Isaiah
1Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.
2Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! 'Ya'yan da na goya sun tayar mini. 3Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama'ata Isra'ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”
4An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya. 5Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra'ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo. 6Daga kanki har zuwa ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.
7An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko'ina kufai. 8Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana. 9Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran jama'a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.
10Ya Urushalima sarakunanki da jama'arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku. 11Ya ce, “Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki. 12Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa'ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina? 13Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku. 14Ina ƙin bukukuwanku na amaryar wata, da na tsarkakan ranaku. Sun zama nawaya wadda na gaji da ita.
15“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku. 16Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta. 17Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”
18Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu. 19Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwa da ƙasa take bayarwa. 20Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”
21Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai. 22Ya Urushalima, dā kamar azurfa kike, amma yanzu ba ki da amfani, dā kamar kyakkyawan ruwan inabi kike, amma yanzu baƙin ruwa ne kaɗai. 23Shugabanninku 'yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari'a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.
24Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra'ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba. 25Zan hukunta ku. Zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe, in kawar da dukan ƙazantarku. 26Zan ba ku shugabanni da mashawarta kamar waɗanda kuke da su dā can. Sa'an nan za a ce da Urushalima adala, amintaccen birni.”
27Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can. 28Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.
29Za ku yi da na sani, ku da kuka taɓa yin sujada ga itatuwa da dashe-dashen masujada. 30Za ku bushe kamar busasshen itacen oak, kamar lambun da ba wanda yake ba shi ruwa. 31Daidai kamar yadda busasshen itacen da tartsatsin wuta ya fāɗa wa, haka mutane masu iko za su hallaka ta wurin mugayen ayyukansu, ba wanda zai iya hana a hallaka su.
(Mik 4.1-3)
1Ga jawabin da Allah ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz a kan Yahuza da Urushalima.
2A kwanaki masu zuwa, Dutse inda aka gina Haikali zai zama mafi tsayi duka. Al'ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi.
3Jama'arsu za su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”
4Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Masunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace, Al'ummai ba za su ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.
5Yanzu fa, zuriyar Yakubu, bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu!
6Ya Allah, ka rabu da jama'arka, zuriyar Yakubu. Ƙasa ta cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas, daga kuma ƙasar Filistiya. Jama'a suna bin baƙin al'adu. 7Ƙasarsu tana cike da azurfa da zinariya, dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu tana cike da dawakai, karusansu kuma ba iyaka. 8Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.
9Za a ƙasƙantar da kowane mutum, a kunyata shi. Kada ka gafarta musu, ya Ubangiji!
10Za su ɓuya a cikin kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa! 11Rana tana zuwa sa'ad da girmankan 'yan adam zai ƙare, zai kuma lalatar da fāriyar 'yan adam. Sa'an nan Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka. 12A wannan rana, Ubangiji Mai Runduna zai ƙasƙantar da kowane mai iko, da kowane mai girmankai, da kowane mai fāriya. 13Zai hallaka dogayen itatuwan al'ul na Lebanon, da dukan itatuwan oak na ƙasar Bashan. 14Zai baje duwatsu da tuddai masu tsayi, 15da kowace doguwar hasumiya, da ganuwar kowace kagara. 16Zai nutsar da jiragen ruwa mafi girma mafi kyau. 17Girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fāriyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa'ad da wannan rana ta yi, 18za a shafe gumaka ƙaƙaf.
19Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya. 20Sa'ad da wannan rana ta yi za su zubar da gumakan da suka yi na zinariya da azurfa, za su bar wa ɓeraye da jemagu. 21Sa'ad da Ubangiji ya zo domin ya girgiza duniya, jama'a za su ɓuya a cikin kogwannin tuddai da ramummukan duwatsu, suna ƙoƙari su ɓuya daga fushinsa, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa.
22Kada ku dogara ga 'yan adam. Wace daraja take gare su>
1Yanzu fa Ubangiji, Ubangiji Mai Runduna, yana gab da ya kwashe kowane abu da kowane mutum da jama'ar Urushalima da na Yahuza suke dogara da su. Zai kwashe abincinsu da ruwan shansu, 2da jarumawansu, da sojojinsu, da alƙalansu, da annabawansu, da masu yi musu duba, da manyan mutanensu, 3da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da 'yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da suke faruwa. 4Ubangiji zai sa yaran da ba su balaga ba su mallaki jama'ar. 5Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.
6Lokaci yana zuwa sa'ad da mutanen wani dangi za su zaɓi ɗaya daga cikinsu, su ce, “Kai da kake da ɗan abin sawa za ka zama shugabanmu a wannan lokaci na wahala.”
7Amma zai amsa, ya ce, “Ba ni ba dai! Ba zan iya taimakonku ba. Ba ni ma da abinci sam, ko tufafi ma. Kada ku naɗa ni shugabanku!”
8Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa. 9Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.
10Adalai za su yi murna, kome zai tafi musu daidai. Za su ji daɗin abin da suka aikata. 11Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.
12Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu. Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
13Ubangiji a shirye yake ya hurta maganarsa, a shirye yake ya hukunta al'ummai. 14Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama'arsa a gaban shari'a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta. 15Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama'ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
16Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas. 17Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”
18Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu, 19da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu, 20da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu, 21da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu. 22Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu, 23da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.
24Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!
25Jama'ar garin, i, har da ƙarfafan mutane, za a kashe su a yaƙi. 26Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka. Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.
1Sa'ad da wannan lokaci ya yi, mata bakwai za su riƙe mutum guda su ce, “Mā iya ciyar da kanmu, mu kuma tufasar da kanmu, amma in ka yarda, bari mu ce kai ne mijinmu, domin kada mu sha kunyar zaman gwagwarci.”
2Lokaci na zuwa sa'ad da Ubangiji zai sa kowane tsiro da kowane itacen da yake a ƙasar su girma su yi kyau. Dukan jama'ar Isra'ila waɗanda suka ragu za su yi fāriya, su yi murna saboda amfanin da ƙasar take bayarwa. 3Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki. 4Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara'anta al'ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can. 5Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka. 6Ɗaukakarsa za ta inuwantar da birnin daga zafin rana, ta sa ya zama lafiyayyen wurin da aka kāre daga ruwan sama da hadiri.
1Ku saurara in raira muku wannan waƙa, Waƙar abokina da gonar inabinsa. Abokina yana da gonar inabi A wani tudu mai dausayi.
2Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun, Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau. Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu, Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin. Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna, Amma ko wannensu tsami ke gare shi.
3Saboda haka, abokina ya ce, “Ku jama'ar da kuke zaune a Urushalima da Yahuza, ku shara'anta tsakanina da gonar inabina. 4Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi 'ya'yan inabi masu tsami, maimakon 'ya'yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.
5“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta. 6Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”
7Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!
8Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar. 9Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye. 10Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”
11Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa. 12A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba. 13Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su. 14Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama'a masu hayaniya.
15Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su. 16Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa. 17A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.
18Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba. 19Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”
20Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.
21Kun shiga uku! A tsammaninku ku masu hikima ne, masu wayo ƙwarai.
22Kun shiga uku! Jarumawan kwalabar ruwan inabi! Masu ƙarfin zuciya marasa tsoro a gauraya shaye-shaye! 23Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari'ar gaskiya. 24Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya koya muku. 25Ubangiji yana fushi da jama'arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.
26Ubangiji ya ba da alama a kirawo al'ummar da take nesa. Ya yi musu fūto su zo daga bangon duniya. Ga shi kuwa sun iso da sauri nan da nan. 27Ko ɗaya ba wanda ya gaji, ba kuwa wanda ya yi tuntuɓe. Ba su yi gyangyaɗi ko barci ba. Ba abin ɗamarar da ya kwance, ba igiyar takalmin da ta tsinke. 28Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne. 29Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.
30Sa'ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra'ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken.
1A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali. 2Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi. 3Suna ta kiran junansu suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne! Ɗaukakarsa ta cika duniya.”
4Amon muryoyinsu ya sa harsashin ginin Haikali ya girgiɗa, Haikalin kansa kuma ya game da hayaƙi.
5Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”
6Sa'an nan ɗaya daga cikin talikan ya tashi ya sauko zuwa gare ni, yana riƙe da garwashin wuta wanda ya ɗauko da arautaki daga bagade. 7Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
8Sai na ji Ubangiji yana cewa, “Wa zan aika? Wa zai zama manzonmu?” Sai na amsa na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
9Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.” 10Sa'an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”
11Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani. 12Zan sa jama'a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango. 13Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.” Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama'ar Allah zuwa gaba.
1Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.
2Labari ya kai gun Sarkin Yahuza, cewa sojojin Suriya sun shiga ƙasar Isra'ila. Sai shi da dukan jama'arsa suka firgita ƙwarai, suna ta kaɗuwa kamar itatuwan da iska take kaɗawa.
3Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Ka ɗauki ɗanka Sheyar-yashub ka je ka sami sarki Ahaz. Za ka same shi a hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a wajen ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga kududdufin da yake sama da ita. 4Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin 'yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba. 5Suriya tare da Isra'ila da sarkinta sun ƙulla maƙarƙashiya. 6Nufinsu su kai wa ƙasar Yahuza yaƙi, su tsoratar da jama'a, don su haɗa kai da su, sa'an nan su naɗa ɗan Tabeyel.
7“Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba. 8Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba. 9Samariya ita ce ƙarfin Isra'ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya. “Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”
10Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce, 11“Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”
12Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”
13Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure? 14Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel. 15In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. 16Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.
17“Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!
18“A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma. 19Za su zo jingim su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, za su rufe kowane fili mai ƙayayuwa da kowace makiyaya.
20“A lokacin nan, Ubangiji zai yi ijara da wanzami daga wancan hayi na Yufiretis, wato Sarkin Assuriya! Zai aske gyammanku, da gashin kawunanku, da na jikunanku.
21“A lokacin nan, ko da karsana ɗaya da awaki biyu kaɗai manomi yake da su, 22za su ba da isasshiyar madarar da za ta biya dukan bukatarsa. Hakika dukan waɗanda suka ragu a ƙasar za su sami yawan albarka su ƙoshi.
23“A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. 24Ba wanda yake da ƙarfin hali da zai iya tafiya can, sai ko wanda yake da kwari da baka. Hakika ƙasar duka za ta cika da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa. 25Dukan tuddai inda dā akan shuka amfanin gona, za su cika da ƙayayuwa, har da ba mai iya zuwa wurin. Zai zama wurin kiwon shanu da tumaki.”
1Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki allo babba ka rubuta a kansa da manyan harufa, “‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.” 2Nemo mutum biyu amintattu, wato Uriya firist, da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama shaidu.”
3Bayan wannan na yi jima'i da matata annabiya. Ta ɗauki ciki, ta haifi ɗa namiji, Ubangiji ya ce mini, “Ka raɗa masa suna, “‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.” 4Kafin yaron ya isa kiran mama ko baba, Sarkin Assuriya zai kwashe dukan dukiyar Dimashƙu da dukan ganimar Samariya.”
5Ubangiji kuma ya sake yi mini magana. 6Ya ce, “Saboda wannan jama'a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa, suka yi ta rawar jiki a gaban sarki Rezin da sarki Feka, 7ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa. 8Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.” Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar.
9Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro! 10Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.
11Bisa ga ikonsa mai girma Ubangiji ya faɗakar da ni kada in bi hanyar da jama'ar ke bi. Ya ce, 12“Kada ka haɗa kanka da jama'a cikin ƙulle-ƙullensu, kada kuma ka ji tsoron abubuwan da su suke jin tsoro. 13Ka tuna fa, ni Ubangiji Mai Runduna, mai tsarki ne. Wajibi ne ni kaɗai za ka ji tsoro. 14Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima. 15Da yawa za su yi tuntuɓe su faɗi. Za su faɗi, a kuwa ragargaza su. Za a kama su da tarko.”
16Almajiraina su ne za su lura, su kuma kiyaye jawabin da Allah ya ba ni. 17Ubangiji ya ɓoye kansa daga jama'arsa, amma ni na dogara gare shi, na kafa zuciyata a gare shi.
18Ga ni tare da 'ya'yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama'ar Isra'ila.
19Mutane za su riƙa ce muku ku nemi shawarar 'yan bori da masu sihiri waɗanda suke shaƙe muryar, har ba a jin abin da suke faɗa. Za su ce, “Ai, ma, ya kamata mutane su nemi shawara daga aljannu, su kuma nemi shawarar matattu saboda masu rai.”
20Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”
21Mutane za su yi ta kai da kawowa a ko'ina cikin ƙasar, cikin matsuwa da yunwa. A yunwar da suke sha da haushin da suke ji, za su zagi sarkinsu, su kuma zagi Allahnsu. Har ma zai yiwu su ɗaga ido su dubi sararin sama, 22ko su zura wa ƙasa ido, amma ba abin da za su gani, sai wahala da duhu mai banrazana, inda za a kora su a ciki.
1Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.
2Jama'ar da suka yi tafiya cikin duhu, Sun ga babban haske! Suka zauna a inuwar mutuwa, Amma yanzu haske ya haskaka su.
3Ka ba su babbar murna, ya Ubangiji, Ka sa su yi farin ciki. Suna murna da abin da ka aikata, Kamar yadda mutane suke murna sa'ad da suke girbin hatsi, Ko sa'ad da suke raba ganima.
4Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu, Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi. Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al'ummar Da ta zalunci jama'arka, ta kuma zambace su, Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni.
5Takalman sojojin da suka kawo yaƙi Da dukan tufafinsu da suka birkiɗe da jini, Za a ƙone su da wuta!
6Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama.”
7Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
8Ubangiji ya hurta hukunci a kan mulkin Isra'ila, da a kan zuriyar Yakubu. 9Dukan jama'ar Isra'ila, duk wanda yake zaune a birnin Samariya, zai sani Ubangiji ne ya aikata haka. Yanzu suna da girmankai suna fāriya. Sun ce, 10“Gine-ginen da aka yi da tubali sun rushe, amma za mu sāke gina su da dutse. An sassare ginshiƙan da aka yi da itacen durumi, amma za mu sāke kakkafa su da kyawawan itatuwan al'ul.”
11Ubangiji ya kuta maƙiyansu daga Rezin su fāɗa su da yaƙi. 12Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra'ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
13Jama'ar Isra'ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba. 14A rana ɗaya Ubangiji zai hukunta shugabannin Isra'ila da jama'arta. Zai hallaka kawunansu da ƙafafunsu, da dabino da iwa, 15wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi! 16Su waɗanda suke bi da jama'an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum. 17Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
18Muguntar jama'a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta yake murtukewa har sama. 19Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko'ina a ƙasar, yana hallakar da jama'a, kowa na ta kansa. 20A ko'ina a ƙasar jama'a sukan wawashe su ci ɗan abincin da suke iya samu, amma ba su taɓa ƙoshi ba. Har 'ya'yansu ma suke ci! 21Jama'ar Manassa da jama'ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
1Kun shiga uku! Kuna kafa dokokin rashin gaskiya don ku zalunci jama'ata. 2Ta haka kuke hana wa talakawa hakkinsu, kuna kuma ƙin yi musu shari'ar gaskiya. Ta haka kuke ƙwace dukiyar gwauraye, wato matan da mazansu suka rasu, da ta marayu. 3Me za ku yi sa'ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa'ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku? 4Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
5Ubangiji ya ce, “Assuriya! Ina yin amfani da Assuriya kamar kulki don in hukunta waɗanda nake fushi da su. 6Na aiki Assuriya ta faɗa wa al'ummar da ba ta tsoron Allah, da yaƙi, wato jama'ar da ta sa na yi fushi. Na aike su su yi waso su yi sata, su tattake jama'a kamar ƙura a tituna.”
7Amma Sarkin Assuriya yana da nasa mugayen shirye-shirye da zai yi. Ya yi niyya ya hallaka al'ummai masu yawa. 8Ya yi kurari, ya ce, “Kowane shugaban mayaƙana sarki ne! 9Na ci biranen Kalno da na Karkemish. Na ci biranen Hamat da na Arfad. Na kuma ci Samariya da Dimashƙu. 10Na miƙa hannuna don in hukunta wa waɗannan mulkoki masu bauta wa gumaka, wato gumakan sun yi yawa fiye da na Urushalima, da na Samariya. 11Na hallaka Samariya da dukan gumakanta, haka ma zan yi wa Urushalima da siffofin da suke yi wa sujada a can.”
12Ubangiji ya ce, “Sa'ad da na gama abin da nake yi a kan Dutsen Sihiyona da cikin Urushalima, zan hukunta Sarkin Assuriya saboda dukan kurarinsa da girmankansa.”
13Sarkin Assuriya ya yi kurari ya ce, “Dukan waɗannan ni da kaina na yi su. Ni ƙaƙƙarfa ne, mai hikima, mai wayo. Na kawar da kan iyakokin da suke tsakanin ƙasashen sauran al'umma, na kwashe dukan abin da suka tattara suka adana. Kamar bijimi, haka na tattake mutanen da suke zaune a can. 14Al'umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”
15Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”
16Ubangiji Mai Runduna zai aukar da cuta don ya hukunta waɗanda suke ƙosassu yanzu. Za su ji jikinsu na ta ƙuna kamar wuta. 17Allah da yake hasken Isra'ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. 18Jeji mai dausayi da ƙasar noma za a lalatar da su ƙaƙaf, kamar yadda ciwon ajali yake hallaka mutum. 19Sai 'yan itatuwa kaɗan za su ragu, ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.
20Lokaci zai yi sa'ad da jama'ar Isra'ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al'ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra'ila. 21Kaɗan daga cikin jama'ar Isra'ila za su koma wurin Allahnsu Mai Iko Dukka. 22Ko da yake yanzu akwai jama'ar Isra'ila da yawa, yawansu kuwa kamar yashin teku, duk da haka, sai kaɗan ne za su komo. An tanada wa jama'a hallaka, sun kuwa cancanci hallakar. 23Hakika a ƙasar duka, Ubangiji Allah Mai Runduna zai kawo hallaka kamar yadda ya ce zai yi.
24Ubangiji Mai Runduna ya ce wa jama'arsa da suke Sihiyona, “Kada ku ji tsoron Assuriyawa, ko da yake suna wahalshe ku kamar yadda Masarawa suka yi. 25Saura kaɗan in gama hukuncin da nake yi muku, sa'an nan in hallaka su. 26Ni, Ubangiji Mai Runduna, zan bulale su da bulalata, kamar yadda na bugi mutanen Madayana a dutsen Oreb. Zan sa Assuriyawa su sha wahala kamar yadda Masarawa suka sha. 27A lokacin nan zan 'yantar da ku daga mulkin Assuriya, karkiyarsu ba za ta ƙara zama kaya mai nauyi a wuyanku ba.”
28Magabta suna cikin Ayiyat! Sun bi ta Migron! Sun bar kayayyakinsu a Mikmash! 29Sun ƙetare hanya suka kwana a Geba! Mutanen Rama suka firgita. Mutanen da suke cikin Gibeya, garin sarki Saul, sun gudu. 30Ku yi ihu, ku mutanen Gallim! Ku kasa kunne, ku mutanen Layish! Ku amsa, ku mutanen Anatot! 31Jama'ar Madmena da na Gebim suna gudu su tsira da rayukansu. 32Yau abokan gāba suna cikin Nob, daga can suke nuna wa Dutsen Sihiyona yatsa, wato wanda yake cikin Urushalima.
33Ubangiji Mai Runduna zai sa su ragargaje har ƙasa, kamar rassan da aka sassare daga itace. Masu girmankai da manyansu za a datse su ƙasa, a ƙasƙantar da su. 34Ubangiji zai sassare su har ƙasa kamar yadda ake sassare itatuwa da gatari a tsakiyar kurmi, kamar yadda itatuwa mafi kyau na Lebanon za su fāɗi.
1Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, hakanan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.
2Ikon Ubangiji zai ba shi hikima, Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa. Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa,
3Zai ji daɗin yin hidimarsa. Ba zai yi shari'ar ganin ido ko ta waiwai ba.
4Zai yi wa matalauta shari'a daidai. Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u. Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar, Mugaye za su mutu.
5Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.
6Kyarketai da tumaki za su zauna tare lafiya. Damisoshi za su kwanta tare da 'yan awaki. 'Yan maruƙa da kwiyakwiyan zaki za su yi kiwo tare, Ƙananan yara ne za su lura da su.
7Shanu da beyar za su yi kiwo tare, 'Yan maruƙansu da kwiyakwiyansu za su kwanta lafiya. Zaki zai ci ciyawa kamar sā.
8Jariri zai yi wasa kusa da maciji mai mugun dafi Amma ba zai cuta ba.
9A kan Sihiyona, dutse tsattsarka, Ba wani macuci ko mugu. Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji Kamar yadda tekuna suke cike da ruwa.
10Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi. 11A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku. 12Ubangiji zai ɗaga tuta, alama ce ta nuna wa sauran al'umma, ya sāke tattara jama'ar Isra'ila da ta Yahuza waɗanda aka warwatsa, ya sāke komo da su daga kusurwoyi huɗu na duniya. 13Masarautar Isra'ila ba za ta ƙara jin kishin Yahuza ba, Yahuza kuma ba za ta zama abokiyar gābar Isra'ila ba. 14Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama'ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya. 15Ubangiji zai kawo iska mai zafi wadda za ta busar da Kogin Nilu, da na Yufiretis. Zai bar ƙananan rafuffuka bakwai ne kaɗai, don kowa da kowa ya taka ya haye. 16Za a yi babbar karauka daga Assuriya domin sauran mutanen Isra'ila da suka ragu a can, kamar yadda aka yi wa kakanninsu sa'ad da suka bar Masar.
1Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni, Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.
2Allah ne Mai Cetona, Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba. Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi, Shi ne Mai Cetona.”
3Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki, Hakanan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.
4A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi! Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata! Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!
5Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata. Bari dukan duniya ta ji labarin.
6Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.”
1Wannan shi ne saƙo a kan Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa daga wurin Allah.
2A kan tudun da yake faƙo ka kafa tutar yaƙi, ka ta da murya ka ba mayaƙa umarni, ka ɗaga hannu, ka ba su alamar kama yaƙi a ƙofofin birni mai alfarma. 3Ubangiji ya kira mayaƙansa masu jin kansu, masu ƙarfin zuciya, domin su yi jahadi, su hukunta wa waɗanda suke fushi da su.
4Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi. 5Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.
6Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka. 7Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa. 8Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya. 9Ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana ce ta zafin fushinsa. Za a mai da duniya jeji, a hallaka kowane mai zunubi. 10Kowane tauraro, da kowace ƙungiyar taurari za su daina ba da haske. Rana za ta yi duhu lokacin da ta fito, wata kuwa ba zai ba da haske ba.
11Ubangiji ya ce, “Zan kawo masifa a duniya. Zan hukunta dukan mugaye saboda zunubansu. Zan ƙasƙantar da kowane mai girmankai. Zan hukunta kowane mai izgili da mai mugunta. 12Sauran da suka ragu za su fi zinariya wuyar samuwa. 13Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa'ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.
14“Baƙin da suke zaune a Babila za su gudu zuwa ƙasashensu, suna a warwatse kamar bareyin da suke tsere wa maharbansu, kamar tumakin da ba su da makiyayi. 15Duk wanda aka kama za a soke shi ya mutu. 16Sa'ad da suke cikin halin ƙaƙa naka yi, za a fyaɗa 'ya'yansu ƙasa, su mutu. Za a washe gidajensu, a yi wa matansu faɗe.”
17Ubangiji ya ce “Ina zuga mutanen Mediya, don su faɗa wa Babila da yaƙi. Ba su kula da azurfa ba, ba kuwa za a jarabce su da zinariya ba. 18Da bakkuna da kibansu, za su karkashe samari. Ba za su nuna jinƙai ga jarirai ba, ba kuwa za su ji tausayin 'yan yara ba. 19Daular Babila ita ce mafi kyau duka, abin fāriya ce ga jama'arta. Amma ni Ubangiji, zan kaɓantar da ita kamar yadda na yi da Saduma da Gwamrata! 20Ba wanda zai ƙara zama a cikinta. Ba wani Balaraben da yake yawo da zai kafa alfarwarsa a can. Ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can. 21Za ta zama wurin zaman namomin jejin hamada, inda mujiyoyi za su yi sheƙarsu. Jiminai za su zauna a can, awakin jeji za su yi ta warnuwa a cikin kufanta. 22A hasumiyarta da fādodinta za a ji amsar ihun koke-koken kuraye da na diloli. Lokacin Babila ya yi! Kwanakinta sun kusa ƙarewa!”
1Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su. 2Al'ummai da yawa za su taimaki jama'ar Isra'ila su koma ƙasarsu wadda Ubangiji ya ba su. A can sauran al'umma za su yi wa Isra'ila hidima kamar bayi. Waɗanda suka kama Isra'ilawa a dā yanzu Isra'ilawa za su kama su. Jama'ar Isra'ila za ta mallaki waɗanda suka taɓa zaluntarsu.
3Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama'ar Isra'ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi. 4Sa'ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba'a. Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba! 5Ubangiji ya ƙare mulkin mugun, 6wanda yake zaluntar jama'a a husace, bai taɓa daina tsananta wa al'ummai ba, wanda ya ci da yaƙi. 7Yanzu magana ta ƙare, duniya duka tana jin daɗin hutawa da salama. Kowa na ta raira waƙar murna. 8Itatuwan fir da itatuwan al'ul na Lebanon suna murna da faɗuwar sarkin! Ba wanda zai tasar musu da sara!
9“Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu. 10Dukansu suka yi kira gare shi, suka ce, “‘Ashe, kai ma rarrauna ne kamarmu! Ka zama ɗaya daga cikinmu. 11Dā ana ɗaukaka ka da kaɗe-kaɗen garaya, amma yanzu ga ka a lahira! Kana kwance a kan tsutsotsi. Kana rufe da tsutsotsi!”
12Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa. 13Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare. 14Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka. 15Amma a maimakon haka an saukar da kai a sashe mafi zurfi a lahira.
16Matattu za su zura maka ido su yi mamaki. Za su yi tambaya su ce, “Ashe, ba wannan mutum ba ne ya girgiza duniya, ya sa mulkoki suka jijjigu? 17Wannan shi ne wanda ya hallaka birane, ya mai da duniya hamada, wanda bai taɓa sakin ɗaurarru ko ya bar su su koma gida ba?” 18Dukan sarakunan duniya suna kwance a cikin manya manyan kaburburansu, 19amma kai ba ka sami kabari ba, jefar da gawarka aka yi don ta ruɓe. Aka hautsuna gawarka da gawawwakin mayaƙan da aka kashe cikin yaƙi. Tare da su aka jefa ka gangaren dutse, aka tattake. 20Ba za a binne ka kamar sauran sarakuna ba, saboda ka lalata da ƙasarka, ka karkashe mutanenka. Daga cikin mugayen iyalinka ba wanda zai ragu. 21A fara yanyanka su! 'Ya'ya maza na sarkin nan za su mutu saboda zunuban kakanninsu. Daga cikinsu ba wanda zai taɓa mallakar duniya, ko ya cika ta da birane.
22Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan. 23Zan su Babila ta zama fadama, mujiyoyi za su zauna a can. Zan kuwa share Babila da tsintsiyar da za ta share kome. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”
24Ubangiji Mai Runduna ya rantse, ya ce, “Abin da na riga na shirya, haka zai faru. Abin da na yi niyyar yi, za a yi. 25Zan hallaka Assuriyawa a ƙasata ta Isra'ila, in tattake su a kan duwatsuna. Zan 'yantar da jama'ata daga karkiyar Assuriyawa, daga nauyin da suka tilasta musu su ɗauka. 26Abin da na shirya zan yi wa duniya, shi ne in miƙa hannuna domin in hukunta wa al'ummai.” 27Ubangiji Mai Runduna ne ya ƙudura ya yi wannan, ya miƙa dantsensa don ya yi hukunci, ba kuwa mai iya hana shi.
28Wannan shi ne jawabin da aka yi shelarsa a shekarar da sarki Ahaz ya rasu.
29Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama! 30Ubangiji zai zama makiyayin jama'arsa wadda take talauce, zai kuma sa su zauna lafiya. Amma ku Filistiyawa, zai aukar muku da matsananciyar yunwa, wadda ba za ta bar ko ɗayanku da rai ba.
31Ku yi kururuwa, ku yi kuka na neman taimako, dukanku biranen Filistiya! Ku razana dukanku! Ƙurar da ta murtuke tana zuwa daga arewa, mayaƙa ne, ba kuwa matsorata a cikinsu.
32Ƙaƙa za mu amsa wa manzannin da suka zo gare mu daga Filistiya? Za mu faɗa musu, cewa Ubangiji ya tabbatar da Sihiyona, jama'arsa da take shan wahala kuwa za su sami zaman lafiya a can.
1Wannan shi ne jawabi a kan Mowab. Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa. 2Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki. 3Mutane a tituna sun sa tsummoki a jikinsu, suka taru a filayen taruwa na birni da a kan rufin ɗakuna, sai makoki suke suna ta kuka. 4Mutanen Heshbon da na Eleyale suka yi kuka da ƙarfi, har ana iya jin kukansu daga Yahaza. Har mayaƙa ma sun yi rawar jiki, zuciyarsu ta karai. 5Zuciyata ta yi kuka ainun saboda Mowab! Mutane sun gudu zuwa cikin garin Zowar. Waɗansu sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka, waɗansu sun tsere zuwa Horonayim, suna hargowa saboda baƙin ciki. 6Rafin Nimra ya ƙafe, ciyawar da take gefensa ta bushe, ba sauran wani ɗanyen abu. 7Mutane sun haye kwarin Larabawa, suna ƙoƙari su tsere da dukan abin da suka mallaka. 8A ko'ina a kan iyakokin Mowab, sai ƙugin kukansu ake ji. Ana kuwa ji daga garuruwan Eglayim da Biyer-elim. 9A garin Dibon, kogin ya yi ja wur da jini, Allah kuwa ya tanada wa mutanen wurin abin da ya fi wannan muni. Hakika za a yi wa duk wanda ya ragu a Mowab mummunan kisa.
1Daga birnin Sela a hamada, mutanen Mowab za su aiko da kaiwar rago ga mai mulki a Urushalima. 2Za su dakata a gaɓar kogin Arnon, za su yi ta kai da kawowa kamar tsuntsayen da aka kora daga sheƙunansu.
3Suna ce wa mutanen Yahuza, “Ku faɗa mana abin da za mu yi. Ku kāre mu, ku bar mu mu huta a inuwarku mai sanyi kamar inuwar itace da tsakar rana. Mu 'yan gudun hijira ne, ku ɓoye mu inda ba wanda zai gan mu. 4Ku bar mu mu zauna ƙasarku. Ku kāre mu daga masu neman hallaka mu.” Zalunci da hallakarwa za su ƙare, masu lalatar da ƙasar za su ƙare. 5Sa'an nan wani daga cikin zuriyar Dawuda zai zama sarki. Zai mallaki jama'a da aminci da ƙauna. Zai aikata abin da yake daidai da hanzari, zai sa a aikata adalci.
6Mutanen Yahuza sun ce, “Mun ji irin fāriyar da mutanen Mowab suke yi. Mun sani su masu girmankai ne, masu ruba, amma fankamarsu ta banza ce.”
7Mutanen Mowab za su yi kuka saboda wahalar da suke sha. Dukansu za su yi kuka sa'ad da suka tuna da kyakkyawan abincin da suka riƙa ci a birnin Kir-hareset. Za a kore su har su fid da zuciya. 8Gonakin da suke kusa da Heshbon, da gonakin inabin da suke Sibma an lalatar da su, gonakin inabin nan waɗanda ruwan inabinsu yake sa masu mulkin al'ummai su bugu. Da kurangunsu sun taɓa yaɗuwa zuwa gabas har suka kai birnin Yazar da cikin hamada, wajen yamma kuma sai da suka dangana da gefen Tekun Gishiri. 9Yanzu ina kuka saboda gonakin inabin Sibma kamar yadda na yi wa na Yazar. Na zub da hawayena saboda Heshbon da Eleyale, domin ba a sami kaka mai albarka ba, wadda za ta sa mutane yin murna. 10Ba wanda yake farin ciki a cikin sauruka masu dausayi. Ba wanda yake sowa ko waƙa a cikin gonakin inabi. Ba mai matse ruwan inabi, sowar murna ta ƙare. 11Na yi nishi da ɓacin zuciya a kan Mowab, na yi nishi da baƙin ciki saboda Kir-heres. 12Mutanen Mowab sun gajiyar da kansu da zuwa wurin matsafarsu na kan dutse da masujadarsu, suna addu'a, amma ba zai amfana musu kome ba.
13Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya riga ya yi a kan Mowab. 14Yanzu Ubangiji ya ce, “A shekara uku daidai, dukiyar Mowab mai yawan nan za ta ƙare. Daga cikin ɗumbun mutanenta 'yan kaɗan ne kaɗai zai su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”
1Wannan shi ne jawabi a kan Dimashƙu. Ubangiji ye ce, “Dimashƙu ba za ta ƙara zama birni ba, za ta zama tsibin kufai ne kawai. 2Za a watse a bar biranen Suriya har abada. Za su zama makiyayar tumaki da shanu. Ba wanda zai tsoratar da su. 3Ba za a kāre Isra'ila ba, Dimashƙu kuma za ta rasa 'yancinta. Suriyawan da suka ragu za su sha wulakanci kamar mutanen Isra'ila. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”
4Ubangiji ya ce, “Rana taba zuwa, ran da girman Isra'ila zai ƙāre, fatara za ta gāje gurbin dukiyarsu. 5Isra'ila za ta zama kamar gonar da aka girbe, aka yanke amfaninta, ta zama marar kome kamar gona a kwarin Refayawa sa'ad da aka ɗebe amfaninta. Mutane kima ne kurum za su ragu. 6Isra'ila kuma za ta zama kamar itacen zaitun wanda aka karkaɗe 'ya'yansa, aka bar biyu ko uku kawai a ƙwanƙolin itacen, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassansa. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”
7A wannan rana, mutane za su juyo neman taimako ga Mahaliccinsu, Allah Mai Tsarki na Isra'ila. 8Ba za su ƙara dogara ga bagaden da suka yi da hannuwansu ba, ko kuwa su dogara ga ayyukan hannuwansu, ko keɓaɓɓun wuraren da suke wa gumaka sujada, ko bagadai don ƙona turare.
9A wannan rana, za a watse a bar birane masu ƙaƙƙarfar kagara su zama kufai a jeji kuwa kamar rassan da aka watsar a gaban jama'ar Isra'ila.
10Isra'ila, kin manta da Allah wanda ya kuɓutar da ke, wanda ya kāre ki kamar babban dutse. Kin dasa wa kanki lambuna masu ni'ima don ki yi wa gumaka sujada. 11Amma ko da za su toho su yi fure a safiyar da kuka dasa su, duk da haka ba za a girbe kome ba. Wahala ce kaɗai da azabar da ba ta warkuwa.
12Al'ummai masu iko sun hargitse suna ta rugugi kamar rurin teku, kamar karon manyan raƙuman ruwa. 13Al'ummai sun ci gaba kamar sukuwar raƙuman ruwa, amma Allah ya tsauta musu suka kuwa janye, aka kora su kamar ƙura a gefen dutse, kamar kuma tattaka a cikin guguwa. 14Da maraice sukan ba da tsoro, amma da safe ba su! Wannan ita ce ƙaddarar duk wanda ya washe ƙasarmu!
1A hayin kogunan Habasha akwai wata ƙasa inda ake jin amon fikafikai. 2Daga waccan ƙasar wakilai sukan gangaro daga Kogin Nilu a cikin jiragen ruwa da aka yi da iwa. Ku koma gida, ku manzanni masu gaggawa! Ku kai saƙo ƙasarku, can a mafarin Kogin Nilu, zuwa ga al'ummarku mai ƙarfi mai iko, zuwa ga dogayen mutanenku masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya.
3Kowane mutum da yake a duniya ya kasa kunne, ko wanne da yake zaune a duniya, ya duba tutar, alama da za a ɗaga sama a ƙwanƙolin duwatsu, ya kasa kunne ga busar ƙaho! 4Ubangiji ya ce mini “Zan duba daga samaniya a hankali kamar yadda raɓa take saukowa a natse da gumin dare a lokacin girbi, hasken rana kuma a yini. 5Kafin a tattara 'ya'yan inabi, sa'ad da furanni duka suka karkaɗe, 'ya'yan inabi suna ta nuna, haka magabta za su hallaka Habasha a sawwaƙe kamar yadda ake faffalle rassan kurangar inabi da wuƙa. 6Za a bar gawawwakin sojojinsu a fili domin tsuntsaye da namomin jeji su zama abincin tsuntsaye de bazara, abincin namomin jeji kuma a lokacin sanyi.”
7A wannan lokaci Ubangiji Mai Runduna zai karɓi hadayu daga wannan ƙasa, a mafarin Kogin Nilu, wato wannan ƙaƙƙarfar al'umma mai iko, waɗannan dogayen mutane masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya. Za su zo Dutsen Sihiyona, inda ake yi wa Ubangiji Mai Runduna sujada.
1Wannan shi ne jawabi a kan Masar. Ubangiji yana zuwa Masar a kan girjije a sukwane. Gumakan Masarawa za su yi rawar jiki a gabansa, zuciyar Masarawa za ta karai. 2Ubangiji ya ce, “Zan ta da hargitsi a yi yaƙin basasa a Masar, ɗan'uwa ya yi gāba da ɗan'uwa, maƙwabci kuma gaba da maƙwabci. Biranen da suke hamayya za su yi faɗa da juna, sarakunan da suke hamayya kuma za su yi faɗa saboda neman iko. 3Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu. 4Zan ba da Masarawa a hannun azzalumi a hannun mugun sarki kuma da zai mallake su. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗi wannan.”
5Ruwan Kogin Nilu zai ƙafe, a hankali kogin zai bushe. 6Mazaunan kogin za su ji wari sa'ad da yake ƙafewa a hankali. Iwa da jema za su bushe. 7Dukan amfanin gonakin da aka shuka a gaɓar Kogin Nilu za su bushe, iska ta fyauce su. 8Duk wanda sana'arsa ta kama kifi ce a Kogin Nilu zai yi ƙugi ya yi kuka, gama ƙugiyoyinsa da tarunansa za su zama marasa amfani. 9Waɗanda suke yin tufafin lilin za su fid da zuciya, 10shugabanni da ma'aikata za su karai su kuma damu.
11Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can? 12Sarkin Masar, ina mashawartan nan naka masu hikima? Watakila za su iya faɗa maka shirye-shiryen da Ubangiji Mai Runduna ya yi domin Masar. 13Shugabannin Zowan da na Memfis wawaye ne. Su ake zaton za su bi da al'ummar, amma sai suka bi da su a karkace. 14Ubangiji ne ya sa su ba da gurguwar shawara. Sakamakon haka sai Masar ta yi ta aikata dukan abu a hugunce, tana tangaɗi kamar bugagge wanda santsi na kwasarsa cikin aman da ya yi. 15A Masar duka, attajiri da matalauci, ƙarami ko babba, ba wanda zai iya yin wani taimako.
16Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su. 17Mutanen Masar za su firgita saboda Yahuza, kowane lokaci za su tuna da ƙaddarar da Ubangiji Mai Runduna ya shirya dominsu.
18A wannan rana, za a yi amfani da harshen Ibrananci a birane biyar na Masar. Mutanen da suke can za su riƙa yin rantsuwarsu da sunan Ubangiji Mai Runduna. Za a sa wa ɗaya daga cikin biranen nan suna, “Birnin Hallaka.”
19A wannan rana, za a gina wa Ubangiji bagade a ƙasar Masar, za a keɓe masa ginshiƙi na dutse a kan iyakar Masar. 20Za su zama alamu na kasancewar Ubangiji Mai Runduna a Masar. Sa'ad da aka zalunci mutanen da suke can, za su yi kira ga Ubangiji su nemi taimako, zai aika musu wanda zai kuɓutar da su. 21Ubangiji zai bayyana kansa ga mutanen Masar, sa'ad da ya yi haka kuwa, za su karɓe shi, su yi masa sujada, su kuma kawo masa hadayu da sadakoki. Za su yi masa alkawarai ƙwarara, su kuwa cika abin da suka alkawarta. 22Ubangiji zai hukunta Masarawa, amma zai warkar da su. Za su juyo gare shi, shi kuma zai ji addu'o'insu ya warkar da su.
23A wannan rana, za a yi wata babbar hanya tsakanin Masar da Assuriya. Mutanen ƙasashen nan biyu za su yi ta kai da kawowa tsakaninsu, al'ummai biyu za su yi sujada tare. 24A wannan rana, za a lasafta Isra'ila tare da Masar da Assuriya, waɗannan al'ummai uku za su zama albarka ga dukan duniya. 25Ubangiji Mai Runduna zai sa musu albarka, ya ce, “Zan sa muku albarka, ke Masar, jama'ata, da take Assuriya wadda na halitta, da ke kuma Isra'ila zaɓaɓɓiyar jama'ata.”
1Bisa ga umarnin Sargon, Sarkin Assuriya, sai sarkin yaƙin Assuriya ya fāɗa wa Ashdod, birnin Filistiyawa, da yaƙi. 2A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa. 3Sa'ad da aka ci Ashdod, sai Ubangiji ya ce, “Bawana Ishaya ya yi ta yawo tsira, ba kuma takalmi a ƙafarsa har shekara uku. Wannan ita ce alamar abin da zai faru a ƙasa Masar da Habasha. 4Sarkin Assuriya zai kwashe kamammun yaƙi waɗanda ya kama a ƙasashen nan biyu, ya tafi da su tsirara. Matasa da manya kuma ba takalmi a ƙafafunsu, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar. 5Waɗanda suke dogara ga Habasha, suna kuwa fāriya da Masar, za su ruɗe, sa zuciyarsu zai wargaje. 6A wannan rana mutanen da suke zaune a gaɓar Filistiyawa za su ce, “‘Dubi abin da ya faru ga jama'ar da muka dogara da su don su tsare mu daga Sarkin Assuriya! Ƙaƙa za mu yi mu tsira?”
1Wannan shi ne jawabi a kan Babila. Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa. 2Na ga wahayi na waɗansu mugayen abubuwa, wato na cin amana da hallakarwa. Rundunar sojojin Elam, ku kama yaƙi! Rundunar sojojin Mediya ku kewaye birane da yaƙi. Allah zai kawar da wahalar da Babila ta haddasa.
3Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda. 4Kaina ya yi yum, ina ta rawar jiki saboda tsoro. Ina ta marmarin maraice ya yi, amma bai kawo mini kome ba, sai razana.
5A wahayin na ga an shirya biki, an shisshimfiɗa darduma inda waɗanda aka gayyata za su zauna. Suna ci suna sha. Farat ɗaya sai aka ji umarni cewa, “Jarumawa! Ku shirya garkuwoyinku.”
6Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sa mai tsaro, ka faɗa masa ya riƙa ba da labarin abin da ya gani. 7Idan ya ga mutane biyu biyu suna zuwa a kan dawakai, waɗansu kuma a kan raƙuma da jakuna, ka faɗa masa ya lura da su sosai.”
8Mai tsaro ya ce, “Ya mai girma, ina ta tsaro dare da rana a wurin da aka sa ni.”
9Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”
10Ya jama'ata, an buga ku kamar yadda ake bugun alkama a masussuka. Amma yanzu na kawo muku albishir wanda na ji daga wurin Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila.
11Wannan shi ne jawabi a kan Edom. Wani daga Edom ya kira ni ya ce, “Ya mai tsaro, gari ya kusa wayewa? Ka gaya mini har sai yaushe zai waye?”
12Sai na amsa na ce, “Gari zai waye, amma za a sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin tambaya, sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”
13Wannan shi ne jawabi a kan Arabiya. Ya ku jama'ar Dedan, waɗanda ayarorinku suka yi zango a ƙasar Arabiya wadda take faƙo, 14ku ba jama'a waɗanda suka zo gare ku masu jin ƙishi ruwa su sha. Ya ku jama'ar ƙasar Tema, ku ba 'yan gudun hijira abinci. 15Mutane suna gudu don su tsere wa takuban da za su kashe su, da bakkunan da za su harbe su, su kuma tsere wa dukan hatsarorin yaƙi.
16Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Saura shekara ɗaya tak girman kabilar Kedar zai ƙare. 17Jarumawan Kedar su ne maharba, amma sai kaɗan za su ragu daga cikinsu, ni, Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”
1Wannan shi ne jawabi a kan kwarin wahayi. Me yake faruwa? Me ya sa jama'ar birni duka suke biki a kan rufin gidaje? 2Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali. Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba. 3Dukan shugabanninku sun gudu, an kuwa kama su tun kafin su harba ko kibiya ɗaya. Dukanku da aka iske tare, aka kama ku, ko da yake kuka gudu da nisa. 4Ni dai ƙyale ni kurum, in yi ta kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta'azantar da ni, saboda yawancin mutanena sun mutu. 5Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.
6Sojojin ƙasar Elam sun zo kan dawakai suna rataye da kwari da baka. Sojojin ƙasar Kir sun shirya garkuwoyinsu. 7Kwarurukansu masu dausayi na ƙasar Yahuza suna cike da karusai, sojoji kuma a kan dawakai suna tsattsaye a ƙofofin Urushalima. 8Dukan kagaran Yahuza sun rushe. Sa'ad da wannan ya faru kun kwaso makamai daga cikin taskar makamai.
12Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki. 13A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”
14Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
15Ubangiji Mai Runduna ya faɗa mini in tafi wurin Shebna, mai hidimar iyalin gidan sarki, in ce masa, 16“Kana tsammani kai wane ne? Wa ya ba ka 'yancin sassaƙa wa kanka kabari a jikin duwatsu? 17Yana yiwuwa kai wani abu ne, amma Ubangiji zai ɗauke ka, ya jefar. 18Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka! 19Ubangiji zai fisshe ka daga maƙaminka, ya ƙasƙantar da kai daga babban matsayinka!”
20Ubangiji ya ce wa Shebna, “Idan haka ya faru zan aika wa bawana Eliyakim ɗan Hilkiya. 21Zan sa masa tufafin sarautarka, in ɗaura masa ɗamara, in kuma ba shi dukan ikon da kake da shi. Zai zama kamar uba ga jama'ar Urushalima da na Yahuza. 22Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa. 23Zan kafa shi da ƙarfi a wurin kamar turke, zai kuwa zama sanadin daraja ga dukan iyalinsa.
24“Amma dukan 'yan'uwansa da masu dogara gare shi za su zama nawaya a gare shi. Za su rataya gare shi kamar tukwane da ƙoren da aka sa a ragaya! 25Sa'ad da wannan ya faru ragayar da aka ɗaura tam za ta tsinke ta fāɗo. Wannan shi ne ƙarshen kowane abin da aka sa a cikin ragayar ke nan. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
1Wannan shi ne jawabi a kan Taya. Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin. 2Ku yi kuka ku fataken Sidon! Kun aika da mutane 3a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al'umma.
4Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar 'ya'ya ba, ban taɓa goyon 'ya'ya mata ko maza ba.”
5Har Masarawa ma za su firgita su razana, sa'ad da suka ji, cewa an hallakar da Taya.
6Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama'ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish! 7Ya yiwu kuwa a ce wannan Taya ce birnin farin ciki, wadda aka kafa ta tuntuni? Wannan kuwa ita ce birnin da ke aikawa da mutane hayin teku su kafa nahiyoyi? 8Wane ne wannan wanda ya shirya ya aukar wa Taya da wannan duka, wannan muhimmiyar alkarya, wadda fatakenta hakimai ne, waɗanda ake ɗaukaka su fiye da sauran mutane a duniya? 9Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.
10Ku je ku nomi ƙasarku jama'ar nahiyoyin Tarshish! Ba wanda zai ƙara kiyaye ku. 11Ubangiji ya miƙa dantsensa a kan tekun, ya hamɓarar da mulkoki. Ya umarta a lalatar da manyan biranen ciniki na Taya. 12Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama'arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.
13(Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)
14Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.
15Lokaci yana zuwa da za a manta da Taya har shekara saba'in, gwargwadon kwanakin sarki. Bayan waɗannan shekaru kuma, Taya za ta yi waƙa irin ta karuwa, cewa
16“Ɗauki garayarki, kewaya cikin gari, Ayya, an manta da karuwa! Yi kiɗa, sāke raira waƙoƙinki, Don ki komo da masoyanki.”
17Bayan shekara saba'in ɗin, Ubangiji zai bar Taya ta koma a kan cinikinta na dā, za ta ba da kanta ijara ga dukan mulkokin duniya. 18Kuɗin da ta samu ta kasuwanci za a keɓe wa Ubangiji. Ba za ta tara wa kanta ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada su za su yi amfani da kuɗinta don su saya wa kansu abinci da sutura da suke bukata.
1Ubangiji zai hallaka duniya ya bar ta kufai. Zai kaɓantar da duniya ya watsar da jama'ar da take cikinta. 2Bala'i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama'a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta. 3Duniya za ta ragargaje ta zama kufai. Ubangiji ne ya faɗa, haka kuwa za a yi.
4Duniya za ta bushe ta ƙeƙashe, duniya duka za ta raunana, duniya da sararin sama za su ruɓe. 5Jama'ar sun ƙazantar da duniya da suka keta dokokin Allah, suka ta da alkawarin da ya yi don ya dawwama. 6Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai. 7Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi, 8kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare. 9Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi. 10A cikin birni kome ya birkice, an kulle kowane gida don a hana mutane shiga. 11Mutane za su tsaya a tituna, suna ihu, suna neman ruwan inabi. Farin ciki ya ƙare har abada, ya ƙare a ƙasar. 12Birnin ya zama kango, an farfashe ƙofofinsa. 13Wannan shi ne abin da zai sami kowace al'umma ko'ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa'ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke 'ya'yan inabi daga kurangar inabi.
14Waɗanda suka tsira za su raira waƙa don farin ciki. Waɗanda suke wajen yamma za su ba da labarin girman Allah, 15waɗanda suke wajen gabas kuma za su yabe shi. Jama'ar da take zaune a gefen teku za su yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila. 16Daga manisantan wurare na duniya za mu ji waƙoƙin yabon Isra'ila, al'umma adala. Amma ba ni da sauran sa zuciya! Lalacewa nake yi! Maciya amana suna ta cin amana, cin amanarsu sai gaba gaba yake yi. 17Ya jama'ar duniya, razana, da wushefe, da tarkuna suna jiranku. 18Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga razana zai fāɗa cikin wushefe, wanda kuma ya tsere daga wushefe za a kama shi a tarko. Za a kwararo ruwa daga sama kamar da bakin ƙwarya, harsashin ginin duniya zai jijjigu. 19Duniya za ta tsage, ta farfashe ta wage. 20Duniya kanta za ta yi tangaɗi kamar mashayi, ta yi ta yin lau kamar rumfa a lokacin hadiri. Nauyin zunuban duniya ya rinjaye ta har ƙasa, za ta fāɗi, ba za ta ƙara tashi ba.
21A wannan rana Ubangiji zai hukunta wa ikoki na sama, da sarakunan da suke a duniya. 22Allah zai tattara sarakuna wuri ɗaya kamar ɗaurarru a rami, zai kulle su a kurkuku kafin lokacin da zai hukunta su ya yi. 23Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.
1Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka. Ka aikata al'amura masu banmamaki, Ka tafiyar da su da aminci, Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.
2Ka mai da birane kufai Ka lalatar da kagaransu, Wuraren da maƙiya suka gina kuwa, An shafe su har abada.
3Jama'ar al'ummai masu iko za su yabe ka, Za a ji tsoronka a biranen mugayen al'ummai.
4Matalauta da 'yan ƙaƙa naka yi sun sheƙa zuwa wurinka, Sun sami zaman lafiya a lokatan wahala. Ka ba su mafaka daga hadura, Ka inuwantar da su daga matsanancin zafi. Mugaye sukan tasar musu kamar hadirin ƙanƙara,
5Kamar fari a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Amma kai, ya Ubangiji, ka rufe bakin abokan gābanmu, Ka sa hayaniyar mugaye ta yi tsit, Kamar yadda girgije yake sanyaya zafin rana.
6A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al'umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau. 7A can ne zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan sauran al'umma. 8Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama'arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!
9Sa'ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”
10Ubangiji zai kiyaye Dutsen Sihiyona, amma za a tattake jama'ar Mowab a ƙasa, kamar yadda ake tattake tattaka cikin taki. 11Za su miƙa hannuwansu kamar suna ƙoƙarin yin ninƙaya, amma girmankansu zai jā hannuwansu ƙasa a duk sa'ad da suka ɗaga. 12Allah zai lalatar da kagaran Mowab da dogayen garukansu, ya rushe su ƙasa su zama ƙura.
1Rana tana zuwa da jama'a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza. Birni ƙaƙƙarfa ne, Allah kansa yake tsare garukansa!
2A buɗe ƙofofin birnin, A bar amintacciyar al'umma ta shiga, Al'ummar da jama'arta take aikata abin da yake daidai.
3Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji, Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi, Waɗanda suke dogara gare ka.
4Ku dogara ga Ubangiji har abada. Zai kiyaye mu kullayaumin.
5Ya ƙasƙantar da masu girmankai, Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki, Ya rusa garunsa ƙasa.
6Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu, Suna tattaka shi da ƙafafunsu.
7Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul, Hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya,
8Muna bin nufinka, muna sa zuciya gare ka. Kai kaɗai ne bukatarmu.
9Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya. Sa'ad da kake yi wa duniya da jama'arta shari'a Dukansu za su san yadda adalci yake.
10Ko da yake kana yi wa mugaye alheri, Duk da haka ba su taɓa koyon abin da yake na kirki ba. Har a nan ma, a ƙasar adalai, Suna ta aikata kuskure, Sun ƙi ganin girmanka.
11Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba. Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala, Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya. Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.
12Kai za ka wadata mu, ya Ubangiji, Duk abin da muka iya yi daga gare ka ne.
13Ya Ubangiji Allahnmu, waɗansu sun mallake mu, Amma kai kaɗai ne Ubangijinmu.
14Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba, Kurwarsu ba za ta tashi ba, Domin ka hukunta su, ka hallaka su. Ba wanda zai ƙara tunawa da su.
15Ya Ubangiji, ka sa al'ummarmu ta yi ƙarfi, Ka faɗaɗa karkararta a kowane gefe, Wannan kuwa ya sa ana girmama ka.
16Ka hukunta jama'arka, ya Ubangiji, A cikin azaba sun yi addu'a gare ka.
17Kai ne, ya Ubangiji, ka sa muka yi kuka, Kamar macen da take naƙuda tana kuka da azaba.
18Muna shan azaba da wahala, Amma ba abin da muka haifa. Ba mu ciwo wa ƙasarmu nasara ba, Ba abin da muka kammala!
19Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.
20Jama'ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa. 21Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.
1A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.
2A wannan rana Ubangiji zai yi magana a kan kyakkyawar gonar inabinsa, 3ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna. 4Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus. 5Amma idan maƙiyan jama'ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.”
6A wannan rana jama'ar Isra'ila, zuriyar Yakubu, za su yi saiwa kamar itace, za su yi toho, su yi fure. 'Ya'yan da suka yi za su cika duniya.
7Ubangiji bai hukunta Isra'ila da tsanani kamar yadda ya yi wa maƙiyanta ba, ba za su yi hasarar mutane da yawa ba. 8Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su. 9Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.
10Birni mai garu ya zama kufai. An bar shi kamar jejin da ba kowa ciki. Ya zama wurin kiwon shanu, inda za su huta su yi kiwo. 11Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.
12A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama'arsa, Isra'ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.
13A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra'ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa.
1Mulkin Isra'ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu. 2Ubangiji yana da wani ƙaƙƙarfa mai iko a shirye don ya fāɗa musu da yaƙi. Zai zo kamar hadirin ƙanƙara, kamar kwararowar ruwan sama, kamar kuma rigyawa mai kirmewa wadda ta shafe ƙasa. 3Za a tattake girmankan bugaggun shugabannin nan. 4Darajan nan mai dushewa ta shugabanni masu girmankai za ta shuɗe kamar 'ya'yan ɓaure, nunan fari, da aka tsinke aka cinye nan da nan da nunarsu.
5Rana tana zuwa da Ubangiji Mai Runduna zai zama kamar rawanin furanni mai daraja ga jama'arsa da suka ragu. 6Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.
7Har da annabawa da firistoci, tangaɗi suke yi, mashaya ne. Sun sha ruwan inabi da barasa da yawa, suna ta tuntuɓe barkatai. Annabawan sun bugu ƙwarai, har ba su iya fahimtar wahayin da Allah ya aiko musu ba, firistoci su ma sun bugu, har sun kāsa yanke shari'un da aka kawo musu. 8Duk sun cika teburorin da suke zaune da amai, ba inda ba su amaye ba.
9Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga 'yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani! 10Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”
11Idan ba za ku saurare ni ba, to, Allah zai yi amfani da baƙi masu magana da harshen da ba ku sani ba, su koya muku darasi. 12Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi. 13Saboda haka ne Ubangiji zai koya muku baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi. Sa'an nan kowane ɗaga ƙafar da kuka yi, za ku yi tuntuɓe, za a yi muku rauni, a kama ku a tarko, a kai ku kurkuku.
14Yanzu fa ku mutane masu girmankai, da kuke mulki a nan a Urushalima a kan wannan jama'a, ku saurara ga abin da Ubangiji yake faɗa. 15Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa'ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku. 16Yanzu fa ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan kafa ƙaƙƙarfan harsashin gini a Sihiyona. A kansa zan sa ƙaƙƙarfan dutsen kusurwa. A kansa an rubuta wannan magana, “‘Amincin da yake kafaffe mai haƙuri ne kuma.” 17Adalci ne zai zama igiyar gwajin tushen ginin, aminci kuma zai zama shacin dirin ginin.” Hadirin ƙanƙara zai share dukan ƙarairayin da kuke dogara gare su, rigyawa za ta hallakar da zaman lafiyarku. 18Alkawarin da kuka ƙulla da mutuwa ya tashi, yarjejeniyar da kuka yi da lahira, an soke ta. Sa'ad da masifa ta auko za a hallaka ku. 19Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana! 20Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana, wanda ya yi ƙoƙari ya kwanta a gajeren gado, ya kuma rufa da ɗan siririn bargo. 21Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al'ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al'ajabi ne.
22Kada ku yi dariya saboda faɗakarwar da nake yi muku! Idan kuwa kun yi, zai ƙara yi muku wuya ku tsira. Na ji niyyar da Ubangiji Mai Runduna ya yi, ta ya hallaka dukan ƙasar.
23Ku kasa kunne ga abin da nake cewa, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa muku. 24Manomi ba zai dinga huɗar gonakinsa har abada ba, ya yi ta shirya su domin shuka. 25Da zarar ya shirya ƙasar yakan shusshuka ganyayen ci, kamar su kanumfari da ɗaɗɗoya, yakan kuma dasa kunyoyin alkama da na sha'ir, a gyaffan gonakin kuwa yakan shuka hatsi. 26Ya san yadda zai yi aikinsa, gama Allah ya koya masa. 27Ba ya bugun kanumfari da ɗaɗɗoya da ƙaton kulki, a maimakon haka yakan yi da 'yan sanduna sirara. 28Ba zai yi ta bugun alkama, har ya ɓata tsabar ba, ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba. 29Dukan wannan hikima daga wurin Ubangiji Mai Runduna ne. Shirye-shiryen da Allah ya yi na hikima ne kullum kuwa sukan yi nasara!
1Bagaden Allah, Urushalima kanta, ƙaddara ta auko mata! Birnin da Dawuda ya kafa zango, ƙaddara ta auko mata! Bari shekara ɗaya ko biyu su zo su wuce suna shagulgulansu, suna bukukuwansu, 2sa'an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa! 3Allah zai tasar wa birnin, ya kewaye shi da yaƙi. 4Urushalima za ta zama kamar fatalwar da take ƙoƙarin yin magana daga ƙarƙashin ƙasa, guni yana fitowa daga turɓaya.
5Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani, 6Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta. 7Sa'an nan dukan sojojin sauran al'umma da suka fāɗa wa birni inda bagaden Allah yake da yaƙi, da dukan makamansu, da kayayyakin yaƙinsu, kome da kome za su shuɗe kamar mafarki, kamar tunanin dare. 8Dukan al'ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro.
9Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba! 10Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu. 11Za a ɓoye muku ma'anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake. 12In kuwa kun ba wanda bai iya karatu ba, kuka roƙe shi ya karanta muku, zai ce bai iya karatu ba.
13Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace. 14Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”
15Waɗanda suke ƙoƙarin ɓoye wa Ubangiji shirye-shiryensu sun shiga uku! Suna gudanar da dabarunsu a ɓoye, suna tsammani ba wanda zai gan su ko ya san abin da suke yi. 16Sun birkitar da kome! Wane ne ya fi muhimmanci, mai ginin tukwane ko yumɓun? Abin da mutum ya yi da hannunsa ya iya ce wa mutumin, “Ba kai ka yi ni ba?” Ko kuma zai iya ce masa, “Ai, ba ka san abin da kake yi ba?”
17Kamar yadda karin maganar ta ce, kafin a jima kurmi zai zama gona, gona kuma za ta zama kurmi.
18A wannan rana, kurame za su ji sa'ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani. 19Matalauta da masu tawali'u za su sāke samun farin ciki wanda Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya bayar. 20Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi. 21Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari'ar adalci.
22Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya fanshi Ibrahim daga wahala, ya ce, “Jama'ata, ba za a ƙara kunyatar da ku ba, fuskokinku ba za su ƙara yanƙwanewa don kunya ba. 23Za ku ga 'ya'yan da zan ba ku, sa'an nan ne za ku tabbatar, cewa ni ne Allah Mai Tsarki na Isra'ila. Za ku girmama ni, ku yi tsorona. 24Wawaye za su koya su gane, waɗanda a kullum sai gunaguni suke yi, za su yi murna su koya.”
1Ubangiji ya yi magana, ya ce, “Waɗanda suke mulkin Yahuza sun shiga uku, domin sun tayar mini. Suna aiki da shirye-shiryen da ba ni ne na yi ba, suka sa hannu a kan yarjejeniya gāba da nufina. Suna ta aikata zunubi a kan zunubi. 2Suna tafiya Masar neman taimako, ba su shawarce ni ba. Suna so Masar ta kāre su, saboda haka suka sa dogararsu ga Sarkin Masar. 3Amma sarkin zai rasa ikon taimakonsu, kāriyar da Masar za ta yi musu ƙarshenta masifa. 4Ko da yake jakadunsu sun riga sun isa Zowan da Hanes, biranen Masar, 5duk da haka jama'ar Yahuza za su yi da na sani, da suka dogara ga al'ummar da ba abar dogara ba ce, al'ummar da ba ta daɗa musu kome a lokacin da suke sa zuciya ga taimako ba.”
6Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba. 7Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, “‘Macijin da ba ya yin kome.”
8Allah ya faɗa mini in rubuta a littafi yadda mutane suke, saboda ya zama tabbatacciyar shaida a kansu. 9A kullum suna tayar wa Allah, a kullum ƙarya suke yi, a kullum suna ƙin kasa kunne ga koyarwar Allah. 10Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu. 11Tashi daga nan, kada ku toshe mana hanya. Ba ma so mu ji kome game da Allah Mai Tsarki na Isra'ila.”
12Amma wannan shi ne abin da Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya ce, “Kun yi banza da abin da nake faɗa muku, kuna dogara ga aikin kamakarya da yin zamba. 13Kun yi laifi. Kuna kamar bango wanda ya tsage daga bisa har ƙasa. Za ku fāɗi ba zato ba tsammani. 14Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami 'yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”
15Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba! 16A maimakon haka sai kuka shirya ku tsere wa maƙiyanku a kan dawakai masu gudu. Daidai ne, tilas ku tsere! Tsammani kuke saurin gudun dawakanku ya isa, amma waɗanda za su fafare ku sun fi ku gudu! 17Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da yake kan tudu. 18Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.
19Ku jama'ar da kuke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa'ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku. 20Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba. 21Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.” 22Za ku kwashe gumakanku waɗanda aka dalaye da azurfa, da waɗanda aka rufe da zinariya, ku jefar da su kamar abin ƙyama, kuna ihu, kuna cewa, “Ku ɓace mana da gani!” 23Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya. 24Takarkaranku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau duka. 25A wannan rana sa'ad da aka kame kagaran abokan gābanku, aka kashe jama'arsu, rafuffukan ruwa za su malalo daga kowane tsauni da kowane tudu. 26Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa'ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.
27Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta. 28Ya aika da iska a gabansa kamar rigyawa wadda take kwashe kome, ta tafi da shi. Yakan gwada al'ummai ya kai su hallaka, yakan sa dukan shirye-shiryensu na mugunta su ƙare. 29Amma ku, jama'ar Allah, za ku yi farin ciki, ku raira waƙa kamar yadda kukan yi a daren tsattsarkan idi. Za ku yi murna kamar waɗanda suke tafiya suna bushe-bushe a hanyarsu ta zuwa Haikalin Ubangiji Mai Tsarki, Mai Ceton Isra'ila.
30Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. 31Assuriyawa za su firgita sa'ad da suka ji muryar Allah, suka kuma ji irin zafin hukuncinsa. 32Sa'ad da Ubangiji ya miƙa sandan hukuncinsa ya yi ta bugun Assuriyawa, jama'arsa kuwa za su yi ta kaɗa ganguna da garayu, su yi murna! 33An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.
1Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba. 2Ya san abin da yake yi! Zai aika da bala'i. Zai ci gaba da niyyarsa ta hukunta wa mugaye duk da masu kiyaye su. 3Masarawa su ba Allah ba ne, mutane ne kurum! Dawakansu ba su wuce ikon ɗan adam ba! Sa'ad da Ubangiji zai matsa, ƙaƙƙarfar al'umma za ta marmashe, al'ummar da aka yi wa taimako kuma za ta fāɗi. Dukansu za su hallaka.
4Ubangiji ya ce mini, “Kamar dai makiyaya ba za su iya tsoratar da zakin da ya kashe dabba ba, kome irin tsawa da ihun da suka yi, haka ni ma, ba abin da zai iya hana ni, ni Ubangiji Mai Runduna, in kiyaye Dutsen Sihiyona. 5Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye 'ya'yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”
6Allah ya ce, “Jama'ar Isra'ila, kun yi mini zunubi, kuna kuwa yin gāba da ni. Amma yanzu ku komo wurina! 7Lokaci zai yi da dukanku za ku watsar da gumakan da kuka yi na azurfa da na zinariya. 8Assuriya za ta hallaka cikin yaƙi, amma ba ta wurin ikon mutum ba. Assuriyawa za su gudu daga bakin dāga, za a mai da majiya ƙarfinsu bayi. 9Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.
1Wata rana za a yi wani sarki mai adalci, da kuma shugabannin ƙasa waɗanda za su yi mulki da gaskiya. 2Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa. 3Idanunsu da kunnuwansu za su kasance a buɗe domin sauraron jama'a. 4Za su zama masu haƙuri sosai, za su yi kome da haziƙanci, za su kuma faɗi abin da suke nufi. 5Ba wanda zai girmama wawayen mutane, ko kuma ya ce da mazambata suna da aminci. 6Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha. 7Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu. 8Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.
9Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa. 10Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara. 11Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku. 12Ku bugi ƙirjinku don baƙin ciki, gama an lalatar da gonaki masu dausayi da kuma gonakin inabi, 13ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama'ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā. 14Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da suke tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.
15Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa. 16A ko'ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya. 17Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada. 18Gidajen jama'ar Allah za su zama da salama da zaman lafiya, ba abin da zai dame su. 19(Amma ƙanƙara za ta faɗo a jeji, za a kuma rurrushe birni.) 20Kowa zai yi murna da ruwan sama mai yawa domin amfanin gona, da kuma lafiyayyiyar makiyaya domin jakuna da shanu.
1Magabtanmu sun shiga uku! Sun yi fashi sun ci amana, ko da yake ba wanda ya yi musu fashi ko cin amana. Amma lokacinsu na fashi da na cin amana zai ƙare, su ne kuma za a yi wa fashi da cin amana.
2Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai. Muna sa zuciyarmu gare ka. Ka dinga kiyaye mu yau da gobe, ka kuma cece mu a lokatan wahala. 3Lokacin da kake yaƙi dominmu, al'ummai sukan gudu daga bakin dāga. 4Akan tsirga a bisa abubuwan da suke da su, a kwashe su ganima.
5Ubangiji da girma yake! Yana mulki a kan kome. Zai cika Urushalima da adalci da mutunci, 6zai kuma sa aminci cikin al'ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama'arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.
7Mutane masu jaruntaka suna kira don a taimake su! Jakadu waɗanda suke ƙoƙarin kawo salama suna kuka mai zafi. 8Manyan karauku suna da hatsari har ba mai iya binsu. Aka keta yarjejeniya, aka ta da sharuɗa. Ba a kuma ganin girman kowa. 9Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.
10Ubangiji ya ce wa al'ummai, “Yanzu zan tashi! Zan nuna irin ikon da nake da shi. 11Kuka yi shirye-shiryen banza, kowane abu da kuke yi kuma ba shi da amfani. Kuna hallakar da kanku! 12Za ku marmashe kamar duwatsun da aka ƙona don a yi farar ƙasa, kamar ƙayayuwan da aka ƙone suka zama toka. 13Bari kowa da yake kusa da na nesa ya ji abin da na yi, ya kuma san ikona.”
14Jama'ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?” 15Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa. 16Sa'an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.
17Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa. 18Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare. 19Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba! 20Ku duba Sihiyona, birni inda muke idodinmu. Ku duba Urushalima! Za ta zama wurin zama mai lafiya! Za ta zama kamar alfarwar da ba ta taɓa gusawa ba, wadda ba a taɓa tumɓuke turakunta ba, igiyoyinta kuma ba su taɓa tsinkewa ba. 21Ubangiji zai nuna mana ɗaukakarsa. Za mu zauna a gefen koguna da rafuffuka masu faɗi, amma ba kuwa jirgin ruwan abokan gāba da zai bi ta cikinsu.
1Ku zo, ku jama'ar dukan al'ummai! Ku tattaru ku kasa kunne. Bari dukan duniya, da kowane mai zama cikinta, ya zo nan ya kasa kunne. 2Ubangiji yana fushi da al'ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka. 3Ba za a binne gawawwakinsu ba, amma za a bar su can, su ruɓe, su yi ɗoyi, duwatsu kuma za su yi ja wur da jini. 4Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.
5Ubangiji ya shirya takobinsa a can Sama, yanzu kuwa zai buga Edom, wato mutanen can da ya zartar musu da hukuncin hallaka. 6Jininsu da kitsensu za su rufe takobinsa, kamar jini da kitsen raguna, da na awaki, da aka miƙa hadaya. Ubangiji zai yi wannan hadaya a birnin Bozara, zai sa wannan ya zama babban kisa a ƙasar Edom. 7Mutane za su fāɗi kamar bijiman jeji da 'yan bijimai, ƙasar za ta yi ja wur da jini, kitse kuma zai rufe ta. 8Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.
9Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo. 10Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta. 11Mujiyoyi da hankaki su ne za su gāji ƙasar. Ubangiji zai maishe ta marar amfani, kamar yadda take tun kafin halitta. 12Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare. 13Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu. 14Namomin jeji za su yi ta kaiwa da komowa a can suna kiran juna. Mugun naman jeji zai je can ya nemi wurin hutawa. 15Mujiyoyi za su yi sheƙarsu a can, su nasa ƙwayaye, su ƙyanƙyashe 'ya'yansu, su kuma lura da su a can. Ungulai za su tattaru a can a kai a kai.
16Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan'uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare. 17Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.
1Hamada za ta yi farin ciki. Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.
2Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna, Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon, Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon. Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, Ya ga girmansa da ikonsa.
3Ku ƙarfafa hannuwan da suka gaji, Da gwiwoyin da suke fama da rashin ƙarfi.
4Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”
5Makaho zai iya ganin gari, Kurma kuma zai iya ji.
6Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa, Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna. Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,
7Yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki, Ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai. Inda diloli suka yi zama, Ciyawar fadama da iwa za su tsiro.
8Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.
9Ba za a sami zakoki a can ba, Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba. Waɗancan da Ubangiji ya fansar Su za su zo gida ta wannan hanya.
10Za su kai Urushalima da murna, Suna raira waƙa suna sowa don murna. Za su yi farin ciki har abada, Ba damuwa da ɓacin rai har abada.
(2 Sar 18.13-37; 2 Tar 32.1-19)
1A shekara ta goma sha huɗu da Hezekiya yake sarautar Yahuza, sai Sennakerib Sarkin Assuriya ya tasar wa birane masu kagara na Yahuza, ya kame su. 2Sa'an nan ya umarci babban shugaban yaƙinsa ya tashi daga Lakish ya tafi Urushalima tare da babbar rundunar mayaƙa don su sa sarki Hezekiya ya ba da kai. Sai shugaban ya mamaye hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a daidai magudanar da take kawo ruwa daga kududdufin da yake daga can bisa. 3Mutanen Yahuza su uku suka fito don su tarye shi, shugaba mai lura da fāda, wato Eliyakim ɗan Hilkiya, da marubucin ɗakin shari'a, wato Shebna, da shugaban da yake kula da tarihin da aka rubuta, wato Yowa ɗan Asaf. 4Sai shugaban Assuriyawa ya faɗa musu, cewa babban sarki yana so ya san ko me ya sa sarki Hezekiya yake dogara ga kansa. 5Ya ce, “Kana tsammani magana da baki kawai ta isa ta yi aiki da gwanayen sojoji, da kuma masu ƙarfi? Wa kake tsammani zai taimake ka, har da za ka yi mini tawaye? 6Kana sa zuciya Masar za ta taimake ka, to, wannan ya zama kamar ka ɗauki kyauro ya zama sandan dogarawa, zai karye, ya yi wa hannunka sartse. Haka Sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara gare shi.”
7Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa'an nan ya faɗa wa jama'ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum. 8Zan yi ciniki da kai da sunan babban sarki, wato Sennakerib. Zan ba ka dawakai dubu biyu idan za ka iya samun yawan mutanen da za su hau su! 9Ba ka yi daidai da ka ƙi ko wani marar maƙami a shugabannin Assuriya ba, duk da haka kana sa rai ga Masarawa su aiko maka da karusai, da mahayan dawakai! 10Kana tsammani na tasar wa ƙasarka na kuma lalatar da ita ba tare da taimakon Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya faɗa mini in tasar wa ƙasarka in lalatar da ita.”
11Sa'an nan sai Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka ce wa shugaba na Assuriya, “Ka yi mana magana da harshen Aramiyanci, muna jinsa. Kada ka yi da Ibrananci, dukan jama'ar da take a kan garu suna saurare.”
12Ya amsa ya ce, “Kuna tsammani babban sarki ya aiko ni don in daɗa wa ku da sarki kurum dukan magana? Sam, ina magana ne da jama'ar da take a kan garu, waɗanda za su ci kāshinsu su kuma sha fitsarinsu, kamar yadda ku kanku za ku yi.”
13Sa'an nan ya tsaya ya ta da murya da harshen Ibrananci, ya ce, “Ku saurara ga abin da Sarkin Assuriya yake faɗa muku. 14Yana muku kashedi, cewa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, Hezekiya ba zai iya cetonku ba. 15Kada kuma ku bari ya rinjaye ku ku dogara ga Ubangiji, har ku sa tsammani Ubangiji zai cece ku, ya hana sojojinmu na Assuriya su cinye birninku. 16Kada ku kasa kunne ga Hezekiya. Sarkin Assuriya yana umartarku ku fito daga cikin birni ku sallama. Za a yardar muku duka ku ci 'ya'yan inabi daga gonakinku, da 'ya'yan ɓaure na itatuwan ɓaurenku, ku kuma sha ruwa daga rijiyoyinku na kanku, 17har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa. 18Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al'ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya? 19Ina suke yanzu, wato gumakan Hamat da na Arfad? Ina gumakan Sefarwayim? Ba ko ɗaya da ya ceci Samariya, ko ba haka ba? 20A yaushe ko gunki ɗaya na dukan waɗannan ƙasashe ya taɓa ceton ƙasarsa daga babban sarkinmu? To, yanzu me ya sa kuke tsammani Ubangiji zai ceci Urushalima?”
21Jama'a suka yi tsit, kamar dai yadda sarki Hezekiya ya faɗa musu, ba su amsa da kome ba. 22Sa'an nan Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka kyakkece tufafinsu don baƙin ciki, suka tafi, suka faɗa wa sarki abin da shugaban mayaƙan Assuriya ya yi ta farfaɗa.
(2 Sar 19.1-37; 2 Tar 32.20-23)
1Da sai sarki Hezekiya ya ji abin da suka faɗa, sai ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki, ya sa tsummoki a jiki, ya shiga Haikalin Ubangiji. 2Ya aiki Eliyakim mai kula da fāda, da Shebna marubucin ɗakin shari'a, da manyan firistoci zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Su kuma suna saye da tsummoki. 3Ga saƙon da ya aike su su faɗa wa Ishaya, “Yau rana ce ta wahala, muna shan hukunci da wulakanci. Mun zama daidai da mace wadda take naƙuda, amma ba ta da ƙarfin da za ta haihu. 4Sarkin Assuriya ya aiko babban shugaban mayaƙansa don ya zagi Allah mai rai. Da ma Ubangiji Allahnka ya ji waɗannan zage-zage ya kuma hukunta waɗanda suka yi su. Don haka sai ka yi addu'a ga Allah saboda mutanenmu waɗanda suka ragu.”
5Sa'ad da Ishaya ya karɓi saƙon sarki Hezekiya, 6sai ya aika masa da amsa cewa, “Ubangiji ya ce kada ka damu da irin zargin da Assuriyawa suke ta yi a kansa. 7Ubangiji zai sa Sarkin Assuriya ya ji jita-jitar da za ta sa ya koma ƙasarsa, Ubangiji kuwa zai kashe shi a can.”
8Shugaban mayaƙan Assuriya ya ji labari sarkin ya bar Lakish, yana can yana yaƙi da birnin Libna sai ya janye. 9Sai Assuriyawa suka ji, cewa mayaƙan Masarawa, waɗanda sarki Tirhaka na Habasha yake yi wa jagora, suna zuwa su far musu da yaƙi. Sa'ad da sarkin ya ji haka sai ya aika wa sarki Hezekiya da wasiƙa, 10ya ce masa, “Allahn da kake dogara gare shi ya faɗa maka, ba za ka faɗa a hannuna ba, amma kada ka yarda wannan ya ruɗe ka. 11Ka dai ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa duk ƙasar da ya yi niyyar hallakarwa. Kana tsammani za ka kuɓuta? 12Kakannina sun hallakar da biranen Gozan, da Haran, da Rezef, suka kuma kashe mutanen Eden, mazaunan Telassar, ba ko ɗaya daga cikin gumakansu da ya iya cetonsu. 13Ina sarakunan biranen Hamat da Arfad, da Sefarwayim, da Hena, da Iwwa?”
14Sarki Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga hannun manzannin, ya karanta ta. Sa'an nan ya shiga Haikali, ya ajiye wasiƙar a gaban Ubangiji, 15ya yi addu'a, 16ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama. 17Yanzu, ya Ubangiji, ka ji mu, ka kuma dube mu. Ka kasa kunne ga dukan abubuwan da Sennakerib yake ta faɗa, yana zaginka, ya Allah mai rai. 18Dukanmu mun sani, ya Ubangiji, yadda sarakunan Assuriya suka hallakar da al'ummai masu yawa, suka mai da ƙasashensu kufai, marasa amfani, 19suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu. 20Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”
21Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki. 22Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a. 23Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba'a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra'ila. 24Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji. 25Ka kuma yi fāriya da cewa ka haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa, ka kuma sha ruwansu, sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu da ƙafafunsu, har ya ƙafe.
26“Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai. 27Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.
28“Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni. 29Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”
30Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan. 31Su da suka tsira daga al'ummar Yahuza za su yi lafiya kamar dashe-dashen da saiwoyinsu suka shiga da zurfi cikin ƙasa, suka kuma ba da amfani. 32Mutanen da za su tsira su ne na cikin Urushalima da na kan Dutsen Sihiyona, gama Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyya ya sa haka ya faru.
33“Wannan shi ne abin da Ubangiji ya ce a kan Sarkin Assuriya, “‘Ba zai shiga wannan birni ba, ko kuwa ya harba ko da kibiya ɗaya a cikinsa. Sojoji masu garkuwoyi ba za su zo ko kusa da birnin ba, ba kuma za su yi mahaurai kewaye da birnin ba. 34Zai koma ta kan hanyar da ya zo, ba kuwa zai taɓa shiga wannan birni ba. Ni, Ubangiji, ni na faɗa. 35Zan kāre wannan birni in kiyaye shi, saboda girmana, domin kuma alkawarin da na yi wa bawana Dawuda.”
36Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu! 37Sa'an nan sai Sarkin Assuriya, wato Sennakerib, ya janye ya koma Nineba. 38Wata rana ya je yana sujada a gidan gunkinsa Nisrok, sai biyu daga cikin 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takubansu, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Wani daga cikin sauran 'ya'yansa, wato Esar-haddon, ya gāje shi ya zama sarki.
(2 Sar 20.1-11; 2 Tar 32.24-26)
1A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”
2Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu'a, ya ce, 3“Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.
4Sa'an nan Ubangiji ya umarci Ishaya, 5cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba. 6Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”
7Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa. 8Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma'aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.
9Bayan da Hezekiya ya warke daga rashin lafiyarsa, sai ya rubuta wannan waƙar yabo.
10Na zaci a gaɓar ƙarfina Zan tafi lahira, Ba zan ƙara rayuwa ba.
11Na zaci ba zan ƙara ganin Ubangiji ba A wannan duniya ta masu rai, Ko kuwa in ga wani mutum mai rai.
12An datse raina, ya ƙare, Kamar alfarwar da aka kwance, Kamar saƙar da aka yanke, Na zaci Allah zai kashe ni.
13Dare farai na yi ta kuka saboda azaba, Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana. Na zaci Allah zai kashe ni.
14Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi, Na kuwa yi kuka kamar kurciya, Idanuna sun gaji saboda duban sama. Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.
15Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan. Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.
16Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai. Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.
17Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama. Ka ceci raina daga dukan hatsari, Ka gafarta dukan zunubaina.
18Ba wanda yake yabonka a lahira, Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.
19Masu rai ne suke yabonka, Kamar yadda nake yabonka yanzu. Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.
20Ya Ubangiji, ka riga ka warkar da ni! Za mu kaɗa garayu mu kuma raira waƙar yabo, Za mu raira yabo cikin Haikalinka muddin ranmu.
21Haka ya faru bayan da Ishaya ya faɗa wa sarki ya sa curin da aka yi da 'ya'yan ɓaure a kan marurun, ya kuwa warke. 22Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”
(2 Sar 20.12-19; 2 Tar 32.27-31)
1A wannan lokaci sai Sarkin Babila, wato Merodak Baladan, ɗan Baladan, ya ji labarin sarki Hezekiya ya yi rashin lafiya, saboda haka sai ya aika masa da wasiƙa da kuma kyautai. 2Hezekiya kuwa ya marabci manzannin, ya kuma nunnuna musu dukiyarsa, wato azurfa da zinariya, da kayan yaji da na ƙanshi, da dukan kayayyakinsa na yaƙi. Ba abin da bai nuna musu ba a ɗakunan ajiya, da ko'ina a mulkinsa. 3Sa'an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”
4Ishaya ya ce, “Me suka gani a fāda?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Suka ga kome da kome. Ba abin da ban nuna musu ba a ɗakunan ajiya.”
5Sa'an nan Ishaya ya faɗa wa sarki ya ce, “Ubangiji Mai Runduna ya faɗi haka, 6“‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe dukan abin da yake a fādarka, da dukan abin da kakanninka suka tara har ya zuwa yau, zuwa ƙasar Babila. Ba abin da za a rage. 7Waɗansu daga cikin zuriyarka ta kanka, za a tafi da su a maishe su babani domin su yi hidima a fādar Sarkin Babila.”
8Da sarki Hezekiya ya gane, wannan zai faru ne a bayansa, wato a zamaninsa ba kome sai lafiya, sai ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”
1Ubangiji ya ce, “Ka ta'azantar da jama'ata. Ka ta'azantar da su!
2Ka ƙarfafa jama'ar Urushalima. Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa, Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu. Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”
3Murya tana kira tana cewa, “Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji! Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!
4Za a cike kowane kwari, Za a baje kowane dutse. Tuddai za su zama fili, Ƙasa mai kururrumai za ta zama sumul.
5Sa'an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji, Dukan 'yan adam kuwa za su gan ta. Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”
6Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!” Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?” “Ka yi shela, cewa dukan 'yan adam kamar ciyawa suke, Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.
7Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu. Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!
8Hakika ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi, Amma maganar Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba!”
9Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima, Ki faɗi albishir! Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona, Ki faɗi albishir! Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro. Ki faɗa wa garuruwan Yahuza, Cewa Allahnsu yana zuwa!
10Ubangiji yana zuwa ya yi mulki da iko, Zai taho tare da mutanen da ya cece su. Ga shi, zai kawo lada Zai kuma yi wa mutane sakamako.
11Zai lura da garkensa kama yadda makiyayi yake yi, Zai tattara 'yan raguna wuri ɗaya, Zai ɗauke su ya rungume su, A hankali zai bi da iyayensu.
12Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu, Ko sararin sama da tafin hannunsa? Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali, Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni>
13Akwai wanda zai iya umartar Ubangiji ya yi abu? Wa zai iya koya wa Ubangiji, ko ya yi masa shawara>
14Da wa Allah yake yin shawara Domin ya sani, ya kuma fahimta, Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa>
15Al'ummai ba kome ba ne a wurin Ubangiji, Ba su fi ɗigon ruwa ba, Manisantan tsibirai ba su fi ƙura nauyi ba.
16Dukan dabbobin da suke a jejin Lebanon Ba su isa hadaya guda ga Allahnmu ba, Itatuwan jejin kuma ba su isa a hura wuta da su ba.
17Al'ummai ba kome ba ne ko kaɗan a gare shi.
18Da wa za a iya kwatanta Allah? Wa zai iya faɗar yadda yake>
19Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi, Maƙera kuma suka dalaye da zinariya, Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.
20Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba, Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yana neman gwanin sassaƙa Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.
21Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ashe, ba a faɗa maka ba tuntuni? Ashe, ba ka ji yadda aka fara duniya ba>
22Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta, Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama, Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar 'yan ƙananan ƙwari. Ya miƙa sararin sama kamar labule, Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.
23Yakan kawo masu mulki masu iko ƙwarai, Ya kuwa mai da su ba kome ba ne,
24Suna kama da ƙaramin dashe Wanda bai daɗe ba, Bai yi ko saiwar kirki ba. Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska, Sai su bushe, iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.
25Da wane ne za a kwatanta Allah Mai Tsarki? Ko akwai wani mai kama da shi>
26Ka dubi sararin sama a bisa! Wane ne ya halicci taurarin da kake gani? Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji, Ya sani ko su guda nawa ne, Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa! Ikonsa da girma yake, Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!
27Isra'ila, me ya sa kake gunaguni, Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba, Ko ya kula ya daidaita abubuwa dominka>
28Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya. Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.
29Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.
30Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala, Samari sukan siƙe su fāɗi,
31Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.
1Allah ya ce, “Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe! Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari'a. Za ku sami zarafi ku yi magana. Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.
2“Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas, Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi? Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai? Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura! Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!
3Yana biye da kora, yana kuma tafiya lafiya, Da sauri ƙwarai, da ƙyar yake taɓa ƙasa!
4Wane ne ya sa wannan ya faru? Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi? Ni Ubangiji, ina can tun da farko, Ni kuma Ubangiji Allah, Zan kasance a can har ƙarshe.
5“Mutanen manisantan ƙasashe suka ga abin da na yi, Suka tsorata, suka yi rawar jiki saboda tsoro. Saboda haka duka suka tattaru wuri guda.
6Masu aikin hannu suka taimaka suka ƙarfafa juna.
7Masassaƙi yakan ce wa maƙerin zinariya, “‘A gaishe ka!” Wanda yake gyara gumaka ya yi sumul Yana ƙarfafa wanda yake harhaɗa su. Wani yakan ce, “‘Haɗin ya yi kyau,” Sukan kuma manne gumakan da ƙusoshi.
8“Amma kai, Isra'ila bawana, Kai ne jama'ar da na zaɓa, Zuriyar Ibrahim, abokina,
9Na kawo ka daga maƙurar duniya, Na kira ka daga kusurwoyi mafi nisa. Na ce maka, “‘Kai ne bawana.” Ban ƙi ka ba, amma maimakon haka na zaɓe ka.
10Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.
11“Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama'ata, Za a ƙasƙantar da su su ji kunya. Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.
12Za ku neme su, amma ba za ku same su ba, Wato waɗanda suke gāba da ku. Waɗanda suka kama yaƙi da ku, Za su shuɗe daga duniya.
13Ni ne Ubangiji Allahnku, Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku, “‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.”
14Ubangiji ya ce, “Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma, Kada ku ji tsoro, zan taimake ku. Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.
15Zan sa ku zama kamar abin sussuka, Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini. Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su, Za a marmashe tuddai kamar ƙura.
16Za ku watsa su sama cikin iska, Iska za ta hure su, ta tafi da su, Hadiri kuma zai warwatsar da su. Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku, Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.
17“Sa'ad da jama'ata ta bukaci ruwa, Sa'ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi, Sa'an nan ni Ubangiji, zan amsa addu'arsu, Ni Allah na Isra'ila, ba zan taɓa yashe su ba.
18Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai, Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka. Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa, Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.
19Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada, Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun. Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi, Jejin itatuwan fir.
20Mutane za su ga wannan, su sani, Ni Ubangiji, na yi shi. Za su fahimta, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya sa abin ya faru.”
21Ubangiji, Sarki na Isra'ila, ya faɗi wannan, “Ku allolin al'ummai ku gabatar da matsalarku. Ku kawo dukan gardandamin da kuke da su!
22Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba, Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru, Ku faɗa mana yadda zai zama duka, Domin lokacin da ya faru mu mu sani.
23Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa. Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne! Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i, Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!
24Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne, Waɗanda suke yi muku sujada kuwa, Abin ƙyama ne su!
25“Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas, Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa. Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka, Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.
26Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri, Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru, Har da za mu ce kun yi daidai? Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan, Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!
27Ni Ubangiji, ni ne na farko da na faɗa wa Sihiyona albishir, Na aiki manzo zuwa Urushalima don ya ce, “‘Jama'arki suna zuwa! Suna zuwa gida.”
28Sa'ad da na duba alloli, Ba wanda yake da abin da zai faɗa, Ko ɗaya, ba wanda ya iya amsa tambayar da na yi.
29Dukan waɗannan alloli ba su da amfani, Ba su iya kome ba, ko kaɗan, Gumakansu ba su da ƙarfi, ba su kuma da iko!”
1Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.
2Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba, Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.
3Zai lallaɓi marasa ƙarfi, Ya nuna alheri ga tafkakku. Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.
4Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba, Zai kuma kafa gaskiya a duniya, Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”
5Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,
6“Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya. Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari, Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai.
7Za ka buɗe idanun makafi, Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.
8“Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka. Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata, Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.
9Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa, Tun kafin ma su soma faruwa.”
10Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji, Ku raira yabo ku dukan duniya! Ku yabe shi, ku da kuke tafiya ta teku, Ku yabe shi, ku dukan halitta a teku! Ku raira, ku manisantan ƙasashe, da dukan waɗanda suke a can!
11Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah, Bari mutanen Kedar su yabe shi! Bari su da suke zaune a birnin Sela Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!
12Bari waɗanda suke a manisantan ƙasashe su yi yabo, Su kuma girmama Ubangiji!
13Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi, Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi. Ya yi gunzar yaƙi da tsawar yaƙi, Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa.
14Allah ya ce, “Na daɗe na yi shiru, Ban amsa wa jama'ata ba. Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu, Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.
15Zan lalatar da tuddai da duwatsu, In kuma busar da ciyawa da itatuwa, Zan mai da kwaruruka inda akwai rafi hamada, In kuma busar da kududdufan ruwa.
16“Zan yi wa mutanena makafi jagora A hanyar da ba su taɓa bi ba. Zan sa duhunsu ya zama haske, In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu. Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.
17Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka, Masu kiran siffofi allolinsu, Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”
18Ubangiji ya ce, “Ku kasa kunne, ya ku kurame! Ku duba da kyau sosai, ku makafi!
19Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta, Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko>
20Isra'ila, kun ga abu da yawa, Amma bai zama da ma'ana a gare ku ba ko kaɗan. Kuna da kunnuwan da za ku ji, Amma a ainihi me kuka ji?”
21Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,
22Amma yanzu an washe mutanensa, Aka kukkulle su a kurkuku, Aka ɓoye su a rami. Aka yi musu fashi, aka washe su, Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.
23Ko akwai wanda zai kasa kunne ga wannan? Ko za ku kasa kunne ku yi lura daga yanzu>
24Wane ne ya ba da Isra'ila ga masu waso? Ubangiji ne kansa, shi wanda muka yi wa zunubi! Ba mu iya zama kamar yadda yake so mu yi ba, Ko mu yi biyayya da koyarwarsa da ya ba mu.
25Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa, Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo. Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra'ila kamar wuta, Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba, Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.
1Ya Isra'ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce, “Kada ku ji tsoro, na fanshe ku. Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.
2Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi, Zan kasance tare da ku, Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba. Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba, Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.
3Gama ni ne Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, wanda ya cece ku. Zan ba da Masar, da Habasha, da Seba Ga Sairus domin fansarku.
4Zan ba da dukan al'ummai don in ceci ranku, Gama kuna da daraja a gare ni, Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.
5Kada ku ji tsoro, ina tare da ku! “Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa, Zan kawo jama'arku zuwa gida.
6Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi, Arewa kuma kada su riƙe su a can. Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe, Daga kowane sashi na duniya.
7Su mutanena ne, na kaina, Na kuwa halicce su don su girmama ni.”
8Allah ya ce, “Kirawo mutanena a ɗakin shari'a. Suna da idanu, amma makafi ne, Suna da kunnuwa, amma kurame ne!
9Kirawo sauran al'umma, su zo ga shari'a. A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba? A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu? Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsu Don su tabbatar daidai suke, Su shaida gaskiyar maganganunsu.
10“Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna, Na zaɓe ku al'umma, baiwata, Domin ku san ni, ku gaskata ni, Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah. In banda ni ba wani Allah, Ba a taɓa yin wani ba, Ba kuwa za a yi ba.
11“Ni kaɗai ne Ubangiji, Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.
12Na faɗi abin da zai faru Sa'an nan na zo domin taimakonku. Ba wani gunkin da ya taɓa yin haka, Ku ne shaiduna.
13Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur, Ba wanda zai iya tserewa daga ikona, Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”
14Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce, “Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila, Zan rushe ƙofofin birni, Sowar mutanen birnin za ta zama kuka.
15Ni ne Ubangiji, Allahnku Mai Tsarki na Isra'ila, Ni na halicce ku, ni ne kuma sarkinku.”
16Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku, Da turba kuma a cikin ruwa.
17Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka, Sojojin karusai da na dawakai. Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba, An hure su kamar 'yar wutar fitila!
18Amma Ubangiji ya ce, “Kada ku maƙale wa abubuwan da suka wuce, Ko ku riƙa tunanin abin da ya faru tuntuni.
19Ku duba abin da nake shirin yi. Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu! Zan yi hanya a cikin jeji, In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.
20Har da namomin jeji za su girmama ni, Diloli da jiminai za su yi yabona Sa'ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada, Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.
21Su ne mutanen da na yi domin kaina, Za su raira yabbaina!”
22Ubangiji ya ce, “Amma ba ni kuka yi wa sujada ba, Kun gaji da ni, ya Isra'ila.
23Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba, Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba. Ban nawaita muku da neman hadayu ba, Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.
24Ba ku sayi turare domina ba, Ko ku gamshe ni da kitsen dabbobinku. Maimakon haka, sai kuka nawaita mini da zunubanku, Kuka gajiyar da ni da abubuwan da kuke aikatawa da ba daidai ba.
25Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku, Na kuwa yi haka saboda yadda nake. Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.
26“Bari mu tafi ɗakin shari'a, ku kawo ƙararrakinku. Ku gabatar da matsalarku don a tabbatar kuna da gaskiya!
27Kakanninku na farko sun yi zunubi, Manyanku sun yi mini laifi.
28Zan musunci masu mulkin tsattsarkan masujadai, Saboda haka zan jawo wa Isra'ila hallaka, Zan bari a la'anta mutanena su sha zagi!”
1Ubangiji ya ce, “Ka saurara yanzu, ya Isra'ila, bawana, Zaɓaɓɓun mutanena, zuriyar Yakubu,
2Ni ne Ubangiji wanda ya halicce ku, Tun farko, na taimake ku. Kada ku ji tsoro, ku bayina ne, Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda nake ƙaunarsu.
3“Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi, In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada. Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku, In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.
4Za su yi kumari kamar ciyawar da ta sami ruwa sosai, Kamar itatuwan wardi a gefen rafuffukan ruwa mai gudu.
5“Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, “‘Ni na Ubangiji ne!” Za su zo su haɗa kai da jama'ar Isra'ila. Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa, Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”
6Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.
7Ko akwai wanda zai iya yin abin da na yi, Ya kuma fito fili ya faɗi abin da zai faru Tun daga farko, har zuwa ƙarshe>
8Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
9Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya. 10Wannan aikin banza ne, mutum ya yi siffa da ƙarfe don ya yi mata sujada! 11Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, 'yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari'a, za su razana, su kuma sha kunya.
12Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.
13Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu. 14Zai yiwu ya sare itacen al'ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma. 15Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada! 16Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!” 17Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”
18Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya. 19Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”
20Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.
21Ubangiji ya ce, “Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra'ila, Ka tuna kai bawana ne. Na halicce ka domin ka zama bawana, Ba zan taɓa mantawa da kai ba.
22Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije, Da girgije kuma zan rufe laifofinka Ka komo wurina, ni ne na fanshe ka.”
23Ku yi sowa ta farin ciki ya ku sammai! Ku yi sowa ku zurfafan wurare na duniya! Ku yi sowa ta murna, ku duwatsu, da kowane itace na jeji! Ubangiji ya fanshi mutanensa, Isra'ila, Saboda haka ya nuna girmansa.
24“Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku. Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu. Ni kaɗai na shimfiɗa sammai, Ba wanda ya taimake ni sa'ad da na yi duniya.
25Na sa masu duba su zama wawaye, Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari. Na bayyana kuskuren maganar masu hikima, Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.
26Amma sa'ad da bawana ya yi annabci, Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena, Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika. Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can, Za a kuma sāke gina biranen Yahuza. Waɗannan birane za su daina zama kufai.
27Na yi umarni na sa teku ta ƙafe.
28Na ce wa Sairus, “‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina, Za ka yi abin da nake so ka yi, Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima, A kuma kafa harsashin ginin Haikali.”
1Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji! Ubangiji ya sa shi ya ci al'ummai, Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna, Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni. Ubangiji ya ce wa Sairus,
2“Ni kaina zan shirya hanya dominka, Ina baji duwatsu da tuddai. Zan kakkarye ƙyamaren tagulla, In kuma daddatse gagara badau na baƙin ƙarfe.
3Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare, Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji, Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.
4Na sa ka domin ka taimaki bawana Isra'ila, Jama'ar da ni na zaɓa. Na ba ka girma mai yawa, Ko da yake kai ba ka san ni ba.
5“Ni ne Ubangiji, ba wani Allah sai ni. Zan ba ka irin ƙarfin da kake bukata, Ko da yake kai ba ka san ni ba.
6Na yi wannan domin dukan waɗanda suke daga wannan bangon duniya zuwa wancan Su sani ni ne Ubangiji, Ba kuwa wani Allah sai ni.
7Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.
8Zan aiko da nasara daga sararin sama kamar ruwan sama. Ƙasa za ta buɗe ta karɓe ta, Za ta kuwa hudo da 'yanci da gaskiya. Ni Ubangiji, ni zan sa haka ya faru.”
9Ko tukunyar yumɓu tana iya gardama da magininta, Tukunyar da take daidai da sauran tukwane? Ko yumɓu ya iya tambayar abin da maginin yake yi? Ko tukunya tana iya gunaguni a kan magininta>
10Ko akwai wanda zai iya ce wa iyayensa, “Don me kuka haife ni kamar haka?”
11Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Shi wanda ya halicce su, ya ce, “Ba ka da iko ka yi mini tambaya game da 'ya'yana, Ko ka faɗa mini abin da ya kamata in yi!
12Ni ne wanda ya halicci duniya, Na kuma halicci mutum don ya zauna cikinta. Da ikona na shimfiɗa sammai, Ina kuwa mallakar rana, da wata, da taurari.
13Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.
14Ubangiji ya ce wa Isra'ila, “Dukiyar Masar da ta Habasha za ta zama taku, Dogayen mutanen Seba kuma za su zama bayinku, Za su bi ku suna a ɗaure da sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su tuba, su ce, “‘Allah yana tare da ku, shi kaɗai ne Allah.”
15Allah na Isra'ila, wanda ya ceci mutanensa, Shi ne yakan ɓoye kansa.
16Su waɗanda suka yi gumaka, dukansu za su sha kunya, Dukansu za su zama abin kunya.
17Amma Ubangiji ya ceci Isra'ila, Nasararsa kuwa za ta tabbata har abada, Mutanensa ba za su taɓa shan kunya ba.
18Ubangiji ne ya halicci sammai, Shi ne wanda yake Allah! Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta, Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo! Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba, Amma wurin zaman mutane. Shi ne wanda ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ba kuwa wani Allah, sai ni.
19Ba a ɓoye na yi magana ba, Ban kuwa ɓoye nufina ba. Ban ce jama'ar Isra'ila Su neme ni a kowace hanyar ruɗami ba. Ni ne Ubangiji, gaskiya kuwa nake faɗa, Ina sanar da abin da yake daidai.”
20Ubangiji ya ce, “Ku taru wuri ɗaya ku jama'ar al'ummai, Dukanku da kuka tsira daga faɗuwar mulki, Ku gabatar da kanku domin shari'a! Waɗancan da suka ɗauka gumakansu na itace, Suna kuma addu'a ga allolin da ba su iya cetonsu, Waɗannan mutane ba su san kome ba ko kaɗan!
21Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari'a, Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna. Wane ne ya faɗi abin da zai faru, Ya kuma yi annabci tuntuni? Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa? Ba wani Allah sai ni.
22“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.
23Abin da na faɗa gaskiya ne, Ba kuwa zai sāke ba. Ni, a dukkan yadda nake, na yi alkawari mai ƙarfi, Kowa da kowa zai zo ya durƙusa a gabana, Ya yi wa'adin zama mai biyayya a gare ni.
24“Za su ce ta wurina kaɗai Za a iya samun nasara da ƙarfi, Amma dukan waɗanda suka raina ni za su sha kunya.
25Ni Ubangiji, zan kuɓutar da dukan zuriyar Yakubu, Za su kuwa yi yabona.”
1“Wannan ne ƙarshen allolin Babila! Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada, Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna, Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!
2Wannan ne ƙarshen waɗannan alloli, Gumaka ba su iya ceton kansu, Aka kame su aka tafi da su.
3“Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu, Dukanku, mutanena da kuka ragu. Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.
4Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku, Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura. Ni na halice ku zan kuwa lura da ku, Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”
5Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni? Akwai wani mai kama da ni>
6Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya, Suna auna azurfa a kan ma'auni. Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki, Sa'an nan suka rusuna suka yi masa sujada!
7Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi, Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can, Ba ya iya motsawa daga inda yake. Idan wani ya yi addu'a gare shi, ba zai iya amsawa ba, Ko ya cece shi daga bala'i.
8“Ku tuna da wannan, ku masu zunubi, Ku dubi irin abin da na yi.
9Ku tuna da abin da ya faru tuntuni, Ku sani, ni kaɗai ne Allah, Ba kuwa wani mai kama da ni.
10Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama, Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru. Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba, Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.
11Ina kiran wani mutum ya zo daga gabas, Zai kawo sura kamar shaho, Zai kammala abin da na shirya. Na yi faɗi, zai kuwa cika.
12“Ku kasa kunne gare ni, ku mutane masu taurinkai, Ku da kuke tsammani nasara tana can da nisa.
13Ina kawo ranar nasara kusa, Ba ta da nisa ko kaɗan. Nasarata ba za ta yi jinkiri ba. Zan ceci Urushalima, Zan kuma kawo ɗaukaka ga Isra'ila a can.”
1Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!
2Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari! Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!
3Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma, A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa. Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”
4Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya fanshe mu, Sunansa Ubangiji Mai Runduna ne!
5Ubangiji ya ce wa Babila, “Ki zauna shiru a cikin duhu, Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al'ummai ba!
6Na yi fushi da mutanena, Na maishe su kamar su ba nawa ba ne. Na sa su a ƙarƙashin ikonki, Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba, Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.
7Kina tsammani za ki yi ta zama sarauniya kullayaumin, Ba ki ɗauki waɗannan al'amura a zuci ba, Ko ki yi tunanin yadda za su ƙare.
8“Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya. Kin ɗauka kina da girma kamar Allah, Har kina ganin ba wani kamarki. Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba, Ko ki sha hasarar 'ya'yanki.
9Amma ba da jimawa ba, a rana ɗaya Dukan waɗannan al'amura za su faru. Kome sihirin da za ki yi, Za ki rasa 'ya'yanki, ki kuwa zama gwauruwa.
10“Kin amince da kanki cikin muguntarki, Kina tsammani ba wanda yake ganinki. Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata, Kika kuwa ce da kanki, “‘Ni ce Allah, Ba mai kama da ni!”
11Duk da haka bala'i zai auko miki, Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba, Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya, Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!
12Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki, Kina amfani da su tun kina ƙarama. Watakila za su yi miki wani taimako, Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.
13Kome shawarar da kika samu ba ki da ƙarfi. Bari mashawartanki su fito su cece ki, Waɗancan mutane masu binciken taurari Waɗanda suka zana taswirar sammai, Su kuma faɗa miki Dukan abin da zai faru da ke wata wata.
14“Za su zama kamar budu, Wuta kuwa za ta ƙone su ƙurmus! Ba ma za su ko iya ceton kansu ba. Harshen wuta zai fi ƙarfinsu, Ba wutar da za su zauna, su ji ɗumi!
15Nan ne inda shawararsu za ta kai ki, Waɗannan masanan taurari da kika yi ta neman shawararsu dukan kwanakin ranki. Dukansu za su bar ki, kowa ya tafi inda ya nufa, Ba wanda zai ragu da zai cece ki.”
1Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila, Ku da kuke zuriyar Yahuza. Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji, Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila, Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.
2Amma duk da haka kuna fāriya, da cewa Ku ne mazaunan birni mai tsarki, Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila, Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.
3Ubangiji ya ce wa Isra'ila, “Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru, Sa'an nan na sa ya faru ba labari!
4Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne, Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.
5Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku, Na hurta abubuwa tun kafin su faru, Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su, Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.
6“Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu, Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo, Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.
7Yanzu ne kaɗai nake sawa su faru, Ba wani abu makamancin wannan da ya faru a baya. Da ya faru, da za ku ɗauka cewa kun san kome a kansa.
8“Na sani ba za a iya gaskata ku ba, Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa. Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan, Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.
9“Saboda mutane su yi yabon sunana Shi ya sa nake danne fushina, Ina kuma ɓoye shi, kada in hallaka ku.
10Na gwada ku da wutar wahala, Kamar yadda ake tace azurfa a tanda, Amma na tarar ba ku da amfani.
11Abin da na yi, na yi shi don kaina ne, Ba zan bari a rasa girmama sunana ba, Ko kuwa wani dabam ya sami ɗaukaka Wadda take tawa ce, ni kaɗai.”
12“Ku kasa kunne gare ni, ya Isra'ila, jama'ar da na kira! Ni ne Allah, farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici!
13Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya, Ya kuma shimfiɗa sammai. Lokacin da na kira duniya da sararin sama, Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!
14“Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne! Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba, Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila, Zai yi abin da na umarce shi.
15Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi, Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.
16“Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni, Ku ji abin da nake faɗa. Tun da farko na yi magana da ku a fili, A koyaushe nakan cika maganata.”
(Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)
17Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.
18“Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa Da suke bugowa zuwa gāɓa.
19Zuriyarku za su yi yawa kamar tsabar yashi, Zan kuma tabbatar, cewa ba za a hallaka su ba.”
20Ku fita daga Babila, ku tafi a sake! Ku yi sowar albishir da farin ciki, ku sa a sani a ko'ina, “Ubangiji ya fanshi bawansa Isra'ila!”
21Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi, Ba su sha wahalar ƙishi ba. Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu, Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.
22Ubangiji ya ce, “Ba mafaka domin masu zunubi.”
1Ku kasa kunne gare ni, ku al'ummai manisanta, Ku mutanen da kuke zaune a can nesa! Ubangiji ya zaɓe ni, tun kafin a haife ni, Ya kuwa sa ni in zama bawansa.
2Ya sa maganata ta yi kaifi kamar takobi, Ya kiyaye ni da ikonsa. Ya sa na zama kamar kibiya Mai tsini shirayayyiya domin harbi.
3Ya ce mini, “Isra'ila, kai bawana ne. Mutane za su yabe ni saboda kai.”
4Na ce, “Na yi aiki, amma a banza ne. Na mori ƙarfina, amma ban ƙulla kome ba.” Duk da haka na dogara ga Ubangiji, ya daidaita al'amura, Shi zai sāka mini abin da na yi.
5Ubangiji ya zaɓe ni tun kafin a haife ni. Ya maishe ni bawansa domin in komo da mutanensa, In komo da jama'ar Isra'ila da aka warwatsar. Ubangiji ya ba ni daraja, Shi ne tushen ƙarfina.
6Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
7Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.
8Ubangiji ya ce wa jama'arsa, “Idan lokacin da zan cece ku ya yi, zan nuna muku alheri. Zan ji kukanku in taimake ku. Zan tsare ku in kiyaye ku, Zan kuwa yi wa dukan mutane alkawari ta wurinku. Zan bar ku ku sāke zama a ƙasarku wadda take kufai a yanzu.
9Zan ce wa 'yan kurkuku, “‘Ku tafi na sake ku!” Waɗanda suke cikin duhu kuwa, in ce musu, “‘Ku fito zuwa wurin haske!” Za su zama kamar tumakin da suke kiwo a tuddai,
10Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba. Ba za su sha zafin rana da na hamada ba, Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su. Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.
11“Zan yi babbar hanya ta kan duwatsu, In kuma shirya hanya domin mutanena su bi.
12Mutanena za su zo daga can nesa, Daga Birnin Sin a kudu, Daga yamma, da arewa.”
13Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya! Bari duwatsu su ɓarke da waƙa! Ubangiji zai ta'azantar da mutanensa, Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.
14Amma mutanen Urushalima suka ce, “Ubangiji ya yashe mu! Ya manta da mu.”
15Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce, “Mace za ta iya mantawa da jaririnta, Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa? Ya yiwu mace ta manta da ɗanta, To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.
16Ya Urushalima, ba zan taɓa mantawa da ke ba, Na rubuta sunanki a gabana.
17“Su waɗanda za su sāke gina ki suna tafe yanzu, Waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su tashi.
18Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa! Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida! Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai, Za ki yi fāriya da mutanenki, Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta!
19“Aka lalatar da ƙasar, ta zama kufai, Amma yanzu za ta yi wa waɗanda suke komowa domin su zauna cikinta kaɗan. Waɗanda suka lalatar da ke kuwa, Za a kawar da su daga gare ki.
20Mutanenki da aka haifa a lokacin zaman talala, Wata rana za su ce miki, “‘Wannan ƙasa ta yi kaɗan ƙwarai, Muna bukatar ƙarin wurin zama!”
21Sa'an nan za ki ce wa kanki, “‘Wa ya haifa mini waɗannan 'ya'ya? Na rasa 'ya'yana, ba kuwa zan iya haifar waɗansu ba. Aka kore ni, aka yi mini ɗaurin talala, Wane ne ya haifi waɗannan 'ya'ya? Aka bar ni, ni kaɗai, Daga ina waɗannan 'ya'ya suka fito?”
22Ubangiji Allah ya ce wa jama'arsa, “Zan nuna alama ga al'ummai, Za su kuwa kawo 'ya'yanku gida.
23Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku, Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma, Da tawali'u za su nuna muku bangirma. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”
24Kuna iya ku ƙwace wa sojoji wason da suka yi? Kuna iya kuɓutar da 'yan kurkuku daga ɗaurin masu baƙin mulki>
25Ubangiji ya amsa ya ce, “Wannan shi ne ainihin abin da zai faru. Za a ƙwace kamammun yaƙi, Za a kuma ƙwace wason da masu baƙin mulki ya yi. Zan yi yaƙi da dukan wanda yake yaƙi da ku, Zan kuwa kuɓutar da 'ya'yanku.
26Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna, Za su yi māye, da kisankai, da fushi. Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji, Wanda ya cece ku, ya fanshe ku. Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.”
1Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.
2“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.
3Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu, In sa ya zama makoki domin matattu.”
4Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa, Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi. A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini.
5Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi.
6Na tsiraita ga masu dūkana. Ban hana su sa'ad da suke zagina ba, Suna tsittsige gemuna, Suna tofa yau a fuskata.
7Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba, Gama Ubangiji Allah yana taimakona. Na ƙarfafa kaina domin in jure da su. Na sani ba zan kunyata ba,
8Gama Allah yana kusa, Zai tabbatar da ni, marar laifi ne, Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari'a tare! Bari ya kawo ƙararrakinsa!
9Ubangiji kansa zai kāre ni, Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne? Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe, Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!
10Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.
11Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku! Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru, Za ku gamu da mummunar ƙaddara.
1Ubangiji ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku, Ku da kuka zo gare ni neman taimako. Ku yi tunanin dutse inda kuka fito, Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.
2Ku yi tunani a kan kakanku Ibrahim, Da Saratu, wadda kuke zuriyarta. Sa'ad da na kira Ibrahim ba shi da ɗa, Amma na sa masa albarka, na ba shi 'ya'ya, Na sa zuriyarsa suka yi yawa.
3“Zan ji juyayi a kan Sihiyona, Da dukan masu zama a kufanta. Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu, Kamar lambun da na dasa a Aidan. Murna da farin ciki za su kasance a can, Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.
4“Ku kasa kunne gare ni, ku mutanena, Ku saurara ga abin da nake faɗa, Na ba da koyarwata ga al'ummai, Dokokina za su kawo musu haske.
5Zan zo da sauri in cece su, Lokacina na nasara ya yi kusa. Ni kaina zan yi mulki a kan al'ummai. Manisantan ƙasashe za su jira ni in zo, Za su jira da sa zuciya, ni in cece su.
6Ku duba sammai, ku duba duniya! Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi, Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa, Dukan mutanenta kuma za su mutu. Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.
7“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.
8Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye! Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata za ta kasance har abada abadin.”
9Ya Ubangiji, ka tashi, ka taimake mu! Ka nuna ikonka, ka cece mu, Ka nuna ikonka kamar yadda ka yi a dā. Kai ne ka daddatse dodon ruwa, wato Rahab.
10Kai ne ka sa teku ta ƙafe, Ka kuma shirya hanya ta ruwa, Domin waɗanda kake cetonsu su haye.
11Su waɗanda ka fansa Za su kai Urushalima da farin ciki, Da waƙa, da sowa ta murna. Za su yi ta murna har abada, Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.
12Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba>
13Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku, Wanda ya shimfiɗa sammai, Ya kuma kafa harsashin ginin duniya? Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku, Da waɗanda suke shiri su hallaka ku? Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!
14'Yan sarƙa za su fita ba da jimawa ba Za su yi tsawon rai, Su kuma sami dukan abincin da suke bukata.
15“Ni ne Ubangiji Allahnku, Na dama teku Na sa raƙumanta suka yi ruri. Sunana Ubangiji Mai Iko Dukka!
16Na shimfiɗa sammai, Na kafa harsashin ginin duniya, Na ce wa Sihiyona, “‘Ku jama'ata ne! Na ba ku koyarwata, Na kuwa kiyaye ku da ikona.”
17Ya Urushalima, ki farka! Ki tashi da kanki, ki miƙe! Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji cikin fushinsa, ya ba ki ki sha, Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!
18Ba wanda zai yi miki jagora, Ba wani daga cikin mutanenki Da zai kama hannunki.
19Masifa riɓi biyu ta auko miki, Yaƙi ya lalatar da ƙasarki, Mutanenki suka tagayyara da yunwa.
20A kan kusurwar kowane titi Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi, Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama. Suka ji ƙarfin fushin Allah.
21Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala, Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,
22Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce, “Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina. Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.
23Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku, Su waɗanda suka sa kuka kwanta a tituna Suka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”
1Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma! Birni mai tsarki na Allah, Ki yafa wa kanki jamali! Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.
2Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima! Ki tashi daga cikin ƙura, Ki hau gadon sarautarki. Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke, Ke kamammiyar jama'ar Sihiyona!
3Ubangiji ya ce wa jama'arsa, “Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba, Amma ga shi, kuka zama bayi. Ba za a biya kuɗin fansa domin a 'yantar da ku ba, Amma, ga shi, za a 'yantar da ku.
4Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar, Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.
5Yanzu kuma, ga shi, yana faruwa a Babila, Kuka zama kamammu a can, ba gaira ba dalili. Su da suke mulkinku suna girmankai, suna fāriya, Suna ta nuna mini raini.
6Amma zuwa gaba za ku sani Ni ne Allah, wanda na yi magana da ku.”
7Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu, Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama. Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona, “Allahnki sarki ne!”
8Waɗanda suke tsaron birni suna sowa, Suna sowa tare saboda murna! Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!
9Ku ɓarke da sowar murna, Ku kufan Urushalima! Ubangiji ya ta'azantar da jama'arsa, Ya fanshi birninsa.
10Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.
11Ku fita, ku bar Babila Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji! Kada ku taɓa abin da aka hana, Ku kiyaye kanku da tsarki, Ku fita ku bar birnin.
12A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba, Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba! Ubangiji Allah ne zai bishe ku, Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.
13Ubangiji ya ce, “Bawana zai yi nasara a aikinsa, Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.
14Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi, Ya munana har ya fita kamannin mutum.
15Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa, Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki. Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”
1Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu? Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan>
2Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin Da zai sa mu kula da shi. Ba wani abin da zai sa mu so shi, Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.
3Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.
4Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce, Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa Hukunci ne Allah yake yi masa.
5Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu, Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.
6Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu.
7Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba.
8Aka kama shi, aka yanke masa shari'a, Aka tafi da shi domin a kashe shi, Ba wanda ya kula da ƙaddararsa. Aka kashe shi saboda zunubin mutanenmu.
9Aka yi jana'izarsa tare da maguye. Aka binne shi tare da masu arziki Ko da yake bai taɓa yin laifin kome, ko ƙarya ba.
10Ubangiji ya ce, “Nufina ne ya sha wahala, Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara, Saboda haka zai ga zuriyarsa, Zai yi tsawon rai, Ta wurinsa nufina zai cika.
11Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.
12Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, Matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa Ya ɗauki rabon masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu.”
1Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa. Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda murna. Yanzu za ki ƙara samun 'ya'ya fiye da na Matar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!
2Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki! Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!
3Za ki faɗaɗa kan iyakar ƙasarki a kowane gefe, Jama'arki za su karɓi ƙasarsu Wadda al'ummai suke mallaka yanzu, Biranen da aka bari ba kowa, za su cika da mutane.
4Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba, Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya, Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki, Mai kama da na gwauruwa.
5Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki, Sunansa Ubangiji Mai Runduna! Allah Mai Tsarki na Isra'ila mai fansarki ne, Shi ne mai mulkin dukan duniya!
6Kina kama da amarya Wadda mijinta ya rabu da ita, tana baƙin ciki ƙwarai. Amma Ubangiji yana kiranki zuwa gare shi, ya ce,
7“A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.
8Na juya, na rabu da ke da fushi da ɗan lokaci, Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.” Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.
9“Na yi alkawari a zamanin Nuhu, Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba. Yanzu kuwa ina miki alkawari, Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba, Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.
10Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.
11Ubangiji ya ce, “Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke. Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.
12Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta, Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu'ulu'ai.
13“Ni kaina zan koya wa mutanenki, Zan kuwa ba su wadata da salama.
14Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki. Za ki tsira daga shan zalunci da razana. Gama ba za su kusace ki ba.
15Idan wani ya far miki, Ya yi ne ba da yardata ba, Dukan wanda ya hau ki da yaƙi zai fāɗi!
16“Ni ne na halicci maƙeri Wanda ya zuga wuta ya kuwa ƙera makamai. Ni ne kuma na halicci mayaƙi Wanda yakan mori makamai domin kisa.
17Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki, Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki. Zan kāre bayina, In kuwa ba su nasara.” Ubangiji ne ya faɗa.
1Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan! Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome ba!
2Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba? Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa? Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa, Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.
3“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.
4Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai, Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.
5Yanzu kuwa za ku kira al'ummai, baƙi, Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya, Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku! Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Zan sa dukan wannan ya faru, Zan ba ku girma da daraja.”
6Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi, Yanzu da yake kusa.
7Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.
8Ubangiji ya ce, “Tunanina ba kamar irin naku ba ne, Al'amurana kuma dabam suke da naku.
9Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, Haka al'amurana da tunanina suke nesa da naku.
10“Maganata kamar dusar ƙanƙara take, Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya. Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba, Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.
11To, haka maganar da na faɗa take, Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata, Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.
12“Za ku fita daga cikin Babila da murna, Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama. Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa, Itatuwa za su yi ta sowa don murna!
13Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu, Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa. Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada, Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”
1Ga jawabin da Ubangiji ya yi, “Ku kiyaye gaskiya ku yi adalci, gama cetona yana zuwa nan da nan, za a kuwa bayyana adalcina. 2Mai albarka ne mutumin da yake aikata wannan, da ɗan adam da yake riƙe da shi kam, wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ƙazantar da ita ba, wanda kuma ya tsame hannunsa daga aikata kowace irin mugunta.”
3Kada baƙon da ya hada kansa da mutanen Ubangiji ya ce, hakika Ubangiji zai ware shi daga jama'arsa. Kada kuma baban ya ce shi busasshen itace ne. 4Ga abin da Ubangiji ya ce, wa mutanen nan, “Ku babani waɗanda kuka kiyaye Asabar ɗina, ku da kuka zaɓi abubuwan da suka gamshe ni, kuka kuwa cika alkawarina da aminci, 5zan ba ku matuni da suna a Haikalina da cikin garukana, da sun fi na 'ya'ya mata da maza. Zan ba ku tabbataccen suna wanda ba za a raba ku da shi ba.”
6Ubangiji ya ce wa baƙin da suka bi shi, don su yi masa hidima, suna ƙaunar sunansa, sun kuma zama bayinsa, dukan wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ɓata ta ba, ya kuma cika alkawarinsa da aminci, 7“Zan kai ku tsattsarkan dutsena, in sa ku yi murna a masujadata. Hadayunku na ƙonawa da sadakokinku za su zama abin karɓa a bagadena. Za a kira Haikalina wurin yin addu'a na dukan jama'a.”
8Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”
9Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji. 10Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi! 11Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba. 12Sukan ce, “Zo mu samo ruwan inabi, bari mu cika cikinmu da barasa. Gobe ma kamar yau za ta zama, har ma fiye da haka.”
1Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala'i. 2Ya shiga da salama yana hutawa a kabarinsa, shi wanda ya yi tafiya da adalci.
3Amma ku ku matso nan kusa, ku 'ya'ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa. 4Wa kuke yi wa ba'a? Ga wa kuke wage baki, kuna zaro harshe? Ashe, ku ba 'ya'yan masu laifi ba ne, zuriyar marikita, 5ku da muguwar sha'awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe 'ya'yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi? 6Rabonku yana cikin duwatsu masu sulɓi na cikin kwari. A gare su kuka kwarara hadaya ta sha, kuka kawo hadaya ta gari. Kuna tsammani zan ji daɗin waɗannan al'amura? 7A kan dogayen duwatsu masu tsayi kuka sa gadonku. A can kuka haura don ku miƙa hadaya. 8A bayan ƙofa da madogaran ƙofa kuka kafa gumakanku. Kun rabu da ni, kun kware gadonku, kuna hau kun fāɗaɗa shi, kuka ƙulla yarjejeniya tsakaninku da su. Kuna ƙaunar gadonsu, kun dubi tsiraici. 9Kun tafi wurin Molek da mai, da turare iri iri da kuka riɓaɓɓanya. Kun aika jakadunku can nesa, kun aike su su gangara, har zuwa lahira. 10Kun damu saboda nisan hanyarku, amma ba ku ce, “Ba shi da wani amfani ba.” Ƙarfinku ya sake sabunta ranku, don haka ba ku suma ba.
11Ubangiji ya ce, “Wa ya sa ku fargaba, kuke jin tsoronsa, har kuka yi ƙarya? Ba ku tuna da ni, ko ku kula da ni ba? Ashe, ban yi haƙuri tun da daɗewan nan ba, duk da haka kuwa ba ku ji tsorona ba? 12Zan ba da labarin adalcinku da ayyukanku, amma ba za su taimake ku ba. 13Sa'ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.”
14Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama'ata!”
15Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba. 16Ba zan yi ta gāba da ku, ko in yi ta fushi da ku har abada ba. Gama ruhu zai yi suma a gabana, da numfashin su waɗanda na halitta. 17Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.
18“Na ga al'amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta'azantar da su tare da masu makoki. 19Salama, salama,” in ji Ubangiji, “Ga wanda yake nesa da wanda yake kusa. Zan warkar da su. 20Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, gama ba ta iya natsuwa. Ruwanta kuma yana tumbatsa, ya gurɓace, ya ƙazantu.” 21Allah ya ce, “Ba salama ga mugaye.”
1Ubangiji ya ce, “Ku yi kuka da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa! Ku ta da muryoyinku kamar busar ƙaho. Ku shaida wa jama'ata laifinsu, ku shaida wa zuriyar Yakubu zunubansu. 2Duk da haka suna ta nemana kowace rana, suna murna su san al'amurana, sai ka ce su al'umma ce wadda take aikata adalci, wadda kuma ba ta rabu da dokokin Allahnta ba. Suna roƙona in yi musu shari'ar adalci, suna murna su zo kusa da Allah.”
3Mutane sukan ce, “Me ya sa muka yi azumi, Ubangiji bai gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, Ubangiji kuwa bai kula ba?” Ubangiji ya ce musu, “Duba, a ranar da kuke azumi, nishaɗin kanku kuke nema, kuna zaluntar dukan ma'aikatanku. 4Duba, kuna azumi don ku yi jayayya ne, ku yi ta faɗa, ku yi ta naushin juna. Irin wannan azumi naku a wannan rana, ba zai sa a ji muryarku a can Sama ba. 5Irin azumin da nake so ke nan ne? Wato ranar da mutum zai ƙasƙantar da kansa kawai. Wato ku sunkuyar da kanku ne kamar jema, ku kuma shimfiɗa tsumma, ku barbaɗa toka a inda kuke zama. Kun iya ce da wannan azumi, karɓaɓɓiyar rana ga Ubangiji>
6“To, ba irin wannan azumi ne na zaɓa ba? Wato ku kwance sarƙoƙin mugunta, ku kwance masu karkiya, ku 'yantar da waɗanda ake zalunta, ku kakkarye kowace karkiya. 7Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.
8“Sa'an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, za ku warke nan da nan. Adalcinku zai yi muku jagora, zatina zai rufa muku baya. 9Sa'an nan za ku yi kira, ni kuwa zan amsa, za ku yi kuka, ni kuwa zan ce muku, “‘Ga ni.” “Idan kuka kawar da karkiya daga cikinku, kuka daina nuna wa juna yatsa, da faɗar mugayen maganganu, 10idan kuka ƙosar da mayunwata, kuka biya bukatar waɗanda suke shan tsanani, sa'an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu, duhunku kuma zai zama kamar hasken tsakar rana. 11Zan bi da ku kullayaumin, zan biya bukatarku da abubuwa masu kyau, in sa ƙasusuwanku su yi ƙarfi, ku zama kamar lambun da ake masa banruwa, za ku zama kamar maɓuɓɓugar ruwa da ba ta ƙonewa. 12Za ku sāke gina tsofaffin kufanku na dā can, za ku sāke kafa tushen zuriya da yawa. Za a kira ku, “‘Masu gyaran abin da ya lalace, masu sāke gyaran gidaje.”
13Ubangiji ya ce, “Idan kun juyo kuna kiyaye ranar Asabar, kuka daina annashuwarku a tsattsarkar ranata, kuka kuma kira Asabar ranar murna, tsattsarkar rana ta Ubangiji, mai daraja, idan kun girmama ta, har kuka daina bin son zuciyarku, ba ku kuma bar shagulgula su ɗauke hankalinku ba, ko ku hurta maganganun banza, 14sa'an nan ne za ku yi murna cikin Ubangiji, zan sa ku a kan maɗaukakan wurare na duniya. Zan kuma ciyar da ku da gādon mahaifinku Yakubu, ni Ubangiji na faɗa.”
1Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba. 2Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku. 3Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.
4Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta. 5Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa. 6Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya. 7Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku. 8Hanyar salama ba ku san ta ba. Ba adalci a hanyoyinku, kukan karkatar da hanyoyinku, ba wanda zai yi tafiya lafiya a cikinku.
9Mutane suna cewa, “Don haka ne, yin gaskiya ya yi nisa da mu, adalci kuwa bai iske mu ba. Muna ta neman haske, sai ga duhu, muna neman haske, sai muka yi tafiya cikin duhu. 10Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke. 11Dukanmu muna gurnani kamar beyar, muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci, amma ina. Muna ta neman ceto, amma ya yi nisa da mu.
12“Gama laifofinmu sun yi yawa a gabanka, zunubanmu kuwa suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu suna tare da mu, muna kuwa sane da laifofinmu, 13wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su. 14Aikata gaskiya ya kawu, adalci ya tsaya daga can nesa, gama gaskiya ta fāɗi a dandali, sahihanci ba zai shiga ba. 15Gaskiya ba ta, wanda ba ya aikata mugunta ya zama ganima.” Ubangiji ya gani, bai kuwa ji daɗi ba, da yake gaskiya ba ta. 16Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa'an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa. 17Ya rufe ƙirjinsa da sulken adalci, da kwalkwalin ceto a kansa. Ya sa rigar ɗaukar fansa, ya yafa alkyabbar ikonsa. 18Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa. 19Saboda haka waɗanda suke yamma za su ji tsoron sunan Ubangiji, waɗanda suke wajen gabas kuma za su ji tsoron ɗaukakarsa, gama zai zo kamar rafi mai tsananin gudu, wanda iskar Ubangiji take korawa.
20Zai zo Sihiyona ya zama mai fansa ga waɗanda suke na Yakubu, su da suka juya suka bar mugunta. 21Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”
1Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana, Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!
2Duhu zai rufe sauran al'umma, Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki, Daukakarsa za ta kasance tare da ke!
3Za a jawo al'ummai zuwa ga haskenki, Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.
4Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa, Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida! 'Ya'yanki maza za su taho daga nesa, Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.
5Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki, Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi. Za a kawo miki dukiyar al'ummai, Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.
6Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa. Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi. Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!
7Dukan tumaki na Kedar da Nebayot, Za a kawo miki su hadaya, A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi. Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.
8Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai, Kamar kurciyoyi suna komowa gida.
9Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe, Suna kawo mutanen Allah gida. Suna tafe da azurfa da zinariya, Domin su girmama sunan Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa.
10Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Baƙi ne za su sāke gina garukanki, Sarakunansu kuma za su bauta miki. Na hukunta ki da fushina, Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.
11Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana, Domin sarakunan al'ummai su kawo miki dukiyarsu.
12Amma al'umman da ba su bauta miki ba, Za a hallakar da su.
13“Itatuwan fir da irinsu Mafi kyau daga jejin Lebanon, Za a kawo su domin a sāke gina ki, ke Urushalima, Domin a ƙawata Haikalina, A darajanta birnina.
14'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo, Su rusuna, su nuna bangirma. Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki. Za su ce da ke, “‘Birnin Ubangiji,” “‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.”
15“Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba, Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki. Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma, Wurin yin farin ciki har abada abadin.
16Al'ummai da sarakuna za su lura da ke Kamar yadda uwa take lura da ɗanta. Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki, Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila ya fanshe ki.
17“Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla, Azurfa maimakon baƙin ƙarfe, Tagulla kuma maimakon itace. Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse. Masu mulkinki ba za ƙara zaluntarki ba, Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.
18Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba, Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba. Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu, Za ki yi yabona domin na cece ki.
19“Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba, Ko wata ya zama haskenki da dare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.
20Kwanakin baƙin cikinki za su ƙare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Mai daɗewa fiye da na rana da na wata.
21Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai, Za su kuwa mallaki ƙasar har abada. Ni na dasa su, ni na yi su Domin su bayyana girmana ga duka.
22Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci, Za su zama babbar al'umma, Kamar al'umma mai iko. Zan sa wannan ya faru nan da nan Sa'ad da lokacin da ya dace ya yi. Ni ne Ubangiji!”
1Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.
2Ya aike ni in yi shela, Cewa lokaci ya yi Da Ubangiji zai ceci mutanensa, Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu. Ya aike ni domin in ta'azantar da masu makoki,
3Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.
4Za su sāke gina biranen da suke a rurrushe tun da daɗewa.
5Ya Urushalima, baƙi za su bauta miki, Za su lura da garkunanki, Za su nome gonakinki, su gyara gonakinki na inabi.
6Amma za a sani, ku firistoci ne na Ubangiji, Za ku mori dukiyar al'ummai, Za ku yi fāriya da cewa, taku ce.
7Kunyarku da shan wulakancinku za su ƙare. Za ku zauna a ƙasarku, Za a riɓanya dukiyarku, Za ku yi ta farin ciki har abada.
8Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunar aikin gaskiya, Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi. Da aminci zan ba mutanena lada, In yi madawwamin alkawari, da su.
9Za su yi suna a cikin al'ummai, Dukan wanda ya gan su zai sani, Su ne mutanen da na sa wa albarka.”
10Urushalima tana murna saboda abin da Ubangiji ya yi. Tana kama da amaryar da ta sha ado a ranar aurenta. Allah ya suturce ta da ceto da nasara.
11Ba shakka, Ubangiji zai ceci jama'arsa, Kamar yadda iri yakan tsiro ya yi girma. Dukan al'ummai kuwa za su yi yabonsa.
1Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima, Ba zan yi shiru ba, Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske, Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.
2Ya Urushalima, al'ummai za su ganki mai gaskiya! Dukan sarakunansu za su ga darajarki. Za a kira ki da sabon suna, Sunan da Ubangiji ya bayar da kansa.
3Za ki zama kamar kyakkyawan rawani ga Ubangiji, Wato kambin sarauta mai daraja gare shi.
4Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba, Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.” Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.” Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,” Domin Ubangiji ya ji daɗinki, Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.
5Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa, Za ku yi murna tare, Kamar murnar amarya da ango.
6Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa, Ba kuwa za su bari ya manta ba!
7Ba za su bari ya huta ba, sai ya ceci Urushalima tukuna, Ya sa ta zama birnin da dukan duniya za ta yaba wa.
8Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi, Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi. “Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba, Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.
9Amma ku da kuka shuka hatsin kuka kuma girbe shi, Za ku ci abinci, ku yi yabon Ubangiji! Ku da kuka lura da itatuwan inabi kuka tara su, Za ku sha ruwan inabi a filayen Haikalina.”
10Ku mutanen Urushalima, ku fita daga cikin birni, Ku gyara hanyoyi domin jama'arku da suke komowa! Ku shirya babbar hanya, Ku kawar da duwatsu daga hanyar! Ku sa alama domin al'ummai su sani,
11Ubangiji yana sanarwa ga dukan duniya, Cewa, “Ku ce wa jama'ar Urushalima, Ubangiji Mai Cetonku yana zuwa, Yana kawo mutanen da ya cece su.”
12Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama'ar Allah,” “Jama'ar da Ubangiji ya Fansa!” Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,” “Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”
1Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa? Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.
2Me ya sa tufafinsa suke da ja haka, kamar na mutumin da ya tattake 'ya'yan inabi domin ya sami ruwan inabi>
3Ubangiji ya amsa ya ce, “Na tattake al'ummai kamar 'ya'yan inabi, ba kuwa wanda ya taimake ni. Na tattake su cikin fushina, jininsu kuwa ya fantsamar wa dukan tufafina. 4Na ga lokacin da zan fanshi mutanena ya yi, lokaci ne da zan hukunta wa abokan gābansu. 5Na yi mamaki sa'ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara. 6Da fushina na tattake dukan sauran al'umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”
7Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa, Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana. Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa, Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.
8Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su 9daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā, 10amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.
11Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama'arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman? 12Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al'amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama'arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”
13Sa'ad da Ubangiji ya bi da su ta ruwa mai zurfi, suka taka kamar ingarmun dawakai, ba su ko yi tuntuɓe ba. 14Kamar yadda ake bi da shanu cikin kwari mai dausayi, haka Ubangiji ya ba mutanensa hutawa. Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.
15Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu. 16Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakonmu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe. 17Don me ka bari muka ɓata daga al'amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.
18Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka. 19Mun zama kamar ba ka taɓa zama mai mulkinmu ba, kamar mu kuma ba mu taɓa zama mutanenka ba.
1Don me ba za ka kware sararin sama, ka sauko ba? Duwatsu za su gan ka, su girgiza saboda tsoro! 2Za su karkaɗu kamar ruwan da yake tafasa a wuta. Ka zo ka bayyana ikonka a kan abokan gābanka, ka sa al'ummai su yi rawar jiki a gabanka. 3Ka taɓa zuwa ka yi abubuwan banrazana waɗanda ba mu sa tsammani ba, duwatsu suka ganka suka kaɗu domin tsoro. 4Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi. 5Ka amince da waɗanda suke murna su aikata abin yake daidai, su waɗanda suka tuna da yadda kake so su yi zamansu. Ka yi fushi da mu, amma muka ci gaba da yin zunubi, har da fushin da ka yi ƙwarai, muka ci gaba da aikata abin da ba daidai ba, tun daga zamanan dā. 6Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su. 7Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu'a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu.
8Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu, 9saboda haka kada ka yi fushi da mu ainun, ko ka riƙe da zunubanmu har abada, mu dai mutanenka ne, ka yi mana jinƙai. 10Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima. 11Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su. 12Ya Ubangiji, dukan wannan bai sa ka yi wani abu ba? Ba za ka yi kome ba, kana kuwa sa mu yi ta shan wuya, har fiye da yadda muke iya daurewa>
1Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu'o'in mutanena, amma ba su yi addu'a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al'ummar ba ta yi addu'a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, “‘Ga ni nan, zan taimake ku.” 2Kullum ina a shirye domin in marabci waɗannan mutane, waɗanda saboda taurinkansu suka yi ta aikata abin da ba daidai ba, suka bi hanyoyin kansu. 3Suka yi ta ƙara sa ni fushi ta wurin rashin kunyarsu. Suka miƙa hadayu irin na arna a ɗakunan tsafi da suke a lambu, suka kuma ƙona turare a kan bagadan arna. 4Da dare sukan tafi cikin kogwanni da kaburbura, suna neman shawarar kurwar matattu. Waɗannan mutane sukan ci naman alade, su kuma sha romon naman da aka miƙa hadaya irin ta arna. 5Sa'an nan su riƙa ce wa sauran mutane, “‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.” Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.
6“Na riga na ƙudura hukuncinsu, shari'ar da aka yanke kuwa an rubuta ta. Ba zan ƙyale abin da suka aikata ba, amma zan sāka musu 7saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”
8Ubangiji ya ce, “Ba wanda ya lalatar da 'ya'yan inabi, maimakon haka sai suka yi ruwan inabi da su. Ni kuwa ba zan hallakar da dukan mutanena ba, zan ceci waɗanda suke bauta mini. 9Zan sa wa Isra'ilawa waɗanda suke na kabilar Yahuza albarka, zuriyarsu kuma za su mallaki ƙasata da duwatsuna. Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda suke bauta mini za su zauna a can. 10Za su yi mini sujada, za su kai tumakinsu da shanunsu wurin kiwo a kwarin Sharon a wajen yamma, da kuma a kwarin Akor a wajen gabas.
11“Amma ba haka zai zama ba, ga ku da kuka rabu da ni, ku waɗanda kuka yi watsi da Sihiyona, tsattsarkan dutsena, kuka yi sujada ga Gad da Meni, wato allolin sa'a da na ƙaddara. 12Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa'ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa'ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta. 13Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya. 14Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci. 15Zaɓaɓɓun mutane ne za su mori sunayenku wajen la'antarwa. Ni, Ubangiji, zan kashe ku. Amma zan ba da sabon suna ga waɗanda suke yi mini biyayya. 16Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”
17Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum. 18Ku yi murna da farin ciki a kan abin da na halitta. Sabuwar Urushalima da nake halittawa za ta cika da murna, jama'arta kuma za su yi farin ciki. 19Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama'arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako. 20Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.
1Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daganan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna? 2Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali'u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.
3“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada. 4Saboda haka zan aukar musu da masifa, ainihin abin da suke jin tsoro, gama ba wanda ya amsa sa'ad da na yi kira, ko ya kasa kunne sa'ad da na yi magana. Suka zaɓa su yi mini rashin biyayya, su kuma aikata mugunta.”
5Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga 'yan'uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba'a suna cewa, “‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.” Amma su za su sha kunya! 6Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!
7“Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba. 8Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al'umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al'umma. 9Kada ku zaci zan kawo jama'ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.
10Ku yi murna tare da Urushalima Ku yi farin ciki tare da ita, Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan! Ku yi murna tare da ita yanzu, Dukanku da kuka yi makoki dominta!
11Za ku ji daɗin wadatarta, Kamar yaro a ƙirjin mamarsa.
12Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al'ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna. 13Zan ta'azantar da ku a Urushalima, kamar yadda uwa take ta'azantar da ɗanta. 14Sa'ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”
15Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su. 16Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.
17Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama. 18Na san tunaninsu da ayyukansu. Ina zuwa domin in tattara jama'ar dukan al'ummai. Sa'ad da suka tattaru, za su ga abin da ikona zai yi, 19su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai. 20Za su taho da 'yan ƙasarku daga al'ummai, su kawo mini su kyauta. Za su zo da su a tsattsarkan dutsena, wato Urushalima, za su kawo su a kan dawakai, da alfadarai, da raƙuma, da cikin karusai, kamar dai yadda Isra'ilawa suke kawo hadaya ta hatsi a Haikali cikin tsabtatattun ƙore. 21Zan sa waɗansu su zama firistoci da Lawiyawa.”
22Ubangiji ya ce, “Kamar yadda sabuwar duniya da sabon sararin sama za su tabbata ta wurin ikona, haka zuriyarku da sunanku za su tabbata. 23A kowane bikin amaryar wata, da kowace ranar Asabar, jama'ar kowace al'umma za su zo su yi mini sujada a nan cikin Urushalima. 24Sa'ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, wutar da take ƙona su kuma ba za ta taɓa mutuwa ba. Dukan mutane za su ji ƙyamarsu.”