Ezekiel

Ezekiyel

1

Ezekiyel ya Ga Wahayi na Ɗaukakar Ubangiji

1A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kobin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah. 2A kan rana ta biyar ga watan, a shekara ta biyar da aka kai sarki Yekoniya bautar talala, 3Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.

4Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla. 5Daga tsakiya wutar, sai ga kamannin waɗansu talikai su huɗu. Ga irin kamanninsu, suna kama da mutane. 6Amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, da fikafikai huɗu. 7Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla. 8Suna kuma da hannuwa kamar na mutane a ƙarƙarshin fikafikansu huɗu. Ga yadda fuskoki da fikafikan talikai huɗu ɗin suke. 9Fikafikansu suna taɓa juna, kowannensu ya miƙe gaba, ba su juyawa sa'ad da suke tafiya.

10Kamannin fuskokinsu, su huɗu ɗin, kowannensu yana da fuska irin ta mutum a gaba, da fuska irin ta zaki a dama, da fuska irin ta bijimi a hagu, da fuska irin ta gaggafa a baya. 11Suka kuma buɗe fikafikansu sama. Kowane taliki yana taɓa fiffiken ɗan'uwansa da fikafikansa biyu, da kuma fikafikansa biyu yake rufe jikinsa. 12Kowannensu kuwa ya miƙe gaba sosai, zuwa inda ruhu ya bishe shi. Sun tafi ba waiwaye.

13A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kima suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa. 14Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.

15Da na dubi talikan, sai na ga ƙafafu huɗu kamar na keke a ƙasa kusa da talikan. Ɗaya domin kowane taliki. 16Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa. 17Sa'ad da suke tafiya, suna tafiya a kowane waje, ba sai sun juya ba. 18Akwai waɗansu ƙarafa kamar zobe, da idanu kuma tantsai kewaye da ƙafafun.

19Duk sa'ad da talikan suka motsa, sai kuma ƙafafun su motsa tare da su. Idan kuma talikan suka ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga tare da su. 20Duk inda ruhu ya nufa, sai talikan su bi, sai kuma ƙafafun su tafi tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun. 21Idan talikan sun motsa, sai ƙafafun kuma su motsa. Idan sun tsaya cik, sai su ma su tsaya. Idan kuma talikan sun ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga sama tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.

22Sama da talikan akwai kamannin al'arshi mai walƙiya kamar madubi. 23A ƙarƙashin al'arshin fikafikansu sun miƙe kyam daura da juna. Kowane taliki yana da fikafikai biyu da su yake rufe jikinsa. 24Sa'ad da suke tafiya, sai na ji motsin fikafikansu kamar amon ruwa, kamar kuma muryar tsawar Maɗaukaki, kamar hayaniyar runduna. Idan sun tsaya cik, sai su saukar da fikafikansu. 25Sai aka ji murya ta fito daga saman al'arshi ɗin.

26A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta. 27Daga kwankwasonsa zuwa sama yana walƙiya kamar tagullar da aka kewaye ta da wuta. Daga kwankwasonsa zuwa ƙasa yana haskakawa kamar wuta. 28Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, hakanan kamannin hasken da ke kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.

2

Kiran Ezekiyel

1Sai ya ce mini, “Dan mutum, ka tashi tsaye, zan yi magana da kai.” 2Da ya yi magana da ni, sai Ruhu ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye, sa'an nan na ji yana magana da ni. 3Ya ce mini, “Ɗan mutum na aike ka zuwa wurin jama'ar Isra'ila, al'umma mai tayarwa, waɗanda suka tayar mini. Su da ubanninsu suna yi ta yi mini laifi har yau. 4Su mutane ne marasa kunya, masu taurinkai. Ga shi kuwa, na aike ka gare su, ka ce musu, “‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.” 5Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.

6“Kai ɗan mutum, kada ka ji tsoronsu, kada kuma ka ji tsoron maganganunsu, ko da ya ke ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya sun kewaye ka, kana kuma zaune tare da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne. 7Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.

8“Amma kai, ya ɗan mutum, ka ji abin da zan faɗa maka, kada ka zama mai tayarwa kamar 'yan tawayen nan. Sai ka buɗe bakinka, ka ci abin da zan ba ka.” 9Da na duba, sai ga hannu yana miƙo mini littafi. 10Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.

3

1Sai ya ce mini, “Ɗan mutum ka ci abin da aka ba ka. Ka ci wannan littafi, sa'an nan ka tafi ka yi wa mutanen Isra'ila magana.”

2Sai na buɗe bakina, sa'an nan ya ba ni littafin in ci. 3Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci littafin nan da na ba ka, ka cika tumbinka da shi.” Sai na ci littafin, na ji shi a bakina da zaƙi kamar zuma.

4Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ka tafi wurin mutanen Isra'ila ka faɗa musu maganata. 5Gama ba a aike ka a wurin mutane waɗanda ke da baƙon harshe wanda ba ka sani ba, amma zuwa mutanen Isra'ila, 6ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda ke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji. 7Amma mutanen Isra'ila ba za su ji ka ba, ba su kuwa da nufi su ji ni, gama suna da taurinkai da taurin zuciya. 8Ga shi, na sa fuskarka da goshinka su zama da tauri kamar nasu. 9Kamar yadda lu'ulu'u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, hakanan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.”

10Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, sai ka ji, ka karɓi dukan maganata da zan faɗa maka. 11Sa'an nan ka tafi wurin mutanenka waɗanda suke cikin bautar talala, ka faɗa musu, ko su ji, ko kada su ji.”

12Sa'an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.” 13Na kuma ji amon fikafikan talikan ne sa'ad da suka taɓa junansu, da kuma amon ƙafafun da ke kusa da talikan, da amon babban motsi. 14Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi. 15Na zo wurin 'yan bautar talala a Telabib, waɗanda ke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.

Ezekiyel ya Zama Mai Tsaron Isra'ila

(Eze 33.1-9)

16A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 17“Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina. 18Idan na ce wa mugu, “‘Lalle za ka mutu,” kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka. 19Amma idan ka faɗakar da mugu, ya kuwa ƙi barin muguntarsa, zai mutu cikin zunubinsa, kai kam ka kuɓuta.

20“Idan kuma adali ya bar adalci sa'an nan ya aikata zunubi, ni kuwa na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Zai mutu saboda zunubinsa domin ba ka faɗakar da shi ba. Ba za a tuna da ayyukansa na adalci waɗanda ya yi ba, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka. 21Amma idan ka faɗakar da adali, kada ya aikata zunubi, shi kuwa bai aikata zunubi ba, hakika zai rayu domin ya ji faɗakar, kai kuma ka kuɓuta.”

Annabi ya Zama Bebe

22Ikon Ubangiji yana tare da ni, Ubangiji kuwa ya ce mini, “Tashi, ka tafi ka tsaya a fili, a can zan yi magana da kai.”

23Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki. 24Ruhu kuwa ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye. Sai ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka cikin gida. 25Ya ɗan mutum, za a ɗaure ka da igiyoyi don kada ka tafi cikin jama'a. 26Ni kuwa zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka zama bebe, ka kasa tsauta musu, gama su 'yan tawaye ne. 27Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi ji musu magana, ka ce, “‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,” gama su 'yan tawaye ne.”

4

Ezekiyel ya Misalta yadda za a Kewaye Urushalima da Yaƙi

1“Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki tubali, ka ajiye a gabanka, sa'an nan kaz 2Sa'an nan ka gina mata kagara, da garu da ɗan tudu. Ka kuma kafa mata sansani ka kewaye ta da dundurusai. 3Ka ɗauki kwano, ka shirya shi kamar garun ƙarfe tsakaninka da birnin, sa'an nan ka zuba ido. Birnin zai zama kamar an kewaye shi da yaƙi, kai kuwa ka kewaye shi da yaƙi. Wannan kuma zai zama alama ga Isra'ilawa.

4“Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra'ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka. 5Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra'ila. 6Sa'ad da ka cika waɗannan kwanaki, sai ka sāke kwantawa, kwanciya ta biyu, a damanka kwana arba'in don ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Yahuza. Kwana ɗaya a bakin shekara guda.

7“Za ka fuskanci Urushalima wadda aka kewaye ta da yaƙi da hannunka a zāge, sa'an nan ka yi annabci a kanta. 8Ga shi, zan ɗaure ka da igiyoyi don kada ka juya har ka gama misalin adadin kwanakin da za a kewaye Urushalima da yaƙi.

9“Ka kuma ɗauki alkama, da sha'ir, da wake, da waken soya, da gero, da acca, ka haɗa su a kasko ɗaya, ka yi abinci da su. Shi ne za ka ci a kwanakin na ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. 10Za a auna maka abincin da za ka ci, kamar nauyin shekel ashirin ne a yini. Za ko ci shi a ƙayyadadden lokaci kowace rana. 11Za a kuma auna maka ruwan da za ka sha, misalin kwalaba biyu ga yini. Za ka sha ruwan a ƙayyadadden lokaci kowace rana. 12Za ka yi waina kamar ta sha'ir, ka ci. Za ka toya ta da najasa a idon jama'a.”

13Ubangiji ya ce, “Haka jama'ar Isra'ila za su ci ƙazantaccen abincinsu a cikin sauran al'umma inda za a kai su bautar talala.”

14Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”

15Sa'an nan ya ce mini, “To, zan bar ka ka mori taroson shanu maimakon najasa, don ka dafa abincinka.”

16Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ga shi, zan datse abinci a Urushalima. Za su auna abincin da za su ci da tsoro, su kuma auna ruwan da za su sha da damuwa. 17Haka abinci da ruwa za su kāsa, za su kuwa dubi juna da damuwa. Za su lalace saboda zunubansu.”

5

Ezekiyel ya Aske Kansa

1Ubangiji ya ce, “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki takobi mai kaifi, ka more shi kamar askar wanzami, ka aske kanka da gemunka. Ka auna gashin da ma'auni, don ka raba shi kashi uku. 2Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa'ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu. 3Za ka ɗibi gashi kaɗan ka ɗaure a shafin rigarka. 4Daga cikin gashi kaɗan ɗin nan kuma, sai ka ɗibi waɗansu ka sa a wuta. Daganan ne wuta za ta tashi a Isra'ila duka.”

5Ubangiji Allah ya ce, “Wannan ita ce Urushalima. Na kafa ta a tsakiyar al'ummai da ƙasashe kewaye da ita. 6Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da la'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da ke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina. 7Domin haka ni na ce, “‘Da ya ke kin cika rikici fiye da sauran ƙasashen da ke kewaye da ke, kin ƙi yin tafiya cikin dokokina, ba ki kiyaye ka'idodin ba, amma kin bi ka'ikodin al'umman da ke kewaye da ke, 8to, ina gāba da ke, zan hukunta ki a idanun al'ummai. 9Saboda yawan abubuwa masu banƙyama da kika aikata, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan sāke yin irinsa ba. 10Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.

11“‘Tun da ya ke kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba. 12Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa'an nan zan watsar da sulusinki ko'ina, zan kuma zare takobi a kansu.

13“‘Ta haka zan sa fushina ya huce, hasalata kuma a kansu ta lafa, ni kuma in wartsake. Sa'an nan za su sani ni Ubangiji na yi magana da zafin kishi sa'ad da na iyar da fushina a kansu. 14Zan kuma maishe ki kufai da abin zargi ga al'ummai da ke kewaye da ke, da kuma a idanun dukan masu wucewa.

15“‘Za ki zama abin zargi, da abin ba'a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al'ummai da ke kewaye da ke sa'ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa. 16Gama zan aiko miki da masifu na yunwa domin hallakarwa. Zan aiko miki da su don su hallaka ki. Zan kawo miki yunwa mai tsanani, in sa abincinki ya ƙare. 17Zan aiko miki da yunwa da namomin jeji, za su washe 'ya'yanki. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki. Zan kuma kawo takobi a kanki, ni Ubangiji na faɗa.”

6

Annabci gāba da Duwatsun Isra'ila

1Ubangiji ya yi magana da ni ya ce, 2“Ya ɗan mutum, ka zuba ido wajen duwatsun Isra'ila, sa'an nan ka yi annabci a kansu. 3Ka ce musu, “‘Ya ku duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Allah! Haka Ubangiji Allah ya ce a kan duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka. Ga shi, ni kaina, zan kawo takobi a kanku, zan hallaka wuraren tsafinku. 4Bagadanku za su zama kango, za a farfasa bagadanku na ƙona turare, zan sa kisassunku su faɗi a gaban gumakansu, 5zan sa gawawwakin Isra'ilawa a gaban gumakansu, zan warwatsa ƙasusuwanku kewaye da bagadanku. 6A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi. 7Za a kashe waɗansu daga cikinku sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.

8“‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al'umma. 9Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata. 10Za su kuma sani, ni Ubangiji, ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.”

11Ubangiji Allah ya ce, “Ka tafa hannunka, ka ɗage ƙafarka, sa'an nan ka ce, “‘Kaito, kaito, saboda dukan mugayen abubuwan ƙyama da mutanen Isra'ila suka yi, gama takobi, da yunwa, da annoba za su kashe su. 12Annoba za ta kashe wanda ke nesa, wanda ke kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu. 13Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa'ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu. 14Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji.”

7

Matuƙa ta Yi

1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ya kai, ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa ƙasar Isra'ila, matuƙa ta yi a kan kusurwa huɗu na ƙasar!

3“Yanzu matuƙarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara'anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan ƙazantarki. 4Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”

5Ubangiji Allah ya ce, “Masifa a kan masifa, ga shi, tana zuwa! 6Matuƙa ta yi, ta farka a kanki, ga shi, ta yi! 7Ƙaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.

8“Yanzu, ba da jimawa ba, zan fashe hasalata a kanku, in aukar da fushina a kanku, in hukunta ku bisa ga ayyukanku. Zan hukunta ku saboda dukan ƙazantarku. 9Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda ke hukunta ku.

10“Ga rana ta zo. Ƙaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho. 11Hargitsi ya habaka, ya zama sandan mugunta. Ba wanda zai ragu cikinsu, ko yawaitarsu, ko dukiyarsu, ko wani muhimmi a cikinsu.

12“Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka. 13Mai sayarwa ba zai ta da ciniki ba sa'ad da suke da rai, gama fushina yana bisa kan dukan taron jama'arsu, ba zai fasa ba. Ba wanda ke zamansa cikin zunubi da zai iya shiryar da kansa.”

Hukunci a kan Zunuban Isra'ila

14“Sun busa ƙaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaƙi, gama fushina yana kan dukan taron jama'a. 15Takobi9 yana zare a waje, annoba da yunwa suna ciki. Wanda ke waje takobi zai kashe shi, wanda kuma yake ciki annoba da yunwa za su kashe shi. 16Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa. 17Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa ƙarfi kamar ruwa. 18Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanƙo a kawunansu. 19Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya ƙosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu. 20Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su ƙazantattun abubuwa a gare su.

21“Zan ba da su ganima ga baƙi, da kwaso ga mugayen mutanen ƙasar. Za su lalatar da su. 22Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su ƙazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su ƙazantar da shi.

23“Sai ka ƙera surƙa, gama ƙasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi. 24Zan kawo al'ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu ƙarfi ta ƙare. Za a ƙazantar da masujadansu. 25Sa'ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba. 26Masifa a kan masifa, jita-jita a kan jita-jita. Suna neman wahayi daga wurin annabi, amma doka ta lalace a wurin firist, shawara kuma ta lalace a wurin dattawa. 27Sarki yana makoki, yarima kuma zai fid da zuciya. Hannuwan mutanen ƙasar sun shanye saboda razana. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su kamar yadda suka hukunta waɗansu. Za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

8

Wahayin Abubuwan Banƙyama da ake Yi a Urushalima

1A kan rana ta biyar ga wata na shida a shekara ta shida ta zaman talala, sa'ad da nake zaune a gidana, dattawan Yahuza kuma suna zaune a gabana, sai ikon Ubangiji Allah ya sauka akaina. 2Da na duba, sai ga siffa wadda ke da kamannin mutum. Daga kwankwason siffar zuwa ƙasa yana da kamannin wuta, daga kwankwason kuma zuwa sama yana da haske kamar na tagulla. 3Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda ke fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.

4Sai ga ɗaukakar Allah na Isra'ila a wurin, kamar wahayin da na gani a fili. 5Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka, ka duba wajen arewa.” Na kuwa ɗaga idanuna wajen arewa, na kuma ga siffa ta tsokano kishi a mashigin ƙofar bagade na wajen arewa.

6Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra'ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”

7Ya kuma kai ni ƙofar shirayi. Sa'ad da na duba, sai ga wani rami a bangon. 8Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa. 9Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.” 10Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon. 11Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama. 12Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ko ka ga abin da dattawan Isra'ilawa suke yi a cikin duhu? Kowa yana cikin ɗakin zānannun siffofin gumaka, sukan ce, “‘Allah ba ya ganinmu. Ubangiji ya rabu da ƙasan nan.”

13Ya kuma ce mini, “Har yanzu dai za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka waɗanda suke aikatawa.” 14Sai ya kai ni a bakin ƙofar arewa ta Haikalin Ubangiji, ga kuwa mata a zaune suna kuka domin gunkin nan, Tammuz.

15Sa'an nan ya ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Har yanzu ma za ka ga abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.” 16Ya kuma kai ni farfajiya ta can cikin Haikalin Ubangiji. Na ga mutum wajen ashirin da biyar a ƙofar Haikalin Ubangiji a tsakanin shirayi da bagade, suka juya wa Haikalin Ubangiji baya, suka fuskanci wajen gabas, suna yi wa rana sujada.

17Ya kuma ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Wato mutanen Yahuza ba su mai da aikata abubuwa masu banƙyama nan wani abu ba. Sun cika ƙasar da hargitsi, suna ta tsokanar fushina. Ga shi, suna hura hanci a gabana. 18Zan yi hukunci mai zafi, ba zan yafe ba, ba kuma zan ji tausayi ba, ko da ya ke suna kuka da babbar murya a kunnuwana ba zan ji su ba.”

9

An Kashe Masu Laifi

1Sai na ji Allah ya yi kira da babbar murya, ya ce, “Ku matso kusa, ku masu hukunta wa birnin, kowa ya zo da makaminsa na hallakarwa a hannu.” 2Sai ga mutum shida sun taho daga wajen ƙofa wadda take daga bisa wadda ta fuskanci arewa. Kowa yana da makaminsa na kisa a hannu. Tare da su kuma akwai wani mutum saye da rigar lilin, yana kuma rataye da gafaka. Sai suka tafi suka tsaya a gefen bagaden tagulla.

3Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tashi daga kan siffar kerubobi inda take zaune zuwa bakin ƙofar Haikalin. Sai Ubangiji ya kira mutumin da ke saye da rigar lilin, wanda ke rataye da gafaka. 4Ya ce masa, “Ka ratsa cikin birni, wato Urushalima, ka sa shaida a goshin mutanen da ke ajiyar zuciya, suna damuwa saboda dukan abubuwa masu banƙyama waɗanda ake aikatawa a birnin.”

5Na kuma ji ya ce wa sauran, “Ku bi shi, ku ratsa cikin birnin, ku kashe, kada ku yafe, kada kuwa ku ji tausayi. 6Ku kashe tsofaffi, da samari, da 'yan mata, da ƙananan yara, da mata, amma kada ku taɓa wanda ke da shaida. Sai ku fara Haikalina.” Suka kuwa fara da dattawan da ke a gaban Haikalin.

7Ya kuma ce musu, “Ku ƙazantar da Haikalin, ku cika farfajiya da kisassu, sa'an nan ku tafi!” Sai suka tafi, suka yi ta kashe mutanen da ke cikin birnin.

8Sa'ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra'ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”

9Sa'an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra'ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, “‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.” 10Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”

11Sai ga mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda kuma yake rataye da gafaka, ya komo da jawabi cewa, “Na aikata yadda ka umarci ni.”

10

Ɗaukakar Ubangiji ta Rabu da Haikali

1Da na duba sararin sama da ke bisa kawunan kerubobi, sai na ga wani abu ya bayyana kamar yakutu. Fasalinsa kamar na kursiyi. 2Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da ke saye da rigar lilin. “Ka shiga ƙarƙashin ƙafafun kerubobin, ka cika tafin hannunka da garwashin wuta wanda ke tsakanin kerubobin, ka watsa bisa kan birnin.” Na kuwa ga ya tafi. 3Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na Haikalin a sa'ad da mutumin ya shiga, girgije kuma ya cika farfajiyar da ke can ciki. 4Ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga kan kerubobin zuwa ƙofar Haikalin. Girgije kuwa ya cika Haikalin, hasken zatin Ubangiji ya cika farfajiyar. 5Sai aka ji amon fikafikan kerubobin a filin da ke can waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa'ad da yake magana.

6Ya kuwa umarci wanda yake saye da lilin ɗin, ya ce, “Ka ɗibi wuta daga ƙarƙashin ƙafafun da ke tsakanin kerubobin.” Sai ya tafi ya tsaya a gefen ƙafar. 7Kerub kuwa ya miƙa hannunsa daga tsakanin kerubobi zuwa wurin wutar da ke tsakanin kerubobin, ya ɗebo wutar, ya zuba a ahnnun mutumin da ke saye da rigar lilin. Shi kuwa ya karba, ya fita.

8Kerubobin suna da hannuwa kamar na 'yan adam a ƙarƙashin fikafikansu. 9Da na duba, sai na ga ƙafa guda huɗu kusa da kerubobin. Kowane kerub yana da ƙafa ɗaya kusa da shi. Ƙafafun suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja. 10Dukansu kuwa kamanninsu ɗaya, kamar ƙafa a cikin ƙafa. 11Sa'ad da suke tafiya, sukan tafi kowane waje, ba sai sun juya ba. Duk wajen da ƙafar gaba ta nufa, nan sauran za su bi, ba sai sun juya ba. 12Suna da idanu a jikunansu ko'ina, a bayansu, da hannuwansu, da fikafikansu da kuma ƙafafunsu. 13Na ji ana kiran ƙafafun, ƙafafun guguwa.

14Kowane kerbu yana da fuska huɗu. Fuska ta fari ta kerub ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuwa ta gaggafa ce. 15Kerubobin kuwa suka tashi sama. Waɗannan su ne talikai huɗu waɗanda na gani a bakin kogin Kebar. 16Sa'ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa'ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu. 17Sa'ad da suka tsaya cik, sai ƙafafun su ma su tsaya cik, sa'ad da suka tashi sama, sai su kuma su tashi tare da su, gama ruhun talikan yana cikinsu.

18Sai ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga bakin ƙofar Haikalin, ta tsaya bisa kerubobin. 19Kerubobin kuwa suka ɗaga fikafikansu, suka tashi daga ƙasa, suka yi sama a kan idona, suka tafi da ƙafafun gab da su. Suka tsaya a ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji. Ɗaukakar Allah na Isra'ila kuwa tana bisa kansu. 20Waɗannan su ne talikan da na gani a ƙarƙarshin kursiyin Allah na Isra'ila a bakin kogin Kebar, na kuwa sani su kerubobi ne.

21Kowannensu yana da fuska huɗu, da fiffike huɗu. A ƙarƙashin fikafikansu suna da hannuwa irin na 'yan adam. 22Kamannin fuskokinsu kuma daidai yake da kamannin fuskokin da na gani a bakin kogin Kebar. Sai suka tafi, kowa ya nufi gabansa sosai.

11

An Tsauta wa Mugayen Shugabanni

1Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda ke fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama'a.

2Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da ke ƙulla mugunta, waɗanda ke ba da muguwar shawara a cikin birnin. 3Waɗanda ke cewa, “‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.” 4Saboda haka ka yi musu annabci marar kyau, ka yi annabci, ya ɗan mutum!”

5Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya ce mini, “Ka ce, “‘In ji Ubangiji, haka kuke tunani, ku mutanen Isra'ila, gama na san abin da ke cikin zuciyarku. 6Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.”

7“Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa. 8Kun tsorata saboda takobi, ni kuwa zan kawo muku takobi,” in ji Ubangiji Allah. 9“‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku. 10Za a kashe ku da takobi. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji. 11Birnin ba ai zama muku tukunya mai ɓararraka ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinsa ba. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra'ila. 12Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, gama ba ku kiyaye dokokina da ka'idodina ba, amma kuka kiyaye ka'idodin sauran al'umma waɗanda suke kewaye da ku.”

13Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”

Allah ya Yi wa Waɗanda aka Kai Bautar Talala Alkawari

14Ubangiji kuwa ya yi magana da ni, ya ce, 15“Ɗan mutum, 'yan'uwanka, da danginka, da mutanenka da ke cikin bautar talala tare da kai, da dukan mutanen Isra'ila, su ne waɗanda mazaunan Urushalima ke ce musu, “‘Ku yi nisa da Ubangiji, mu aka mallakar wa wannan ƙasa.”

16“Domin haka, ka ce, “‘Ni Ubangiji Allah na ce, ko da ya ke na kai su nesa tsakanin al'ummai, na warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama Haikali a gare su a ɗan lokaci, a ƙasashen da suka tafi.”

17“Saboda haka ka ce, “‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.” 18Sa'ad da suka koma a ƙasar za su kawar da dukan abin da ya ƙazantar da ita, da dukan irin abar ƙyama da ke cikinta. 19Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi, 20domin su kiyaye dokokina, da ka'idodina, su aikata su. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu. 21Amma waɗanda zuciyarsu ta karkata zuwa ga bin ƙazantattun abubuwa masu banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, ni Ubangiji na faɗa.”

Ɗaukakar Ubangiji ta Rabu da Urushalima

22Sa'an nan kerubobin suka ɗaga fikafikansu tare da ƙafafunsu. Ɗaukakar Ubangiji kuwa tana bisa kansu. 23Sai ɗaukakar Ubangiji ta bar tsakiyar birni, ta tsaya a bisa kan dutse wanda ke wajen gabas da birnin. 24Ruhu kuwa ya ɗauke ni a cikin wahayi, ya kai ni Kaldiya wurin 'yan zaman talala. Sa'an nan wahayin da na gani ya rabu da ni. 25Sai na faɗa wa 'yan zaman talala dukan abin da Ubangiji ya nuna mini.

12

Kwatancin Kwashewarsu zuwa Bautar Talala

1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne. 3Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne. 4Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi. 5Ka huda katanga a kan idonsu, sa'an nan ka fita daga ciki. 6A gabansu za ka ɗauki kayan, ka saɓa shi a kafaɗarka, ka tafi da shi da dare. Za ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na maishe ka alama ga jama'ar Isra'ila.”

7Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa'an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.

8Da safe kuwa Ubangiji ya yi mini magana, ya ce, 9“Ɗan mutum, ashe, mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan, ko suka ce maka, “‘Me kake yi?” 10Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, “‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra'ila, waɗanda ke cikinta.” 11Ka ce musu, “‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.” 12Sarkin da ke cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa. 13Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da ya ke zai rasu a can. 14Zan warwatsa dukan waɗanda ke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko'ina. Zan zare takobi in runtume su.

15“Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe. 16Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, da yunwa, da annoba, don su tuba, su hurta dukan ayyukansu na banƙyama a cikin al'ummai inda suka tafi. Za su sani ni ne Ubangiji.”

Kwatancin Annabin da ke Rawar Jiki

17Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 18“Ɗan mutum, ka ci abincinka da rawar jiki, ka sha ruwanka da makyarkyata da damuwa. 19Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da ke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da ke ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda ke zaune cikinta. 20Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

Sanannen Karin Magana da Jawabi Marar Daɗi

21Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 22“Ɗan mutum, menene wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra'ila cewa, “‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba?” 23Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.

24“Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra'ila. 25Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

26Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 27“Ɗan mutum, ga shi, mutanen Isra'ila suna cewa, “‘Wahayin da ya gani na wani lokaci ne can gaba, yana annabci a kan wani zamani ne na can.” 28Domin haka ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji na ce maganata ba za ta yi jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

13

An La'anci Maƙaryatan Annabawa

1Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ya ɗan mutum, ka yi annabci a kan annabawan Isra'ila. Ka yi annabci a kan waɗanda suke annabci bisa ga ra'ayin kansu, ka ce, “‘Ku ji maganar Ubangiji!”

3“Ubangiji Allah ya ce kaito ga wawayen annabawa waɗanda suke bin ra'ayin zuciyarsu, ba su kuwa ga wani wahayi ba. 4Ya Isra'ila, annabawanki suna kamar diloli a kufai. 5Ba ku ƙaura zuwa inda garu ya tsage ba, ba ku gina wa mutanen Isra'ila garu don su kāre kansu a lokacin yaƙi, a ranar Ubangiji ba. 6Suna faɗar ƙarya, suna kuma yin duban ƙarya, suna cewa, “‘Ubangiji ya ce,” alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba, duk da haka sun sa zuciya ga cikawar maganarsu. 7Wahayin ƙarya ne kuka gani, kuna yin duban ƙarya, sa'ad da kuke cewa, “‘Ubangiji ya faɗa,” ko da ya ke ni Ubangiji ban faɗa ba.

8“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, da ya ke kun yi maganar wofi, kun ga wahayin ƙarya, ina gāba da ku. 9Ikona zai yi gāba da annabawan da ke ganin wahayin ƙarya, waɗanda suke kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin mutanen Isra'ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani, ni ne Ubangiji Allah.

10“Domin sun ɓad da mutanena suna cewa, “‘Salama,” sa'ad da ba salama, sa'ad da kuma mutanen ke gina garu marar aminci, sai annabawan nan su shafe shi da farar ƙasa, 11ka faɗa wa waɗanda suka shafe garun da farar ƙasa, cewa zai faɗi. Za a yi rigyawa da ƙanƙara, da babban hadiri mai iska. 12Sa'ad da garun ya faɗi, ashe, ba za a tambaye ku ba cewa, “‘Ina shafen farar ƙasar da kuka yi masa?”

13“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da hasalata zan sa babban hadiri mai iska, da rigyawa, da manyan ƙanƙara su hallaka shi. 14Zan rushe garun da kuka shafe da farar ƙasa. Za a baje shi, a bar tushen a fili. Za ku halaka a tsakiyarsa sa'ad da ya fāɗi, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

15“Ta haka zan aukar da hasalata a kan garun, da a kan waɗanda suka shafe shi da farar ƙasa. Sa'an nan zan faɗa muku, cewa garun ya faɗi tare da waɗanda suka shafe shi da farar ƙasa. 16Wato annabawan Isra'ila waɗanda suka yi annabci a kan Urushalima, suka ga wahayin salama dominta, ga shi kuwa, ba salama, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

An La'anci Mata Masu Annabcin Ƙarya

17“Kai kuwa ɗan mutum, sai ka ɗaure wa matan mutanenka fuska, waɗanda ke annabci bisa ga son zuciyarsu. Ka yi annabci a kansu, 18ka ce, “‘Ubangiji Allah ya ce, kaiton matan da ke ɗinka wa mutane kambuna, suna yi wa mutane rawunan dabo bisa ga zacinsu don su farauci rayukan mutane. Za ku farauci rayukan mutanena, sa'an nan ku bar rayukan waɗansu don ribar kanku? 19Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha'ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda ke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.”

20“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, ina gāba da kambunanku da kuke farautar rayuka da su. Zan tsintsinke su daga damatsanku, in saki rayuka waɗanda kuka farauto kamar tsuntsaye. 21Zan kuma kyakketa rawunanku na dabo, in ceci mutanena daga hannunku, ba za su ƙara zama ganima a hannunku ba, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

22“Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da ya ke ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira. 23Domin haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi dūba. Zan ceci mutanena daga hannunku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

14

An La'anci Bautar Gumaka

1Waɗansu dattawa na Isra'ila suka zo wurina, suka zauna a gabana. 2Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 3“Ɗan mutum, waɗannan mutane sun sa zukatansu ga bin gumaka, sun sa abin tuntuɓe a gabansu, zan fa yarda su yi tambaya a wurina>

4“Sai ka faɗa musu, cewa Ubangiji Allah ya ce duk mutumin Isra'ila, wanda ya manne wa gumaka, ya sa abin tuntuɓe a gabansa sa'an nan kuma ya zo wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa gwargwadon yawan gumakansa, 5domin in kama zukatan mutanen Isra'ila waɗanda suka zama baƙi a gare ni, saboda gumakansu.

6“Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, “‘Ubangiji ya ce ku tuba, ku rabu da gumakanku, da abubuwanku na banƙyama.

7“‘Gama duk wanda ke na Isra'ila da dukan baƙin da ke baƙunta cikin Isra'ila, wanda ya rabu da ni, ya manne wa gumakansa, ya sa abin tuntuɓe a gabansa, sa'an nan ya zo yana roƙona a wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa. 8Zan yi gāba da mutumin nan, zan sa ya zama abin nuni, da abin karin magana, in datse shi daga cikin mutanena, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

9“‘Idan aka ruɗi annabin har ya yi magana, ni Ubangiji, ni ne na rinjaye shi, zan miƙa hannuna gāba da shi, zan hallaka shi daga cikin mutanena, Isra'ila. 10Za su ɗauki alhakin hukuncinsu, wato hukuncin annabin, da hukuncin mai yin roƙonsa duk ɗaya ne, 11don kada mutanen Isra'ila su ƙara rabuwa da ni, ko kuma su ƙara ƙazantar da kansu ta wurin laifofinsu, amma za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu,” ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Hukuncin Allah a kan Urushalima

12Ubangiji ya yi magana da ni ya ce, 13“Ɗan mutum, sa'ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba, 14ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.

15“Idan na sa namomin jeji su ratsa cikin ƙasar, su lalatar da ita har ta zama kufai yadda mutum ba zai iya ratsawa ta cikinta ba saboda namomin jejin, 16ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, su ne kaɗai za su tsira, amma ƙasa za ta zama kufai.

17“Idan kuwa na jawo wa ƙasar takobi, na ce bari takobi ya ratse ƙasar, har na kashe mata mutum duk da dabba, 18ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, su kaɗai za su tsira. 19Ko kuma na aika da annoba a ƙasar, na kashe mutum duk da dabba da fushina, 20ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu.

21“Ni Ubangiji Allah na ce, “‘Balle fa sa'ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi, wato takobi, da yunwa, da mugayen namomin jeji, da annoba, don in kashe mutum duk da dabba! 22Idan kuwa waɗansu sun wanzu daga cikinta suka fita da 'ya'yansu mata da maza zuwa wurinta, za ka ga halinsu da ayyukansu, za ka tabbata, masifar da na aukar wa Urushalima, ba kawai ba ne. 23Bisa ga halinsu da ayyukansu za ka gane abin da na yi musu ba kawai ba ne,” ni Ubangiji na faɗa.”

15

Misali a kan Kurangar Inabi

1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum da me itacen kurangar inabi ya fi wani itace? Da me reshen kurangar inabi ya fi wani reshen itacen da ke a kurmi? 3Za a sami itace a cikin kuranga a yi aiki da shi? Ko kuwa mutane za su iya samun maratayi a cikinta don su rataye kaya? 4Ga shi, akan sa ta a wuta. Sa'ad da wutar ta cinye kanta da gindinta tsakiyarta kuma ta babbake, tana da amfani don yin wani aiki kuma? 5Ga shi ma, lokacin da take cikakkiya, ba ta da wani amfani, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita>

6“Domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, kamar itacen kurangar inabi a cikin itatuwan kurmi, wanda na sa ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama. 7Zan yi gāba da su, ko da ya ke sun tsere wa wuta, duk da haka wuta za ta cinye su. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tashi yin gāba da su. 8Zan sa ƙasar ta zama kufai domin sun yi rashin aminci, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

16

Rashin Amincin Urushalima da Samariya

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta na banƙyama. 3Ka faɗa wa Urushalima abin da ni Ubangiji Allah na ce mata.” Ubangiji ya ce, “Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan'ana ne. Mahaifinki Ba'amore ne, mahaifiyarki kuwa Bahittiya ce. 4Game da haihuwarki kuwa, ran da aka haife ki, ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka da ruwa don a tsabtace ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba, ba a naɗe ki cikin tsummoki ba. 5Ba wanda ya ji tausayinki da zai yi miki waɗannan abubuwa na jinƙai, amma aka jefar da ke a waje, gama kin zama abin ƙyama a ranar da aka haife ki.

6“Sa'ad da na wuce kusa da ke, na gan ki kina birgima cikin jinin haihuwarki, sai na ce miki lokacin da kike cikin jinin, “‘Ki rayu!” Ji, na ce miki lokacin da kike cikin jinin, “‘Ki rayu!” 7Na sa kin girma kamar tsiro a cikin saura. Kika yi girma, kika yi tsayi, kika zama cikakkiyar budurwa, kika yi mama, gashin kanki kuwa ya yi tsawo, amma duk da haka tsirara kike tik a lokacin.

8“Sa'ad da na sāke wucewa kusa da ke, na dube ki, ga shi, kin kai lokacin da za a kaunace ki, sai na yafe miki tufata, na rufe tsiraincinki, na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

9“Sa'an nan na yi miki wanka da ruwa, na wanke jinin haihuwarki na shafe ki da mai. 10Na sa miki rigar da aka yi wa ado, na kuma sa miki takalmin fata, na yi miki ɗamara da lilin mai kyau, na yi miki lulluɓi da siliki. 11Na kuwa caɓa miki ado, na sa mundaye a hannuwanki, da abin wuya a wuyanki. 12Na kuma sa ƙawanya a hancinki, da 'yan kunne a kunnenki, da kyakkyawan kambi bisa kanki. 13Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa. Tufafinki kuwa na lilin mai kyau ne, da siliki waɗanda aka yi musu ado. Kin ci lallausan gāri, da zuma, da mai. Kin yi kyau ƙwarai har kin zama sarauniya. 14Kin shahara a cikin sauran al'umma saboda kyanki, gama kyanki ya zama cikakke saboda ƙawata ki da na yi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

15“Amma kin dogara ga kyanki, kika yi karuwanci saboda shahararki. Kin yi ta karuwancinki da kowane mai wucewa. 16Kin ɗauki waɗansu rigunanki, kika yi wa kanki masujadai masu ado, sa'an nan kika yi karuwanci a cikinsu, irin abin da ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a yi ba nan gaba. 17Kin kuma ɗauki kayan adonki na zinariyata da azurfata waɗanda na ba ki, kin yi wa kanki siffofin mutane don ki yi karuwanci da su. 18Kin ɗauki tufafinki da aka yi musu ado, kika lulluɓe su, sa'an nan kika ajiye maina da turarena a gabansu. 19Abincina da na ba ki kuma, wato lallausan gāri, da mai, da zuma, waɗanda na ciyar da ke da su, kin ajiye a gabansu don ƙanshi mai daɗi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

20“Kin kuma kwashe 'ya'yana mata da maza waɗanda kika haifa mini kin miƙa su hadaya ga gumaka. Karuwancinki, ba ƙanƙanen abu ba ne. 21Kin karkashe 'ya'yana, kin sa su ratsa cikin wuta. 22A cikin aikata dukan abubuwanki na banƙyama kuma, da karuwancinki, ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, lokacin da kike tsirara tik, kina birgima cikin jinin haihuwarki.

23“Bayan dukan muguntarki Kaito, kaitonki! Ni Ubangiji Allah na faɗa, 24sai kika gina wa kanki ɗakunan tsafi a kowane fili. 25Kika kuma gina ɗakin tsafi a kowane titi. Kin waƙala darajarki, kin ba da kanki ga kowane mai wucewa, ta haka kika yawaita karuwancinki. 26Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi. Kin yawaita karuwancinki don ki tsokani fushina.

27“Domin haka na miƙa hannuna gāba da ke, na rage rabonki, na ba da ke ga abokin gābanki masu haɗama, 'yan matan Filistiyawa waɗanda suka ji kunya saboda halinki na lalata.

28“Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa domin ba ki ƙoshi ba. Kin yi karuwanci da su duk da haka ba ki ƙoshi ba. 29Kin yawaita karuwancinki da Kaldiya, ƙasar ciniki, duk da haka ba ki ƙoshi ba.

30“Kin cika uzuri,” in ji Ubangiji Allah. “Duba, kin aikata waɗannan abubuwa duka, ayyuka na karuwa marar kunya. 31Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da ya ke ba ki karɓar kuɗi. 32Ke mazinaciyar mace, mai kwana da kwartaye maimakon mijinki! 33Maza sukan ba dukan karuwai kuɗi, amma ke ce mai ba kwartayenki kuɗi, kina ba su kuɗi don su zo wurinki don kwartanci daga ko'ina. 34Kin yi dabam da sauran mata a cikin karuwancinki, da ya ke ba wanda ya bi ki don yin karuwanci, ba a ba ki kuɗi, ke ce kike ba da kuɗi, domin haka kin sha bamban.”

35Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.

36“Ubangiji Allah ya ce, da ya ke kunyarki ta bayyana, an buɗe tsiraicinki cikin karuwancinki, saboda kuma gumakanki, da jinin 'ya'yanki da kika miƙa wa gumakanki, 37domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani. 38Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina. 39Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.

40“Za su kuta taron mutane a kanki, za su jajjefe ki da duwatsu, su yayanka ki gunduwa gunduwa da takubansu. 41Za su kuma ƙone gidajenki, su hukunta ki a gaban mata da yawa. Ni kuwa zan sa ki bar karuwanci, ba za ki ƙara ba da kuɗi ga kwartayenki ba. 42Sa'an nan fushina a kanki zai huce, kishina a kanki zai ƙare. Zan huce, ba zan yi fushi ba kuma. 43Da ya ke ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, domin haka zan sāka miki alhakin ayyukanki. Kin yi lalata, banda ayyukanki na banƙyama kuma, ni Ubangiji na faɗa.”

44Ubangiji ya ce, “Ga shi, duk mai yin amfani da karin magana, zai faɗi wannan karin magana a kanki. “‘Kamar yadda mahaifiya take haka 'yar take.” 45Ke 'yar mahaifiyarki ce wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta. Ke kuma 'yar'uwar 'yar'uwanki mata ce waɗanda suka ƙi mazansu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahittiya ce, mahaifinki kuwa Ba'amore ne.

46“'Yarki ita ce Samariya wadda ke zaune da 'ya'yanta mata wajen arewa da ke. Ƙanwarki ita ce Saduma wadda ke zaune kudu da ke tare da 'ya'yanta mata. 47Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.

48“Hakika ni Ubangiji Allah na ce Saduma ƙanwarki da 'ya'yanta mata ba su yi kamar yadda ke da 'ya'yanki mata kuka yi ba. 49Wannan shi ne laifin Saduma, ƙanwarki, ita da 'ya'yanta mata, suna da girmankai domin suna da abinci a wadace, suna zama a sangarce, amma ba su taimaki matalauta da masu bukata ba. 50Su masu alfarma ne, sun aikata abubuwa masu banƙyama a gabana, saboda haka na kawar da su sa'ad da na gani.

51“Samariya ba ta aikata rabin zunubin da kika aikata ba. Abubuwan banƙyama da kika aikata sun sa 'yan'uwanki sun zama kamar adalai. 52Ke kuma sai ki sha kunyarki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su sami rangwamin shari'a saboda zunubanki da kika aikata fiye da nasu, gama gwamma su da ke. Sai ki ji kunya, ki sha ƙasƙancinki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su zama kamar adalai.”

53Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Zan komo da Saduma da Samariya da 'ya'yansu mata daga bauta. Sa'an nan zan komo da ke daga bauta tare da su, 54don ki sha ƙasƙanci saboda abin kunyar da kika aikata. Ƙasƙancinki zai ta'azantar da 'yan'uwanki mata. 55'Yan'uwanki mata, wato Saduma da 'ya'yanta mata za su koma kamar yadda suke a dā, Samariya kuma da 'ya'yanta mata za su koma kamar yadda suke a dā. Ke kuma da 'ya'yanki mata za ku koma kamar yadda kuke a dā. 56Ashe, ba ƙanwarki, Saduma, ta zama abar karin magana a bakinki a kwanakin fariyarki, 57kafin asirin muguntarki ya tonu ba? Amma yanzu kin zama abin zargi ga 'ya'yan Edom mata, da waɗanda ke kewaye da ita, da 'ya'yan Filistiyawa mata waɗanda ke kewaye, waɗanda suke raina ki. 58Kina ɗauke da hukuncin lalatarki da na abubuwanki masu banƙyama, ni Ubangiji na faɗa.”

Alkawarin da zai Dawwama

59“Ni Ubangiji Allah na ce, zan yi miki yadda kika yi, ke da kika yi rantsuwar kafara, kika ta da alkawari. 60Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin kuruciyarki. Zan ƙulla madawwamin alkawari da ke. 61Sa'an nan za ki tuna da ayyukanki, ki ji kunya, sa'ad da na ɗauki yarki da ƙanwarki, na ba ki su, su zama 'ya'yanki mata, amma ba a kan alkawarin da na yi da ke ba. 62Zan ƙulla alkawarina da ke, za ki sani ni ne Ubangiji, 63domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa'ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

17

Misalin Gaggafa da Kurangar Inabi

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen Isra'ila ka-cici-ka-cici, da kuma misali. 3Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, “‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafika da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul. 4Ta karya kan tohonsa mafi tsawo, ta kai shi a ƙasar ciniki, ta dasa shi a birnin 'yan kasuwa. 5Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi. 6Ya yi toho, ya zama kuranga mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajenta. Saiwoyinta suka kama ƙasa sosai. Haka ta zama kuranga, ta yi rassa da ganyaye.

7“‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa. 8An dasa ta a wuri mai dausayi inda akwai ruwa da yawa don ta yi ganyaye, ta kuma ba da 'ya'ya, ta zama kurangar inabi ta ƙwarai.” 9Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, “‘Ko wannan kurangar inabi za ta ci gaba? Ashe, gaggafa ta farko ba za ta tumɓuke saiwoyinta, ta sassare rassanta, don ganyayenta da ke tohuwa su bushe ba? Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba. 10Idan aka sāke dasa ta kuma za ta yi amfani? Ba za ta bushe sarai sa'ad da iskar gabas ta hura ba? Lalle za ta bushe tun daga inda aka dasa ta ta yi girma.”

Fassarar Misalin

11Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 12“Ka tambayi mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan cewa, “‘Ba ku san ma'anar waɗannan abubuwa ba?” Ka faɗa musu, cewa Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya tafi da sarkinta da shugabanninta zuwa Babila. 13Sai ya dauƙi wani daga zuriyar sarauta, ya yi alkawari da shi, ya kuma rantsar da shi. Ya kwashe mutanen ƙasa masu maƙami, 14don sarautar ƙasar ta raunana, ta kāsa ɗaga kanta, amma ta tsaya dai ta wurin cika alkawarinsa. 15Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere>

16“Ni Ubangiji Allah, na ce, hakika wannan sarki zai mutu a Babila, domin bai cika rantsuwarsa da alkawarin da ya yi wa Sarkin Babila, wanda ya naɗa shi ba. 17Fir'auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa'ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa. 18Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.

19“Domin haka ni Ubangiji Allah, na ce, hakika zan nemi hakkin rantsuwar da ya yi mini, da alkawarin da ya yi mini, waɗanda bai cika ba. 20Zan kafa masa tarko in kama shi, sa'an nan in kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda ya tayar mini. 21Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a watsar da waɗanda suka ragu ko'ina. Za ku sani ni Ubangiji ne na faɗa.”

Alkawarin Sa Zuciya

22Ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Ni kaina zan cire toho a kan itacen al'ul mai tsawo. Daga cikin sababbin rassansa zan karya lingaɓu, In dasa shi a tsauni mai tsayi.

23A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shi Don ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya, Ya zama itacen al'ul na gaske. Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa, Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.

24Dukan itatuwan jeji za su sani, Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana, In sa ƙanana kuma su zama manya, In sa ɗanyen itace ya bushe, In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”

18

Hakkin Kowa

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa, “‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami, Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu?”

3“Ni Ubangiji Allah na ce, hakika, ba za a ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. 4Ga shi, dukan rayuka nawa ne, da ran uban da na ɗan, duka nawa ne. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu.

5“Ga irin mutumin da zai rayu, mutumin da yake adali, yana bin shari'a, yana kuma aikata abin da ke daidai, 6idan ba ya cin abinci a ɗakin tsafi, bai bauta wa gumakan mutanen Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, ba yakan kwana da mace a lokacin hailarta ba, 7wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa, 8wanda ba ya ba da bashi da ruwa, ko tare da wani ƙari, wanda yake hana hannunsa yin mugunta, amma yana goyon bayan gaskiya tsakanin masu gardama, 9wanda ke bin dokokina, yana kuma kiyaye ka'idodina da aminci, shi adali ne. Hakika zai rayu, ni Ubangiji na faɗa.

10“Amma idan ya haifi ɗa wanda ya zama ɗan fashi, mai kisankai, yana yi wa ɗan'uwansa ɗaya daga cikin abubuwan nan, (ko shi kansa, 11bai yi irin waɗannan abubuwa ba), wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa, 12yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama, 13yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.

14“Amma idan wannan mutum ya haifi ɗa wanda ya ga dukan laifofin da mahaifinsa ya yi, sa'an nan ya ji tsoro, bai kuwa yi haka ba, 15bai ci abinci a ɗakin tsafi ba, bai bauta wa gumakan mutanen gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, 16bai ci zalin kowa ba, bai karɓi jingina ba, bai yi ƙwace ba, amma yana ba mayunwaci abinci, yana ba huntu tufa, 17yana hana hannunsa aikata mugunta, bai ba da bashi da ruwa ko wani ƙari ba, yana kiyaye ka'idodina, yana kuma bin dokokina, ba zai mutu saboda laifin mahaifinsa ba, amma zai rayu. 18Amma mahaifinsa, da ya ke ya yi zalunci, ya yi wa ɗan'uwansa ƙwace ya aikata mugun abu a cikin mutanensa, zai mutu saboda muguntarsa.

19“Za ku yi tambaya cewa, “‘Me ya sa ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba?” Sa'ad da ɗan ya bi shari'a, ya yi abin da ke daidai, ya kiyaye dokokina sosai, lalle zai rayu. 20Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.

Ayyukan Allah daidai Ne

(Eze 33.10-20)

21“Amma idan mugu ya bar dukan muguntarsa da ya aikata, ya kiyaye dokokina, ya bi shari'a, ya yi abin da ke daidai, zai rayu, ba zai mutu ba. 22Ba za a bi hakkin laifin da ya aikata ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi. 23Ni Ubangiji Allah, na ce, ina jin daɗin mutuwar mugu ne? Ban fi so ya bar mugun halinsa ya rayu ba>

24“Amma idan adali ya bar yin adalci, ya aikata mugunta, ya yi abubuwa masu banƙyama waɗanda mugu ke aikatawa, zai rayu? Ayyukansa na adalci waɗanda ya aikata, ba za a tuna da su ba, faufau. Zai mutu saboda rashin amincin da ya yi da laifin da ya aikata.

25“Amma kum ce, “‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.” Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba? 26Sa'ad da adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda muguntarsa. 27Idan kuma mugu ya bar muguntarsa da yake yi, ya kuwa bi shari'a, ya yi abin da ke daidai, zai rayu. 28Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba. 29Amma mutanen Isra'ila suna cewa hanyar Ubangiji ba daidai ba ce. Ya mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba>

30“Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka. 31Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa'an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama'ar Isra'ila? 32Ni Ubangiji Allah na ce ba na murna da mutuwar kowa, saboda haka sai ku tuba domin ku rayu.”

19

Makoki a kan Hakiman Isra'ila

1“Sai ka yi makoki domin hakiman Isra'ila,

2Ka ce, “‘Mahaifiyarka zakanya ce a cikin zakoki, Ta yi zamanta tare da 'yan zakoki, Ta yi renon kwiyakwiyanta.

3Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, Ya zama sagari, Sai ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.

4Da al'ummai suka ji labarinsa, Sai suka kama shi cikin wushefensu, Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa Masar.

5Sa'ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi, Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta, Ta goye shi ya zama sagari.

6Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki, Ya zama sagari, Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.

7Ya lalatar da kagaransu, Ya mai da biranensu kufai, Ƙasar da waɗanda ke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.

8Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje, Sun kafa masa tarko, Suka kama shi cikin wushefensu.

9Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka sa shi cikin suru, Suka kai shi wurin Sarkin Babila. Suka sa shi a kurkuku don kada a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra'ila.”

Busasshiyar Kurangar Inabi

10“‘Mahaifiyarka tana kama da kurangar inabi, Wadda aka dasa kusa da ruwa, Ta ba da 'ya'ya da rassa da yawa, saboda isasshen ruwa.

11Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki, Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan, Ana hangenta daga nesa.

12Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi, Aka jefar da ita ƙasa. Iskar gabas ta busar da ita, 'Ya'yanta suka kakkaɓe, Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.

13Yanzu na dasa ta a jeji, cikin busasshiyar ƙasa,

14Wuta ta fito daga jikinta Ta cinye rassanta da 'ya'yanta, Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki. Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.”

20

Yadda Ubangiji ya Bi da Isra'ila

1A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta bakwai, sai waɗansu dattawan Isra'ila suka zo don su yi roƙo a wurin Ubangiji. Suka zauna a gabana. 2Ubangiji kuwa ya yi magana da ni ya ce, 3“Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila cewa, “‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.”

4“Za ka shara'anta su? Ɗan mutum, shara'anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi. 5Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, 6a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da ke da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka. 7Sai na ce musu, “‘Bari kowane ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama da kuke jin daɗinsu, kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masarawa, gama ni ne Ubangiji Allahnku.” 8Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar. 9Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi mutanen Isra'ila suke zaune, gama na sanar da kaina ga mutanen Isra'ila, a gaban sauran al'umma kuma, sa'ad da na fito da mutanen Isra'ila, daga ƙasar Masar.

10“Sai na fisshe su daga ƙasar Masar, na kawo su cikin jeji. 11Na ba su dokokina da ka'idodina, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. 12Na kuma ba su ranar Asabar don ta zama alama tsakanina da su, don kuma su sani ni ne Ubangiji wanda ke tsarkake su. 13Amma mutanen Isra'ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu. 14Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana a cikin sauran al'umma waɗanda a kan idonsu na fisshe su. 15Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da ke cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka, 16domin sun ƙi su bi ka'idodina da dokokina. Suka ɓata ranar Asabar ɗina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumaka.

17“Duk da haka na yafe musu, ban hallaka su ba, ban kuma shafe su a jeji ba. 18Sai na ce wa 'ya'yansu a jeji, “‘Kada ku bi dokokin ubanninku, ko kuwa ku kiyaye ka'idodinsu, kada kuma ku ɓata kanku da gumakansu. 19Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka'idodina sosai. 20Ku kiyaye ranar Asabar ɗina domin ta zama alama tsakanina da ku, domin kuma ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.”

21“Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji. 22Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al'umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar. 23Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al'umma, da sauran ƙasashe 24domin ba su kiyaye ka'idodina da dokokina ba, suka ɓata ranar Asabar ɗina, suka bauta wa gumakan kakanninsu. 25Sai kuma na ba su dokoki da ka'idodi marasa amfani, waɗanda ba za su rayu ta wurinsu ba. 26Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.

27“Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, “‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba. 28Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.” 29Sai na ce, “‘Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?” Domin haka aka kira sunan wurin Bama, wato tudu. 30Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, “‘Ni Ubangiji Allah na ce za ku ƙazantar da kanku kamar yadda kakanninku suka yi? Za ku bi abubuwan da suka yi na banƙyama? 31Sa'ad da kuke miƙa hadaya, kuna miƙa 'ya'yanku hadaya ta ƙonawa, kuna ƙazantar da kanku ta wurin gumakanku har wa yau, to, za ku iya tambayata, ya ku mutanen Isra'ila? Ni Ubangiji Allah ba na tambayuwa gare ku. 32Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku, cewa kuna so ku zama kamar sauran al'umma da kabilan ƙasashe, ku bauta wa itace da dutse, ba zai taɓa faruwa ba.”

33“Hakika, ni Ubangiji Allah na ce, zan sarauce ku ƙarfi da yaji, da fushi, 34da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku. 35Zan kawo ku cikin ruƙuƙin jama'a, in yi muku shari'a fuska da fuska. 36Kamar yadda na yi wa kakanninku shari'a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari'a, ni Ubangiji Allah na faɗa.

37“Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sanda, in ƙulla alkawarina da ku. 38Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.

39“Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da ya ke ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.

40“Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau. 41Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fisshe ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku. Zan nuna tsarkina a cikinku a idon sauran al'umma. 42Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na kawo ku ƙasar Isra'ila, ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. 43A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata. 44Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na yi muku haka saboda sunana, ba saboda mugayen ayyukanku ba, ya ku mutanen Isra'ila. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Annabci a kan Kudu

45Ubangiji ya yi magana da ni ya ce, 46“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen kudu ka ja kunnen mutanen kudu, ka kuma yi annabci gāba da kurmin ƙasar Negeb. 47Ka ce wa kurmin Negeb, “‘Ka ji maganar Ubangiji, gama Ubangiji Allah ya ce zai kunna wuta a cikinka, za ta kuwa cinye kowane ɗanyen itace, da kowane busasshen itacen da ke cikinka. Ba za a kashe harshen wutar ba. Harshen wutar zai babbake kowace fuska daga kudu zuwa arewa. 48Dukan masu rai za su sani ni Ubangiji ne na kunna wutar, ba wanda zai kashe ta.”

49Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, suna cewa misalai kawai, nake yi.”

21

Takobin Ubangiji

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ya ɗan mutum, ka fuskanci Urushalima, ka yi magana gāba da masujadanta, ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra'ila. 3Ka faɗa wa ƙasar Isra'ila, ka ce, ni Ubangiji na ce ina gāba da ita. Zan zare takobina daga cikin kubensa, in karkashe adalai da mugaye daga cikinta. 4Da ya ke zan karkashe adalai da mugaye daga cikinta, domin haka takobina zai fito daga cikin kubensa, ya karkashe dukan mutane daga Negeb wajen kudu, har zuwa arewa. 5Dukan mutane kuwa za su sani, ni Ubangiji, na zare takobina daga cikin kubensa, ba kuwa zan sāke mayar da shi a kubensa ba.

6“Domin haka, ya kai ɗan mutum, sai ka yi nishi, da ajiyar zuciya, da baƙin ciki mai zafi a gabansu. 7Idan sun tambaye ka, “‘Me ya sa kake nishi?” Sai ka ce musu, “‘Saboda labarin abin da ke zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,” ni Ubangiji Allah na faɗa.”

8Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 9“Ya ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce ni Ubangiji na ce, “‘Takobi, takobi wasasshe, Kuma gogagge!

10An wasa shi domin kisa, An goge shi don ya yi walwal kamar walƙiya!” Ba wanda zai iya tsai da shi, domin kun ƙi karɓar shawara. 11An ba da takobin a goge shi domin a riƙe. An wasa shi, an kuma goge shi domin a ba mai kashewa. 12Ka yi kuka, ka yi ihu, ya ɗan mutum, gama takobin yana gāba da jama'ata da dukan shugabannin Isra'ila. An ba da shugabanni da jama'ata ga takobi, sai ka buga ƙirjinka da baƙin ciki. 13Gama ba don jarraba shi ba ne, sai me kuma idan ka raina sandan? Ni Ubangiji na faɗa.

14“Domin haka, ya kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka tafa hannuwanka, ka kaɗa takobi sau biyu, har sau uku. Takobin zai kashe waɗanda za a kashe. Takobi ne na yin kashe-kashe mai yawa. Zai kewaye su. 15Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe. 16Ka yi sara dama da hagu, duk inda ka juya. 17Ni kuma zan tafa hannuwana, zan aukar da fushina, ni Ubangiji na faɗa.”

Takobin Sarkin Babila

18Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 19“Ya ɗan mutum, ka nuna hanya biyu inda takobin Sarkin Babila zai bi. Dukansu biyu za su fito daga ƙasa ɗaya. Ka kafa shaidar hanya a kan magamin hanya zuwa birni. 20Ka nuna wa takobin hanya zuwa Rabba ta Ammonawa, da hanya zuwa Yahuza, da Urushalima, birni mai garu. 21Gama Sarkin Babila yana tsaye a mararrabar hanya, inda hanyar ta rabu biyu, yana yin dūbā, yana girgiza kibau, yana neman shawara wurin kan gida, yana dūbān hanta. 22A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi. 23Amma a gare su dūbān nan ba gaskiya ba ce, gama sun riga sun yi rantsuwa mai nauyi, amma zai tuna musu da laifinsu, don a kama su. 24Domin haka ni Ubangiji Allah na ce, tun da ya ke kun sa a tuna da laifofinku, an kuma tone su, laifofinku kuma sun bayyana cikin ayyukanku, kun tonu, to, za a kama ku a cikinsu.

25“Kai kuma ƙazantaccen mugu, yariman Isra'ila, ranarka ta zo, lokacin hukuncinka ya yi. 26Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma. 27Halaka, halaka, zan hallakar, ba za a bar ko alama ba, sai mai shi ya zo, shi ne zan ba shi.”

Hukunci a kan Ammonawa

28“Kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce, ga abin da Ubangiji Allah ya ce a kan Ammonawa, da a kan zarginsu. “‘An zare takobi don kashe-kashe, An goge shi don ya yi sheƙi kamar walƙiya!

29Ka faɗa wa Ammonawa, cewa wahayin da suke gani ƙarya ne annabcin da suke yi kuma ƙarya ne. Su mugaye ne, ranar hukuncinsu tana zuwa. Za a sare wuyansu da takobi.

30“‘Ka mai da takobinka cikin kubensa. Zan hukunta ka a ƙasarka inda aka haife ka. 31Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa. 32Za ka zama itacen wuta, za a zubar da jininka a tsakiyar ƙasar. Ba za a ƙara tunawa da kai ba, ni Ubangiji na faɗa.”

22

Laifofin Urushalima

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Kai ɗan mutum, za ka shara'anta? Za ka shara'anta birni mai kisankai? To, sai ka faɗa masa dukan ayyukansa na banƙyama. 3Sai ka ce masa, “‘Ni Ubangiji Allah na ce, birnin da ke kisankai, yana kuma bauta wa gumaka don ya ƙazantar da kansa, lokacinsa zai yi! 4Ka yi laifi saboda ka zubar da jini, ka ƙazantar da kanka da gumakan da ka yi. Saboda haka ka matso da lokacinka kusa, ƙayyadaddun shekarunka sun cika. Domin haka na maishe ka abin zargi ga sauran al'umma, da abin ba'a ga dukan ƙasashe. 5Waɗanda ke kusa, da waɗanda ke nesa za su yi maka ba'a, gama kai shahararren mugu ne, cike da hargitsi. 6Ga shi, kowane shugaban Isra'ila da ke cikinka ya himmantu ga zub da jini bisa ga ikonsa. 7A cikinka ana raina mahaifi da mahaifiya, ana kuma tsananta wa baƙo, ana cin zalin marayu, da gwauruwa, wato wadda mijinta ya mutu. 8Ka raina tsarkakan abubuwa, ka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. 9Akwai mutane a cikinka waɗanda ke haddasa rikici don su zubar da jini, akwai kuma mutanen da ke cin abinci a matsafai, akwai mutanen da ke aikata lalata. 10A cikinka, mutane suna kwana da matan mahaifansu, waɗansu suna kwana da mata a lokacin hailarsu. 11Wani yakan yi lalata da matar maƙwabcinsa, wani kuma ya kwana da matar ɗansa, wani ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa. 12A cikinka mutane suka karɓi toshi don su zub da jini. Kana ba da rance da ruwa da ƙari, kana kuma cin riba a kan maƙwabcinka saboda cutar da kake yi masa, ka kuwa manta da ni, ni Ubangiji na faɗa.

13“‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar. 14Zuciyarka za ta iya ɗaurewa, hannuwanka kuma za su ƙarfafa a ranar da zan gamu da kai? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata. 15Zan watsar da kai cikin al'ummai, in warwatsa ka cikin ƙasashe, zan kawo ƙarshen mugayen ayyukanka. 16Za a ƙasƙantar da kai a gaban sauran al'umma, sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji.”

Tanderun Tsarkakewa

17Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 18“Ɗan mutum, mutanen Isra'ila sun zama kamar ƙwan maƙera a gare ni. Dukansu sun zama kamar tagulla, da kuza, da baƙin ƙarfe, da darma, a tanderu, sun zama ƙwan maƙera na azurfa. 19Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da ya ke dukanku kun zama ƙwan maƙera zan tattara dukanku a Urushalima. 20Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da darma, da kuza a cikin tanderu, su hura wuta a kansu, don su narkar da su, haka zan tattara ku da zafin fushina in narkar da ku. 21Zan tattaro ku, in hura muku wutar hasalata, za ku narke a cikinta. 22Kamar yadda azurfa takan narke a cikin tanderu, haka kuma za ku narke, za ku sani ni, Ubangiji ne, na zubo muku da zafin fushina.”

Laifofin Shugabannin Isra'ila

23Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 24“Ɗan mutum, ka ce mata, “‘Ke ƙasa ce marar tsarki, wadda ba a yi ruwan sama a kanki ba a lokacin da na yi fushi.” 25Annabawanta suna kama da zakoki masu ruri waɗanda suke yayyage ganimar da suka samu. Sun kashe mutane, sun ƙwace dukiya da abubuwa masu daraja. Sun sa mata da yawa sun rasa mazansu. 26Firistocinta sun karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana. Ba su bambanta tsakanin abin da ke mai tsarki da marar tsarki ba, ba su kuma koyar da bambancin da ke tsakanin halal da haram ba. Ba su kiyaye ranar Asabar ɗina ba, da haka suke saɓon sunana. 27Shugabanninta sun zama kamar kyarketai masu yayyage ganima. Suna yin kisankai don su sami ƙazamar riba. 28Annabawanta sun yi musu shafe da farar ƙasa, wato wahayan da suke gani, da duban da suke yi musu ƙarya ne. Suna cewa Ubangiji ne ya faɗa, alhali kuwa ni Ubangiji ban faɗa musu kome ba. 29Mutanen ƙasar sun yi zalunci, sun yi fashi, sun zalunci matalauta da masu fatara. Ba su yi wa baƙo adalci ba, sai cuta. 30Sai na nemi mutum a cikinsu wanda zai gina garun ya tsaya a hauren garun a gabana, domin kada in hallaka ƙasar, amma ban sami kowa ba. 31Saboda haka na kwarara musu fushina, na ƙone su da wutar hasalata, na ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

23

'Yan Mata Biyu

1Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, akwai waɗansu mata biyu, uwarsu ɗaya. 3Sun yi karuwanci a Masar, a lokacin 'yan matancinsu, aka rungumi mamansu da ƙirjinsu. 4Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima. 5Ohola ta yi karuwanci sa'ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa, 6waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha'awa, suna bisa kan dawakansu. 7Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. 8Ba ta bar karuwancinta ba, wanda ta yi tun tana a Masar, gama a lokacin 'yan matancinta mutane sun kwana da ita, sun rungumi ƙirjinta, suka biya kwaɗayinsu a kanta. 9Domin haka na bashe ta a hannun kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. 10Waɗannan suka tsiraita ta, suka kama 'ya'yanta mata da maza, suka kashe ta da takobi. Sai ta zama abin karin magana a wurin mata sa'ad da aka hukunta ta.

11“Ƙanwarta kuwa ta ga wannan, amma duk da haka ta fi ta lalacewa saboda kai da kawowa na karuwanci, wanda ya fi na 'yar uwarta muni. 12Ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, a wurin masu mulki da manyan sojoji waɗanda ke saye da kayan yaƙi, suna bisa kan dawakai, dukansu samari ne masu bansha'awa. 13Na ga ta ƙazantu. Dukansu biyu suka bi hanya ɗaya.

14“Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a jikin bango, siffofin Kaldiyawa ne aka zāna da jan launi! 15Sun sha ɗamara a gindinsu, da rawuna a kansu suna kaɗawa filfil. Dukansu suna kama da jarumawa. Su siffofi suna kama da mutanen Babila na ƙasar Kaldiya. 16Sa'ad da ta gan su, sai ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Ta aiki jakadu a wurinsu, wato a Kaldiya. 17Sai Babilawa suka zo wurinta, a gadonta na nishaɗi, suka ƙazantar da ita ta wurin kwana da ita. Bayan da sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su. 18Ta yi ta karuwancinta a fili, ta bayyana tsiraicinta. Sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita kamar yadda na rabu da 'yar'uwarta. 19Duk da haka ta yi ta ƙara karuwancinta, tana tunawa da kwanakin 'yan matancinta, a lokacin da ta yi karuwancinta a ƙasar Masar. 20Ta yi ta kai da kawowa tsakanin kwartayenta waɗanda al'auransu kamar na jakai ne, maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne. 21Haka kika yi ƙawar zucin lalatar da kika yi a lokacin 'yan matancinki, sa'ad da Masarawa suka rungumi mamanki na ƙuruciya.”

Hukuncin Allah a kan 'Yan Matan nan Biyu

22“Domin haka, ya Oholiba, ni, Ubangiji Allah na ce zan kuta kwartayenki su yi gāba da ke, waɗanda kika ji ƙyamarsu, kika rabu da su. Daga kowane sashi zan sa su zo su yi gāba da ke. 23Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha'awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai. 24Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu. 25Zan yi fushi da ke don su wulakanta ki. Za su datse hancinki da kunnuwanki. Waɗanda suka rage miki za a kashe su da takobi. Za su kama 'ya'yanki mata da maza, waɗanda suka rage miki kuwa, za a ƙone su da wuta. 26Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu'ulu'anki. 27Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.

28“Gama ni Ubangiji Allah na ce, “‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su. 29Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki. 30Lalatarki da karuwancinki su suka jawo miki wannan, gama kin yi karuwanci da sauran al'umma kika ƙazantar da kanki da gumakansu. 31Kin bi halin 'yar'uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.”

32Ubangiji Allah ya ce, “Za ki sha babban hukuncin da 'yar'uwarki ta sha, Za a yi miki dariya da ba'a, Gama hukuncin yana da tsanani.

33Za ki sha wahala da baƙin ciki, Hukunci na bantsoro da lalacewa, Shi ne irin hukuncin da aka yi wa 'yarki Samariya.

34Ƙoƙon da kika sha hukunci daga ciki, za ki lashe shi, Ki tattaune sakainunsa, Ki tsattsage nononki, Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

35Ubangiji ya ce, “Da ya ke kin manta da ni, kin ba ni baya. Don haka ki ɗauki hakkin lalatarki da karuwancinki.”

36Sai Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ko ka shara'anta wa Ohola da Oholiba? To, sai ka faɗa musu mugayen ayyukansu. 37Gama sun yi zina da kisankai, sun bauta wa gumakansu, har ma sun miƙa musu 'ya'yansu maza da suka haifa mini, su zama abincinsu. 38Ga kuma abin da suka yi mini, sun ƙazantar da Haikalina a ranar, sun kuma ɓata ranar Asabar ɗina. 39Gama a ranar da suka kashe 'ya'yansu, suka miƙa su hadaya ga gumakansu, sai suka shiga Haikalina suka ƙazantar da shi. Abin da suka yi ke nan cikin Haidalina.

40“Kun aiki manzo wurin mutanen da ke nesa su kuwa suka zo. Saboda su kun yi wanka, kun sa kwalli, kun ci ado. 41Kun zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabansa. A kansa kuka ajiye turarena da maina. 42A wurinta akwai hayaniyar taron mutane marasa kula, sai kuma aka kawo mutane irinsu, mashaya daga jeji. Suka sa mundaye a hannuwan matan, suka kuma sa kambi masu kyau a kawunansu. 43Sai na yi magana a kanta, ita wadda ta ƙare ƙarfinta da yin zina, yanzu za su yi zina da ita da ta zama haka? 44Suka shiga wurinta kamar yadda akan shiga wurin karuwa. Haka kuwa suka shiga wurin Ohola da Oholiba don su yi zina da su. 45Amma adalai za su yanka musu hukunci irin wanda akan yi wa mata mazinata, da mata masu kisankai, gama su mazinata ne masu kisankai.

46“Gama ni Ubangiji Allah na ce, a kawo rundunar soja ta yi yaƙi da su, don su firgita su, su washe su. 47Rundunar za ta jajjefe su da duwatsu, ta sassare su da takuba. Za ta kuma kashe 'ya'yansu mata da maza, ta ƙone gidajensu. 48Ta haka zan kawo ƙarshen lalata a cikin ƙasar domin dukan mata su sami faɗaka, kada su yi lalata kamar yadda kuka yi. 49Za a hukunta ku saboda lalatarku, za ku sha hukunci saboda zunubin bautar gumaka, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.”

24

Misali a kan Tukunyar da ke Tafasa

1A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka rubuta sunan wannan rana. Ranar ke nan da Sarkin Babila ya kewaye Urushalima da yaƙi. 3Ka yi wa 'yan tawayen nan magana da misali, ka faɗa musu cewa, ni Ubangiji na ce, “‘Ka ɗora tukunya, ka ɗora ta a wuta, Ka cika ta da ruwa.

4Ka zuba gunduwoyin nama a ciki, Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa, Ka cika ta da tantakwashi.

5Ka kama mafi kyau daga cikin garken, Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa, Ka tafasa gunduwoyin, Ka kuma tafasa tantakwashin.”

6“Ni Ubangiji Allah na ce, “‘Domin haka kaiton birnin nan mai zubar da jini, Da tukunya wadda ke da tsatsa, Wadda tsatsarta ba ta fita cikinta ba! Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa, Kada ka yi zaɓe.

7Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta, Ta zubar da shi a kan dutse, Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.

8Don a tsokani fushina har in yi sakayya, Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse, Don kada a rufe shi.”

9“Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce, “‘Kaitonka, ya birni, mai zubar da jini! Ni kuma zan tsiba itace da yawa.

10Ka tula gumagumai, ka kunna wuta, Ka tafasa naman sosai, Ka zuba kayan yaji a ciki, Ka bar ƙasusuwan su ƙone.

11Ka ɗora tukunyar da ba kome cikinta a bisa garwashi Domin ta yi zafi, tagullarta ta yi ja wur, Domin dauɗarta ta narke a ciki, Tsatsarta kuma ta ƙone.

12Ta gajiyar da ni a banza, Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.

13Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki. Da ya ke na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba, To, ba za ki ƙara yin tsabta ba, Har lokacin da na fashe fushina a kanki.”

14Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa”

Rasuwar Matar Ezekiyel

15Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 16“Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye. 17Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”

18Sai na yi magana da mutane da safe, da maraice kuwa matata ta rasu. Kashegari da safe, sai na yi kamar yadda aka umarce ni. 19Mutane kuwa suka tambaye ni dalilin da ya sa nake yin haka.

20Sai na ce musu, “Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 21in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, “‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi. 22Za ku kuwa yi kamar yadda na yi, wato ba za ku ja amawali ba, ba kuwa za ku ci abincin masu makoki ba. 23Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi. 24Da haka Ezekiyel zai zama muku alama. Za ku yi kamar yadda ya yi duka. Sa'ad da wannan ya faru, za ku sani nine Ubangiji Allah.”

25“Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da ke faranta zuciyarsu, da 'ya'yansu mata da maza, 26a wannan rana wanda ya tsere zai kawo maka labarin. 27A ranar bakinka zai buɗe, za ka yi magana da wanda ya tsere, ba kuma za ka zama bebe ba. Da haka za ka zama alama gare su, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

25

Annabci a kan Ammonawa

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa, ka yi annabci a kansu. 3Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da ya ke kun ce, “‘Madalla,” a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala, 4domin haka zan bashe ku abin mallaka ga mutanen gabas. Za su kafa alfarwansu a cikinku, su zauna tare da ku. Za su ci amfanin gonakinku, su sha madararku. 5Zan mai da Rabba makiyayar raƙuma, in mai da biranen Ammonawa garken awaki da tumaki. Sa'an nan ku sani ni ne Ubangiji Allah.”

6Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da ya ke kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila, 7domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

Annabci a kan Mowab

8Ubangiji Allah ya ce, “Da ya ke Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai, 9saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab daga garuruwan da ke kan iyaka, waɗanda su ne darajarta, wato Bet-yeshimot, da Ba'al-meyon, da Kiriyatayim. 10Zan bashe ta duk da Ammonawa su zama abin mallakar mutanen gabas, don kada um'ƙara tunawa da su a cikin al'ummai. 11Zan hukunta Mowab, sa'an nan za ta sani ni ne Ubangiji.”

Annabci a kan Edom

12Ubangiji Allah ya ce, “Da ya ke Edom ta ɗaukar wa kanta fansa a kan mutanen Yahuza, ta yi babban laifi da ta ɗaukar wa kanta fansa, 13domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan. 14Mutanen Isra'la za su ɗaukar mini fansa a kan Edom. Za su aukar da fushina da hasalata a kan Edom, sa'an nan Edom za ta san sakayyata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Annabci a kan Filistiyawa

15Ubangiji Allah ya ce, “Tun da ya ke Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar, 16domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Filistiyawa. Zan kashe Keretiyawa, in hallaka sauran mazaunan gāɓar teku. 17Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”

26

Annabci a kan Taya

1A rana ta fari ga watan, a shekara ta goma sha ɗaya, sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni ya ce, 2“Ɗan mutum, da ya ke Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, “‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,” 3domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, “‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al'ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa. 4Za su hallaka garun Taya, su rurrushe hasumiyarta. Zan ƙan'kare ƙasarta, in maishe ta fā. 5Za ta zama wurin shanya taruna a tsakiyar teku. Za ta kuma zama ganima ga sauran al'umma. Ni Ubangiji na faɗa. 6Ya'yanta mata waɗanda ke zaune a filin kasar za a kashe su da takobi, sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

7Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji. 8Zai kashe ya'yanki mata waɗanda ke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi. 9Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura. 10Saboda yawan dawakansa, ƙurar da za su tayar za ta rufe ki. Garunki kuma zai girgiza saboda motsin sojojin doki, da na ƙafafu kamar na keke, da na karusai sa'ad da ya shiga ƙofofinki, kamar yadda akan shiga birnin da garunsa ya rushe. 11Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki, zai kashe mutanenki da takobi. Manyan ginshiƙanki za su rushe. 12Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku. 13Zan sa a daina raira waƙoƙi da kaɗa garayu. 14Zan maishe ki fā, wato wurin shanya taruna. Ba za a sāke gina ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

15Ubangiji Allah ya ce wa Taya, “Sa'ad da kika fāɗi, ƙasashen da ke a gāɓar teku za su girgiza saboda amon fāɗuwarki, da nishin waɗanda ake yi wa rauni, da kashe-kashen da aka yi a cikinki. 16Sa'an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci. Za su razana saboda abin da ya same ki. 17Za su yi makoki saboda ke, su ce, “‘Ke wadda ake zaune cikinki, kin bace daga tekuna, Ya shahararren birni, wanda yake babba a bakin teku, Ke da mazaunan da ke cikinki, kun sa mazaunan gāɓar teku su ji tsoro!

18Yanzu tsibiran za su yi rawar jiki a ranar faɗuwarki. Ji, tsibiran teku za su gigice saboda shuɗewarki.”

19Gama Ubangiji Allah ya ce, “Sa'ad da na maishe ki kufai kamar biranen da ba a zauna cikinsu ba, sa'ad da kuma na dulmuye ki cikin zurfin teku, 20sa'an nan zan tura ki tare da waɗanda ke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda ke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai. 21Zan sa ki yi mummunan ƙarshe, ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a same ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa!”

27

Makoki a kan Taya

1Sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ya kai ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya. 3Ka ce mata, ita wadda ke zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da ke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce, “‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!

4Teku ta kewaye kan iyakarki, Maginanki sun ƙawata ki.

5Sun yi katakanki da itacen fir na Senir, Sun sari itacen al'ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.

6Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan. Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim, Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.

7An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar, Don ya zama alama. An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.

8Mazaunan Sidon da Arwad su ne matuƙa, Masu hikima, waɗanda ke cikinki, su ne jagora.

9Dattawan Gebal da masu hikimarta suna tare da ke, Suna tattoshe mahaɗan katakon jirginki, Dukan matuƙan jiragen ruwa sun zo wurinki don kasuwanci.

10“‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja. 11Mutanen Arward sun kewaye kan garunki. Mutanen Gamad kuma suna tsaron hasumiyarki. Sun rataya garkuwoyinsu a jikin garunki. Sun ƙawata ki ƙwarai.

12“‘Tarshish abokiyar cinikinki ce, saboda yawan dukiyarki ta sayi kayan cinikinki da azurfa, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma. 13Mutanen Yawan, da na Tubal, da na Meshek, abokan kasuwancinki, sun sayi kayan cinikinki da mutane da tasoshin tagulla. 14Mutanen Togarma kuma sun sayi kayan cinikinki da dawakai da dawakan yaƙi, da alfadarai. 15Mutane Dedan abokan cinikinki ne. Kasashe da yawa kuma na gaɓar teku sun zama kasuwarki. Sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya. 16Suriya kuma abokiyar cinikinki ce saboda yawan kayan cinikinki. Sun sayi kayan cinikinki, da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu. 17Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra'ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da 'ya'yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi. 18Dimashƙu kuma ta zama abokiyar cinikinki saboda yawan kayan cinikinki da yawan dukiyarki. Ta sayi kayanki da ruwan inabin Helbon, da farin ulu. 19Mutanen Dan, da Yawan, da ulu suka sayi kayanki, wato gyararren ƙarfe da kayan yaji. 20Dedan ta sayi kayanki da kayan dawakai. 21Mutanen Arabiya da shugabannin Kedar sun sayi kayanki da 'yan raguna, da raguna, da awaki. 22'Yan kasuwar Sheba da Ra'ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya. 23Garuruwan Haran, da Kanne, da Aidan, da fataken Sheba, da Asshur, da Kilmad sun yi ciniki da ke. 24Sun sayar miki da tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da darduma masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tufka da kyau. 25Jiragen ruwan Tarshish suna jigilar kayan cinikinki. Don haka kin bunƙasa, Kin ɗaukaka a tsakiyar tekuna.

26“‘Matuƙanki sun kai ki cikin babbar teku, Iskar gabas ta farfasa ki a tsakiyar teku.

27Dukiyarki, da kayan cinikinki, da hajarki, Da ma'aikatanki da masu ja miki gora, Da masu tattoshe mahaɗan katakanki, Da abokan cinikinki, da dukan sojojinki, Da dukan taron jama'ar da ke tare da ke, Sun dulmuya cikin tsakiyar teku a ranar halakarki.

28Saboda kukan masu ja miki gora, ƙasa ta girgiza.

29“‘Daga cikin jiragen ruwansu dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su zo. Matuƙan jiragen ruwa da masu jagora za su tsaya a gaɓar teku.

30Za su yi kuka mai zafi dominki. Za su yi hurwa, su yi birgima cikin toka.

31Za su aske kansu saboda ke, su sa tufafin makoki. Za su yi kuka mai zafi dominki.

32A cikin makokinsu dominki, suna kuka, suna cewa, Wa ke kama da Taya, Ita wadda ke shiru a tsakiyar teku>

33Sa'ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, Kin wadatar da al'ummai, Kin arzuta sarakunan duniya da yawan dukiyarki da hajarki.

34Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafa, Hajarki da dukan ma'aikatan jirgin ruwanki sun nutse tare da ke.

35Dukan mazaunan ƙasashen gāɓar teku Sun gigice saboda masifar da ta auko miki. Dukan sarakunansu sun tsorata ƙwarai, Fuskokinsu sun yamutse.

36'Yan kasuwa a cikin al'ummai suna yi miki ba'a, Saboda kin zama musu barazana. Ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.”

28

Annabci a kan Sarkin Taya

1Ubangiji ya yi magana da ni ya ce, 2“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, “‘Da ya ke zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da ya ke ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.

3Lalle ka fi Daniyel hikima, Ba asirin da ke ɓoye a gare ka.

4Ta wurin hikimarka da ganewarka ka samo wa kanka dukiya, Ka tattara zinariya da azurfa a baitulmalinka.

5Saboda yawan hikimarka na yin kasuwanci, ka ƙara dukiyarka, Sai dukiyarka ta sa zuciyarka ta cika da alfarma.”

6“Saboda haka Ubangiji Allah ya ce, “‘Da ya ke ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah,

7Don haka zan tura baƙi a kanka, Waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al'umma. Za su zare takubansu a kan kyakkyawar hikimarka, Za su ɓara darajarka.

8Za su jefar da kai cikin rami, Za ka mutu kamar waɗanda suka mutu a tsakiyar teku.

9Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da ya ke kai mutum ne kawai, ba Allah ba>

10Za ka yi mutuwa irin ta kare ta hannun baƙi, Gama ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Makoki a kan Sarkin Taya

11Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce, 12“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce, “‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!

13Kana cikin Aidan, gonar Allah. An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja, Tare da zinariya. Kana da molo da abin busa. A ranar da aka halicce ka Suna nan cikakku.

14Na keɓe ka ka zama mala'ika mai tsaro, Kana bisa tsattsarkan dutsen Allah, Ka yi tafiya a tsakiyar duwatsu na wuta.

15Daga ranar da aka halicce ka ba ka da laifi cikin al'amuranka, Sai ran da aka iske mugunta a cikinka.

16A wurin yawan kasuwancinka, Ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi. Don haka na jefar da kai daga dutsen Allah Kamar ƙazantaccen abu. Na hallaka ka daga tsakiyar duwatsu na wuta, Kai mala'ikan tsaro.

17Zuciyarka ta yi alfarma saboda kyanka, Ka lalatar da hikimarka ta wurin nuna darajar kanka. Na jefar da kai zuwa ƙasa, Na tone asirinka a gaban sarakuna don su kallace ka.

18Saboda yawan muguntarka da rashin gaskiyarka cikin kasuwanci, Ka ƙazantar da tsarkakakkun wurarenka. Don haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, Na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suka kallace ka.

19Dukan waɗanda suka san ka a cikin al'ummai Za su gigice saboda masifar da ta auko maka, Za ka zama barazana ga al'ummai, Ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.”

Annabci a kan Sidon

20Ubangiji ya yi magana da ni kuma, ya ce, 21“Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon, ka yi annabci a kanta. 22Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, “‘Duba, ina gāba da ke, ya Sidon, Zan bayyana ikona a cikinki, Za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na hukunta ta, Na bayyana tsarkina a cikinta.

23Zan aukar mata da annoba da jini a titunanta. Waɗanda za a ji musu rauni da takobi Za su fāɗi matattu a tsakiyarta. Za a tasar mata a kowane waje. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

Isra'ila za ta Sami Albarka

24“‘A kan mutanen Isra'ila kuwa, al'ummai da ke kewaye da su, waɗanda suka raina su, ba za su ƙara zamar musu kamar sarƙaƙƙiya da ƙaya ba. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”

25“Ubangiji Allah ya ce, “‘Sa'ad da na tattara mutanen Isra'ila daga cikin sauran al'umma, inda na watsar da su, na kuma bayyana tsarkina a cikinsu a kan idon al'ummai, sa'an nan za su zauna a ƙarsarsu wadda na ba bawana Yakubu. 26Za su zauna lafiya a cikinta, za su gina gidaje, su yi gonakin inabi. Za su zauna gonakin inabi. Za su zauna lafiya sa'ad da na hukunta maƙwabtansu waɗanda suka wulakanta su. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu.”

29

Annabci a kan Masar

1A kan rana ta goma sha biyu ga watan goma a shekara ta goma, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci Fir'auna Sarkin Masar, ka yi annabci gāba da shi da dukan Masar.

3Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce, “‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar, Babban mugun dabba wanda ke kwance a tsakiyar koguna, Wanda ke cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.

4Zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka, In kuma sa kifayen kogunanka su manne a ƙamborinka, Zan jawo ka daga cikin tsakiyar kogunanka, Da dukan kifayen kogunanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,

5Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji. Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka. Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.

6A sa'an nan mazaunan Masar za su sani ni ne Ubangiji, Domin sun zama wa mutanen Isra'ila kamar sandan iwa.

7Sa'ad da suka riƙe ka, Sai ka karye ka tsattsaga hannuwansu. Sa'ad da suka jingina da kai, Sai ka karye, har ka sa kwankwasonsu ya firgiza.

8Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce zan jawo takobi a kanka, in kashe mutanenka, duk da dabbobi. 9Ƙasar Masar za ta zama kufai, marar amfani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji. “‘Domin ka ce, “Kogin Nilu nawa ne, ni na yi shi,” 10ina gāba da kai da kogunanka. Zan mai da ƙasar Masar kufai sosai, marar amfani, tun daga Migdol zuwa Sewene har zuwa iyakar Habasha. 11Mutum ko dabba ba zai ratsa ta cikinta ba. Za ta zama kufai har shekara arba'in. 12Zan mai da ƙasar Masar kufai fiye da sauran ƙasashe. Biranenta za su zama kufai marar amfani, fiye da sauran birane har shekara arba'in. Zan kuma warwatsar da Masarawa a cikin sauran al'umma.”

13Ubangiji Allah ya ce, “Bayan shekara arba'in zan tattaro Masarawa daga cikin sauran al'umma inda aka warwatsar da su. 14Zan komo da Masarawa, in maido su a ƙasar Fatros, ƙasarsu ta ainihi. Za su zama mulki marar ƙarfi. 15Za su zama rarraunan mulki a cikin mulkoki. Ba za su ƙara ɗagawa sauran al'umma kai ba. Zan sa su zama kaɗan, har da ba za su ƙara mallakar waɗansu al'ummai ba. 16Ba za su ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra'ila ba, gama Isra'ilawa za su tuna da laifin suka yi, suka nemi taimakon Masarawa. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”

17A kan rana ta fari ga watan fari a shekara ta ashirin da bakwai, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 18“Ɗan mutum, Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya sa sojojinsa su matsa wa Taya. Kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta yi kanta, amma duk da haka shi, tare da sojojinsa, bai sami hakkin wahalar da ya sha a Taya ba.” 19Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Zan ba Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ƙasar Masar, zai kwashe dukiyarta, ya lalatar da ita, ya washe ta ganima. Za ta zama abin biyan sojojinsa. 20Na ba shi ƙasar Masar saboda wahalar da ya sha, gama ni suka yi wa aiki. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

21“A ranan nan zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda ya zama babban sarki, zan kuma buɗe bakinka a tsakiyarsu. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

30

Lalacewar Masar

1Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce Ubangiji Allah ya ce maka ka yi kuka, kana cewa, “‘Kaito, kaito saboda wannan rana!”

3Gama ranar ta gabato, Ranar Ubangiji ta yi kusa, Rana ce ta gizagizai, Ranar halakar al'ummai.

4Takobi zai fāɗa a kan Masar, Azaba kuma za ta sami Habasha. Za a kashe mutane a Masar, Za a kwashe dukiyarta, A rushe harsashin gininta.

5“Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”

6Ubangiji ya ce, “Waɗanda ke goyon bayan Masar za su fāɗi. Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.

7Za ta zama kufai fiye da sauran ƙasashe, Biranenta kuma za su zama kufai, marar amfani, fiye da sauran birane.

8Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, Sa'ad da na kunna wuta cikin Masar, Na kuma kakkarya dukan masu taimakonta.

9“A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”

10Ubangiji Allah ya ce, “Zan sa dukiyar Masar ta ƙare Ta hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila,

11Shi da mutanensa, Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma, Za a kawo su don su hallakar da ƙasar. Za su zare takubansu a kan Masar, Su cika ƙasar da gawawwaki.

12Zan busar da Kogin Nilu, Zan kuma sayar da ƙasar ga mugaye. Zan sa ƙasar ta lalace Da dukan abin da ke cikinta, Ta hannun baƙi, Ni Ubangiji, na faɗa.”

13Ubangiji Allah ya ce, “Zan hallakar da gumaka Da siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba, Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.

14Zan sa Fatros ta zama kufai, Zan kunna wa Zowan wuta, Zan kuma shara'anta No.

15Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, Wato kagarar Masar, Zan datse jama'ar No.

16Zan kunna wa Masar wuta. Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani, No kuwa za a tayar mata da hankali, Za a rurrushe garukanta. Za a tasar wa Memfis dukan yini.

17Samarin Awen da na Fi-beset Za a kashe su da takobi, Matan kuma za su tafi bauta.

18A Tafanes rana za ta yi duhu, Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar, Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare, Za a rufe ta da gizagizai. 'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.

19Ta haka zan hukunta Masar, Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

20A kan rana ta bakwai ga watan fari, a shekara ta goma sha ɗaya, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 21“Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, Sarkin Masar, ga shi, ba za a ɗora hannun ba, don kada ya warke ya zama da ƙarfi yadda zai iya riƙon takobi.” 22Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir'auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa. 23Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in kuma warwatsa su a ƙasashen duniya. 24Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali. 25Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su shanye. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar. 26Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in warwatsa su a ƙasashen duniya. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

31

Ƙaddarar da za ta Sami Fir'auna da Jama'arsa

1A kan rana ta fari ga watan uku a shekara ta goma sha ɗaya, Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka ce wa Fir'auna, Sarkin Masar, da jama'arsa. “‘Da wa za a kamanta girmanka>

3Kana kama da Assuriya mai kama da itacen al'ul a Lebanon, Mai rassa masu kyau da inuwar kurmi, Mai tsayi ainun, kansa ya kai cikin gizagizai.

4Ruwa ya sa ya yi girma, Danshi ya sa ya yi tsayi. Koguna sun gudu kewaye da wurin da aka shuka shi. Yana aikar da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.

5Sai ya yi tsayi fiye da dukan itatuwan da ke a kurmi, Rassansa suka yi kauri, suka kuma yi tsayi, Saboda isasshen ruwa a lokacin tohonsa.

6Dukan tsuntsayen sararin sama sun yi sheƙunansu a rassansa, Namomin jeji kuma suka haifi 'ya'yansu ƙarƙashin rassansa. Dukan al'ummai suka zauna ƙarƙashin inuwarsa.

7Girmansa yana da kyau, haka kuma dogayen rassansa, Gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin ruwa.

8Ko itatuwan al'ul da ke cikin gonar Allah, ba su kai kyansa ba. Itatuwan kasharina kuma ba du kai rassansa ba. Itatuwan durumi kuma ba su kai rassansa ba. Ba wani itace a gonar Allah wanda ya kai kyansa.

9Na sa shi ya yi kyau, ga kuma rassansa da yawa. Dukan itatuwan Aidan, waɗanda ke cikin gonar Allah sun yi ta jin ƙyashinsa.”

10Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa, 11zan bashe shi a hannun mai ƙarfi, a cikin al'ummai. Zai sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na fitar da shi. 12Baƙi mafi bantsoro daga cikin al'ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da ke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi. 13Dukan tsuntsayen sararin sama za su zauna a gorarsa. Namomin jeji kuma za su yi ta yawo a cikin rassansa. 14An yi wannan domin kada itatuwan da ke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da ke shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”

15Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da ya gangara zuwa lahira, na sa zurfi ya rufe shi, ya yi makoki dominsa. Na tsai da kogunansa, yawan ruwansa ya ƙafe. Na sa Lebanon ta yi duhu saboda shi. Dukan itatuwan jeji kuwa sun yi yaushi saboda shi. 16Al'ummai suka yi rawar jiki saboda amon faɗuwarsa, sa'ad da na jefar da shi cikin lahira tare da waɗanda suke gangarawa zuwa cikin kabari. Dukan itatuwan Aidan da itatuwa mafi kyau na Lebanon waɗanda suka ƙoshi da ruwa, sun ta'azantu a lahira. 17Su kuma suka gangara tare da shi zuwa lahira, suka tarar da waɗanda aka kashe da takobi, wato waɗanda daga cikin al'ummai suka yi zama a inuwarsa.

18“A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir'auna ke nan, da dukan jama'arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

32

Makoki saboda Fir'auna

1A kan rana ta fari, ga watan goma sha biyu, a shekara ta goma sha biyu, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir'auna, Sarkin Masar, ka ce, “‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al'ummai, Amma kai kada ne a cikin ruwa. Ka ɓullo cikin kogunanka, Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka, Ka ƙazantar da kogunansu.”

3Ubangiji Allah ya ce, “‘Zan jefa taruna a kanka, a babban taron mutane, Zan jawo ka cikin taruna.

4Zan jefar da kai a tudu, A fili zan jefa ka. Zan sa tsuntsayen sararin sama su ɗira a kanka, Zan ƙosar da namomin jeji na dukan duniya da namanka.

5Zan watsa namanka a kan duwatsu, In cika kwaruruka da gawarka.

6Zan watsar da jininka a ƙasa da tuddai, Magudanan ruwa za su cika da jininka.

7Sa'ad da na shafe ka, zan rufe sammai, In sa taurarinsu su duhunta, Zan sa girgije ya rufe rana, Wata kuma ba zai haskaka ba.

8Dukan haskokin sama zan sa su zama duhu a gare ka, In sa ƙasarka ta duhunta, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

9“Zukatan al'ummai da yawa za su ɓaci, sa'ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba. 10Al'ummai da yawa za su gigice saboda abin da zai same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa'ad da na kaɗa takobi a gabansu. A ranar faɗuwarka za su yi rawar jiki a kowane lokaci, kowa saboda ransa.”

11Ubangiji Allah ya ce, “Takobin Sarkin Babila zai auko maka. 12Zan sa ƙarfafan mutane masu bantsoro daga cikin al'ummai su kashe jama'arka da takuba. Za su wofinta girmankan Masar, Su kuma hallaka jama'arta.

13Zan hallaka dukan dabbobinta da ke bakin ruwa, Ba ƙafar mutum ko ta dabba da za ta ƙara gurɓata ruwa.

14Zan sa ruwansu ya yi garau, In sa kogunansu su malala kamar mai, Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15Sa'ad da na mai da ƙasar Masar kufai, In raba ƙasar da abin da take cike da shi, Sa'ad da na bugi dukan waɗanda ke cikinta, Daganan za su sani ni ne Ubangiji.

16Wannan ita ce waƙar makokin. 'Yan matan al'ummai za su raira wa Masar da jama'arta duka, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Lahira

17A rana ta goma sha biyar ga wata na fari, a shekara ta goma sha biyu, Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 18“Ɗan mutum, ka yi kuka saboda jama'ar Masar. Ka tura su tare da sauran al'umma zuwa lahira wurin waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari. 19Ka ce, “‘Su wa kika fi kyau? Ki gangara, ki kwanta tare da marasa imani.”

20“An zare takobi don a kashe jama'ar Masar. Za su fāɗi a tsakiyar waɗanda aka kashe da takobi. 21Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, “‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!”

22“Assuriya tana can da dukan taron jama'arta. Kaburburansu suna kewaye da ita. An kashe dukansu da takobi. 23An binne su a can ƙurewar lahira. Taron jama'arta suna kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Su ne suka haddasa tsoro a cikin ƙasar.

24“Elam tana can da dukan jama'arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari. 25An shirya mata gado tare da matattu. Kaburburan dukan sojojinta suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, amma a dā sun yaɗa tsoro a duniya. Yanzu kuwa suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari. An tara su tare da waɗanda aka kashe.

26“Meshek da Tubal suna can da dukan sojojinsu. Kaburburan sojojinsu suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, gama sun yaɗa tsoro a duniya. 27Ba su kwanta kusa da manyan jarumawan da aka kashe ba, waɗanda suka tafi lahira da makamansu, aka yi musu matasan kai da takubansu, aka rufe ƙasusuwansu da garkuwoyinsu, gama manyan jarumawan nan sun baza tsoro a duniya. 28Amma za a karya ku, ku kwanta tare da marasa imani, tare da waɗanda aka kashe da takobi.

29“Edom kuma tana can tare da sarakunanta da dukan shugabanninta masu iko, Suna kwance tare da waɗanda aka kashe da takobi, marasa imani, masu gangarawa zuwa cikin kabari.

30“Dukan shugabannin arewa suna can, da dukan Sidoniyawa. Da kunya, suna gangarawa tare da waɗanda aka kashe, ko da ya ke a dā sun haddasa tsoro saboda ikonsu. Yanzu suna kwance tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.

31“Sa'ad da Fir'auna zai gan su, zai ta'azantu a kan rundunarsa da aka kashe da takobi. Lalle Fir'auna da dukan rundunarsa za su ta'azantu. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

32“Ko da ya ke na sa Fir'auna ya haddasa tsoro a duniya, duk da haka zan sa a kashe shi tare da rundunarsa. Za su kwanta tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

33

Wajibin Mai Tsaro

(Eze 3.16-21)

1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, “‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu, 3idan ya ga an taso wa ƙasar da takobi, sai ya busa ƙaho don ya faɗakar da jama'ar. 4Idan wani ya ji amon ƙahon, amma bai kula ba, har takobin ya zo ya kashe shi, hakkin jininsa yana bisa kansa. 5Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa. 6Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.”

7“Yanzu fa, kai ɗan mutum, na sa ka zama ɗan tsaro a al'ummar Isra'ila. Duk lokacin da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su. 8Idan na hurta, cewa hakika mugu zai mutu, amma ba ka faɗakar da shi don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa ba, wannan mugun zai mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka. 9Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.

Ayyukan Allah daidai Ne

(Eze 18.21-32)

10“Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, “‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ” 11Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, “‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?”

12“Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi. 13Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa'an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi. 14Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci, 15idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba. 16Ba za a tuna da laifofin da ya aikata a dā ba, gama ya aikata adalci da gaskiya, zai rayu.

17“Amma mutanenka sun ce, “‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce,” alhali kuwa tasu ce ba daidai ba. 18Sa'ad da adali ya daina aikata adalci, ya shiga aikata laifi, zai mutu saboda laifinsa. 19Sa'ad da kuma mugu ya daina aikata mugunta, ya shiga aikata adalci da gaskiya, zai rayu saboda adalcinsa. 20Amma duk da haka kun ce, “‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.” Ya mutanen Isra'ila, zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”

Labarin Faɗuwar Urushalima

21A rana ta biyar ga watan goma, a shekara ta goma sha biyu ta zaman bautar talala da aka kai mu, sai wani ɗan gudun hijira daga Urushalima ya zo wurina, ya ce, “Birnin ya fāɗi.” 22A maraicen da ya wuce kafin ɗan gudun hijirar ya iso, Ubangiji ya ƙarfafa ni, ya kuma buɗe bakina a lokacin da mutum ya zo wurina da safe. Bakina kuwa ya buɗe, ban zama bebe ba kuma.

23Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 24“Ɗan mutum, mazaunan wuraren nan da aka lalatar a ƙasar Isra'ila, suna cewa, “‘Ibrahim shi kaɗai ne, duk da haka an ba shi ƙasar duka, balle fa mu da muke da yawa, lalle ƙasar tamu ce.”

25“Domin haka, sai ka faɗa musu, “‘Ubangiji Allah ya ce, “Kuna cin nama da jininsa, kuna bautar gumaka, kuna kuma yin kisankai, da haka za ku mallaki ƙasar? 26Kun sa dogararku ga takobi kuna aikata abubuwan bankyama, kowannenku kuma yana zina da matar maƙwabcinsa, da haka za ku iya mallakar ƙasar?” ”

27“Ka faɗa musu, “‘Ubangiji ya ce, “Hakika, waɗanda ke a wuraren da aka lalatar, za a kashe su da takobi, wanda kuma ke a saura zan sa namomin jeji su cinye shi. Waɗanda kuma ke cikin kagara, da kogwannin duwatsu, annoba za ta kashe su. 28Zan mai da ƙasar kufai marar amfani, fariya za ta ƙare. Tuddan Isra'ila za su zama kufai, ba wanda zai ratsa ta cikinsu. 29Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na mai da ƙasar kufai marar amfani saboda dukan ayyukansu na banƙyama.” ”

Sakamakon Wa'azin Annabin

30Ubangiji ya ce, “Ɗan mutum, mutanenka sun taru a kan garu da cikin ƙofofin gidaje, suna magana da juna a kanka cewa, “‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.” 31Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba. 32A gare su ka zama gwanin kiɗa da waƙa, gama suna so su ji abin da kake faɗa, amma ba za su aikata ba. 33Sa'ad da abin da kake faɗa ya cika (ba shakka kuwa zai cika), sa'an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”

34

Annabci a kan Makiyayan Isra'ila

1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra'ila, ka ce musu, “‘Ku masu kiwon mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra'ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne ke kiwon tumaki ba? 3Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba. 4Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji. 5Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji. 6Tumakina sun watse, suna yawo a kan dukan duwatsu da tuddai, sun warwatsu a duniya duka, ba wanda zai nemo su.”

7“Domin haka, ku ji maganata, ku makiyaya. 8Ni Ubangiji Allah na ce, “‘Hakika da ya ke tumakina sun zama ganimar dukan namomin jeji, saboda rashin makiyayin kirki, makiyayana kuma ba su nemo su ba, amma suka yi kiwon kansu, ba su yi kiwon tumakin ba, 9to, ku makiyaya, sai ku saurara ga maganata. 10Ga shi, ina gāba da ku, zan nemi tumakina a hannunku. Zan hana ku yin kiwon tumakin, ku kuma ba za ku ƙara yin kiwon kanku ba. Zan ƙwace tumakina daga hannunku, domin kada su ƙara zama abincinku.”

Makiyayi Mai Kyau

11“Ni Ubangiji Allah na ce, ni kaina zan nemi tumakina. 12Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu. 13Zan fito da su daga cikin sauran al'umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra'ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane ke zaune a ƙasar. 14Zan yi kiwonsu a makiyaya mai kyau. Ƙwanƙolin tuddan Isra'ila zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a makiyaya mai kyau, za su yi kiwo a makiyaya mai dausayi a kan tuddan Isra'ila. 15Ni kaina zan yi kiwon tumakin, in ba su hutawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.

17“Ni Ubangiji Allah na ce, “‘Ku kuma garkena, zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin rago da bunsuru. 18A ganinku abu mai kyau ne, bayan da kun yi kiwo a makiyaya mai kyau, sa'an nan ku tattake sauran makiyayar da ƙafafunku? Sa'ad da kuka sha ruwa mai kyau, sai kuma ku gurɓata sauran da ƙafafunku? 19Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku!”

20“Saboda haka, ni, Ubangiji Allah, na ce, “‘Zan shara'anta tsakanin turkakkun tumaki da ramammu. 21Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku, har kun watsar da su. 22Zan ceci garken tumakina, ba za su ƙara zama ganima ba. Zan kuma shara'anta tsakanin tunkiya da tunkiya. 23Zan sa musu makiyayi guda, wato bawana Dawuda. Zai yi kiwonsu, ya zama makiyayinsu. 24Ni kuma, Ubangiji, zan zama Allahnsu. Bawana Dawuda kuwa zai zama sarkinsu.” Ni Ubangiji na faɗa.

25“Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi. 26Zan sa su, da wuraren da ke kewaye da tuduna dalilin samun albarka. Zan aiko da ruwan sama a lokacinsa, zai kuma zama ruwan albarka. 27Itatuwan saura za su yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani. Za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su. 28Ba za su ƙara zama ganimar al'ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su. 29Zan ba su gonaki masu dausayi don kada yunwa ta ƙara far musu a ƙasar, kada kuma su ƙara shan zargi wurin sauran al'umma. 30Za su sani ni Ubangiji Allahnsu, ina tare da su, mutanen Isra'ila kuwa su ne mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

31“Ku tumakin makiyayata, ku mutane ne, ni kuwa Allahnku ne, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

35

Annabci a kan Dutsen Seyir

1Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa. 3Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce, Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir. Zan miƙa hannuna gāba da shi, Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.

4Zan lalatar da biranensa, In maishe su kufai marar amfani, Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.

5“Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra'ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika, 6don haka, ni Ubangiji na ce, hakika zan sa a zub da jininsa. Mai zub da jini zai fafare shi, da ya ke shi ma ya zub da jini, domin haka mai zub da jini zai fafare shi. 7Zan mai da Dutsen Seyir kufai marar amfani. Zan kashe duk mai shiga ko mai fita a cikinsa. 8Zan cika duwatsunsa da gawawwaki. Waɗanda za a kashe da takobi za su faɗi a kan tuddansa, da cikin kwarurukansa, da cikin dukan kwazazzabansa. 9Zan maishe shi kufai marar amfani har abada. Ba wanda zai zauna a cikin biranensa. Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.

10“Da ya ke ya ce al'umman nan biyu, da ƙasashen nan biyu za su zama nasa, ya mallake su, ko da ya ke Ubangiji yana cikinsu, 11domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa'ad da na hukunta shi. 12Zai sani Ubangiji ne wanda ya ji dukan zarge zargen da ya yi wa duwatsun Isra'ila, da ya ce, “‘An maishe su kufai marar amfani, an ba mu su mu cinye!” 13Na ji tsiwa da dukan surutan da ya yi mini.

14“Ni Ubangiji Allah zan maishe shi kufai marar amfani, domin dukan duniya ta yi farin ciki. 15Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama'ar Isra'ila, da ya zama kufai marar amfani, hakanan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa'an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”

36

Albarkar Ubangiji a kan Ƙasar Isra'ila a Gaba

1“Kai ɗan mutum, ka yi annabci a kan duwatsun Isra'ila, ka ce, “‘Ya duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji.” 2Ubangiji Allah ya ce, da ya ke maƙiya suna cewa, “‘Madalla, tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu,” 3sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, “‘Da ya ke sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane. 4Domin haka, ku duwatsun Isra'ila, sai ku ji maganar Ubangiji Allah. Ni Ubangiji Allah, na ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, da kufai, da yasaassun birane waɗanda suka zama ganima da abin ba'a ga al'umman da ke kewaye, 5ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al'umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.”

6“Domin haka ka yi wa ƙasar Isra'ila annabci, ka ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, ni Ubangiji Allah na ce, “‘Ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al'ummai.”

7“Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al'umman da ke kewaye da ku su ma za su sha zargi. 8Amma ku, ya duwatsun Isra'ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanen Isra'ila, gama za su komo gida ba da jimawa ba. 9Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka! 10Zan sa dukan mutanen Isra'ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare. 11Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daganan za ku sani, ni ne Ubangiji. 12Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.

13“Ni Ubangiji Allah na ce, da ya ke mutane sukan ce muku, 'Kuna cinye mutane, kuna kuma kashe 'ya'yan al'ummarku, 14saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe 'ya'yan al'ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa. 15Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al'umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama'a ba, ba kuma zan ƙara sa al'ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

16Ubangiji Kuma ya yi magana da ni, ya ce, 17“Ɗan mutum, sa'ad da mutanen Isra'ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta. 18Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu. 19Na warwatsa su cikin al'ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu. 20Amma sa'ad da suka tafi cikin al'ummai, sai suka ɓata sunana mai tsarki a duk inda suka tafi. Sai mutane suka yi magana a kansu cewa, “‘Waɗannan jama'ar Ubangiji ne, amma dole ne su fita daga cikin ƙasarsa.” 21Amma na damu saboda sunana mai tsarki wanda mutanen Isra'ila suka sa aka ɓata shi a wurin al'ummai inda suka tafi.

22“Domin haka sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, “‘Ba saboda ku ba ne, ya mutanen Isra'ila, zan yi wani abu, amma saboda sunana mai tsarki wanda kuka ɓata a wurin al'ummai inda kuka tafi. 23Zan ɗauki fansa saboda sunana mai tsarki, mai girma, wanda aka ɓata a wurin al'ummai, ku kuma kuka ɓata shi a cikinsu. Al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tabbatar da tsarkina a wurinku a kan idonsu. 24Zan kwaso ku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga dukan ƙasashe, in kawo ku cikin ƙasarku. 25Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku. 26Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi. 27Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka'idodina. 28Za ku zauna cikin ƙasar da na ba kakanninku. Za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku. 29Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba. 30Zan sa 'ya'yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al'ummai. 31Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama. 32Ni Ubangiji Allah na ce, sai ku sani, ba saboda ku ba ne zan aikata wannan. Ku kunyata, ku gigita saboda hanyoyinku, ya mutanen Isra'ila!”

33Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da zan tsarkake ku daga dukan muguntarku, zan sa ku zauna cikin biranenku, ku gina rusassun wurare. 34Ƙasar da take kufai a dā za ku kafce ta maimakon yadda take kufai a kan idon dukan masu wucewa. 35Za su ce, “‘Wannan ƙasa wadda take kufai a dā ta zama kamar gonar Aidan, ga kuma rusassun wuraren da suka zama kufai, da rusassun birane, yanzu ana zaune a cikinsu, an kuma gina musu garu.” 36Sa'an nan al'umman da suka ragu kewaye da ku za su sani, ni Ubangiji na sāke gina rusassun wuraren da suka zama kufai. Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”

37Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki. 38Kamar garken tumaki na hadaya, kamar garken tumaki a Urushalima a lokacin ƙayyadaddun idodi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

37

Kwarin Busassun Ƙasusuwa

1Ikon Ubangiji kuwa ya sauko a kaina, Ruhunsa kuma ya fito da ni ya ajiye ni a tsakiyar kwari wanda ke cike da ƙasusuwa. 2Sai ya zagaya da ni cikinsu, ga su kuwa, suna da yawa a cikin kwarin, busassu ragau. 3Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa kuwa za su rayu?” Ni kuwa na amsa na ce, “Ya Ubangiji Allah, sani na gare ka.”

4Sai ya ce mini, “Ka yi annabci a kan ƙasusuwan nan ka faɗa musu su saurari maganata. 5Gama ni Ubangiji Allah zan hura musu numfashi, za su kuwa rayu. 6Zan sa musu jijiyoyi da tsoka, in rufe da fata, in kuma hura musu numfashi, sa'an nan za su rayu, su sani ni ne Ubangiji.”

7Sai na yi annabci kamar yadda ya umarce ni. Da na yi annabcin sai aka ji motsi da girgiza. Sai ƙasusuwan suka harhaɗu da juna, ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu. 8Da na duba, sai ga jijiyoyi a kansu, nama kuma ya baibaye su, sa'an nan fata ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.

9Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”

10Na kuwa yi annabci kamar yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga cikinsu, suka rayu, suka tashi, suka tsaya da ƙafafunsu. Sun zama babbar runduna ƙwarai.

11Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, “‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.”

12“Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra'ila. 13Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu. 14Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”

Mutanen Yahuza da Isra'ila za su Zama Mulki Guda

15Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce, 16“Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, “‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.” Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, “‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.” 17Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka. 18Sa'ad da kuma jama'arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan, 19sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda ke a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.

20“Sa'ad da sandunan da ka yi rubutu a kansu suna hannunka a gabansu, 21sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama'ar Isra'ila daga wurin al'ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko'ina, in maido su ƙasarsu. 22Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba. 23Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu. 24Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina. 25Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da 'ya'yansu da jikokin 'ya'yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada. 26Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada. 27Wurin Zamana zai kasance a tsakiyarsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena. 28Sa'an nan al'ummai za su sani, ni ne na tsarkake Isra'ila sa'ad da na kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.”

38

Annabci a kan Gog

1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci Gog na ƙasar Magog, babban shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal, ka yi annabci a kansa, 3ka ce Ubangiji Allah ya ce, “‘Ga shi, ina gaba da kai, ya Gog, babban shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal. 4Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi cikin muƙamuƙanka, in fitar da kai, da dukan sojojinka, da dawakai da mahayansu. Su babbar runduna ce saye da makamai, wato garkuwoyi, da takuba a zāre, 5mutanen Farisa, da Habasha, duk da Fut. Dukansu suna saye da garkuwa da kwalkwali, 6da Gomer tare da dukan sojojinsa, da Bet-togarma daga ƙurewar arewa, da dukan sojojinsa, su jama'a mai yawa, suna tare da kai. 7Ka shirya, ka kuma zama da shiri, kai da dukan rundunar da suka tattaru kewaye da kai, ka zama ɗan tsaronsu. 8Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya. 9Za ka ci gaba, kana zuwa kamar hadiri, za ka rufe ƙasar kamar gizagizai, kai da rundunarka, da jama'a masu yawa tare da kai.”

10Ubangiji Allah ya ce, “A wannan rana tunani zai shiga cikin zuciyarka, za ka ƙirƙiro muguwar dabara, 11ka ce, “‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da ke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare, 12don in washe su ganima, in fāda wa wuraren da aka ɓarnatar waɗanda ake zaune a cikinsu yanzu, in kuma fāɗa wa jama'ar da aka tattaro daga cikin al'ummai waɗanda suka sami shanu da dukiya, suna zaune a cibiyar duniya.” 13Sheba da Dedan, da 'yan kasuwar Tarshish, da dukan garuruwa za su ce maka, “‘Ka zo kwasar ganima ne? Ko ka zo ka tattaro rundunarka don ka yi waso, ka kwashe azurfa da zinariya, da bisashe, da dukiya, ka kwashe babbar ganima?”

14“Saboda haka ɗan mutum, yi annabci, ka faɗa wa Gog, cewa ni Ubangiji Allah na ce, “‘A wannan rana sa'ad da jama'ata Isra'ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba? 15Za ka taso daga wurin da kake, can ƙurewar arewa, da jama'a mai yawa tare da kai, babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi, dukansu a kan dawakai. 16Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.”

17Ubangiji Allah ya ce, “Kai ne wanda na yi magana a kanka a zamanin dā ta wurin bayina annabawan Isra'ila, cewa a shekaru masu zuwa zan kawo ka, ka yaƙe su. 18Amma a wannan rana sa'ad da Gog zai kawo wa ƙasar Isra'ila yaƙi, ni Ubangiji Allah zan hasala. 19Gama a kishina da zafin hasalata na hurta, cewa a wannan rana za a yi babbar girgiza a ƙasar Isra'ila. 20Kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da bisashe, da dukan masu rarrafe, da dukan mutanen da ke duniya, za su yi makyarkyata a gabana. Za a jefar da duwatsu ƙasa, tsaunuka za su fādi, kowane bango zai rushe. 21Zan razana Gog da kowace irin razana, ni Ubangiji Allah na faɗa. Mutanensa za su sassare junansu da takubansu. 22Zan hukunta shi da annoba da kuma zub da jini. Zan yi masa ruwa da ƙanƙara, da wuta, da kibritu za a makaka a kansa da rundunarsa, da dukan jama'ar da ke tare da shi. 23Da haka kuwa zan bayyana girmana da tsarkina in kuma sanar da kaina ga al'ummai. Ta haka za su sani ni ne Ubangiji.”

39

Cin Nasara a kan Gog

1“Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa Gog shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal cewa, “‘Ni Ubangiji Allah ina gāba da kai. 2Zan juya ka in sa ka gaba in tashi daga ƙurewar arewa, in kawo ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra'ila. 3Sa'an nan zan karya bakan da ke a hannun hagunka, in sa kiban da ke a hannun damanka su fāɗi. 4Za ka fāɗi matacce a kan duwatsun Isra'ila, kai da dukan rundunanka, da jama'ar da ke tare da kai. Zan ba da gawawwakinka ga tsuntsaye da dabbobi masu cin nama. 5Za ka mutu a filin saura, gama haka ni Ubangiji Allah na faɗa.” 6Zan aika da wuta a kan Magog, da a kan waɗanda suke zaman lafiya a ƙasashen gāɓar teku, za su kuwa sani ni ne Ubangiji. 7Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama'ata, wato Isra'ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra'ila.

8“Ga shi, ranar da na ambata tana zuwa, hakika kuwa tana zuwa, ni Ubangiji Allah na faɗa. 9Sa'an nan su mazaunan biranen Isra'ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai. 10Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.

11“A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra'ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da ke tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog. 12Jama'ar Isra'ila za su yi wata bakwai suna binne su don su tsabtace ƙasar. 13Dukan jama'ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa. 14A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko'ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta. 15Sa'ad da waɗannan suke bibiyawa a cikin ƙasar, duk wanda ya ga ƙashin mutum, sai ya kafa wata alama kusa da ƙashin don masu binnewa su gani, su ɗauka, su binne a Kwarin Rundunar Gog. 16Akwai gari a wurin, za a sa masa suna Hamona, wato runduna. Ta haka za su tsabtace ƙasar.

17“Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko'ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra'ila. Za su ci nama su kuma sha jini. 18Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da 'yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan. 19Za su ci kitse, har su gundura, su sha jini kuma, har su bugu a idin da nake shirya musu. 20Za a ƙosar da su da naman dawakai, da na mahayansu da na mutane masu iko, da na dukan mayaƙa, ni Ubangiji na faɗa.”

Komowar Mutanen Isra'ila

21“Zan nuna ɗaukakata a cikin al'ummai, dukan al'ummai kuwa za su ga hukuncin da na yi da ikon da na nuna kansu. 22Tun daga wannan rana har zuwa gaba, jama'ar Isra'ila za su sani, ni ne Ubangiji Allahnsu. 23Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi. 24Na yi gwargwadon lalatarsu da laifofinsu, na kawar da fuskata daga gare su.

25“Saboda haka, ni Ubangiji Allah, na ce yanzu zan komo da zuriyar Yakubu daga bauta in nuna mata jinƙai. Zan yi kishi domin sunana mai tsarki. 26Sa'ad da suka komo suka zauna lafiya a ƙasarsu, za su manta da abin kunyar da suka yi da dukan ha'incin da suka yi mini. Ba wanda zai ƙara firgita su, ba kuwa mai tsorata su. 27Zan nuna wa sauran al'umma ni mai tsarki ne ta wurin komo da mutanen Isra'ila daga cikin al'ummai, da ƙasashen al'ummai magabtansu. 28Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu, domin na kore su daga ƙasarsu zuwa bautar talala cikin al'ummai, sa'an nan na sāke tattaro su zuwa cikin ƙasarsu. Daga cikinsu ba zan bar ko ɗaya a cikin al'ummai ba. 29Ba kuma zan ƙara kawar da fuskata daga gare su ba, sa'ad da na saukar da Ruhuna a kan jama'ar Isra'ila, ni Ubangiji na faɗa.”

40

Wahayin Haikalin da Ezekiyel ya Gani

1A ranar goma ga wata na farko a shekara ta ashirin da biyar ta zamanmu a bautar talala, a shekara ta goma sha huɗu da cin birnin, ikon Ubangiji ya sauko a kaina. 2A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni. 3Sa'ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.

4Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”

5Abin da na gani Haikali ne. Akwai katanga kewaye da filin Haikalin. Tsawon karan awon kuma da ke a hannun mutumin kamu shida ne. Sai ya auna faɗin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida. 6Ya tafi kuma wajen ƙofar gabas ya hau matakanta, ya auna dokin ƙofar, faɗinta kamu shida ne. 7Tsawon ɗakin 'yan tsaro kamu shida ne, faɗinsa kuma kamu shida. Kamu biyar ne ke tsakanin ɗaki da ɗaki. Dokin ƙofa kuma da ke kusa da shirayin bakin ƙofar Haikali kamu shida ne. 8Ya kuma auna shirayin bakin ƙofar da ke fuskantar Haikali, kamu shida. 9Sa'an nan ya auna shirayin bakin ƙofar kamu takwas ne. Sai kuma ya auna ginshiƙan shirayin kamu biyu ne. Shirayin ƙofar yana fuskantar ciki. 10Akwai ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe na ƙofar gabas, girmansu iri ɗaya ne. Ginshiƙansu kuma girmansu ɗaya ne.

11Ya kuma auna fāɗin bakin ƙofar, kamu goma ne, tsayin ƙofar kuwa kamu goma sha uku ne. 12Akwai, 'yar katanga a gaban ɗakunan 'yan tsaron, faɗinta kamu ɗaya ne a kowane gefe. Girman ɗakunan 'yan tsaron kuwa kamu shida ne a kowane gefe. 13Daga bayan rufin ɗaya ɗakin 'yan tsaro zuwa bayan ɗayan rufin ya auna filin ya sami kamu ashirin da biyar. 14Ya yi ginshiƙai kamu sittin. Akwai ɗakuna kewaye da shirayin da ke bakin ƙofa. 15Daga gaban ƙofar shiga, zuwa kurewar shirayi na can ciki kamu hamsin ne. 16Akwai tagogi masu murfi da ke fuskantar ɗakunan 'yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda ke wajen ƙofa a kewaye, hakanan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.

17Sai ya kawo ni a fili na waje, ga ɗakuna da daɓe kewaye da filin. Akwai ɗakuna talatin a gaban daɓen. 18Daɓen ya bi ta daidai gefen ƙofofin. Wannan shi ne daɓen da ke ƙasa ƙasa.

19Sai ya auna nisan da ke tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da ke ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.

20Ya kuma auna tsayin ƙofar arewa da faɗinta wadda ke fuskantar filin waje. 21Tana da ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe. Girman ginshiƙanta da shirayinta, daidai suke da ƙofa ta fari. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar. 22Girman tagoginta, da na shirayin, da na siffar itatuwan dabinon da aka zana iri ɗaya ne da na ƙofar da ta fuskanci gabas. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki. 23Fili na ciki yana da ƙofa daura da ƙofar arewa da ta gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

24Ya kuma kai ni wajen kudu, sai kuma ga wata ƙofa. Ya auna ginshiƙanta da shirayinta. Girmansu ɗaya ne, kamar na sauran. 25Akwai tagogi kewaye da ƙofar, da shirayinta kamar na sauran. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar. 26Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki. An zana siffar itatuwan dabino a ginshiƙanta, ɗaya a kowane gefe. 27Akwai wata ƙofa a kudancin fili na can ciki. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

28Ya kuma kai ni fili na can ciki, wajen ƙofar kudu, sai ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran. 29Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu ɗaya yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kamu ashirin da biyar ni. 30Akwai shirayi kewaye, tsawonsa kamu ashirin da biyar ne, faɗinsa kuma kamu biyar ne. 31Shirayinta yana fuskantar filin da ke waje. An zana siffar itatuwan dabino a ginshikanta. Tana kuma da matakai takwas.

32Sai kuma ya kai ni a fili na can ciki wajen gabas. Ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran. 33Hakanan kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu daidai yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar. 34Shirayinta yana fuskantar filin da ke waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Tana da matakai takwas.

35Sa'an nan kuma ya kai ni ƙofar arewa, ya auna ta. Girmanta daidai yake da na sauran. 36Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar. 37Ginshiƙai suna fuskantar filin da ke waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Ita ma matakanta takwas ne.

38Akwai ɗaki, wanda ƙofarsa ke duban ginshiƙan gyaffan ƙofofin, a wurin ake wanke hadayar ƙonawa. 39A shirayin ƙofar akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yanka hadayar ƙonawa, da hadaya don zunubi da laifi. 40Akwai tebur biyu a sashin waje na shirayin ƙofar arewa, akwai kuma waɗansu tebur biyu a ɗayan sashin shirayin ƙofar. 41A gab da ƙofar akwai tebur huɗu, a waje ɗaya kuma akwai huɗu. Duka guda takwas ke nan, inda za a riƙa yanka dabbobin da za a yi hadaya da su. 42Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka. 43Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye da cikin ɗakin, tsawonsu taƙi-taƙi. Za a riƙa ajiye naman hadaya a kan teburorin.

44Ya kai ni fili na can ciki, sai ga ɗakuna biyu a filin. Ɗaya yana wajen ƙofar arewa, yana fuskantar kudu. Ɗayan kuma yana wajen ƙofar kudu yana fuskantar arewa. 45Sai ya ce mini, “Wannan ɗaki wanda ke fuskantar kudu na firistoci ne waɗanda ke lura da Haikalin. 46Ɗakin da ke fuskantar arewa na firistoci ne waɗanda ke lura da bagade. Waɗannan su ne zuriyar Zadok waɗanda su kaɗai ne daga cikin Lawiyawa da suke da iznin kusatar Ubangiji don su yi masa hidima.”

47Ya auna filin, tsawonsa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu ɗari, wato murabba'i ke nan. Bagade kuma yana a gaban Haikalin. 48Ya kuma kai ni a shirayin Haikalin. Ya auna ginshiƙan shirayin, kamu biyar ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar kuwa kamu uku ne a kowane gefe. 49Tsawon shirayin kamu ashirin ne, faɗinsa kuwa kamu goma sha ɗaya. Akwai matakan hawa, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe.

41

1Sai ya kai ni cikin Haikalin, sa'an nan ya auna ginshiƙai. Fāɗin ginshiƙan kamu shida ne a kowane gefe. 2Fāɗin ƙofar kamu goma ne. Madogaran ƙofar kamu biyar ne a kowane gefe. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu arba'in ne faɗinsa kuma kamu ashirin ne.

3Sai ya shiga ɗaki na can ciki, ya auna madogaran ƙofar, ya sami kamu biyu biyu. Tsayin ƙofar kuma kamu shida ne. Faɗin ƙofar kamu bakwai ne. 4Ya kuma auna ɗaki na ƙurewar ciki, tsawonsa kamu ashirin ne, faɗinsa kuma kamu ashirin. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”

5Sai kuma ya auna bangon Haikalin, kaurinsa kamu shida ne. Faɗin ɗakunan da ke kewaye da Haikalin kamu huɗu ne. 6Ɗakunan benaye ne masu hawa uku. Akwai ɗakuna talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da Haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon Haikalin. 7Faɗin ɗakunan yana ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, gama katangar da ke kewaye da Haikali ta yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. A gefen Haikalin akwai matakan hawa. Don haka ana iya hawa daga ɗaki na ƙasa zuwa hawa na uku ta hanyar hawa na biyu. 8Na ga harsashi mai faɗi kewaye da Haikalin. Tsawon harsashin gini na ɗakunan karan awo mai tsawon kamu shida ne. katangar waje ta ɗakunan kamu biyar ne. Faɗin filin da ke tsakanin ɗakunan waje da na Haikali kamu ashirin ne kewaye da Haikalin. 11Ana buɗe ƙofofin ɗakuna a wajen filin da ke tsakanin ɗakuna. Ƙofa ɗaya tana fuskantar wajen arewa, ɗaya kuma tana fuskantar wajen kudu. Faɗin filin da ya ragu kamu biyar ne.

12Ginin da ke fuskantar farfajiyar Haikali a wajen yamma, faɗinsa kamu saba'in ne. Kaurin ginin kamu biyar ne, tsawonsa kuma kamu tasa'in ne.

13Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu ɗari. Tsawon farfajiyar, da ginin, da katangarsa, kamu ɗari. 14Faɗin Haikalin da farfajiyar a fuskar gabas, kamu ɗari. kuma auna tsawon ginin da ke fuskantar farfajiyar da ke wajen yamma da hanyar fita, kamu ɗari ne. Cikin Haikalin, da ɗaki na can ciki, da shirayi, dukansu uku suna da tagogi masu gagara badau. An manne bangon Haikalin da ke fuskantar shirayin da katako, tun daga ƙasa har zuwa tagogi. (Tagogin kuma an rufe su.) zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a bangon Haikali ciki da waje har zuwa kan ƙofar shiga. Zanen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu. 19Fuska ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe. Ɗaya fuskar kamar ta sagarin zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zana dukan jikin bangon Haikalin da su. 20Daga ƙasa zuwa ɗaurin ƙofa, an zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. 21-22Madogaran ƙofofin Haikalin murabba'i ne. Akwai wani abu mai kama da bagaden itace a gaban Wuri Mai Tsarki, tsayinsa kamu uku ne, tsawonsa kamu biyu ne. Kusurwoyinsa da gindinsa, da jikinsa na itace ne. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da ke a gaban Ubangiji.”

23Haikali da Wuri Mai Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe. 24Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje. 25A ƙofofin Haikalin an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangon Haikalin. Akwai rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin waje. 26Akwai tagogi masu gagara badau a kowane gefen ɗakin. An kuma zāna bangon da siffar itatuwan dabino.

42

1Sa'an nan ya kai ni a farfajiya da ke waje, ya kuma kai ni ɗakunan da ke kusa da farfajiyar Haikali, daura da ginin da ke wajen arewa. 2Tsawon ginin da ke wajen gefen arewa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu hamsin. 3A gaban kamu ashirin na farfajiyar da ke can ciki, da kuma a gaban daɓen farfajiyar da ke waje, akwai jerin ɗakuna hawa uku uku. 4A gaban ɗakunan akwai hanya mai faɗin kamu goma, tsawonta kuwa kamu ɗari. Ƙofofinsu suna fuskantar arewa. 5Ɗakunan da ke a hawa na uku ba su da fāɗi, gama hanyar benen ya cinye wuri fiye da ɗakunan da ke a hawa na ƙasa da na tsakiya. 6Ɗakunan suna da hawa uku, amma ba su da ginshiƙai kamar na farfajiyar da ke waje. Saboda haka ɗakunan da ke a hawa na uku ba su kai girman waɗanda ke a hawa na ƙasa da na tsakiya ba. 7Tsawon katangar waje wadda ke gefen ɗakunan farfajiyar waje wanda ke daura da ɗakunan kamu hamsin ne. 8Tsawon ɗakunan da ke fuskantar farfajiyar waje kamu hamsin ne. Waɗanda ke fuskantar Haikalin kuwa tsawonsu kamu ɗari ne. 9Ƙasa da ɗakunan nan akwai ƙofa a gefen gabas, in za a shiga cikinsu daga farfajiyar waje. 10Akwai kuma ɗakuna a faɗin katangar farfajiyar a wajen gabas a gaban wata farfajiyar da gaban wani gini. 11Akwai hanya a gaban ɗakunan, sun kuma yi kama da ɗakunan da ke wajen arewa. Tsawonsu, da faɗinsu, da yadda aka shirya su, da ƙofofinsu duk iri ɗaya ne. 12Kamar ƙofofin ɗakunan da ke wajen kudu, hakanan kuma akwai ƙofa a hanyar da ke gaban katanga a wajen gabas, in za a shiga.

13Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da ke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda ke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne. 14Sa'ad da firistoci suka shiga Wuri Mai Tsarki, ba za su fita daga cikinsa zuwa farfajiyar da ke waje ba, sai sun tuɓe rigunan aikinsu, gama rigunan tsarkakakku ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su tafi inda mutane suke.”

15Sa'ad da ya gama auna cikin Haikalin, ya fito da ni ta ƙofar gabas, sa'an nan ya auna filin da ke kewaye da Haikalin. 16Ya auna kusurwar gabas da karan awo, kamu ɗari biyar. 17Sai kuma ya auna kusurwar arewa, kamu ɗari biyar. 18Kusurwar kudu kamu ɗari biyar. 19Kusurwar yamma, ita ma kamu ɗari biyar. 20Ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana kewaye da katanga mai tsawo kamu ɗari biyar ne, fāɗi kuma kamu ɗari biyar don ya raba Wuri Mai Tsarki da sauran wurin.

43

Zatin Ubangiji ya Koma Haikalin

1Bayan haka kuma sai ya kai ni ƙofar da ke fuskantar gabas. 2Sai ga zatin Allah na Isra'ila yana tahowa daga gabas. Muryar Allah ta yi amo kamar rurin teku. Duniya kuwa ta haskaka da zatinsa. 3Wahayin da na gani ya yi kama da wahayin da na gani lokacin da ya hallaka birnin, kamar kuma wanda na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki. 4Zatin Ubangiji ya shiga Haikalin ta ƙofar gabas.

5Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali. 6Sa'ad da mutumin ke tsaye kusa da ni, sai Ubangiji ya yi magana da ni daga cikin Haikalin. 7Ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wuri shi ne kursiyin sarautata da kilisaina, inda zan zauna tsakiyar mutanen Isra'ila har abada. Mutanen Isra'ila da sarakunansu ba za su ƙara ɓata sunana mai tsarki ta wurin bauta wa gumaka da gina siffofin sarakunansu da suka mutu ba, 8ko kuwa ta wurin sa dokin ƙofarsu kusa da dokin ƙofata, da kuma ta kafa madogaran ƙofarsu kusa da nawa, sai dai katangar da ta yi mana tsakani. Sun ɓata sunana mai tsarki da ayyukansu masu banƙyama, don haka na hallaka su saboda sun sa na husata. 9Yanzu sai su zubar da gumakansu da siffofin sarakunansu nesa da ni, ni kuwa zan zauna a cikinsu har abada.

Ka'idodin Haikali da Bagade

10“Kai kuwa ɗan mutum, sai ka bayyana Haikalin ga mutanen Isra'ila domin su kunyata saboda muguntarsu, ka kuma sa su auna fasalin Haikalin. 11Idan sun ji kunyar dukan abin da suka aikata, sai ka nuna musu fasalin Haikalin, da tsarinsa, da wuraren fita, da wuraren shiga, da fasalinsa duka. Ka kuma sanashe su dukan ka'idodinsa, da dukan dokokinsa. Ka rubuta a gaban idanunsu don su kiyaye, su aikata dukan dokokinsa da dukan ka'idodinsa. 12Wannan ita ce dokar Haikalin. Dukan filin da ke kewaye a kan dutsen, za ta zama wuri mai tsarki ƙwarai.

13“Wannan shi ne girman bagaden bisa ga tsawon kamu. A nan kamu guda daidai yake da kamu guda da taƙi. Gindinsa kamu ɗaya ne, faɗinsa kuma kamu ɗaya, faɗin da'irarsa taƙi guda ne. 14Tsayin bagaden zai zama kamu biyu daga gindinsa zuwa ƙaramin mahaɗinsa fāɗinsa kuma kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗi zai zama kamu huɗu, faɗinsa kuwa kamu ɗaya. 15Tsayin murhun bagaden zai zama kamu huɗu. A kan murhun akwai zanko guda huɗu sun miƙe sama, tsawonsu kamu guda ne. 16Murhun bagaden zai zama murabba'i ne, wato tsawonsa kamu goma sha biyu, faɗinsa kuma kamu goma sha biyu. 17Mahaɗin kuma zai zama kamu goma sha huɗu, murabba'i. Faɗin da'irarsa zai zama rabin kamu, kewayen gindinsa zai zama kamu ɗaya. Matakan bagaden za su fuskanci gabas.”

18Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka'idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa, 19sai ka ba firistoci na zuriyar Zadok, masu yi mini hidima, bijimai na yin hadaya domin zunubi. 20Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da'irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa. 21Za ka kuma ɗauki bijimi na yin hadaya domin zunubi, ka kai shi waje, a wurin da aka shirya a bayan Haikalin, ka ƙone shi. 22A kan rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin yin hadaya don zunubi, bagaden kuma zai tsarkaka, kamar yadda aka tsarkake shi da bijimin. 23Sa'ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa bijimi da rago marar lahani. 24Za ka kawo su a gaban Ubangiji, firistoci za su barbaɗe su da gishiri, su miƙa su hadayar ƙonawa ga Ubangiji. 25Kowace rana za ka riƙa miƙa akuya, da bijimi, da rago, marasa lahani domin yin hadaya don zunubi, har kwana bakwai. 26Za su yi kafara har kwana bakwai don su tsarkake bagaden, su keɓe shi. 27Sa'ad da suka cika kwanakin nan bakwai, sa'an nan a kan rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayun ƙonawa da na salama a kan bagaden. Ni kuwa zan karɓe ku, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

44

Hidimar Haikali

1Ya kuma komo da ni ƙofar waje ta Haikali wadda ke wajen gabas. Ƙofar kuwa tana rufe. 2Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofa za ta kasance a rufe, ba za a buɗe ta ba, ba wanda kuma zai shiga ta cikinta, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya shiga ta cikinta, saboda haka za ta kasance a rufe. 3Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”

4Sa'an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki. 5Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka'idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.

6“Ka ce wa 'yan tawaye, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, “‘Ku daina ayyukanku na banƙyama. 7Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama. 8Ba ku lura da hidimomina masu tsarki ba, amma kuka sa baƙi su lura da wurina mai tsarki.”

9Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da ke cikin jama'ata Isra'ila da zai shiga wurina mai tsarki.

10“Amma Lawiyawa waɗanda suka yi nisa da ni, suka rabu da ni, suna bin gumakansu, sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkata, za su ɗauki alhakin muguntarsu. 11Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima. 12Da ya ke sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu. 13Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama. 14Amma duk da haka zan sa su lura da Haikalin, su yi dukan hidimomin da za a yi a cikinsa.

15“Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa. 16Za su shiga Wuri Mai Tsarki, su kusaci teburina, su yi mini hidima, su kuma kiyaye umarnina. 17Sa'ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, sai su sa rigunan lilin, kada su sa abin da aka yi shi da ulu, sa'ad da suke hidima a ƙofofin fili na can ciki, da cikin Haikalin. 18Za su naɗa rawunan lilin, su sa wandunan lilin. Kada su sa abin da zai sa su yi zuffa. 19Sa'ad da suka fita zuwa filin da ke waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.

20“Ba za su aske kansu ba, ba kuma za su bar zankayensu su yi tsayi ba, sai su sausaye gashin kansu. 21Kada firist ya sha ruwan inabi sa'ad da zai shiga fili na can ciki. 22Ba za su auri gwauruwa ba, wato wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, sai budurwa daga zuriyar Isra'ila, ko kuwa matar firist wanda ya rasu.

23“Za su koya wa jama'ata bambancin halal da haram, su kuma nuna musu yadda za su rarrabe tsakanin tsattsarka da marar tsarki. 24Za su zama masu raba gardama, za su yanke magana bisa ga doka. Za su kiyaye idodina bisa ga tsarinsu. Za su kuma kiyaye ranakun Asabar masu tsarki.

25“Ba za su kusaci gawa ba, don kada su ƙazantar da kansu, amma saboda mahaifi, ko mahaifiya, ko ɗa, ko 'ya, ko 'yar'uwar da ba ta kai ga yin aure ba, ko ɗan'uwa, sa iya ƙazantar da kansu. 26Bayan ya tsarkaka, sai ya dakata har kwana bakwai. 27A ranar da zai shiga Wuri Mai Tsarki, can fili na ciki, domin ya yi hidima a wurin, sai ya miƙa hadayarsa don zunubi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

28“Ba za su sami rabon gādo ba, gama ni ne rabon gādonsu. Ba za ku ba su abin mallaka a cikin Isra'ila ba, ni ne abin mallakarsu. 29Za su ci hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya domin laifi, kowane keɓaɓɓen abu kuma cikin Isra'ila zai zama nasu. 30Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku. 31Firistoci ba za su ci mushen kowane irin tsuntsu ko dabba ba, ba kuma za su ci waɗanda wata dabba ta kashe ba.”

45

Yankin Ƙasar da za a Keɓe wa Ubangiji

1“Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗinsa kuwa kamu dubu goma (10,000). Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki. 2Daga cikin wannan, murabba'i mai tsawo kamu ɗari biyar, da faɗi ɗari biyar, zai zama wuri mai tsarki, fili kuma mai kamu hamsin zai kewaye wurin nan mai tsarki. 3A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), da faɗi kamu dubu goma (10,000), inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance. 4Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda ke hidima a cikin Haikali, waɗanda ke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin. 5Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), da faɗi kamu dubu goma (10,000), zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki. 6Za ku tsaga wa birnin hurumi mai fāɗi kamu dubu biyar, da tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), rabe da yankin nan mai tsarki. Hurumin zai zama na mutanen Isra'ila duka.”

Ƙasar Sarki

7“Ƙasar da ke a sashin yankin nan mai tsarki, da hurumin birnin, zai zama na sarki. Zai zama hannun riga da yanki mai tsarki da hurumin birnin a wajen yamma da gabas. Tsawonta zai zama daidai da yanki ɗaya na yankunan kabilan. Za ta miƙe daga yamma zuwa iyakar ƙasar daga gabas. 8Wannan zai zama yankin ƙasarsa a cikin Isra'ila. Sarakunana kuma ba za su ƙara zaluntar mutanena ba, amma za su ba mutanen Isra'ila ƙasar bisa ga kabilansu.”

Ma'aunai na Gaskiya

9“Ni Ubangiji Allah na ce ku sarakunan Isra'ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari'a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

10“Sai ku kasance da ma'aunai na gaskiya, kamar su mudu da garwa.

11“Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma'auni.

12“Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”

Hadayu da Sadakoki

13“Wannan ita ce bayarwar da za ku yi. Za ku ba da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta alkama, da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta sha'ir. 14Za ku ba da ɗaya daga cikin goma ta garwa daga kowace ganga ta mai. Ganga tana cin garwa goma. 15Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra'ila. “Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16“Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra'ila. 17Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra'ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra'ila kafara.”

Idin Ƙetarewa

18“Ni Ubangiji Allah na ce, rana ta fari ga watan fari, za ku ɗauki bijimi marar lahani don a tsarkake Haikalin. 19Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki. 20Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan, saboda wanda ya yi laifi da kuskure, ko da rashin sani. Ta haka ne za ku yi wa Haikalin kafara.

21“A kan rana ta goma sha huɗu ga watan fari kuma za ku kiyaye Idin Ƙetarewa. Za ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai. 22A ranar, sarki zai ba da bijimi domin kansa da jama'ar ƙasar, saboda yin hadaya don zunubi. 23A ranaku bakwai na Idin, zai ba da bijimi bakwai da raguna bakwai marasa lahani hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Kowace rana kuma zai ba da bunsuru hadaya don zunubi. 24Zai kuma ba da hadaya ta gari, mudu guda domin kowane bijimi, da mudu guda domin kowane rago, da wajen kwalaba shida na mai tare da kowane mudu.

25“A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, zai kuma ba da abubuwan nan har kwana bakwai domin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari game da mai.”

46

Sarki da Hidimomin Idodi

1“Ni Ubangiji Allah na ce za a rufe ƙofar fili ta can ciki wadda ke fuskantar gabas dukan ranaku shida na aiki, amma za a buɗe ta a ranar Asabar da a amaryar wata. 2Sarki zai shiga ta ƙofar shirayi daga waje, sa'an nan ya tsaya kusa da ginshiƙin ƙofar. Sai firistoci su miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayunsa na salama, shi kuwa ya yi sujada s bakin ƙofar, sa'an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da maraice. 3Jama'ar ƙasar za su yi wa Ubangiji sujada a bakin wannan ƙofa a ranakun Asabar da a amaryar wata. 4Hadaya ta ƙonawa da sarki zai miƙa wa Ubangiji a ranar Asabar 'yan raguna shida ne da rago ɗaya marasa lahani. 5Gārin hadaya da za a yi tare da rago wajen garwa guda ne. Wanda za a yi tare da 'yan raguna kuwa zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da mai wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta gari. 6A amaryar wata kuwa zai miƙa bijimi, da 'yan raguna shida, da rago, dukansu marasa lahani. 7Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da 'yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin. 8Sa'ad da sarki zai shiga, sai ya shiga ta ƙofar shirayin, ya kuma fita ta nan.

9“Sa'ad da jama'ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga. 10Sa'ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa'ad da suka fita kuma, sai ya fita. 11A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.

12“Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da ke fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.

13“Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani. 14Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum. 15Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.

16“Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo. 17Amma idan sarki ya yi wa wani daga cikin barorinsa kyauta daga cikin gādonsa, kyautar za ta zama tasa har shekarar 'yantarwa, sa'an nan kyautar za ta koma a hannun sarki. 'Ya'yansa maza ne kaɗai za su riƙe kyauta daga cikin gādonsa din din din. 18Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama'a, ya hana musu. Sai ya ba 'ya'yansa maza rabon gādo daga cikin abin da ke nasa, amma kada ya ƙwace wa jama'ata abin da suka mallaka har su warwatse.”

19Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar da ke gefen ƙofa mai fuskantar arewa, wajen jerin tsarkakakkun ɗakuna na firistoci, waɗanda ke fuskantar arewa. Na kuma ga wani wuri daga can ƙurewar yamma. 20Sai ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya domin laifi, da hadaya domin zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gāri, domin kada su kai su a filin waje, su sa wa mutane tsarki.”

21Ya kuma kai ni a farfajiyar waje, ya bi da ni zuwa kusurwa huɗu na farfajiya. Akwai ɗan fili a kowace kusurwa. 22Girman kowane ɗan fili tsawonsa kamu arba'in ne, faɗin kuma kamu talatin. 23A cikin kowane ɗan fili na kusurwa huɗu ɗin akwai jerin duwatsu. Aka gina murhu ƙarƙashin jerin duwatsun. 24Sa'an nan ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a Haikali za su dafa hadayun da jama'a suka kawo.”

47

Kogin da ke Malalowa daga Haikali

1Ya komo da ni zuwa ƙofar Haikalin, sai ga ruwa yana bulbulowa daga ƙarƙashin bakin ƙofar Haikalin a wajen gabas, gama Haikalin na fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa daga gefen kudancin bakin ƙofar Haikalin, a kudancin bagaden. 2Sai ya fito da ni ta hanyar ƙofar arewa, ya kewaya da ni zuwa ƙofar waje wadda take fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa kaɗan kaɗan daga wajen kudu. 3Mutumin ya nufi wajen gabas da ma'auni a hannunsa, ya auna kamu dubu, sa'an nan ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan ya kama ni idon ƙafa. 4Sai kuma ya auna kamu dubu, ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan kuwa ya kama ni gwiwa. Sai ya sāke auna kamu dubu, ya sa in haye ruwan, sai zurfin ruwan ya kai ga kama ni gindi. 5Ya sāke auna kamu dubu kuma, sai ruwan ya zama kogi har ban iya in haye ba, gama ruwan ya hau, ya zama da zurfin da ya isa ninƙaya. Ya zama kogin da ba za a iya hayewa ba. 6Sai ya tambaye ni, ya ce. “Ɗan mutum, ka ga wannan?” Sa'an nan ya komo da ni zuwa gāɓar kogin. 7Sa'ad da nake tafiya, sai na ga itatuwa da yawa a kowace gāɓar kogin. 8Ya kuma ce mini, “Wannan ruwa yana gangarowa zuwa wajen gabas har zuwa cikin Araba. Zai shiga ruwan teku marar gudu, ruwan tekun kuwa zai zama ruwan daɗi. 9Kowace halitta mai rai da ke cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu. 10Masunta za su tsaya a gāɓar tekun daga En-gedi zuwa En-eglayim. Gāɓar teku za ta zama wurin shanya taruna. Za a sami kifaye iri iri a cikinta kamar kifaye na Bahar Rum. 11Amma ruwan fadamunsa ba zai yi daɗi ba, za a bar shi a gishirinsa. 12A kowace gāɓar kogin, itatuwa iri iri na abinci za su yi girma. Ganyayensu ba za su bushe ba, itatuwan kuma ba za su fasa yin 'ya'ya ba, amma su za su yi ta bayarwa a kowane wata, gama ruwansu yana malalowa daga Haikalin. 'Ya'yansu abinci ne, ganyayensu kuwa magani ne.”

Iyakar Ƙasar

13Ubangiji Allah ya ce, “Waɗannan su ne kan iyaka da za su raba ƙasar gādo ga kabilan Isra'ila goma sha biyu. Yusufu zai sami rabo biyu. 14Za ku raba daidai, gama na rantse zan ba kakanninku wannan ƙasa, za ta kuwa zama gādonku.

15“A wajen arewa, iyakar za ta kama daga Bahar Rum, ta bi ta hanyar Hetlon zuwa Zedad, 16da Hamat, da Berota, da Sibrayim, wadda ke a iyakar tsakanin Dimashƙu da Hamat, har zuwa Hazer-hattikon wadda ke iyakar Hauran. 17Iyakar za ta bi daga teku zuwa Hazar-enan wadda ke iyakar Dimashƙu. Iyakar Hamat tana wajen arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.

18“A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra'ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.

19“A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

20“A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

21“Za ku kuwa raba ƙasar a tsakaninku bisa ga kabilan Isra'ila. 22Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da ke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila, 23a cikin kabilar da baƙon yake zaune, nan ne za ku ba shi nasa gādo, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

48

Rarraba Ƙasar

1“Ga sunayen kabilan da rabon gādonsu. Yankin Dan, shi ne daga iyakar arewa daga tekun. Ya bi ta Hetlon zuwa ƙofar Hamat, har zuwa Hazar-enan wadda ke iyakar Dimashƙu daga arewa, daura da Hamat. Ya zarce daga gabas zuwa yamma. 2Yankin Ashiru yana kusa da yankin Dan, daga gabas zuwa yamma. 3Yankin Naftali yana kusa da yankin Ashiru daga gabas zuwa yamma. 4Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma. 5Yankin Ifraimu yana kusa da yankin Manassa daga gabas zuwa yamma. 6Yankin Ra'ubainu yana kusa da yankin Ifraimu daga gabas zuwa yamma. 7Yankin Yahuza yana kusa da yankin Ra'ubainu daga gabas zuwa yamma.

8“Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.

9“Yankin da za ku keɓe wa Ubangiji, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗinsa kuwa kamu dubu goma (10,000). 10Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma (10,000) ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma (10,000), a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000). Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa. 11Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci daga zuriyar Zadok waɗanda suka kiyaye umarnina, ba su karkace kamar yadda Lawiyawa suka yi lokacin da jama'ar Isra'ila suka karkace ba. 12Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da ke kusa da yankin Lawiyawa. 13Gab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗi kuma kamu dubu goma (10,000). Tsawonsa duka zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), faɗi kuwa kamu dubu goma (10,000). 14Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.

15“Ragowar yankin mai faɗin kamu dubu biyar (5,000), da tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), zai zama hurumin birnin, inda za a yi gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar yankin. 16Ga yadda girman birnin zai kasance, a wajen arewa kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500), a wajen kudu kuwa kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500), a wajen gabas kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500), a wajen yamma kuma kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500). 17Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin. 18Ragowar tsawon yankin da ke gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma (10,000) a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma (10,000). Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma'aikatan birnin. 19Ma'aikatan birnin za su samu daga dukan kabilan Isra'ila, za su noma yankin.

20“Dukan yankin da za ku keɓe zai zama murabba'i mai kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000), wato tsattsarkan yankin tare da hurumin birnin.

21“Ragowar kowane gefe na tsattsarkan yankin da hurumin birnin, zai zama na sarki. Tun daga kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) na tsattsarkan yankin, zuwa iyakar da ke wajen gabas, daga kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) kuma zuwa iyakar wajen yamma, hannun riga da yankunan kabilan zai zama na sarki. Tsattsarkan yankin da wuri mai tsarki na Haikali za su kasance a tsakiyarsa. 22Rabon Lawiyawa da hurumin birnin za su kasance a tsakiyar yankin da ke na ɗan sarki. Yankin ɗan sarki zai kasance a tsakanin yankin Yahuza da yankin Biliyaminu.

23“Sauran kabilan kuwa za su samu. Biliyaminu zai sami yankinsa daga gabas zuwa yamma. 24Yankin Saminu yana kusa da yankin Biliyaminu daga gabas zuwa yamma. 25Yankin Issaka yana kusa da yankin Saminu daga gabas zuwa yamma. 26Yankin Zabaluna yana kusa da yankin Issaka daga gabas zuwa yamma. 27Yankin Gad yana kusa da yankin Zabaluna daga gabas zuwa yamma.

28“Kusa da yankin Gad zuwa kudu, iyakar za ta bi ta Tamar zuwa ruwan Meriba-kadesh, sa'an nan ta bi rafin Masar zuwa Bahar Rum.”

29Ubangiji ya ce, “Wannan ita ce hanyar da za ku raba gādo tsakanin kabilan Isra'ila. Waɗannan kuwa su ne yankunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Ƙofofin Birni

30“Ƙofofin birnin a gefen arewa, kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500) ne. 31Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Ra'ubainu, da Ƙofar Yahuza, da Ƙofar Lawi. Ana kiran sunayen ƙofofin birnin da sunayen kabilan Isra'ila. 32A gefen gabas, kamu dubu huɗu ne da ɗari biyar (4,500). Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Yusufu, da Ƙofar Biliyaminu, da Ƙofar Dan. 33A gefen kudu, kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500). Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Saminu, da Ƙofar Issaka, da Ƙofar Zabaluna. 34A gefen yamma, kamu dubu huɗu da ɗari biyar (4,500) ne. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Gad, da Ƙofar Ashiru, da Ƙofar Naftali. 35Da'irar birnin kamu dubu goma sha takwas (18,000) ne. Daga wannan lokaci za a kira birnin, “‘Ubangiji Yana Nan!”