma sha uku ga watan sha biyu, wato watan Adar, a ranar da za a aikata maganar sarki da dokarsa, wato a ranar da maƙiyan Yahudawa za su fāɗa musu, sai ranar ta zama ranar da Yahudawa ne za su tasar wa maƙiyansu. 2 Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane. 3 Dukan sarakunan larduna, da hakimai, da masu mulki, da ma'aikatan sarki, suka taimaki Yahudawa, gama tsoron Mordekai ya kama su. 4 Gama Mordekai ya zama babban mutum a gidan sarki, ya kuma yi suna a dukan larduna, gama ya yi ta ƙasaita gaba gaba. 5 Yahudawa kuwa suka kashe dukan maƙiyansu da takobi. Suka hallaka maƙiyansu yadda suke so.

6 A Shushan, masarauta kanta, Yahudawa suka hallaka mutum ɗari biyar. 7 Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata, 8 da Forata, da Adaliya, da Aridata, 9 da Farmashta, da Arisai, da Aridai, da Waizata. 10 Su ne 'ya'ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.

11 A ranar ce aka faɗa wa sarki yawan mutanen da aka kashe a Shushan, masarauta. 12 Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, "A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma 'ya'yan Haman guda goma. Menene suka yi a sauran lardunan sarki? Mecece kuma bukatarki? Za a yi miki. Menene kuma roƙonki? Za a ba ki."

13 Esta ta ce, "Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da ke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma a bisa gumagumai." 14 Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma. 15 Yahudawan da ke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.

Bikin Furim

16 Yahudawan da ke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kāre rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba. 17 A rana ta goma sha uku ga watan Adar ne suka aikata wannan abu. A rana ta goma sha huɗu suka huta, suka mai da ranar ta zama ta biki, da farin ciki. 18 Amma Yahudawan da ke a Shushan suka taru a rana ta goma sha uku, da rana ta goma sha huɗu, suka huta ran goma sha biyar, suna biki da murna. 19 Yahudawan da ke zaune a kauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.

20 Mordekai kuwa ya rubuta abubuwan nan da suka faru, ya aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa waɗanda ke a dukan lardunan sarki Ahasurus, na kusa da na nesa. 21 Ya yi musu umarni, cewa su kiyaye rana ta goma sha huɗu da ta goma sha biyar na watan Adar a kowace shekara. 22 Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta. 23 Sai Yahudawa suka ɗauka su yi kamar yadda suka fara, da kuma yadda Mordekai ya rubuta musu.

24 Haman Ba'agage, ɗan Hammedata, maƙiyin dukan Yahudawa, ya ƙulla wa Yahudawa makirci don ya hallaka su. Ya jefa Fur, wato kuri'a don ya hallaka su. 25 Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce, cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai. 26 Saboda haka suka sa wa ranakun nan suna Furim, wanda asalinsu daga Fur ne, wato kuri'a. Domin haka dukan abin da aka rubuta a wannan takarda, da abin da suka gani a wannan al'amari, da abin da ya same su, 27 sai Yahudawa suka ga wajibi ne a gare su, da zuriyarsu, da waɗanda suke tare da su, su kiyaye ranaku biyu ɗin nan ba fashi kowace shekara, bisa ga abin da aka rubuta. 28 Za a tuna da ranakun nan, a kiyaye su a kowane zamani, da kowane iyali, da lardi, da birni. Ranakun Furim ɗin nan, Yahudawa ba za su daina tunawa da su ba, zuriyarsu kuma ba za ta daina tunawa da su ba.

29 Sa'an nan sarauniya Esta 'yar Abihail da Mordekai Bayahude, ta ba da cikakken iko a rubuce don ta tabbatar da takardan nan ta biyu game da Furim. 30 Aka aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa da ke a lardi ɗari da ashirin da bakwai na mulkin Ahasurus, da kalmomin salama da na gaskiya, 31 da cewa a kiyaye ranakun Furim a lokacinsu, kamar yadda Mordekai Bayahude, da sarauniya Esta, suka umarci Yahudawa, kamar yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu lokacin tunawa da azuminsu da bakin cikinsu. 32 Da umarnin Esta aka kafa ƙa'idodin Furim, aka kuwa rubuta su a littafi.

10. Ƙasaitar Mordekai

1 Sarki Ahasurus ya fasa haraji a ƙasar tudu da ta bakin teku. 2 An rubuta a littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa, dukan ayyukan iko, da isa, da cikakken labarin darajar Mordekai, wadda sarki ya ba shi. 3 Gama sarki Ahasurus kaɗai ke gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama'ar 'yan'uwansa, gama ya nemi lafiyar jama'arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane.

F. An Cika Mafarkin Mordekai

1 Sai Mordekai ya ce, "Dukan wannan, ai, aikin Allah ne. 2 Na ma tuna da irin mafarkin da na yi a kan waɗannan al'amura, duk kuwa sun tabbata gaskiya ne, 3 'yar maɓuɓɓugar da ta zama babban kogi, wutar da ta yi hasken nan na rana, da ambaliyan nan kuma ta ruwa. Esta ce ta zama kogin, ita da sarki ya aura, ya mai da ita sarauniya. 4 Ƙattin macizan nan guda biyu masu faɗa da juna kuwa, su ne ni da Haman. 5 Al'umman nan su ne waɗanda suka yi shirin shafe sunan Yahudawa. 6 Amma al'umman nan guda, wato tawa, ita ce ta Isra'ilawa, wadda ta yi kuka ga Allah, ya kuwa cece ta.

"I, Ubangiji ya ceci mutanen nan nasa, ya fanshe mu daga dukan mugayen nan, Allah ya aikata wadansu irin manyan alamu da ba su taɓa faruwa da wata al'umma dabam ba. 7 Saboda haka Allah ya yi ƙaddara biyu, ɗaya ta mutanensa, ɗayar kuma ta sauran al'umma. 8 Ƙaddara biyun kuwa an cika su a kan kari, a sa'ar da lokacin da Allah ya shirya a yi su ga dukan al‑'ummai. 9 Ta haka ne Ubangiji ya tuna da jama'arsa, ya kare su daga zalunci.

10 "Saboda haka, Isra'ilawa za su riƙa taruwa a ranaku na goma sha huɗu da sha biyar ga watan nan na Adar, su yi farin ciki da murna a gaban Allah har abada abadin."