Habakkuk

Habakuk

1

Damuwar Habakuk a kan Rashin Gaskiya

1Jawabin da annabi Habakuk ya hurta ke nan.

2Ya Ubangiji, ina ta kukan neman taimako, Amma ka ƙi ji, sai yaushe za ka ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci, Amma ba ka yi taimako ba.

3Me ya sa ka sa ni in ga mugunta, In kuma dubi wahala? Hallaka da zalunci suna a gabana. Jayayya da gardama sun tashi.

4Ba a bin doka, Shari'a kuma ba ta aiki. Mugaye sun fi adalai yawa nesa, Don haka shari'a tana tafe a karkace.

Kaldiyawa za su Hori Yahuza

5Ubangiji ya ce, “Ka duba cikin al'umman duniya! Ka gani! Ka yi al'ajabi! Ka yi mamaki! Gama zan yi aiki a kwanakinka, Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.

6Ga shi, ina tā da Kaldiyawa, Al'umman nan mai zafi, mai fitina, Waɗanda suke tafiya ko'ina a duniya, Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.

7Suna da bantsoro da firgitarwa. Adalcinsu da ikonsu sun danganta ga yadda suke so.

8“Dawakansu sun fi damisa sauri, Sun fi kyarketan maraice zafin hali, Sojojin dawakansu suna zuwa a guje. Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa, Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.

9“Sun zo don su yi kama-karya. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo. Sun tattara bayi kamar yashi.

10Sukan yi wa sarakuna ba'a, Sukan mai da masu milki abin wasa. Kowace kagara abin dariya ce a wurinsu, Sukan tsiba ƙasa, su hau, su cinye ta.

11Sukan wuce da sauri kamar iska, Su yi tafiyarsu. Su masu laifi ne, Ƙarfinsu shi ne gunkinsu.”

Habakuk ya Ƙara Kuka ga Ubangiji

12Ba kai ne madawwami ba? Ya Ubangiji Allahna Mai Tsarki. Ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji, kai ne ka sa su su yi hukunci, Ya dutse, kai ne ka kafa su don su yi horo.

13Kai mai tsarki ne, Ka fi ƙarfin ka dubi mugunta. Kai da ba ka duban laifi. Me ya sa kake duban marasa imani? Kana iya shiru sa'ad da mugu yake haɗiye Mutumin da ya fi shi adalci>

14Gama ka mai da mutane kamar kifaye a cikin teku, Kamar abubuwa masu rarrafe da ba su da shugaba.

15Kaldiyawa sukan kama mutane da ƙugiya, Sukan jawo su waje da tarunsu, Sa'an nan su tara su cikin ragarsu, Su yi murna da farin ciki.

16Domin haka sukan miƙa hadaya ga tarunsa, Su ƙona turare ga ragarsu, Domin su ne suka jawo musu wadata, da abinci mai yawa.

17Za su ci gaba da juye tarunsa ke nan? Su yi ta karkashe al'umman duniya ba tausayi>

Ubangiji ya Amsa wa Habakuk

2

1Zan tsaya a wurin tsayawata, In zauna kuma a kan hasumiya, In jira in ji abin da zai ce mini, Da abin da zai amsa a kan kukata.

2Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna, Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.

3Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.

4Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi, Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.

5“Ruwan inabi kuma yana yaudarar mai fāriya, Don haka ba ya zama a gida. Haɗamarsa tana da fāɗi kamar Lahira, Kamar kuma mutuwa yake, ba ya ƙoshi. Ya tattara wa kansa al'ummai duka, Ya kwaso wa kansa mutane duka.”

Marasa Adalci, Tasu ta Ƙare

6“Ai, waɗannan duka za su yi ta yi masa zambo, Su yi masa dariya ta raini, Su ce, “‘Tasa ta ƙare, shi wanda ya tattara abin da ba nasa ba, Har yaushe zai riƙa arzuta kansa ta hanyar ba da rance?”

7Mabartanka za su tasar maka nan da nan, Waɗanda suke binka bashi za su farka. Za ka zama ganima a gare su.

8Saboda ka washe al'umman duniya da yawa, Sauran mutanen duniya duka za su washe ka, Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.

9“Tasa ta ƙare, shi wanda ya arzuta gidansa da ƙazamar riba, Ya kuma gina gidansa a bisa don ya tsere wa masifa!

10Ka jawo wa gidanka kunya, Saboda ka karkashe mutane da yawa, Ka hallaka kanka da kanka.

11Dutse zai yi kuka daga garu, Katako kuwa zai amsa masa daga aikin da aka yi da itace.

12“Tasa ta ƙare, shi wanda ya gina gari da jini, Ya kuma kafa birni da mugunta!

13Ba Ubangiji Mai Runduna ne ya sa mutanen duniya, su yi wahala, wuta ta cinye ba? Sun kuma gajiyar da kansu a banza>

14Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, Kamar yadda ruwa ya cika teku.

15“Taka ta ƙare, kai wanda kake sa maƙwabtanka su sha, Kana zuba musu dafinka har su bugu, Don ka dubi tsiraicinsu!

16A maimakon daraja, za ka sha ƙasƙanci. Ka sha kai da kanka, ka yi tangaɗi. Ƙoƙon da yake a hannun Ubangiji zai fāɗo a kanka, Kunya za ta rufe darajarka.

17Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka, Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka, Saboda jinin mutanen da ka zubar, Da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.

18“Ina amfanin gunki sa'ad da mai yinsa ya siffata shi? Shi siffa ne da aka yi da ƙarfe, mai koyar da ƙarya. Gama mai yinsa yakan dogara ga abin da ya siffata, Sa'ad da ya yi bebayen gumaka.

19Tasa ta ƙare, shi wanda ya ce da abin da aka yi da itace, “‘Farka!” Ya kuma ce wa dutse wanda ba ya ji, “‘Tashi!” Wannan zai iya koyarwa? Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa, Ba ya numfashi ko kaɗan.

20“Amma Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Bari duniya ta yi tsit a gabansa.”

3

Addu'ar Habakuk

1Addu'ar nasara wadda annabi Habakuk ya yi.

2Ya Ubangiji, na ji labarinka, Sai tsoro ya kama ni. Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu, Ayyukan da ka saba yi. Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.

3Daga Edom Allah ya zo, Daga dutsen Faran Mai Tsarki yake tahowa. Ɗaukakarsa ta rufe sammai, Duniya kuwa ta cika da yabonsa.

4Walƙiyarsa kamar hasken rana ce, Haske yana haskakawa daga gare shi, A nan ne ya lulluɓe ikonsa.

5Annoba tana tafe a gabansa, Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.

6Ya tsaya, ya auna duniya, Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya. Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe, Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya. Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.

7Na ga alfarwan Kushan suna cikin azaba, Labulen ƙasar Madayana suna rawar jiki.

8Ya Ubangiji, ka hasala da koguna ne? Ko kuwa ka yi fushi da koguna? Ko kuwa ka hasala da teku ne, Sa'ad da ka hau dawakanka, kana bisa karusarka ta nasara>

9Ka ja bakanka, Ka rantsar da sandunan horo. Ka rarratsa duniya da koguna.

10Duwatsu sun gan ka, sun ƙame, Ruwaye masu hauka suka gudu. Zurfi kuma ya ta da muryarsa, Raƙuman ruwansa sun kwanta.

11Rana da wata sun tsaya cik a inda suke, A lokacin da kibanka masu haske suke wucewa fyu, Da lokacin walƙatawar hasken māshinka.

12Ka ratsa duniya da hasala, Ka kuma tattake al'umman duniya da fushi.

13Ka fito saboda ceton mutanenka, Saboda ceton shafaffenka kuma. Ka fasa kan mugu, Ka kware shi daga cinya zuwa wuya.

14Ka kuje kan mayaƙansa da sandunansa, Waɗanda suka zo kamar guguwa don su watsar da mu. Suna murna kamar waɗanda suke zaluntar matalauci a ɓoye.

15Ka tattake teku da dawakanka, Da haukan ruwa mai ƙarfi.

16Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa, Leɓunana suka raurawa. Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki. Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.

17Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba, Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi, Zaitun kuma bai ba da amfani ba, Gonaki ba su ba da abinci ba, An kuma raba garken tumaki daga cikin garke, Ba kuma shanu a turaku,

18Duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, Zan yi murna da Allah Mai Cetona.

19Ubangiji Allah shi ne ƙarfina, Ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi, Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.