Galatians

WASIƘAR BULUS ZUWA GA
Galatiyawa

1

Gaisuwa

1Daga Bulus, manzo, ba kuwa manzon mutum ba, ba kuma ta wurin wani mutum ba, sai dai ta wurin Yesu Almasihu, da Allah Uba, wanda ya tashe shi daga matattu, 2da kuma dukan 'yan'uwa da suke tare da ni, zuwa ga ikilisiyoyin ƙasar Galatiya.

3Alheri da salama na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu, 4wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu, domin ya cece mu daga mugun zamanin nan, bisa ga nufin Allahnmu, wato Ubanmu. 5Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

Ba wata Bishara

6Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara, 7alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu. 8Amma ko mu, ko kuma wani mala'ika daga sama, in waninmu zai yi muku wata bishara dabam da wadda muka yi muku, to, yă zama la'ananne! 9Kamar yadda muka faɗa a dā, haka yanzu ma nake sāke faɗa, cewa kowa ya yi muku wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, to, yă zama la'ananne!

10To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.

Shigar Bulus Manzanci

11Ina so in sanar da ku, 'yan'uwa, bisharar nan da na sanar ba ta ɗan adam ba ce, 12domin ba daga wurin mutum na samo ta ba, ba kuma koya mini ita aka yi ba, sai dai ta wurin bayyanar Yesu Almasihu a gare ni ne na same ta. 13Kun dai ji irin zamana na dā a cikin addinin yahudanci, yadda na riƙa tsananta wa Ikilisiyar Allah ƙwarai da gaske, har ina ta watsa ta, 14yadda kuma a cikin addinin Yahudanci har na tsere wa yawancin tsararrakina a cikin mutanenmu, na himmantu ƙwarai da gaske ga bin al'adun kakanninmu. 15Amma sa'ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin 16bayyana Ɗansa a gare ni, domin in sanar da shi ga al'ummai, ban yi shawara da ɗan adam ba, 17ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa'an nan na komo Dimashƙu.

18Bayan shekara uku kuma sai na tafi Urushalima ganin Kefas, na kuwa kwana goma sha biyar a gunsa. 19Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan'uwan Ubangiji. 20Abin nan da nake rubuto muku fa, ba ƙarya nake yi ba, a gaban Allah nake faɗa. 21Daga baya kuma, na tafi ƙasar Suriya da ta Kilikiya. 22Amma kuwa ikilisiyoyin Almasihu da suke a ƙasar Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna. 23Sai dai kawai sun ji an ce, “Wanda dā yake tsananta mana, ga shi, a yanzu yana sanar da bangaskiyar nan da dā yake ta rusawa!” 24Sai suka ɗaukaka Allah saboda ni.

2

Sauran Manzanni sun Karɓi Bulus

1Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima tare da Barnaba, na kuma ɗauki Titus. 2Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce. 3Kai, ko Titus ma da yake a tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne. 4Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta. 5Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku. 6Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba. 7Amma da suka ga an amince mini in yi wa marasa kaciya bishara, kamar yadda aka amince wa Bitrus ya yi wa masu kaciya bishara, 8(domin shi da ya yi aiki a zuciyar Bitrus ya sa shi manzo ga masu kaciya, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata, ya sa ni manzo ga al'ummai), 9sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya. 10Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.

Bulus ya Tsawata wa Bitrus a Antakiya

11Amma da Kefas ya zo Antakiya, sai na tsaya masa fuska da fuska don laifinsa a fili yake. 12Don kafin waɗansu su zo daga wurin Yakubu, yakan ci abinci da al'ummai. Amma da suka zo, ya janye jiki ya ware kansa, yana tsoron ɗariƙar masu kaciyar nan. 13Haka ma sauran Yahudawa masu bi suka nuna fuska biyu kamarsa, ko da Barnaba ma sai da suka ciwo kansa da munafuncinsu. 14Amma da na ga dai ba sa bin gaskiyar bishara sosai, na ce wa Kefas a gaban idon kowa, “Kai da kake Bayahude, in ka bi al'adar al'ummai ba ta Yahudawa ba, yaya kake tilasta wa al'ummai su bi al'adar Yahudawa>

Ceton Yahudawa duk da Al'ummai ta wurin Bangaskiya

15“Mu da aka haifa Yahudawa, ba al'ummai masu zunubi ba, 16da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a. 17In kuwa ya zamana, sa'ad da muke neman kuɓuta ga Allah ta wurin Almasihu, an tarar har mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, Almasihu yana hidimar zunubi ne? A'a, ko kusa! 18Amma in na sāke ginin abin da dā na rushe, na tabbata mai laifi ke nan. 19Gama ni ta wurin Shari'a matacce ne ga Shari'a domin in rayu ga Allah. 20An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina. 21Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”

3

Shari'a ko Bangaskiya

1Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ɗauke hankalinku? Ku da aka bayyana muku Yesu Almasihu gicciyeyye sosai. 2Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari'a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji? 3Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? 4Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne! 5Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji>

6Haka ma Ibrahim “Ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.” 7Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne 'ya'yan Ibrahim. 8A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.” 9To, ashe, masu bangaskiya su ne aka yi wa albarka a game da Ibrahim mai bangaskiyar nan.

10Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.” 11To, a fili yake, ba mai samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, domin “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.” 12Shari'a kuwa ba ta dangana ga bangaskiya ba, domin ta ce, “Wanda ya aikata ta, ta gare ta ne zai rayu.” 13Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.” 14An yi wannan kuwa domin albarkar nan da aka yi wa Ibrahim ta saukar wa al'ummai ta wurin Almasihu Yesu, mu kuma ta hanyar bangaskiya mu sami Ruhun nan da aka yi alkawari.

Shari'a da Alkawari

15To, 'yan'uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutum ne kawai, in dai an riga an tabbatar da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai. 16To, alkawaran nan, an yi wa Ibrahim ne, da kuma wani a zuriyarsa. Ba a ce, “Da zuriya” ba, kamar suna da yawa. A'a, sai dai ɗaya kawai, aka ce, “Wani a zuriyarka,” wato Almasihu. 17Ga abin da nake nufi. Shari'ar nan, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi. 18Don da gādon nan ta hanyar Shari'a yake samuwa, ashe, da ba zai zama na alkawarin ke nan ba. Amma Allah ya bai wa Ibrahim ta wurin alkawari ne.

19To, mece ce manufar Shari'a? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala'iku ne, ta hannun matsakanci. 20Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.

Manufar Shari'a

21Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan. 22Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.

23Tun kafin bangaskiya ta zo, a cikin ƙangin Shari'a muke a kulle, sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana. 24Ashe kuwa, Shari'a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya. 25A yanzu kuwa da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a hannun wata uwargijiya. 26Domin dukanku 'ya'yan Allah ne, ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu. 27Duk ɗaukacinku da aka yi wa baftisma ga bin Almasihu, kun ɗauki halin Almasihu ke nan. 28Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu. 29In kuwa ku na Almasihu ne, ashe, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda ne kuma bisa ga alkawarin nan.

4

1Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome. 2A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa. 3Haka yake a gare mu, wato sa'ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al'adun duniya muke. 4Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a, 5domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari'a, a mai da mu a matsayin 'ya'yan Allah. 6Tun da yake ku 'ya'ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!” 7Don haka, kai ba bawa ba ne kuma, amma ɗa ne. Da yake ɗa ne kuma, to, magāji ne bisa ga ikon Allah.

Alhinin Bulus a kan Masu Bangaskiya

8Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin kome suke ba. 9Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu? 10Ga shi, al'adun ranaku, da na watanni, da na lokatai, da na shekaru ba sa wuce ku! 11Amma kun ba ni tsoro, kada ya zamana na yi wahala a kanku a banza!

12Ina roƙonku, ya ku 'yan'uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba. 13Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari. 14Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na'am da ni kamar wani mala'ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa. 15To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni! 16Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya? 17Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su. 18Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba. 19Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku! 20Da ma a ce ina tare da ku a yanzu in sauya muryata! Gama na ruɗe a kan sha'aninku.

Ishara da Hajaratu da Saratu

21Ku gaya mini, ku da kuke son Shari'a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne? 22Domin a rubuce yake, Ibrahim yana da 'ya'ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan 'ya. 23Ɗan kuyangar nan, an haife shi ne bisa ga ɗabi'a, ɗan 'yar kuwa ta cikar alkawarin ne. 24Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina'i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan. 25To, ai, Hajaratu Dutsen Sina'i ce a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da 'ya'yanta duk a bauta suke. 26Amma Urushalima ta sama, ai 'ya ce, ita ce kuma uwarmu. 27Domin a rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki, ya ke bakarariya da ba kya haihuwa, Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda, Don yasasshiya ta fi mai miji yawan 'ya'ya.”

28To, 'yan'uwa, mu ma 'ya'yan alkawari ne kamar Ishaku. 29Kamar yadda dā, shi da aka haifa bisa ga ɗabi'a ya tsananta wa wanda aka haifa bisa ga ikon Ruhun, haka a yanzu ma yake. 30Amma me Nassin ya ce? “Ka kori kuyangar da ɗanta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gādo tare da ɗan 'ya ba.” 31Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan kuyanga ba ne, na 'ya ne.

5

Ku Dāge a cikin 'Yanci

1Almasihu ya 'yanta mu, 'yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.

2To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan. 3Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a. 4Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah. 5Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya. 6In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.

7Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya? 8Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa. 10Na dai amince da ku a cikin Ubangiji, ba za ku bi wani ra'ayi dabam da nawa ba. Wannan da yake ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wane ne. 11Amma 'yan'uwa, in da har yanzu wa'azin yin kaciya nake yi, to, don me har yanzu ake tsananta mini? In da haka ne, ashe, an kawar da hamayyar da gicciyen Almasihu yake sawa ke nan! 12Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!

13Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna. 14Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 15Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.

Albarkar Ruhu da Halin Mutuntaka

16Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba. 17Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so. 18In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari'a ba ta da iko da ku, ke nan.

19Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci, 20da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya, 21da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.

22Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, 23da tawali'u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari'a ta kama su. 24Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.

25In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al'amuranmu ta wurin ikon Ruhu. 26Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.

6

Ku Ɗauki Wahalar Juna

1Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu. 2Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu. 3Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan. 4Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba. 5Lalle kowa yă ji da kayansa.

6Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.

7Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba. 8Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami. 9Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba. 10To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.

Kashedi da kuma Gaisuwa

11Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna! 12To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu. 13Ai, ko waɗanda aka yi wa kaciya ma ba sa kiyaye Shari'a. Sonsu ne a yi muku kaciya, don su yi fāriya da ku a kan an yi muku kaciya. 14Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina. 15Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu. 16Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.

17Daga nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.

18Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, 'yan'uwa. Amin.