Genesis

FARAWA

1

Allah ya Halicci Duniya ya kuma Halicci Mutum

1A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya, 2duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen. 3Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance. 4Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu, 5ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.

6Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.” 7Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance. 8Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.

9Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance. 10Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. 11Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa ke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 12Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau. 13Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.

14Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai. 15Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 16Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin. 17Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya, 18su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.

20Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.” 21Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, “Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya.” 23Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.

24Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.” 25Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

26Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.” 27Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su. 28Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.” 29Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itace da yake da ƙwaya cikin 'ya'yansa su zama abincinku. 30Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabba da take duniya, da kowane irin tsuntsu da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi.” Haka nan ya kasance. 31Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.

2

1Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu. 2A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi. 3Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.

4Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa'ad da aka halicce su. A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama, 5a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar, 6amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka.

7Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

Gonar Aidan

8Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata. 9Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.

10Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu. 11Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. 12Zinariyar ƙasar nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin. 13Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush. 14Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne.

15Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta. 16Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da 'yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar, 17amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.”

18Sa'an nan sai Ubangiji Allah ya ce, “Bai kyautu mutumin ya zauna shi kaɗai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.” 19Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan. 20Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.

21Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama, 22haƙarƙarin nan kuwa da Ubangiji Allah ya cire daga mutumin ya yi mace da shi, ya kuwa kawo ta ga mutumin. 23Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.” 24Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya.

25Da mutumin da matarsa dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba.

3

Faɗuwar Mutum

1Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, “‘Ba za ku ci daga wani itace da yake a gonar ba?”

2Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar, 3amma Allah ya ce, “‘Ba za ku ci daga cikin 'ya'yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.”

4Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”

6Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci. 7Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.

8Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la'asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”

10Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”

11Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”

12Mutumin ya ce, “Matar nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci.”

13Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”

14Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la'ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka. 15Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”

16Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”

17Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, “‘Kada ka ci daga cikinsu.” Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.

18“Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.”

20Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa'u, domin ita ce uwar 'yan adam. 21Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.

An Fitar da Adamu da Hawwa'u daga Gonar

22Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.” 23Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato, inda aka ɗauko shi.

24Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.

4

Kayinu da Habila

1Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.” 2Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. 3Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. 4Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa, 5amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har ya kwantsare fuskarsa.

6Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har fuskarka ya kwantsare? 7In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”

8Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi.

9Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?” Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”

10Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka. 12In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”

13Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina. 14Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”

15Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi.

16Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.

Zuriyar Kayinu

17Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu. 18An haifa wa Anuhu ɗa, wato, Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek. 19Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai. 20Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi. 21Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa. 22Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubal-kayinu Na'ama ne. 23Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa, na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni. 24Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba'in da bakwai.”

Zuriyar Shitu

25Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.” 26Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.

5

Zuriyar Adamu

(1 Tar 1.1-14)

1Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah. 2Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su. 3Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu. 4Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza. 5Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.

6Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh. 7Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 8Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.

9Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan. 10Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 11Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.

12Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel. 13Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 14Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.

15Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared. 16Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 17Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu.

18Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu. 19Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza. 20Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.

21Sa'ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela. 22Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi 'ya'ya mata da maza. 23Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar. 24Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.

25Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek. 26Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 27Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.

28Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa, 29ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.” 30Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 31Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba'in da bakwai, ya rasu.

32Sa'ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

6

Muguntar 'Yan Adam

1Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi 'ya'ya mata, 2sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. 3Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.” 4A waɗannan kwanaki kuwa, 'ya'yan Allah suka shiga wurin 'yan matan mutane, suka kuwa haifa musu 'ya'ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.

5Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin. 6Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai. 7Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.” 8Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah. 10Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet. 11Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina. 12Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

Nuhu ya Sassaƙa Jirgi

13Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi. 14Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro. 15Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba'in da biyar, tsayinsa ƙafa arba'in da biyar. 16Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. 17Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu. 18Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da 'ya'yanka, da matarka, da matan 'ya'yanka tare da kai. 19Daga kowane irin mai rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai, amma su kasance namiji da ta mace. 20Tsuntsaye bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kowane irin mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsa, biyu biyu na kowane iri za su shiga tare da kai, su rayu. 21Ka ɗauki kuma kowane irin abinci da ake ci, ka tanada, zai kuwa zama abincinka da nasu.” 22Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.

7

Ruwan Tsufana

1Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni. 2Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace, 3da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka. 4Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.” 5Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

6Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya. 7Nuhu da 'ya'yansa da matarsa, da matan 'ya'yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana. 8Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa, 9biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu. 10Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.

11A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. 12Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba'in da dare arba'in.

13A wannan rana Nuhu da 'ya'yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan 'ya'yansa tare suka shiga jirgin, 14su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi. waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya.

17Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba'in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya. 18Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye. 19Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da suke ƙarƙashin sammai duka. 20Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar. 21Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum, 22da kowane abu da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu. 23Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi. 24Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.

8

Ƙarshen Ruwan Tsufana

1Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye. 2Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai, 3ruwa ya yi ta janyewa daga duniya. Bayan kwana ɗari da hamsin sai ruwa ya ragu. 4Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat. 5Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.

6A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya. 8Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye, 9amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi. 10Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin. 11Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya. 12Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba.

13A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya. 14Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe.

15Sa'an nan sai Allah ya ce wa Nuhu, 16“Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai. 17Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato, tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.” 18Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi, 19da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.

Nuhu ya Miƙa Hadaya

20Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden. 21Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā. 22Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba.”

9

Allah ya Yi Alkawari da Nuhu

1Allah kuwa ya sa wa Nuhu da 'ya'yansa albarka, ya ce musu, “Ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku cika duniya. 2Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku. 3Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome. 4Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato, mushe. 5Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan'uwansa.

6“Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa. 7Amma ku, ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”

8Allah kuwa ya ce wa Nuhu da 'ya'yansa. 9“Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku, 10da kowane mai rai da yake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya. 11Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

12Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa, 13na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya. 14Sa'ad da na kawo gizagizai bisa duniya, aka ga bakan a cikin gizagizai, 15zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba. 16Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da yake bisa duniya.”

17Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”

Nuhu da 'Ya'yansa Maza

18'Ya'yan Nuhu waɗanda suka fito daga jirgi su ne Shem, da Ham, da Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan'ana. 19Su uku ɗin nan su ne 'ya'yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane.

20Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi. 21Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa. 22Sai Ham, mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa 'yan'uwansa biyu waɗanda suke waje. 23Sai Shem da Yafet suka ɗauki riga, suka ɗibiya bisa kafaɗunsu, suka yi tafiya da baya da baya suka rufa tsiraicin mahaifinsu, suka juya fuskokinsu, ba su kuwa ga tsiraicin mahaifinsu ba. 24Sa'ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa. 25Sai ya ce, “La'ananne ne Kan'ana, bawan bayi zai zama ga 'yan'uwansa.” 26Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan'ana kuwa ya bauta masa. 27Allah ya sa Yafet ya yawaita, ya sa ya zauna a alfarwan Shem, Kan'ana kuwa ya bauta masa.”

28Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin. 29Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.

10

Zuriyar 'Ya'yan Nuhu, Maza

(1 Tar 1.5-23)

1Waɗannan su ne zuriyar 'ya'yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu 'ya'ya. 2'Ya'yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras. 3'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma. 4'Ya'yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim. 5Daga waɗannan ne mazauna a bakin gāɓa suka yaɗu bisa ga ƙasashensu, kowanne da harshensa, bisa ga iyalansu da kabilansu.

6'Ya'yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana. 7'Ya'yan Kush kuma Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama kuwa Sheba da Dedan. 8Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya. 9Shi riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji, domin haka akan ce, “Shi kamar Lamirudu ne riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji.” 10Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke. 11Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala, 12da Resen wadda take tsakanin Nineba da Kala, wato, babban birni.

13Mizrayim shi ne mahaifin Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Neftuhawa, 14da Fatrusawa, da Kasluhawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.

15Kan'ana ya haifi Sidon ɗan farinsa, da Het, 16shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa, 17da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa, 18da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan'aniyawa suka yaɗu. 19Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha. 20Waɗannan su ne 'ya'yan Ham, bisa ga iyalansu, da harsunansu da ƙasashensu, da kabilansu.

21An kuma haifa wa Shem, wan Yafet, 'ya'ya, shi ne kakan 'ya'yan Eber duka. 22'Ya'yan Shem su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram. 23'Ya'yan Aram kuma Uz, da Hul, da Geter, da Meshek. 24Arfakshad ya haifi Shela, Shela ya haifi Eber. 25An haifa wa Eber 'ya'ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan. 26Yokatan ya haifi Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera, 27da Adoniram, da Uzal, da Dikla, 28da Ebal, da Abimayel, da Sheba, 29da Ofir, da Hawila da Yobab, dukan waɗannan 'ya'yan Yokatan ne. 30Yankin ƙasar da suka zauna shi ne ya milla tun daga Mesha, har zuwa wajen Sefar, ƙasar tudu ta gabas. 31Waɗannan su ne 'ya'yan Shem bisa ga iyalansu, da harsunansu, da ƙasashensu, da kabilansu.

32Waɗannan duka su ne zuriyar Nuhu, bisa ga lissafin asalinsu, bisa ga kabilansu. Daga waɗannan ne al'ummai suka yaɗu bisa duniya bayan Ruwan Tsufana.

11

Hasumiyar Babila

1A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. 2Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can. 3Sai suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka. 4Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.”

5Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina. 6Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su. 7Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.” 8Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin. 9Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.

Zuriyar Shem

(1 Tar 1.24-27)

10Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu. 11Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

12Sa'ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela. 13Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

14Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber, 15Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

16Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg, 17Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

18Sa'ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu. 19Feleg ya yi shekara metan da tara bayan haihuwar Reyu, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

20Sa'ad da Reyu ya yi shekara talatin da biyu ya haifi Serug. 21Reyu kuwa ya yi shekara metan da bakwai bayan haihuwar Serug, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

22Sa'ad da Serug ya yi shekara talatin ya haifi Nahor, 23Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

24Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera, 25Nahor kuwa ya yi shekara ɗari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

26Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.

27Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu.

28Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa. 29Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya. 30Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato, ba ta da ɗa.

31Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato, matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kaldiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can. 32Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.

12

Allah ya Kira Abram

1Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka. 2Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka. 3Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”

4Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran. 5Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan'uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran. Sa'ad da suka kai ƙasar Kan'ana, 6Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar. 7Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi. 8Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji. 9Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.

Abram a Masar

10A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar. 11Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce, 12lokacin da Masarawa suka gan ki za su ce, “‘Wannan matarsa ce,” za su kashe ni, amma za su bar ki da rai. 13Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin dalilinki kome sai ya tafi mini daidai a kuma bar ni da raina.” 14Sa'ad da Abram ya shiga Masar sai Masarawa suka ga matar kyakkyawa ce ƙwarai. 15Da fādawan Fir'auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir'auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir'auna. 16Saboda ita Fir'auna ya yi wa Abram alheri. Abram yana da tumaki, da takarkarai, da jakai maza, da barori mata da maza, da jakai mata, da raƙuma.

17Sai Ubangiji ya wahalar da Fir'auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya. 18Sai Fir'auna ya kirawo Abram, ya ce, “Mene ne wannan da ka yi mini? Don me ba ka faɗa mini ita matarka ce ba? 19Don me ka ce ita 'yar'uwarka ce, har na ɗauke ta ta zama matata? To, ga matarka, ka ɗauke ta ka tafi.” 20Fir'auna kuma ya umarci mutanensa a kan Abram, su raka shi da matarsa, da dukan abin da yake da shi.

13

Rabuwar Abram da Lutu

1Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu. 2Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya. 3Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai, 4a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.

5Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai, 6domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba. 7Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne.

8Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne. 9Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.” 10Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata. 11Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna. 12Abram ya zauna a ƙasar Kan'ana, Lutu kuwa ya zauna a biranen kwari, ya zakuɗar da alfarwarsa har zuwa Saduma. 13Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.

Abram ya yi Ƙaura zuwa Hebron

14Sai Ubangiji ya ce wa Abram, bayan da Lutu ya rabu da shi, “Ɗaga idanunka sama, daga inda kake, ka dubi kusurwoyin nan huɗu, 15gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada. 16Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka. 17Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan ba ka ita.” 18Sai Abram ya cire alfarwarsa, ya zo ya zauna kusa da itatuwan oak na Mamre, waɗanda suke Hebron. A can ya gina wa Ubangiji bagade.

14

Abram ya 'Yanto Lutu

1A zamanin Amrafel Sarkin Shinar, shi da Ariyok Sarkin Ellasar, da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim, 2suka fita suka yi yaƙi da Bera Sarkin Saduma, da Birsha Sarkin Gwamrata, da Shinab Sarkin Adma, da Shemeber Sarkin Zeboyim, da kuma Sarkin Bela, wato, Zowar. 3Waɗannan sarakuna biyar suka haɗa kai don su kai yaƙi, suka haɗa mayaƙansu a kwarin Siddim, inda Tekun Gishiri take. 4Shekara goma sha biyu suka bauta wa Kedarlayomer, amma suka tayar a shekara ta goma sha uku. 5A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim, 6da kuma Horiyawa cikin dutsen nan nasu, wato, Seyir, har zuwa Elfaran a bakin jeji. 7Sai suka juya suka je Enmishfat, wato, Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar. 8-9Sai Sarkin Saduma, da Sarkin Gwamrata, da Sarkin Adma da Sarkin Zeboyim, da Sarkin Bela, wato, Zowar, suka fita suka ja dāga da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim, da Amrafel Sarkin Shinar, da Ariyok Sarkin Ellasar a kwarin Siddim, sarakuna huɗu gāba da biyar. 10Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen. 11Sai abokan gāba suka kwashe dukan kayayyakin Saduma da na Gwamrata, da abincinsu duka, suka yi tafiyarsu. 12Suka kuma kama Lutu ɗan ɗan'uwan Abram, wanda yake zaune a Saduma, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.

13Sai wani da ya tsere, ya zo ya faɗa wa Abram Ba'ibrane wanda yake zaune wajen itatuwan oak na Mamre, Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, waɗanda suke abuta da Abram. 14Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan. 15Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu. 16Sai ya washe kayayyakin duka, ya kuma ƙwato ɗan'uwansa Lutu da kayayyakinsa da mata da maza.

Malkisadik ya Sa wa Abram Albarka

17Sai Sarkin Saduma ya fita ya taryi Abram sa'ad da ya komo daga korar Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi, a Kwarin Shawe, wato, Kwarin Sarki. 18Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato, Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki. 19Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, “Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka. 20Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.

21Sai Sarkin Saduma ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanen, amma ka riƙe kayayyakin don kanka.”

22Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa, 23cewa, ba zan ɗauki ko da zare ɗaya ko maɗaurin takalmi ba, ko kowane abin da yake naka, domin kada ka ce, “‘Na arzuta Abram.” 24A ni kaina ba zan ɗauki kome ba illa abin da samari suka ci, da rabon mutanen da suka tafi tare da ni. Sai dai kuma Aner, da Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu rabo.”

15

Alkawarin da yake tsakanin Allah da Abram

1Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”

2Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?” 3Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”

4Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.” 5Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.” 6Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.

7Ubangiji kuma ya ce masa, “Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ka daga Ur ta Kaldiyawa, don in ba ka wannan ƙasa ka gāje ta.”

8Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, yaya zan mallake ta?”

9Ya ce masa, “Kawo mini karsana bana uku, da burguma bana uku, da rago bana uku, da hazbiya da ɗan tattabara.” 10Ya kawo masa waɗannan abu duka, ya yanyanka su ya tsattsaga su a tsaka, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. 11Sa'ad da tsuntsaye masu cin nama suke sauka bisansu sai Abram ya kore su.

12Sa'ad da rana take faɗuwa, barci mai nauyi ya kwashe Abram, sai ga babban duhu mai bantsoro ya rufe shi. 13Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani lalle ne zuriyarka za ta yi baƙunci cikin ƙasar da ba tata ba ce, za ta kuwa yi bauta, za a kuma tsananta mata har shekara arbaminya, 14amma zan hukunta al'ummar da suka bauta wa, daga baya kuma da dukiya mai yawa za ta fita. 15Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka. 16A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”

17Sa'ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka. 18A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato, Kogin Yufiretis ke nan, 19ƙasar Keniyawa, da Kenizziyawa, da Kadmoniyawa, 20da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Refayawa, 21da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Girgashiyawa, da kuma Yebusiyawa.”

16

Hajaratu da Isma'ilu

1Saraya matar Abram ba ta taɓa haihuwa ba, amma tana da baranya Bamasariya, sunanta Hajaratu. 2Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya. 3A lokacin nan kuwa Abram yana da shekara goma da zama a ƙasar Kan'ana sa'ad da Saraya matar Abram ta ɗauki Hajaratu Bamasariya, baranyarta, ta bai wa Abram mijinta ta zama matarsa. 4Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine. 5Sai Saraya ta ce wa Abram, “Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara'anta tsakanina da kai.”

6Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.

7Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato, maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur. 8Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?” Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”

9Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.” 10Mala'ikan Ubangiji kuma ya ce mata, “Zan riɓaɓɓanya zuriyarki ainun har da ba za a iya lasafta su ba saboda yawansu.” 11Mala'ikan Ubangiji kuma ya ƙara ce mata, “Ga shi, kina da ciki, za ki haifi ɗa, za ki kira sunansa Isma'ilu, domin Ubangiji ya lura da wahalarki. 12Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka.”

13Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?” 14Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered.

15Hajaratu ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya sa wa ɗa da Hajaratu ta haifa suna, Isma'ilu. 16Abram yana da shekara tamanin da shida sa'ad da Hajaratu ta haifa masa Isma'ilu.

17

Kaciya ita ce Shaidar Alkawarin

1A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili. 2Zan yi maka alkawari, in ba ka zuriya mai yawa.” 3Sai Abram ya yi ruku'u, Allah kuwa ya ce masa, 4“Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa. 5Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa. 6Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.

7“Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka. 8Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato, dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”

9Allah kuma ya ce wa Ibrahim, “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, da kai da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu. 10Wannan shi ne alkawarina da za ka kiyaye, da kai da zuriyarka a bayanka. Sai a yi wa kowane ɗa namiji kaciya. 11Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku. 12Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba. 13Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan. 14Kowane ɗa namiji da bai yi kaciya ba, wato, wanda bai yi kaciyar loɓarsa ba, za a fitar da shi daga jama'arsa, don ya ta da alkawarina.”

15Allah ya ce wa Ibrahim, “Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta. 16Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta.”

17Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?” 18Sai Ibrahim ya ce wa Allah, “Da ma dai a bar Isma'ilu kawai ya rayu a gabanka.”

19Allah ya ce, “A'a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa. 20Ga zancen Isma'ilu kuwa, na ji, ga shi, zan sa masa albarka in kuma riɓaɓɓanya shi ainun. Zai zama mahaifin 'ya'yan sarakuna goma sha biyu, zan maishe shi al'umma mai girma. 21Amma ga Ishaku ne zan tsai da alkawarina, wato, wanda Saratu za ta haifa maka a baɗi war haka.” 22Sa'ad da Allah ya gama magana da Ibrahim, sai ya tafi ya bar Ibrahim.

23Ibrahim kuwa ya ɗauki Isma'ilu ɗansa, da dukan bayi, haifaffun gidansa, da waɗanda aka sayo su da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji na jama'ar gidansa kaciyar loɓarsa a wannan rana bisa ga faɗar Allah. 24Ibrahim na da shekara tasa'in da tara sa'ad da aka yi masa kaciyar loɓarsa. 25Isma'ilu ɗansa yana ɗan shekara goma sha uku sa'ad da aka yi masa kaciya. 26A wannan rana, Ibrahim da ɗansa Isma'ilu aka yi musu kaciya, 27da mazajen gidansa duka, da waɗanda suke haifaffun gidan da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙi, aka yi musu kaciya tare da shi.

18

An Alkawarta Haihuwar Ishaku

1Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana. 2Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku'u, 3ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima. 4Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace, 5ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da yake kun biyo ta wurin baranku.” Sai suka ce, “Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.”

6Ibrahim kuwa ya gaggauta zuwa cikin alfarwa wurin Saratu, ya ce, “Ki shirya mudu uku na gari mai laushi da sauri, ki cuɗa, ki yi waina.” 7Sai Ibrahim ya sheƙa zuwa garke, ya ɗauki maraƙi, matashi mai kyau, ya ba baransa, ya kuwa shirya shi nan da nan. 8Ya ɗauki kindirmo da madara, da maraƙin da ya shirya, ya ajiye a gabansu, ya tsaya kusa da su a gindin itacen a sa'ad da suke ci.

9Suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ya ce, “Tana cikin alfarwa.”

10Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne. 11Ga shi kuwa, Ibrahim da Saratu sun tsufa, sun kwana biyu, gama Saratu ta daina al'adar mata.

12Sai Saratu ta yi dariya a ranta, tana cewa, “Bayan na tsufa mai gidana kuma ya tsufa sa'an nan zan sami wannan gatanci?”

13Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya, har da ta ce, “‘Ashe zan haifi ɗa, a yanzu da na riga na tsufa?” 14Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”

15Amma Saratu ta yi mūsu, tana cewa, “Ai, ban yi dariya ba,” Gama tana jin tsoro. Ya ce, “A'a, hakika kin yi dariya.”

Ibrahim ya Yi Roƙo don Saduma

16Sai mutanen suka tashi daga wurin, suka fuskanci Saduma, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya ya sallame su. 17Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa? 18Ga shi kuwa, Ibrahim zai ƙasaita ya zama al'umma mai iko, sauran al'umman duniya duka za su sami albarka ta dalilinsa. 19Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa. 20Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai, 21zan sauka in gani ko sun aikata kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”

22Sa'an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji. 23Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun? 24Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba? 25Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato, da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”

26Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.”

27Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka. 28Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?” Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba'in da biyar a wurin.”

29Ya kuma sāke yin masa magana, ya ce, “Da a ce za a sami arba'in a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da arba'in ɗin ba zan yi ba.”

30Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan yi magana. Da a ce za a sami talatin a wurin fa?” Ya amsa, “Ba zan yi ba, in na sami talatin a wurin.”

31Ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji. Da a ce za a sami ashirin a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da ashirin ɗin ba zan hallaka shi ba.”

32Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan sāke yin magana, sau ɗayan nan kaɗai. Da a ce za a sami goma a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da goma ɗin ba zan hallaka shi ba.” 33Ubangiji kuwa ya yi tafiyarsa, bayan ya gama magana da Ibrahim. Ibrahim kuwa ya koma gida.

19

Zunubin Sadumawa ya Haɓaka

1Mala'ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa'ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku'u a gabansu, 2ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.” Suka ce, “A'a, a titi za mu kwana.” 3Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.

4Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan. 5Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.”

6Lutu ya fita daga cikin gida ya rufe ƙofar a bayansa ya je wurin mutane, 7ya ce, “Ina roƙonku 'yan'uwana, kada ku aikata mugunta haka. 8Ga shi, ina da 'ya'ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.”

9Amma suka ce, “Ba mu wuri!” Suka kuma ce, “Wannan mutum ya zo baƙunci ne, yanzu kuma zai zama alƙali! Yanzu za mu yi maka fiye da yadda za mu yi musu.” Sai suka tutture Lutu suka matsa kusa don su fasa ƙofar. 10Amma baƙin suka miƙa hannunsu, suka shigar da Lutu cikin gida inda suke, suka rufe ƙofa. 11Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.

Lutu ya Bar Saduma

12Mutanen suka ce wa Lutu, “Kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko 'ya'ya mata da maza, ko dai kome naka da yake cikin birnin? Fito da su daga wurin, 13gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.”

14Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.

15Sa'ad da safiya ta gabato, mala'ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da 'ya'yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.” 16Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na 'ya'yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin. 17Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”

18Sai Lutu ya ce musu, “A'a, ba haka ba ne iyayengijina, 19ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu. 20Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”

21Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. 22Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.

Halakar Saduma da Gwamrata

23Da hantsi Lutu ya isa Zowar. 24Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama, 25ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire. 26Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri.

27Da sassafe kuwa sai Ibrahim ya tafi wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji, 28ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar. 29Amma sa'ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.

Asalin Mowabawa da Ammonawa

30Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da 'ya'yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da 'ya'yansa biyu mata. 31Sai 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Mahaifinmu ya tsufa, ba wanda zai aure mu yadda aka saba yi ko'ina a duniya. 32Zo dai, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi, sa'an nan sai mu kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” 33Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi. Da daren nan kuwa 'yar farin ta shiga ta kwana da mahaifinta, shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta. 34Kashegari kuma, 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Ga shi, daren jiya na kwana da mahaifina, bari daren yau kuma, mu sa shi ya sha ruwan inabi, ke ma sai ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” 35Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta. 36Haka nan kuwa, 'ya'yan Lutu biyu ɗin nan suka sami ciki daga mahaifinsu. 37Ta farin, ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Mowab. Shi ne asalin Mowabawa har yau. 38Ƙaramar kuma ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Benammi, shi ne asalin Ammonawa har yau.

20

Ibrahim da Abimelek

1Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi zuwa wajen karkarar Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. A lokacin da Ibrahim yake baƙunci a Gerar, 2ya ce, matarsa Saratu 'yar'uwarsa ce. Sai Abimelek Sarkin Gerar ya aika, aka ɗauko masa Saratu. 3Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.”

4Abimelek bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ubangiji, za ka hallaka marar laifi? 5Ba shi ya faɗa mini, “‘Ita 'yar'uwata ce” ba? Ba ita kanta kuma ta ce, “‘Shi ɗan'uwana ne” ba? Cikin mutunci da kyakkyawan nufi na aikata wannan.”

6Allah ya ce masa cikin mafarki, “I, na sani ka yi wannan cikin mutunci, ai, ni na hana ka ka aikata zunubin, don haka ban yarda maka ka shafe ta ba. 7Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”

8Abimelek ya tashi da sassafe, ya kira barorinsa duka ya kuma faɗa musu waɗannan abubuwa duka. Mutanen kuwa suka ji tsoro ƙwarai. 9Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.” 10Abimelek kuma ya ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan abu?”

11Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata. 12Banda haka nan ma, hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina amma ba ta mahaifiyata ba ce. Na kuwa aure ta. 13A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawaceyawace, na ce mata, “‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.”

14Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu. 15Abimelek kuwa ya ce, “Ga shi, ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda ya yi maka daɗi.” 16Ga Saratu kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ɗan'uwanki azurfa guda dubu, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa, cewa, ba ki da laifi.”

17Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa. 18Gama dā Allah ya kulle mahaifar dukan gidan Abimelek saboda Saratu matar Ibrahim.

21

Haihuwar Ishaku

1Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta. 2Saratu kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Ibrahim ɗa cikin tsufansa a lokacin nan da Allah ya faɗa masa. 3Sai Ibrahim ya raɗa wa ɗansa wanda Saratu ta haifa masa, suna, Ishaku. 4Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi. 5Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa'ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku. 6Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, har dukan wanda ya ji zai yi dariya tare da ni.” 7Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa 'ya'ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.”

8Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.

Korar Hajaratu da Isma'ilu

9Amma Saratu ta ga ɗan Hajaratu Bamasariya wanda ta haifa wa Ibrahim yana wasa da ɗanta Ishaku. 10Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”

11Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa. 12Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka. 13Zan kuma yi al'umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.”

14Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba. 15Sa'ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. 16Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da 'yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.

17Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me ke damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake. 18Tashi, ki ɗauki yaron, ki rungume shi da hannunki gama zan maishe shi babbar al'umma.” 19Sai Allah ya buɗe idanunta, ta ga rijiyar ruwa, ta kuwa tafi, ta cika salkar da ruwa ta ba yaron ya sha. 20Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi. 21Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.

Ibrahim da Abimelek suka Ƙulla Yarjejeniya

22A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha'aninka duka, 23don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa, ba za ka ci amanata, ko ta 'ya'yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.”

24Sai Ibrahim ya amsa, “I, zan rantse.”

25Sa'ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace, 26Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan abu ba, ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba sai yau.” 27Ibrahim ya ɗibi tumaki da takarkarai ya bai wa Abimelek, su biyu ɗin kuwa suka yi alkawari. 28Ibrahim ya ware 'yan raguna bakwai daga cikin garke. 29Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Ina ma'anar waɗannan 'yan raguna bakwai da ka keɓe?”

30Ya ce, “Waɗannan 'yan raguna bakwai za ka karɓe su daga hannuna domin su zama shaida a gare ni, cewa, ni na haƙa rijiyan nan.” 31Don haka aka kira wannan wuri Biyer-sheba, domin a can ne su duka suka yi rantsuwa.

32Saboda haka suka yi alkawari a Biyer-sheba. Sai Abimelek, tare da Fikol shugaban sojojinsa, ya tashi ya koma ƙasar Filistiyawa. 33Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami. 34Ibrahim kuwa ya daɗe yana baƙunci a ƙasar Filistiyawa.

22

An Umarci Ibrahim ya yi Hadaya da Ishaku

1Bayan waɗannan al'amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!” Sai ya ce, “Ga ni.”

2Ya ce, “Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka.”

3Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa. 4A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa. 5Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa'an nan mu komo wurinku.”

6Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare. 7Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!” Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.” Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?”

8Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.

9Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden. 10Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa. 11Amma mala'ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai ya ce, “Ga ni.”

12Ya ce, “Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba.” 13Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa. 14Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, “Ubangiji zai tanada,” kamar yadda ake faɗa har yau, “A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada.”

15Mala'ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama, 16ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba, 17hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka, 18ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.” 19Sai Ibrahim ya koma wurin samarinsa. Suka tashi suka tafi Biyer-sheba tare. Ibrahim ya yi zamansa a Biyer-sheba.

Zuriyar Nahor

20Ana nan bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Ibrahim, “Ga shi, Milka ta haifa wa ɗan'uwanka Nahor, 'ya'ya. 21Uz ɗan fari, da Buz ɗan'uwansa, da Kemuwel mahaifin Aram, 22da Kesed, da Hazo, da Fildash, da Yidlaf, da Betuwel.” 23Betuwel kuwa ya haifi Rifkatu, su takwas ɗin nan Milka ta haifa wa Nahor, ɗan'uwan Ibrahim. 24Banda haka, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifi Teba, da Gaham, da Tahash, da Ma'aka.

23

Ibrahim ya Sayi Makabarta a Rasuwar Saratu

1Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya, 2sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato, Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.

3Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa, 4“Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”

5Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce, 6“Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”

7Ibrahim ya tashi ya sunkuya wa Hittiyawa, mutanen ƙasar. 8Sai ya ce musu, “Idan kun yarda in binne matata in daina ganinta, to, ku ji ni, ku roƙar mini Efron Bahitte ɗan Zohar, 9ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.”

10A sa'an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce, 11“Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama'ata na ba ka ita, ka binne matarka.”

12Ibrahim kuwa ya sunkuya a gaban jama'ar ƙasar. 13Ya ce wa Efron, a kunnuwan jama'ar ƙasar, “In dai ka yarda, ka ji ni. Zan ba da kuɗin saurar. Ka karɓa daga gare ni don in binne matata a can.”

14Efron ya amsa wa Ibrahim, 15“Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.” 16Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.

17Don haka saurar Efron da ke cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka 18an tabbatar wa Ibrahim, cewa, mallakarsa ce a gaban Hittiyawa, a gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsu. 19Bayan wannan, Ibrahim ya binne Saratu matarsa a kogon da yake a saurar Makfela a gabashin Mamre, wato, Hebron, cikin ƙasar Kan'ana. 20Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.

24

Aka Auro wa Ishaku Mata

1Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka. 2Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, 3ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa, ba za ka auro wa ɗana mata daga 'yan matan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba. 4Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”

5Sai baransa ya ce masa, “Watakila matar ba za ta yarda ta biyo ni zuwa wannan ƙasa ba, tilas ke nan, in koma da ɗanka ƙasar da ka fito?”

6Ibrahim ya ce masa, “Ka kiyaye wannan fa, kada ka kuskura ka koma da ɗana can. 7Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, “‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,” shi zai aiki mala'ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can. 8Amma idan matar ba ta yarda ta biyo ka ba, ka kuɓuta daga rantsuwan nan tawa. Kai dai kada ka koma da ɗana can.” 9Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar Ibrahim maigidansa, ya kuwa rantse masa zai yi.

10Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor. 11Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato, lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa. 12Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim. 13Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma 'yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa. 14Bari budurwar da zan ce wa, “‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,” wadda za ta ce, “‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,” bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”

15Kafin ya rufe baki, sai ga Rifkatu wadda aka haifa wa Betuwel ɗan Milka, matar Nahor ɗan'uwan Ibrahim, ta fito da tulun ruwanta a bisa kafaɗarta. 16Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro. 17Sai baran ya tarye ta a guje, ya ce, “Roƙo nake, ki ba ni ruwa kaɗan daga cikin tulunki in sha.”

18Ta ce, “Sha, ya shugabana.” Nan da nan ta sauke tulunta ta riƙe a hannunta, ta ba shi ya sha. 19Sa'ad da ta gama shayar da shi, ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka kuma, har su gama sha.” 20Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka. 21Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu>

22Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta, 23ya ce, “Ki faɗa mini ke 'yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”

24Sai ta ce masa, “Ni 'yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.” 25Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.”

26Mutumin ya yi ruku'u ya yi wa Ubangiji sujada, 27ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.”

28Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa. 29Rifkatu kuwa tana da ɗan'uwa sunansa Laban. Sai Laban ya sheƙo zuwa wurin mutumin a bakin rijiya. 30Sa'ad da ya ga zoben da mundaye da suke hannuwan 'yar'uwarsa, sa'ad da kuma ya ji maganar Rifkatu 'yar'uwarsa cewa, “Ga abin da mutumin ya faɗa mini,” sai ya je wurin. Ya kuwa same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. 31Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.” 32Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi. 33Aka sa abinci a gabansa domin ya ci, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Laban ya ce, “Faɗi maganarka.”

34Ya ce, “Ni baran Ibrahim ne. 35Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai. 36Saratu ta haifa wa maigidana ɗa cikin tsufanta, a gare shi kuma ya ba da dukan abin da yake da shi. 37Maigidana ya rantsar da ni da cewa, “‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin 'ya'yan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba, 38amma ka tafi gidan mahaifina da dangina, ka auro wa ɗana mace.” 39Sai na ce wa maigidana, “‘Watakila matar ba za ta biyo ni ba.” 40Amma ya amsa mini ya ce, “‘Ubangiji wanda nake tafiya a gabansa zai aiki mala'ikansa tare da kai, ya arzuta hanyarka, za ka kuwa auro wa ɗana mace daga cikin dangina daga gidan mahaifina. 41Sa'an nan za ka kuɓuta daga rantsuwata. Sa'ad da ka zo wurin dangina, idan kuwa ba su ba ka ita ba, za ka kuɓuta daga rantsuwata.”

42“Yau kuwa da na iso bakin rijiyar, sai na ce a raina, “‘Ya Ubangiji, Allah na shugabana Ibrahim, in nufinka ne ka arzuta tafiyata. 43Ga ni, ina tsaye a bakin rijiyar kuwa, bari budurwar da za ta fito ɗibar ruwa, wadda in na ce mata, “Roƙo nake, ba ni ruwa kaɗan daga ruwan tulunki in sha,” 44in ta amsa mini, “To, sha, zan ɗebo wa raƙumanka kuma,” bari ta zama ita ce wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.” 45Kafin in gama tunani a zuciyata, sai ga Rifkatu ta fito ɗauke da tulun ruwa a kafaɗarta, ta gangara zuwa rijiya ta ɗebo. Na ce mata, “‘Roƙo nake, ki ba ni, in sha.” 46Nan da nan ta sauke tulunta daga kafaɗarta, ta ce, “‘To, sha, zan kuma shayar da raƙumanka.” Na sha, ta kuma shayar da raƙuman. 47Na kuwa tambaye ta, “‘'Yar gidan wane ne ke?” Ta ce, “‘Ni 'yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.” Sai na sa mata zobe a hanci, mundaye kuma a hannu. 48Sa'an nan na yi ruku'u, na yi wa Ubangiji sujada, na yabi Ubangiji Allah na maigidana, Ibrahim, wanda ya bishe ni a hanya sosai, in auro wa ɗansa 'yar danginsa. 49Yanzu fa, idan za ku amince ku gaskata da maigidana, ku faɗa mini, in ba haka ba, sai ku faɗa mini, domin in san abin yi, in juya dama ko hagu.”

50Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al'amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a'a. 51Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.” 52Sa'ad da baran Ibrahim ya ji wannan, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada a gaban Ubangiji. 53Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan'uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada.

54Shi da mutanen da suke tare da shi suka ci suka sha, suka kwana wurin. Da suka tashi da safe, sai ya ce, “A sallame ni, in koma wurin maigidana.”

55Ɗan'uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Ka bar budurwar tare da mu har ɗan lokaci, kada ya gaza kwana goma, bayan wannan ta tafi.”

56Amma ya ce musu, “Kada ku makarar da ni, tun da yake Allah ya arzuta tafiyata, a sallame ni domin in koma wurin maigidana.”

57Suka ce, “Za mu kira budurwar mu tambaye ta.” 58Suka kirawo Rifkatu suka ce mata, “Za ki tafi tare da wannan mutum?” Sai ta ce, “Zan tafi.”

59Suka kuwa sallami Rifkatu 'yar'uwarsu da uwar goyonta, da baran Ibrahim da mutanensa. 60Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata, “'Yar'uwarmu, ki zama mahaifiyar dubbai, Har dubbai goma, Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofin maƙiyansu!”

61Sai Rifkatu da kuyanginta suka tashi suka hau raƙuman, suka bi mutumin. Haka nan kuwa baran ya ɗauki Rifkatu ya koma.

62A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb. 63A gabatowar maraice, sai Ishaku ya fita saura ya yi tunani, ya ɗaga idanunsa ya duba, ya ga raƙuma suna zuwa. 64Da Rifkatu ta ɗaga idanunta, ta hangi Ishaku, sai ta sauka daga raƙumi, 65ta ce wa baran, “Wane ne mutumin can da yake zuwa daga saura garin ya tarye mu?” Sai baran ya ce, “Ai, maigidana ne.” Ta ɗauki mayafinta ta yi lulluɓi. 66Sai baran ya faɗa wa Ishaku dukan abin da ya yi. 67Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta'azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.

25

Sauran Zuriyar Ibrahim

(1 Tar 1.32-33)

1Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura. 2Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 3Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. 'Ya'yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le'umomim. 4'Ya'yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka 'ya'yan Ketura ne.

5Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi. 6Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.

Rasuwar Ibrahim da Jana'izarsa

7Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba'in da biyar. 8Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi. 9Ishaku da Isma'ilu 'ya'yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre, 10wato, saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa. 11Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.

Zuriyar Isma'ilu

(1 Tar 1.28-31)

12Waɗannan su ne zuriyar Isma'ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim. 13Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma'ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam, 14da Mishma, da Duma, da Massa, 15da Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema. 16Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, bisa ga ƙauyukansu da zangonsu, hakimai goma sha biyu, bisa ga kabilansu. 17Waɗannan su ne shekarun Isma'ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi. 18Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.

Haihuwar Isuwa da Yakubu

19Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ya haifi Ishaku. 20Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye. 21Ishaku kuwa ya yi addu'a ga Ubangiji domin matarsa Rifkatu, da shike ita bakarariya ce. Ubangiji ya ji addu'arsa, sai matarsa Rifkatu ta yi ciki. 22'Ya'yan kuwa suka kama kokawa da juna a cikinta, har ta ce, “In haka ne don me zan rayu?” Sai ta je ta tambayi Ubangiji.

23Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”

24Sa'ad da kwanakin haihuwarta suka cika, sai ga shi, ashe, tagwaye ne suke a cikin mahaifarta. 25Na farin ya fito ja wur kamar riga mai gashi, saboda haka suka raɗa masa suna Isuwa. 26Daga baya kuma ɗan'uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa'ad da ya haife su.

Isuwa ya Sayar da Matsayinsa na Ɗan Fari

27Sa'ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida. 28Ishaku ya ƙaunaci Isuwa saboda yakan ci naman da ya farauto, amma Rifkatu ta ƙaunaci Yakubu.

29Wata rana, sa'ad da Yakubu yake dafa fate, Isuwa ya komo daga jeji, yana jin yunwa ƙwarai. 30Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom.

31Yakubu ya ce, “Sai dai ko in yau za ka sayar mini da matsayinka na ɗan fari.”

32Sai Isuwa ya ce, “Ni da nake bakin mutuwa, wane amfani matsayina na ɗan fari zai yi mini?”

33Yakubu ya ce, “Yau sai ka rantse mini.” Sai ya rantse masa ya kuwa sayar wa Yakubu da matsayinsa na ɗan fari. 34Sa'an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.

26

Ishaku a Gerar da Biyer-sheba

1Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa. 2Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar, ka zauna a ƙasar da zan faɗa maka. 3Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka. 4Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka, 5saboda Ibrahim ya yi biyayya da muryata, ya kuma kiyaye umarnina, da dokokina, da ka'idodina, da shari'una.”

6Ishaku ya yi zamansa a Gerar. 7Sa'ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita 'yar'uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce. 8Sa'ad da ya dakata 'yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu.

9Sai Abimelek ya kira Ishaku, ya ce, “Ashe lalle ita matarka ce, ƙaƙa fa ka ce, “‘Ita 'yar'uwata ce?” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”

10Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ai, da wani daga jama'a ya kwana da matarka a sawwaƙe, da ka jawo laifi a bisanmu.” 11Abimelek ya umarci dukan mutane ya ce, “Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa, za a kashe shi.”

12Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekarar nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka, 13har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. 14Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa. 15Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai.

16Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.” 17Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can. 18Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu.

19Amma sa'ad da barorin Ishaku suka haƙa rijiya a kwarin, sai suka tarar da idon ruwa. 20Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa, “Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta. 21Suka haƙa wata rijiya, suka yi jayayya a kan wannan kuma, ya sa mata suna Sitna. 22Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.”

23Daga nan ya haura zuwa Biyer-sheba. 24Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.” 25Ishaku ya gina bagade a wurin ya kira bisa sunan Ubangiji, a can kuwa ya kafa alfarwarsa. A can ne kuma barorin Ishaku suka haƙa rijiya.

Yarjejeniya tsakanin Ishaku da Abimelek

26Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku. 27Sai Ishaku ya ce musu, “Me ke tafe da ku zuwa gare ni, ga shi kun ƙi ni, kun kuma kore ni nesa da ku?”

28Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa, bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai, 29cewa, ba za ka cuce mu ba, daidai kamar yadda ba mu taɓe ka ba, ba mu yi maka kome ba sai alheri, muka kuwa sallame ka cikin salama. Yanzu, kai albarkatacce ne na Ubangiji.” 30Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha. 31Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama.

32Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.” 33Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba.

34Sa'ad da Isuwa yake da shekara arba'in, ya auro Judit, 'yar Biyeri Bahitte, da Basemat 'yar Elon Bahitte, 35suka baƙanta wa Ishaku da Rifkatu rai.

27

Yakubu ya Karɓi Albarka daga wurin Ishaku

1Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!” Sai ya amsa, “Ga ni nan.”

2Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba. 3Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama, 4ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”

5Rifkatu kuwa tana ji lokacin da Ishaku yake magana da ɗansa Isuwa. Don haka, sa'ad da Isuwa ya tafi jeji garin ya farauto nama ya kawo, 6sai Rifkatu ta ce wa ɗanta Yakubu, “Na ji mahaifinka ya yi magana da ɗan'uwanka Isuwa, ya ce, 7“‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.” 8Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka. 9Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so. 10Kai kuwa ka kai wa mahaifinka, ya ci, domin ya sa maka albarka kafin ya rasu.”

11Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan'uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne. 12Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la'ana maimakon albarka.”

13Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.” 14Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so. 15Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su, 16fatun 'yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi. 17Sai ta bai wa ɗanta, Yakubu, abinci mai daɗin ci da gurasar da ta shirya.

18Ya kuwa shiga wurin mahaifinsa, ya ce, “Baba.” Mahaifin ya ce, “Ga ni, wane ne kai, ya ɗana?”

19Yakubu ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini, in ka yarda ka tashi ka ci naman da na harbo, domin ka sa mini albarka.”

20Amma Ishaku ya ce wa ɗansa, “Ƙaƙa aka yi ka same shi da sauri haka, ɗana?” Sai ya amsa, “Domin Ubangiji, Allahnka, ya ba ni sa'a.”

21Ishaku kuwa ya ce wa Yakubu, “Matso kusa in ka yarda, don in lallaluba ka, ɗana, domin in hakikance ko kai ne ɗana Isuwa, ko babu.” 22Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.” 23Amma bai gane shi ba, gama hannuwansa gargasa ne kamar hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, saboda haka ya sa masa albarka. 24Ya ce, “Hakika, kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa, “Ni ne.”

25Ya ce, “Kawo mini naman da ka harbo, in ci in sa maka albarka.” Sai ya kawo masa, ya kuwa ci, ya kawo masa ruwan inabi, ya sha. 26Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.” 27Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce, “Duba, ƙanshin ɗana Yana kama da ƙanshin jeji Wanda Ubangiji ya sa wa albarka!

28Allah ya ba ka daga cikin raɓar sama, Daga cikin ni'imar ƙasa, Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.

29Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.”

30Ishaku yana gama sa wa Yakubu albarka, Yakubu yana fita daga gaban mahaifinsa ke nan sai ga Isuwa ɗan'uwansa ya komo daga farauta. 31Shi kuma ya shirya abinci mai daɗin ci, ya kawo wa mahaifinsa. Sai ya ce wa mahaifinsa, “In ka yarda baba, ka tashi, ka ci naman da na harbo don ka sa mini albarka.”

32Mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”

33Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka?ūI, albarkatacce zai zama.”

34Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi kūwwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.”

35Amma ya ce, “Ɗan'uwanka ya zo cikin makirci, ya karɓe albarkarka.”

36Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”

37Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”

38Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.

39Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisanci mazauninka, Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za ta nisance ka.

40Ta wurin takobinka za ka rayu Za ka yi wa ɗan'uwanka barantaka, Amma sa'ad da ka ɓalle, Za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”

41Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”

42Amma maganganun Isuwa babban ɗanta suka kai a kunnen Rifkatu. Saboda haka, sai ta aika aka kirawo Yakubu ƙaramin ɗanta. Ta ce masa, “Ga shi, ɗan'uwanka Isuwa, yana ta'azantar da kansa da nufin ya kashe ka, ya ɗau fansa. 43Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan'uwana a Haran, 44ka zauna tare da shi 'yan kwanaki, har zafin fushin ɗan'uwanka ya huce, 45ya manta da abin da ka yi masa, sa'an nan zan aika in komo da kai daga can. Don me zan rasa ku, ku biyu a rana ɗaya?”

Ishaku ya Aika da Yakubu wurin Laban

46Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato, daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”

28

1Ishaku ya kira Yakubu ya sa masa albarka, ya umarce shi da cewa, “Ba za ka auri ɗaya daga cikin 'ya'yan matan Kan'aniyawa ba. 2Tashi, ka tafi Fadan-aram, zuwa gidan Betuwel kakanka na wajen mahaifiya, ka zaɓo wa kanka mata daga cikin 'ya'ya mata na Laban ɗan'uwan mahaifiyarka a can. 3Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i, 4ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!” 5Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba'aramiye ɗan'uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.

Isuwa ya Ƙara Auro Wata

6Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka, ya kuwa sallame shi zuwa Fadan-aram domin ya auro mace daga can. Da Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka ya kuma umarce shi da cewa, “Ba za ka auro wata daga cikin 'yan matan Kan'aniyawa ba,” 7ya kuma ga Yakubu ya biye wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, har ya tafi Fadan-aram, 8sai Isuwa ya gane 'yan matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba. 9Saboda haka Isuwa ya tafi wurin Isma'ilu ya auro Mahalat 'yar'uwar Nebayot, 'yar Isma'ilu ɗan Ibrahim, banda matan da yake da su.

Mafarkin Yakubu a Betel

10Yakubu ya bar Biyer-sheba ya kama hanya zuwa Haran. 11Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci. 12Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa! 13Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka. 14Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka. 15Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasar nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”

16Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.” 17Ya tsorata, sai ya ce, “Wane irin wuri ne wannan mai banrazana haka! Ba shakka wannan wurin Allah ne, nan ne kuma ƙofar Sama.”

18Sai Yakubu ya tashi tun da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al'amudi, ya kuwa zuba mai a kan al'amudin. 19Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz. 20Yakubu ya yi wa'adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa, 21har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna, 22wannan dutse kuwa wanda na kafa shi al'amudi zai zama wurin sujada ga Allah. Daga cikin dukan abin da ya ba ni, zan ba shi ushirinsa.”

29

Yakubu ya Isa Gidan Laban

1Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya. 2Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba. 3A sa'ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa'an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.

4Yakubu ya ce musu, “'Yan'uwana, daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga Haran muke.”

5Sai ya ce musu, “Kun san Laban ɗan Nahor?” Suka ce, “Mun san shi.”

6Ya ce musu, “Lafiyarsa ƙalau?” Suka ce, “I, lafiya ƙalau yake, ga ma Rahila 'yarsa, tana zuwa da bisashensa!”

7Ya ce, “Ga shi kuwa, da sauran rana da yawa, lokacin tattaruwar dabbobi bai yi ba, me zai hana ku shayar da tumakin, ku sāke kai su wurin kiwo?”

8Amma suka ce, “Ba za mu iya ba, sai sauran garkunan duka sun taru, sa'an nan a kawar da dutsen daga bakin rijiyar, sa'an nan mu shayar da garkuna.”

9Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu. 10Sa'ad da Yakubu ya ga Rahila, 'yar Laban kawunsa, da bisashen, sai Yakubu ya hau ya kawar da dutsen daga bakin rijiyar, ya shayar da garken Laban, kawunsa. 11Yakubu kuwa ya sumbaci Rahila, ya fara kuka da ƙarfi. 12Ya faɗa mata shi dangin mahaifinta ne, shi kuma ɗan Rifkatu ne, sai ta sheƙa ta faɗa wa mahaifinta. 13Sa'ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al'amura duka. 14Laban ya ce masa, “Hakika, kai ƙashina ne da namana!” Yakubu ya zauna wata guda tara da Laban.

Yakubu ya yi wa Laban Barantaka domin Rahila da Lai'atu

15Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?” 16Laban dai yana da 'ya'ya mata biyu, sunan babbar Lai'atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila. 17Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.

18Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.”

19Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.” 20Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.

21Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.” 22Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki. 23Amma da maraice, ya ɗauki 'yarsa Lai'atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta. 24(Laban ya ba 'yarsa Lai'atu Zilfa ta zama kuyangarta). 25Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”

26Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin 'yar fari. 27Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa'an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.” 28Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa'an nan Laban ya aurar masa da 'yarsa Rahila. 29(Laban ya ba 'yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta). 30Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai'atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.

An Haifa wa Yakubu 'Ya'ya

31Sa'ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai'atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce. 32Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.” 33Ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Saboda Ubangiji ya ji ana ƙina ya ba ni wannan ɗa kuma,” ta kuwa raɗa masa suna Saminu. 34Sai kuma ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Yanzu, a wannan karo mijina zai shaƙu da ni, domin na haifa masa 'ya'ya uku maza.” Saboda haka ta raɗa masa suna Lawi. 35Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.

30

1Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”

2Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?”

3Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami 'ya'ya ta wurinta.” 4Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta. 5Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa. 6Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan. 7Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu. 8Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da 'yar'uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali.

9Sa'ad da Lai'atu ta ga ta daina haihuwa, sai ta ɗauki kuyangarta Zilfa, ta ba Yakubu ta zama matarsa. 10Kuyangar Lai'atu, Zilfa, ta haifa wa Yakubu ɗa. 11Lai'atu kuma ta ce, “Sa'a!” Saboda haka ta sa masa suna Gad. 12Kuyangar Lai'atu ta sāke haifa wa Yakubu ɗa na biyu. 13Lai'atu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Gama mata za su ce da ni mai farin ciki,” saboda haka ta raɗa masa suna Ashiru.

14A kwanakin kakar alkama, Ra'ubainu ya fita ya samo manta mahaifiya a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai'atu. Sai Rahila ta ce wa Lai'atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”

15Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?” Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”

16Sa'ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai'atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan. 17Allah ya saurari Lai'atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar. 18Lai'atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka. 19Lai'atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida. 20Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna. 21Daga baya ta haifi 'ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.

22Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta. 23Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,” 24ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”

Yakubu ya Yi Jinga da Laban

25Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu. 26Ka ba ni matana da 'ya'yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.”

27Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa, Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai. 28Ka faɗa mini ladanka in ba ka.”

29Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna. 30Gama kafin in zo, kana da 'yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?”

31Ya ce, “Me zan ba ka?” Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi, 32bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana. 33Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa'ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”

34Laban ya ce, “Madalla! Bari ya kasance kamar yadda ka faɗa.” 35Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun 'ya'yansa maza, 36ya sa nisan tafiya ta kwana uku tsakaninsu da Yakubu, Yakubu kuma ya ci gaba da kiwon sauran garken Laban.

37Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili. 38Ya kafa tsabgogin da ya ɓare a gaban garkuna a magudana, wato, kwamame na banruwa, don sukan yi barbara a wurin sa'ad da suka zo shan ruwa. 39Garkunan suka yi barbara a gaban tsabgogin, don haka garkunan sukan haifi masu zāne, dabbare-dabbare da masu sofane. 40Yakubu kuwa yakeɓe 'yan raguna, ya sa garkuna su fuskanci tsabgogin da ya shasshauta, da dukan baƙaƙen da ke cikin garken Laban. Sai ya ware waɗanda suke nasa, bai kuwa haɗa su da garken Laban ba. 41A kowane lokacin da ƙarfafan suke barbara Yakubu yakan sa tsabgogin a magudana a gaban idanun garken, domin su yi barbara a tsakanin tsabgogin. 42Amma ga marasa ƙarfi na garken, ba ya sa musu. Don haka marasa ƙarfin ne na Laban, ƙarfafan kuwa na Yakubu. 43Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙen mai arziki, yana da manya manyan garkuna da barori mata da maza, da raƙuma, da jakuna.

31

Yakubu ya Gudu daga wurin Laban

1Yakubu ya ji 'ya'yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.” 2Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā. 3Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.”

4Saboda haka Yakubu ya aika a kirawo Rahila da Lai'atu zuwa cikin saura inda garkensa yake, 5ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni. 6Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina, 7duk da haka mahaifinku ya cuce ni, ya yi ta sassauya ladana har sau goma, amma Allah bai ba shi ikon zambatata ba. 8In ya ce, “‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,” duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce “‘masu sofane ne ladanka,” sai garken duka ya haifi masu sofane. 9Ta haka Allah ya kwashe dukiyar mahaifinku ya ba ni.

10“A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garke, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne. 11Sai mala'ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, “‘Yakubu,” sai na ce, “‘Ga ni.” 12Ya kuwa ce, “‘Ta da idanunka ka gani, dukan bunsuran da ke hawan awaki masu sofane ne, dabbare-dabbare da roɗi-roɗi, gama na ga dukan abin da Laban yake yi maka. 13Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasar nan, ka koma ƙasar haihuwarka.”

14Rahila da Lai'atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu? 15Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu. 16Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da 'ya'yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.”

17Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki 'ya'yansa, da matansa a bisa raƙumansa, 18ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku. 19Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta. 20Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba'aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba. 21Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.

Laban ya Bi Sawun Yakubu

22Sa'ad da aka sanar da Laban, cewa, Yakubu ya gudu da kwana uku, 23sai ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi sawunsa har kwana bakwai, yana biye da shi kurkusa har zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai. 24Amma Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.” 25Sai Laban ya ci wa Yakubu. A yanzu Yakubu ya riga ya kafa alfarwarsa a ƙasa ta tuddai, Laban da danginsa kuma suka yi zango a ƙasar Gileyad ta tuddai.

26Laban ya ce wa Yakubu, “Me ka yi ke nan, da ka cuce ni, ka gudu da 'ya'yan matana kamar kwason yaƙi? 27Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya. 28Don me ba ka bari na sumbaci 'ya'yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta. 29Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, “‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.” 30Amma yanzu, ka gudu domin kana kewar gidan mahaifinka ƙwarai, amma don me ka sace mini gumakana?”

31Yakubu ya amsa wa Laban, ya ce, “Domin na ji tsoro ne gama na yi zaton za ka ƙwace 'ya'yanka mata ƙarfi da yaji. 32Ga duk wanda ka iske gumaka a wurinsa, a kashe shi. Yanzu a nan gaban danginmu, ka nuna abin da nake da shi wanda yake naka, ka ɗauka.” Ashe, Yakubu bai sani Rahila ce ta sace su ba.

33Laban ya shiga alfarwar Yakubu, da ta Lai'atu, da na kuyangin nan biyu, amma bai same su ba. Sai ya fita daga alfarwar Lai'atu, ya shiga ta Rahila. 34Ashe, Rahila ta kwashe gumakan ta zuba su cikin sirdin raƙumi, ta zauna a kansu. Laban ya wawaka alfarwar duka, amma bai same su ba. 35Sai ta ce wa mahaifinta, “Kada ubangijina ya yi fushi da ban iya tashi ba, don ina al'adar mata ne.” Ya kuwa bincike, amma bai sami gumakan ba.

36Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina? 37Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gidanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari'a tsakanina da kai. 38Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba. 39Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna. 40Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci. 41A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma. 42Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”

Yarjejeniya Tsakanin Yakubu da Laban

43Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa? 44Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”

45Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al'amudi. 46Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu,” sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin. 47Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.

48Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed. 49Laban kuma ya kira wurin Mizfa, gama ya ce, “Ubangiji ya kiyaye tsakanina da kai sa'ad da muka rabu da juna. 50Idan ka wulakanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda 'ya'yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.” 51Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al'amudi, wanda na kafa tsakanina da kai. 52Wannan tsibi, shaida ce, al'amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al'amudi zuwa wurina don cutarwa ba. 53Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara'anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku. 54Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen. 55Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da 'ya'yansa mata, ya sa musu albarka. Sa'an nan ya tashi ya koma gida.

32

Yakubu ya yi Shirin Saduwa da Isuwa

1Yakubu ya yi tafiyarsa, mala'ikun Allah kuma suka gamu da shi. 2Sa'ad da Yakubu ya gan su ya ce, “Waɗannan rundunar Allah ce!” Saboda haka ya sa wa wannan wuri suna Mahanayim.

3Yakubu kuwa ya aiki jakadu a gabansa zuwa wurin Isuwa ɗan'uwansa a cikin ƙasar Seyir a karkarar Edom, 4yana umartarsu da cewa, “Haka za ku faɗa wa shugabana Isuwa, “‘Ga abin da baranka Yakubu ya ce, “Na yi baƙunta a ƙasar Laban, na zauna har wa yau. 5Ina da takarkarai, da jakai, da garkuna, da barori mata da maza, na kuwa aika a faɗa wa shugabana domin in sami tagomashi a idonka.” ”

6Jakadun kuwa suka komo wurin Yakubu, suka ce, “Mun je wurin ɗan'uwanka Isuwa, yana kuwa zuwa ya tarye ka da mutum arbaminya tare da shi.”

7Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu, 8yana tunani cewa, “In Isuwa ya zo ya hallaka ƙungiya guda, ƙungiyar da ta ragu sai ta tsira.”

9Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, “‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,” 10ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu. 11Ka cece ni ina roƙonka daga hannun ɗan'uwana, wato, daga hannun Isuwa, gama ina jin tsoronsa, kada ya zo ya karkashe mu duka, 'ya'ya da iyaye. 12Gama ka riga ka ce, “‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.”

13Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan'uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi, 14awakai metan da bunsurai ashirin, tumaki metan da raguna ashirin, 15raƙuman tatsa talatin tare da 'yan taguwoyi, shanu arba'in da bijimai goma, jakai mata ashirin da jakai maza goma. 16Waɗannan ya sa su a hannun barorinsa ƙungiya ƙungiya, ya ce wa barorinsa, “Ku yi gaba, ku ba da rata tsakanin ƙungiya da ƙungiya.” 17Ya umarci na kan gaba, ya ce, “Sa'ad da Isuwa ɗan'uwana ya gamu da ku, ya tambaye ku cewa, “‘Ku mutanen wane ne? Ina za ku? Waɗannan da suke gabanku na wane ne?” 18Sa'an nan sai ku ce, “‘Na Yakubu baranka ne, kyauta ce zuwa ga shugabana Isuwa, ga shi nan ma biye da mu.” 19Da haka nan ya umarci na biyu da na uku da dukan waɗanda suke korar garkunan, ya ce, “Sai ku faɗa wa Isuwa daidai haka nan. 20Ku kuma ce, “‘Ga shi ma, Yakubu ɗan'uwanka yana biye da mu.” Gama, cikin tunaninsa ya ce, “Ya yiwu in gamshe shi da kyautar da ta riga ni gaba, daga baya in ga fuskarsa, watakila ya karɓe ni.” 21Saboda haka kyautar ta yi gaba, shi kansa kuwa a daren, ya sauka a zango.

Yakubu ya Yi Kokawa a Feniyel

22A wannan dare kuwa ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da kuyanginsa biyu da 'ya'yansa goma sha ɗaya ya haye mashigin Jabbok. 23Ya ɗauke su ya haye da su rafi, haka kuma ya yi da dukan abin da yake da shi. 24Aka bar Yakubu shi kaɗai. Sai wani mutum ya kama shi da kokawa har wayewar gari. 25Sa'ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi. 26Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.” Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”

27Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Yakubu.”

28Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”

29Sa'an nan Yakubu ya tambaye shi, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.” Amma ya ce, “Don me kake tambayar sunana?” A nan mutumin ya sa masa albarka.

30Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.” 31Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa. 32Saboda haka, har wa yau, Isra'ilawa ba sā cin jijiyar kwatangwalo wadda take a kwarin kwatangwalo, domin an taɓi kwarin kwatangwalon Yakubu ta jijiyar kwatangwalo.

33

Yakubu ya Sadu da Isuwa

1Yakubu ya ɗaga ido ya duba ke nan, sai ga Isuwa na zuwa da mutum arbaminya tare da shi. Sai ya raba wa Lai'atu da Rahila 'ya'yan, tare da kuyangin nan biyu. 2Ya sa kuyangin da 'ya'yansu a gaba, sa'an nan Lai'atu sa'an nan Rahila da Yusufu a ƙarshen duka. 3Shi kansa ya wuce gabansu, ya yi ta sunkuyar da kansa ƙasa sau bakwai, har sa'ad da ya kai kusa da ɗan'uwansa. 4Amma Isuwa ya sheƙa ya tarye shi, ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa, ya sumbace shi, suka kuwa yi kuka. 5Sa'ad da Isuwa ya ta da idonsa ya ga mata da 'ya'ya, ya ce, “Suwane ne waɗannan tare da kai?” Yakubu ya ce, “Su ne 'ya'ya waɗanda Allah cikin alherinsa ya ba baranka.” 6Sai kuyangin suka matso kusa, su da 'ya'yansu, suka sunkuya ƙasa. 7Haka nan kuma Lai'atu da 'ya'yanta suka matso, suka sunkuya ƙasa, a ƙarewa Yusufu da Rahila suka matso kusa, su kuma suka sunkuya ƙasa.

8Isuwa kuwa ya ce, “Ina manufarka da duk waɗannan ƙungiyoyi da na gamu da su?” Yakubu ya amsa, ya ce, “Ina neman tagomashi ne a idon shugabana.”

9Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”

10Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni. 11Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.

12Sa'an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.”

13Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani 'ya'yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka. 14Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.”

15Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.” Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.” 16A ran nan Isuwa ya koma a kan hanyarsa zuwa Seyir. 17Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot.

18Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin. 19Ya kuma sayi yankin saura inda ya kafa alfarwarsa daga 'ya'yan Hamor, mahaifin Shekem, a bakin azurfa ɗari. 20A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.

34

An Yi wa Dinatu Faɗe

1Yanzu fa Dinatu 'yar Lai'atu, wadda ta haifa wa Yakubu, ta fita ta ziyarci waɗansu matan ƙasar, 2sai Shekem, ɗan Hamor Bahiwiye, yariman ƙasar, da ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta. 3Ransa kuwa ya zaƙu da son Dinatu 'yar Yakubu. Ya ƙaunaci budurwar, ya kalallame ta da maganganu masu daɗi. 4Sai Shekem ya yi magana da mahaifinsa, Hamor, ya ce, “Ka auro mini wannan budurwa ta zama matata.”

5Yakubu kuwa ya ji an ɓata 'yarsa, Dinatu, amma 'ya'yansa maza suna tare da garken cikin saura, saboda haka Yakubu ya yi shiru har kafin su komo. 6Sai Hamor mahaifin Shekem ya fita ya je wurin Yakubu, ya yi magana da shi. 7'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi kwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba. 8Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen 'yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure. 9Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu 'yan matanku, ku kuma ku auri 'yan matanmu. 10Sai ku zauna tare da mu, ƙasar kuma tana gabanku. Ku zauna a cikinta ku yi sana'a, ku sami dukiya.”

11Shekem kuma ya ce wa mahaifin Dinatu da 'yan'uwanta, “Bari in sami tagomashi a idanunku, dukan abin da kuka ce kuwa, sai in yi. 12Ku fada mini ko nawa ne dukiyar auren da sadakin, zan kuwa bayar bisa ga yadda kuka faɗa mini, in dai kawai ku ba ni budurwar ta zama matata.”

13'Ya'yan Yakubu, maza, suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor a ha'ince, domin ya ɓata 'yar'uwarsu Dinatu. 14Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da 'yar'uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu. 15Ta wannan hali ne kaɗai za mu yarda, wato, idan za ku zama kamarmu, ku yi wa dukan mazajenku kaciya. 16Sa'an nan za mu ba ku auren 'ya'yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu 'ya'yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya. 17Amma idan ba ku saurare mu kun yi kaciya ba, sai mu ɗauki 'yarmu, mu kama hanyarmu.”

18Hamor da ɗansa Shekem suka yi na'am da sharuɗan. 19Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin 'yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan.

20Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce, 21“Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri 'ya'yansu mata, mu kuma mu aurar musu da 'ya'yanmu mata. 22Ga sharaɗin da mutanen za su yarda su zauna tare da mu, mu zama jama'a ɗaya, wato, kowane namiji a cikinmu ya yi kaciya kamar yadda su suke da kaciya. 23Da shanunsu, da dukiyarsu da dukan dabbobinsu, ashe, ba za su zama namu ba? Bari dai kurum mu yarda da su, su zauna tare da mu.” 24Duk jama'ar birnin suka yarda da maganar Hamor da ɗansa Shekem. Aka kuwa yi wa kowane namiji kaciya.

25A rana ta uku, sa'ad da jikunansu suka yi tsami, biyu daga cikin 'ya'yan Yakubu, Saminu da Lawi, 'yan'uwan Dinatu, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka karkashe mazajen duka. 26Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dinatu daga gidan Shekem suka yi tafiyarsu. 27'Ya'yan Yakubu kuwa suka tarar da kisassun, suka washe birnin, saboda sun ɓata 'yar'uwarsu. 28Suka kwashe garkunan awaki da tumaki, da garkunan shanu da jakunansu da dukan abin da yake cikin birnin da na cikin saura, 29dukan dukiyarsu, da 'yan ƙananansu, da matansu, wato, dukan abin da yake cikin gidajen, suka kwashe.

30Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan'aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.”

31Amma 'ya'yansa suka ce, “Zai mai da ƙanwarmu kamar karuwa?”

35

Allah ya Sa wa Yakubu Albarka a Betel

1Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa'ad da kake guje wa ɗan'uwanka Isuwa.”

2Sai Yakubu ya ce wa iyalin gidansa da dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku kawar da gumakan da suke wurinku, ku tsarkake kanku, ku sāke rigunanku, 3sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.” 4Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda yake kusa da Shekem.

5Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin 'ya'yan Yakubu. 6Sai Yakubu ya zo Luz, wato, Betel, wadda take cikin Kan'ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi. 7A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa'ad da yake guje wa ɗan'uwansa. 8Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.

9Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka. 10Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra'ila.” Don haka aka kira sunansa Isra'ila. 11Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka. 12Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.” 13Sa'an nan Allah ya tashi Sama ya bar shi a wurin da ya yi masa magana. 14Sai Yakubu ya kafa al'amudin dutse a inda Allah ya yi masa magana, ya zuba masa sadaka ta sha, ya kuma zuba mai a bisansa. 15Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.

Rasuwar Rahila

16Da suka tashi daga Betel, tun suna da 'yar rata da Efrata, sai lokaci ya yi da Rahila za ta haihu, amma ta sha wahala kafin ta haihu. 17Sa'ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.” 18Da tana suma, sai ta sa masa suna Ben-oni, amma mahaifinsa ya sa masa suna Biliyaminu.

19Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato, Baitalami. 20Yakubu ya kafa al'amudi bisa kabarinta, al'amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau. 21Isra'ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.

'Ya'yan Yakubu Maza

(1 Tar 2.1-2)

22A lokacin da Isra'ila ke zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari. 'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne. 23'Ya'yan Lai'atu, su ne Ra'ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna. 24'Ya'yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu. 25'Ya'yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali. 26'Ya'yan Zilfa, kuyangar Lai'atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne 'ya'yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.

Rasuwar Ishaku

27Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato, Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci. 28Yanzu kuwa kwanakin Ishaku shekara ce ɗari da tamanin. 29Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, 'ya'yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.

36

Zuriyar Isuwa

(1 Tar 1.34-36)

1Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, wato, Edom. 2Isuwa ya auri matansa daga cikin Kan'aniyawa, wato, Ada 'yar Elon Bahitte, da Oholibama 'yar Ana ɗan Zibeyon Bahiwiye, 3da Basemat, 'yar Isma'ilu, 'yar'uwar Nebayot. 4Ada ta haifa wa Isuwa, Elifaz, Basemat kuma ta haifi Reyuwel. 5Oholibama ta haifi Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa waɗanda aka haifa masa a ƙasar Kan'ana.

6Isuwa ya kwashi matansa, da 'ya'yansa mata da maza, da dukan jama'ar gidansa, da shanunsa, da dabbobinsa duka, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan'ana, ya kuwa tafi wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu. 7Gama abin mallakarsu ya yi yawa har ba zai yiwu su zama tare ba, ƙasar baƙuntarsu kuwa ba ta wadace su ba saboda yawan dabbobinsu. 8Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom.

9Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, kakan Edomawa, a ƙasar Seyir ta tuddai. 10Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isuwa, maza, wato, Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa. 11'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz. 12Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa.

13Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.

14Waɗannan su ne 'ya'yan Oholibama matar Isuwa 'yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora.

15Waɗannan su ne shugabanni na zuriyar Isuwa. Ga 'ya'yan Elifaz, maza, ɗan farin Isuwa, shugaba Teman, da Omar, da Zeho, da Kenaz, 16da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'yan Ada.

17Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.

18Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, 'yar Ana ta haifa. 19Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa, maza, wato, Edom, da shugabanninsu.

Zuriyar Seyir

(1 Tar 1.38-42)

20Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, 21da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, 'ya'yan Seyir, maza, a ƙasar Edom. 22'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, 'yar'uwarsa Timna ce. 23Waɗannan su ne 'ya'yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam. 24Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon. 25Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana. 26Waɗannan su ne 'ya'yan Dishon, maza, Hemdan da Eshban, da Yitran, da Keran. 27Waɗannan su ne 'ya'yan Ezer, maza, Bilha, da Zayawan, da Akan. 28Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran. 29Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, 30da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.

Sarakunan Edom

(1 Tar 1.43-54)

31Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra'ilawa. 32Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba. 33Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa. 34Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa. 35Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne. 36Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa. 37Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa. 38Da Shawul ya rasu, sai Ba'al-hanan ɗan Akbor ya ci sarauta a bayansa. 39Da Ba'al-hanan ɗan Akbor ya rasu, sai Hadad ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetebel 'yar Matred, 'yar Mezahab.

40Waɗannan su ne sunayen sarakunan Isuwa bisa ga dangoginsu da bisa ga wurin zamansu. Ga sunayensu, sarki Timna, da Alwa, da Yetet, 41da Oholibama, da Ila, da Finon, 42da Kenaz, da Teman, da Mibzar, 43da Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne sarakunan Edom, (wato, Isuwa ne kakan Edomawa) bisa ga wuraren zamansu a ƙasar mallakarsu.

37

1Yakubu ya zauna a ƙasar Kan'ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci. 2Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.

Yusufu da 'Yan'uwansa Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa,

3Isra'ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da ko wannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado. 4Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.

5Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. 6Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi. 7Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”

8'Yan'uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.

9Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”

10Amma sa'ad da ya faɗa wa mahaifinsa da 'yan'uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da 'yan'uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?” 11'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.

An Sayar da Yusufu zuwa Masar

12Wata rana, da 'yan'uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem, 13Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba 'yan'uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.” Sai ya ce masa, “Ga ni.”

14Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar 'yan'uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron. Da Yusufu ya isa Shekem, 15wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”

16Yusufu ya ce, “Ina neman 'yan'uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”

17Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, “‘Bari mu tafi Dotan.” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun 'yan'uwansa, ya kuwa same su a Dotan.

18Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi. 19Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa. 20Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa'an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa'an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”

21Amma sa'ad da Ra'ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa. 22Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyar nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu. 23Don haka, sa'ad da Yusufu ya zo wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa. 24Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki.

25Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma'ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar. 26Yahuza ya ce wa 'yan'uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan'uwanmu, muka ɓoye jininsa? 27Ku zo mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan'uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” 'Yan'uwansa suka yarda da shi. 28Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.

29Sa'ad da Ra'ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa, 30ya koma wurin 'yan'uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”

31Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin. 32Suka kuma ɗauki rigan nan mai ado, suka kawo ta ga mahaifinsu, suka ce, “Ga abar da muka samu, duba ka gani, ta ɗanka ce, ko kuwa?”

33Da ya gane ita ce, ya ce, “Rigar ɗana ce, wani mugun naman jeji ne ya cinye shi, ba shakka an yayyage Yusufu.” 34Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa. 35Dukan 'ya'yansa mata da maza suka tashi domin su ta'azantar da shi, amma ya ƙi ta'azantuwa, yana cewa, “A'a, a Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Haka mahaifinsu ya yi kuka dominsa. 36A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir'auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir'auna.

38

Yahuza da Tamar

1Ya zama fa a wannan lokaci, Yahuza ya bar 'yan'uwansa ya gangara, ya zauna wurin wani Ba'adullame mai suna Hira. 2A can, sai Yahuza ya ga 'yar wani Bakan'ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta, 3ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, ya kuwa raɗa masa suna Er. 4Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan. 5Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.

6Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar. 7Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi. 8Sa'an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan'uwanka, ka yi mata wajibin ɗan'uwan miji, ka samar wa ɗan'uwanka zuriya.” 9Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan'uwansa zuriya. 10Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi. 11Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar 'yan'uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.

12A kwana a tashi, ga matar Yahuza, 'yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta'aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba'adullame. 13Sa'ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,” 14sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.

15Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta. 16Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce. Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?”

17Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.” Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”

18Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?” Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki. 19Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba.

20Sa'ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba'adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba. 21Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?” Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.”

22Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, “‘Ba wata karuwa da ta zo nan.”

23Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.”

24Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.” Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”

25Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”

26Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.

27Sa'ad da lokaci ya yi da za ta haihu, ashe, cikin tagwaye ne. 28Da tana cikin naƙuda, sai hannun wani ya fara fitowa, ungozoma kuwa ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, tana cewa, “Wannan shi ya fara fitowa.” 29Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan'uwansa ya fito, sai ta ce, “A'a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa. 30Daga baya ɗan'uwansa ya fito da jan zare a hannunsa, aka kuwa sa masa suna Zera.

39

Yusufu da Matar Fotifar

1Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir'auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma'ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can. 2Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren. 3Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka. 4Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi. 5Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji. 6Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci. Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani. 7Ya zamana fa, wata rana, sai matar maigidansa ta sa idonta kan Yusufu, ta ce, “Ka kwana da ni.” 8Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna. 9Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?” 10Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.

11Amma wata rana, sa'ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan, 12sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita. 13Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje, 14sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba'ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi. 15Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.”

16Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo. 17Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba'ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina, 18amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”

19Sa'ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata. 20Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda 'yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku. 21Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun. 22Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan 'yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi. 23Yarin kurkukun, ba ruwansa da dukan abin da Yusufu yake kula da shi, domin Ubangiji yana tare da shi, dukan abin da ya yi kuwa Ubangiji yakan sa wa abin albarka.

40

Yusufu ya Fassara Mafarkan 'Yan Kurkuku

1Bayan waɗannan al'amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi. 2Fir'auna ya yi fushi da ma'aikatan nan nasa biyu, wato, shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya. 3Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato, kurkuku inda Yusufu yake a tsare. 4Shugaban 'yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.

5Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin. 6Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu. 7Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”

8Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.” Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”

9Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana. 10A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi. 11Finjalin Fir'auna na hannuna, sai na ɗauki 'ya'yan inabi na matse su cikin finjalin Fir'auna, na sa finjalin a hannun Fir'auna.”

12Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne, 13bayan kwana uku Fir'auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir'auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa. 14Amma ka tuna da ni sa'ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir'auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida. 15Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”

16Sa'ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina. 17A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir'auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato, wanda yake bisa kaina ɗin.”

18Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne, 19bayan kwana uku Fir'auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”

20A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa. 21Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna, 22amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu. 23Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.

41

Yusufu ya Fassara wa Fir'auna Mafarkansa

1Bayan shekaru biyu cif, Fir'auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu, 2sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa. 3Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu. 4Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir'auna ya farka. 5Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara guda. 6Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar. 7Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir'auna ya farka, ashe, mafarki ne. 8Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.

9Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir'auna, “Yau, na tuna da laifofina. 10Sa'ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, 11muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin. 12Akwai wani Ba'ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa'ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa ko wannenmu fassara bisa kan mafarkinsa. 13Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.”

14Sai Fir'auna ya aika a kirawo Yusufu, da gaggawa suka fito da shi daga cikin kurkuku. Da Yusufu ya yi aski, ya sāke tufafinsa ya zo gaban Fir'auna. 15Fir'auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”

16Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.”

17Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu, 18ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa. 19Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu. 20Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko, 21amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka. 22Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda, 23zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu. 24Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.”

25Yusufu ya ce wa Fir'auna, “Mafarkin Fir'auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa. 26Waɗannan shanu bakwai, shekaru bakwai ne, kyawawan zangarkun nan bakwai kuma shekaru bakwai ne, mafarkin ɗaya ne. 27Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa. 28Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir'auna, Allah ya nuna wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa. 29Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka, 30amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar. 31Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar. 32Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa, Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.

33“Yanzu fa bari Fir'auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar. 34Bari Fir'auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi. 35Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir'auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi. 36Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”

An Naɗa Yusufu Mai Mulki a Masar

37Fir'auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara. 38Sai Fir'auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?” 39Domin haka Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka, 40za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama'ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.” 41Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.” 42Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya, 43ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar. 44Har yanzu dai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir'auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.” 45Fir'auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat 'yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.

46Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar. 47A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske, 48sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi. 49Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.

50Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu 'ya'ya biyu maza, waɗanda Asenat 'yar Fotifera, firist na On ta haifa masa. 51Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.” 52Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”

53Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika, 54aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci. 55Sa'ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir'auna kuka domin abinci, sai Fir'auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.” 56Domin haka sa'ad da yunwar ta bazu ko'ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar. 57Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.

42

'Yan'uwan Yusufu sun Zo Masar Sayen Abinci

1A sa'ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa 'ya'yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido? 2Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.” 3Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar. 4Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan'uwan Yusufu tare da 'yan'uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”

5Haka nan 'ya'yan Isra'ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan'ana. 6Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama'ar ƙasar duka. 'Yan'uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 7Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.”

8Yusufu kuwa ya gane da 'yan'uwansa amma su ba su gane shi ba. 9Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”

10Suka ce masa, “A'a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo. 11Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”

12Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”

13Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”

14Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku. 15Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir'auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan. 16Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan'uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir'auna, lalle ku magewaya ne.” 17Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku.

18A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah, 19sai ku bar ɗan'uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata, 20sa'an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi.

21Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”

22Sai Ra'ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.” 23Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu. 24Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.

'Yan'uwan Yusufu suka Komo Kan'ana

25Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu. 26Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi. 27Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa. 28Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!” Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”

29Sa'ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan'ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa, 30“Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa. 31Amma muka ce masa, “‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne. 32Mu sha biyu ne 'yan'uwan juna, 'ya'ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan'ana.”

33“Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, “‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan'uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku. 34Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan'uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.”

35Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin ko wannensu a cikin taikinsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana. 36Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”

37Ra'ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe 'ya'yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”

38Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”

43

'Yan'uwan Yusufu sun Sāke Komawa Masar da Biliyaminu

1A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar. 2Sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”

3Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, “‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.” 4In za ka yarda ka aiki ɗan'uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci. 5Amma idan ba haka ba, ba za mu tafi ba, gama mutumin ya ce mana, “‘Ba za ku ga fuskata ba idan ba ku zo tare da ɗan'uwanku ba.”

6Sai Isra'ila ya ce, “Don me kuka cuce ni, da kuka faɗa wa mutumin nan, kuna da wani ɗan'uwa?”

7Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, “‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan'uwa?” Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, “‘Ku zo da ɗan'uwanku?”

8Sai Yahuza ya ce wa Isra'ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu. 9Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada, 10gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”

11Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure. 12Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi. 13Ku kuma ɗauki ɗan'uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin. 14Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”

15Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu. 16Sa'ad da Yusufu ya ga Biliyaminu tare da su, ya faɗa wa mai hidimar gidansa, ya ce, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.” 17Mutumin kuwa ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa, ya shigo da mutanen a gidan Yusufu.

18Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.” 19Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida, 20suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci, 21amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin ko wannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su, 22ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”

23Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.

24Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna, 25sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan. 26Sa'ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa. 27Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”

28Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya'a.

29Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan'uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri, ɗana!” 30Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan'uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka. 31Sa'an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci. 32Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa. 33Aka zaunar da 'yan'uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. 'Yan'uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki. 34Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na ko wannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

44

Finjalin Yusufu a Taikin Biliyaminu

1Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa, 2ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa. 3Gari na wayewa aka sallami mutanen da jakunansu. 4Tun ba su riga suka yi nisa da garin ba, Yusufu ya ce wa mai hidimar gidansa, “Tashi, ka bi mutanen, in ka iske su ka ce musu, 5“‘Don me kuka rama alheri da mugunta? Don me kuka sace mini finjalina na azurfa? Da shi ne maigidana ke sha, da shi ne kuma yake yin istihara. Kun yi kuskure da kuka yi haka.”

6Lokacin da ya iske su sai ya yi musu waɗannan maganganu. 7Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan! 8Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan'ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka? 9Daga cikinmu barorinka, duk wanda aka sami abin a wurinsa, bari ya mutu, mu kuwa mu zama bayinka, ranka ya daɗe.” 10Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.” 11Nan da nan kowa ya saukar da taikinsa ƙasa, kowa kuwa ya buɗe taikinsa. 12Ya bincika, ya fara daga babba zuwa ƙarami, sai aka iske finjalin a cikin taikin Biliyaminu. 13Suka kyakkece rigunansu, ko wannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin.

14Sa'ad da Yahuza da 'yan'uwansa suka zo gidan Yusufu, suka iske yana nan har yanzu, sai suka fāɗi ƙasa a gabansa. 15Yusufu ya ce musu, “Wane abu ke nan kuka aikata? Ba ku sani ba, mutum kamata yakan yi istihara?”

16Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”

17Amma Yusufu ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da in yi haka! Sai shi wanda aka sami finjalin a hannunsa, shi zai zama bawana, amma ku, ku yi tafiyarku lafiya zuwa wurin mahaifinku.” 44.18 Yahuza ya yi Gūdū domin Biliyaminu Yahuza ya yi Gūdū domin Biliyaminu.

18Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir'auna kake. 19Ranka ya daɗe, ka tambaye mu, ka ce, “‘Kuna da mahaifi ko ɗan'uwa?” 20Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, “‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.” 21Sai ka ce wa barorinka, “‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.” 22Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, “‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.” 23Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, “‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.”

24“Sa'ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce. 25Don haka sa'ad da mahaifinmu ya ce, “‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,” 26sai muka ce, “‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.” 27Sa'an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, “‘Kun sani 'ya'ya biyu matata ta haifa mini, 28ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba. 29In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.” 30-31“Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. 32Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, “‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina dukan raina.” 33Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da 'yan'uwansa. 34Gama yaya zan iya komawa wurin mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? Ina jin tsoron ganin ɓarnar da za ta auko wa mahaifina.”

45

Yusufu ya Bayyana Kansa ga 'Yan'uwansa

1Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa'ad da Yusufu ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa. 2Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir'auna. 3Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma 'yan'uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa. 4Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan'uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar. 5Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai. 6Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. 7Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa. 8Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir'auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.

9“Ku gaggauta, ku hau zuwa wurin mahaifina ku ce masa, “‘Ga abin da Yusufu ɗanka ya ce, “Allah ya maishe ni shugaban Masar duka, ka gangaro wurina kada ka yi wata wata. 10Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da 'ya'yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi. 11A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.” ” 12Yanzu, da idanunku kun gani, idanun ɗan'uwana Biliyaminu kuma sun gani, cewa, bakina ne yake magana da ku. 13Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.”

14Sai Yusufu ya rungumi ɗan'uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu. 15Ya sumbaci 'yan'uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai 'yan'uwansa suka yi taɗi da shi.

16Sa'ad da labari ya kai gidan Fir'auna cewa, “'Yan'uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir'auna da fādawansa daɗi ƙwarai.

17Sai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa 'yan'uwanka su yi wannan, “‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan'ana. 18Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.” 19Ka kuma umarce su ka ce, “‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo. 20Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.”

21Haka kuwa 'ya'yan Isra'ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir'auna, ya ba su guzuri don hanya. 22Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar. 23Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa. 24Ya sallami 'yan'uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.”

25Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan'ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu. 26Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.

27Amma sa'ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa'ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo. 28Isra'ila ya ce, “I, ya isa, ɗana Yusufu yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”

46

Yakubu da Iyalinsa suka Tafi Masar

1Isra'ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku. 2Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.” Ya amsa ya ce, “Na'am.”

3Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma. 4Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.”

5Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, 'ya'yan Isra'ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da 'yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aika a ɗauko su. 6Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka, 7'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.

8Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, wato, Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra'ubainu, ɗan farin Yakubu. 9'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. 10'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan'aniya. 11'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari. 12'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul. 13'Ya'yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron. 14'Ya'yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel, 15(waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).

16'Ya'yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli. 17'Ya'yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, 'yar'uwarsu. 'Ya'yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel. 18Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai'atu, 'yarsa.

19'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu. 20Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar. 21'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar. 22Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.

23Hushim shi ne ɗan Dan. 24'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. 25Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila.

26Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan 'ya'yansa, su mutum sittin da shida ne. 27'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.

Yakubu da Iyalinsa a Masar

28Isra'ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen, 29sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra'ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa. 30Isra'ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”

31Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir'auna, in ce masa, “‘'Yan'uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā suke a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina, 32mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.” 33To, sa'ad da Fir'auna zai kira ku, ya tambaye ku, “‘Mece ce sana'arku?” 34Sai ku ce, “‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna 'yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,” don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”

47

1Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir'auna, ya ce, “Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan'ana, yanzu suna ƙasar Goshen.” 2Daga cikin 'yan'uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir'auna.

3Sai Fir'auna ya ce wa 'yan'uwan nan nasa, “Mece ce sana'arku?” Suka amsa wa Fir'auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.” 4Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”

5Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka. 6Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”

7Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka. 8Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”

9Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.” 10Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna. 11Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta. 12Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.

Hidimar Yusufu a Lokacin Yunwa

13A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar. 14Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan'ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir'auna. 15Sa'ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan'ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.”

16Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.” 17Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.

18Sa'ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa, kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana. 19Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir'auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”

20Ta haka Yusufu ya saya wa Fir'auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir'auna. 21Yusufu ya mai da jama'ar bayi daga wannan kan iyaka na Masar zuwa wancan. 22Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir'auna ya yanka musu, da rabon da Fir'auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba. 23Yusufu ya ce wa jama'ar, “Ga shi, a yau na saya wa Fir'auna ku da gonakinku. Yanzu fa, ga iri dominku, za ku shuka gonakin. 24Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir'auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na 'yan ƙanananku.”

25Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ko ya gamshe ka, ya shugaba, mā zama bayin Fir'auna.” 26Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir'auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir'auna ba.

Wasiyyar Yakubu

27Ta haka fa Isra'ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai. 28Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato, shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba'in da bakwai. 29A sa'ad da lokaci ya gabato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar, 30amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.” Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.”

31Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa'an nan sai Isra'ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.

48

Yakubu ya Sa wa Ifraimu da Manassa Albarka

1Ya zama fa bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Yusufu, “Ga mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki 'ya'yansa biyu maza, Manassa da Ifraimu ya tafi ya gai da mahaifinsa.

2Sa'ad da aka ce wa Yakubu, “Ɗanka Yusufu ya zo wurinka,” sai Yakubu ya ƙoƙarta ya tashi zaune a kan gadon.

3Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan'ana ya sa mini albarka, 4ya ce mini, “‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al'ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.” 5Yanzu fa, a kan waɗannan 'ya'yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra'ubainu da Saminu suke. 6'Ya'ya waɗanda za a haifa a bayansu za su zama naka, za a kira su da sunan 'yan'uwansu cikin gādonsu. 7Sa'ad da nake zuwa daga Mesofotamiya, sai Rahila ta rasu a hannuna a ƙasar Kan'ana a kan hanya, ga shi kuwa, da sauran tazara kafin a kai Efrata. Na kuwa binne ta a Efrata,” wato, Baitalami.

8Sa'ad da Isra'ila ya ga 'ya'yan Yusufu, maza, ya ce, “Suwane ne waɗannan?”

9Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “'Ya'yana ne maza waɗanda Allah ya ba ni a nan.” Sai ya ce, “Kawo su gare ni, ina roƙonka, domin in sa musu albarka.” 10Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su. 11Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na 'ya'yanka.” 12Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra'ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.

13Yusufu ya ɗauki su biyu ɗin, Ifraimu a hannunsa na dama zuwa hannun hagun Isra'ila, Manassa kuma a hannunsa na hagu zuwa dama na Isra'ila, ya kawo su kusa da shi. 14Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama, ya ɗora bisa kan Ifraimu wanda yake ƙarami, hannunsa na hagu kuma bisa kan Manassa, yana harɗe da hannuwansa, gama Manassa shi ne ɗan fari. 15Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce, “Allah na Ibrahim da Ishaku, Iyayena da suka yi tafiyarsu a gabansa, Allah da ya bi da ni Dukan raina har wa yau, ya sa musu albarka.

16Mala'ikan da ya fanshe ni Daga dukan mugunta, Ya sa wa samarin albarka, Bari a dinga ambatarsu da sunana, Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena, Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama taron jama'a a tsakiyar duniya.”

17Sa'ad da Yusufu ya ga mahaifinsa ya ɗora hannun damansa a bisa kan Ifraimu, ransa bai so ba, ya ɗauke hannun mahaifinsa, domin ya kawar da shi daga kan Ifraimu zuwa kan Manassa. 18Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “Ba haka ba ne baba, gama wannan ne ɗan fari. Sa hannunka na dama a bisa kansa.”

19Amma mahaifinsa ya ƙi, ya ce, “Na sani, ɗana, na sani, shi ma zai zama al'umma, zai ƙasaita, duk da haka ƙanensa zai fi shi ƙasaita, zuriyarsa kuwa za ta zama taron al'ummai.”

20Ya sa musu albarka a wannan rana, yana cewa, “Ta gare ku Isra'ila za su sa albarka da cewa, “‘Allah ya maishe ku kamar Ifraimu da Manassa.” Da haka ya sa Ifraimu gaba da Manassa.

21Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka. 22Ni ne nake ba ka Shekem, kashi ɗaya fiye da 'yan'uwanka, wanda na ƙwace da takobina da bakana daga hannun Amoriyawa.”

49

Faɗar Yakubu a kan 'Ya'yansa

1Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa.

2“Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yan Yakubu, maza, Ku kuma kasa kunne ga Isra'ila mahaifinku.

3“Ra'ubainu, kai ɗan farina ne, ƙarfina, Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi ƙarfi duka cikin 'ya'yana.

4Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi.

5“Saminu da Lawi 'yan'uwa ne, Suka mori takubansu cikin ta da hankali.

6Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba, Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu ba, Gama cikin fushinsu suka kashe mutane, Cikin gangancinsu kuma suka gurgunta bijimai.

7La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.

8“Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka.

9Yahuza ɗan zaki ne, Ya kashe ganima sa'an nan ya komo wurin ɓuyarsa. Yahuza kamar zaki yake, Yakan kwanta a miƙe, Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi.

10Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.

11Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi, A kuranga mafi kyau, Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi, Ruwan inabi ja wur kamar jini.

12Idanunsa za su yi ja wur saboda shan ruwan inabi, Haƙoransa kuma su yi fari fat saboda shan madara.

13“Zabaluna zai zauna a gefen teku, Zai zama tashar jiragen ruwa, Kan iyakarsa kuma zai kai har Sidon.

14“Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa, Ya kwanta a miƙe tsakanin jakunkunan shimfiɗa.

15Saboda ya ga wurin hutawa ne mai kyau, Ƙasar kuma mai kyau ce, Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa domin ɗaukar kaya, Ya zama bawa, yana yin aiki mai wuya.

16“Dan zai zama mai mulki ga mutanensa Kamar ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila.

17Dan zai zama maciji a gefen hanya, Zai zama kububuwa a gefen turba, Mai saran diddigen doki Don mahayin ya fāɗi da baya.

18“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

19“Gad, 'yan fashi za su kai masa hari, Shi kuwa zai runtume su.

20“Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfani mai yawa, Zai kuma yi tanadin abincin da ya dace da sarki.

21“Naftali sakakkiyar barewa ce, Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya.

22“Yusufu jakin jeji ne, Jakin jeji a gefen maɓuɓɓuga Aholakan jeji a gefen tuddai.

23Maharba suka tasar masa ba tausayi Suka fafare shi da kwari da baka.

24Duk da haka bakunansu sun kakkarye. Damatsansu sun yayyage Ta wurin ikon Allah Mai Girma na Yakubu, Makiyayi, Dutse na Isra'ila.

25Ta wurin Allah na mahaifinka wanda zai taimake ka, Ta wurin Allah Mai Iko Dukka wanda zai sa maka albarka Albarkun ruwan sama daga bisa, Da na zurfafa daga ƙarƙashin ƙasa, Da albarkun mama da na mahaifa.

26Albarkun hatsi da na gari Albarkun daɗaɗɗun duwatsu, Abubuwan jin daɗi na madawwaman tuddai, Allah ya sa su zauna a kan Yusufu, Da a goshin wanda aka raba shi da 'yan'uwansa.

27“Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa, Da safe yakan cinye abin da ya kaso, Da maraice kuma yakan raba abin da ya kamo.”

28Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa ko wannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.

Rasuwar Yakubu da Jana'izarsa

29Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte, 30a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta. 31A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai'atu. 32Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.” 33Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.

50

1Yusufu kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya sumbace shi. 2Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra'ila da maganin hana ruɓa. 3Suka ɗauki kwana arba'in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi masa makoki na kwana saba'in.

4Sa'ad da kwanakin makokin suka wuce, Yusufu ya yi magana da iyalin gidan Fir'auna, ya ce, “Idan fa yanzu na sami tagomashi a wurinku, ku yi magana, ina roƙonku a gaban Fir'auna, ku ce masa, 5“‘Sa'ad da mahaifina yake bakin mutuwa, ya sa ni in yi masa alkawari, cewa, zan binne shi a kabarin da ya haƙa wa kansa a ƙasar Kan'ana.” Don haka in ya yarda ya bar ni in je in binne mahaifina, sa'an nan in komo.”

6Fir'auna ya amsa, ya ce, “Ka haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya rantsar da kai.”

7Saboda haka, Yusufu ya haura ya binne mahaifinsa, tare da shi kuma dukan barorin Fir'auna suka haura, da dattawan gidan Fir'auna, da dukan dattawan ƙasar Masar, 8da kuma dukan iyalin gidan Yusufu, da 'yan'uwansa, da iyalin gidan mahaifinsa. Sai 'yan ƙananansu, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanunsu, aka bari a ƙasar Goshen. 9Da karusai da mahayan dawakai kuma suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiya ce ƙwarai.

10Sa'ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa. 11Sa'ad da Ka'aniyawa mazaunan ƙasar, suka ga makokin da aka yi a farfajiyar masussukar Atad, sai suka ce, “Wannan makoki mai zafi ne ga Masarawa.” Don haka aka sa wa wurin suna Abel-mizrayim, wanda yake wajen Urdun.

12Haka 'ya'yansa suka yi masa kamar yadda ya umarta, 13gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta. 14Bayan da Yusufu ya binne mahaifinsa, ya koma Masar tare da 'yan'uwansa da dukan waɗanda suka tafi tare da shi don jana'izar mahaifinsa.

Yusufu ya Tabbatar wa 'Yan'uwansa ba zai Rama Ba

15Sa'ad da 'yan'uwan Yusufu suka ga mahaifinsu ya rasu, suka ce, “Mai yiwuwa ne Yusufu zai ƙi jininmu, ya sāka mana dukan muguntar da muka yi masa.” 16Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa, 17ya ce, “‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.” Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi.

18'Yan'uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”

19Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba. 20A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama'a masu yawa waɗanda suke da rai a yau. 21Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta'azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.

Rasuwar Yusufu

22Haka fa Yusufu ya zauna a Masar, shi da iyalin gidan mahaifinsa. Yusufu kuwa ya yi shekara ɗari da goma a duniya. 23Yusufu fa ya ga 'ya'yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi 'ya'yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu. 24Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” 25Sa'an nan Yusufu ya rantse wa 'ya'yan Isra'ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.” 26Yusufu ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Sai suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Aka kuwa sa shi a akwatin gawa cikin Masar.