James
1Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.
2Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai. 3Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri. 4Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.
5In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi. 6Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.
9Ƙasƙantaccen ɗan'uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa. 10Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa. 11In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar da harkarsa.
12Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari. 13Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa. 14Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi. 15Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.
16Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. 17Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. 18Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.
19Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi, 20don fushin mutum ba ya aikata adalci. 21Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.
22Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba. 23Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi, 24don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa. 25Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.
26In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne. 27Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.
1Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki. 2Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki, 3sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,” 4ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani? 5Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba? 7Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba>
8Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla. 9Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni. 10Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari'a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari'a gaba ɗaya ke nan. 11Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari'a ke nan. 12Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari'a bisa ga ka'idar 'yanci. 13Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.
14Ya ku 'yan'uwana, ina amfani mutum ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya, bangaskiyar nan tāsa ta iya cetonsa? 15Misali, in wani ɗan'uwa ko 'yar'uwa suna zaman huntanci, kullum kuma abinci bai wadace su ba, 16waninku kuma ya ce musu, “To, ku sauka lafiya, Allah ya ba ci, da sha, da tufatarwa” ba tare da kun biya musu bukata ba, ina amfanin haka? 17Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.
18To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata. 19Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro. 20Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce? 21Sa'ad da kakanmu Ibrahim ya miƙa ɗansa Ishaku a bagadin hadaya, ashe, ba ta wurin aikatawa ne ya barata ba? 22Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala. 23Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah. 24Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba. 25Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam? 26To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.
1Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani. 2Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma. 3Ga misali, idan mun sa linzami a bakin doki, don mu bi da shi, mukan sarrafa dukan jikinsa ma. 4Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa. 5Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta!
6Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi. 7Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma, 8amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa. 9Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah. 10Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba! 11Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda? 12Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.
13Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali'u da hikima suke sawa. 14Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya. 15Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya, ta Shaiɗan kuma. 16A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke. 17Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma. 18Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.
1Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha'awace-sha'awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba? 2Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Kukan yi kwaɗayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da faɗa. Kukan rasa don ba kwa addu'a ne. 3Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.
4Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan. 5Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah ya sa a cikinmu yana tsaronmu ƙwarai?” 6Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.” 7Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku. 8Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu. 9Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya. 10Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.
11Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. 12Mai ba da Shari'a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wane ne har da za ka ɗora wa ɗan'uwanka laifi>
13To, ina musu cewa, “Yau ko gobe za mu je gari kaza, mu shekara a can, mu yi ta ciniki, mu ci riba?” 14Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Wane iri ne ranku? Ai, kamar hazo yake, jim kaɗan sai ya ɓace. 15Sai dai ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya nufa, ya kai rai, ma yi kaza da kaza.” 16Amma ga shi, kuna fariya ta alfarmar banza da kuke yi. Duk irin wannan fariya kuwa muguwar aba ce. 17Saboda haka, duk wanda ya san abin da ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya yi zunubi ke nan.
1To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙin ciki iri iri da za su aukar muku. 2Arzikinku mushe ne! Tufafinku kuma duk cin asu ne! 3Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan! 4Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna. 5Kun yi zaman duniya da annashuwa da almubazzaranci, ashe, kiwata kanku kuka yi saboda ranar yanka! 6Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.
7Domin haka, sai ku yi haƙuri, 'yan'uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka. 8Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, domin ranar komowar Ubangiji ta yi kusa. 9'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa! 10A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, 'yan'uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji. 11Ga shi, mukan yaba wa waɗanda suka jure. Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarshen da Ubangiji ya yi masa, yadda Ubangiji yake mai yawan tausayi, mai jinƙai kuma.
12Amma fiye da kome, 'yan'uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I,” ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A'a,” ya tsaya a kan “A'a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.
13In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu'a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah. 14In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikilisiya su yi masa addu'a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji. 15Addu'ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa. 16Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske. 17Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba. 18Da ya sāke yin addu'a kuwa, sai sama ta sako ruwa, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
19Ya ku 'yan'uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi, 20to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi a hanya daga bauɗewarsa, ya kuɓutar da ran mai zunubin nan ke nan daga mutuwa, ya kuma rufe ɗumbun zunubansa.