Hebrews

Ibraniyawa

1

Allah ya yi Magana ta wurin Ɗansa

1A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa, 2amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya. 3Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama.

Fifikon Yesu a kan Mala'iku

4Ta haka yake da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gāda yake da fifiko nesa a kan nasu.

5Domin kuwa wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau?” da kuma, “Zan kasance Uba a gare shi, Shi kuma, zai kasance Ɗa a gare ni?”

6Amma da zai sāke shigo da magāji a duniya, sai ya ce, “Dukkan mala'ikun Allah su yi masa sujada.”

7A game da mala'iku kuma sai ya ce, “Yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, Masu hidimarsa kuma harsunan wuta.”

8Amma a game da ɗan, sai ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne, Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya.

9Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin sāɓo. Saboda haka Allah, wato, Allahnka, ya shafe ka Da man farin ciki fiye da tsararrakinka.”

10Da kuma, “Ya ubangiji, kai ne ka halicci duniya tun farko, Sammai kuma aikinka ne.

11Su za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufa,

12Za ka naɗe su kamar mayafi, Za su kuma sauya, Amma kai kana nan ba sākewa, Har abada shekarunka ba za su ƙare ba.”

13Amma wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Zauna a damana, Sai na sa ka take maƙiyanka?”

14Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aiki, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima>

2

Maganar Ceto Mai Girma

1Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana. 2In kuwa maganar nan da aka faɗa ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowane keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su, 3to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi, 4sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.

Shugaban Ceto

5Ai, ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar da za a yi, wanda muke zance. 6Amma wani ya tabbatar a wani wuri cewa, “Mutum ma mene ne, har da za ka tuna da shi? Ko ɗan mutum ma, har da za ka kula da shi>

7Kā sa shi ya gaza mala'iku a ɗan lokaci kaɗan, Kā naɗa shi da ɗaukaka da girma, Kā ɗora shi a kan dukkan halittarka.

8Kā sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” To, a wajen sarayar da dukkan abubuwa a ƙarƙashinsa ɗin nan, Allah bai bar kome a keɓe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba. 9Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi a ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.

10Saboda haka, ya dace da Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance dominsa, ta gare shi ne kuma dukkan abubuwa suka samu, yă kammala shugaban cetonsu ta wurin shan wuya, a wajen kawo 'ya'ya masu yawa ga samun ɗaukaka. 11Domin da shi mai tsarkakewar da kuma waɗanda aka tsarkaken, duk tushensu ɗaya ne. Shi ya sa ba ya jin kunyar kiransu 'yan'uwansa, 12da ya ce, “Zan sanar da sunanka ga 'yan'uwana, A tsakiyar ikilisiya zan yabe ka da waƙa.”

13Har wa yau, ya ce, “Zan dogara a gare shi.” Da kuma, “Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni.”

14Wato tun da yake 'ya'yan duk suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato iblis, ta wurin mutuwarsa, 15yă kuma 'yanta duk waɗanda tun haihuwarsu suke zaman bauta saboda tsoron mutuwa. 16Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako. 17Saboda haka, lalle ne ya zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin ya zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a. 18Tun da yake shi ma ya sha wuya, sa'ad da aka gwada shi, ashe, zai taimaki waɗanda ake yi wa gwaji.

3

Fifikon Almasihu a kan Musa

1Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa, 2shi da yake mai aminci ga wannan da ya sa shi, kamar yadda Musa ya yi ga duk jama'ar Allah. 3Amma kuwa an ga Yesu ya cancanci ɗaukaka fiye da ta Musa nesa, kamar yadda mai gina gida ya fi gidan martaba. 4Kowane gida ai, da wanda ya gina shi, amma maginin dukkan abubuwa Allah ne. 5To, shi Musa mai aminci ne ga dukkan jama'ar Allah a kan shi bara ne, saboda shaida a kan al'amuran da za a yi maganarsu a nan gaba, 6amma Almasihu mai aminci ne, yana mulkin jama'ar Allah a kan shi Ɗa ne, mu ne kuwa jama'arsa, muddin mun tsaya gabanmu gaɗi, muna gadara da begenmu ƙwarai.

Shiga Inuwar Allah, Hutawar Mutanensa ke Nan

7Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau in kun ji muryarsa,

8Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan, Wato, ranar gwaji a jeji,

9A inda kakanninku suka gwada ni, suka jarraba ni, Suna ganin ayyukana har shekara arba'in.

10Saboda haka ne, na yi fushi da mutanen wannan zamani, Har na ce, “‘A kullum zuciyarsu a karkace take, Ba su kuwa san hanyoyina ba.”

11Sai na yi rantsuwa da fushina, na ce, “‘Ba za su shiga inuwata ba sam.”

12Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye. 13Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya muddin akwai “Yau,” don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi. 14Don kuwa mun zama masu tarayya da Almasihu, muddin muna tsaye da ƙarfi a kan amincewar nan tamu ta fari, har zuwa ƙarshe. 15Domin kuwa an ce, “Yau in kun ji muryarsa, Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan.”

16To, su wane ne suka ji, duk da haka suka yi tawaye? Ashe, ba duk waɗanda suka fito daga ƙasar Masar ba ne, waɗanda Musa ya shugabantar? 17Da su wa kuma ya yi fushi har shekara arba'in? Ashe, ba da waɗanda suka yi zunubi ba ne, waɗanda gawawwakinsu suka fādi a jeji? 18Su wa kuma ya rantse wa, cewa ba za su shiga inuwarsa ba, in ba marasa biyayyar nan ba? 19Sai muka ga, ashe, saboda rashin bangaskiyarsu ne suka kāsa shiga.

4

1Saboda haka tun alkawarin shiga inuwarsa tana nan, sai mu yi tsananin kula, kada ya zamana waninku ya kāsa shiga. 2Ai kuwa, an yi mana albishir kamar yadda aka yi musu, sai dai maganar da aka yi musu ba ta amfane su da kome ba, don kuwa ba ta gamu da bangaskiya ga majiyanta ba. 3Mu kuwa da muka ba da gaskiya, muna shiga inuwar, yadda ya ce, “Sai na yi rantsuwa da fushina, na ce, “‘ba za su shiga inuwata ba sam,” ko da yake ayyukan Allah gamammu ne tun daga farkon duniya. 4Domin a wani wuri ya yi maganar rana ta bakwai cewa, “A rana ta bakwai Allah ya huta daga ayyukansa duka.” 5Amma a wannan wuri kuwa sai ya ce, “Ba za su shiga inuwata ba sam.”

6Wato, tun da yake har yanzu dai da sauran dama waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya, 7to, sai ya sāke sa wata rana, ya ce, “Yau,” yana magana ta bakin Dawuda bayan da aka daɗe, kamar an riga an faɗa cewa, “Yau in kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”

8Da dai a ce Joshuwa ya kai su cikin inuwar Allah, da Allah bai yi maganar wata rana nan gaba ba, 9wato, har yanzu dai akwai sauran wani hutun Asabar ga jama'ar Allah, 10domin kuwa duk wanda ya shiga inuwar Allah, ya huta ke nan daga ayyukansa, kamar yadda Allah ya hutu daga nasa.

11Saboda haka, sai mu yi himmar shiga inuwar nan, kada wani ya kāsa shiga, saboda irin wannan rashin biyayya. 12Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta. 13Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.

Yesu Babban Firist Mai Girma

14To, tun da ya ke muna da Babban Firist mai girma, wanda ya ratsa sammai, wato Yesu Ɗan Allah, sai mu tsaya a kan abin da muka bayyana yarda a gare shi. 15Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabe shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba. 16Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.

5

1Kowane babban firist, da yake an zaɓe shi ne daga cikin mutane, akan sa shi ya wakilci mutane ga al'amarin Allah, don ya miƙa sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai. 2Ya kuma zamana wanda zai iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da yake rarrauna ne shi ta ko'ina. 3Saboda haka, wajibi ne ya miƙa hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kaɗai ba, har ma don nasa. 4Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.

5Haka kuma, Almasihu ba shi ya ɗaukaka kansa ya zama Babban Firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau.”

6Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, “Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”

7Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa. 8Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha, 9da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya, 10gama Allah yana kiransa Babban Firist, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.

Faɗakarwa a kan wata Koyarwa Dabam

11Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe. 12Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba. 13Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake. 14Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.

6

1Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sāke koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da ɗora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukunci. 3Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4Domin waɗanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka ɗanɗana baiwar nan ta Basamaniya, suka kuma sami rabo na ruhu mai tsarki, 5har suka ɗanɗana daɗin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, 6sa'an nan kuma suka ridda, ba mai yiwuwa ba ne a sāke jawo su ga tuba, tun da yake sāke gicciye Ɗan Allah suke yi, su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari. 7Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka. 8Amma tsire-tsirenta ƙaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, ƙarshenta dai ƙonewa ne.

Tabbataccen Bege

9Ko da yake mun faɗi haka, a game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna a kan abubuwa mafiya kyau na zancen ceto. 10Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. 11Muna dai bukata ƙwarai kowannenku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa ƙarshe, 12don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da waɗanda suka karɓi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da haƙurinsu.

13Sa'ad da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa, 14ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma riɓanya zuriyarka.”

15Ta haka Ibrahim, bayan da ya jure da haƙuri, ya karɓi cikar alkawarin. 16Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su, rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa a duk lokacin gardama. 17Don haka, sa'ad da Allah yake son ƙara tabbatar wa magādan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sākewa ba ne sam, sai ya haɗa da rantsuwa, 18domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sākewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu ƙarfafa ƙwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai. 19Begen nan kuwa da muke da shi, kamar anka yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen, 20a inda saboda mu ne Yesu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.

7

Firist Kwatancin Malkisadik

1Shi wannan Malkisadik, Sarkin Urushalima, firist na Allah Maɗaukaki, ya gamu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim yake dawowa daga kisan sarakuna, ya sa masa albarka. 2Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma'anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa'an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato, sarkin salama. 3Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haihuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, firist ne har abada.

4Kai, ku dubi irin girmansa! Har kakanmu Ibrahim ma ya ba shi ushirin ganima! 5Ga shi kuma, waɗansu na zuriyar Lawi, in sun sami matsayin firist, akan umarce su bisa ga Shari'a su karɓi ushiri a gun jama'a, wato a gun 'yan'uwansu, ko da yake su ma zuriyar Ibrahim ne. 6Amma wannan, wanda ma ba a asalin Lawi yake ba, ya karɓi ushiri a gun Ibrahim, har ya sa masa albarka, shi ma da aka yi wa alkawarai. 7Ai, ba abin musu ba ne, cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. 8Ga shi, a nan masu karɓar ushiri, mutane ne masu mutuwa, a can kuwa mai karɓar wanda aka shaida shi, rayayye ne. 9A ma iya cewa ko Lawi ma da kansa, mai karɓar ushiri, ya ba da ushiri ta wurin Ibrahim, 10don shi Lawi yana daga tsatson kakansa Ibrahim, sa'ad da Ibrahim ɗin ya gamu da Malkisadik.

11Gama da a ce kammala tana samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama'a suka karɓi shari'a), wace bukata kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatancin ɗabi'ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatancin ɗabi'ar Haruna ba? 12Domin in an sauya matsayin firistoci, sai tilas a sauya Shari'a kuma. 13Domin kuwa shi wannan da aka faɗi waɗannan abubuwa a game da shi, ai, na wata kabila ne dabam, wadda ba waninta da ya taɓa hidimar bagadin hadaya. 14Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.

15Wannan kuma ya ƙara fitowa fili sosai, sa'ad da wani firist dabam ya bayyana kamar Malkisadik, 16wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka'ida ta al'adar 'yan adam ba, sai dai ta wurin ikon rai marar gushewa. 17Domin an shaide shi shi da cewa, “Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”

18Ta wani hali an soke wani umarni ta dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa, 19don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah.

20Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. 21Waɗancan sun zama firistoci, ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam, sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, Ba kuwa zai ta da maganarsa ba cewa, “‘Kai firist ne har abada.”

22A sanadin wannan ne Yesu ya zama lamunin alkawarin da ya fi wancan nesa.

23Waɗancan firistoci, an yi su da yawa, domin mutuwa ta hana su tabbata a aikin. 24Amma shi da yake madawwami ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani. 25Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.

26Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai. 27Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya. 28Wato shari'a tana sa mutane su zama manyan firistoci duk da rauninsu, amma maganar nan ta rantsuwa da ta sauko bayan Shari'a, ta sa Ɗa wanda yake kammalalle har abada.

8

Babban Firist na Sabon Alkawari

1Wato, duk manufar maganarmu ita ce wannan. Shi ne irin babban firist wanda muke da shi, wato wanda ya zauna a dama da kursiyin Maɗaukaki a can sammai, 2mai hidima a Wuri Mafi Tsarki, da kuma masujada ta gaskiya, wadda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba. 3Kowane babban firist akan sa shi domin ya miƙa sadakoki da hadayu, saboda haka wajibi ne wannan shi ma, ya zamanto yana da abin da zai miƙa. 4To, ashe, da har yanzu yana duniya, da bai zama firist ba ke nan, tun da yake akwai firistocin da suke miƙa sadakoki bisa ga Shari'a. 5Suna bauta wa makamantan abubuwan Sama da kuma ishararsu, kamar yadda Allah ya gargaɗi Musa sa'ad da yake shirin kafa alfarwar nan, da ya ce, “Ka lura fa, ka shirya kome da kome daidai yadda aka nuna maka a kan dutsen.” 6Amma ga ainhi, Almasihu ya sami hidima wadda take mafificiya, kamar yadda alkawarin nan, wanda shi ne matsakancinsa, yake da fifiko nesa, tun da yake an kafa shi ne a kan mafifitan alkawarai. 7Domin da wancan alkawari na farko bai gaza ba kome ba, da ba sai an sāke neman na biyu ba.

8Gama da ya ga laifinsu da ya ce, “Lokaci yana zuwa, in ji Ubangiji, Da zan tsara sabon alkawari da jama'ar Isra'ila, Da kuma zuriyar Yahuza.

9Ba irin alkawarin da na yi da kakanninsu ba, A ranar da na kama hannunsu Domin in fito da su daga ƙasar Masar. Saboda ba su tsaya ga alkawarina ba, Shi ya sa na ƙyale su, in ji Ubangiji.

10Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama'ar Isra'ila, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Wato, zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.

11Ba kuma sai sun koya wa ɗan garinsu ba, Balle wani ya ce ɗan'uwansa, “‘Kă san Ubangiji!” Domin kowa zai san ni, Daga ƙaraminsu, har ya zuwa babbansu.

12Domin zan yi musu jinƙai a kan muguntarsu, Ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”

13Da ya ce sabon alkawari, ashe kuwa, ya mai da na farkon tsoho ke nan. Abin da yake tsufa, yana kuwa daɗa tsofewa, lalle ya yi kusan shuɗewa ke nan.

9

Wurare Tsarkaka na Duniya da na Sama

1Alkawarin farko yana da ka'idodinsa na yin sujada, da kuma wurin yinta tsattsarka wanda mutane suka shirya. 2Wato, an kafa alfarwa wadda sashinta na farko yake da fitila, da tebur, da kuma keɓaɓɓiyar gurasa. Ana kiran wannan sashi Wuri Mai Tsarki. 3Bayan labule na biyu kuma, akwai sashin alfarwa da ake kira Wuri Mafi Tsarki. 4A cikinsa kuwa da faranti na zinariya domin ƙona turare, da kuma akwatin alkawari da aka yi masa laffa da zinariya ta kowane gefe. A cikinsa kuwa akwai tasar zinariya da manna a ciki, da sandar Haruna wadda ta yi toho, da kuma allunan dutse na alkawarin nan. 5A bisa akwatin alkawari kuma akwai kerubobin nan na ɗaukakar Allah, waɗanda suka yi wa murfin akwatin nan laima. Ba za mu iya yin maganar waɗannan abubuwa filla filla ba a yanzu.

6In an gama waɗannan shirye-shirye haka, sai firistoci kullum su riƙa shiga sashin farko an alfarwar, suna hidimarsu ta ibada. 7Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a. 8Ta haka Ruhu Mai Tsarki yake yin ishara, cewa ba a buɗe hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin alfarwa tana nan a tsaye, 9wadda take ishara ce ga wannan zamani. Bisa ga wannan ishara akan yi miƙa sadaka da hadaya, amma ba sa iya kammala lamirin mai ibadar, 10tun da yake ci da sha da wankewanke iri iri kaɗai suke shafa, ka'idodi ne a game da jiki kurum, waɗanda aka sa kafin a daidaita al'amari.

11Amma Almasihu ya riga ya zo, yana babban firist na kyawawan abubuwan da suke akwai. Masujadar da yake hidima a ciki mafi ɗaukaka ce, mafi kammala kuwa (wadda ba yin mutum ba ce, wato, ba ta wannan halittacciyar duniya ba ce). 12Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa. 13To, jinin awaki ne fa da na bijimai, da kuma tokar karsana da ake yayyafa wa waɗanda suka ƙazantu, suke tsarkake su da tsabtacewar jiki, 14balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.

15Saboda haka, shi ne matsakancin sabon alkawari, domin waɗanda aka kira su karɓi dawwamammen gādon da aka yi musu alkawari, tun da yake an yi wata mutuwa mai fansar waɗanda suke keta umarni a game da alkawarin farko. 16A game da al'amarin wasiyya, lalle ne a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta tukuna. 17Domin ba a zartar da wasiyya sai bayan an mutu, tun da yake ba a yin aiki da ita muddin wanda ya yi ta yana a raye. 18Ashe kuwa, mun ga alkawarin nan na farko, ba a tabbatar da shi ba, sai a game da jini. 19Don bayan Musa ya sanar da kowane umarnin Shari'a ga dukan jama'a, sai ya ɗebi jinin 'yan maruƙa da na awaki, tare da ruwa, da jan ulu, da kuma ganyen izob, ya yayyafa wa Littafin kansa, da kuma duk jama'a, 20yana cewa, “Wannan shi ne jini na tabbatar alkawarin nan, da Allah ya yi umarni a game da ku.” 21Haka kuma, ya yayyafa jinin ga alfarwar nan, da dukan kayanta na yin hidima. 22Hakika, bisa ga Shari'a, kusan kowane abu da jini ake tsarkake shi, in ba a game da zubar da jini ba kuwa, to, ba gafara.

Almasihu ya Miƙa Kansa domin Kawar da Zunubi

23Da waɗannan abubuwa ne, ya wajaba a tsarkake makamantan abubuwan da ke a Sama, sai dai ainihin abubuwan Sama za a tsarkake su ne da hadayar da ta fi waɗannan kyau. 24Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu. 25Ba kuwa domin ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki a kowace shekara da jinin da ba nasa ba ne. 26In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. 27Tun da yake an ƙaddara wa ɗan adam ya mutu sau ɗaya ne, bayan haka kuma sai shari'a, 28shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.

10

1To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara. 2In haka ne kuwa, ashe, ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadar nan sarai, ai, da ba su ƙara damuwa da zunubai ba. 3Amma a game da irin waɗannan hadayu, akan tuna da zunubai a kowace shekara, 4domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.

5Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, “Hadaya da sadaka kam, ba ka so, Amma kā tanadar mini jiki.

6Ba ka farin ciki da hadayar ƙonewa, da kuma hadayar kawar da zunnbai.

7Sa'an nan na ce, “‘Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,” Kamar yadda yake a rubuce a game da ni a Littafi.”

8Sa'ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da sadaka, da hadayar ƙonewa, sa hadayar kawar da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu,” wato, irin waɗanda ake miƙawa ta hanyar Shari'a, 9sai kuma ya ƙara da cewa, “Ga ni, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon ne, don yă kafa na biyun. 10Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.

11Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba. 12Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna a dama ga Allah, 13tun daga lokacin nan yana jira, sai an sa ya take maƙiyansa. 14Gama ya hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada. 15Ruhu Mai Tsarki ma yana yi mana shaida haka, domin bayan ya ce,

16“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”

17sai kuma ya ƙara cewa, “Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba.”

18To, a inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi.

Mu Matsa kusa, mu Dage

19Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu, 20ta wurin sabuwar hanya, rayayyiya wadda ya buɗe mana ta labulen nan, wato jikinsa, 21da yake kuma muna da Firist mai girma, mai mulkin jama'ar Allah, 22sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa. 23Sai mu tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga begen nan namu, domin shi mai yin alkawarin nan amintacce ne, 24mu kuma riƙa kula da juna, ta yarda za mu ta da juna a tsimi mu mu yi ƙauna da aika nagari. 25Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu suke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranar nan tana kusatowa ba.

26In kuwa mun ci gaba da yin zunubi da gangan, bayan mun yi na'am da sanin gaskiya, to, ba fa sauran wata hadaya domin kawar da zunubai, 27sai dai matsananciyar fagabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi, wadda za ta cinye maƙiyan Allah. 28Kowa ya yar da Shari'ar Musa, akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku. 29To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan? 30Domin mun san shi, shi wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce, ni zan sāka.” Da kuma, “Ubangiji zai yi wa jama'arsa hukunci.” 31Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.

32Amma dai ku tuna, a shekarun baya, bayan da aka haskaka zukatanku, kun jure tsananin fama da shan wuya, 33wata rana ana zaginku, ana ta wahalshe ku, ana wulakanta ku a gaban jama'a, wata rana kuma kuna mai da kanku ɗaya da waɗanda aka yi wa haka, 34domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa. 35Saboda haka, kada ku yar da amincewar nan taku, domin tana da sakemako mai yawa. 36Gama yin jimiri ya kama ku, domin bayan da kun aikata nufin Allah, ku sami abin da aka yi muku alkawari.

37“Sauran lokaci kaɗan, Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.

38Amma adalina, ta wurin bangaskiya zai rayu. Amma in ya ja da baya, ba zan yi farin ciki da shi ba.”

39Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.

11

Bangaskiya

1To, bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar abubuwan da ake bege, a kai, ita ce kuma tabbatawar abubuwan da ba a gani ba. 2Domin ta gare ta ne shugabannin dā suka sami yardar Allah. 3Ta wurin bangaskiya muka fahimta, cewa ta faɗar Allah ce aka tsara duniya, har ma abubuwan da ake gani, daga abubuwan da ba a gani ne, suka kasance.

4Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan Kayinu, ta wurin wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta wurin bangaskiyar nan tasa har ya zuwa yanzu yana magana. 5Saboda bangaskiya ce aka ɗauke Anuhu, shi ya sa bai mutu ba, ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Tun kafin a ɗauke shi ma, an shaide shi a kan ya faranta wa Allah rai. 6In ba a game da bangaskiya ba kuwa, ba shi yiwuwa a faranta masa rai. Domin duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata cewa, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa. 7Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.

8Ta wurin bangaskiya Ibrahim ya yi biyayya, sa'ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasa da zai karɓa gādo. Ya kuwa fita, bai ma san inda za shi ba. 9Ta wurin bangaskiya kuma ya yi baƙunci a ƙasar alkawari, kamar dai a ƙasar bare, suna zaune a cikin alfarwai, shi da Ishaku da Yakubu, abokan tarayya ga gādon alkawarin nan. 10Yana ta jiran birnin nan mai tushe, wanda mai fasalta shi, mai gina shi kuma, Allah ne. 11Ta wurin bangaskiya Saratu da kanta ta sami ikon yin ciki, ko da yake ta wuce lokacin haihuwa, tun da dai ta amince, cewa shi mai yin alkawarin nan amintacce ne. 12Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurari, kamar yashi kuma dangam a bakin teku.

13Waɗannan duka sun mutu cikin bangaskiyarsu, ba su kuwa sami abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkato su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda su baƙi ne, bare kuma a duniya. 14Mutane masu irin wannan magana, ai, sun bayyana a fili, suna neman wata ƙasa ta kansu ne. 15Da suna marmarin ƙasar nan da suka baro ne, da sun sami damar komawa. 16Amma bisa ga hakika sun ɗokanta ne a kan wata ƙasa mafi kyau, wato ta Sama. Saboda haka ne, Allah ba ya jin kunya a ce da shi Allahnsu, don kuwa ya shirya musu birni.

17Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa'ad da aka gwada shi, ya miƙa Ishaku hadaya, wato shi da ya yi na'am da alkawaran nan, ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, 18wanda a kansa aka yi faɗi cewa, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.” 19Ya amince da cewa, ko daga matattu Allah yana da iko ya ta da mutum. Ai kuwa, bisa ga misali, sai a ce daga matattu ne ya sāke samun Ishaku. 20Ta wurin bangaskiya Ishaku ya sa wa Yakubu da Isuwa albarka a kan al'amuran da za su zo. 21Ta wurin bangaskiya Yakubu, sa'ad da yake bakin mutuwa, ya sa wa 'ya'yan Yusufu albarka dukkansu biyu, ya kuma yi sujada, yana sunkuye a kan sandarsa. 22Ta wurin bangaskiya Yusufu, da ajalinsa ya yi, ya yi maganar ƙaurar Isra'ilawa, har ya yi wasiyya a game da ƙasusuwansa.

23Ta wurin bangaskiya ne, sa'ad da aka haifi Musa, iyayensa suka ɓoye shi har wata uku, domin sun ga yaron kyakkyawa ne, ba su kuma ji tsoron umarnin sarki ba. 24Ta wurin bangaskiya Musa, sa'ad da ya girma, ya ƙi yarda a kira shi ɗan 'yar Fir'auna, 25ya gwammaci ya jure shan wuya tare da jama'ar Allah, da ya mori romon zunubi, mai saurin wucewa. 26Ya amince, cewa wulakanci saboda Almasihu wadata ce a gare shi, fiye da dukiyar ƙasar Masar, domin ya sa ido a kan sakamakon. 27Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa. 28Ta wurin bangaskiya ya ci Jibin Ƙetarewa, ya yayyafa jini, domin kada mai hallakar da 'ya'yan fari ya taɓa Isra'ilawa. 29Ta wurin bangaskiya suka haye Bahar Maliya ta busasshiyar ƙasa, amma da Masarawa suka yi ƙoƙarin yin haka, sai aka dulmuyar da su. 30Ta wurin bangaskiya garun Yariko ya rushe, bayan an yi ta kewaya shi har kwana bakwai. 31Ta wurin bangaskiya Rahab karuwar nan ba ta hallaka tare da maƙiya biyayya ba, ta karɓi 'yan ganganimar nan kamar aminai.

32Me kuma zan ƙara cewa? Ai, lokaci zai ƙure mini a wajen ba da labarin su Gidiyon, da Barak, da Samson, da Yefta, da Dawuda, da Sama'ila, da kuma sauran annabawa, 33waɗanda ta wurin bangaskiya suka ci masarautai, suka aikata adalci, suka sami cikar alkawarai, suka rurrufe bakunan zakoki, 34suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe. 35Aka mayar wa mata da matattunsa da aka tasar. Waɗansu mutane kuma an azabta su har suka mutu, amma sun ƙi yarda da irin 'yancin da za a ba su, domin a tashe su su rayu da rayuwa mafi kyau. 36Har wa yau kuma, waɗansu suka sha ba'a da bulala, har ma da ɗauri da jefawa a cikin kurkuku. 37Aka jejeffe su da duwatsu, an gwada su, aka raba su biyu da zarto, aka sare su da takobi. Sun yi yawo saye da buzun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, da ƙunci, da wukakanci. 38Su kam, duniya ba ta ma cancanci su zama a cikinta ba. Sun yi yawo a jazza da a kan duwatsu, suna kwana a cikin kogwanni da ramummuka.

39Waɗannan duka, ko da yake Allah ya shaide su saboda bangaskiyarsu, duk da haka, ba su sami cikar alkawarin ba, 40tun da Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau, sai kuwa tare da mu ne za a kammala su.

12

Horon Ubangiji

1Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri, 2muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.

3Ku fa, dubi wannan da ya jure irin a gābar nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai. 4Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba. 5Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku 'ya'yansa ne, wato “Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji, Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.

6Domin Ubangiji, wanda yake ƙauna, shi yake horo, Yakan kuma hori duk ɗan da ya karɓa.”

7Shan wuyar da kuke jurewa, ai, duk don horo ne. Allah ya riƙe ku, ku 'ya'yansa ne. To, wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8In kuwa ba ku da horo irin horon da ake yi wa kowa, to, ashe, kun zama shegu ke nan, ba 'yan halal ba. 9Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi ya wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu? 10Su kam, sun hore mu a ɗan lokaci kaɗan don ganin damarsu, amma shi, don amfanin kanmu ne yake horonmu, domin mu zama abokan tarayya a cikin tsarkinsa. 11Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

Faɗakarwa a kam Ƙin Alherin Allah

12Domin wannan, ku miƙe hannuwanku da suke reto, da gwiwoyinku marasa ƙarfi. 13Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi ɗoɗar, don kada mai ɗingishi ya gulle, a maimakon ya warke. 14Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji. 15Ku kula fa, kada kowa ya kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka, 16kada kuma wani ya zama fasiki, ko mai sāɓon Allah, kamar isuwa, wanda ya sayar da hakkinsa na ɗan fari a kan cimaka a ɗaya tak. 17Kun dai sani daga baya, da ya so ya gāji albarkar nan, sai aka ƙi shi, domin bai sami hanyar tuba ba, ko da yake ya yi ta nemanta har da hawaye.

18Ai, ba ga abin da za a taɓa ne, kuka iso ba, ko wuta mai ruruwa, ko baƙin duhu duhu ƙirin, ko hadiri, 19ko ƙarar ƙaho, ko wata murya, wadda har masu jin maganarta suka yi roƙo kada su ƙara ji, 20don ba su iya jure umarnin da aka yi musu ba cewa, “Ko da dabba ce ta taɓa dutsen, sai a kashe ta da jifa.” 21Amma ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake! Har ma Musa ya ce, “Ina rawar jiki don matuƙar tsoro.” 22Amma ku kan iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku. 23Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu ke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala. 24Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.

25Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama? 26A lokacin nan muryarsa ta girgiza duniya, amma a yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba duniya kaɗai zan girgiza ba, amma har sama ma.” 27To, wannan cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak,” ya nuna kawar da abubuwan da aka girgiza, wato abubuwan da aka halitta, don abubuwan da ba sa girgizuwa su wanzu. 28Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa, 29domin Allahnmu wuta ne mai cinyewa.

13

Gudunmawar da yake Faranta wa Allah Rai

1Sai ku nace da ƙaunar 'yan'uwa. 2Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne waɗansu suka sauki mala'iku ba da sani ba. 3Ku riƙa tunawa da waɗanda ke kurkuku, kamar tare kuke a ɗaure, da kuma waɗanda ake gwada wa wuya, kamar ku ake yi wa. 4Kowa yă girmama aure, Gădon aure kuwa yă zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su, 5Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” 6Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji shi ne mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”

7Ku tuna da shugabanninku na dā, waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. 8Yesu Almasihu ba ya sākewa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma. 9Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su. 10Muna da bagadin hadaya, wanda masu ibada a alfarwar nan ba su da izini su ci abincin wurin, 11domin naman dabbobin da babban firist ke ɗiban jininsu yă kai Wuri Mafi Tsarki domin kawar da zunubai, akan ƙone shi ne a bayan zango. 12Haka ma, Yesu ya sha wuya a waje bayan birni, domin yă tsarkake jama'a da nasa jini. 13Saboda haka, sai mu fita mu je a gare shi a bayan zango, muna shan irin wulakancin da aka yi masa. 14Domin ba mu da wani dawwamammen birni a nan, birnin nan mai zuwa muke nema. 15To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa. 16Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa, domin irin waɗannan su ne suke faranta wa Allah rai.

17Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.

18Ku yi mana addu'a, gama mun tabbata muna da lamiri mai kyau, muna kuwa so mu tafiyar da al'amuranmu da halin kirki ne. 19Musamman nake tsananta roƙonku ku yi haka, don a hanzarta a komo da ni a gare ku.

Sa Albarka da kuma Gaisuwa

20Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari, 21yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.

22To, ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi haƙuri da gargaɗina, don taƙaice na rubuto muku. 23Ku sani, an sāki ɗanuwanmu Timoti, da shi ma za mu gan ku, in ya zo da wuri. 24Ku gai da dukan shugabanninku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke daga ƙasar Italiya suna gaishe ku. 25Alharin Ubangiji yă tabbata a gare ku, ku duka. Amin.