Hosea
1Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha'u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra'ila.
2Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”
3Sai ya tafi ya auri Gomer, 'yar Diblayim. Ta yi ciki, ta haifi masa ɗa namiji. 4Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Yezreyel, gama ba da daɗewa ba zan ziyarci gidan Yehu da hukunci saboda jinin da ya zubar a Yezreyel. Zan sa mulkin Isra'ila ya ƙare. 5A wannan rana zan karya bakan Isra'ila a kwarin Yezreyel.”
6Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi 'ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha'u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama'ar Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata. 7Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”
8Sa'ad da ta yaye Ba-jinƙai, ta sāke ɗaukar ciki, ta haifi ɗa namiji. 9Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
10“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, “‘Ku ba mutanena ba ne,” Za a ce, “‘Ku mutanen Allah ne mai rai.”
11Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya, Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya. Za su shugabanci ƙasar Gama ranahakuncir Yezreyel babba ce.”
1“Ka ce wa 'yan'uwanka maza, “‘Ku mutanena ne,” ka kuma ce wa 'yar'uwarka, “‘Kin sami jinƙai!”
2Ku roƙi uwarku, Gama ita ba matata ba ce, Ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta ta daina karuwancinta, Ta rabu da masu rungumar mamanta.
3In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici, In bar ta kamar ran da aka haife ta. In maishe ta kamar jeji, In bar ta kamar busasshiyar ƙasa, In kashe ta da ƙishi.
4Ba zan yi wa 'ya'yanta jinƙai ba, Domin su 'ya'yan karuwanci ne
5Gama uwarsu ta yi karuwanci. Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya. Gama ta ce, “‘Zan bi samarina Waɗanda ke ba ni ci da sha, Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.”
6“Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya, Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.
7Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba. Za ta neme su, amma ba za ta same su ba. Sa'an nan za ta ce, “‘Zan koma wurin mijina na fari, Gama zamana na dā ya fi na yanzu!”
8“Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai, Da azurfa, da zinariya da yawa Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.
9Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa, Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilin Waɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.
10Yanzu zan buɗe tsiraicinta A idon samarinta, Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.
11Zan sa ta daina farin cikinta, Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata, Da hutawar ranar Asabar, Da ƙayyadaddun idodinta.
12Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaure Waɗanda take cewa, “‘Waɗannan su ne hakkina Wanda samarina suka ba ni.” Zan sa su zama kurmi, Namomin jeji su cinye su.
13Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al. A kwanakin nan takan ƙona musu turare, Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai, Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.” In ji Ubangiji.
14“Don haka, ga shi, zan rarrashe ta, In kai ta cikin jeji, In ba ta magana.
15Can zan ba ta gonar inabi, In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege. A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta, Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.
16Ni Ubangiji na ce, a waccan rana Za ta ce da ni, “‘Mijina,” ba za ta ƙara ce da ni Ba'al ba.
17Zan kawar da sunayen Ba'al daga bakinta. Ba za a ƙara kiransu da sunayensu ba.
18“A waccan rana zan yi alkawari Da namomin jeji, da tsuntsaye, Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra'ila. Zan kuma kakkarya baka da takobi, In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar, Sa'an nan za su yi zamansu lami lafiya.
19Zan ɗaura aure da ke cikin adalci, Da bisa kan ka'ida, da ƙauna.
20Zan ɗaura aure da ke cikin aminci, Za ki kuwa sani, ni ne Ubangiji.
21“A waccan rana, zan amsa wa sammai, Su kuma za su amsa wa ƙasa.
22Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, da ruwan inabi, da mai, Su ma za su amsa wa Yezreyel.
23Zan dasa ta a ƙasa domin kaina. Zan kuma yi wa “‘Ba-jinƙai,” jinƙai, In kuma ce wa “‘Ba-mutanena ba,” “‘Mutanena!” Su ma za su ce, “‘Kai ne Allahna!”
1Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka sāke tafiya, ka ƙaunaci karuwa wadda take tare da kwartonta. Ka ƙaunace ta kamar yadda ni Ubangiji nake ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da ya ke suna bin gumaka, suna ƙaunar wainar zabibi da aka miƙa wa gumaka.”
2Sai na ba da sadakinta a bakin tsabar azurfa goma sha biyar, da buhu biyu na sha'ir. 3Sa'an nan na ce mata, “Ki keɓe kanki kwanaki da yawa domina, kada ki yi kwartanci, ki kwana da wani, ni kuma ba zan shiga wurinki ba.” 4Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida. 5Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.
1Ya ku mutanen Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji, Gama Ubangiji yana da shari'a da ku, ku mazaunan ƙasar. “Gama ba gaskiya, ko ƙauna, Ko sanin Ubangiji a ƙasar.
2Akwai rantsuwa, da ƙarya, da kisankai, da sata, da zina, Da kama-karya, da zub da jini a kai a kai.
3Saboda haka ƙasar za ta yi makoki, Dukan waɗanda ke zaune a cikinta za su yi yaushi. Namomin jeji kuma, da tsuntsaye, da kifaye za su ƙare.
4“Duk da haka kada wani ya sa wa mutum laifi, Kada wani kuma ya tsautar. Da ku nake magana, ku firistoci.
5Za ku yi tuntuɓe da rana, Annabi kuma zai yi tuntuɓe tare da kai da dare, Ni kuwa zan hallaka mahaifiyarku.
6Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tun da ya ke sun ƙi ilimi, Ni ma na ƙi ku da zan firist ɗina. Tun da ya ke kun manta da umarnan Allahnka, Ni ma zan manta da 'ya'yanku.
7“Yawan ƙaruwar firistoci, yawan ƙaruwar zunubi. Zan sāke darajarsu ta zama kunya.
8Suna ciyar da kansu da zunubin mutanena, Suna haɗamar ribar muguntarsu.
9Kamar yadda mutane suke, haka firistocin suke, Zan hukunta su saboda al'amuransu, Zan sāka musu gwargwadon ayyukansu.
10Za su ci, amma ba za su ƙoshi ba. Za su yi karuwanci, amma ba za su ƙaru ba. Gama sun rabu da Ubangiji don su bauta wa gumaka.
11“Karuwanci, da ruwan inabi, Da ruwan inabin da bai sa hauka ba sukan kawar da hankali.
12Mutanena sukan yi tambaya a wurin abin da aka yi da itace, Sandansu yakan faɗa musu gaiɓu, Gama ruhun karuwanci ya ɓad da su, Sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci.
13Suna miƙa sadaka a bisa ƙwanƙolin duwatsu. Suna yin hadaya a bisa tuddai, Da kuma a gindin itacen oak, da aduruku, da katambiri, Domin suna da inuwa mai kyau. “Don haka 'ya'yanku mata suke karuwanci, Surukanku mata suke yin zina.
14Ba zan hukunta 'ya'yanku mata sa'ad da suka yi karuwanci ba, Ko kuwa surukanku mata sa'ad da suka yi zina ba, Gama mazan da kansu sukan shiga wurin karuwai. Sukan miƙa sadaka tare da karuwai a Haikali, Mutane marasa fahimi za su lalace.
15“Ko da ya ke mutanen Isra'ila suna karuwanci, Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi. Kada ku tafi Gilgal, Ko ku haura zuwa Bet-awen. Kada ku yi rantsuwa da cewa, “‘Har da zatin Ubangiji!”
16Mutanen Isra'ila masu taurinkai ne kamar alfadari. Ta yaya Ubangiji zai yi kiwonsu Kamar 'ya'yan tumaki a makiyaya mai fāɗi>
17Mutanen Ifraimu sun haɗa kai da gumaka, Sai a rabu da su.
18Su taron mashaya ne kawai, Karuwai ne kuma. Suna ƙaunar abin kunya.
19Iska ta ƙunshe su cikin fikafikanta. Za suji kunyar bagadansu.”
1“Ku ji wannan, ya ku firistoci! Ku saurara, ya mutanen Isra'ila! Ku kasa kunne, ya gidan sarki! Gama za a yi muku hukunci, Domin kun zama tarko a Mizfa, Da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.
2Sun tayar, sun yi zurfi cikin zunubi, Zan hore su duka.
3Na san Ifraimu, Isra'ila kuma ba a ɓoye take a gare ni ba. Gama Ifraimu ta yi aikin karuwanci, Isra'ila kuma ta ƙazantu.
4“Ayyukansu ba su bar su Su koma wurin Allahnsu ba, Gama halin karuwanci yana cikinsu, Don haka kuma ba su san Ubangiji ba.
5Girmankan mutanen Isra'ila yana ba da shaida a kansu. Mutanen Ifraimu za su yi tuntuɓe cikin laifinsu. Mutanen Yahuza kuma za su yi tuntuɓe tare da su.
6Da garkunan tumaki da na awaki, da na shanunsu Za su tafi neman Ubangiji, Amma ba za su same shi ba, Gama ya rabu da su.
7Sun ci amanar Ubangiji. Su haifi shegu. Yanzu amaryar wata za ta cinye su da gonakinsu.
8“Ku busa ƙaho cikin Gibeya, Ku busa kakaki cikin Rama, Ku yi gangami cikin Bet-awen, Ku yi rawar yaƙi, ya ku Biliyaminu!
9Ifraimu za ta zama kango a ranar hukunci. A kabilan Isra'ila na sanar da abin da zai faru, ba makawa.
10“Shugabannin Yahuza sun zama kamar masu cin iyaka, Zan zubo musu da fushina kamar ruwa.
11An danne Ifraimu, shari'a ta murƙushe ta, Domin ta ƙudura ta bi banza.
12Domin haka na zama kamar asu ga Ifraimu, Kamar ruɓa ga mutanen Yahuza.
13“Sa'ad da Ifraimu ta ga ciwonta, Yahuza kuma ta ga rauninta, Sai Ifraimu ta aika zuwa Assuriya, Wurin babban sarki. Amman ba zai iya warkar da ciwonki, ko rauninki ba.
14Zan zama kamar zaki ga Ifraimu, Kamar sagarin zaki ga mutanen Yahuza. Ni kaina zan yayyage, in yi tafiyata. Zan ɗauka, in tafi, ba wanda zai yi ceto.
15“Zan koma wurin zamana Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni. A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”
1Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji, Gama shi ne ya yayyaga, Shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.
2Bayan kwana biyu zai rayar da mu. A rana ta uku kuwa zai tashe mu Mu yi zammanmu a gabansa.
3Mu nace domin mu san Ubangiji Zuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari. Zai zo wurinmu kamar ruwan sama, Kamar ruwan bazara da ke shayar da ƙasa.”
4Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu? Me zan yi da ke, ya Yahuza? Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi, Kamar kuma raɓar da ke watsewa da wuri.
5Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu, Na karkashe su da maganar bakina. Hukuntaina suna kama da hasken da ke ketowa.
6Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba, Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.
7“Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu, Sun ci amanata.
8Gileyad gari ne na masu aikata mugunta. Tana da tabban jini.
9Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, Hakanan firistoci suka haɗa kansu Don su yi kisankai a hanyar Shekem, Ai, sun aikata mugayen abubuwa.
10Na ga abin banƙyama a cikin Isra'ila, Karuwancin Ifraimu yana wurin, Isra'ila ta ƙazantar da kanta.
11“Ku kuma, ya mutanen Yahuza, an shirya muku ranar girbi, A lokacin da zan mayar wa mutanena da dukiyarsu.”
1“Sa'ad da zan warkar da mutanen Isra'ila, Sai zunubin Ifraimu da muguntar Samariya su bayyana, Gama suna cin amana. Ɓarawo yakan fasa, ya shiga, 'Yan fashi suna fashi a fili,
2Amma ba su tunani, Cewa zan tuna da dukan muguntarsu. Yanzu ayyukansu sun kewaye su, Ina ganinsu.
3“Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu, Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
4Dukansu mazinata ne, Suna kama da tanda da aka zafafa, Wadda matoyi ya daina iza mata wuta, Tun daga lokacin cuɗe kullu Har zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.
5A ranar bikin sarki, Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi. Yakan yi cuɗanya da shakiyai.
6Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu. Fushinsu na ci dare farai, Da safe fushinsu yana ci ba-ba kamar harshen wuta.
7“Dukansu suna da zafi kamar tanderu. Suna kashe masu mulkinsu. Dukan sarakunansu sun faɗi. Ba wanda ya kawo mini kuka.”
8Ubangiji ya ce, “Mutanen Ifraimu sun haɗa kansu da al'ummai, Sun zama kamar wainar da ba a juya ba.
9Baƙi sun cinye ƙarfinsu, su kuwa ba su sani ba, Furfura ta faso musu, amma ba su sani ba.
10Girmankan mutanen Isra'ila ya kai ƙararsu, Duk da haka ba wanda ya komo wurin Ubangiji Allahnsu, Ba su kuwa neme shi ba.
11Ifraimu kamar kurciya take, marar wayo, marar hankali, Takan tafi Masar da Assuriya neman taimako.
12Lokacin da suke tafiya, zan shimfiɗa musu ragata, Zan saukar da su ƙasa kamar yadda akan yi wa tsuntsun da ke tashi sama. Zan hukunta su saboda mugayen ayyukansu.
13“Tasu ta ƙare, gama sun ratse, sun rabu da ni. Halaka za ta auka musu domin sun tayar mini. Ko da ya ke zan cece su, duk da haka suna faɗar karya a kaina.
14Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.
15Ko da ya ke na horar da su, na ƙarfafa damatsansu, Duk da haka suna shirya mini maƙarƙashiya.
16Sun juya mini baya, suna bin gunkin nan Ba'al. Suna kama da tankwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi Saboda maganganunsu na fariya. Za su zama abin ba'a a ƙasar Masar.”
1Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki, Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji, Domin mutanena sun ta da alkawarina, Sun kuma keta dokokina.
2Sun yi kuka a wurina, Suna cewa, “‘Ya Allah, mu Isra'ila mun san ka!”
3Isra'ila ta ƙi abin da ke mai kyau, Don haka abokan gāba sun fafare ta.
4“Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba. Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba. Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu, Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.
5Ya mutanen Samariya, ina ƙin maraƙinku na siffa. Ina jin haushinsu ƙwarai! Sai yaushe za su rabu da gumaka>
6Ai, mai aikin hannu ne ya yi shi a Isra'ila! Gunki ne ba Allah ba ne. Za a farfashe siffar maraƙin Samariya.
7Gama sun shuka iska Don haka zu su girbe guguwa. Hatsin da ke tsaye ba shi da zangarniya, Ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,
8Isra'ila kamar kowace al'umma ce. Suna cikin al'ummai Kamar kaskon da ba shi da amfani,
9Gama sun haura zuwa Assuriya, Kamar jakin jeji da ke yawo shi kaɗai. Mutanen Ifraimu sun yi ijara da abokan tsafinsu.
10Ko da ya ke sun yi ijara da abokai daga cikin al'ummai, Yanzu zan tattara su, in hukunta su. Sa'an nan za su fara ragowa, Ta wurin tunanin nawayar Sarkin sarakuna.
11“Da ya ke Ilfraimu ta yawaita bagadan zunubi, Sun zama mata bagadai na yin zunubi.
12Ko da na rubuta mata dokokina sau kam, Za ta ɗauke su wani baƙon abu ne kawai.
13Suna jin daɗin miƙa hadayu don cin naman, Amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Ubangiji zai tuna da muguntarsu, Zai hukunta su saboda zunubansu. Za su koma Masar.
14“Gama mutanen Isra'ila sun manta da Mahaliccinsu, Sai sun gina manyan gidaje masu daraja. Mutanen Yahuza kuma sun yawaita biranensu masu garu, Amma ni Ubangiji, zan aika da wuta a kan biranensu, Ta ƙone fādodinsu.”
1Kada ku yi farin cikin, ya mutanen Isra'ila! Kada ku yi murna kamar sauran mutane! Gama kun yi karuwanci, kun rabu da Allahnku. Kuna ƙaunar ijarar karuwanci a kowane masussuka.
2Masussuka da wurin matsa ruwan inabi ba za su ciyar da su ba. Sabon ruwan inabi kuma ba zai ishe su ba.
3Ba za su zauna a ƙasar Ubangiji ba, Amma mutanen Ifraimu za su koma Masar. Za su ci haramtaccen abinci a Assuriya.
4Ba za su yi wa Ubangiji hadaya ta sha ba. Ba za su faranta zuciyarsa da sadakoki ba. Abincinsu zai zama irin na masu makoki. Duk wanda ya ci shi zai haramta. Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai, Ba za su kai shi Haikalin Ubangiji ba.
5Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar idi? Da a ranar idin Ubangiji>
6Ga shi kuma, suna tafiya zuwa halaka, Masar za ta tattara su, Memfis za ta binne su. Ƙayayuwa za su mallaki abubuwan tamaninsu na azurfa. Sarƙaƙƙiya za ta tsiro a cikin alfarwansu.
7Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso, Isra'ila za ta sani! An ce annabi wawa ne, Mutumin da ke da ruhu kuwa mahaukaci ne, Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.
8Ifraimu mai tsaro ne a gaban Allahna, annabi kuwa, Duk da haka sun zama kamar mai kafa tarkon kama tsuntsu, a farkon kaka. Akwai ƙiyayya a cikin Haikalin Allahnsu.
9Sun yi zurfi cikin rashin gaskiya Kamar a kwanakin Gibeya, Ubangiji zai tuna da muguntarsu. Zai hukunta su saboda zunubansu.
10Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi, Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure, Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al. Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.
11Darajar Ifraimu za ta tashi kamar tsuntsu, Ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki!
12Ko sun goyi 'ya'ya, Zan sa su mutu tun ba su balaga ba. Tasu ta ƙare sa'ad da na rabu da su!”
13Ya Ubangiji, na ga yadda Ifraimu Ta mai da 'ya'yanta ganima Tana fitar da su zuwa wurin yanka.
14Ya Ubangiji, me zan ce ka ba su? Me za ka ba su? Ka ba su cikin da ba ya haihuwa da busassun mama.
15Ubangiji ya ce, “Kowace irin muguntarsu tana a Gilgal, A can na ƙi su! Saboda mugayen ayyukansu, zan kore su daga ƙasata, Ba kuma zan ƙaunace su ba. Dukan shugabanninsu 'yan tayarwa ne.
16An ka da mutanen Ifraimu, saiwarsu ta bushe. Ba za su yi 'ya'ya ba. Ko ma sun haihu, zan kashe 'ya'yan nan nasu waɗanda suke ƙauna.”
17Allahna zai ƙi su Domin ba su yi masa biyayya ba. Za su zama masu yawo cikin al'ummai.
1Isra'ila kurangar inabi ce mai bansha'awa Wadda ke ba da 'ya'ya da yawa. Ƙara yawan arzikinsu, Ƙara gina bagadansu. Ƙara yawan wadatar ƙasarsu. Ƙara kyautata ginshiƙansu.
2Zuciyarsu ta munafunci ce, Yanzu tilas za su ɗauki hakkin laifinsu, Ubangiji zai farfashe bagadansu da ginshiƙansu.
3Gama yanzu za su ce, “Ba mu da sarki, Domin ba mu ji tsoron Ubangiji ba. Amma me sarki zai yi mana?”
4Surutai kawai suke yi, Suna yin alkawaran ƙarya, Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona.
5Mazaunan Samariya suna rawar jiki Domin ɗan maraƙin Bet-awen, Mutane za su yi makoki dominsa, Firistoci matsafa, za su yi kururuwa dominsa, Da kuma darajarsa wadda ta rabu da shi.
6Za a kai ɗan maraƙin a Assuriya Don a biya wa sarki haraji. Za da kunyatar da Ifraimu, Isra'ila kuwa za ta ji kunya saboda shawararta.
7Sarakunan Samariya za su ɓace, Kamar kumfa a bisa ruwa.
8Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi, Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu. Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!” Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”
9Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra'ila! Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba. Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba>
10Zan fāɗa wa waɗannan mutane masu zunubi, in hukunta su. Za a tattara al'ummai, su yi gāba da su, Za a hukunta su saboda yawan zunubansu.
11“Ifraimu horarriyar karsana ce, Wadda ke jin daɗin yin sussuka, Amma na sa wa kyakkyawan wuyanta karkiya, Na sa Yahuza ta ja garmar noma, Yakubu kuwa za ta ja garmar bajiya.
12Ku shuka wa kanku adalci, Kugirbe albarkun ƙauna, Ku yi kautun saurukanku, Gama lokacin neman Ubangiji ya yi, Domin ya zo, ya koya muku adalci.
13Kun shuka mugunta, Kun girbe rashin adalci, Kun ci amfanin ƙarya. “Da ya ke dogara ga hanyarku da ɗumbun sojojinku,
14Domin haka hayaniyar yaƙi za ta tashi a tsakanin jama'arku. Dukan kagaranku za a hallaka su. Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaƙi. An fyaɗa uwaye da 'ya'yansu a ƙasa.
15Haka za a yi muku, ya mutanen Betel, saboda yawan muguntarku. Da asuba za a datse Sarkin Isra'ila.”
1“A lokacin da Isra'ila ke yaro, na ƙaunace shi, Daga cikin Masar na kirawo ɗana.
2Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini, Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi, Suna ƙona turare ga gumaka.
3Ko da ya ke ni ne na koya wa Ifraimu tafiya. Na ɗauke su a hannuna, Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.
4Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna, Na zama musu kamar wanda ke ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu. Na sunkuya, na ciyar da su.
5“Ba su koma ƙasar Masar ba, Amma Assuriya za ta zama sarkinsu Gama sun ƙi yarda su koma wurina.
6Takobi zai ragargaje biranensu, Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu, Zai cinye su domin muguwar shawararsu.
7Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da ya ke an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.
8“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.
9Ba zan aikata fushina mai zafi ba, Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba, Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Maitsarki wanda ke tsakiyarku, Ba zan zo wurinku da hasala ba.
10“Za su bi Ubangiji, Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri 'Ya'yansa za su zo da rawar jiki da yamma.
11Da sauri za su zo kamar tsuntsaye daga Masar, Kamar kurciyoyi daga ƙasar Assuriya, Zan komar da su gidajensu, ni Ubangiji na faɗa.”
12Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi, Jama'ar Isra'ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta, Yahuza kuma ta tayar wa Allah, Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.
1Ifraimu tana kiwon iska, Tana ta bin iskar gabas dukan yini. Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya. Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya, Tana kai mai a Masar.”
2Ubangiji yana da magana game da mutanen Yahuza, Zai hukunta Isra'ila saboda hanyoyinta, Zai sāka mata gwargwadon ayyukanta.
3A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa, Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.
4Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye. Ya yi kuka, ya roƙi albarka. Ya sadu da Allah a Betel, A can Allah ya yi magana da shi.
5Ubangiji Allah Mai Runduna, Sunansa Ubangiji,
6Sai ku koma wurin Allahnku, Ku yi alheri, ku yi adalci, Ku saurari Allahnku kullayaumin.
7Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda ke da ma'aunin algus a hannunsa. Yana jin daɗin yin zalunci.
8Mutanen Ifraimu sun ce, “‘Hakika, mun zama attajirai, Mun samar wa kanmu dukiya. A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.”
9Ni ne Ubangiji Allahnku tun daga ƙasar Masar, Zan kuma sa ku zauna cikin alfarwai, Kamar lokatan ƙayyadaddun idodi.
10“Na yi magana da annabawa, Ni ne na ba da wahayi da yawa, Da misalai kuma ta wurin annabawa.
11Idan akwai laifi a Gileyad, Hakika za su zama wofi. A Gilgal ana sadaka da bijimai, Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsu A gyaffan kunyoyin gona.”
12Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram, A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace, Saboda mace ya yi kiwon tumaki.
13Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar, Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.
14Mutanen Ifraimu sun yi muguwar tsokana mai ta da fushi, Domin haka Ubangiji zai ɗora musu hakkin jini a kansu, Zai saka musu cin mutuncin da suka yi.
1Sa'ad da Ifraimu ta yi magana, mutane suka yi rawar jiki. An ɗaukaka ta cikin Isra'ila, Amma ta yi laifi ta wurin bauta gunkin nan Ba'al, Ta kuwa mutu.
2Har yanzu suna ta ƙara yin zunubi, Suna yi wa kansu gumaka na zubi, Da gwaninta sukan yi gumaka da azurfarsu, Dukansu aikin hannu ne. Sukan ce, “Ku miƙa wa waɗannan hadayu!” Mutane sukan sumbaci siffofin maruƙa.
3Don haka za su zama kamar ƙāsashi da akan yi da safe, Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri. Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka, Ko kuwa kamar hayaƙin da ke fita ta bututu.
4Ubangiji ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku Tun daga ƙasar Masar. Banda ni ba ku san wani Allah ba, Banda ni kuma ba wani mai ceto.
5Ni ne wanda ya san ku a cikin jeji, A ƙasar da ke da ƙarancin ruwan sama.
6Sa'ad da suka sami wurin kiwo, suka ƙoshi, Sai suka yi girmankai, Suka manta da ni.
7Zan zama musu kamar zaki, Kamar damisa zan yi kwanto a gefen hanya.
8Zan auka musu kamar beyar, Wadda aka ƙwace mata 'ya'ya. Zan yage ƙirjinsu, in cinye su kamar zaki, Kamar mugun naman jeji zan yayyage su.
9“Zan hallaka ku, ya mutanen Isra'ila! Wanene zai taimake ku>
10Yanzu ina sarkinku da zai cece ku? Ina kuma dukan shugabanninku da za su kāre ku? Su waɗanda kuka roƙa, kun ce, “‘Ku naɗa mana sarki da shugabanni.”
11Da fushina na naɗa muku sarki, Da hasalata kuma na tuɓe shi.
12“An ƙunshe muguntar Ifraimu, Zunubinsa kuwa an ajiye shi a rumbu.
13Naƙudar haihuwarsa ta zo, Amma shi wawan yaro ne, Bai fito daga mahaifar ba.
14Zan fanshe su daga ikon lahira. Zan fanshe su daga mutuwa. Ya mutuwa, ina annobanki? Ya kabari, ina halakarka? Kan kawar da juyayi daga wurina.
15Ko da ya ke Isra'ila tana bunƙasa kamar ciyayi, Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji, Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu, Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da ke cikin taskarsu.
16Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, Gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, A kuma tsage matanta masu ciki.”
1Ya mutanen Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku, Gama zunubinku ya sa kun yi tuntuɓe.
2Ku komo wurin Ubangiji, ko roƙe shi, Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu, Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.
3Assuriya ba za mu hau dawakai ba. Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu, “‘Kai ne Allahnmu,” ba. A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”
4Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu. Zan kuma ƙaunace su sosai, Gama fushina zai huce.
5Zan ama kamar raɓa ga Isra'ila, Isra'ila za ta yi fure kamar lili, Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.
6Tohonta zai buɗo, Kyanta zai zama kamar itacen zaitun, Ƙashinta kuwa kamar itacen al'ul na Lebanon.
7Waɗanda za su komo, za su zauna a inuwarta, Za su yi noman hatsi da yawa. Za su yi fure kamar kurangar inabi. Ƙanshinsu zai zama kamar ruwan inabi na Lebanon.
8Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka? Ni ne wanda ke amsa muku, mai lura da ku kuma. Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar. Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”
9Duk wanda ke da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan. Duk wanda ke da ganewa, bari ya san abubuwan nan, Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu, Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.