Haggai

1

An Zuga Mutane su Gina Haikali

1A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. 2Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Mutanen nan suna cewa lokaci bai yi ba tukuna da za a sāke gina Haikalin Ubangiji.”

3Ubangiji kuwa ya yi magana da annabi Haggai ya ce, 4“Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi wa rufin katako, amma Haikalin nan yana zaman kufai? 5Yanzu, ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku lura da al'amuranku! 6Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.” 7Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku lura da al'amuranku! 8Ku haura zuwa kan tuddai, ku kawo itace don ku gina Haikalina, in ji daɗinsa, a kuma ɗaukaka ni.

9“Kun sa zuciya za ku sami da yawa, sai kuka sami kaɗan. Sa'ad da kuma kuka kawo shi gida, sai na hurar da shi. Me ya sa haka? Saboda Haikalina da yake zaman kufai, amma ko wannenku yana fama da ginin gidansa. 10Domin haka sama ta ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfani. 11Na kawo fari a kan ƙasa, da kan tuddai, da kan hatsi, da kan 'ya'yan inabi, da kan 'ya'yan zaitun, da kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da kan mutane, da kan dabbobi, da kan ayyukansu.”

12Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji. 13Sai Haggai, manzon Ubangiji, ya faɗa wa mutane maganar Ubangiji, ya ce, “Ubangiji ya ce, “‘Ni Ubangiji ina tare da ku.” 14Ubangiji kuwa ya zuga zuciyar Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da zuciyar dukan sauran mutane. Suka zo, suka fara aikin Haikalin Ubangiji Allahnsu Mai Runduna 15a ranar ashirin da huɗu ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus.

2

Darajar Sabon Haikalin

1A rana ta ashirin da ɗaya ga watan bakwai sai Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai ya ce, 2“Ka yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, ka ce, 3“‘Wa ya ragu a cikinku da ya ga wannan Haikali da darajarsa ta dā? Ƙaƙa kuke ganinsa yanzu? A ganinku ba a bakin kome yake ba? 4Duk da haka yanzu sai ku yi ƙarfin hali, kai Zarubabel, da kai Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukanku mutanen ƙasar, ku kama aikin, gama ina tare da ku. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 5Na yi muku alkawari a sa'ad da kuka fito daga Masar, cewa Ruhuna zai zauna tare da ku, haka yake yanzu, kada ku ji tsoro!”

6“Ni Ubangiji Mai Runduna, ina cewa ba da jimawa ba, zan girgiza sammai, da duniya, da teku, da sandararriya ƙasa. 7Zan kuma girgiza al'umman duniya duka don dukiyar al'umman duniya ta samu. Zan kuwa cika Haikalin nan da daraja. 8Azurfa tawa ce, zinariya kuma tawa ce. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 9Darajar Haikalin nan ta nan gaba za ta fi ta dā. A wannan wuri zan ba da salama. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

An Tsauta wa Mutane saboda Rashin Amincinsu

10A rana ta ashirin da huɗu ga watan tara a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji kuma ya yi magana da annabi Haggai ya ce, 11“Ka tambayi firistoci a kan wannan doka. 12“‘Idan mutum yana riƙe da nama tsattsarka a rigarsa, idan rigar ta taɓa gurasa, ko dafaffen abinci, ko ruwan inabi, ko mai, ko kowane irin abinci, wannan zai sa abin ya tsarkaka?” Sai firistocin suka amsa suka ce, “A'a.”

13Sai kuma Haggai ya ce, “Idan wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, wannan zai sa abin ya ƙazantu?” Sai firistoci suka ce, “Wannan zai sa abin ya ƙazantu!”

14Sai Haggai ya ce, “Ubangiji ya ce, “‘Haka yake da wannan jama'a da wannan al'umma da suke gabana da kowane irin aikinsu. Abin da suke miƙawa kuma marar tsarki ne.

15“‘Ina roƙonku, ku tuna a ran nan tun kafin a ɗora dutse a kan dutse na gina Haikalin Ubangiji, yaya kuke? 16A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai ya iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don ya ɗebo mudu hamsin, sai ya tarar da mudu ashirin kawai. 17Na aukar muku da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara a kan amfanin gonakinku, duk da haka ba ku komo wurina ba, ni Ubangiji na faɗa. 18Yanzu ku tuna a ran nan, wato rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji. 19Ba sauran iri a rumbu. Kurangar inabi kuma, da itacen ɓaure, da rumman, da itacen zaitun ba su ba da amfani ba tukuna. Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.”

Ubangiji ya yi wa Zarubabel Alkawari

20Ubangiji kuma ya yi magana da Haggai a rana ta ashirin da huɗu ga watan, ya ce, 21“Ka faɗa wa Zarubabel, mai mulkin Yahuza cewa, “‘Ina cikin shirin girgiza sammai da duniya. 22Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al'umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba. 23A wannan rana, ni Ubangiji Mai Runduna, zan ɗauke ka, kai Zarubabel, bawana ɗan Sheyaltiyel, in maishe ka kamar zobe mai hatimi, gama na zaɓe ka, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”