Judges

Littafin Mahukunta

1

Yahuza da Saminu sun Ci Adoni-bezek

1Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”

2Sai Ubangiji ya ce, “Yahuza ne zai tafi, ga shi, na ba da ƙasar a gare shi.”

3Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan'uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan'aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi. 4Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan'aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek. 5Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan'aniyawa da Ferizziyawa. 6Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.

7Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.

Kabilar Yahuza ta Ci Urushalima da Hebron

8Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta. 9Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari. 10Suka kuma tafi su yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.

Otniyel ya Ci Birnin Debir ya Auri Aksa

(Josh 15.15-19)

11Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer. 12Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.” 13Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure.

14Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”

15Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.

Yawan Wuraren da Yahuza da Biliyaminu Suka Ci

16Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da yake a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa. 17Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la'anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa. 18Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta. 19Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe. 20Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, a can. 21Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.

Kabilar Yusufu ta Ci Betel

22Jama'ar kabilar Yusufu kuwa suka haura don su yaƙi Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su. 23Suka aika a leƙi asirin Betel wadda a dā ake kira Luz. 24Sai 'yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.” 25Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka. 26Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.

Yawan Wuraren da Manassa da Ifraimu suka Ci

27Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta'anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan'aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar. 28Sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan'aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba.

29Mutanen Ifraimu kuma ba su kori Kan'aniyawan da suke zaune cikin Gezer ba, amma Kan'aniyawa suka yi zamansu a Gezer tare da su.

Yawan Wuraren da sauran Kabilai suka Ci

30Mutanen Zabaluna ma ba su kori mazaunan Kattat da na Nahalal ba, amma Kan'aniyawa suka zauna tare da su, suna yi musu aikin gandu.

31Haka kuma mutanen Ashiru ba su kori mazaunan Akko, da na Sidon, da Alab, da Akzib, da Helba, da Afek, da Rehob ba. 32Amma Ashirawa suka yi zamansu tare da Kan'aniyawan ƙasar, gama ba su kore su ba.

33Mutanen Naftali ma ba su kori mazaunan Bet-shemesh, da na Bet-anat ba, amma suka zauna tare da Kan'aniyawan ƙasar, duk da haka mazaunan Bet-shemesh da na Bet-anat suka zama masu yi musu aikin gandu.

34Amoriyawa suka matsa wa Danawa, suka angaza su cikin ƙasar tuddai, ba su yarda musu su zauna a filayen ba. 35Amoriyawa kuwa suka nace su zauna a Heres, da Ayalon, da Shalim. Amma mutanen kabilar Yusufu suka mallake su har suka zama masu yi musu aikin gandu. 36Iyakar Amoriyawa ta nausa ta kan hawan Akrabbim daga Sela zuwa gaba.

2

Mala'ikan Ubangiji a Bokim

1Mala'ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra'ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, “‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba. 2Ku kuma ba za ku yi alkawari da mazaunan ƙasar nan ba, amma za ku rurrushe bagadansu.” Duk da haka ba ku yi biyayya da maganata ba. Me ke nan kuka yi? 3Don haka na ce, “‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.” 4Da mala'ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi. 5Saboda haka suka sa wa wuri suna Bokim, wato waɗanda suke kuka. Suka kuma miƙa sadakoki ga Ubangiji a wurin.

Rasuwar Joshuwa

(Josh 24.29-31)

6Da Joshuwa ya sallami Isra'ilawa, kowane mutum ya tafi domin ya ɗauki gādonsa, don ya mallaki tasa ƙasa. 7Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra'ilawa. 8Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma. 9Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash, a ƙasar gādonsa. 10Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.

Isra'ilawa sun bar Yi wa Ubangiji Sujada

11Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al. 12Suka bar yi wa Ubangiji Allah na kakanninsu sujada, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar. Suka fara yi wa allolin mutanen da suke zaune kewaye da su sujada. Suka rusuna wa allolin, da haka suka sa Ubangiji ya yi fushi. 13Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba'al da Ashtarot. 14Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra'ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba. 15A duk sa'ad da suka tafi yaƙi sai Ubangiji ya yi gāba da su kamar dai yadda ya faɗa. Saboda haka suka shiga wahala ƙwarai.

16Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su. 17Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha'inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin. 18Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.

19Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba. 20Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa ya ce, “Saboda al'umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba, 21don haka daganan gaba ba zan ƙara kore musu wata al'umma daga cikin al'umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba. 22Da haka ne zan jarraba Isra'ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.” 23Don haka Ubangiji ya bar waɗannan al'ummai, bai kore su nan da nan ba, bai kuma ba da su ga Joshuwa ba.

3

Al'umman da suka Ragu don a Jarraba Isra'ilawa

1Ubangiji ya bar waɗansu al'ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra'ilawan da ba su san yaƙin Kan'ana ba. 2Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba. 3Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat, 4don a jarraba Isra'ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa. 5Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 6Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.

Otniyel ya Ceci Isra'ilawa

7Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada. 8Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushanrishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas. 9Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa. 10Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi. 11Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba'in sa'an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.

Ehud ya Ceci Isra'ilawa daga Mowabawa

12Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su. 13Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra'ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko. 14Isra'ilawa suka bauta wa Eglon Sarkin Mowab, shekara goma sha takwas.

15Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud. 16Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa. 17Sa'an nan ya ɗauki kyautan, ya kai wa Eglon Sarkin Mowab. Eglon kuwa mai ƙiba ne. 18Da Ehud ya gama ba shi kyautan, sai ya sallami mutanen da suka ɗauko kyautan. 19Amma Ehud ya juya ya koma daga wajen sassaƙaƙƙun duwatsu kusa da Gilgal, ya ce wa Eglon, “Ranka ya daɗe, na kawo maka saƙo na asiri.” Sai sarki ya ce wa fādawansa, “Ku ba mu wuri!” Dukansu kuwa suka fita, suka ba da wuri. 20Ehud kuwa ya je wurinsa, yana zaune shi kaɗai a jinkakken shirayi mai sanyi. Sai Ehud ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah zuwa gare ka!” Sarki kuwa ya tashi daga inda yake zaune, 21Ehud ya sa hannun hagunsa, ya zaro takobin da yake wajen cinyarsa ta dama, ya kirɓa masa a ciki. 22Takobin ya shiga duk da ƙotar, kitse ya rufe ruwan takobin gama bai zare takobin daga cikin sarkin ba. Ƙazanta kuwa ta fita. 23Ehud kuwa ya fita ta shirayin, ya kukkulle ƙofofin ɗakin. 24Bayan da ya tafi, fādawan suka zo, suka ga ƙofofin ɗakin suna a kulle, sai suka zaci sarkin ya zaga ne ya yi bawali. 25Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ba, suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe, sai ga ubangijinsu a ƙasa matacce.

26Sa'ad da suke ta jira, Ehud ya riga ya tsere, ya wuce sassaƙaƙƙun duwatsu zuwa Seyira. 27Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama'ar Isra'ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba. 28Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa. 29A lokacin ne suka kashe ƙarfafan mutane na Mowabawa mutum wajen dubu goma (10,000), ba wanda ya tsira. 30A ranar nan Isra'ilawa suka rinjayi Mowabawa. Ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya har shekara tamanin.

Shamgar ya Ceci Isra'ilawa daga Filistiyawa

31Bayan Ehud kuma, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya kashe Filistiyawa ɗari shida da tsinken korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra'ilawa.

4

Debora da Barak sun Ci Sisera

1Bayan rasuwar Ehud, Isra'ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji. 2Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin. 3Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

4Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra'ilawa. 5Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra'ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari'a. 6Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, “‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna. 7Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.”

8Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.”

9Sai ta ce masa, “Hakika zan tafi tare da kai, amma darajar wannan tafiya ba za ta zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Debora kuwa ta tashi, ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh. 10Barak kuwa ya kirawo kabilar Zabaluna da ta Naftali zuwa Kedesh. Mutum dubu goma (10,000) suka rufa masa baya, Debora kuwa ta haura tare da shi.

11Eber, Bakene, kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za'anannim wanda yake kusa da Kedesh.

12Aka faɗa wa Sisera cewa, Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa Dutsen Tabor. 13Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al'ummai, har zuwa Kogin Kishon. 14Debora ta ce wa Barak, “Tashi! Gama wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka, gama Ubangiji yana bi da kai!” Sai Barak ya gangaro daga Dutsen Tabor da mutum dubu goma (10,000) biye da shi. 15Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa. 16Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al'ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira.

17Amma Sisera ya gudu da ƙafa zuwa alfarwar Yayel matar Eber, Bakene, gama akwai jituwa tsakanin Yabin Sarkin Hazor da gidan Eber, Bakene. 18Sai Yayel ta fito, ta taryi Sisera, ta ce masa, “Shigo nan, ubangijina, kada ka ji tsoro.” Ya kuwa bi ta zuwa cikin alfarwa, ta ɓoye shi bayan labule.

19Ya ce mata, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa kaɗan in sha, gama ina jin ƙishi.” Ta kuwa buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, ta kuma lulluɓe shi. 20Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar alfarwar, idan wani ya zo ya tambaye ki, “‘Ko akwai wani a nan?” Sai ki ce, “‘Babu.”

21Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa'ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu. 22Barak kuwa yana bin sawun Sisera. Da Yayel ta gan shi, sai ta fita, ta tarye shi, ta ce masa, “Ka zo, zan nuna maka inda mutumin da kake nema yake.” Ya shiga alfarwarta, sai ga Sisera nan kwance matacce da turke a gindin kunnensa.

23A wannan rana Allah ya fatattaki Yabin Sarkin Kan'ana, a gaban Isra'ilawa. 24Isra'ilawa suka yi ta tsananta wa Yabin Sarkin Kan'ana har suka hallaka shi.

5

Waƙar Debora da Barak

1A wannan rana Debora da Barak, ɗan Abinowam, suka raira wannan waka,

2Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi. Mutane suka sa kansu da farin ciki. Alhamdu lillahi!

3Ku kasa kunnenku ya ku sarakuna, Ku lura, ya ku hakimai, Zan raira waƙa in yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra'ila.

4Ya Ubangiji, sa'ad da ka bar duwatsun Seyir, Sa'ad da ka fito daga jihar Edom, Ƙasa ta girgiza, Ruwan sama ya zubo daga sararin sama, I, gizagizai suka kwararo da ruwa.

5Duwatsu suka girgiza a gaban Ubangijin Sina'i, A gaban Ubangiji, Allah na Isra'ila.

6A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, Ayarori suka daina bi ta ƙasar, Matafiya suka bi ta ƙananan hanyoyi.

7Garuruwan Isra'ila, ba kowa ciki, Ba kowa ciki, sai da na zo. Na zo kamar uwa ga Isra'ila,

8Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli, Sai ga yaƙi a ƙasar. Ba a ga garkuwa ko mashi A wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.

9Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra'ila, Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

10Ku ba da labari, Ku da kuke haye da fararen jakuna, Kuna zaune a shimfiɗu, Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.

11Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyi Suna ba da labarin nasarar Ubangiji, Wato nasarar jama'ar Isra'ila! Sa'an nan jama'ar Ubangiji Suna tahowa daga biranensu.

12Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba! Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba! Ka ci gaba, kai Barak, Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba!

13Sa'an nan amintattu sun zo wurin shugabanninsu, Jama'ar Ubangiji suka zo wurina a shirye domin yaƙi.

14Daga Ilraimu mutane suka gangaro zuwa kwari, Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta. Daga Makir shugabannin sojoji suka zo, Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro.

15Shugabannin Issaka suna tare da Debora, Hakika, Issaka ya zo, Barak kuma ya zo, Suka bi bayansu zuwa kwari. Amma kabilar Ra'ubainu ta rarrabu, Ba su shawarta su zo ba.

16Don me suka tsaya daga baya tare da tumaki? Don su saurari makiyaya na kiran garkuna? Hakika kabilar Ra'ubainu ta rarrabu, Ba su shawarta su zo ba.

17Kabilar Gad suna tsaya a gabashin Urdun, Kabilar Dan kuma ta tsaya a wuraren kiwo. Kabilar Ashiru ta zauna a bakin teku, Sun zauna a gefen teku.

18Amma mutanen Zabaluna da na Naftali Suka kasai da ransu a bakin dāga.

19Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta'anak, A rafin Magiddo. Sarakunan Kan'ana suka yi yaƙi, Amma ba su kwashe azurfa ba.

20Daga sama, taurari suka yi yaƙi, Suna gilmawa a sararin sama Suka yi yaƙi da Sisera.

21Ambaliyar Kishon ta kwashe su, Wato tsohon Kogin Kishon. Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!

22Sa'an nan dawakai sun yi ta rishi Suna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu.

23Mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ka la'anta Meroz, Ka la'anta mazauna cikinta sosai, Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba, Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”

24Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin mata, sai Yayel, Matar Eber, Bakene, Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin matan da suke a alfarwai.

25Sisera ya roƙi ruwan sha, Sai ta ba shi madara, Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya.

26Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta, Ta riƙe guduma a guda hannun, Ta bugi Sisera, kansa ya fashe, Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje.

27Ya fāɗi a gwiwoyinta, Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta. A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi, Ya fāɗi matacce har ƙasa.

28Mahaifiyar Sisera ta duba ta tagogi, Ta leƙa ta kariyar taga, ta ce, “Me ya sa karusarsa ta yi jinkirin zuwa? Don me dawakansa ba su komo da wuri ba?”

29'Yan matanta mafi hikima suka amsa mata, Ita kuwa ta yi nanatawa, tana cewa,

30“Nema suke kurum su sami ganima, su raba, Yarinya ɗaya ko biyu domin kowane soja, Tufafi masu tsada domin Sisera, Rinannun tufafi masu ado domin sarauniya.”

31Ta haka, ya Ubangiji ka sa maƙiyanka su mutu, Amma abokanka su haskaka kamar fitowar rana! Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in.

6

Kiran Gidiyon

1Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai. 2Madayanawa kuwa sun fi Isra'ilawa ƙarfi, saboda haka Isra'ilawa suka yi ta ɓuya a kogon dutse, da waɗansu wuraren ɓuya a tsaunuka. 3Duk lokacin da Isra'ilawa suka yi shuka, sai Madayanawa, da Amalekawa, da waɗansu kabilai na hamada su zo su fāɗa musu. 4Sukan zo su kafa musu sansani, su ɓaɓɓata amfanin ƙasar har zuwa kusa da Gaza. Ba su barin wani abinci a ƙasar Isra'ila, domin Isra'ilawa ko dabbobinsu. 5Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar. 6Isra'ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

7Da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda wahalar da Madayanawa suke ba su, 8sai Ubangiji ya aika musu da wanda ya faɗa musu saƙon Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ni ne na fito da ku daga bauta a Masar. 9Na cece ku daga Masarawa, da kuma waɗanda suka yi yaƙi da ku a nan. Na kore su a gabanku, na ba ku ƙasarsu. 10Na faɗa muku, “‘Ni ne Ubangiji Allahnku, kada ku bauta wa gumakan Amoriyawa, waɗanda kuke zaune a ƙasarsu.” Amma ba ku yi biyayya da maganata ba.”

11Mala'ikan Ubangiji ya zo, ya zauna a gindin itacen oak na Yowash mutumin Abiyezer, a ƙauyen Ofra. Ɗansa Gidiyon kuwa yana susukar alkama daga ɓoye, a wurin da ake matse ruwan inabi, don ya ɓuya daga Madayanawa. 12Mala'ikan Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kai jarumi ne, Ubangiji kuma yana tare da kai.”

13Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, “‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar?” Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.”

14Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra'ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.”

15Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra'ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.”

16Ubangiji kuwa ya ce masa, “Za ka iya, gama zan taimake ka. Za ka muttsuke Madayanawa kamar mutum guda.”

17Gidiyon kuwa ya ce masa, “Idan ka amince da ni, ka nuna mini alama don in sani kai kake magana da ni. 18Ina roƙonka, kada ka tashi daga nan, sai na kawo maka hadaya ta abinci.” Ya amsa cewa, “Zan tsaya har ka kawo.”

19Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak. 20Mala'ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa'an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi. 21Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.

22Da Gidiyon ya gane mala'ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Kaitona, Ubangiji Allah, gama na ga mala'ikan Ubangiji fuska da fuska.”

23Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.” 24Gidiyon kuwa ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya sa masa suna, Ubangiji Salama Ne. Har wa yau bagaden yana nan a Ofra, ta iyalin Abiyezer.

25A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi. 26Sa'an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.” 27Gidiyon fa ya ɗauki mutum goma daga cikin barorinsa, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa. Amma domin yana tsoron, mutanen gidansa da na gari, bai yi wannan da rana ba, sai da dare.

28Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba'al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina. 29Suka ce wa juna, “Wa ya yi wannan abu?” Da suka binbincika, sai suka tarar Gidiyon ne, ɗan Yowash, ya yi shi. 30Sai suka ce wa Yowash, “Ka kawo ɗanka a kashe, gama ya rushe bagaden gunkin nan Ba'al, ya kuma sare gumakan da suke kusa da shi.”

31Yowash kuwa ya ce wa dukan waɗanda suka tasar masa, “Za ku yi hamayya domin gunkin nan Ba'al, ko kuwa za ku goyi bayansa? Duk wanda ya yi hamayya dominsa za a kashe shi da safe. Idan shi allah ne, to, bari ya yi hamayya don kansa, gama an farfashe bagadensa.” 32A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba'al, wato “Bari gunki Ba'al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.”

33Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel. 34Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi. 35Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi.

36Sa'an nan Gidiyon ya ce wa Allah, “Ka ce za ka sa ni in ceci Isra'ilawa. 37To, zan shimfiɗa uku a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, sa'an nan zan sani za ka ceci Isra'ilawa ta hannuna kamar yadda ka faɗa.” 38Haka kuwa ya zama Kashegari Gidiyon ya tashi da sassafe, sai ya matse ulun, ruwan raɓa da ya matse daga ulun kuwa, ya cika ƙwarya. 39Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.” 40Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.

7

Gidiyon ya Ci Madayanawa

1Sai Yerubba'al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin.

2Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra'ilawa su yi mini fāriya, su ce, “‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.” 3Yanzu sai ka ce wa mutanen, “‘Duk mai jin tsoro da mai rawar jiki, ya koma gida!” Da Gidiyon ya gwada su, mutum dubu ashirin da biyu (22,000) suka koma, dubu goma (10,000) suka tsaya.

4Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai su bakin rafi domin in jarraba maka su a can. Wanda na faɗa maka shi zai tafi tare da kai, to, shi ne zai tafi, wanda kuma na faɗa ba zai tafi tare da kai ba, to, ba zai tafi ba.” 5Gidiyon ya kai mutanen bakin rafi, Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Duk wanda ya tanɗi ruwa kamar kare, sai ka ware shi waje ɗaya. Wanda kuma ya durƙusa ya sha ruwa, ka ware shi waje ɗaya.” 6Yawan waɗanda suka tanɗi ruwa su ɗari uku ne. Sauran mutane duka kuwa sun durƙusa ne suka sha ruwan. 7Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa zan cece ku. Zan ba da Madayanawa a gare ku, ka sallami sauran, kowa ya koma gidansa.” 8Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin.

9A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka. 10Amma idan kana jin tsoro ka tafi kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka. 11Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba. 12Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.

13Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”

14Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba'isra'ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!”

15Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.” 16Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun. 17Sa'an nan ya ce musu, “Sa'ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka. 18Sa'ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoni, sai ku kuma ku busa ƙahonin a kowane gefen sansani, sa'an nan ku yi ihu, ku ce, “‘Ubangiji da Gidiyon!”

19Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu. 20Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!” 21Kowannensu ya yi tsaye a inda yake kewaye da sansanin. Dukan rundunar Madayanawa kuwa suka gudu, suna ihu. 22Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat.

23Jama'ar kabilar Naftali, da Ashiru, da Manassa, suka ji kira, suka fito, suka runtumi Madayanawa. 24Gidiyon kuma ya aika a dukan ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce musu, “Ku gangaro, ku yaƙi Madayanawa, ku tare mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.” Aka kuwa kira dukan Ifraimawa, su kuwa suka hana wa Madayanawa mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara. 25Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.

8

1Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai.

2Amma ya ce musu, “Yanzu, me na yi fiye da ku? Ai, kalar inabin Ifraimu ta fi dukan girbin Abiyezer, wato ɗan abin da kuka yi ya fi wanda kabilata ta yi nesa. 3Ga shi, Allah ya ba da Oreb da Ziyib sarakunan Madayanawa a gare ku. To, me na yi wanda ya fi naku?” Da ya faɗi haka, sai suka huce.

Nasara ta Ƙarshe a kan Madayanawa

4Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta. 5Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.”

6Shugabannin Sukkot kuwa suka ce, “Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka abinci?”

7Gidiyon ya ce, “To, sa'ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayuwan jeji.” 8Daga can ya tafi Feniyel, ya roƙe su yadda ya roƙi mutanen Sukkot. Mutanen Feniyel kuma suka amsa masa daidai yadda mutanen Sukkot suka amsa masa. 9Sai Gidiyon ya ce wa mutanen Feniyel, “Sa'ad da na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiya.”

10Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba. 11Gidiyon kuwa ya bi ta hanyar gefen hamada wadda take gabas da Noba da Yogbeha, ya faɗa wa rundunar, ta yadda ba su zato. 12Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice.

13Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres. 14Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba'in da bakwai. 15Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, “‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?” To, ga su!” 16Ya kama dattawan garin Sukkot ya hukunta su da ƙayayuwa. 17Ya kuma rushe hasumiyar Feniyel, ya karkashe mutanen birnin.

18Sa'an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka kashe a Tabor?” Suka amsa, “Kamar yadda kake, haka suke. Suna kama da 'ya'yan sarki.”

19Gidiyon ya ce musu, “Su 'yan'uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.” 20Ya ce wa Yeter, ɗan farinsa, “Tashi, ka kashe su.” Amma saurayin bai zare takobinsa ba, gama yana jin tsoro domin shi yaro ne.

21Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.

Sauran Ayyukan Gidiyon

22Sa'an nan mutanen Isra'ila suka ce wa Gidiyon, “Ka yi mulkinmu, kai da 'ya'yanka, da jikokinka, gama ka cece mu daga hannun Madayanawa.” 23Gidiyon ya ce musu, “Ba zan yi mulkinku ba, ɗana kuma ba zai yi mulkinku ba, Ubangiji ne zai yi mulkinku.” 24Ya ci gaba ya ce, “Ina roƙon kowannenku ya ba ni 'yan kunne daga cikin ganimar da ya kwaso.” (Gama Madayanawa suna da 'yan kunne na zinariya, gama su mutanen hamada ne.)

25Suka ce, “Lalle, za mu ba ka su.” Nan da nan suka shimfiɗa mayafi, kowa ya zuba 'yan kunnen da ya kwaso ganima. 26Nauyin 'yan kunnen zinariya da ya roƙa ya kai shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), banda kayan ado, da na rataye-rataye, da tufafin shunayya waɗanda sarakunan Madayanawa suke sawa, banda ɗan gaba da yake a wuyan raƙumansu. 27Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra'ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa.

28Da haka Isra'ilawa suka mallaki Madayanawa har ba su zamar musu barazana ba. Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in a zamanin Gidiyon.

Mutuwar Gidiyon

29Gidiyon kuwa ya tafi ya zauna a gidansa na kansa. 30Yana kuma da 'ya'ya maza saba'in, gama yana da mata da yawa. 31Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take a Shekem, ta haifi masa ɗa, ya sa masa suna Abimelek. 32Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya rasu da kyakkyawan tsufa. Aka binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa, a Ofra, birnin kabilar Abiyezer.

33Bayan rasuwar Gidiyon, sai Isra'ilawa suka sāke yin rashin aminci ga Allah, suka yi wa Ba'al sujada. Suka yi Ba'al-berit ya zama allahnsu. 34Suka daina bauta wa Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga magabtan da suke kewaye da su. 35Ba su kuwa sāka wa iyalin Gidiyon da alheri ba, saboda dukan alherin da ya yi wa Isra'ilawa.

9

Sarautar Abimelek

1Abimelek, ɗan Yerubba'al, wato Gidiyon, ya tafi Shekem wurin dukan dangin mahaifiyarsa, ya ce musu, 2“Ina roƙonku, ku yi magana da shugabannin Shekem, ku ce, “‘Me ya fi muku kyau, 'ya'yan Yerubba'al, maza saba'in su yi mulkinku, ko kuwa mutum ɗaya ya yi mulkinku?” Amma ku tuna fa ni jininku ne.”

3Sai dangin mahaifiyarsa suka yi magana da shugabannin Shekem saboda shi. Zuciyarsu kuwa ta saje da Abimelek, gama suka ce, “Shi ɗan'uwanmu ne.” 4Suka kuma ba shi azurfa saba'in daga cikin gidan gunkin nan Ba'al-berit. Da wannan azurfa Abimelek ya yi ijarar 'yan iska waɗanda suka bi shi. 5Ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra, ya kashe 'yan'uwansa maza, wato 'ya'yan Yerubba'al, mutum saba'in a kan dutse guda. Amma Yotam ƙaramin ɗan Yerubba'al, shi kaɗai ya ragu domin ya ɓuya. 6Sai shugabannin Shekem duka da na Betmillo suka taru suka naɗa Abimelek sarki kusa da itacen oak na al'amudin da yake a Shekem.

7Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku! 8Wata rana itatuwa suka taru don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, “‘Kai ka zama sarkinmu.” 9Amma itacen zaitun ya ce musu, “‘In bar maina wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?” 10Sai kuma itatuwa suka ce wa itacen ɓaure, “‘Ka zo, ka zama sarkinmu.” 11Amma itacen ɓaure ya ce musu, “‘In bar kyawawan 'ya'yana masu zaƙi, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?” 12Itatuwa kuma suka ce wa kurangar inabi, “‘Ki zo, ki mallake mu.” 13Sai kurangar inabi ta ce, “‘In bar ruwan inabina wanda yake faranta zuciyar alloli da ta mutane, don in tafi, in yi ta fama da itatuwa?” 14Sa'an nan dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, “‘Ka zo, ka zama sarkinmu.” 15Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, “‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al'ul na Lebanon.”

16Yotam ya ci gaba da cewa, “Yanzu kun naɗa Abimelek sarki da zuciya ɗaya ke nan? Kun yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ke nan? Wannan ne abin da ya cancance shi? 17Ku tuna fa mahaifina ya yi yaƙi dominku. Ya kasai da ransa domin ya cece ku daga Madayanawa. 18Amma ga shi, yau kun juya kuna gāba da gidan mahaifina. Kun kashe 'ya'yansa maza, su saba'in, a dutse guda, kuka naɗa Abimelek, ɗan da baiwa ta haifa, ya zama sarki a Shekem, don dai kawai shi ɗan'uwanku ne. 19Yanzu dai idan abin da kuka yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ne, to, sai ku yi farin ciki da Abimelek, ku sa shi kuma ya ji daɗinku. 20Amma idan ba haka yake ba, Allah ya sa wuta ta fito daga wurin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet-millo. Bari Allah ya sa kuma wuta ta fito daga wurin mutanen Shekem da na Bet-millo ta cinye Abimelek.” 21Sa'an nan Yotam ya tsere. Ya tafi ya zauna a Biyer, gama yana tsoron ɗan'uwansa Abimelek.

22Abimelek kuwa ya yi shekara uku, yana mulkin Isra'ila. 23Ubangiji kuma ya sa husuma ta tashi tsakanin Abimelek da mutanen Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka tayar masa. 24Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa. 25Shugabannin Shekem kuwa suka sa mutane su yi kwanto a kan dutwatsu gāba da Abimelek. Suka yi wa duk wanda ya bi ta wannan hanya fashi. Sai aka faɗa wa Abimelek.

26Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa suka yi ƙaura zuwa Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka amince da shi. 27Suka tafi gona, suka ɗebo inabi, suka matse, suka yi biki a gidan gunkinsu. Suka ci, suka sha, suka zazzagi Abimelek. 28Ga'al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba'al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku! 29Da ma a ce nake shugabancin mutanen nan, da sai in hamɓare Abimelek!” Sai ya ce wa Abimelek, “Ka tara yawan rundunarka ka fito.”

30Zebul, shugaban birnin ya ji maganganun Ga'al, ɗan Ebed, sai ya husata. 31Ya aiki jakadu wurin Abimelek a Aruma, ya ce, “Ga fa Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa sun zo Shekem, suna kutta garin ya tayar maka. 32Yanzu sai ka tashi, ka zo da dare tare da mutanen da suke tare da kai, ku yi kwanto a cikin saura. 33Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”

34Abimelek da mutanen da suke tare da shi kuwa suka tashi da dare suke yi wa Shekem kwanto da ƙungiya huɗu. 35Ga'al, ɗan Ebed, kuwa ya fita zuwa ƙofar garin daidai lokacin da Abimelek da mutanensa suka tashi daga wurin kwantonsu. 36Sa'ad da Ga'al ya ga mutanen, ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna zuwa daga kan duwatsu.” Sai Zebul ya ce masa, “Ai, inuwar duwatsu ce kake gani kamar mutane.”

37Ga'al kuma ya ƙara yin magana, ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa kan hanya, ga kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen oak na masu duba.”

38Sa'an nan Zebul ya ce masa, “Ina cika bakin nan naka, kai da ka ce, “‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa?” Waɗannan su ne mutanen da ka raina. Fita, ka yaƙe su mana.” 39Ga'al kuwa ya fita ya yi jagorar shugabannin Shekem, suka yi yaƙi da Abimelek. 40Abimelek kuwa ya runtumi Ga'al, shi kuwa ya gudu. Mutane da yawa suka ji rauni, ya bi su har bakin ƙofar birnin. 41Sai Abimelek ya zauna a Aruma. Zebul kuwa ya kori Ga'al da 'yan'uwansa, ya hana su zama a Shekem.

42Kashegari mutanen Shekem suka tafi saura, sai aka faɗa wa Abimelek. 43Shi ma ya kwashi mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, suka yi kwanto a saura. Da ya duba, ya ga mutane suna fitowa daga cikin birnin. Ya fāɗa musu, ya karkashe su. 44Abimelek kuma da ƙungiyar da take tare da shi, suka hanzarta, suka tsare ƙofar birnin. Sauran ƙungiya biyu suka ruga, suka faɗa wa dukan waɗanda suke cikin saura, suka karkashe su. 45Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.

46Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba'al-berit don su tsira. 47Abimelek kuwa ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru wuri ɗaya. 48Sai ya tafi da mutanen da suke tare da shi suka hau Dutsen Zalmon. Ya ɗauki gatari ya sari reshen itace, ya saɓe a kafaɗa. Ya ce wa mutanen da suke tare da shi, su yi hanzari su yi kamar yadda ya yi. 49Kowane mutum kuwa ya sari reshen itace, ya bi Abimelek. Suka tara rassan a jikin hasumiyar. Suka sa wa hasumiyar wuta, duk da mutanen da suke cikinta. Ta haka dukan mutanen hasumiyar Shekem suka mutu, mata da maza, wajen mutum dubu.

50Sa'an nan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta da sansani, ya ci birnin. 51Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar. 52Abimelek kuwa ya zo ya yaƙi hasumiyar. Ya je kusa da ƙofar hasumiyar don ya ƙone ta. 53Amma wata mace ta jefi Abimelek da ɗan dutsen niƙa a kā, ƙoƙon kansa ya ragargaje. 54Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, “‘Mace ta kashe shi.” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu. 55Da Isra'ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai dukansu suka tafi gida.

56Ta haka Allah ya saƙa wa Abimelek muguntar da ya yi wa mahaifinsa, da ya kashe 'yan'uwansa maza, su saba'in. 57Haka kuwa Allah ya sa muguntar mutanen Shekem ta koma kansu. Bakin Yotam, ɗan Yerubba'al, kuma ya kama su.

10

Tola da Yayir sun Shugabanci Isra'ilawa

1Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra'ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu. 2Ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da uku, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a Shamir.

3Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da biyu. 4Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir. 5Yayir ya rasu aka binne shi a Kamon.

Ammonawa sun Matsa wa Isra'ilawa

6Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada. 7Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa. 8Suka murƙushe Isra'ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra'ilawa da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune. 9Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra'ilawa kuwa suka matsu ƙwarai.

10Sa'an nan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba'al sujada.”

11Ubangiji ya amsa musu, ya ce, “Ban cece ku daga hannun Masarawa, da Amoriyawa, da Ammonawa, da Filistiyawa, 12da Sidoniyawa, da Amalekawa, da Mawonawa ba, wato su da suka matsa muku a dā, ku kuma kuka yi kuka gare ni? 13Amma duk da haka kuka bar bina, kuka yi sujada ga waɗansu alloli, don haka ni kuma ba zan ƙara cetonku ba. 14Tafi, ku yi wa allolin da kuka zaɓa kuka, don su cece ku a lokacin wahalarku.”

15Amma Isra'ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mun yi zunubi, ka yi mana duk irin abin da ka ga dama, amma in ka yarda ka cece mu yau.” 16Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha.

17Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra'ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa. 18Shugabanni da mutanen Gileyad suka ce wa junansu. “Wa zai fara yaƙi da Ammonawa? Shi zai zama shugaban duk wanda yake Gileyad.”

11

Yefta ya Ceci Isra'ilawa daga Hannun Ammonawa

1Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa. 2Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.” 3Sai Yefta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. 'Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi.

4Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi. 5Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob. 6Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.”

7Amma Yefta ya ce wa dattawan Gileyad, “Ba ku kuka ƙi ni, kuka kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuka zo wurina a lokacina da kuke shan wahala?”

8Sai dattawan Gileyad suka amsa masa, “Abin da ya sa muka zo wurinka yanzu, shi ne domin ka tafi tare da mu ne mu yi yaƙi da Ammonawa, ka kuma zama shugaban dukan jama'ar Gileyad.”

9Yefta kuwa ya ce musu, “Idan kuka koma da ni gida domin in yi yaƙi da Ammonawa, idan Ubangiji ya ba da su a hannuna, to, zan zama shugabanku.”

10Suka amsa suka ce wa Yefta, “Ubangiji shi ne shaida tsakaninmu, lalle za mu yi maka kamar yadda ka ce.” 11Yefta kuwa ya tafi tare da dattawa Gileyad. Su kuwa suka naɗa shi shugabansu da sarkin yaƙinsu. Yefta kuwa ya faɗi dukan abin da yake zuciyarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.

12Yefta kuwa ya aiki jakadu wurin Sarkin Ammonawa da cewa, “Me ya haɗa ka da ni, da ka zo ƙasata da yaƙi?”

13Sarkin Ammonawa ya amsa wa jakadun Yefta cewa, “Domin lokacin da Isra'ilawa suna tahowa daga Masar sun ƙwace mini ƙasa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa Kogin Urdun. Yanzu sai ka mayar mini da ita cikin lumana.”

14Yefta kuma ya sāke aike da jakadu wurin Sarkin Ammonawa, 15tare da amsa, ya ce, “Isra'ilawa ba su ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba. 16Amma sa'ad da suka baro Masar, sun bi ta jeji zuwa Bahar Maliya, suka zo Kadesh. 17Sa'an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra'ilawa suka zauna a Kadesh.

18“Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab. 19Sa'an nan Isra'ilawa suka aike da jakadu wurin Sihon Sarkin Heshbon ta Amoriyawa, suka roƙe shi, suka ce, “‘Ka yarda mana mu wuce ta ƙasarka.” 20Amma Sihon bai amince wa Isra'ilawa su bi ta ƙasarsa, su wuce ba. Ya kuwa tattara mutanensa, ya kafa sansaninsa a Yahaza, ya yi yaƙi da Isra'ilawa. 21Ubangiji Allah na Isra'ila kuwa ya ba da Sihon da mutanensa duka ga Isra'ilawa, suka ci su da yaƙi. Suka kuwa mallaki dukan ƙasar Amoriyawa da mazaunan ƙasar. 22Suka mallaki dukan ƙasar Amoriyawa tun daga Kogin Arnon har zuwa Kogin Yabbok, tun kuma daga jeji zuwa Kogin Urdun. 23To, ai, ka ga Ubangiji Allah na Isra'ila ne ya kori Amoriyawa saboda jama'ar Isra'ila. To, yanzu so kake ka ƙwace mana? 24Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi. 25Kana zaton ka fi Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab? Ka ji ya taɓa hamayya da Isra'ilawa? Ko kuwa ka ji ya taɓa yin yaƙi da su? 26Shekara ɗari uku Isra'ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba? 27Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara'anta tsakanin Isra'ilawa da Ammonawa.” 28Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba.

29Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa. 30Yefta kuwa ya yi wa'adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna, 31duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa'ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.” 32Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa. 33Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra'ilawa.

'Yar Yefta

34Da Yefta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga 'yarsa, tilo ta fito da kiɗa da rawa don ta tarye shi. Ita ce kaɗai 'yarsa, banda ita ba shi da ɗa ko 'ya. 35Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”

36Sai ta ce masa, “Baba, idan ka riga ka yi wa'adi ga Ubangiji, sai ka yi da ni bisa ga wa'adinka, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa, abokan gābanka.” 37Ta kuma ce masa, “Ina so ka yardar mini in tafi kan duwatsu ni da ƙawayena in yi makokin budurcina har wata biyu.”

38Sai ya ce mata, “Tafi.” Ya sallame ta, ta tafi har wata biyu ɗin. Ita da ƙawayenta kuwa suka yi makokin budurcinta a kan duwatsu. 39Bayan wata biyu, sai ta koma wurin mahaifinta, shi kuwa ya yi abin da ya yi wa Ubangiji wa'adi. Ta rasu ba ta taɓa sanin namiji ba. Wannan kuwa ya zama al'ada a cikin Isra'ila, 40wato matan Isra'ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don 'yar Yefta, mutumin Gileyad.

12

Yefta da Mutanen Ifraimu

1Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”

2Amma Yefta ya amsa musu, ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya da Ammonawa, na kira ku don ku cece ni, amma ba ku cece ni daga hannunsu ba. 3Sa'ad da na ga ba ku cece ni ba, sai na yi kasai da raina, na haye don in yi karo da Ammonawa. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna. Me ya sa kuka zo yau don ku yi yaƙi da ni?”

4Sa'an nan Yefta ya tara dukan mutanen Gileyad, suka yi yaƙi da mutanen Ifraimu, suka ci su. Mutanen Ifraimu suka ce musu, “Ku mutanen Gileyad masu neman mafaka ne a cikin Ifraimu da Manassa!” 5Mutanen Gileyad suka hana mutanen Ifraimu hayewa ta mashigan Kogin Urdun. Idan wani mutumin Ifraimu gujajje ya ce, “Ku bar ni in haye.” Sai mutanen Gileyad su tambaye shi, “Kai mutumin Ifraimu ne?” Idan ya ce, “A'a,” 6sai su ce masa, to, ka ce, “Shibbolet,” sai mutum ya ce, “Sibbolet,” gama ba ya iya faɗa daidai. Sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Mutanen Ifraimu da aka kashe a lokacin su dubu arba'in da dubu biyu (42,000) ne.

7Yefta mutumin Gileyad ya shugabanci Isra'ilawa shekara shida, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a garinsu, wato Gileyad.

Ibzan, da Elon, da Abdon sun Shugabanci Isra'ilawa

8Bayan Yefta, sai Ibzan, mutumin Baitalami ya shugabanci Isra'ilawa. 9Yana da 'ya'ya maza talatin, da 'ya'ya mata talatin. Ya aurar da 'ya'yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa 'ya'yansa maza 'yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara bakwai. 10Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami.

11Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra'ilawa shekara goma. 12Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Ayalon a ƙasar Zabaluna.

13Bayan Elon kuma, sai Abdon, ɗan Hillel, mutumin Firaton, ya shugabanci Isra'ilawa. 14Yana da 'ya'ya maza arba'in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba'in. Abdon ya shugabanci Isra'ilawa shekara takwas. 15Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Firaton ta ƙasar Ifraimu a tudun Amalekawa.

13

Haihuwar Samson

1Isra'ilawa kuma suka sāke yi wa Ubangiji zunubi, sai Ubangiji ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba'in.

2Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa. 3Ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa. 4Yanzu sai ki lura, kada ki sha ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, kada kuma ki ci haramtaccen abu, 5gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa.”

6Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala'ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba. 7Amma ya ce mini, zan yi juna biyu, in haifi ɗa, don haka kada in sha ruwan inabi, ko abin sa maye, kada kuma in ci haramtaccen abu, gama yaron zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki har zuwa ranar da zai rasu.”

8Sa'an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”

9Allah kuwa ya ji roƙon Manowa, ya sāke aiko da mala'ikansa wurin matar, sa'ad da take a saura, mijinta kuwa ba ya tare da ita. 10Don haka sai ta sheƙa a guje zuwa wurin mijinta, ta faɗa masa, “Ga mutumin da ya zo wurina ran nan, ya sāke zuwa.”

11Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?” Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.”

12Manowa kuma ya ce, “Lokacin da maganarka ta cika, wane irin yaro ne zai zama, me kuma za mu yi?”

13Mala'ikan Ubangiji ya amsa, ya ce wa Manowa, “Sai matarka ta kiyaye dukan abin da na faɗa mata. 14Kada ta ci kowane irin abu da aka yi da inabi, kada kuma ta sha ruwan inabi ko abin sa maye. Kada ta ci haramtaccen abu, amma ta kiyaye dukan abin da na umarce ta.” 15-16Manowa dai bai san mala'ikan Ubangiji ne ba, sai ya ce wa mala'ikan, “Ina roƙonka ka jira, mu yanka maka ɗan akuya.” Amma mala'ikan ya ce masa, “Ko na jira ba zan ci abincinku ba, amma idan kana so ka yanka, sai ka shirya hadayar ƙonawa, ka miƙa ta ga Ubangiji.”

17Manowa ya ce, “Ka faɗa mana sunanka domin lokacin da maganarka ta cika mu girmama ka.”

18Mala'ikan Ubangiji ya ce masa, “Don me kake tambayar sunana? Sunana asiri ne.” 19Manowa kuwa ya yanka ɗan akuya, ya kuma kawo hadayar gari, ya miƙa a kan dutse ga Ubangiji, mala'ika kuma ya yi al'ajabi. Manowa da matarsa suka yi kallo. 20Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa. 21Mala'ikan Ubangiji bai sāke bayyana ga Manowa da matarsa ba. Manowa kuma ya gane mala'ikan Ubangiji ne.

22Manowa ya ce wa matarsa, “Ba shakka za mu mutu gama mun ga Ubangiji!”

23Amma matarsa ta ce masa, “Da Ubangiji yana so ya kashe mu, ai, da bai karɓi hadayar ƙonawa da hadayar gārinmu ba, da kuma bai nuna mana, ko ya faɗa mana waɗannan abubuwa ba.”

24Matar kuwa ta haifi ɗa, aka raɗa masa suna Samson. Yaron ya yi girma, Ubangiji ya sa masa albarka. 25Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa'ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.

14

Samson da Budurwa a Timna

1Samson kuwa ya gangara zuwa Timna inda ya ga ɗaya daga cikin 'yan matan Filistiyawa. 2Sa'ad da ya hauro zuwa gida sai ya faɗa wa iyayensa, ya ce, “Na ga ɗaya daga cikin 'yan matan Filistiyawa a Timna, ina so ku auro mini ita.”

3Amma iyayensa suka ce masa, “Cikin 'yan'uwanka da mutanenka duka, ba yarinyar da za ka aura daga cikin 'yan matansu, har ka tafi ka auro mace daga na Filistiyawa marasa kaciya?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ita ce wadda nake bukata, ka auro mini ita. Ina sonta.”

4Iyayensa ba su san al'amarin nan daga wurin Ubangiji ne ba, gama Ubangiji yana so wannan ya zama sanadin yaƙi da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa ne suke mulkin Isra'ilawa.

5Samson kuwa ya gangara zuwa Timna, shi da iyayensa. Da ya isa gonakin inabin Timna, sai ga sagarin zaki ya taso masa da ruri. 6Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.

7Sa'an nan ya gangara ya yi zance da budurwar, yana kuwa sonta. 8Bayan 'yan kwanaki sai ya koma don ya auro ta. Ya ratse don ya duba gawar zakin da ya kashe, sai ya tarar da cincirindon ƙudan zuma, da kuma zuma a cikin gawar zakin, ya yi mamaki. 9Ya ɗebo zuman a hannunsa, yana tafe yana sha, har ya isa wurin iyayensa, ya ba su, suka sha, amma bai faɗa musu daga cikin gawar zaki ya ɗebo zuman ba.

10Mahaifinsa ya tafi gidan iyayen yarinyar, Samson kuma ya shirya liyafa a can, gama haka samari sukan yi. 11Sa'ad da Filistiyawa suka gan shi suka sa samari talatin su zauna tare da shi. 12Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado. 13Amma idan kun kāsa ba ni amsar, to, ku ne za ku ba ni riguna talatin na ado.” Sai suka ce, “To, faɗi ka-cici-ka-cicin mu ji.”

14Sai ya ce musu, “Daga mai ci, abinci ya fito, Daga kuma mai ƙarfi, zaƙi ya fito.” Ba su iya ba da amsar ba har kwana uku.

15A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?”

16Sai matar Samson ta yi kuka a gabansa tana cewa, “Kai dai maƙiyina ne, ba masoyina ba, ka yi wa mutanena ka-cici-ka-cici, amma ba ka gaya mini amsarsa ba.” Amma ya ce mata, “Ko iyayena ma ban faɗa musu ba, sai in faɗa miki?” 17Ta kuwa yi ta yi masa kuka har rana ta bakwai ta ƙarewar bikinsu. Amma a rana ta bakwai, ya faɗa mata amsar saboda yawan fitinarta. Ita kuwa ta faɗa wa mutanenta amsar ka-cici-ka-cicin.

18A rana ta bakwai, kafin rana ta faɗi, mutanen garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaƙi? Me kuma ya fi zaki ƙarfi?” Ya kuwa ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, Da ba ku san amsar ka-cici-ka-cicin ɗin nan ba.”

19Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru. 20Aka ɗauki matar Samson aka ba wanda ya yi masa abokin ango.

15

1Bayan 'yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.” Amma mahaifinta bai yardar masa ba. 2Ta ce wa Samson, “Na yi tsammani ba ka sonta ne sam, don haka sai na ba da ita ga wanda ya yi maka abokin ango. Amma ƙanwarta ta fi ta kyau. Ina roƙonka ka ɗauki ƙanwar maimakon matarka.”

3Sai Samson ya ce musu, “A wannan lokaci, zan zama marar laifi saboda abin da zan yi wa Filistiyawa.” 4Ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku, ya haɗa wutsiyoyinsu, wato wutsiya da wutsiya, sa'an nan ya ɗaura jiniya tsakanin kowaɗanne wutsiya biyu. 5Da ya sa wa jiniyar wuta, ya sake su zuwa cikin hatsin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi, da hatsin da yake a tsaye, da gonakin zaitun.

6Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?” Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.

7Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!” 8Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa'an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.

Samson ya ci Nasara a kan Filistiyawa

9Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai. 10Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?” Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”

11Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?” Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”

12Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.” Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”

13Suka ce masa, “A'a, ba za mu kashe ka ba, mu dai za mu kama ka, mu miƙa ga Filistiyawa.” Sa'an nan suka ɗaure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka sauko da shi daga dutsen.

14Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta. 15Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin. 16Sa'an nan Samson ya raira waƙa ya ce. “Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu, Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.”

17Da ya gama, ya jefar da muƙamuƙin. Sai aka ba wurin suna, Ramat-Lihai, wato tudun muƙamuƙi.

18Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?” 19Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.

20Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.

16

Samson a Gaza

1Daga can Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa, sai ya shiga wurinta. 2Aka faɗa wa mutanen Gaza, Samson yana nan. Suka kewaye wurin, suka yi fakonsa a ƙofar garin dukan dare. Suka yi shiru dukan dare, suka ce wa junansu, “Za mu jira sai gari ya waye sa'an nan mu kashe shi.” 3Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa'an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a gaban Hebron.

Samson da Delila

4Bayan wannan kuma sai ya kama ƙaunar wata mace mai suna Delila a kwarin Sorek. 5Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”

6Delila kuwa ta ce wa Samson, “Ina roƙonka ka faɗa mini inda babban ƙarfin nan naka yake, da kuma yadda za a ɗaure ka ka rasa kuzari.”

7Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.” 8Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su.

9Tana kuwa da mutane a laɓe cikin wani ɗaki, sai ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da jin haka, sai ya katse tsarkiyoyi kamar zare idan an sa masa wuta. Asirin ƙarfinsa kuwa bai sanu ba.

10Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba'a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”

11Ya ce mata, “Idan suka ɗaure ni da sababbin igiyoyi waɗanda ba a yi amfani da su ba, to, zan rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

12Sai Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi, ta ɗaure shi da su, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa na zuwa kanka, Samson!” Amma ya katse igiyoyin da ta ɗaure shi da su kamar silin zare. Mutanen kuwa na nan laɓe a wani ɗaki.

13Delila ta ce wa Samson, “Har yanzu dai, ka maishe ni shashasha, kana ta ruɗina. Ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.” Ya ce mata, “Idan kin saƙa tukkwayen bakwai da suke kaina haɗe da zare, kika buga da akwasha sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

14Sa'ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren.

15Delila ta ce masa, “Ƙaƙa za ka ce kana ƙaunata, alhali kuwa ba na a zuciyarka? Sau uku ke nan ka maishe ni shashasha, ba ka faɗa mini inda ƙarfin nan naka yake ba.” 16Sa'ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu.

17A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”

18Sa'ad da Delila ta gane ya faɗa mata ainihin gaskiya, sai ta aika a kirawo shugabannin Filistiyawa tana cewa, “A wannan karo ku zo, domin ya faɗa mini ainihin gaskiyar.” Shugabannin Filistiyawa kuwa suka zo wurinta da kuɗi a hannu. 19Ta kuwa sa shi ya yi barci a cinyoyinta, sai ta kira wani mutum, ta sa shi ya aske tukkwayen nan bakwai da suke kansa. Sa'an nan ta yi ƙoƙari ta sa ya harzuƙa, amma ƙarfinsa ya rabu da shi. 20Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi. 21Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku. 22Amma gashin kansa ya fara tohowa.

Samson ya Mutu

23Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!”

24Da mutane suka gan shi, sai suka raira waƙar yabon allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya ba da maƙiyinmu a hannunmu, wanda ya fallasa ƙasarmu, ya kashe mutanenmu da yawa.” 25Sa'ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.

26Samson kuwa ya ce wa yaron da yake jagoransa, “Bari in taɓa ginshiƙan da yake ɗauke da gidan nan, domin in jingina.” 27Gidan kuwa yana cike da mutane mata da maza. Shugabannin nan biyar na Filistiyawa suna wurin. Akwai mutum dubu uku mata da maza, a kan benen da suka zo kallon wasan Samson.

28Sa'an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.” 29Sai Samson ya kama ginshiƙai biyu da suke a tsakiya, waɗanda suke ɗauke da gidan. Ya riƙe su da hannunsa biyu, ɗaya a kowane hannu, sa'an nan ya jingina jikinsa a kansu, 30ya yi kuwwa ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Ya sunkuya da iyakar ƙarfinsa. Ɗakin kuwa ya faɗa a kan shugabannin da dukan mutanen da suke a cikin ɗakin. Mutanen da Samson ya kashe a rasuwarsa sun fi waɗanda ya kashe sa'ad da yake da rai.

31'Yan'uwansa da dukan danginsa, suka gangara, suka ɗauki gawarsa, suka binne a kabarin Zora da Eshtawol. Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin.

17

Gumakan Mika

1Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika. 2Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.” Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.” 3Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la'anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.” 4Da ya mayar mata da azurfar, ta ɗibi azurfa ɗari biyu ta ba maƙerin azurfa, shi kuwa ya sassaƙa gunki ya kuma yi na zubi. Aka ajiye su a gidan Mika.

5Mika kuwa yana da ɗakin gumaka. Ya yi gumaka, da falmaransu, da kan gida. Ya keɓe ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza domin ya zama firist nasa. 6A wannan lokaci ba sarki a Isra'ila, kowa yana ta yin yadda ya ga dama.

7Akwai wani saurayi Balawe da yake zama a Baitalami ta Yahudiya. 8Saurayin kuwa ya yi ƙaura daga Baitalami. Sa'ad da yake tafiya sai ya iso gidan Mika, a ƙasar tudu ta Ifraimu. 9Mika ya tambaye shi, “Daga ina ka zo?” Ya ce, “Ni Balawe ne na Baitalami ta Yahudiya, ina neman wurin da zan zauna.”

10Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni, ka zama mai ba ni shawara, da kuma firist, ni kuwa zan riƙa ba ka azurfa goma, da tufafi, da abin zaman gari kowace shekara.” 11Balawen kuwa ya yarda ya zauna tare da Mika. Ya kuwa zama kamar ɗa ga Mika. 12Mika kuma ya naɗa shi ya zama firist ɗinsa. Ya kuwa zauna a gidansa. 13Sa'an nan Mika ya ce, “Yanzu na sani Ubangiji zai sa mini albarka, da yake na sami Balawe ya zamar mini firist.”

18

Mika da Kabilar Dan

1A kwanakin nan ba sarki a Isra'ila. A wannan lokaci kuwa kabilar Dan suna ta neman yankin ƙasar da za su samu, su zauna. Gama har yanzu ba su sami nasu gādon ƙasa tare da sauran kabilar Isra'ila ba. 2Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika. 3Sa'ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?”

4Ya ce musu, “Mun yi yarjejeniya da Mika, in yi masa aikin firist, shi kuma ya biya ni.”

5Suka ce masa, “In ka yarda ka roƙar mana Allah ko tafiyarmu na da sa'a.”

6Firist ɗin ya ce musu, “Kada ku damu, Ubangiji yana tare da ku a tafiyarku.”

7Saboda haka mutanen nan biyar suka tashi, suka zo Layish, suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa. Ba su da rigima, natsattsu ne, ba su jayayya da kowa, suna da wadata. Suna nesa da Sidoniyawa, ba su sha'anin kome da kowa. 8Da mutanen nan biyar suka koma wurin 'yan'uwansu a Zora da Eshtawol, sai 'yan'uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu. 9Suka ce, “Ku tashi, mu tafi mu fāɗa musu, gama mun ga ƙasar tana da ni'ima ƙwarai. Kada ku zauna ku ɓata lokaci, ku shiga ku mallake ta! 10Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.”

11Mutum ɗari shida daga kabilar Dan suka yi shirin yaƙi, suka kama hanya daga Zora da Eshtawol. 12Suka tafi suka kafa sansani a yammacin Kiriyat-yeyarim, birni ne a Yahudiya. Saboda haka ake kiran wurin Mahanedan, wato sansanin Dan, har wa yau. 13Daga can suka wuce zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka zo gidan Mika.

14Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?” 15Sai suka juya zuwa gidan Mika, inda saurayin nan Balawe yake, suka gaishe shi. 16Danawa ɗari shida ɗin da suka yi shirin yaƙi, suka tsaya a bakin ƙofa. 17Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi.

18Sa'ad da mutum biyar ɗin nan suka shiga gidan Mika suka ɗauki falmaran, da sassaƙaƙƙen gunki, da kan gida, da gunki na zubi, sai firist ɗin ya ce musu, “Me kuke yi?”

19Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra'ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?” 20Da firist ɗin ya ji haka, sai ya yi murna, ya ɗauki falmaran da kan gida da sassaƙaƙƙen gunki, ya tafi tare da su.

21Suka juya, suka tafi da 'ya'yansu da dabbobinsu, da mallakarsu. 22Sa'ad da suka yi 'yar tazara daga gidan Mika sai aka kira maƙwabtan Mika, suka je suka ci wa Danawa. 23Suka yi wa Danawa tsawa. Da suka waiga, sai suka ce wa Mika, “Me ya faru? Me ya kawo waɗannan 'yan iska?”

24Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa'an nan ku ce mini, “‘Me ya faru?”

25Danawa kuma suka ce masa, “Kada ka kuskura ka ce kome, idan ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.” 26Sa'an nan Danawa suka kama hanyarsu. Da Mika ya ga dai sun fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.

27Da Danawa suka ɗauke gumakan da Mika ya yi, da firist ɗinsa, sai suka je Layish inda suka sami mutane suna zamansu a huce. Suka hallaka su, suka ƙone birnin. 28Ba wanda zai ceci mutanen Layish, gama suna nesa da Sidon, ba su kuma sha'ani da kowa. A kwari guda ne da Bet-rehob. Danawa kuwa suka sāke gina birnin, suka zauna a ciki. 29Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne. 30Danawa fa suka kafa gunkin domin su yi masa sujada. Jonatan, ɗan Gershom, ɗan Musa, shi da 'ya'yansa maza, suka zama firistocin Danawa, har zuwa ranar da aka kwashe mutanen zuwa bauta. 31Haka fa suka kafa gunkin Mika har duk lokacin da alfarwar Ubangiji take a Shilo.

19

Balawe da Ƙwarƙwararsa

1A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawe da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa. 2Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu. 3Sa'an nan mutumin ya tafi ya yi bikonta. Ya tafi da baransa da jaki biyu. Da ya zo gidan mahaifinta, sai ta shigo da shi gidan, mahaifin ya karɓe shi da farin ciki. 4Mahaifin macen ya i masa ya dakata, sai ya tsaya har kwana uku. Suka ci suka sha tare. 5A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa'an nan ka tafi.”

6Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.”

7Sa'ad da mutumin ya tashi zai tafi sai mahaifin macen ya roƙe shi, ya kuma kwana. 8A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare.

9Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”

10Amma mutumin bai yarda ya sāke kwana ba, sai ya tashi shi da ƙwarƙwararsa suka kama hanya. Ya kai daura da Yebus, wato Urushalima ke nan. Yana tare da jakinsa biyu da ya yi musu shimfiɗa, da ƙwarƙwararsa. 11Baran kuwa ya ce wa maigidansa, “In ka yarda mu ratse mu kwana a birnin Yebusiyawan nan.”

12Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra'ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya, 13mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.” 14Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa'ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu. 15Suka ratse don su kwana a Gibeya. Balawen ya tafi ya zauna a dandalin garin, gama ba wanda ya kai su gidansa su kwana.

16To, ga wani tsoho yana komowa daga gona da yamma. Tsohon kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya, amma mutanen Gibeya kabilar Biliyaminu ne. 17Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”

18Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungu da yake ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa. 19Ina da baro domin jakuna, ina kuma da abinci da ruwa inabi don kaina, da ƙwarƙwarata da barana, ba mu rasa kome ba.”

20Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.” 21Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa'an nan suka ci suka sha.

22Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”

23Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya. 24Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!” 25Amma 'yan iskan ba su yarda ba, sai Balawen ya fitar da ƙwarƙwararsa gare su. Suka yi mata faɗe, suka wulakanta ta dukan dare har kusan wayewar gari, sa'an nan suka ƙyale ta.

26Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira. 27Sa'ad da Balawen ya tashi da safe, ya buɗe ƙofa, ya fita domin ya kama hanyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa kwance a ƙofar gida, da hannuwanta a dokin ƙofar. 28Ya ce mata, “Tashi mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya aza gawarta a kan jaki, sa'an nan ya kama hanya zuwa gida. 29Da ya isa gida, ya ɗauki wuƙa ya yanyanka gawar ƙwarƙwararsa gunduwa gunduwa har goma sha biyu, ya aika a ko'ina cikin dukan ƙasar Isra'ila.

30Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra'ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al'amari?”

20

Yaƙi da Mutanen Biliyaminu

1Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa. 2Dukan shugabannin kabilar Isra'ila suna cikin wannan taron jama'ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000). 3Mutanen Biliyaminu kuwa sun ji labari sauran Isra'ilawa sun haura zuwa Mizfa. Isra'ilawa suka tambayi Balawen suka ce, “Ka faɗa mana yadda wannan mugun abu ya auku.”

4Balawe, mai ƙwarƙwarar da ka kashe, ya amsa ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata muna biyo Gibeya ta Biliyaminu mu kwana. 5Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa. 6Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila. 7Dukanku nan Isra'ilawa ne, me za mu yi a kan wannan al'amari?”

8Dukan jama'a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa. 9Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi. 10Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.” 11Saboda haka dukan mutanen Isra'ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.

12Kabilar Isra'ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata? 13Yanzu sai ku ba da mutanen nan 'yan iska da suke cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra'ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar 'yan'uwansu, Isra'ilawa ba. 14Mutanen Biliyaminu kuwa suka fita daga Gibeya gaba ɗaya domin su yi yaƙi da jama'ar Isra'ila. 15A ran nan mutanen Biliyaminu suka tattaru daga garuruwansu, mutum dubu ashirin da dubu shida (26,000). Banda waɗannan, sai da mazaunan Gibeya suka tara zaɓaɓɓun mutane ɗari bakwai. 16Daga cikin waɗannan duka akwai zaɓaɓɓun mutane bakwai, bahagwai. Kowannensu yana iya ya baraci gashi guda da majajjawa ba kuskure. 17Isra'ilawa kuwa banda kabilar Biliyaminu, suka tara mayaƙa dubu ɗari huɗu (400,000) horarru.

Yaƙi da Mutanen Biliyaminu

18Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.” 19Sa'an nan Isra'ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya. 20Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya. 21Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra'ila a ranar. 22-23Mutanen Isra'ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu mutanen Biliyaminu?” Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.” Saboda haka sai sojojin Isra'ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā. 24Sai mutanen Isra'ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu. 25Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000) daga cikin Isra'ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne. 26Dukan rundunan Isra'ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa'an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama. sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?” Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele'azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.

29Isra'ilawa kuwa suka sa 'yan kwanto kewaye da Gibeya. 30Sa'an nan suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta uku. Suka jā dāgar yaƙi gaba da Gibeya kamar dā. 31Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra'ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye. 32Sai mutanen Biliyaminu suka ce, “Mun fatattake su kamar dā.” Amma Isra'ilawa suka ce, “Mu gudu don mu jawo su nesa da birnin zuwa karauka.”

33Isra'ilawa duka suka tashi daga wurin da suke, suka jā dāga a Ba'altamar. Mutanensu da suke kwanto a yammacin Gibeya suka fito. 34Horarrun sojojin Isra'ila, su dubu goma (10,000), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba. 35Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne. 36Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi. Mutanen Isra'ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto. 37Sai 'yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin. 38Alamar da mayaƙan Isra'ila da na 'yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin. 39Idan mutanen Isra'ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra'ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.” 40Amma sa'ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama. 41Da mutanen Isra'ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu. 42Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin 'yan kwanto da sauran sojojin Isra'ilawa. 43Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas. 44Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000). 45Sauran suka juya, suka gudu, suka nufi wajen hamada zuwa Dutsen Rimmon. A kan hanyoyi, aka kashe musu mutum dubu biyar. Aka kuma runtumi sauran da suka ragu har zuwa Gidom inda suka kashe mutum dubu biyu. 46Mutanen Biliyaminu da aka kashe a ran nan dubu ashirin da biyar (25,000) ne. Dukansu kuwa jarumawa ne.

47Amma mutum ɗari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata huɗu. 48Mutanen Isra'ila kuma suka komo, suka fāɗa wa sauran mutanen Biliyaminu. Suka karkashe su, mutane, da dabbobi, da dukan abin da suka iske. Suka ƙone garuruwan wannan yankin ƙasa.

21

Mata domin Mutanen Biliyaminu

1Mutanen Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji ƙaƙƙarfan alkawari a Mizfa cewa, “Ba wani daga cikinmu da zai ba da 'yarsa aure ga mutumin Biliyaminu.” 2Sai mutanen Isra'ila suka zo Betel, suka zauna a nan a gaban Allah har maraice. Suka yi makoki mai zafi. 3Suka ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa wannan abu ya faru a cikin Isra'ila, har da za a rasa kabila guda ta Isra'ila?”

4Kashegari mutanen suka tashi da safe, suka gina bagade a can. Suka miƙa hadayun ƙonawa da na salama. 5Suka kuma ce, “Daga cikin kabilar Isra'ila, wace ce ba ta halarci wannan taro na gaban Ubangiji ba?” Gama sun riga sun yi ƙaƙƙarfan alkawari cewa, “Duk wanda bai hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba, za a kashe shi.” 6Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi juyayin 'yan'uwansu, mutanen Biliyaminu, suka ce, “Yau an hallaka kabila guda daga cikin Isra'ila. 7Ƙaƙa za mu yi don mutanen da suka ragu su sami mata. Ga shi, mum riga mu rantse da Ubangiji ba za mu ba su 'ya'yanmu mata su aura ba?”

8Sa'an nan suka ce, “Wace kabila ce daga cikin kabilar Isra'ila ba ta hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba?” Sai suka ga, ashe, ba wani daga Yabesh-gileyad da ya halarci taron. 9Gama sa'ad da aka tattara mutanen, aka ga ba wani daga cikin mazaunan Yabesh-gileyad a wurin. 10Taron jama'a kuma suka aiki jarumawansu mutum dubu goma sha biyu (12,000) zuwa Yabesh-gileyad. Suka umarce su cewa, “Ku je ku karkashe mazaunan Yabesh duka har da mata da yara. 11Abin da za ku yi ke nan, ku je ku kashe dukan maza, da kowace mace wadda ba budurwa ba ce.” 12Suka sami budurwai ɗari huɗu daga mutanen Yabesh-gileyad, sai suka kawo su zango a Shilo, wadda take a ƙasar Kan'ana.

13Sa'an nan taron jama'a suka aika wa mutanen Biliyaminu da suke a Dutsen Rimmon, cewa, yaƙi ya ƙare, sai salama. 14Mutanen Biliyaminu kuwa suka komo, aka ba su budurwan nan da aka bar su da rai aka kawo su Yabesh-gileyad, amma budurwan ba su ishe su ba.

15Sai mutanen suka yi juyayin mutanen Biliyaminu domin Ubangiji ya naƙasa kabila daga kabilar Isra'ila. 16Saboda haka dattawan taron jama'a suka ce, “Ƙaƙa za mu yi da waɗanda suka ragu da ba su sami mata ba, da yake an hallaka matan kabilar Biliyaminu?” 17Sai suka ce, “Tilas, waɗanda suka ragu daga mutanen Biliyaminu su sami gādo domin kada a shafe kabila daga cikin Isra'ila, 18amma fa ba za mu iya aurar musu da 'ya'yanmu mata ba.” Sun faɗi haka ne kuwa, domin sun riga sun rantse cewa, “Duk wanda ya aurar da 'yarsa ga mutumin Biliyaminu la'ananne ne.” 19Suka kuma ce, “Ga shi, idin Ubangiji na shekara shekara a Shilo ya kusa.” (Shilo tana arewacin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.)

20Suka umarci mutanen Biliyaminu suka ce, “Ku tafi ku yi kwanto a gonakin inabi, 21ku lura, idan 'yan matan Shilo sun fito domin su yi rawa, sai ku fito daga cikin gonakin inabi, kowa ya kama daga cikin 'yan matan da ƙarfi, ya sami mata ke nan, ya tafi da ita a ƙasar Biliyaminu. 22Sa'ad da iyayensu ko 'yan'uwansu sun kawo ƙara gare mu, za mu ce musu, “‘Ku bar mana su, muna roƙonku, domin ba daga wurin yaƙi muka kamo su domin su zama matanmu ba. Amma tun da ba ku ba mu su ba, ba ku da laifin ta da alkawari.” 23Haka kuwa mutanen Biliyaminu suka yi. Suka kama budurwai gwargwadon yawansu daga cikin masu rawa. Sa'an nan suka koma zuwa yaƙin ƙasarsu ta gādo. Suka sāke gina garuruwansu, suka zauna. 24Hakanan kuma sauran mutanen Isra'ila suka tashi daga can. Kowa ya tafi wurin kabilarsa, da iyalinsa, da abin da ya mallaka.

25A lokacin ba sarki a Isra'ila, sai kowa ya yi ta yin abin da ya ga dama.