HIKIMAR SULEMANU

1. Ladan Adalci

Ku ƙaunaci yin adalci, ya ku sarakunan duniya,

      A halin kirkinku ku tuna da Ubangiji

      Ku neme shi da zuciya daya.

2 Gama waɗanda ba su jarraba shi ba, za su same shi,

      Zai bayyana kansa ga waɗanda suka amince da shi.

Masu mugun tunani za su rabu da Allah,

      In wawaye sun jarraba ikonsa, zai hore su.

4 Gama hikima ba za ta shiga zuciyar mai aikata mugunta ba,

      Ba ta ma tarayya da wanda ke aikata saɓo.

5 Gama horo tsattsarkan ruhu ne, yana ƙyamar ƙarya,

      Yana ma yin nesa da yawan soki burutsu,

      In an aikata rashin adalci, sai ya damu.

6 Ai, hikima hali ne na ƙaunar yan adam,

      Ba ma za ta yafe wa mai saɓo abin da ya hurta ba.

      Gama Allah ya san burin mai saɓo.

Allah ne gwanin mabinciken zuciyarsa,

      Ya ma san dukan abin da yake faɗa.

7 Gama Ruhun Ubangiji ya cika dukan duniya,

      Ya kuma san dukan abu, har ma hirar da mutane ke yi.

Don haka ba wanda zai aikata rashin adalci, ya kwana lafiya,

      Ai, kowa ya yi, a yi masa horo.

9 Gama za a bincika tunanin mugun mutum.

      Ubangiji kuma zai ji duk abin da ya faɗa,

      A kuma hore shi saboda rashin bin sharia.

10 Allah mai kishi ne, yana sauraron kowa,

      Ai, raɗe‑raɗen gunaguni ma ba a ɓoye suke gare shi ba.

11 Don haka ku rabu da gunaguni marasa amfani,

      A kuma guji wa ɗora wa Allah laifi.

Gama ba abin da aka hurta a asirce, da ba zai tonu ba,

      Baki ke yanka wuya.

12 Kada ku jawo wa kanku mutuwa ta aikinku na baudewa,

      Kada ma ku hallaka kanku da abin da kuke yi,

13 Gama Allah bai halicci mutuwa ba.

      Ba ya ma farin ciki in yan adam sun halaka.

14 Ya halicci dukan abubuwa domin su wanzu,

      An kuma yi dukan abubuwan duniya don su biya wa mutum bukata.

Ba ma dafin da zai hallaka mutum a cikinsu.

      Mutuwa ma ba ta da mulki a duniya,

      15 Gama adalci madawwamin abu ne.

Masu Saɓo na More wa Duniya

16 Amma masu saɓo ne suke kiran mutuwa ta wurin aikinsu da maganarsu,

      Sun ɗauke ta abuya, suna marmarinta.

Sun ƙulla yarjejeniya da ita.

      Domin sun cancanci zama abokanta.

2.

1 A cikin soki burutsun masu saɓo suka ce,

      Ba mu da tsawon rai,

Kwanakinmu cike suke da yawan faɗi ka tashi,

      In ciwon ajali ya kama mutum, ba magani,

      Ba ma wanda ya taɓa dawowa daga lahira,

2 Gama ba da gangan an haife mu ba,

      Daga baya sai ka ce ba mu taɓa zama ba.

Ai, numfashinmu ma hayaƙi ne,

      Azancinmu kuma tartsatsin wuta ne kawai daga zuciyarmu.

3 In an kashe wutar, sai jikin ya koma toka,

      Sai ruhu ya wuce kamar iska.

Nan da nan sai a mance da sunamnu,

      Ba ma wanda zai tuna da ayyukanmu.

Ranmu zai shuɗe kamar girgije,

      Zai kakkaɓe kuma kamar raɓa

Wadda hasken rana ke kora,

      Zafinta kuma ke rinjaya.

5 Gama ranmu yana shuɗewa kamar inuwa,

      In kuma kwana ya ƙare, ba tsimi ba dabara,

      An ƙaddara mutuwarmu, ba mai iya ƙetarewa.

6 Don haka, duk ku zo mu more wa abubuwan da ke akwai,

      Mu more a cikin ƙuruciyarmu.

7 Mu sha barasa, mu sa turaren dan goma,

      Duk inda za a faɗi, a tashi gidan biki da mu,

8 Mu naɗa wa kamnu furannin wardi

      kafin sun yanƙwane.

9 Mu yi fasikancinmu a kowane wuri,

      Mu yi farin cikinmu a koina,

      Gama raboranu ke nan, shi ne katarinmu.

Masu Sabo na Tsananta Adalai

10 Mu tsananta wa gajiyayyen matalauci, in ji masu saɓo,

      Kada ma mu ƙyale gwauruwa,

Kada mu girmama tsoho mai

      hurhura wanda ya kwana biyu.

11 Adalcinmu shi ne mu gwada karfi,

      Gama kumama bai amfana kome ba.

12 Amma bari mu yi fakon adali, tun da ya dame mu.

      Gama yana tsauta mana a kan abubuwan da muke yi,

Yana zargin mun keta doka,

      Yana sa mana laifi kan bauɗewarmu,

13 Yana nuna ya san Allah,

      Har yana kiran kansa baran Ubangiji.

14 Ya hana mu sakat,

      Har ganinsa ma yana damunmu.

15 Zamansa ya bambanta da na sauran mutane,

      Hanyoyinsa dabam suke.

16 Ya mai da mu jujin ƙofar guda,

      Ya ƙi maamala da mu, ya haramta mu,

Ya ce adalai a raye ko a mace, za su yi farin ciki,

      Ya kuma yi fariya, cewa Allah ubansa ne.

17 Bari mu gani ko maganarsa za ta zama gaskiya,

      Mu bincike abin da zai same shi a lokacin da zai ƙaura.

18 In adali ɗan Allah ne, ai, Allah zai kāre shi,

      Ya cece shi daga hannun maƙiyansa.

19 Bari mu gasa masa azaba da gangan,

      Domin mu gane iyakar sanyin halinsa,

      Mu kuma ga tsananin dauriyarsa.

10 Mu hukunta shi ta kisan cin mutunci,

      Gama za a cece shi, in ji shi.

21 Haka masu saɓon Allah suka ƙulla a ransu,

      Amma sun baude,

      Gama muguntarsu ta makanta su.

22 Ba su san asiran Allah ba,

      Ba su fatar samun sakamakon nan na zuciya mai tsabta ba,

      Ba su ma san ladan da adalai za su samu ba.

23 Ai, Allah bai halicci mutum don halaka ba,

      Ya halicce shi a cikin surarsa,

      Da kamannin madawwamin zatinsa.

24 Gama ta kishin Iblis ne mutuwa ta shigo duniya,

      Waɗanda suke na Iblis kuwa, su ne za su ɗanɗana ta.

3. A kan Lahirar Adalai da ta Masu Saɓo

1 Amma ruhohin adalai suna a ikon Allah,

      Ba ko wahalar da za ta same su.

2 A ganin wawaye, ai, sun mutu muɗus,

      Barin dunyarsu ya zama rashin katari,

3 Kauracewarsu, ta zama halaka,

      Amma a ainihin gaskiya cikin jin daɗi suke.

4 Ko sun sha horo a idon mutane,

      Sun tabbata za su sami madawwamin rai.

5 Tun da ya ke an ɗan hore su, za su amfana gaba da kima,

      Gama Allah ya jarraba su,

      Ya ga sun kai bante, ya amince da su.

6 Kamar zinariya a maƙera, ya gwada su,

      Ya yi naam da su kamar hadayar ƙonawa.

7 A ranar tashin kiyama za su haskaka,

      Za su ci nasara kamar wuta da saɓi.

8 Za su sharaanta alummai, su mallaki jamaa,

      Ubangiji ne zai zama sarkinsu har abada.

9 Waɗanda suka amince da Allah za su gane gaskiya,

      Amintattu za su zauna da shi a cikin ƙauna,

Domin tsarkakansa suna samun alheri da jinƙai,

      Waɗanda ya zaɓa ma, yana kula da su.

10 Amma za a hori masu saɓon Allah ta hujarsu,

      Gama sun ƙi sauraren adalci, sun yi wa Ubangiji tawaye.

11 Waɗanda suka raina hikima da horo miskilai ne,

      Fatar banza gare su, aikinsu ba shi da amfani,

      Ya ma zama a banza.

12 Matansu ba su da azanci, yayansu maƙetata ne,

      An ma laanta jikokinsu.

A kan Marasa Yaya

13 Mai albarka ce juyar da ba ta ƙazantu ba,

      Wato ita wadda ba ta ƙetare doka ba,

      Wadda take da yabanya a ranar tashin kiyama.

14 Haka kuma dandaƙaƙƙe yake wanda bai aikata saɓo ba,

      Bai ma yi abubuwan magudi ba ga Ubangiji.

Gama shi ne za a ba zaɓaɓɓen ladan aminci,

      Za a ƙara masa da wani muhimmin rabo a cikin Haikalin Allah.

15 Daukaka ce amfanin kyakkyawan aiki,

      Ganewa tana fitowa daga tushen da ba ya tumɓuko.

16 Yayan fasikai ba su kai bante ba,

      Za a shafe zuriyar mazinata.

17 Gama ko sun wanzu, za a san su a kan shakiyanci,

      Daga ƙarshe ma ba mai girmama su in sun tsufa.

18 In kuma sun mutu ba zato ba tsammani, sun damu,

      Ba za a yi musu taaziyya a ranar sharia ba.

19 Ai, ko ƙarshen kabilar marar adalci da bantausayi yake!

4.

1 Gara rashin yaya na mai adalci,

      Tun da ya ke za a yi ta tunawa da shi kullum,

      Da ya ke Allah da mutane sun yarda da shi.

2 In yana da rai, mutane za su ɗauki hannunsa

      In ya mutu kuma za su yi ta begensa.

Har abada za a yi ta yi masa shagalin bangirma,

      Domin ya yi nasara a kan gasa,

      An ma ba shi lada mai tsabta.

3 Amma taron marasa adalci ba zai yi wata haiba ba,

      Tushen shege ba zai yi ƙarƙo ba,

      Ba ma zai kafa tushe mai makama ba.

4 Gama ko sun yi rassa, da kaka kawai za su yi toho,

      Ba su kahu sosai ba, iska za ta kaɗa su,

      Gawurtacciyar iska ce ma za ta tuƙe su.

5 An yanke rassansu kafin su yi girma,

      Yayansu ba su da amfani,

Ba za su nuna ba, a ci.

      Ba a iya yin kome da su.

6 Yayan da aka haifa ta fasikanci

      Su ne shaidun ƙetar iyayensu in an bi asali.

A kan Mutuwar da ta Yi wa Adali Garaje

7 Amma adali, ko ya mutu da sauri, zai huta lafiya,

      8 Gama yawan shekaru ba su ne dattako ba,

      Ba ma a kula da yawan shekaru.

9 Amma ganewa ita ce hurhurar jamaa,

      Rai kuma marar saiɓi shi ne yawan shekaru.

10 Saboda faranta wa Allah rai an so shi kwarai,

      An kuma sauya zamansa daga cikin masu saɓo.

11 Sai aka tsame shi, don kada ƙeta ta sauya ganewarsa,

      Ko hila ta ruɗi ransa.

12 Gama dabarar ƙeta na ɓata abubuwa masu kyau,

      Ai, guguwar shaawa ce ke sauya azancin mai gaskiya,

13 Ya bunƙasa a ɗan lokaci,

      Amma waɗansu sun yi shekarun maiko.

14 Gama ransa ya gamshi Allah,

      Saboda haka ne ma, ya fauce shi daga cikin maƙetata.

Amma alummai sun gani, ba su gane ba,

      Ba su ma fahirnta ba.

15 Waɗanda Allah ya zaɓa suna samun alheri da jinƙai,

      Tsarkakansa ma yana kula da su.

16 Gama adalin da ya mutu zai Iaanta jairin da ke raye,

      Saurayin da ya kai bante da sauri zai Iaanta yawan shekarun tsoho mai saɓo.

17 Gama masu saɓo sun ga karshen mai hikima,

      Ba su kuma gane abin da Ubangiji ya ƙaddara game da shi ba,

      Ba su sani mutuwar da ya yi mafaka ce aka kai shi ba.

18 Sun kalli mai hikima, sun raina shi,

      Amma Ubangiji ya yi musu dariyar raini.

19 Daga baya sai suka zama mushe marar daraja,

      Za a yi musu gwalo a cikin matattu har abada.

Gama zai ƙwala su da kasa, ba kuwa za su iya cewa kome ba.

      Zai tuge su daga tushensu.

Za su ma bushe, su lalace,

      Za su zauna a halin ƙaka naka yi,

      Ba ma za a ƙara tunawa da su ba.

A kan Sharia ta Ƙarshe

A lokacin lissafin saɓonsu za su firgita,

      Yawan saɓonsu zai tashi, ya kuma hukunta su.

5.

1 Saan nan adali zai mike gaba,

      Tsaye a gaban fuskokin waɗanda suka gasa masa azaba,

      Da kuma waɗanda suka raina aikaceaikacensa.

2 Da suka gan shi, za su fāɗi sumammu don tsoro,

      Za su yi matuƙar mamaki yadda aka tsirar da shi ba zato ba tsammani.

3 Za su tuba a zukatansu,

      Za su yi ƙugi a kan ransu da ke shan wuya, su ce,

4 Ai, wannan shi ne wanda muka rika yi wa baa,

      Muka zarge shi, da ya ke mu wawaye ne.

Mun ce irin zamansa hauka ce,

      Mutuwarsa kuma ta Allah wadai.

5 Amma ga shi an lasafta shi a cikin yayan Allah,

      An kuma ba shi rabo a cikin tsarkaka.

6 Lalle mun bauɗe wa hanyar gaskiya,

      Hasken adalci ma bai haskaka mu ba,

      Rana ba ta ɓullo mana ba.

7 Mu yi saɓo da hallaka rayuka, har sun ginshe mu,

      Mun ratse cikin jeji,

      Mun bauɗe wa hanyar Ubangiji.

8 Me girmankanmu ya amfana mana yanzu?

      Me ma wadatarmu da alfarmarmu suka kawo mana?

9 Dukansu sun shuɗe sai ka ce inuwa,

      Ai, ma sai ka ce amon iska mai wucewa.

10 Kamar jirgin ruwa da ya wuce ta kan raƙumin ruwa,

      Wanda ba a iya ganin sawun hanyar da ya bi,

      Ba a ma ganin zāne inda muciyar jirgin ta bi.

11 Ai, ma kamar tsuntsu ne wanda ya tashi ƙoli,

      Wanda ba wani zāne na hanyar da ya bi.

Da yake tashi, fikafikansa na bugun iska,

      Saboda ƙarfinsu suna raba iska.

Da tsuntsun ya kaɗa fiffike, sai ya zarce,

      Amma ba alamar hanyar da ya bi.

12 Ko a lokacin da aka harba kibiya,

      Da ta raba iska, sai iskar ta komo nan da nan ta haɗe,

      Don haka ba za a gane hanyar da kibiyar ta bi ba.

13 Haka ma mu da aka haifa, wam lokaci za mu shude,

      Ba mu kuma da alamar halin kirki da za mu nuna,

      Amma mun hallakar da kanmu saboda ƙetarmu.

14 Ai, begen maƙetata kamar audugar rimi ne wadda iska ke ɗaukewa,

      Kamar ma yayyafi ne wanda iska ke tunkudewa.

Sai ya warwatsu kamar hayaƙi,

      Ya wuce kamar zangon Buzu na kwana ɗaya.

15 Amma adalai za su wanzu har abada,

      Sakamakonsu kuma yana wurin Ubangiji,

      Maɗaukaki ne kuma ke kula da su.

16 Don haka kuwa za su sami mulki mai daraja,

      Da kyakkyawan kambin sarauta daga wurin Ubangiji.

Gama zai rufe su da ikonsa,

      Da dantsensa kuma zai kāre su.

17 Allah zai mai da kishin ƙaunarsa babban makami,

      Ya mai da kukan halitta kayan faɗansa don su kara da maƙiyansa.

18 Zai tufantar da kansa da adalci kamar garkuwa,

      Zai kuma sa hukuncin gaskiya kamar hular kwano.

19 Zai mai da tsabtar zuciya garkuwa,

      20 Zai kaifafa fushinsa kamar takobi,

      Zai sa duniya ta yi gaba da jairai masu ɓaranci.

21 Walƙiya za ta auni wurin da suke daidai,

      Za ta fito daga gizagizai kamar harbin kibiya,

      Ta kai inda aka nufe ta da zuwa.

22 Fushin Allah kamar bakan danko ne yanajeho ƙanƙara.

      Ruwan teku ma zai auku wa abokan gāba na Allah,

      Koguna kuma za su haɗiye su.

23 Gawurtacciyar iska za ta yi gāba da su,

      Za ta ma angaje su kamar ƙaiƙayi.

I, rashin bin sharia zai mai da dukan duniya kufai,

      Rashin adalci ne ke sa hamɓarar da mulkin kasar.

6. A Nemi Hikima

1 Ku saurara, ku sarakuna, ku fahimta kuma,

      Ku yi koyi, ku alƙalan dukan duniya.

2 Ku kasa kunne, ku da ke mulkin jamaa,

      Da waɗanda ke cika gwada wa taron talakawa iko.

3 Gama Allah ne ya ƙaddara muku yin mulki,

      Ikonku kuma daga Maɗaukaki yake,

      Shi ne zai gwada aikinku, ya bincike shawararku.

4 Don ko da ya ke ku bayin mulkinsa ne,

      Ba ku aikata daidai ba,

Kun ma ƙetare sharia,

      Ba ku kuma aikata mifin Allah ba.

5 Zai auko muku da garaje,

      Don za a yi wa masu sarauta sharia, ba sani ba sabo.

6 Daidai ne a gafarta wa talakawa,

      Amma ƙusoshin gari hukuncinsu da girma yake!

7 Ai, Ubangijin duka ba zai tauye don ganin fuska ba,

      Ba zai ma kula da girman mutum ba.

Gama shi ne ya yi babba da ƙarami duka,

      Yana kuma kula da su daidai wa daida,

8 Amma zai bincike ƙusoshin gari ba da rangwame ba.

      9 Ga jawabina nan gare ku, ya ku azzaluman sarakuna

      Domin ku koyi hikima: kada ku bauɗe.

10 Gama waɗanda suka kiyaye abubuwa masu tsarki,

      Su ma za su tsarkaka.

      Waɗanda aka koya wa, su ma sun sami makari.

11 Ku yi begen jawabina,

      Ku neme su, za ku koye su.

12 Hikima, haske gare ta, ba ta kuma dushewa,

      Ba ta da wuyar samuwa ga mai nemanta,

Masu nemanta, ai, samunta suke ta yi.

      13 Tana sanar musu da kanta kafin su farga,

14 Duk wanda ya yi sammakon nemanta ba zai taɓe ba,

      Gama zai same ta tanajiransa a ƙofa.

15 Tunanin hikima ma dabara ce mafificiya,

      Wanda ya tashi nemanta ma,

      Nan da nan zai kuɓuta daga damuwa.

16 Gama tana kewayawa, tana neman masu dacewa da ita,

      Tana ɓullo musu da alheri duk inda suka nufa,

      Tana malalawa a cikin dukan tunaninsu.

17 Begen. horo shi ne tushen shiga hikima,

      Ankara da horo ita ce ƙaunarta,

18 Ƙaunarta kuma ita ce bin kaidodinta.

      Bin sharia tabbatar dawwamar rai ke nan,

19 Dawwamar rai ke sa a matsi Allah,

      20 Don haka begen hikima yana kawo faida.

21 In kuna son sarauta, ku da ke shugabannin alummai,

      Sai ku darajanta hikima, domin ku yi mulki har abada.

Gabatarwar Bayanin Sulemanu a kan Hikima

22 Amma zan bayyana yadda hikima take, da yadda ta wanzu,

      Ba ma zan ɓoye muku asiranta ba.

Amma zan bi ta filla filla, tun daga farkon halitta,

      In bayyana saninta tangaran,

Ba zan ɓoye gaskiya ba.

23 Ba ma zan yi aiki da ƙyashi ba,

      Gama hikima da ƙyashi ba su haɗuwa.

24 Amma yawan masu hikima shi ne fansar duniya,

      Wayayyen sarki shi ne ke kafa jamaarsa kankan,

25 Don haka ku kula da jawabina,

      Zai yi muku amfanin gaske.

7. Sulemanu Kamar Sauran Mutane Yake

1 Ai, ni ma mai mutuwa ne, kamar kowa,

      Jikan mutum na fari da aka halitta daga ƙasa.

      A cikin mace aka siffata ni,

2 Gkin wata goma aka yi ni daga jini

      Da maniyyin wani da morewarsa.

3 Da aka haife ni, irin iskar da kowa ke sha, na sha.

      Na yi rarrafe a ƙasa wadda take asalina,

Na yi kukana yadda dai sauran jarirai ke yi,

      4 Aka naɗe ni a zanen goyo, aka lura da ni.

5 Ba wani sarki da ke da hanyar rayuwa dabam da wannan,

      Amma dukanyan adam hanyar shigowarsu duniya guda ce,

      Haka kuma ta komawa.

Sulemanu ya Girmama Hikima

7 Don haka na yi addua, sai kuwa aka ba ni fahimi,

      Na yi kira, nan da nan aka aiko mini da zuciyar hikima.

8 Na fi sonta da gadon sarauta,

      A ganina gwamma hikima da wadata.

9 Na fi sonta da duwatsu masu daraja,

      Gama zinariya a gare ta kamar ɗan tarin rairayi take,

In an gwada ta da azurfa,

      Azurfa za ta koma kamar yumɓu.

10 Na fi ƙaunar hikima da lafiya da kyan diri,

      Na ma fi son ta da haske,

      Gama haskenta ba ya dushewa.

11 Daga wurin hikima ne dukan abubuwan alheri suka zo mini,

      Tana da wadata iri iri.

12 Sai na ji daɗinsu duka,

      Gama hikima ce ke shugabantarsu,

Duk da haka ban sani ba,

      Ashe, ita ce uwar waɗannan abubuwa.

13 Ba don riba na koye ta ba,

      Zan kuma bayyana ta hankali kwance,

      Ban ɓoye wadatarta ba.

14 Hikima dukiya ce mai dorewa ga yan adam,

      Wadda waɗanda suka rike ta suke kara kusatar Allah,

Gama halayen kirki na horonta ne

      ke sa mutane su sami karɓuwa ga Allah.

Roƙon Taimakon Hikima

Amma ni Allah dai ya ba ni bakin yin magana mai azanci,

      Don in darajanta abubuwan da aka ba ni yadda ya kamata.

Gama shi ne jagoran hikima,

      Shi ne ma jamiin masu basira.

16 Don a hannunsa muke, mu da aikin da muke yi,

      Dukan gwaninta kuma da sanin fannin aikace‑aikace.

17 Gama shi ne ya fahinitar da ni a kan abubuwan da suka wanzu,

      Don in san kaidar duniya,

      Da aikin kowace halittar da ke cikinta.

18 Da farko, da ƙarshe, da kuma ganiyar lokaci,

      Sauyawar rana kudu da arewa, da sauyawar lokaci,

19 Kewayawar shekaru, da matsayin taurari,

      20 Tsabiar dabbobi da halinsu,

Ikon iskoki da tunanin yan adam,

      Itatuwa dabam dabam da amfanin saiwoyinsu.

Na san duk abin asiri da wanda ke a bayyane,

      Gama hikima ce ta koya mini su duka.

Yabon Hikima

A cikin hikima da ganewa,

      Tilo, mai tsarki, wadatacce,

Mai ratsa koina, mai hanzarin tafiya, mai tangarewa,

      Marar aibu, mai tabbata, marar lahani,

Mai kaunar abin kirki, mai ganewa da aniya, wadda ba a tsare ba,

      23 Mai amfana mutane, mai son jamaa,

Kafaffiya, ba waninta, marar damuwa,

      Mai iko duka, mai bincike kome,

Mai ratsa dukan ruhohin masu hanzarin fahimta,

      Masu tsabta, masu tangarewa.

24 Gama hikima ta fi kome hanzari,

      I, tana ratsa kome saboda tsabtarta.

25 Gama ita ce tururi na ikon Allah,

      Ɗaukakar Mai Iko Dukka da ke gudana zahiri,

      Saboda haka ba wani ƙazamin abu da zai kusace ta.

26 Gama ita ce hasken madawwamin haske,

      Madubi marar aibu na ikon Allah,

      Surar alherin Allah ce kuma.

27 Hikima ita kaɗai ce, amma tana iya yin kome,

      Tana sabunta kome, amma ita ba ta sauyawa.

A kowace tsara tana shiga ruhohin masu tsarki,

      Tana mai da su aminan Allah da annabawansa.

      28 Ai, Allah ya fi son abokin zaman hikima da kome.

29 Hikima ta fi rana haske,

      Ta ma fi sansanin taurari.

      In a gwada da haske ne, duk ta yi musu zakara,

30 Gama dare yana duhunta hasken rana,

      Amma ƙeta ba ta rinjayar hikima.

8.

1 Hikima ta kai daga wannan bangon duniya zuwa wancan saboda ikonta,

      Tana kirfa dukan abu da kyau.

Hikima Ce Asalin dukan Arziki

2 Na ƙaunaci hikima,

      Ita na nema da ƙwazo a cikin ƙuruciyata,

Na nema ma in ɗauke ta ta zama amaryata,

      Sai na yi shaawar kyanta.

3 Ko da mutum ɗan sarki ne, hikima tana kara masa daraja,

      Ta haɗa shi zumunci da Allah,

Ubangijin sama da ƙasa ma yana ƙaunarta.

      4 Ai, ita masaniyar ilimin Allah ce,

      Allah ya sa ta shirya aikin da zai yi.

5 Amma in wadata mutum ke so ya mallaka ransa,

      Wace wadata ce ta fi hikima, wadda take yin kome?

6 In ana son aiki da dabara,

      Me ya fi hikima bijinta?

7 In adalci ne mutum ke so,

      Hikima, cinikinta halayen nagarta ne.

Gama tana koya wa mutum kamunkai da hankali,

      Adalci da kumajaruntaka,

      Ba abin da ya fi abubuwan nan amfani a ran mutum.

8 Amma in ilimi mai yawa ne mutum ke so,

      Hikima ta san abubuwan tarihin da,

      Ta ma san abin da zai auku.

Ta san manufar karin magana,

      Da kuma bayanin ka‑cici‑ka‑cici,

Tana hangen alamu da abubuwan mamaki, tun kafin su iso,

      Ta san maƙurar fasalolin shekara da na zamanai.

Hikima Mashawarciyar Sarakuna Ce

9 Sai na yi niyya in ɗauke ta, mu zauna tare,

      Gama na sani za ta zama mai ba ni shawarar kirki,

      Za ta yaye mini ɓacin rai, ta taazantar da ni.

10 Ta wurinta zan sami girma a jamaa,

      Zan sami daraja a cikin dattawa,

      Ko da ya ke ni yaro ne.

11 Zan yanka daidai idan na yi sharia,

      Zan ma yi farin jini a gaban manyan sarakuna.

12 Da na yi ɗan shiru, sai su ce, Wane, me ya dame ka?

      In kuwa na yi magana, duk sai su saurare ni sosai,

Ko na daɗe ina mai da kalami,

      Sai dai su yi tagumi kawai suna jina.

13 Ta wurin hikima zan sami dawwamammen rai,

      Jikokina za su yi ta tunawa da ni din din din.

14 Zan mallaki jamaa, kabilai kuma za su zama talakawana,

      15 Hutsayen sarakuna za su yi fargaba in sun ji labarina,

A gaban mutane zan fito kai tsaye,

      Lokacin yaƙi kuma zan nuna mazakuta.

16 Lokacin da na koma gida, zan huta tare da hikima,

      Gama mai maamala da ita ba shi da ɓacin rai,

Mai zama da ita ba shi da damuwa,

      Sai dai murna da farin ciki kawai.

Hikima Kyautar Allah Ce

Ina ta tunanin waɗannan abubuwa ni kadai,

      Na ma ce a zuciyata,

Ai, akwai dawwamammen rai a dangantakar hikima,

      18 A ƙaunarta akwai farin ciki,

A aikinta akwai wadata dangas.

      A zumunci da ita ana samun hankali,

A gab da jawabanta mutum zai yi babban suna,

      Sai na yi ta neman yadda zan mai da ita tawa.

19 Dā ni yaro ne mai kyan diri,

      Na ma yi gamon katar da tsabia mai kyau,

20 Amma saboda tsabiata mai kyau

      Na sami jikin da ba shi da aibu.

21 Amma dai na sani ba ni da damar riƙon hikima,

      Sai ko in Allah ya yarda.

Sanin wannan kuma kyautar Allah ce.

      Sai na roƙi Ubangiji,

      Da dukan zuciyata na faɗa.

9. Adduar Sulemanu

1 Ya Allah na kakannina, Ubangijin jinƙai,

      Wanda ka halicci kome ta kalmarka,

2 Ta hikimarka ka siffata mutum,

      Domin ya mallaki abubuwan da ka halitta,

3 Ya mallaki duniya da tsarki da adalci,

      Ya zartar da sharia da adalcin zuciya,

4 Ka ba ni hikimar da ke kewaye da kursiyinka,

      Kada ma ka ware ni daga cikin yayanka,

5 Gama ni bawanka ne kamar yadda iyayena suke dā,

      Mutum ne kuma, ina da kwanakin rai yan kadan,

Na kasa gane sharia da kaidodinta.

      6 Ko da ɗan adam ya zama cikakke,

      In ya rasa hikimarka zai fāɗi ba nauyi.

7 Kai ka zaɓe ni in sarauci jamaarka,

      Domin in sharaanta yayanka mata da maza.

8 Kai ne ka umarce ni in gina masujadarka a kan dutsenka mai tsarki,

      Bagade kuma a birnin da kake zaune,

      In kuma bi fasahar alfarwa mai tsarki wadda ka shirya tun zamanin dā.

9 A wurinka hikima take wadda ta san aikinka,

      A kan idanunta ne ma lokacin da ka halicci duniya,

Ta san abin da ke faranta maka rai,

      Da kuma abin da ya wajaba a bi cikin dokokinka.

10 Sai ka kwararo ta daga sammanka masu tsarki,

      Ka ma aiko ta daga kursiyin ɗaukakarka,

Don ta zauna da ni, ta yi aiki a cikina,

      Ai, ta haka ne zan san abin da ke daidai a gabanka.

11 Gama ita ta sani, ta kuma gane dukan kome,

      Za ta kāre ni da himma a cikin aikina.

      Ta bi da ni da ɗaukakarta.

12 Ta haka aikina zai zama abin karɓa,

      Zan sharaanta jamaarka da adalci,

      Zan zama magajin gadon sarautar ubana da cancanta.

13 To, wane mutum ne ya san shawarar Allah?

      Ko kuwa wa ke iya bincike nufin Ubangiji?

14 Ai, tunanin yan adam taka tsantsan ne,

      Nufe‑nufenmu abubuwan faduwa ne.

15 Gama jiki mai ruɓewa na rinjayar ruhu,

      Yana ma hana kula da shaanonin duniya masu yawa.

16 Muna bara da kā a kan abin da ke bisa duniya.

      Sai ta tsananin aiki kuma muke gane abin da ke kusa da mu,

      To, ta yaya za mu iya binciken abin da ke Sama?

17 Wa ke iya sanin shawararka, in ba ka ba shi hikima ba,

      Ka kuma aiko masa ruhunka mai tsarki daga Sama?

18 Ta haka ne ka daidaita hanyar yan adam a duniya,

      Ka koya wa mutane abin da ke faranta ranka,

      Ka cece su ta hanyar hikima.

10. Tarihin Hikima, daga Adamu zuwa Musa

1 Hikima ta kiyaye mutum na fari, kakan dukan duniya,

      Da ya ke shi kaɗai ne lokacin da aka halicce shi.

Ta cece shi daga saɓon da ya yi,

      2 Ta ba shi ikon mallakar dukan abu.

3 Amma da Kayinu, marar gaskiya, ya watsar da hikima ta wurin fushinsa,

      Ya ma kashe ƙanensa, sai fushinsa ya sa ya halaka.

4 Ai, a loton da ƙasa ke nutsewa ma,

      Hikima ce ta fanshe ta,

      Ta bi da Nuhu adali a sassaƙaƙƙen jirgi.

5 Ita ma, ta zaɓi Ibrahim adali a loton da aka ƙaskanta alummai, suna hacrin gwiwa a ƙetarsu,

      Ta keɓe shi marar aibu a gaban Allah,

Ta ƙarfafa shi kyam,

      Lokacin da aka umarce shi ya yanka ɗansa.

6 Ta fanshi Lutu adali daga jairan da ake hallakarwa,

      Lokacin da yake gudu daga wutar da ke saukowa kan birane biyar,

7 Waɗanda har yanzu akwai shaidar ƙetarsu,

      Kufai na yin hayaƙi,

Itatuwa na yin yayan da ba su nuna ba,

      Surin gishirin na tsaye,

      Alamar wadda ba ta gaskata ba.

8 Lokacin da mutanen biranen suka raina wayon hikima,

      Ba kasa gane abubuwa masu kyau kawai suka yi ba,

Amma sun ma har wa yan baya abin faɗa na saunancinsu,

      Ta haka ba su guji yadda a gane kasawarsu ba.

9 Amma hikima na fansar masu yi mata hidima daga wahala.

      Ta keɓe Yakubu adali, da yake guje wa fushin ɗanuwansa,

Ta bi da shi ta miƙaƙƙun hanyoyi,

      Ta nuna masa mulkin Allah,

Ta ba shi sanin asirai masu tsarki,

      Ta sa masa albarka a aikinsa,

      Ta ƙara amfanin aikin hannunsa.

11 Loton da ake wahalar da shi, sai ta tsaya a kusa da shi,

      Ta ma wadata shi.

12 Ta keɓe shi daga maƙiya,

      Ta ma tsare shi daga masu shirin kashe shi.

Ta ba shi nasara a faɗa mai tsanani,

      Domin ya san tsoron Allah ya fi kome iko.

13 Ba ta juya wa Yusufu, adalin da aka sayar bawa ba,

      Amma ta tsare shi daga yin zunubi.

14 Ta bi shi har kurkuku,

      Ba ta ma rabu da shi ba,

      Duk lokacin da yake cikin sarƙa,

Sai da ta ba shi ragamar mulkin,

      Ta ba shi iko bisa waɗanda suka matsa masa lamba,

Ta kunyata waɗanda suka yi masa ɓatanci,

      Ta ba shi ɗaukaka mai dawwama.

Fitowar Israilawa daga Masar

15 Hikima ta tsirar da jamaa mai tsarki

      Daga alumma mai tsanantawa.

16 Ta shiga zuciyar Musa, bawan Ubangiji,

      Ta yi gāba da sarakuna masu bantsoro,

      Ta wurin yin muujizai da ayoyi,

17 Ta ba masu tsarki ladan aikinsu.

      Ta bi da su ta hanya mai banmamaki,

Ta zamar musu girgije mai dushe musu zafin rana,

      Da wuta mai haskaka musu da dad dare.

18 Ta ratsar da su ta tsakiyar Bahar Maliya,

      Ta bi da su wurin ruwa mai yawa.

19 Amma sai ta hallakar da maƙiyansu,

      Ta ma tura gawawwakinsu gaci.

20 Saboda haka sai adalai suka sami kayan abokan gabansu,

      Sai suka raira waƙar sunanka mai tsarki, ya Ubangiji,

      Suka kuma yabi dantsenka mai nasara a yaƙi.

21 Gama hikima ce ta buɗe bakin bebe,

      Ita ce ma ta sa masha mama yin magana tangaran.

11.

1 Ta sa wa aikin adalai albarka

      ta hannun Musa tsattsarkan annabi.

2 Sun ratsa ta hamadar da ba kowa a ciki.

      Sun kafa alfarwansu a ƙungurmin jeji,

3 Sun yi ja‑in‑ja da abokan hamayya,

      Sun ma faskari abokan gdba,

4 Sun ji ƙishi, sun kuma kira bisa gare ka,

      Sai aka ba su ruwa daga cikin fa,

      Aka shayar da su daga dutse mai rearfi.

5 Gama ta wurin abubuwan nan aka hori abokan gābansu,

      Ta wurin waɗannan ma aka biya wa jamaar Allah bukatarsu.

Da ƙuwa ne aka Hori Masarawa, aka Amfani Israilawa

6 Maimakon dawwamammen ruwan kogin Nilu,

      Abokan gāba suka sami gurɓataccen ruwa cike da jini,

7 Domin tsawata musu saboda kisan jariran da suka yi.

      Amma ka ba jamaarka wadataccen ruwa da ba su tsammaci samu ba,

8 Bayan da matuƙar ƙishinsu ta nuna musu yadda ka hori abokan gābansu.

      9 Gama a lokacin da ka tsananta wa jamaarka, da jinƙai kawai ka hore su.

      Ta haka ne suka gane yadda ka hori masu saɓo da fushinka.

10 Ai, lokacin da ka hori jamaarka da abokan gābansu

      11 Ka hori jamaarka kamar yadda uba ke yin gargaɗi,

      Amma kamar matsanancin sarki ka hukunci abokan gābansu.

12 Baƙin cikin abokan gāba ya ninka har sau biyu.

      Suka yi ta gumani a kan masifun da suka same su,

13 Suka kuma ji a kan horonsu, waɗansu su wadata,

      Sai suka gane wannan aikin Ubangiji ne.

14 Gama jaririn da suka raina dā,

      Suka yar da shi bakin ruwa,

Daga baya sai suka yi mamakinsa  ƙwarai,

      Suka ƙishirta fiye da adalai a hamada.

Ta Kwari ne aka Hori Masarawa

15 Amma saboda wawancinsu na rashin sanin adalci,

      Sai suka koma, suna bauta wa macizai da ƙwari,

      Sai ka aiko musu sakayya ta mahaukatan majaya ciki da masu tashi,

16 Domin su gane abubuwan da ke sa mutum yin saɓo,

      A kan hore shi ta kansu.

Allah ya Rage Horon

17 Dantsenka ne mai iko duka,

      Wanda ya halicci duniya ba da kayan aiki ba,

      Bai rasa ikon aiko da garken kuraye ko zakoki a kan abokan gāba ba,

18 Ko sababbin dabbobin jeji mahaukata, abin tsoro, wadanda ba a taɓa gani ba,

      Masu yin numfashi na gurnanin wuta,

Ko masu ƙugi har hayaƙi na fita,

      Ko ka ga har wadansu tartsatsai masu bantsoro na fitowa daga idanunsu,

19 Waɗanda ba faɗansu kawai ne ke hallaka abokan gāba ba,

      Amma ganinsu ma kurum da bantsoro,

      Yana iya hallakar da jamaa.

20 I, banda dabbobin nan, da ka kashe su da yar iskar numfashinka,

      Da ya ke ramuwa ta tasa ƙyeyarsu,

Ikonka kuma ya warwatsa su,

      Amma ka daidaita dukan abu ta iyakar girmansa, da yawansa, da nauyinsa.

21 Gama gawurtaccen ƙarfi naka ne a kowane lokaci,

      Girman dantsen nan naka, wa ke iya daurewa da shi?

22 Ai, kamar kwayar tamba dukan duniya take a gare ka,

      Kamar digon raɓa ne wanda ya fada Rasa da sanyin safiya.

23 Amma kana da jinƙai a kan dukan jamaa,

      Don kana da iko kan dukansu,

      Kana kuma ƙyale zunuban mutane domin su tuba.

24 Gama kana ƙaunar dukan abin da  ya wanzu,

      Ba ka ma ƙin korne da ka yi,

      Gama in ba ka son abu, ba za ka halicce shi ba.

25 Yaya wani abu zai ɗore in ba ka yi nufin haka ba?

      Ko kuwa yaya wani abu zai adanu in ba ka umarce shi ba?

26 Amma kana kāre dukan abu, gama  naka ne,

      Ya Ubangiji mai ƙaunar rayuka.

12.

      1 Gama ruhun nan naka marar ru6a yana cikin dukan abu.

2 Don haka kana hukunta waɗanda suka yi laifi kaɗan kaɗan,

      Kana kuma tuna musu da abubuwan da suka yi laifi a kai,

Kana yi musu gargaɗi,

      Domin su guji ƙetarsu, su amince da kai, ya Ubangiji.

Hakurin Allah da Kananiyawa

3 Kananiyawa dā, da ke ƙasarka mai tsarki,

      4 Kana ƙinsu saboda abin ƙyamar da suke yi,

      Ayyukan maita da yin hadayu marasa tsarki,

5 I, suna cin yan cikin yan adam, duk da namansu da jininsu,

      Ana shigar da sababbin shiga bikin bugaggu.

Ba su da jinƙai, har ma yayansu suke kashewa,

6 Iyayen, da nufinsu suke kashe yayansu, ba mai iya hana su.

      Ka ma so ka hallaka mutanen nan ta hannun kakanninmu,

7 Domin ƙasan nan taka wadda ta fi kome,

      Ta karɓi sabon zaman yayanka macancanta.

8 Amma Kananiyawan nan ma da ya ke yan adam ne, sai ka keɓe su,

      Sai ka aika da jirnaƙo su zama mataimakan rundunarka,

      Domin a hallaka masu saɓo bi da bi.

9 Kana da ikon shafe marasa. adalci nan da nan

      Ta wurin sa adalanka su ci su da yaƙi,

Ko ta wurin aika da dabbobi masu hallakarwa,

      Ko ta faɗar kalma ɗaya mai tsanani.

10 Amma da ya ke kana sharaanta su bi da bi,

      Sai ka ba su damar tuba,

Ba dolo kake ba ga zancen muguntarsu,

      Ka sani ƙetarsu ta yi musu kauci,

      Mugun tunaninsu ma ba zai sauya ba har abada.

11 Gama jamaa ce laananniya tun farko,

      Ba don ka ji tsoron wani ba ne,

      Ka bar su suka sha galla, duk da zunuban da suka yi.

12 To, wa zai ce, Menene ka aikata haka?

      Ko kuwa wa zai ja da shariarka?

Ko kuma wa zai iya ganin laifinka a kan hallaka alummar da ka halitta?

      Ko wanene kuma zai tsaya gabanka, ya kare marasa adalci?

13 Gama ba ma wani allah banda kai, mai lura da duka,

      Wanda za ka nuna masa ba ka sharaanta da zalunci ba.

14 Ba ma wani sarki ko hakimi

      Wanda zai iya zarginka a kan waɗanda ka horar.

15 Amma da ya ke kai adali ne, kana fito da kome a adalci,

      Ka ce bai dace da ikonka ba,

      Ba ka hukunta wanda bai cancanci hukunci ba.

16 Gama ikonka shi ne farkon adalci,

      Domin kuma kana da sarauta a kan dukan halitta,

      Kana nuna wa kowa jinƙai.

17 Kana nuna ikonka lokacin da aka ƙi gaskata cikakken ikonka,

      Kana ma tsauta wa rashin ladabin wadanda suka san ikonka.

18 Amma tun da ya ke kai sarkin iko ne,

      Kana sharia da sassaftawa,

Kana ma mulkinmu da matuƙar jinƙai,

      Gama ikon naka ne, sai abin da ka yi.

19 Ta wannan irin aiki ne ka koya wa jamaarka, cewa

      Dole ne adali ya zama mai ƙaunar jamaa,

Ka ma faranta wa yayanka rai,

      Domin ko da ya ke sun yi saɓo, kana ba su damar tuba.

20 Gama in magabtan barorinka waɗanda daidai ne a kashe su,

      Ka hore su da lalama da hakuri,

      Kana ba su dama su sauya daga ƙetarsu,

21 Da wace irin kula za ka sharaanta yayanka

      Wadanda aka yi wa kakanninsu rantsuwa da yarjejeniyar alkawari mai faida?

22 Duk lokacin da ka hore mu,

      Ai, ninki dubu goma ne kake horon abokan gābanmu,

Don lokacin da muke sharaanta waɗansu,

      Mu tuna da alherinka,

Amma in an sharaanta mu,

      Sai mu sa rai ga jinƙai.

Horon Bauta wa Macizai da Kwari

23 Don haka ne ma maƙetatan da suka  yi zaman wauta,

      Ka hore su ta aikinsu na ƙyama.

24 Gama sun ratse hanya, har sun fi kuskure-kuskure,

      Suka mai da rayayyun abubuwa mafi ƙazanta allolinsu,

      Aka ruɗe su kamar yara ƙanana.

25 Sai ma ka ce yaran da ba su san ciwon kansu ba,

      Ka aiko musu da hukuncinka kamar baa,

26 Amma waɗanda ba su kula da  hannunka mai sanda ba,

      Sai suka sha hukuncin da ya cancanci ikon Allah.

27 Ta wurin horon da aka yi musu ta halittattun dabbobin nan da suka mayar allolinsu,

      Sai suka san wanda suka ƙi sani dā,

Suka gane Allah ne na gaskiya,

      A kan haka ma sai hukuncin ƙarshe ya auko musu na kashe yan farinsu.

13. A kan Bauta wa Halittar Allah

1 Gama duk wadanda suka yi jahilci zancen Allah, mahaukata ne,

      Daga abubuwa masu kyau da ake gani,

Ba su gane wanda yake rayuwa ta hakika ba.

      Ba su ma saurara ga ayyukansa ba, domin su gane mai yinsu.

2 Amma ko dai wuta, ko iska,

      Ko hanyar taurari, ko ambaliyar ruwa,

Ko fitilun sama, ko hakiman duniya,

      Sun tsammaci su alloli ne.

3 Duk da haka, in sun zaci don kyansu su alloli ne,

      Bari su yi tunani yadda Mahaliccin waɗannan abubuwa

Zai fi su nesa ba kusa ba.

      Gama tushen kyau ne ya halicce su.

4 Amma in sun yi mamakin ikonsu da ƙarfinsu,

      Bari su yi tunani yadda ikon wanda ya yi su ya fi nasu girma.

5 Gama saboda girman halitta da kyansa ne

      Ake gane fifikon wanda ya halicce su.

6 Amma duk da haka waɗannan masu bauta wa halittar Allah ba su da laifi sosai,

      Mai yiwuwa ne sun yi kuskure kurum,

      Sun nemi Allah da nufi su iske shi.

7 Da ya ke sun saba da ayyukansa,

      Suna bincikensu da himma,

Sai suka yarda da abubuwan da suke gani,

      Cewa abubuwan nan kyawawa ne,

8 Amma duk da haka ba su da wata huja,

      9 Gama da ya ke suna da ikon sanin abubuwa da yawa,

Suna ma iya kintata duniya,

      Don me suka kasa sanin Ubangijin waɗannan abubuwa da sauri?

A kan Bauta wa Gumaka

10 Anuna yanzu akwai masu matuƙar baƙin ciki,

      Masu begen abubuwan banza,

Su ne waɗanda suka kira aikin hannun yan adam allolinsu,

      Abubuwan da suka yi da zinariya da azurfa,

Ko kamannin dabbobi,

      Ko duwatsun banza, aikin hannun mutanen dā.

11 I, har ma in gwanin masassaƙi ya sassaƙi itace,

      Ya gyara shi, ya ɓare ɓawo,

Ya shirya shi yadda yake so,

      Har ya yi akushi don a sa abinci ciki,

12 Sai ya kwashi yan ɓalle‑ɓallen itacen

      Don ya dafa abincinsa, ya ci ya ƙoshi.

13 Amma abin da ya ragu, ba ya amfanar kowa,

      Ɗan karkataccen itace wanda ya cika ƙullutu,

Sai ya sassaƙa shi a huce, ya shirya shi da azancinsa,

      Ya yi masa siffar mutum,

14 Ko ya siffata wata dabba marar goshin gari,

      Ya shafe ta da jan gargari da laka,

      Ya shafe kowane wurin da ke da lahani,

15 Ya gina mata ɗakin da za ta wala,

      Ya jingina ta da bangon ɗakin,

      Ya ɗaɗɗaure da ƙarafa,

16 Sai ya yi ta tunani a kai don kada ta faɗi,

      Don ya sani ba ta da ƙarfin taimakon kanta,

      Gama siffa ce wadda take bukatar taimako.

17 Amma duk da haka, sai ya rika roƙonta

      Domin lafiyar mallakarsa, da matarsa, da yayansa,

      Ba ya jin kunyar roƙon mataccen abu.

I, har ma. yana roƙon lafiyar jiki,

      Gun abin da ba shi da ƙarfi,

18 Ya roƙi mataccen abu tsawon rai.

      Don taimako kuma, sai ya roƙi abin da bai san kome ba,

      Lokacin tafiya kuma ya roƙi abin da ba ya ma ko iya muɗawa.

19 Har ma don neman mahibbar kasuwanci,

      Da cin gaban aikin hannu,

      Sai ya roƙi taimako gun abin da ya fi kome kasawa.

14.

1 Wanda ke shirin tafiya kuma ta jirgin ruwa,

      Ya yi tafiya a kan rakuman ruwan,

      Yana roƙcon itacen da ya fi jirgin da zai shiga saurin ragargazawa.

2 Gama don cin riba ne aka yi jirgin ruwa,

      Wani masassaki ya sassaƙa shi da hikima.

3 Amma ƙaddararka ce, ya Uba, ta bi da jirgin,

      Gama ka ba da hanya, har ma cikin ruwa,

      A cikin raƙuman ruwa ka ba da tafiya lafiya.

4 Ta haka ne ka nuna yadda kake ceto daga kome,

      Don ko bami ya iya shiga jirgin.

5 Gama mifinka ne ayyukan hikimarka su nuna mazakuta,

      Don haka jamaa sun amince su hau jirgin,

Ko da ya ke ba shi da tabbas,

      Su haye tekun lafiya, ba wani hatsari.

6 Gama dā, lokacin da ƙattin nan suka halaka,

      Sai Nuhu, jigon dukan duniya,

Ya tsira a jirgi marar tabbas,

      Da ya ke kai ne ka yi masa jagora,

      Sai ya har wa duniya iri.

7 Mai albarka ne itace wanda ta gunsa adalci ya zo,

      8 Amma gunkin da aka yi da hannu laananne ne,

      Har da mutumin da ya yi shi,

Mutumin, domin ya siffata shi,

      Gunkin nan kuwa mai ruɓewa, domin an ce da shi allah.

9 Gama marar adalci, da shi da rashin adalcinsa duk,

      Allah na ƙinsu.

10 Ai, abin da aka yi,

      Allah zai bore shi da kuma wanda ya yi shi.

11 Don haka za a hukunta gumakan arna,

      Gama ko da ya ke sashi ne na halittar Allah,

Sun zama abin ƙyama,

      Sun zama abin tuntuɓe ga rayukan jamaa,

      Tarko kuma ga ƙafafun wawaye.

Asalin Bauta wa Gwnaka

12 Dabarar yin gumaka mafarin fasikanci ce,

      Ƙago su kuma shi ne tushen lalata.

13 Gama ba su wanzu ba tun da farko,

      Ba ma za su ɗore ba,

14 Ai, ta tsammanin banza na mutane ne,

      Gumaka suka sami shigowar duniya,

      Don haka har an ƙaddara musu shuɗewa.

15 Gama sai makokin da ya auko wa uba kwaram,

      Sai ya yi siffar da wanda ya rasu a ganiyar ƙuruciya.

Nan da nan ya girmama mutum,

      Wanda ya taɓa mutuwa, kamar wani dan Allah,

      Ya har wa yan baya asirai da tsarin ibada,

16 Daga baya aladan nan ta saɓo,

      Ta sami tushe, aka mai da ita doka,

Haka kuma sarakuna suka sa aka riƙa sassaƙa siffofi,

      Ana bauta musu.

17 In kuma jamaa suka kasa girmama sarki a gabansa don nisa,

      Sai su kimanci yadda yake a can nisan,

Su yi siffar sarkin da suke girmamawa,

      Wai don su bauta wa wanda ba ya nan kamar yana nan.

18 Amma sai kishin zucin mazānan ya gabatar da aladar,

      Don waɗanda ba su san abin da ake yi ba,

      Su riƙa bautar wa siffar.

19 Gama watakila don mazānin ya gamshi sarkin,

      Sai ya ƙara wa siffar kyan gaske,

20 Taron kuma, wanda ya riɓato ta gwanintar aikinsa,

      Yanzu suka mai da sarkin abin bauta wa,

      Wanda a ɗan zamanin baya suke girmamawa kamar mutum.

21 Wannan kuwa ya zama tarko ga mutane,

      Saboda makoki ne ko tsananin sarakuna,

Mutane suka raɗa wa itace da duwatsu sunan Allah

      Wanda bai kamata a gauraya da na waɗansu ba.

Annobar da Bauta wa Gumaka ta Kawo

22 Duk da haka bai ishe su

      Su bauɗe wa sanin Allah ba,

Amma suna nan zaune a babbar hamayyar da jahilci ya sa,

      Har suka kira irin wannan mugun zama, wai salama.

23 Suna kashe yara lokacin hadaya,

      Suna bikin ɓoyayyun asirai,

Suna haukansu na ibada,

      Wato fasikancin da ba a taɓa ganin irinsa ba.

24 Ba su mai da rai ko darajar aure wani abu ba,

      Amma sai wani mutum ya faki wani, ya kashe shi,

      Ko kuwa ya baƙanta masa rai ta wurin fasikanci da matarsa.

25 Sai kome ya rude ta wurin zub da jini,

      Da kisankai, da sata, da zamba,

      Da lalata, da rashin aminci, da saɓani, da shaidar zur,

26 Da damun mutanen kirki, da rashin godiya a kan aikin alheri,

      Da Ialacewar hali, maza na kwana da maza,

      Da zaman aure marar kangado, da zina, da batsa.

27 Gama bauta wa gumakan nan, marasa bakin magana,

      Shi ne farkon jawo kowace mugunta da cikawarta.

28 Gama saboda bauta wa gumakan,

      Daɗi na haukata mutanen, ko suna annabcin ƙarya,

Ko suna zaman rashin adalci,

      Ko suna rantse-rantsen ƙarya nan da nan,

29 Ai, tun da ya ke sun gaskata. da matattun gumaka,

      Ba su san lahani zai same su ba, in sun yi rantsuwar ƙeta.

30 Amma ai, adalci zai nuna musu ranar ƙin dillanci,

      Gama sun yi mugun tunani a kan Allah,

Sun saurari gumakansu,

      Sun kuma yi rantsuwar rashin adalci

      Don ɓad da sawu, suna keta haddin addini.

31 Gama ba ikon yan allolin da ake rantsuwa da su ba ne,

      Amma sakayya ce ga waɗanda suka yi saɓon,

      Ita ce ke bin hakkin saɓon marasa adalci.

15 Israilawa ba Mabautan Gumaka ba Ne

1 Amma kai, Allalmmu, mai alheri ne da gaskiya,

      Kana da haƙuri, kana shugabantar korne da jinƙai.

2 Gama ko mun yi zunubi ma,

      Mu naka ne, mun san ikonka,

Amma ba za mu yi zunubi ba,

      Don mun san mu mallakarka ne.

3 Gama saninka kawai ma adalcin gaske ne,

      Sanin ikonka kurna shi ne tushen dawwamar rai

4 Gama laantacciyar dabara ta muturn ba ta ruɗe mu ba,

      Ai, gwanintar mazanan ma ba ta ɗaukar mana hankali ba,

      Siffar da yake shafewa da launi dabam dabam.

5 Ganin siffar na jawo hankalin wawaye,

      Suna marmarin siffar da ba ta da rai.

6 Wadanda suka yi gumaka, da masu begensu,

      Da kuma masu bauta musu,

Su ne maƙaunatan mugunta,

      Masu begen abin banzan nan da ya dace da su.

Bauta wa Gurnakan Yumɓu

7 Maginin tukwane, mai mulmula yumɓu,

      Yana shan dawainiyar gyara abin amfaninmu.

Ai, daga yurnɓu guda ne ya gina gine-gine dabam dabam,

      Da ake jin daɗin yin amfani da su,

      Ko tukunya, ko randa, ko kwatarniya, ko tulu.

Amma me ya sa suke da shiri dabam dabam?

      Magini ne ya yi su haka.

8 A wani lokaci ma don sakarci,

      Sai ya siffata wani ɗan allah daga gun yumɓun nan,

Ko da ya ke maginin nan daga ƙasa ya ɓullo,

      Bayan dan lokaci kuma zai koma makoma,

      A lokacin ne za a kira kurwar da aka ara masa,

9 Amma yanzu bai damu da rasuwa ba,

      Ko da ɗan gajeren ransa,

Amma yana ta yin gasa da maƙeran zinariya da na azurfa,

      Ya ma ɗauki hannun maƙeran jan ƙarfe,

      Ya tsammaci abin kirki ne, in ya iya ƙera yan jabu.

10 Zuciyarsa toka ce,

      Turɓaya ta fi abin da yake bege daraja,

      Ransa kuma bai kai darajar yurnɓu ba.

11 Gama bai ankara da wanda ya yi shi ba,

      Ya ba shi ran da zai yi faɗi ka tashi,

      Ya hura masa numfashin rai.

12 Amma ya mai da ranmu abin wasa,

      Ko abin kasuwanci mai kawo riba,

Gama ya ce, dole ne mutum ya ci riba ko ta ƙaƙa,

      Ko ta yin maguɗi ne ma.

13 Ai, warman ya fi sauran mutane  sanin ya yi saɓo,

      Lokacin da ya gina tukwane da gumaka daga yumɓu baki ɗaya.

Masarawa sun Bauta wa Gumaka

14 Amma abokan gāban jamaarka,

      Waɗanda suka matsa musu lamba.

      Sun cika wawanci, sun ma fi yayayyen yaro banhaushi.

15 Gama sun yi laakari da dukan gumaka na allolin arna,

      Waɗanda idanunsu ba su gani,

      Hancinsu ba ya yin nurnfashi.

Kunnuwansu ba su jin magana,

      Yatsotsin hannunsu ba su taɓa  kome,

      Kafafunsu ma ba su yin tafiya.

16 Ai, mutum ne ya yi su,

      Wanda aka ba aron kurwa ne ma, ya siffata su.

Ba wani muturn da zai iya siffata ɗan allah

      Wanda ya kai ga masiffaci,

17 Gama mutum mai mutuwa ne,

      Abin da ya mulmula da hannunsa  mai saɓo,

      Ai, ba shi da rai.

Ai, ya fi abubuwan da yake bauta wa  daraja,

      Gama shi yana da rai, amma ba su da shi.

18 Tasu ta ƙare, suna bauta wa  rayayyun abubuwan da aka fi ƙin jini,

      Ai, in a gwada ne, sun ma kasa ga waɗansu rayayyun halitta don ɓarancinsu,

19 Ba su ma kai kyan sauran rayayyun halitta ba, balle a yi shaawarsu,

      Amma sun kauce wa yabon Allah da albarkarsa.

16. Ƙwari sun Dami Masarawa, Israilawa na ta Jin Daɗi

1 Don haka sai aka hori Masarawa gwargwado,

      Daidai kaya daidai gammo,

      Aka gasa musu azaba da ƙananan ƙwari maɓarnata.

2 Maimakon wannan horo, sai  jamaarka suka sami amfani,

      Don ma ka biya musu bukata,

Sai ka shirya musu abinci mai daɗin ɗranɗano,

      Ka ba su makware su ci.

3 Domin a lokacin da sauran suka ji yunwa

      Saboda munanan abubuwan da aka aiko musu,

Har ba su marmarin cin abinci,

      Jamaarka, da sun ji yar yunwa kaɗan,

      Sai a ba su wani abu mai daɗin ɗanɗano.

4 Gama dole ne sauran manyan gwaza su ji yunwa mai tsanani,

      Amma jamaarka sun ji yar yunwa kaɗan,

      Don a nuna musu yadda abokan gābansu suka sha ƙasƙanci.

Fāri sun Dami Masarawa, Israilawa sun Tsira daga Annobar Macizai

5 Lokacin da mahaukatan macizai  suka auka wa jamaarka,

      Har suka yi ta saransu,

      Bayan ɗan lokaci sai ka hana mutanenka su ɗanɗana kuɗarsu.

6 Amma sai aka ɗan burge su kaɗan,

      Don a gargaɗe su,

Ai, an ba su alarnar macijin jan ƙarfe,

      Mai tuna musu da dokokin shariarka.

7 Dukan wanda ya juya ga alamar, sai a cece shi,

      Ba don abin da ya gani ba,

      Amma saboda kai ne Mai Ceton kowa.

8 Ta haka ne ka koya wa abokan gābanmu.

      Kai ne ke fansa daga kowane irin aibu.

9 Gama an kashe abokan gāba ta cizon fari da ƙudaje,

      Ba su kurna sami makari ba,

      Don ya kamata a hore su ta haka.

10 Amma ba ɗafin macijin ne

      Ya yi wa yayanka lahani ba,

      Gama jinƙanka ya yi taimako, ya warkar da su.

11 Gama don a tuna musu da saƙonka ne, aka yi ta saransu,

      Nan da nan kuma aka tsame su,

Don kada a yi sakainan kashi da su,

      Su mance su gode wa alherinka.

12 Gama ba lungaɓen itace ba ne,

      Ko da bandeji suka warkar da su,

      Amma kalmarka ce, ya Ubangiji, wadda ke warkar da kowa.

13 Ai, kana da iko bisa rai da mutuwa,

      Kana aikawa da mutane lahira, ka kuma dawo da su.

14 Mutum na iya yin kisankai don ƙeta,

      Amma da kurwar ta fita, ba ya iya ce mata ta dawo,

      Ba ya ma iya kwance ɗaurarriyar kurwa.

Hadiri ya Wahalar da Masarawa, Israilawa sun Ci Abincin Sama

15 Amma ba mai iya kuɓuta daga hannunka,

16 Gama masu saɓo, masu ƙin saninka,

      Ka fatattake su da dantsenka,

      An bi su ta ƙanƙara da ruwan sama,

Ba tsattsautawa, wanda ba su taɓa gani ba,

      An cinye su ma da wuta.

17 Amma mafi duk bantsoro shi ne,

      Lokacin da ake yi ruwan sama mai kashe kome,

Wutar sai ƙara haɓaka take yi,

      Gama ikon Allah ne ke yi wa adalai yaƙi.

18 Ai, yanzu an kwantar da wutar,

      Don kada ta kashe dabbobin da ake aika su hori mugaye,

Amma don mugaye su gani,

      Su gane, cewa shariar Allah ce ke binsu.

19 A wani lokaci ne kuma,

      Sai wutar ta kama cikin ruwan da wani gawurtaccen iko,

      Don ta hallaka hatsin ƙasar mugaye.

20 Maimakon haka, sai ka ba jamaarka abincin malaiku,

      Ka dinga aiko musu da abinci daga sama,

Shiryayye, wanda ba sai sun yi wahalar nema ba,

      Mai daɗin ci kuma, ga daɗin ɗanaɗno ga kowa,

21 Gama abincin da ka bayar ya nuna jin daɗinka ga yayanka

      Yana kuma biyan bukatar wanda ya ci,

      Aka sauya shi ga duk irin ɗanɗanon da mutum zai nema.

22 Amma wutar ke wahalar da Masarawa,

      Sai ƙanƙara ta jure mata, ba ta ko narkewa,

Domin jamaarka su sani,

      Lokacin ƙanƙara, wuta ta lalata hatsin magabtansu,

      Ta kuma fizga haske lokacin ruwan.

23 Wutar ma, don a ciyar da adalai ne,

      Sai ta mance ikonta, ta lafa.

24 Gama halittar duniya, da ya ke tana yi maka hidima,

      Kai da kake Mahaliccinta,

Sai ta tsananta wa maƙetata don horo,

      Amma ta sassafta wa masu amincewa da kai, don agaji.

25 Saboda haka ma, sai ta ɗauki siffa dabam dabam,

      Ta yi wa rahamarka mai ciyar da kome hidima

      Bisa ga begen masu bukata,

2ɓ Don yayanka da kake ƙauna, ya Ubangiji, su koya,

      Cewa ba dumbun hatsi ba ne ke riƙe da mutum,

      Amma kalmarka ce ke kiyaye waɗanda suka gaskata da kai,

27 Gama abin da wuta ba ta lalata ba,

      Sai ya narke ta ɗan hasken rana kawai.

28 Wannan ya nuna dole ne mu tashi kafin ketowar rana,

      Mu gode maka

      Mu roƙe ka da asuba.

29 Gama abin da marar yi maka godiya ke bege,

      Zai narke kamar ƙanƙara,

      Ya gangare kuma kamar ruwa kan tudu.

17. Duhu ya Wahalar da Masarawa, Israilawa na cikin Haske

1 Gaskiyarka da girma take,

      Mai wuyar bayani kuma,

      Don haka marasa horo ke baudewa.

2 Gama lokacin da marasa adalci suka yi tsammani sun rinjayi alummarka mai tsarki,

      Sai suka riƙa zama ɗaurarru a gidajensu,

Yan ɗaure na duhu, bayin yaƙi na tsawon dare,

      Suna gudu daga ƙaddarar Allah.

3 Lokacin da suka tsammaci an manta da asirtattun zunubansu,

      Sai aka yi ɗaya ɗaya da su, suka firgita,

      Suna ganin kurwoyl.

4 Gama ko sun shiga saƙo, ba su daina jin tsoro,

      Amma kurwa na kurari kusa da su,

      Waɗansu kurwoyi na bayyana shiru, masu fuskar shanu.

5 Ba wata wutar da za ta iya haskaka su,

      Ko farin hasken taurari ma,

      Albarka ba ta iya rinjayar wannan mugun dare ba.

6 Sai wani lokaci ne hasken walkiya ke ɓullo musu,

      Wanda yake ba su tsoro,

      Sai suka tsammaci ganinsa ya fi zamansu a duhu bantsoro.

7 Borinsu bai yi musu taimako ba,

      Hikimar da suke taƙama da ita ta kunyata.

8 Gama waɗanda suka ce su bokaye ne,

      Suna iya korar kurwoyin da ke damun jamaa,

Sai ciwon ya koma musu,

      Har suna ganin kurwoyi duk inda suka duba.

9 Ai, in ba wani abin da ya firgita su ba,

      Ko motsin kwari da tsuwar macizai na iya yin haka.

10 Sun mutu a tsorace,

      Suna ma ƙin fuskantar iska,

      Wadda ba damar a zuƙe mata.

11 Gama ƙeta matsoracciyar aba ce,

      Ita ce ke laanta kanta,

Tana ma cin kanta da buguzun,

      Tana ba da labarin shan wuyarta, har ta ƙara gishiri.

12 Gama tsoro ba kome ba ne,

      Ba da kai ne kawai, don an ƙi bin taimakon azanci.

13 Ba zuciyar mutum ce ta ƙare ba,

      Sai ya ƙara karaya da rashin sanin abin da zai same shi.

14 Ta haka ne, dukan dare, wanda ba shi da wani iko,

      Domin ya auko musu daga lahira,

Mulkin da ba shi da iko,

      Lokacin da masu saɓo suke gyangyacrin ƙarya,

15 Sai suka gurgunta saboda waɗansu kurwoyi masu bantsoro sun burge su,

      Da kuma ba da kai da suka yi,

      Gama tsoro ya yi musu farmakin ba zata.

16 Saan nan duk wanda ke nan, sai ya fāɗi don tsoro,

      Sai ka ce an zuba su a kurkukun da ba a yi da ƙarfe ba.

17 Gama ko mutum manomi ne ko maƙiyayi,

      Ko ɗan ƙodagon da ke aiki a jeji,

Sai a rarume shi, ya sha wahalar da ba makawa,

      An ɗaure dukansu da sarƙar duhu.

18 Ko sun ji ƙugin iska,

      Ko kukan tsuntsaye a rassan itatuwa,

Ko motsin gudun ruwa,

      Ko ƙarar gangarawar duwatsu cikin kwari,

19 Ko gudun dabbobin da ba a gani,

      Ko gunzar mugun naman jeji,

Ko amon maganar da aka yi, da duwatsu ke amsawa,

      Duk suna karya musu zuciya sosai.

20 Ko da ya ke an cika dukan duniya da haske,

      Sauran mutane kuma suna ta yin aikinsu,

      Ba mai hanawa,

21 A kan masu saɓo ne kawai aka jibga duhu,

      Kwatanci ne na dulum da zai karɓe su a lahira,

Amma sun dami kansu fiye da yadda duhun ya dame su.

18.

1 Amma tsarkakanka suka moni haske mai girma,

      Sauran kuwa suna jin muryarsu,

      Amma ba su ganinsu,

Sai suka ce da su masu albarka,

      Da ya ke ba wahalar da ta dame su,

2 Sai kuma suka gode, da ya ke kuwa sun saɓa wa jamaarka,

      Jamaarka ba su yin sakayya,

      Sai suka roƙi jamaarka gafarar saɓon da suka yi musu.

3 Maimakon wahalar da sauran ke sha,

      Sai ka aiko wa jamaarka da ginshikin wuta,

Ya yi musu jagora a tafiyarsu

      Zuwa wurin da ba su san hanya ba.

      Rana kuma ta dunɗe saboda darajar tafiyarsu.

4 Gama ya kamata a tura masu saɓon sāƙo

      Don kada su ga haske,

Domin sun killace yayanka a kurkuku,

      Yaya naka waɗanda ta kansu ne

      Ka nufi ba duniya hakikanin hasken sharia.

An Kashe Yan Fari na Masarawa, an Keɓe Israilawa

5 Lokacin da masu saɓo suka ƙudura kashe jariran tsarkakakku,

      Ko da ya ke an yar da jariri Musa, an ma tsamo shi,

Ka tsawata musu ta fafarar rundunar samarinsu,

      Ka hallaka su duka a ambaliyar Bahar Maliya.

6 An sanar da kakanninmu da daren nan tun kafin ya iso,

      Domin su tabbatar da rantsuwar da suka gaskata da ita,

      Su ƙara ƙarfin zuciya.

7 Aɗana adalai da halakar abokan gābansu

      Cikar aya ce ga mutanenka.

8 Gama ta horon maƙiyansu ne

      Ka dawo da mu gunka, ka kuma ɗaukaka mu.

9 Gama a asirce ne jikokin adalai suka miƙa hadaya,

      Da nufi guda kuma suka yi yarjejeniya da Allah,

Bisa ga sharudan shariarsa,

      Su ji daɗi tare, su wahala tare,

Nan da nan sai suka raira yabo ga Allah

      Kamar yadda kakanninsu suka yi.

10 Amma maƙiyansu suka amsa da kuka

      Da makoki mai bantausayi a kan rasuwar yayansu.

11 Gama an hori bawa da ubangidansa da azaba iri guda,

      Talakawa da sarakuna na shan ukuba iri ɗaya.

12 An yi mutuwa iri ɗaya a gidan kowa,

      Aka tara gawa hululu,

Har rayayyu sun kasa rufe matattu don yawansu,

      Don da ƙyiftawar ido aka hallaka yayansu na gaban goshi.

13 Gama ko da ya ke ba su gaskata Musa ba,

      Don sun dogara ga sihirinsu,

Da aka hallaka yan farinsu,

      Sai suka ce da jamaan nan yayan Allah.

14 Ai, duk garin, sai ya yi tsit,

      Da tsakar dare ne kuwa,

15 Sai kalmarka mai iko duka ta gangaro daga Sama, daga kursiyi,

      Jarumin yaƙi, ya auko wa ƙasar da zai ci da yaƙi,

16 Yana ɗaukar kaifin takobi na dokarka da ba ta sauyuwa.

      Ya tsaya tsayin daka, ya kwararo wa kome mutuwa,

A lokacin da ƙafafunsa ke tafiya a ƙasa,

      Kansa ya taɓo sama.

17 Ba zato ba tsammani mafarkai masu bantsoro suka auko wa masu saɓo,

      Sai suka firgita ƙwarai.

18 Ga wani nan an bari kwance, rai ga Allah, ga wani can,

      Suna hurta dalilin da ya sa suke macewa.

19 Domin mafarki mai bantsoro

      Da suka yi gargaɗi ne,

      Don kada su halaka, ba su san dalili ba.

20 Amma mutuwa ta shafi jamaarka ma,

      Aka hallaka yar ƙungiya mai kauri tasu a hamada.

      Amma fushin bai ɗore ba,

21 Gama wani adali, Haruna ne,

      Ya yi hanzari ya kāre su.

Ya kawo babbar garkuwa ta firistancinsa,

      Wato addua da turaren ƙonawa masu kawo sulhuntawa.

Ya gagari fushin, ya kawo ƙarshen shan wuyar,

      Yana nuna shi bawanka ne.

22 Amma ya gagari fushin,

      Ba ta ƙarfin tuwo ba,

Ba ta kayan fada ba,

      Amma ta kalmarsa ne ya i wa mai yin horon,

Yana roƙon Allah ya taimake shi

      Saboda rantsuwa da yarjejeniya da aka yi wa kakanni.

23 Gama lokacin da gawawwaki suka yi ta faɗuwa tsibi tsibi,

      Sai ya tsaya a tsaka ya datse zafin fushin,

      Ya falle wancan da ya nufi wajen rayayyu.

24 Gama rigarsa ta alamta dukan duniya,

      An kuma siffata sunaye masu ɗaukaka na kakanni,

      A kan duwatsu goma sha biyu,

Sunanka mai girma kuwa,

      Aka rubuta bisa rawanin sarautar da ya nada a kā.

25 A gaban waɗannan sai mai hallakarwa ya ba da baya,

      Gama yana jin tsoronsu,

Gama ɗan horon da suka sha,

      Ya ishe su su ji tsoron Allah.

19. Haye Bahar Maliya

1 Amma a kan maketata,

      Sai fushin ƙeta ya yi ƙuna ƙwarai,

      Gama Allah ya san burinsu tuntuni.

2 Da suka ba jamaarka dama su tashi,

      Suka ma ɗan kore su da sauri,

      Sai suka sauya nufinsu, su wawure su.

3 Gama tun suna yan koke‑kokensu

      Suna makoki bakin kaburburan matattu,

Sai suka duƙufa kan wata dabarar wofi,

      Suka yi ta rarumar waɗanda suka kora da

      Don Allah, ku har mana garinmu.

4 Gama taurinkai mai dacewa da ajalinsu ya sa sun ce,

      Mu je, mu dawo da su.

Ya sa suka mance da abubuwan da suka faru,

      Domin a cika musu horonsu daidai wa daida,

5 Jamaarka kuma su yi tafiya a nasarance,

      Sauran kuwa su gamu da mutuwar gilla.

6 Gama dukan halitta dabam dabam an sabunta ta

      Domin ta yi wa nufinka hidima,

      Ta kai barorinka tudu su tsira, ba lahani.

7 Aka ga girgije ya rufe alfarwar,

      Aka kuma ga busasshiyar ƙasa inda ake maƙare da ruwa dā.

An keto hanya ta tsakiyar Bahar Maliya,

      Ga ciyawa inda dā sai raƙuman ruwa.

8 Ta wurin ne, waɗanda dantsenka ya keɓe,

      Suka bi suka wuce,

      Sun ga alamun alajabai.

9 Gama sun sha fili kamar dawakai,

      Sun yi tsalle kamar yan raguna,

      Suna yabonka, ya Ubangiji, wanda ka cece su.

An Sauya Halitta don Israilawa

10 Gama jamaarka ba su mance da abubuwan nan na baƙuncin da suka yi a Masar ba,

      Yadda maimakon haihuwar dabbobi,

      Sai ƙasa ta hangazo kwarkwata,

Maimakon kifaye,

      Sai ruwa ya yi ta aman kwaɗi zuɗu zuɗu.

11 Amma daga baya, da jamaarka suka ji yunwa,

      Suna neman abin marmari,

Sai suka ga wani irin sabon tsuntsu.

      Gama makware daga wajen teku suke fitowa, a kama a ci.

Masarawa sun fi Sadumawa Ƙeta

13 Masu saɓo kuwa, bayan sun ƙi bin gargaɗin da aka yi musu ta manyan tsawoyin hadiri,

      Sai suka sha wuya ja wur.

Gama an saka musu gwargwadon ƙetarsu,

      Don sun gwada wa baƙi ƙiyayya zahiri.

14 Ai, Sadumawa ba su yin naam da baƙin da ba su sani ba,

      Amma waɗannan mutane sun mai da baƙi masu alheri bayi.

15 Banda haka ma, an hori Sadumawa daidai,

      Domin sun wulakanta baƙinsu.

16 Amma mutanen nan ko da ya ke sun marabci jamaarka

      Da gagarumin biki da yancin da ya kamata,

      Sai suka mai da alheri mugunta, ta tilasta yin aiki.

17 A nan ma sai suka yi dindimi

      Kamar waɗancan Sadumawa, a gidan Lutu adali,

Waɗanda aka kewaye su da duhu baƙi ƙirin,

      Sai kowa ya yi ta Ialuben hanyar gida.

An Sauya Halitta don Fitowar Israilawa

18 Gama halittattun Allah sun yi musaya da juna,

      Kamar yadda garaya mai tsarkiyoyi take yin murya dabam dabam

Lokacin da ake kaɗa ta.

      Ana iya ganin haka, in an duba alajaban da suka faru,

19 A ƙasa, sai aka sauya dabbobi su zama na ruwa,

      Sai na ruwa, aka sauya su su zama mataka ƙasa.

20 Wuta ta riƙe ikonta a ruwa,

      Sai ruwa ya mance da ikonsa na kashe wuta.

21 Amma wuta ba ta ƙone ko gashin dabbobin da ke yawo a cikinta ba,

      Abincin sama ma, mai saurin narkewa kamar ƙanƙara, bai narke ba.

Karshen Labari

22 A kome dai, kai ne, ya Ubangiji,

      Ka ƙara girman jamaarka, da darajarsu,

Ba ka juya musu baya ba,

      Amma ka tsaya musu a kowane lokaci da kowane wuri.

*      *      *      *      *
*      *      *
*