Jeremiah

Irmiya

1

Kiran Irmiya da Keɓewarsa

1Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu, 2wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa, 3da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.

4Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

5“Na san ka tun kafin a yi cikinka, Na keɓe ka tun kafin a haife ka, Na sa ka ka zama annabi ga al'ummai.”

6Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah! Ban san abin da zan faɗa ba, Gama ni yaro ne.”

7Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce kai yaro ne, Kai dai ka tafi wurin mutanen da zan aike ka,

8Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai, Zan kiyaye ka. Ni Ubangiji na faɗa.”

9Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini, “Ga shi, na sa maganata a bakinka.

10Ga shi, a wannan rana na ba ka iko a kan al'ummai da mulkoki, Don ka tumɓuke, ka rusar, Ka hallakar, ka kaɓantar, Ka gina, ka dasa.”

11Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?” Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”

12Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”

13Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Me kuma ka gani?” Na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, daga wajen arewa kamar za ta jirkice wajen kudu.”

14Sai Ubangiji ya ce mini, “Daga wajen arewa masifa za ta fito ta auka wa dukan mazaunan ƙasar. 15Ga shi kuwa, ina kiran dukan kabilan mulkokin arewa, za su kuwa zo su kafa gadajen sarautarsu a ƙofofin Urushalima, su kewaye dukan garukanta da dukan sauran biranen Yahuza. 16Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi. 17Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu. 18Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar. 19Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”

2

Ubangiji ya Ji da Isra'ila da Masu Ridda

1Ubangiji ya ce mini, 2in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba.

3Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji, Nunar fari ta girbina. Dukan waɗanda suka ci daga cikinki sun yi laifi, Masifa za ta auko miki. Ni Ubangiji, na faɗa.”

4Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila.

5Ubangiji ya ce, “Wane laifi ne na yi wa kakanninku, Da suka bar bina? Suka bauta wa gumaka marasa amfani, Su kuma suka zama marasa amfani.

6Ba su kula da ni ba, Ko da yake na cece su daga ƙasar Masar. Na bi da su a cikin hamada, A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai, Busasshiya mai yawan hatsari, Ba a bi ta cikinta, Ba wanda yake zama cikinta kuma.

7Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama.

8Firistoci kuma ba su ce, “‘Ina Ubangiji Yake ba?” Masanan shari'a ba su san ni ba. Masu mulki sun yi mini laifi, Annabawa sun yi annabci da sunan Ba'al, Sun bi waɗansu abubuwa marasa amfani.”

Shari'ar da Ubangiji yake Yi wa Mutanensa

9“Domin haka, ni Ubangiji zan gabatar da ku gaban shari'a, Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan 'ya'yanku, wato jikokinku.

10Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajen yamma, ku gani, Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, ku duba da kyau, A dā an taɓa yin wani abu haka>

11Akwai wata al'umma da ta taɓa sāke gumakanta Ko da yake su ba kome ba ne? Amma mutanena sun sauya darajarsu da abin da ba shi da rai.

12Sammai, ku girgiza saboda wannan, ku razana, Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.

13Mutanena sun yi zunubi iri biyu, Sun rabu da ni, ni da nake maɓuɓɓugar ruwan rai, Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa, hudaddu, Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.

14“Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kuma haife shi bawa ba, Amma me ya sa ya zama ganima>

15Zakuna suna ruri a kansa, Suna ruri da babbar murya. Sun lalatar da ƙasarsa, Garuruwansa sun lalace, Ba wanda yake zaune cikinsu.

16Mutanen Memfis kuma da na Tafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.

17Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kanka wannan, Da ka rabu da Ubangiji Allahnka, Sa'ad da ya bishe ka a hanya.

18Wace riba ka samu, har da ka tafi Masar, Don ka sha ruwan Kogin Nilu? Wace riba ka samu, har da ka tafi Assuriya, Don ka sha ruwan Kogin Yufiretis>

19Muguntarka za ta hore ka, Riddarka kuma za ta hukunta ka. Sa'an nan za ka sani, ka kuma gane, Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare ka Ka rabu da Ubangiji Allahnka, Ba ka tsorona a zuciyarka. Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na faɗa.”

Isra'ila ya Ƙi yi wa Ubangiji Biyayya

20“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, “‘Ba zan yi bauta ba.” Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace.

21Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi kyau. Ta yaya ka lalace haka ka zama rassan kurangar inabi ta jeji, Waɗanda ba zan yarda da su ba>

22Ko da za ka yi wanka da sabulun salo, Ka yi amfani da sabulu mai yawa, Duk da haka zan ga tabban zunubanka. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

23Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da kanka ba, Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba? Ka duba hanyarka ta zuwa cikin kwari, ka san abin da ka yi. Kana kama da taguwa, mai yawon neman barbara.

24Kamar jakar jeji kake, wadda take son barbara, Wadda take busar iska, Sa'ad da take son barbara, wa zai iya hana ta? Jakin da yake sonta, ba ya bukatar wahalar da kansa Gama a watan barbararta za a same ta.

25Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunka ba takalma, Kada kuma ka bar maƙogwaronka ya bushe. Amma ka ce, “‘Wannan ba amfani, Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa zan bi.”

26“Kamar yadda ɓarawo yakan sha kunya sa'ad da aka kama shi, Hakanan mutanen Isra'ila za su sha kunya, Da su, da sarakunansu, da shugabanninsu, Da firistocinsu, da annabawansu.

27Waɗanda suka ce wa itace, “‘Kai ne mahaifinmu.” Suna kuma ce wa dutse, “‘Kai, ka haife mu.” Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, “‘Ka zo ka taimake mu.”

28Ina gumakan da kuka yi wa kanku? Bari su tashi in sun iya cetonku lokacin wahalarku. Yahuza, yawan gumakanku sun kai Yawan garuruwanku.

29Ni Ubangiji, ina tambayarku, “‘Wace ƙara kuke da ita game da ni?” Kun yi mini tawaye dukanku.

30Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba su horu ba, Kun kashe annabawanku da takobi kamar mayunwacin zaki.

31Ya ku mutanen zamanin nan, ku saurari maganata. Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasar da take da kurama? Don me fa mutanena suke cewa, “‘Mu 'yantattu ne, Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba?”

32Budurwa ta manta da kayan kwalliyarta? Ko kuwa amarya ta manta da kayan adonta? Amma mutanena sun manta da ni kwanaki ba iyaka.

33Kun sani sarai yadda za ku yi ku farauci masoya, Har mugayen mata ma, kun koya musu hanyoyinku.

34Tufafinku sun ƙasantu da jinin marasa laifi, Waɗanda ba ku same su suna fasa gidajenku ba. Amma duk da haka kuna cewa,

35“‘Ba mu da laifi, hakika kuwa, Ubangiji bai yi fushi da mu ba.” Amma ni Ubangiji zan hukunta ku, Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.

36Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya, Sai ku yi nan ku yi can? Masar za ta kunyata ku kamar yadda Assuriya ta yi.

37Da hannuwanku a kā za ku komo daga Masar don kunya. Gama waɗanda kuke dogara gare su, ni Ubangiji, na ƙi su, Ba za ku yi arziki tare da su ba.”

3

1Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa.

2Ki ta da idonki, ki duba filayen tuddai ki gani, Akwai wurin da ba ki laɓe kin yi karuwanci ba? Kin yi ta jiran abokan sha'anin karuwancinki a kan hanya, Kamar Balaraben da ke fako a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da mugun karuwancinki.

3Saboda haka aka ƙi yin ruwa, Ruwan bazara bai samu ba. Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jin kunya.

4“Yanzu kin ce, “‘Kai ne mahaifina, Ka ƙaunace ni tun ina cikin ƙuruciyata.

5Za ka dinga yin fushi da ni? Za ka husata da ni har abada?” Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi, kin aikata dukan muguntar da kika iya yi.”

Dole Isra'ila da Yahuza su Tuba

6A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da ta yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta. 7Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar 'yar'uwarta, wato Yahuza, ta gani. 8Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci. 9Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa. 10Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”

11Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da ya ke Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba. 12Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce, “Ki komo ya Isra'ila, marar aminci, Ni Ubangiji, na faɗa. Domin ni mai jinƙai ne, Ba zan yi fushi da ke ba. Ba zan yi fushi da ke har abada ba, Ni, Ubangiji na faɗa.

13Ke dai ki yarda da laifinki, Da kika yi wa Ubangiji Allahnki, Kin kuma watsar da mutuncinki a wurin baƙi A gindin kowane itace mai duhuwa. Kika ƙi yin biyayya da maganata, Ni, Ubangiji, na faɗa.

14“Ku komo, ya ku mutane marasa aminci, Gama ni ne Ubangijinku. Zan ɗauki mutum guda daga kowane gari, In ɗauki mutum biyu daga kowane iyali, Zan komo da su zuwa Dutsen Sihiyona.

15Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi. 16Sa'ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. 17In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a'umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba. 18A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.

19“Isra'ila, na yi niyya in karɓe ku kamar ɗana, In gādar muku da kyakkyawar ƙasa Mafi kyau a dukan duniya. Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku, Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba.

20Hakika kamar yadda mace marar aminci takan bar mijinta, Haka kun zama marar aminci a gare ni, ya jama'ar Isra'ila. Ni Ubangiji, na faɗa.”

21An ji murya a kan filayen tuddai, Kūka da roƙo ne na 'ya'yan Isra'ila maza, Domin sun rabu da hanyarsu, Sun manta da Ubangiji Allahnsu.

22“Ku juyo ku marasa aminci, Zan warkar da rashin amincinku.” “To, ga shi, mun zo gare ka, Gama kai ne Ubangiji Allahnmu,

23Daga kan tuddai ba mu da wani taimako, Ko daga hayaniyar da ake yi a kan duwatsu, Daga wurin Ubangiji Allahnmu ne kaɗai taimakon Isra'ila yake fitowa.

24“Amma yin sujada ga gunkin nan Ba'al ya cinye mana amfanin wahalar da kakanninmu suka sha tun muna yara, wato na garkunan tumakinsu, da na awakinsu, da na shanunsu, da 'ya'yansu mata da maza. 25Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”

4

1Ubangiji ya ce, “Ya mutanen Isra'ila, idan za ku juyo ku komo wurina, Idan kuka kawar da abubuwan banƙyama daga gabana, Kuka kuma bar yin shakka,

2Idan kun yi rantsuwa kuka ce, “‘Har da ran Ubangiji kuwa,” Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”

3Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima, “Ku kafce saurukanku, Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.

4Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”

Yahuza tana cikin Barazanar Yaƙi

5“Ku yi shela a cikin Yahuza, Ku ta da murya a Urushalima, ku ce, “‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!” Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce, “‘Ku tattaru, mu shiga birane masu garu.”

6Ku ta da tuta wajen Sihiyona! Ku sheƙa a guje neman mafaka, kada ku tsaya! Gama zan kawo masifa da babbar halaka daga arewa.

7Zaki ya hauro daga cikin ruƙuƙinsa, Mai hallaka al'ummai ya kama hanya, Ya fito daga wurin zamansa don ya mai da ƙasarku kufai, Ya lalatar da biranenku, su zama kango, ba kowa.

8Domin haka sai ku sa tufafin makoki, Ku yi makoki ku yi kuka, Gama fushin Ubangiji bai rabu da mu ba.”

9Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”

10Sai na ce, “Kaito, kaito, ya Ubangiji Allah, ka ruɗi jama'an nan da Urushalima, da ka ce musu, “‘Za ku zauna lafiya,” amma ga shi, takobi zai sassare su.”

11Lokaci yana zuwa da za a faɗa wa mutanen Urushalima cewa, “Iska mai zafi za ta huro daga tuddan hamada zuwa wajen jama'ata, ba domin a sheƙe ta ko a rairaye ta ba! 12Wannan iska da za ta zo daga wurin Ubangiji, tana da mafificin ƙarfi. Yanzu fa zan yanke hukunci a kansu.”

Abokan Gāba sun Kewaye Yahuza da Yaƙi

13Duba, ga abokin gāba yana zuwa kamar gizagizai, Karusan yaƙinsa suna kama da guguwa, Dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaitonmu, mun shiga uku!

14Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, Domin a cece ki, Har yaushe mugayen tunaninki za su yi ta zama a cikinki>

15Gama wata murya daga Dan ta faɗa, Ta kuma yi shelar masifar da za ta fito daga duwatsun Ifraimu.

16“A faɗakar da al'ummai, yana zuwa, A faɗa wa Urushalima cewa, “‘Masu kawo mata yaƙi suna zuwa daga ƙasa mai nisa, Suna yi wa biranen Yahuza ihu.

17Za su kewaye Yahuza kamar masu tsaron saura, Saboda ta tayar wa Ubangiji.” Ni Ubangiji na faɗa.

18“Al'amuranki da ayyukanki suka jawo miki wannan halaka, Tana da ɗaci kuwa, Ta soki har can cikin zuciyarki.”

Irmiya ya yi Baƙin Ciki don Mutanensa

19Azaba! Ba zan iya daurewa da azaba ba! Zuciyata! Gabana yana faɗuwa da ƙarfi, Ba zan iya yin shiru ba, Gama na ji amon ƙaho da hargowar yaƙi.

20Bala'i a kan bala'i, Ƙasa duka ta zama kufai, An lalatar da alfarwaina, ba zato ba tsammani, Labulena kuwa farat ɗaya.

21Har yaushe zan yi ta ganin tuta, In yi ta jin amon ƙaho>

22Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”

23Da na duba duniya sai na ga kufai ce kawai ba kome, Na kuma dubi sammai sai na ga ba haske.

24Da na duba duwatsu, sai na ga suna makyarkyata, Dukan tuddai kuma suna rawar jiki, su yi gaba su yi baya.

25Na duba sai na ga ba ko mutum ɗaya, Dukan tsuntsaye kuma sun tsere.

26Na duba, sai na ga ƙasa mai dausayi ta zama hamada, An mai da dukan biranenta kangwaye A gaban Ubangiji saboda zafin fushinsa.

27Gama Ubangiji ya ce, “Ƙasar duka za ta zama kufai, amma duk da haka, ba wannan ne zai zama ƙarshenta na har abada ba.

28Duniya za ta yi makoki saboda wannan, Sammai za su duhunta, Gama ni na faɗa, haka kuwa na nufa in yi, Ba zan ji tausayi ba, Ba zan kuwa fāsa ba.”

29Da jin motsin mahayan dawakai da na maharba Kowane gari zai fashe. Waɗansu za su shiga kurama, Waɗansu kuma su hau kan duwatsu. Dukan birane za su fashe tas, Ba wanda zai zauna a cikinsu.

30Ya ke da kike kufai marar kowa, Me kike nufi da kika ci ado da mulufi, Kike caɓa ado da kayan zinariya, Kika sa wa idanunki tozali ram? Kin yi kwalliyarki a banza, Abokan sha'anin karuwancinki sun raina ki, Ranki suke nema.

31Na ji kuka kamar na mace wadda ke naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”

5

Zunubin Urushalima da Yahuza

1“Ku bi titunan Urushalima ko'ina! Ku dudduba ku lura! Ku bincika kowane dandali, ku gani, Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya Mai aikata adalci, mai son gaskiya, Sai in gafarta mata.

2Ko da ya ke suna cewa, “‘Na rantse da ran Ubangiji,” Duk da haka rantsuwar ƙarya suke yi.”

3Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.

4Sai na ce, “Waɗannan mutane ba su da kirki, Ba su da hankali, Ba su san hanyar Ubangiji, Ko shari'ar Allahnsu ba.

5Zan tafi wurin manyan mutane, in yi musu magana, Gama sun san nufin Ubangiji, da shari'ar Allahnsu.” Amma dukansu sun ƙi yarda Ubangiji ya mallake su, Suka ƙi yi masa biyayya.

6Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.

7“Don me zan gafarce ki? 'Ya'yanki sun rabu da ni, Sun yi rantsuwa da gumaka, Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai, Suka yi karuwanci, suka ɗunguma zuwa gidajen karuwai,

8Kamar ƙosassun ingarmu suke, masu jaraba, Kowa yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.

9Ba zan hore su saboda waɗannan abubuwa ba? Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wa kaina fansa a kan wannan al'umma ba>

10Ku haura, ku lalatar da gonar kurangar inabinta, Amma kada ku yi mata ƙarƙaf, Ku sassare rassanta, Gama su ba na Ubangiji ba ne.

11Gama mutanen Isra'ila da mutanen Yahuza Sun zama marasa aminci a gare ni. Ni Ubangiji na faɗa.”

12Sun yi ƙarya a kan Ubangiji, Suka ce, “Ba abin da zai yi, Ba wata masifa da za ta same mu. Ba kuwa za mu ga takobi ko yunwa ba.

13Annabawa holoƙo ne kawai, Maganar ba ta cikinsu. Haka za a yi da su!”

Urushalima tana gab da Faɗuwa

14Saboda haka Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Domin sun hurta wannan magana, Ga shi, zan sa maganata a bakinka ta zama wuta, Waɗannan mutane kuwa su zama itace, Wutar za ta cinye su.

15“Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, ina kawo muku Wata al'umma daga nesa,” in ji Ubangiji, “Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tun zamanin dā. Al'umma wadda ba ku san harshenta ba, Ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.

16Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne, Dukansu jarumawa ne.

17Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku. Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza. Za su cinye garkunanku na tumaki, da na awaki, da na shanu, Za su kuma cinye 'ya'yan inabinku da na ɓaurenku. Za su hallaka biranenku masu kagara da takobi, waɗanda kuke fariya da su.

18“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji. 19“Sa'ad da mutanenki suka ce, “‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?” Sai ki ce musu, “‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.”

20“Ka sanar wa zuriyar Yakubu da wannan, Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, ka ce,

21“‘Ku ji wannan, ya ku wawaye, marasa hankali, Kuna da idanu, amma ba ku gani, Kuna da kunnuwa, amma ba ku ji.”

22Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da ya ke raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.

23Amma mutanen nan suna da taurin zuciya, masu halin tayarwa ne, Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.

24A zuciya ba su cewa, “‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu Wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari, Na kaka da na bazara, Wanda yake ba mu lokacin girbi.”

25Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa. Zunubanku kuma sun hana ku samun alheri.

26“Gama an sami mugaye, a cikin jama'ata, Suna kwanto kamar masu kafa ashibta. Sun ɗana tarko su kama mutane.

27Kamar kwando cike da tsuntsaye, Hakanan gidajensu ke cike da cin amana, Don haka suka zama manya, suka sami dukiya.

28Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul, Ba su da haram a kan aikata mugunta, Ba su yi wa marayu shari'ar adalci, don kada su taimake su. A wajen shari'a ba su bin hakkin matalauta.

29“Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba>

30“Abin banmamaki da bantsoro Ya faru a ƙasar.

31Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”

6

Ajalin Urushalima da Yahuza

1“Ya ku mutanen Biliyaminu, ku gudu neman mafaka, Daga cikin Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa, Ku ba da alama a Bet-akkerem, Gama masifa da babbar halaka sun fito daga arewa.

2Ya Sihiyona, ke kyakkyawar makiyaya ce, zan hallaka abin da kika hahhaifa.

3Makiyaya da garkunansu za su zo wurinki, Za su kafa alfarwansu kewaye da ke, Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.

4Za su ce, “‘Mu yi shiri mu fāɗa mata da yaƙi! Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakar rana!” Sai kuma suka ce, “‘Kaitonmu, ga rana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.

5Mu tashi mu fāɗa mata da dare, Mu lalatar da fādodinta.”

6Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku sassare itatuwanta, Ku tula ƙasa kewaye da Urushalima, Dole in hukunta wannan birni saboda ba kome cikinsa sai zalunci,

7Kamar yadda rijiya take da ruwa garau, Haka Urushalima take da muguntarta, Ana jin labarin kama-karya da na hallakarwa a cikinta, Kullum akwai cuce-cuce, da raunuka a gabana,

8Ku ji faɗaka, ya ku mutanen Urushalima, Don kada a raba ni da ku, Don kada in maishe ku kufai, Ƙasar da ba mazauna ciki.”

9Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Za a kalace ringin Isra'ila sarai, kamar yadda ake wa inabi, Ka miƙa hannunka a kan rassanta kamar mai tsinkar 'ya'yan inabi.”

10Da wa zan yi magana don in faɗakar da shi, don su ji? Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su ji, Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta zama abin ba'a a gare su, Ba su marmarinta. 11-12Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da ke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.

13Gama daga ƙaraminsu zuwa babba, Kowannensu yana haɗama ya ci ƙazamar riba, Har annabawa da firistoci, Kowannensu ya shiga aikata rashin gaskiya.

14Sun warkar da raunin mutanena sama sama, Suna cewa, “‘Lafiya, Lafiya,” alhali kuwa ba lafiya.

15Sun ji kunya sa'ad da suka aikata abubuwan banƙyama? Ba su ji kunya ba ko kaɗan. Ko gezau ba su yi ba, Don haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a hamɓarar da su. Ni Ubangiji na faɗa.”

16Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, “‘Ai, ba za mu bi ta ba.”

17Na sa muku matsara cewa, in kun ji an busa ƙaho ku kula! Amma suka ce, “‘Ba za mu kula ba.”

18“Don haka, ku ji, ya ku al'ummai, Ku sani, ku taron jama'a, Don ku san abin da zai same ku.

19Ki ji, ya ke duniya, Ga shi, ina kawo masifa a kan wannan jama'a, Sakayyar ƙulle-ƙullensu, Don ba su kula da maganata ba, Sun ƙi dokokina.

20Da wane nufi kuke kawo mini turare daga Sheba, Ko raken da kuke kawowa daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba, Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinku ba.

21Don haka, ni Ubangiji na ce, Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannan jama'a, Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi. Iyaye tare da 'ya'yansu, da maƙwabci, Do abokansu za su lalace.”

22Haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, jama'a tana fitowa daga ƙasar arewa. Babbar al'umma ce, Ta yunƙuro tun daga manisantan wurare na duniya.

23Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi, Motsinsu kamar ƙugin teku ne. Suna haye a kan dawakai, A jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi Gāba da ke, ya 'yar Sihiyona.”

24Mutanen Urushalima sun ce, “Mun ji labarin yaƙin, Hannuwanmu suka yi rauni. Azaba ta kama mu, Ciwo irin na mai naƙuda.

25Kada ku fita zuwa gona, Kada kuma ku yi yawo a kan hanya, Gama abokin gāba yana da takobi, Razana a kowane sashi.”

26“Ya mutanena, ku sa tufafin makoki, Ku yi birgima cikin toka, Ku yi makoki mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, Gama mai hallakarwa zai auko mana nan da nan.”

27Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Na maishe ka mai aunawa da mai jarraba mutanena Domin ka sani, ka auna al'amuransu,

28Su duka masu taurinkai ne, 'yan tawaye, Suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da baƙin ƙarfe, Dukansu lalatattu ne.

29Ana zuga da ƙarfi, Dalma ta ƙone, Tacewar aikin banza ne, Gama ba a fitar da mugaye ba.

30Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfa ne, Gama ni na ƙi su.”

7

Ku Gyara Hanyoyinku da Ayyukanku

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce, 2“Ka tafi ka tsaya a ƙofar Haikalin Ubangiji, ka yi shelar wannan magana, ka ce, su kasa kunne ga maganar Ubangiji, dukansu mutanen Yahuza, su da suke shiga ta ƙofofin nan don su yi wa Ubangiji sujada! 3Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, “‘Ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, ni kuwa zan ƙyale ku, ku zauna a wannan wuri. 4Kada ku amince da maganganun nan na ruɗarwa, cewa wannan shi ne Haikalin Ubangiji. Wannan shi ne Haikalin Ubangiji, wannan shi ne Haikalin Ubangiji!

5“‘Idan dai kun gyara hanyoyinku, da ayyukanku bisa kan gaskiya, idan da gaskiya kuke aikata adalci ga junanku, 6idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka, 7sa'an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.

8“‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani. 9Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba? 10Sa'an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama? 11Wannan Haikali wanda ake kira da sunana ya zama kogon mafasa a idanunku. Ga shi, ni da kaina na gani,” in ji Ubangiji. 12“‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra'ila. 13Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al'amura, sa'ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa'ad da na kira ku, ba ku amsa ba, 14domin haka zan yi wa Haikali wanda ake kira da sunana, wanda kuma kuka amince da shi, da kuma wurin da na ba ku, ku da kakanninku, kamar yadda na yi wa Shilo. 15Zan kore ku daga gabana kamar yadda na yi wa dukan 'yan'uwanku, dukan zuriyar Ifraimu.”

Fushin Allah a kan Bin Gumaka

16“Kai kuwa, Irmiya kada ka yi wa mutanen nan addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba. 17Ba ka ga abin da suke yi a biranen Yahuza da titunan Urushalima ba? 18Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.” 19In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?” 20Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”

Horon Yahuza saboda Tayarwa

21Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ku ba da hadayunku na ƙonawa da na sadakarku, ku ci naman. 22A ranar da na fito da kakanninku daga ƙasar Masar, ban yi magana da su, ko na umarce su, a kan hadayun ƙonawa da na sadaka ba. 23Amma na umarce su su yi biyayya da maganata, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena, su bi dukan al'amuran da na umarce su, domin lafiyarsu, don su zama lafiya. 24Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba. 25Tun daga ran da kakanninku suka fito ƙasar Masar, har zuwa yau na yi ta aika musu da dukan bayina annabawa kowace rana. 26Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.

27“Saboda haka za ka faɗa musu waɗannan abubuwa duka, amma ba za su ji ka ba. Za ka kira su, amma ba za su amsa ba. 28Za ka faɗa musu ka ce, wannan ita ce al'ummar da ba ta yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnta ba, ba ta karɓi horo ba. Gaskiya kuma ta ƙare sam, ba ta a bakinsu.

29“Ku aske gashin kanku, ku zubar da shi. Ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi 'yan zamanin nan, ya rabu da su saboda fushinsa. 30Ni Ubangiji, na faɗa, cewa mutanen Yahuza sun yi mugun abu a gabana. Suna ajiye gumakansu a Haikalina, sun ƙazantar da shi. 31A cikin kwarin ɗan Hinnon sun gina bagade, mai suna Tofet, don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadayar ƙonawa. Ni ban umarce su su yi haka ba, irin wannan abu ba shi a zuciyata. 32Domin haka, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa lokacin da ba za a ƙara faɗar Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a kira shi Kwarin Kisa, gama za a binne mutane a Tofet domin ba sauran wuri a ko'ina. 33Gawawwakin mutanen nan za su zama abincin tsuntsaye da na namomin jeji, ba wanda zai kore su. 34Zan sa muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya su ƙare a biranen Yahuza da titunan Urushalima, gama ƙasar za ta zama kufai.”

8

1“Ni Ubangiji na faɗa, cewa a wancan lokaci, za a fitar da ƙasusuwa daga kaburburan sarakunan Yahuza, da na sarakansu, da na firistoci, da na annabawa, da na mazaunan Urushalima. 2Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa. 3Sauran mutanen muguwar tsaran nan waɗanda ke a wuraren da na warwatsa su, za su fi son mutuwa fiye da rayuwa. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Zunubi da Hukunci

4“Ka faɗa musu, ka ce, ni Ubangiji na ce, “‘Wanda ya fāɗi ba zai sāke tashi ba? Idan wani ya kauce ba zai komo kan hanya ba>

5Me ya sa, mutanen nan na Urushalima suke ratsewa, suke komawa baya kullayaumin? Sun riƙe ƙarya kan-kan Sun ƙi komowa.

6Na kula sosai, na saurara, Amma ba wanda ya faɗi wata maganar kirki, Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa, Kowa cewa yake, “Me na yi?” Kamar dokin da ya kutsa kai cikin fagen fama.

7Ko shamuwa ta sararin sama ma, ta san lokatanta, Tattabara da tsattsewa, da gauraka suna kiyaye lokacin komowarsu. Amma mutanena ba su san dokokina ba.

8“‘Ƙaƙa za ku ce, “Muna da hikima, Dokar Ubangiji tana tare da mu?” Ga shi kuwa, alkalamin ƙarya na magatakarda, ya yi ƙarya.

9Za a kunyatar da masu hikima. Za su tsorata, za a kuma tafi da su. Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji. Wace hikima suke da ita>

10Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu, Gonakinsu kuma ga waɗanda suke cinsu da yaƙi, Saboda tun daga ƙarami har zuwa babba Kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba, Tun daga annabawa zuwa firistoci Kowannensu aikata ha'inci yake yi.

11Sun warkar da raunin mutanena sama sama, Suna cewa, “Lafiya, lafiya,” alhali kuwa ba lafiya.

12Ko sun ji kunya Sa'ad da suka aikata ayyuka masu banƙyama? A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan, Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba. Domin haka za su faɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a ci su da yaƙi. Ni Ubangiji na faɗa.”

13“Ni Ubangiji na ce, “‘Sa'ad da zan tattara su kamar amfanin gona, Sai na tarar ba 'ya'ya a kurangar inabi, Ba 'ya'ya kuma a itacen ɓaure, Har ganyayen ma sun bushe. Abin da na ba su kuma ya kuɓuce musu. Ni Ubangiji na faɗa.”

14Mutanen Urushalima sun ce, “Don me muke zaune kawai? Bari mu tattaru, mu tafi cikin garuruwa masu garu, Mu mutu a can, Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa, Ya ba mu ruwan dafi, Domin mun yi masa laifi.

15Mun sa zuciya ga salama, amma ba lafiya, Mun sa zuciya ga lokacin samun warkewa, Amma sai ga razana!

16Daga Dan, an ji firjin dawakai. Dakan ƙasar ta girgiza saboda haniniyar ingarmunsu. Sun zo su cinye ƙasar duk da abin da ke cikinta, Wato da birnin da mazauna cikinsa.”

17“Ni Ubangiji na ce, “‘Zan aiko muku da macizai, da kāsā, Waɗanda ba su da makari, Za su sassare ku.”

18Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa, Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!

19Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”

20Mutane suna ta cewa, “Damuna ta ƙare, kaka kuma ta wuce, Amma ba a cece mu ba.”

21Raunin da aka yi wa jama'ata, Ya yi wa zuciyata rauni. Ina makoki, tsoro kuma ya kama ni ƙwarai.

22Ba abin sanyayawa a Gileyad ne? Ba mai magani a can ne? Me ya sa ba a warkar da jama'ata ba>

9

1Da ma kaina ruwa ne kundum, Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne, Da sai in yi ta kuka dare da rana, Saboda an kashe jama'ata!

2Da ma ina da wurin da zan fake a hamada, Da sai in rabu da mutanena, in tafi can! Gama dukansu mazinata ne, Ƙungiyar mutane maciya amana.

3Ubangiji ya ce, “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, Ƙarya ce take rinjayar gaskiya a ƙasar. Suna ta cin gaba da aikata mugunta, Ba su kuwa san ni ba.

4“Bari kowane mutum ya yi hankali da maƙwabcinsa, Kada kuma ya amince da kowane irin ɗan'uwa, Gama kowane ɗan'uwa munafuki ne, Kowane maƙwabci kuma mai kushe ne.

5Kowane mutum yana ruɗin maƙwabcinsa da abokinsa, Ba mai faɗar gaskiya, Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya. Suna aikata laifi, Sun rafke, sun kasa tuba.

6Suna ƙara zalunci a kan zalunci, Yaudara a kan yaudara, Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.

7Saboda haka, Ubangiji Mai Runduna, ya faɗa cewa, “Zan tsabtace su, in gwada su, Gama me zan yi kuma saboda jama'ata>

8Harshensu kibiya ce mai dafi, yana faɗar ƙarya, Kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa Amma a zuciyarsa yana shirya masa maƙarƙashiya.

9Ba zan hukunta su saboda waɗannan al'amura ba? Ba zan sāka wa al'umma irin wannan ba?”

10Zan yi kuka in yi kururuwa saboda tsaunuka, Zan yi kuka saboda wuraren kiwo, Domin sun bushe sun zama marasa amfani. Ba wanda yake bi ta cikinsu. Ba a kuma jin kukan shanu, Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu sun tafi.

11“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Urushalima tsibin kufai, Wurin zaman diloli, Zan kuma mai da biranen Yahuza kufai, inda ba kowa.”

Za a Rushe Birni a Kai su Zaman Talala

12Wa ke da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda ke iya ratsa ta, kamar hamada>

13Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba. 14Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu. 15Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi. 16Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.

17“Haka ni Ubangiji Mai Runduna na ce, Ku yi tunani, ku kirawo mata masu makoki su zo, Ku aika wa gwanaye fa.”

18Jama'a suka ce, “Su gaggauta, su ta da murya, Su yi mana kuka da ƙarfi, Har idanunmu su cika da hawaye, Giranmu kuma su jiƙe sharaf.

19“Gama ana jin muryar kuka daga Sihiyona cewa, “‘Ga yadda muka lalace! Aka kunyatar da mu ɗungum! Don mun bar ƙasar, domin sun rurrushe wuraren zamanmu.”

20Irmiya ya ce, “Ya ku mata, ku ji maganar Ubangiji, Ku kasa kunne ga maganar da ya faɗa, Ku koya wa 'ya'yanku mata kukan makoki, Kowacce ta koya wa maƙwabciyarta waƙar makoki,

21Gama mutuwa ta shiga tagoginmu, Ta shiga cikin fādodinmu, Ta karkashe yara a tituna, Ta kuma karkashe samari a dandali.

22Ubangiji ya ce mini, “‘Ka yi magana, cewa gawawwakin mutane za su fāɗi tuli Kamar juji a saura, Kamar dammunan da masu girbi suka ɗaura, Ba wanda zai tattara su.”

23Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa. 24Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”

25Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa sa'ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya, 26da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda ke zaune a hamada, da waɗanda ke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”

10

Gumaka da Allah na Gaskiya

1Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku. 2Ubangiji ya ce, “Kada ku koyi abubuwan da al'ummai suke yi, Kada ku ji tsoron alamun da ke a sama, Ko da ya ke al'ummai suna jin tsoronsu.

3Gama al'adun mutane na ƙarya ne, Daga cikin jeji aka sare wani itace, Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi da gizago.

4Mutane sukan yi masa ado na azurfa da zinariya, Sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, Don kada ya motsa.

5Gumakansu dodon gona suke, a cikin gonar kabewa, Ba su iya yin magana, Ɗaukarsu ake yi domin ba su iya tafiya! Kada ku ji tsoronsu. Gama ba su da ikon aikata mugunta ko alheri.”

6Ya Ubangiji, ba wani kamarka, Kai mai girma ne, Sunanka kuma yana da girma da iko.

7Wanene ba zai ji tsoronka ba, ya Sarkin dukan al'ummai? Ka isa a ji tsoronka, Gama babu kamarka a cikin dukan masu hikima na al'ummai, Da kuma cikin dukan mulkokinsu, Ba wani kamarka.

8Dukansu dakikai ne wawaye, Koyarwar gumaka ba wani abu ba ne, itace ne kawai!

9An kawo fallayen azurfa daga Tarshish, Da zinariya kuma daga Ufaz, Aikin gwanaye da maƙeran zinariya. Tufafinsu na mulufi ne da shunayya, duka aikin gwanaye.

10Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.

11Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”

12Shi ne, ta wurin ikonsa ya yi duniya, Ta wurin hikimarsa ya kafa ta, Ta wurin basirarsa kumaya ya shimfiɗa sammai.

13Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin ruwa a cikin sammai Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar duniya, Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan sama, Daga cikin taskokinsa yakan kawo iska.

14Kowane mutum dakiki ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa, Gama siffofinsa ƙarya ne, Ba numfashi a cikinsu.

15Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne, A lokacin da za a hukunta su za su lalace.

16Gama shi ba kamar waɗannan yake ba, Shi na Yakubu ne. Shi ne ya yi dukan kome, Kabilan Isra'ilawa gādonsa, Sunansa Ubangiji Mai Runduna.

Risɓewar Yahuza

17Ku tattara kayayyakinku, Ku mazaunan wurin da aka kewaye da yaƙi.

18Gama haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, ina jefar da mazaunan ƙasar daga ƙasarsu a wannan lokaci, Zan kawo musu wahala, za su kuwa ji jiki.”

19Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini. Raunina mai tsanani ne, Amma na ce, lalle wannan azaba ce, Tilas in daure da ita.

20An lalatar da alfarwata, Dukan igiyoyi sun tsintsinke, 'Ya'yana maza sun bar ni, ba su nan. Ba wanda zai kafa mini alfarwata Ya kuma rataya labulena.

21Makiyayan dakikai ne, Ba su roƙi Ubangiji ba, Don haka ba su sami wadata ba, An watsa dukan garkensu.

22Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shi kuma, yana tafe. Akwai babban hargitsin da ya fito daga arewa, Don a mai da biranen Yahuza kufai, wurin zaman diloli.

23“Ya Ubangiji, na sani al'amuran mutum ba a hannunsa suke ba, Ba mutum ne ke kiyaye takawarsa ba

24Ka tsauta mini, ya Ubangiji, amma da adalcinka, Ba da fushinka ba, don kada ka wofinta ni.

25Ka kwarara hasalarka a kan sauran al'umma da ba su san ka ba, Da a kan jama'ar da ba su kiran sunanka, Gama sun cinye Yakubu, Sun cinye shi, sun haɗiye shi, Sun kuma mai da wurin zamansa kufai.”

11

An Ta da Alkawari

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya cewa, 2“Ka ji maganar wannan alkawari, sa'an nan ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. 3Ka faɗa musu cewa, “‘In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, la'ananne ne wanda bai kula da maganar alkawarin nan ba. 4Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu. 5Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda ke cike da albarka kamar yadda yake a yau.” Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”

6Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuza da titunan Urushalima duka, cewa su ji maganar alkawarin nan, su aikata. 7Lokacin da na fito da kakanninsu daga ƙasar Masar na faɗakar da su musamman, na yi ta faɗakar da su har wannan rana, ina cewa, “‘Ku yi biyayya da maganata.” 8Amma duk da haka ba su yi biyayya ba, ba su kuma kasa kunne ba. Kowa ya bi tattaurar zuciyarsa mai mugunta. Domin haka na kawo musu dukan maganar alkawarin nan wanda na umarce su su yi, amma ba su yi ba.”

9Ubangiji ya kuma ce mini, “Akwai tawaye a cikin mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. 10Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama'ar Isra'ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu. 11Saboda haka ni Ubangiji na ce, “‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba. 12Sa'an nan biranen Yahuza da mazaunan Urushalima za su tafi, su yi kuka ga gumaka waɗanda suka ƙona musu turare, amma ba za su iya cetonsu a lokacin wahalarsu ba. 13Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba'al turare ne.” 14Don haka kada ka yi wa waɗannan mutane addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, gama ba zan kasa kunne gare su ba, ko da sun yi kirana a lokacin wahalarsu.”

15Ubangiji ya ce, “Wane iko ƙaunatacciyata take da shi cikin Haikalina, da ya ke ta aikata mugayen ayyuka? Ko alkawarai da naman hadayu za su iya kawar miki da ƙaddararki, har da za ki yi taƙama? 16Dā na kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakkyawa, mai kyawawan 'ya'ya, amma da ƙugin babbar iska za a cinna miki wuta, za ta kuwa cinye rassanki.”

17Ubangiji Mai Runduna, wanda ya dasa ku, ya hurta masifar da za ta same ku saboda muguntar da mutanen Isra'ila da na Yahuza suka yi, suka tsokane ni in yi fushi saboda suna ƙona wa Ba'al turare.

An Shirya Maƙarƙashiya don a Kashe Irmiya

18Ubangiji ya sanasshe ni, Na kuwa sani, Sa'an nan ya nuna mini mugayen ayyukansu.

19Amma ina kama da lafiyayyen ɗan rago, Wanda aka ja zuwa mayanka, Ashe, ni suke ƙulla wa munafuncin! Ni kuwa ban sani ba, da suke cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da 'ya'yansa. Bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, Har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”

20Amma ya Ubangiji Mai Runduna, mai shari'ar adalci, Kakan gwada zuciya da tunani, Ka yarda mini in ga sakayyar da za ka yi mini a kansu, Gama a gare ka na danƙa maganata.

21Saboda haka ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka, da suka ce, “Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji, in ba haka ba, da hannunmu za mu kashe ka.” 22Domin haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga shi kuwa, zan hukunta su, za a kashe samarinsu da takobi, 'ya'yansu mata da maza, yunwa za ta kashe su. 23Ba wanda zai ragu daga cikin mutanen Anatot, gama zan kawo wa mutanen Anatot masifa, a shekarar hukuncinsu.”

12

Fatawar Irmiya da Amsar Ubangiji

1Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye ke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba>

2Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa, Suna girma, suna kuma ba da 'ya'ya, Sunanka na a cikin bakinsu, amma kana nesa da zuciyarsu.

3Amma kai, ya Ubangiji, kana sane da ni, kana ganina, Kai kanka kake gwada tunanina. Ka jawo su kamar tumaki zuwa mayanka, Ka ware su domin ranar yanka.

4Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”

5Ubangiji ya ce, “Idan kai da mutane kun yi tseren ƙafa sun gajiyar da kai, Yaya za ka iya gāsa da dawakai? Idan ka fāɗi a lafiyayyiyar ƙasa, Ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun>

6Gama har da 'yan'uwanka da gidan mahaifinka, Sun ci amanarka, Suna binka da kuka, Kada ka gaskata su, Ko da ya ke suna faɗa maka maganganu masu daɗi.”

7Ubangiji ya ce, “Na bar jama'ata. Na rabu da gādona, Na ba da wanda raina ke ƙauna a hannun maƙiyansa.

8Abin gādona ya zama mini kamar zaki a cikin kurmi, Ya ta da murya gāba da ni, Domin haka na ƙi shi.

9Ashe, abin gadon nan nawa ya zama dabbare-dabbaren tsuntsun nan ne mai cin nama? Tsuntsaye masu cin nama sun kewaye shi? Tafi, ka tattaro namomin jeji, Ka kawo su su ci.

10Makiyaya da yawa sun lalatar da gonar inabina. Sun tattake nawa rabo, Sun mai da nawa kyakkyawan rabo kufai da hamada.

11Sun maishe shi kufai, ba kowa, Yana makoki a gare ni, Ƙasar duka an maishe ta kufai, Amma ba wanda zuciyarsa ta damu a kan wannan.

12A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.

13Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”

14Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu. 15Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa. 16Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, “‘Da zatin Ubangiji,” kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata. 17Amma idan wata al'umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”

13

Misali da Abin Ɗamara

1Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, ya ce, “Tafi ka sayo lilin na yin ɗamara, ka sha ɗamara da shi kada kuwa ka tsoma shi a ruwa.” 2Sai na sayo abin ɗamara kamar yadda Ubangiji ya ce, na sha ɗamara da shi. 3Ubangiji kuma ya sāke yin magana da ni sau na biyu, 4ya ce, “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi Kogin Yufiretis, ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.” 5Sai na tafi, na ɓoye shi a Yufiretis kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.

6Bayan an ɗan daɗe, sai Ubangiji ya ce mini, “Tashi, ka tafi Yufiretis, ka ɗauko abin ɗamara wanda na umarce ka ka ɓoye a can.” 7Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.

8Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 9“Haka zan lalatar da alfarmar Yahuza da yawan alfarmar Urushalima. 10Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani. 11Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra'ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama'a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”

Misali da Tulun Ruwan Inabi

12“Sai ka faɗa musu wannan magana cewa, “‘Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, a cika kowane tulu da ruwan inabi.” Su kuwa za su ce maka, sun sani sarai za a cika kowane tulu da ruwan inabi. 13Sa'an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, “‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima. 14Zan sa su kara da junansu, iyaye maza da 'ya'yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi, ko juyayi, ko jinƙai ba za su sa in fasa hallaka su duka ba.”

Yahuza bai Tuba ba, za a Kai shi Zaman Talala

15Ku kasa kunne, ku ji, Kada ku yi girmankai, gama Ubangiji ya yi magana.

16Ku girmama Ubangiji Allahnku, Kafin ya kawo duhu, Kafin kuma ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan dutse, da duhu duhu, Sa'ad da kuke neman haske, sai ya maishe shi duhu, Ya maishe shi duhu baƙi ƙirin.

17Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.

18Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Ka faɗa wa sarki da sarauniya, uwarsa, su sauka daga gadon sarautarsu, Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin sarautarsu daga kansu.

19An kulle biranen Negeb, Ba wanda zai buɗe su, Yahuza duka an kai ta zaman dole, Dukanta an kai ta zaman dole.

20“Ku ta da idanunku, ku ga waɗanda ke zuwa daga arewa! Ina kyakkyawan garken nan da aka ba ku>

21Me za ku ce sa'ad da aka naɗa muku shugabanni, Waɗanda ku da kanku kuka koya musu, suka zama abokanku? Ashe, azabai ba za su auko muku ba Kamar yadda sukan auko wa mace mai naƙuda>

22Idan kun ce a zuciyarku, “‘Me ya sa waɗannan abubuwa suka same mu?” Saboda yawan zunubanku ne, Shi ya sa an tone tsiraicinku, Aka wahalshe ku.

23Mutumin Habasha zai iya sāke launin fatar jikinsa? Ko kuwa damisa za ta iya sāke dabbare-dabbarenta? Idan haka ne, ku kuma za ku iya yin nagarta, Ku da kuka saba da yin mugunta.

24Zan warwatsar da ku Kamar yadda iskar hamada ke watsar da ƙaiƙayi.”

25Ubangiji ya ce, “Wannan shi ne rabonku, Rabon da na auna muku, ni Ubangiji na faɗa. Domin kun manta da ni, kun dogara ga ƙarairayi,

26Ni kaina kuma zan kware muku suturarku ta rufe fuskarku Don a ga tsiraicinku.

27Na ga abubuwanku masu banƙyama, Wato zinace-zinacenku, da haniniya kamar dawakai, Da muguwar sha'awarku ta karuwanci a kan tuddai da filaye, Ya Urushalima, taki ta ƙare! Har yaushe za a tsarkake ki?”

14

Babban Fari

1Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,

2“Yahuza tana makoki, Ƙofofin biranenta suna lalacewa, Mutanenta suna kwance a ƙasa, suna makoki, Urushalima tana kuka da babbar murya.

3Manyan mutanenta sun aiki barorinsu su ɗebo ruwa. Da suka je maɓuɓɓuga, sai suka tarar ba ruwa. Sai suka koma da tulunansu hakanan, An kunyatar da su, an ƙasƙantar da su, Suka lulluɓe kansu don kunya.

4Saboda ƙasar ta bushe, Tun da ba a yi ruwa a kanta ba, Manoma sun sha kunya, Suka lulluɓe kansu don kunya.

5Barewa ma a saura takan gudu, Ta bar ɗanta sabon haihuwa, Domin ba ciyawa.

6Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddan da ba ciyawa, Suna haki kamar diloli, Idanunsu ba su gani Domin ba abinci.”

7Irmiya ya ce, “Ko da ya ke zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.

8Ya kai, wanda kake begen Isra'ila, Mai Cetonta a lokacin wahala, Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar? Kamar matafiyi wanda ya kafa alfarwarsa a gefen hanya don ya kwana, ya wuce>

9Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai san abin da zai yi ba, Kamar jarumin da ya kasa yin ceto? Duk da haka, ya Ubangiji, kana nan a tsakiyarmu. Da sunanka ake kiranmu, Kada ka bar mu!”

10Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”

11Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan. 12Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”

13Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ga shi, annabawa sun faɗa musu, sun ce, “‘Ba za ku ga takobi ko yunwa ba, amma zan ba ku dawwamammiyar salama a wannan wuri.”

14Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai. 15Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da ke yin annabci da sunana, ko da ya ke ban aike su ba, waɗanda suke cewa, “‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.” Za a hallaka su da takobi da yunwa. 16Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.

17“Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin ciki da ya same ka, Ka ce, “‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana, Kada su daina, saboda an buge budurwa, 'yar jama'ata, An yi mata babban rauni da dūka mai tsanani.

18Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda ke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.”

Mutane Sun Roƙi Ubangiji

19“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.

20Mun san muguntar da muka yi, ya Ubangiji, Da wadda kakanninmu suka yi, Gama mun yi maka zunubi.

21Saboda darajar sunanka, kada ka wulakanta mu, Kada kuma ka ƙasƙantar da darajar kursiyinka, Ka tuna da alkawarin da ka yi mana, Kada ka ta da shi.

22A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”

15

Fushin Ubangiji da Yahuza bai Huce Ba

1Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu! 2Sa'ad da suka tambaye ka, “‘Ina za mu tafi?” Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, “‘Waɗanda suke na annoba, su tafi ga annoba! Waɗanda suke na takobi, su tafi ga takobi! Waɗanda suke na yunwa, su tafi ga yunwa! Waɗanda suke na bauta, su tafi ga bauta!”

3Zan sa musu masu hallakarwa huɗu,” in ji Ubangiji, “Da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar. 4Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.

5“Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi baƙin ciki dominki? Wa kuma zai ratso wurinki don ya tambayi lafiyarki>

6Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna ta komawa da baya, Don haka na nuna ikona gāba da ku, na hallaka ku, Na gaji da jin tausayinku!

7Na sheƙe su da abin sheƙewa a ƙofofin garuruwan ƙasar. Na sa 'ya'yansu su mutu, na hallaka mutanena, Ba su daina yin mugayen ayyukansu ba.

8Na yawaita gwauraye, wato mata da mazansu suka mutu, Fiye da yashin teku. Na kawo wa uwayen samari mai hallakarwa da tsakar rana. Na sa azaba da razana su auka musu farat ɗaya.

9Ita wadda ta haifi 'ya'ya bakwai ta yi yaushi ta suma, Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba, An kunyatar da ita, an wulakantar da ita. Waɗanda suka ragu daga cikinsu Zan bashe su ga takobi gaban abokan gābansu. Ni Ubangiji na faɗa.”

10Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina. 11Ubangiji ya ce mini, “Zan keɓe ka domin alheri, hakika zan sa abokan gaba su yi roƙo gare ka a lokacin bala'i da kuma lokacin damuwa. 12Wa zai iya karya ƙarfe ko tagulla daga arewa?”

13Ubangiji ya ce mini, “Zan ba da wadatarku da dukiyarku ganima kyauta, saboda dukan zunubanku a dukan ƙasar. 14Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”

15Sa'an nan Irmiya ya ce, “Ya Ubangiji, ka sani. Kai ne, ka ziyarce ni, Ka kuma sāka wa waɗanda ke tsananta mini. Ka sani saboda kai nake shan zargi.

16Maganarka da na samu na ci. Maganarka kuwa ta zama abar murna a gare ni, Ta faranta mini zuciya. Gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.

17Ban zauna cikin ƙungiyar masu annashuwa ba. Ban kuwa yi murna ba, Na zauna ni kaɗai saboda kana tare da ni, Gama ka sa na cika da haushi.

18Me ya sa azabata ta ƙi ƙarewa, Raunukana kuma ba su warkuwa, Sun kuwa ƙi warkewa? Za ka yaudare ni kamar rafi, Ko kamar ruwa mai ƙafewa?”

19“Domin haka ga abin da ni, Ubangiji na ce, Idan ka komo sa'an nan zan kawo ka. Za ka tsaya a gabana. Idan ka hurta abin da yake gaskiya ba na ƙarya ba, Za ka zama kakakina. Za su komo gare ka, Amma kai ba za ka koma wurinsu ba.

20Zan maishe ka garun tagulla saboda waɗannan mutane, Za su yi yaƙi da kai, amma ba za su yi nasara a kanka ba, Gama ina tare da kai don in cece ka, in kuɓutar da kai.

21Zan kuɓutar da kai daga hannun mugaye, Zan ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”

16

Umarnin Ubangiji zuwa ga Irmiya

1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ba za ka yi aure ka haifi 'ya'ya mata da maza a wannan wuri ba. 3Ga abin da ni Ubangiji na faɗa a kan 'ya'ya mata da maza da aka haifa a wannan wuri, da kuma a kan iyayensu mata da maza da suka haife su a wannan ƙasa, 4za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”

5Ubangiji kuma ya ce, “Kada ka shiga gidan da ake makoki, ko ka tafi inda ake baƙin ciki, kada ka yi baƙin ciki saboda su, gama na ɗauke salamata, da ƙaunata, da jinƙaina daga wurin jama'an nan. 6Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu. 7Ba wanda zai ba mai makoki abinci don ya ta'azantar da shi saboda mamacin, ba kuma wanda zai ba shi abin sha don ya ta'azantar da shi saboda mahaifinsa ko mahaifiyarsa.

8“Kada kuma ka shiga gidan da ake biki, ka zauna ka ci ka sha tare da su. 9Gama ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan sa muryar murna, da ta farin ciki, da ta ango, da ta amarya, su ƙare a wurin nan a idonka da zamaninka.

10“Sa'ad da ka faɗa wa mutanen nan wannan magana duka, za su kuwa ce maka, “‘Me ya sa Ubangiji ya hurta wannan babbar masifa a kanmu? Menene laifinmu? Wane irin zunubi muka yi wa Ubangiji Allahnmu?” 11Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, “‘Domin kakanninku sun rabu da ni, sun bi gumaka, sun bauta musu, sun yi musu sujada. Sun rabu da ni, sun ƙi kiyaye dokokina. 12Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni. 13Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.”

14“Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “Da ba za a ƙara cewa, “‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar ba.” 15Amma za a ce, “‘Na rantse da Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga ƙasar arewa, da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su,” gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu.

16“Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “Za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu. 17Gama ina ganin dukan ayyukansu, ba a ɓoye suke a gare ni ba, muguntarsu kuma ba a ɓoye take a gare ni ba. 18Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, abin gādona kuma sun cika shi da abubuwansu na banƙyama.”

Addu'ar Irmiya ta Dogara ga Allah

19“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, “‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.”

20Mutum zai iya yi wa kansa alloli? Ai, waɗannan ba alloli ba ne!”

21Ubangiji ya ce, “Saboda haka, ga shi, zan sa su sani, Sau ɗayan nan kaɗai zan sa su su san ikona da ƙarfina, Za su kuma sani sunana Ubangiji ne.”

17

Zunubin Yahuza ya yi Kanta

1Ubangiji ya ce, “An rubuta zunubin mutanen Yahuza da alƙalamin ƙarfe, mai bakin yakutu. An zana shi a allon zuciyarsu da a zankayen bagadansu. 2Idan sun tuna da 'ya'yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi. 3Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar. 4Za ku rasa abin da ke hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”

5Ubangiji ya ce, “La'ananne ne mutumin da ke dogara ga mutum, Wanda jiki ne makaminsa, Wanda ya juya wa Ubangiji baya,

6Gama yana kama da sagagi a hamada, Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren hamada, A ƙasar gishiri, inda ba kowa.

7“Mai albarka ne mutumin da ke dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa.

8Shi kamar itace ne wanda ake dasa a bakin rafi Wanda ke miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.

9“Zuciya ta fi kome rikici, Cuta gare ta matuƙa, Wa zai san kanta>

10Ni Ubangiji nakan bincike tunani, In gwada zuciya, Domin in sāka wa kowane mutum gwargwadon al'amuransa, Da kuma gwargwadon ayyukansa.

11“Kamar makwarwar da ta kwanta kan ƙwan da ba ita ta nasa ba, Haka yake ga wanda ya sami dukiyar haram, Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu da shi, A ƙarshe zai zama wawa.”

12Kursiyi mai daraja, Da aka sa a bisa tun daga farko, Wurin ke nan inda Haikalinmu yake.

13Ya Ubangiji, begen Isra'ila, Duk waɗanda suka rabu da kai, za su sha kunya. Waɗanda suka ba ka baya a duniya za a rubuta su Domin sun rabu da Ubangiji, maɓuɓɓugar ruwan rai.

Irmiya ya Roƙi Ubangiji ya Kiyaye Shi

14Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwa warke, Ka cece ni, zan kuwa cetu, Gama kai ne abin yabona.

15Ga shi, suna ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Ta zo mana!”

16Amma ni ban yi gudun zaman makiyayi a gabanka ba, Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba, Ka kuwa sani. Abin da ya fito daga bakina kuwa, A bayyane yake gare ka.

17Kada ka zamar mini abin razana, Kai ne mafakata cikin ranar masifa,

18Bari waɗanda suka tsananta mini su sha kunya, Amma kada ka bar ni in kunyata. Bari su tsorata, Amma kada ka bar ni in tsorata. Ka aukar musu da ranar masifa, Ka hallaka su riɓi biyu!

A kan Kiyaye Ranar Asabar

19Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza ke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima. 20Ka ce, “‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuza, da dukan Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. 21Haka Ubangiji ya ce, ku yi hankali saboda rayukanku, kada ku ɗauki kaya a ranar Asabar, ko ku shigar da kowane abu ta ƙofofin Urushalima. 22Kada ku ɗauki kaya, ku fita da shi daga gidajenku a ranar, ko ku yi kowane irin aiki, amma ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarci kakanninku.” 23Amma duk da haka ba su kasa kunne, ko su mai da hankali ba. Amma suka taurare don kada su ji, su karɓi koyarwa.

24“‘Amma idan kun kasa kunne gare ni,” in ji Ubangiji, “‘ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofin wannan birni a ranar Asabar ba, amma kuka kiyaye ranar Asabar da tsarki, ba ku yi aiki a cikinta ba, 25sa'an nan ne sarakuna waɗanda za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda, za su shiga ta ƙofofin wannan birni, suna hawan karusai, da dawakai, su da sarakunansu, da jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima. Za a zauna a wannan birni har abada. 26Mutane za su zo daga biranen Yahuza da wuraren da ke kewaye da Urushalima, daga ƙasar Biliyaminu, da ta Shefela, da ta ƙasar tuddai, da kuma ta Negeb, suna kawo hadayu na ƙonawa da sadakoki, da hadayu na sha, da na turare, za su kuma kawo hadayu na godiya a Haikalin Ubangiji. 27Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.”

18

Irmiya a Gidan Maginin Tukwane

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce, 2“Ka tashi, ka gangara zuwa gidan maginin tukwane, a can zan yi maka magana.” 3Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, na iske shi yana ginin tukwane a kan na'urar ginin tukwanen. 4Abin da yake ginawa ya lalace a hannunsa, sai ya sāke gina wani abu dabam da yumɓu ɗin, yadda ya ga dama.

5Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, 6“Ya jama'ar Isra'ila, ashe, ba zan yi da ku kamar yadda maginin tukwanen nan ya yi ba? Duba, kamar yadda yumɓu yake a hannun maginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya ku jama'ar Isra'ila. 7A duk lokacin da na ce zan tumɓuke, in kakkarya in hallaka wata al'umma, ko wani mulki, 8idan wannan al'umma da na yi magana a kanta, ta juyo, ta tuba daga mugayen ayyukanta, zan janye masifar da na yi niyyar aukar mata. 9A duk kuma lokacin da na ce zan gina, in kafa wata al'umma, ko wani mulki, 10amma idan al'ummar ta aikata mugunta a gabana, ta ƙi saurarawa ga maganar, zan janye alherin da na yi niyyar yi mata. 11Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, “‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.” 12Amma za su ce, “‘Wannan ba abin da za mu kula da shi ba ne, mu ra'ayinmu za mu bi, kowannenmu kuwa zai yi bisa ga nufin tattaurar muguwar zuciyarsa.”

13“Domin haka ni Ubangiji na ce, “‘Ka tambayi sauran al'umma. Wa ya taɓa jin irin wannan? Budurwa Isra'ila, ta yi mugun abu ƙwarai!

14Dusar ƙanƙara mai danshi ta taɓa rabuwa da tsaunukan Lebanon? Ko ruwan rafuffuka mai sanyi na kan dutse ya taɓa ƙonawa>

15Amma mutanena sun manta da ni, Sun ƙona wa gumaka turare. Sun yi tuntuɓe a cikin al'amuransu, a hanyoyin dā, Sun bi ɓarayin hanyoyi, ba su bi karauka ba.

16Sun mai da ƙasarsu abar banƙyama, Abin raini har abada. Duk wanda ya wuce ta wurin zai razana ya kaɗa kansa.

17Haka zan warwatsa su Kamar yadda iskar gabas ke yi, a gaban abokan gābansu, Zan juya musu baya, ba za su ga fuskata ba, A ranar masifarsu.”

Maƙarƙashiyar Mutane da Addu'ar Irmiya

18Sa'an nan suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya, gama firist ba zai bar bin shari'a ba. Hakanan ma masu hikima ba za su bar yin shawara ba, hakanan kuma annabi ba zai bar yin magana ba! Ku zo mu kai ƙararsa, kada mu kula da abin da zai faɗa.”

19Irmiya kuwa ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji, ka kasa kunne gare ni, ka ji ƙarar maƙiyana!

20Daidai ne a rama alheri da mugunta? Duk da haka sun kafa wa raina tarko. Ka tuna yadda na tsaya a gabanka, Na yi maganar alheri a kansu, Domin ka janye fushinka daga gare su.

21Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansu yunwa, Ka bashe su ga takobi, Bari matansu su rasa 'ya'ya, mazansu su mutu, Ka sa annoba ta kashe mazansu, A kashe samarinsu da takobi a yaƙi.

22Bari a ji kururuwa daga gidajensu, Saboda maharan da ka aika musu farat ɗaya, Gama sun haƙa rami don in fāɗa, Sun kafa wa ƙafafuna tarkuna.

23Amma ya Ubangiji, Ka san dukan maƙarƙashiyarsu, su kashe ni, Kada ka gafarta musu muguntarsu, kada kuma ka shafe zunubinsu daga gabanka. Ka sa a jefar da su daga gabanka, Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”

19

Fasasshen Tulu

1Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sayo tulu a wurin maginin tukwane. Sa'an nan kuma ka ɗauki waɗansu daga cikin dattawan jama'a, da waɗansu manyan firistoci, 2ku tafi kwarin ɗan Hinnom na mashigin Ƙofar Kasko, ka yi shelar maganar da zan faɗa maka a can. 3Za ka ce, “‘Ku ji maganar Ubangiji, ya ku sarakunan Yahuza da mazaunan Urushalima, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, zan kawo wata irin masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa. 4Ga shi, mutanen nan sun rabu da ni, sun ƙazantar da wannan wuri sun ƙona wa gumaka turare, waɗanda su, ko kakanninsu, ko sarakunan Yahuza, ba su san su ba. Sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi. 5Sun gina wa Ba'al masujadai don su miƙa masa 'ya'yansu maza hadayar ƙonawa, abin da ban umarta ba, ban kuma ba da izni ba, ban ma yi tunanin haka ba. 6Saboda haka rana tana zuwa da ba za a ƙara ce da wannan wuri Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a ce da shi Kwarin Kisa. 7A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama'arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda ke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji. 8Zan mai da wannan birni abin ƙyama, abin raini, dukan wanda ya wuce wurin zai yi mamaki, ya yi tsaki saboda dukan masifun da suka auka wa birnin. 9Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda ke neman ransa.”

10“Sa'an nan sai ka fasa tulun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai, 11ka kuwa ce musu, “‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, haka zai farfasa jama'a, da wannan birni kamar yadda aka fashe tulun maginin tukwanen, ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne mutane a Tofet domin za a rasa makabartar da za a binne su. 12Haka zai yi wa wurin nan da mazauna cikinsa, ya mai da birnin nan kamar Tofet. 13Gidajen Urushalima da gidajen sarakunan Yahuza da dukan gidaje waɗanda a kan rufinsu aka ƙona wa rundunar sararin sama turare, aka zuba wa gumaka hadayu na sha, za su ƙazantu kamar Tofet.”

14Sa'an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don ya yi annabci, sai ya tsaya a fili na Haikalin Ubangiji, ya ce wa dukan jama'a, 15“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, “‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.”

20

Saɓani Tsakanin Irmiya da Fashur Firist

1Sa'ad da Fashur, firist, ɗan Immer, shugaban Haikalin Ubangiji ya ji Irmiya yana annabci a kan waɗannan abubuwa, 2sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka, aka kuma sa shi cikin turu a ƙofar Biliyaminu, a Haikalin Ubangiji. 3Kashegari sa'ad da Fashur ya fitar da Irmiya daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashur ba, amma ya ba ka suna Magormissabib, wato razana ta kowace fuska. 4Haka Ubangiji ya ce, “‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi. 5Banda haka kuma zan ba da dukan dukiyar wannan birni, da dukan ribarsa, da dukan abubuwa masu tamani, da dukan dukiyar sarakunan Yahuza, ga abokan gābansu, waɗanda za su washe su, su kama su, su kai Babila. 6Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda ke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.”

Kukan Irmiya

7“Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu, Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni. Na zama abin dariya dukan yini, Kowa yana ta yi mini ba'a.

8Duk lokacin da zan yi magana, Nakan ta da murya in yi magana da ƙarfi cewa, “‘Hargitsi da hallakarwa!” Gama saboda maganar Ubangiji na zama abin zargi, Da abin ba'a dukan yini.

9Idan na ce, “‘Ba zan ambaci Ubangiji ba, Ban zan ƙara yin magana da sunansa ba,” Sai in ji damuwa a zuciyata, An kulle ta a ƙasusuwana, Na gaji da danne ta a cikina, Ba zan iya jurewa ba.

10Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, “‘Razana ta kowace fuska,” Suna cewa, “‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!” Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, “‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.”

11Amma Ubangiji kana tare da ni Kamar jarumi mai bantsoro, Don haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe, Ba za su rinjaye ni ba. Za su sha kunya ƙwarai, Gama ba za su yi nasara ba. Ba za a manta da su ba.

12Ya Ubangiji Mai Runduna, mai gwada adali, Mai ganin zuciya duk da tunani, Ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, Gama a gare ka nake kawo ƙarata.”

13Ku raira waƙa ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Gama ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannun mugaye.

14La'ananniya ce ranar da aka haife ni, Kada ranar da uwata ta haife ni ta yi albarka!

15La'ananne ne mutum da ya kai wa mahaifina labari Cewa, “An haifa maka ɗa,” don ya sa shi farin ciki.

16Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Ubangiji ya kaɓantar ba tausayi. Bari ya ji kuka da safe, Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,

17Domin bai kashe ni tun ina ciki ba. Da ma cikin uwata ya zama mini kabari, In yi ta kwanciya a ciki har abada.

18Me ya sa na fito daga cikin mahaifa, Don in ga wahala da baƙin ciki, Don kwanakin raina su ƙare da kunya>

21

An yi Faɗi a kan Faɗuwar Urushalima

1Wannan ita ce maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa Irmiya sa'ad da sarki Zadakiya ya aiki Fashur ɗan Malkiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, wurin Irmiya cewa, 2“Ka tambayar mana Ubangiji, gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kawo mana yaƙi. Ko Ubangiji zai yi mana al'amuran nan nasa masu ban al'ajabi kamar yadda ya saba, ya sa Sarkin Babila ya janye, ya rabu da mu?”

3Sai Irmiya ya ce musu, 4“Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, “‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da ke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan. 5Ni kaina zan yi yaƙi da kai da dukan ƙarfina, da hasalata, da dukan zafin fushina. 6Zan kuwa kashe mazaunan birnin nan, mutum da dabba, da babbar annoba. 7Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.”

8“Sai ka faɗa wa wannan jama'a, ka ce, “‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, na sa tafarkin rai da na mutuwa a gabanku. 9Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa. 10Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.”

Annabci a kan Sarakunan Yahuza

11“Sai ka faɗa wa gidan sarautar Yahuza cewa, “‘Ku ji maganar Ubangiji,

12Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce, Ku aikata adalci kowace safiya. Ku ceci wanda aka yi masa ƙwace daga hannun mai matsa masa, Don kada hasalata ta tashi kamar wuta, Ta yi ƙuna, har ba mai iya kashe ta, Saboda mugayen ayyukanku.

13Ga shi, ina gāba da ku, ya ku mazaunan kwarin, Ya dutsen da ke a fili,” in ji Ubangiji. “‘Ku da kuke cewa, wa zai iya gangarowa wurinku, Ko kuwa wa zai shiga wurin zamanku>

14Zan hukunta ku bisa ga ayyukanku,” in ji Ubangiji, “‘Zan sa wa jejin ƙasar wuta. Za ta cinye duk abin da ke kewaye da ita.”

22

1Haka Ubangiji ya faɗa, “Ka tafi ka gangara zuwa gidan Sarkin Yahuza, ka faɗi wannan magana a can, 2ka ce, “‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda ke shiga ta ƙofofin nan. 3Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri. 4Hakika idan ka kiyaye wannan magana, sa'an nan sarakunan da za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan gida da karusai da dawakai, su da barorinsu da jama'arsu. 5Amma idan ba ka kula da waɗannan zantuttuka ba, na rantse da zatina,” in ji Ubangiji, “‘wannan fāda ta zama kufai.”

6Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza, “Kyanta kamar Gileyad take a gare ni, Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon. Duk da haka zan maishe ta hamada, Birnin da ba kowa ciki.

7Zan shirya waɗanda za su hallaka ta. Kowannensu da makamansa, Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwan al'ul ɗinta, a jefa su a wuta.

8“Al'ummai masu yawa za su wuce ta gefen wannan birni, kowane mutum zai ce wa maƙwabcinsa, “‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?” 9Za su amsa, su ce, “‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada ga gumaka, suka bauta musu.”

10Ku mutanen Yahuza, kada ku yi kuka saboda sarki Yosiya, Kada ku yi makokin rasuwarsa, Amma ku yi kuka ƙwarai saboda ɗansa Yehowahaz. Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zai ƙara komowa ba, Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar da aka haife shi ba.

11Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba. 12Amma a wurin da suka kai shi zaman talala, a can zai mutu, ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.

13Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, Benayensa kuma ta hanyar rashin gaskiya. Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yi masa aiki a banza, Bai ba shi hakkinsa ba.

14Kaiton wanda ya ce, “Zan gina wa kaina babban gida Da waɗansu irin benaye musamman.” Ya yi masa tagogi, Ya manna masa itacen al'ul, Sa'an nan ya yi masa jan shafe.

15Kana tsammani kai sarki ne, Da ya ke ƙasarka ta itacen al'ul ce? Amma ubanka ya ci, ya sha, Ya yi gaskiya, ya aikata adalci, Ya kuwa zauna lafiya.

16Ya biya wa matalauta da masu bukata hakkinsu, Ya kuwa yi kyau. Abin da ake nufi da sanina ke nan, In ji Ubangiji.

17Amma ka sa idonka da zuciyarka ga ƙazamar riba, Da zubar da jinin marar laifi, Da yin zalunci da danniya.

18Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, “Ba za su yi makoki dominsa ba, ko su ce, “‘Wayyo ɗan'uwanmu!” ko, “‘Wayyo 'yar'uwarmu!” Ba za su yi makoki dominsa ba, su ce, “‘Wayyo ubangidanmu!” ko “‘Wayyo mai martaba!”

19Za a binne shi kamar jaki, Za a ja shi a yar a bayan ƙofofin Urushalima.”

20Ku haura zuwa Lebanon, ku yi kuka, Ku ta da muryarku cikin Bashan, Ku yi kuka daga Abarim, Gama an hallakar da dukan ƙaunatattunku.

21Ubangiji ya yi muku magana a lokacin wadatarku. Amma kun ce, “Ba za mu kasa kunne ba!” Wannan shi ne halinku tun kuna samari, Don ba ku yi biyayya da murya Ubangiji ba.

22Iska za ta kwashe shugabanninku, Za a kai ƙaunatattunku cikin bauta, Sa'an nan za ku sha kunya ku ruɗe, Saboda dukan muguntarku.

23Ya ku mazaunan Lebanon, Waɗanda ke zaune cikin itatuwan al'ul, Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba ta same ku, Azaba ce irin ta mace mai naƙuda!

24“Ni Ubangiji na rantse da raina, ko da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, zoben hatimi ne a yatsan hannun damana, duk da haka zan kwaɓe shi, 25in bashe shi a hannun waɗanda suke neman ransa, da a hannun wanda yake jin tsoronsa, wato Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da Kaldiyawa. 26Zan jefar da shi da uwarsa a wata ƙasa inda ba a haife shi ba, a can zai mutu. 27Amma ƙasan nan da suke marmarin komowa cikinta, ba za su koma cikinta ba.”

28Ashe, Yekoniya kamar fasasshen tulu yake, Wanda ba wanda ya kula da shi? Me ya sa aka watsar da shi da 'ya'yansa, A ƙasar da ba su sani ba>

29Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa! Ki ji maganar Ubangiji!

30Haka Ubangiji ya ce, “Rubuta wannan mutum, marar 'ya'ya. Mutumin da ba zai yi albarka a duk kwanakinsa ba. Gama ba wani daga zuriyarsa Da zai gāji gadon sarautar Dawuda, Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”

23

Komowar waɗanda suka Ragu

1“Taku ta ƙare! Makiyayan da suka lalatar, suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji. 2Haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya faɗa a kan makiyayan jama'arsa. “Kun warwatsar da garkena kun kore su, ba ku lura da su ba. Ni ma haka zan yi da ku saboda muguntarku, ni Ubangiji na faɗa. 3Sa'an nan zan tattaro sauran garkena daga wuraren da aka warwatsa su, zan komo da su cikin garkensu, zan sa su hayayyafa su riɓaɓɓanya. 4Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.

5“Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci daga zuriyar Dawuda Wanda zai ci sarauta. Zai yi sarauta da hikima, Zai aikata abin da ke daidai a ƙasar.

6A zamaninsa za a ceci Yahuza, Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya. Sunan da za a kira shi da shi ke nan, “‘Ubangiji Adalcinmu.”

7“Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa, ni Ubangiji na faɗa, sa'ad da mutane ba za su ƙara cewa, “‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin ƙasar Masar ba,” 8amma za su ce, “‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da zuriyar Isra'ila daga ƙasar arewa, daga kuma dukan ƙasashen da ya warwatsa su!” Sa'an nan za su zauna a ƙasarsu ta kansu.”

Jawabi a kan Annabawan Ƙarya

9A kan annabawa kuwa, zuciyata ta karai, Dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa, Saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki. Na zama kamar mashayi, wanda ya bugu da ruwan inabi,

10Gama ƙasar cike take da mazinata, Saboda la'ana, ƙasar za ta yi makoki, Wuraren kiwo na jeji sun bushe, Manufarsu mugunta ce, Ba su mori ƙarfinsu a inda ya kamata ba.

11“Annabi da firist, dukansu biyu marasa tsoron Allah ne, Har a cikin Haikalina na tarar da muguntarsu.” Ubangiji ya faɗa.

12“Saboda haka hanyarsu za ta zama da santsi da duhu, Inda za a runtume su, su fāɗi. Gama zai kawo musu masifa a shekarar da za su sha hukuncinsu.” Ubangiji ya faɗa.

13“A cikin annabawan Samariya, Na ga abu marar kyan gani. Da sunan Ba'al suke yin annabci, Suna ɓad da jama'ata Isra'ila

14Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”

15Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa, “Ga shi, zan ciyar da su da abinci mai ɗaci, In shayar da su da ruwan dafi. Daga wurin annabawan Urushalima Rashin tsoron Allah ya fito ya mamaye dukan ƙasar.”

16Ubangiji Mai Runduna ya ce wa mazaunan Urushalima, “Kada ku kasa kunne ga maganar annabawa, Gama sukan cika kunnuwanku da ƙarairayi. Suna faɗar ganin damarsu, Ba faɗar Ubangiji ba.

17Suna ta faɗa wa waɗanda ke raina maganar Ubangiji cewa, “‘Za ku zauna lafiya!” Ga kowane mai bin nufin tattaurar zuciyarsa, “‘Ba masifar da za ta same ka.”

18Irmiya ya ce, “Gama wanene a cikin annabawan nan ya taɓa neman shawarar Ubangiji don ya fahimci maganarsa, ko kuwa wanene ya taɓa kasa kunne don ya ji maganarsa>

19Ga shi, hadirin hasalar Ubangiji ya taso, Kamar iskar guguwa, Zai tashi a bisa kan mugaye.

20Ubangiji ba zai huce ba, Sai ya aikata nufin zuciyarsa. Amma sai daga baya za ku gane sarai.”

21Ubangiji ya ce, “Ni ban aiki waɗannan annabawa ba, Duk da haka sun tafi, Ban kuwa yi musu magana ba, Amma sun yi annabci.

22Amma da a ce sun tsaya cikin shawarata, Da sun yi shelar maganata, ga jama'ata, Da sun juyar da su daga muguwar hanyarsu, Da mugayen ayyukansu.

23“Ni Allah na kusa ne kaɗai, Banda na nesa?” In ji Ubangiji.

24“Mutum ya iya ɓoye kansa a wani lungu Inda ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji. “Ashe, ban cika sammai da duniya ba>

25Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da ke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, “‘Na yi mafarki!” 26Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da ke a zuciyarsu? 27Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba'al. 28Bari annabin da ke da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda ke da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa. 29Maganata kamar wuta ce, kamar guduma mai farfashe dutse. Ni Ubangiji na faɗa. 30Domin haka, ga shi, ina gāba da annabawan da ke satar maganata daga wurin junansu. Ni Ubangiji na faɗa. 31Ina kuma gāba da annabawan da ke faɗar ra'ayin kansu, sa'an nan su ce, “‘Ubangiji ne ya faɗa.” 32Ina kuma gāba da annabawan da ke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama'a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”

33“Kai Irmiya, sa'ad da wani mutum daga cikin mutanen nan, ko annabi, ko firist ya tambaye ka cewa, “‘Mecece nawayar Ubangiji?” Sai ka ce masa, “‘Ku ne nawayar, zan kuwa rabu da ku,” ni Ubangiji na faɗa. 34Idan annabi ko firist, ko wani daga cikin jama'a, ya ce, “‘Nawayar Ubangiji,” zan hukunta shi duk da iyalin gidansa. 35Haka kowannenku zai ce wa maƙwabcinsa da ɗan'uwansa, “‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?” 36Amma ba za ku ƙara ambatar nawayar Ubangiji ba, gama maganar kowane mutum za ta zama nawaya, ga shi, kun ɓata maganar Allah mai rai, Ubangiji Mai Runduna, Allahnmu. 37Haka za ka faɗa wa annabi, “‘Wace amsa Ubangiji ya bayar? Me Ubangiji ya faɗa?” 38Amma idan kun ce, “‘Nawayar Ubangiji,” ga abin da ni Ubangiji na ce, tun da ya ke kun faɗi wannan magana, wato “‘Nawayar Ubangiji,” alhali kuwa na aika muku cewa, kada ku ce, “‘Nawayar Ubangiji,” 39saboda haka, hakika zan ɗaga in jefar da ku daga gabana, da ku da birni wanda na ba ku, ku da kakanninku. 40Zan sa ku zama abin zargi da abin kunya har abada, ba kuwa za a manta da wannan ba.”

24

Kwando Biyu na 'Ya'yan Ɓaure

1Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji. 2A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu. 3Sai Ubangiji ya ce mini, “Irmiya, me ka gani?” Sai na ce, “'Ya'yan ɓaure, akwai masu kyau ƙwarai, akwai kuma marasa kyau ƙwarai, har da ba za su ciwu ba.”

4Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, 5“Haka ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, kamar kyawawan ɓauren nan, haka nake ganin mutanen Yahuza waɗanda aka kai su bautar talala a ƙasar Kaldiyawa. 6Zan lura da su da kyau, in kuma komo da su a wannan ƙasa. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan kafa su, ba zan tumɓuke su ba. 7Zan ba su zuciyar da za su sani ni ne Ubangiji. Za su kuwa zama jama'ata, ni kuwa zan zama Allahnsu, gama za su komo wurina da zuciya ɗaya.

8“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Zadakiya Sarkin Yahuza, da sarakunansa, da sauran mutanen Urushalima da suka ragu a ƙasar, da mutanen da suka tafi Masar, kamar ruɓaɓɓen ɓauren nan da suka lalace har ba su ciwuwa. 9Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su. 10Zan aika musu da takobi, da yunwa, da annoba har an hallaka su sarai daga cikin ƙasar da na ba su, su da kakanninsu.”

25

Za a Zama Kufai har Shekara Saba'in

1A shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana a kan dukan mutanen Yahuza. A shekarar da Nebukadnezzar ya ci sarautar Babila, 2a shekarar ce, annabi Irmiya ya yi wa dukan mutanen Yahuza da dukan mazaunan Urushalima magana cewa, 3“Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba. 4Ba ku saurara ba, ba ku kasa kunne don ku ji ba, ko da ya ke Ubangiji ya yi ta aiko muku da dukan bayinsa annabawa, 5yana cewa, “‘Sai kowane ɗayanku ya juyo daga mugun halinsa da mugayen ayyukansa don ya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku, ku da kakanninku tun daga zamanin dā har abada. 6Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa'an nan ba zan hore ku ba.” 7Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.

8“Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “‘Tun da ya ke kun ƙi yin biyayya da maganata, 9zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da ke kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada. 10Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu. 11Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in. 12Sa'an nan bayan cikar shekara saba'in ɗin, zan hukunta Sarkin Babila da ƙasarsa, wato ƙasar Kaldiyawa. Zan maishe ta kango har abada, saboda zunubinsa. 13Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al'umman nan. 14Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.”

Hukuncin da Allah zai yi wa Al'ummai

15Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al'umman da na aike ka gare su, su sha. 16Za su sha, su yi tangaɗi su yi hauka saboda takobin da zan aiko a cikinsu.”

17Sai na karɓi ƙoƙon daga wurin Ubangiji, na sa dukan al'umman da Ubangiji ya aike ni gare su, su sha daga cikinsa. 18Urushalima, da biranen Yahuza, da sarakunanta, da shugabanninta, za su zama kango da abin ƙyama da abin raini, da abin la'ana. Haka yake a yau. 19-26Ga lissafin sauran da za su sha ƙoƙon. Fir'auna Sarkin Masar da kuma barorinsa, da sarakunansa, Dukan jama'arsa, da dukan baƙin da ke tare da su, dukan sarakunan ƙasar Uz, dukan sarakunan ƙasar Filistiyawa, wato Ashkelon, da Gaza, da Ekron, da saura na Ashdod, Edom da Mowab, da 'ya'yan Ammon maza, dukan sarakunan Taya, da dukan sarakunan Sidon, dukan sarakunan da ke gaɓar Bahar Rum da waɗanda ke a tsibiran tekun, Dedan, da Tema, da Buz, da dukan waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, dukan sarakunan Arabiya, dukan sarakunan tattarmukan mutane da ke zaune a hamada, dukan sarakunan Zimri, da dukan sarakunan Elam, da dukan sarakunan Mediya, dukan sarakunan arewa, na nesa da na kusa bi da bi. Dukan mulkokin da ke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daganan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.

27“Za ka kuma faɗa musu cewa, “‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.” 28Idan kuwa sun ƙi su karɓi ƙoƙon daga hannunka su sha sai ka faɗa musu cewa, “‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, dole ne ku sha! 29Gama ga shi, na fara sa masifa ta yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana. To, kuna tsammani ba za a hukunta ku ba? Sai an hukunta ku, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

30“Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa, “‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama, Zai yi magana daga wurin zamansa mai tsarki, Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfi ƙwarai, Zai yi ihu kamar masu matse 'ya'yan inabi, Zai yi gāba da dukan mazaunan duniya.

31Za a ji hayaniya har iyakar duniya, Gama Ubangiji yana da ƙara game da al'ummai, Zai shiga hukunta wa dukan 'yan adam, Zai kashe mugaye da takobi, Ubangiji ya faɗa.”

32Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga masifa tana tahowa daga al'umma zuwa al'umma, Hadiri kuma yana tasowa daga dukan manisantan wurare na duniya.

33Waɗanda Ubangiji ya kashe a wannan rana, Za su zama daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi makoki dominsu ba, Ba kuwa za a tattara gawawwakinsu a binne ba. Za su zama taki ga ƙasa.

34“Ku yi makoki, ku yi kuka, ku makiyaya, Ku yi ta birgima a cikin toka ku iyayengijin garke, Gama ranar da za a yanka ku da ranar da za a warwatsa ku ta zo, Za ku fāɗi kamar zaɓaɓɓen kasko.

35Ba mafakar da ta ragu domin makiyaya, Iyayengijin garken ba za su tsira ba.

36Ji kukan makiyayan, Da kukan iyayengijin garken, Gama Ubangiji yana lalatar da wurin kiwonsu.

37Garkunan da ke zaune lafiya kuwa, an yi kaca-kaca da su Saboda zafin fushin Ubangiji.

38Ya rabu da wurin ɓuyarsa kamar zaki, Gama ƙasarsu ta zama marar amfani, Saboda takobin Ubangiji, da kuma zafin fushinsa.”

26

Maƙarƙashiya a Kashe Irmiya

1A farkon sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce, 2“Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya. 3Mai yiwuwa ne su ji, har kowa ya juyo ya bar muguwar hanyarsa. Ni ma sai in janye masifar da na yi niyyar aukar musu da ita, saboda mugayen ayyukansu.”

4Ubangiji ya faɗa wa Irmiya ya ce wa jama'a, “Haka Ubangiji ya ce, idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, ku yi tafiya a dokata wadda na sa a gabanku ba, 5ku kuma kula da zantuttukan bayina, annabawa, waɗanda na yi ta aiko muku, to, amma ba ku kula ba. 6Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”

7Firistoci, da annabawa, da dukan jama'a sun ji dukan maganan nan da Irmiya ya faɗa a cikin Haikalin Ubangiji. 8Sa'ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama'a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama'a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi! 9Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama'a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.

10Sa'ad da sarakunan Yahuza suka ji waɗannan al'amura, sai suka fito daga gidan sarki zuwa Haikalin Ubangiji, suka zauna a bakin Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji. 11Sai firistoci da annabawa suka faɗa wa sarakunan nan da jama'a duka, suka ce, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa, gama ya yi annabci gāba da wannan birni kamar yadda kuka ji da kunnuwanku.”

12Sa'an nan sai Irmiya ya yi magana da dukan sarakuna da dukan jama'a, ya ce, “Ubangiji ne ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan Haikali da wannan birni, da irin maganar da kuka ji. 13Saboda haka yanzu sai ku gyara al'amuranku da ayyukanku, ku yi biyayya kuma da muryar Ubangiji Allahnku. Ubangiji kuwa zai janye masifar da ya hurta gāba da ku. 14Amma ni kaina kuwa a hannunku nake, sai ku yi mini yadda kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku. 15Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”

16Sarakuna kuwa da dukan jama'a suka ce wa firistoci da annabawa, “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”

17Sai waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka miƙe tsaye, suka ce wa dukan taron jama'a, 18“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, “‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.”

19Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”

20Akwai wani mutum kuma wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji. Sunansa Uriya ɗan Shemaiya mutumin Kiriyat-yeyarim. Ya yi annabci gāba da birnin nan da ƙasan nan da magana irin ta Irmiya. 21Sa'ad da sarki Yehoyakim, da dukan jarumawansa, da dukan sarakunansa suka ji maganarsa, sai sarki yana so ya kashe shi, amma sa'ad da Uriya ya ji, sai ya ji tsoro, ya gudu ya tsere zuwa Masar. 22Sa'an nan sai sarki Yehoyakim ya aiki waɗansu mutane zuwa Masar, wato Elnatan ɗan Akbor da waɗansu tare da shi. 23Suka kamo Uriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoyakim, sai ya sa aka kashe shi da takobi, aka binne gawarsa a makabartar talakawa.

24Amma Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bashe shi ga mutane don su kashe shi ba.

27

Irmiya ya Ɗaura Karkiyar Shanu a Wuyansa

1A farkon sarautar Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana. 2Ya ce ya yi wa kansa karkiyar itace da maɗaurai na fata ya ɗaura su a wuyansa, 3ya aika da magana zuwa ga Sarkin Edom, da Sarkin Mowab, da Sarkin Ammon, da Sarkin Taya, da Sarkin Sidon ta hannun manzannin da suka zo Urushalima wurin Zadakiya Sarkin Yahuza. 4Ubangiji ya ce wa Irmiya ya umarce su, su tafi, su faɗa wa iyayengijinsu cewa, “In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga abin da za ku faɗa wa iyayengijinku, 5“‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda ke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama. 6Yanzu fa na ba bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila, dukan ƙasashen nan, na kuma ba shi namomin jeji su bauta masa. 7Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.

8“‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa. 9Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu duba, da masu mafarkai, da matsubbata, ko masu sihiri waɗanda suka ce muku ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba. 10Suna yi muku annabcin ƙarya ne, za su kuwa sa a kai ku wata ƙasa nesa da ƙasarku. Zan kore ku, za ku kuwa lalace. 11Amma duk al'ummar da za ta ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanta, ta kuma bauta masa, zan bar ta a ƙasarta, ta yi noman ƙasarta, ta zauna a ciki, ni Ubangiji na faɗa.”

12Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu! 13Don me kai da mutanenka za ku mutu ta takobi, da yunwa, da annoba, kamar yadda Ubangiji ya yi magana a kan kowace al'umma da ta ƙi ta bauta wa Sarkin Babila? 14Kada ka kasa kunne ga maganar annabawan da suke ce maka, “‘Ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.” Annabcin ƙarya suke yi muku. 15Gama Ubangiji ya ce shi bai aike su ba, annabcin ƙarya suke yi muku da sunansa, don ya kore ku, ku halaka, ku da annabawan da suke yi muku annabci.”

16Sa'an nan na faɗa wa firistoci da jama'a cewa, “In ji Ubangiji, kada ku kasa kunne ga abin da annabawanku suke muku annabci cewa, “‘Ba da daɗewa ba za a komo da kayan Haikalin Ubangiji daga Babila.” Ƙarya ce suke yi muku. 17Kada ku ji su, amma ku bauta wa Sarkin Babila don ku rayu! Don me birnin nan zai zama kufai? 18Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima. 19Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan, 20wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.

21“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima, 22“‘Za a kwashe su a kai Babila, a can za su kasance har lokacin da zan sāke kulawa da su. Sa'an nan ne zan komo da su, in maishe su a wannan wuri.”

28

Annabcin Ƙarya na Hananiya

1Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama'a, ya ce, 2“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, “‘Na karya karkiyar Sarkin Babila. 3Bayan shekara biyu zan komo da kayayyakin Haikalin Ubangiji zuwa wurin nan. Kayayyakin da Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya kwashe daga wannan wuri, ya kai Babila. 4Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.”

5Sa'an nan annabi Irmiya ya yi magana da annabi Hananiya a gaban firistoci da dukan jama'ar da ke tsaye a Haikalin Ubangiji, ya ce, 6“Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka, Ubangiji ya sa annabcin da ka yi ya zama gaskiya, Ubangiji ya komo da kayayyakin Haikalinsa da dukan waɗanda aka kai su zaman talala a Babila. 7Amma yanzu sai ka ji maganan nan da zan faɗa maka, kai da dukan jama'an nan. 8Annabawan da suka riga mu, ni da kai a zamanin dā, sun yi wa ƙasashe masu yawa da manyan mulkoki annabcin yaƙi da yunwa, da annoba. 9Idan maganar wannan annabi kuwa da ya yi annabcin salama ta cika, sa'an nan ne za a sani gaskiya Ubangiji ne ya aiko shi.”

10Sai annabi Hananiya ya cire karkiyar daga wuyan annabi Irmiya ya karya ta. 11Sa'an nan Hananiya ya yi magana a gaban dukan jama'a, ya ce, “In ji Ubangiji, haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, daga wuyan dukan al'ummai kafin shekara biyu.” Sai annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.

12Da ɗan daɗewa bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar da ke a wuyan annabi Irmiya, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce 13ya tafi ya faɗa wa Hananiya, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, “‘Ka karya karkiya ta itace, amma zan yi karkiya ta ƙarfe a maimakonta. 14Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al'ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.”

15Sai annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka ji, ya Hananiya, Ubangiji bai aike ka ba, kana sa mutanen nan su dogara ga ƙarya. 16Saboda haka, in ji Ubangiji, “‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.”

17A wannan shekara kuwa, a watan bakwai, sai annabi Hananiya ya mutu.

29

Wasiƙar Irmiya Zuwa ga Yahudawan da ke Babila

1Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila. 2(Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.) 3Ya aika da wasiƙar ta hannun Elasa ɗan Shafan, da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Zadakiya Sarkin Yahuza ya aika zuwa Babila, wurin Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Ga abin da wasiƙar ta ce.

4“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila. 5“‘Ku gina gidaje, ku zauna a ciki, ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu. 6Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu. 7Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu'a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.” 8Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. “‘Kada ku yarda annabawanku da malamanku na duba waɗanda ke tare da ku su ruɗe ku, kada ku kasa kunne ga mafarkansu. 9Gama annabcin da suke yi muku da sunana, ƙarya ne, ni ban aike su ba.”

10“Ubangiji ya ce, “‘Sa'ad da kuka cika shekara saba'in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri. 11Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya. 12Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku. 13Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya. 14Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.”

15“Domin kun ce, Ubangiji ya ba ku annabawa a Babila, 16ku ji abin da Ubangiji ya faɗa a kan sarkin da ya hau gadon sarautar Dawuda, da a kan dukan jama'ar da ke zaune a wannan birni, wato a kan danginku waɗanda ba a kwashe su zuwa zaman talala ba. 17Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “‘Ga shi, zan aiko musu da takobi, da yunwa, da masifa, zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓaure waɗanda suka lalace ƙwarai, har ba su ciwuwa. 18Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su. 19Domin ba su ji maganata wadda ni Ubangiji na faɗa ba, na yi ta aika muku da ita ta wurin bayina annabawa, amma kuka ƙi, ni Ubangiji na faɗa. 20Ku ji maganar Ubangiji, dukanku da aka kai ku zaman talala waɗanda na kora daga cikin Urushalima zuwa Babila.”

21“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda ke yi muku annabcin ƙarya da sunana. Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku. 22Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la'ana cewa, “‘Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!” 23Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.

Saƙo ga Shemaiya

24“Zancen Shemaiya mutumin Nehelam, 25haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama'ar da ke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma'aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa 26Ubangiji ya naɗa ka firist a madadin Yehoyada firist, ka lura da Haikalin Ubangiji, ka sa kowane mahaukacin da zai yi annabci a turu, ka sa masa ƙangi. 27To, me ya sa ba ka tsauta wa Irmiya, mutumin Anatot, wanda yake yin maka annabci ba? 28Gama ya aiko mana a Babila, cewa za mu daɗe a zaman talala, mu gina wa kanmu gidaje, mu zauna a ciki, mu dasa gonaki mu ci amfaninsu.”

29Sai Zafaniya firist, ya karanta wasiƙan nan a gaban annabi Irmiya. 30Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya, ya ce, 31ya aika wa dukan waɗanda ke zaman talala ya ce, “Haka Ubangiji ya ce a kan Shemaiya mutumin Nehelam, “‘Saboda Shemaiya ya yi muku annabci, alhali ni ban aike shi ba, ya sa ku dogara ga ƙarya,” 32saboda haka Ubangiji ya ce, “‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,” in ji Ubangiji.

30

Tabbatarwar Komowa daga Zaman Talala

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce, 2“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, “‘Ka rubuta dukan maganar da na faɗa maka a littafi. 3Gama kwanaki suna zuwa sa'ad da zan komo da mutanena, wato Isra'ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,” ni Ubangiji na faɗa.”

4Waɗannan ne maganar da Ubangiji ya faɗa a kan Isra'ila da Yahuza.

5“Ni Ubangiji na ce, Mun ji kukan gigitacce, Kukan firgita ba kuma salama.

6Yanzu ku tambaya, ku ji, Namiji ya taɓa haihuwa? To, me ya sa nake ganin kowane namiji yana riƙe da kwankwaso, Kamar mace mai naƙuda, Fuskar kowa kuma ta yi yaushi>

7Kaito, gama wannan babbar rana ce, Ba kuma kamarta, Lokaci ne na wahala ga Yakubu, Duk da haka za a cece shi daga cikinta.”

8Ubangiji Mai Runduna ya ce, “A wannan rana zan karya karkiya da ke a wuyansu, in cire musu ƙangi, ba kuma za su ƙara zama bayin baƙi ba. 9Amma za su bauta mini, ni Ubangiji Allahnsu, da Dawuda sarkinsu, wanda zan tayar musu da shi.”

10Ubangiji ya ce, “Kada ka ji tsoro, ya barana Yakubu, Kada kuma ka yi fargaba, ya Isra'ila, Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa rai a kwance, Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.

11Gama ina tare da kai don in cece ka, Zan hallaka dukan al'ummai sarai, Inda na warwatsa ku. Amma ku ba zan hallaka ku ba, Zan hore ku da adalci, Ba yadda za a yi in ƙyale ku ba hukunci, Ni Ubangiji na faɗa.”

12Ubangiji ya ce, “Rauninku ba ya warkuwa, Mikinku kuwa mai tsanani ne ƙwarai.

13Ba wanda zai kula da maganarku, Ba magani domin mikinku, Ba za ku warke ba.

14Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.

15Don me kuke kuka a kan rauninku? Ciwonku ba zai warke ba. Saboda laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke, Shi ya sa na yi muku waɗannan abubuwa.

16Domin haka dukan waɗanda suka cinye ku, za a cinye su, Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansu zai tafi bauta, Waɗanda suka washe ku, za a washe su. Dukan waɗanda suka kwashe ku ganima, su ma za a kwashe su ganima.

17Zan mayar muku da lafiyarku, Zan kuma warkar da raunukanku, Ko da ya ke maƙiyanku suna kiranku yasassu, Suna cewa, “‘Ai, Sihiyona ce, ba wanda ya kula da ita.” Ni Ubangiji na faɗa.”

18Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan komar wa alfarwar Yakubu arzikinta, Zan kuma nuna wa wuraren zamansa jinƙai, Za a sāke gina birnin a kufansa, Fādar kuma za ta kasance a inda take a dā.

19Daga cikinsu za a ji waƙoƙin godiya. Da muryoyin masu murna. Zai riɓaɓɓanya su, ba za su zama kaɗan ba, Zan kuwa ɗaukaka su, ba za a ƙasƙantar da su ba.

20'Ya'yansu za su zama kamar dā, Jama'arsu kuma za su kahu a gabana, Zan hukunta dukan waɗanda suka zalunce su.

21Sarkinsu zai zama ɗaya daga cikinsu, Mai mulkinsu kuma zai fito daga cikinsu. Zan kawo shi kusa, zai kuwa kusace ni, Gama wanene zai yi ƙarfin hali ya kusace ni? Ni Ubangiji na faɗa.

22Za ku zama mutanena, Ni kuwa zan zama Allahnku.”

23Ga hadirin hasalar Ubangiji ya taso, wato iskar guguwa, Zai huce a kan mugaye.

24Zafin fushin Ubangiji ba zai huce ba, Sai ya aikata, ya kammala abubuwan da ya yi niyya a tunaninsa. A nan gaba mutanensa za su fahimci wannan.

31

1Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra'ila, za su kuwa zama jama'ata.”

2Haka Ubangiji ya ce, “Jama'ar da suka tsere wa takobi, Sun sami alheri a cikin jeji, A sa'ad da Isra'ila suka nemi hutawa.” 3-4Ubangiji ya bayyana gare ni tun daga nesa cewa, “Ya Isra'ila, budurwa! Na kusace ki da madawwamiyar ƙaunata, Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata a gare ki ba. Zan sāke gina ki, Za ki kuwa ginu, Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe, Za ki shiga rawar masu murna.

5Za ki sāke dasa gonar inabi A kan duwatsun Samariya, Masu dashe za su dasa, Za su mori 'ya'yan.

6Gama rana tana zuwa sa'ad da mai tsaro zai yi kira A ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce, “‘Ku tashi mu haura zuwa Sihiyona Zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.”

7Ga abin da Ubangiji ya ce, “Raira wa Yakubu waƙar farin ciki da ƙarfi, Ku ta da murya saboda shugaban al'ummai, Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce, “‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka, Wato ringin mutanen Isra'ila,”

8Ga shi, zan fito da su daga ƙasar arewa, Zan tattaro su daga manisantan wurare na duniya, Tare da su makafi da guragu, Da mace mai goyo da mai naƙuda, Za su komo nan a babbar ƙungiya.

9Da kuka za su komo. Da ta'aziyya zan bishe su, in komar da su, Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan ruwa, A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba za su yi tuntuɓe ba. Gama ni uba ne ga Isra'ila, Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”

10“Ku ji maganar Ubangiji, Ya ku al'ummai, Ku yi shelarsa har a ƙasashen da ke nesa, na gāɓar teku. Ku ce, “‘Shi wanda ya warwatsa Isra'ila zai tattaro ta, Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa.”

11Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu. Ya fanshe shi daga hannuwan waɗanda suka fi ƙarfinsa.

12Za su zo su raira waƙa da ƙarfi, A bisa ƙwanƙolin Sihiyona, Za su yi annuri saboda alherin Ubangiji, Saboda hatsi, da ruwan inabi, da mai, Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu. Rayuwarsu za ta zama kamar lambu, Ba za su ƙara yin yaushi ba.

13Sa'an nan 'yan mata za su yi rawa da farin ciki, Samari da tsofaffi za su yi murna. Zan mai da makokinsu ya zama murna, Zan ta'azantar da su, in ba su farin ciki maimakon baƙin ciki.

14Zan yi wa ran firistoci biki da wadata, Jama'ata za su ƙoshi da alherina, Ni Ubangiji na faɗa.”

15Ga abin da Ubangiji ya ce, “An ji murya daga Rama, Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta, ba su.

16Ki yi shiru, ki daina kuka, Ki shafe hawaye daga idanunki. Za a sāka miki wahalarki, Za su komo daga ƙasar abokin gāba, Ni Ubangiji na faɗa.

17Akwai sa zuciya dominki a nan gaba, Ni Ubangiji na faɗa. 'Ya'yanki za su komo ƙasarsu.

18“Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana cewa, “‘Ka hore ni, na kuwa horu, Kamar ɗan maraƙin da ba shi da horo, Ka komo da ni don in zama kamar yadda nake a dā, Gama kai ne Ubangiji Allahna.

19Gama na tuba saboda na rabu da kai, Bayan da aka ganar da ni, sai na sunkuyar da kai, Kunya ta kama ni, na gigice, Domin ina ɗauke da wulakancin ƙuruciyata.”

20Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.

21“Ki kafa wa kanki alamun hanya, Ki kafa wa kanki shaidu, Ki lura da gwadabe da kyau, Hanyar da kin bi, kin tafi. Ya budurwa Isra'ila, ki komo, Komo zuwa biranen nan naki.

22Har yaushe za ki yi ta shakka, Ya ke 'yar marar bangaskiya? Gama Ubangiji ya halitta sabon abu a duniya, Mace ce za ta kāre namiji.”

23Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu. “‘Ubangiji ya sa maka albarka, Ya wurin zaman adalci, Ya tsattsarkan tudu!”

24Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu. 25Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

26Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.”

Sabon Alkawari

27“Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra'ila da na Yahuza. 28Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa. 29A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa, “‘Ubanni suka ci 'ya'yan inabi masu tsami, Haƙoran 'ya'ya suka mutu” ba.

30Amma kowa zai mutu saboda zunubin kansa, Wanda ya ci inabi masu tsami, Shi ne haƙoransa za su mutu.”

31Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza. 32Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da ya ke ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa. 33Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata. 34Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, “‘Ka san Ubangiji” ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”

35Haka Ubangiji ya ce, Shi wanda ya ba da rana ta haskaka yini, Ya sa wata da taurari su ba da haske da dare, Shi ne yakan dama teku, ya sa raƙumanta su yi ruri, Sunansa Ubangiji Mai Runduna.

36“Idan dai wannan kafaffiyar ka'ida ta daina aiki a gabana, Ni Ubangiji na faɗa, To, ashe, zuriyar Isra'ila za ta daina zama al'umma a gabana ke nan har abada.

37Idan a iya auna sammai a kuma iya bincike tushen duniya a ƙarƙas, To, ashe, zan watsar da dukan zuriyar Isra'ila ke nan saboda dukan abin da suka yi, Ni Ubangiji na faɗa.

38“Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa. 39Sa'an nan ma'aunin zai daɗa gaba, har ya kai tudun Gareb, sa'an nan ya nausa zuwa Gowa. 40Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”

32

Irmiya ya Sayi Saura a Anatot

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya a shekara ta goma ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza. A lokacin kuwa Nebukadnezzar yana da shekara goma sha takwas da sarauta a Babila. 2A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza. 3Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi. 4Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido. 5Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”

6Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa 7ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, “‘Ka sayi gonata wadda ke a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.” 8Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda ke a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce. 9Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa. 10Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni. 11Na ɗauki takardun ciniki waɗanda aka rubuta sharuɗan a ciki da wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, 12na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma'aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda ke zaune a gidan waƙafi. 13Sai na umarci Baruk a gabansu cewa, 14“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.” 15Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, “‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.”

Addu'ar Irmiya

16Bayan da na ba Baruk, ɗan Neriya, takardar sharuɗan ciniki, sai na yi addu'a ga Ubangiji, na ce, 17“Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka. 18Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna. 19Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa. 20Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau. 21Ta wurin alamu da al'ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama'arka Isra'ila daga ƙasar Masar. 22Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da ke cike da yalwar albarka. 23Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.

24“Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani. 25Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, “‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da ya ke an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.”

26Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya, 27“Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina. 28Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin. 29Kaldiyawa da ke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi. 30Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa. 31Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana. 32Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima. 33Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da ya ke na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba. 34Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin Haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi. 35Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”

Alkawari na Sa Zuciya

36“Domin haka ga abin da ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce a kan wannan birni wanda ka ce, “‘An ba da shi ga Sarkin Babila, da takobi, da yunwa, da annoba.” 37Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya. 38Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. 39Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na 'ya'yansu a bayansu. 40Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina. 41Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”

42Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama'an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu. 43Za a sayi gonaki a wannan ƙasa wadda kake cewa ta zama kufai, ba mutum, ba dabba a ciki, wadda aka ba da ita ga Kaldiyawa. 44Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da ke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”

33

Komo da Harka a Urushalima

1Ubangiji ya sāke yin magana da Irmiya sa'ad da yake a kulle a gidan waƙafi. 2Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce, 3“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.” 4Gama haka Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, a kan gidajen da ke a wannan birni, da gidajen sarakunan Yahuza, waɗanda aka rurrushe domin a yi wa garukan jigo saboda mahaurai da suka kewaye birni, da kuma saboda yaƙi. 5“Sa'ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu. 6Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya. 7Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā. 8Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini. 9Sunan wannan birni zai zama mini abin murna, da abin yabo, da darajantawa ga dukan al'umman duniya waɗanda za su ji dukan alherin da na yi dominsu, za su ji tsoro su yi rawar jiki saboda dukan alheri da dukan wadata da na tanada musu.”

10Haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan wuri da ka ce ya zama kufai, ba mutum ko dabba, wato a biranen Yahuza da titunan Urushalima, inda ba kowa, ba mutum ko dabba a ciki, 11za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.” Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”

12Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu. 13A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da ke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.

14“Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza. 15A waɗannan kwanaki da a lokacin nan, zan sa wani reshe mai adalci ya fito daga zuriyar Dawuda, zai aikata gaskiya da adalci a ƙasar. 16A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, “‘Adalcinmu Ubangiji ne.” 17Gama ni Ubangiji na ce Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra'ila ba. 18Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”

19Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya ya ce, “Haka Ubangiji ya faɗa, 20idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu, 21to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma'aikatana, zai tashi. 22Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, hakanan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”

23Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya, 24“Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, “‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!” Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba. 25Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka'idodin da ke mulkin sammai da duniya ba, 26sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”

34

Faɗaka ga Zadakiya

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da ke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta. 2Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce wa Irmiya ya tafi, ya faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza cewa, “Ni Ubangiji, zan ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa ƙone shi da wuta. 3Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila. 4Ya Zadakiya, Sarkin Yahuza, ka ji maganar da ni Ubangiji na faɗa a kanka, ba za ka mutu ta wurin takobi ba. 5Za ka mutu da salama. Kamar yadda aka ƙona wa sarakuna marigayanka turare, haka kai ma mutane za su ƙona maka turare, za su yi makoki dominka suna cewa, “‘Kaito, sarki ya rasu.” Ni Ubangiji na faɗa.”

6Sai annabi Irmiya ya faɗa wa Zadakiya, Sarkin Yahuza, dukan maganan nan a Urushalima, 7sa'ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.

Ta da Alkawari game da Bayi, Ibraniyawa

8Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya bayan da Zadakiya ya yi alkawari da dukan mutanen Urushalima don a yi musu shelar ba da 'yanci, 9cewa kowa ya saki bayinsa, mata da maza, waɗanda ke Yahudawa. Kada kowa ya riƙe bawa wanda yake Bayahude, ɗan'uwansa. 10Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama'a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai 'yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka 'yantar da su. 11Daga baya kuwa suka sāke komo da waɗannan bayi, mata da maza waɗanda suka 'yantar, suka kuma mai da su bayi.

12Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce, 13“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari da kakanninku lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar daga bauta, na ce, 14“‘A shekara ta bakwai, dole ne ku 'yantar da 'yan'uwanku, Ibraniyawa, waɗanda aka sayar muku, suka kuwa bauta muku shekara shida. Dole ne ku 'yantar da su daga bautarku.” Amma kakanninku ba su kasa kunne gare ni ba. 15A 'yan kwanakin da suka wuce kuka yi abu mai kyau a gabana da kuka tuba, har kuka yi wa juna shelar 'yanci. Kuka yi alkawari a gabana a Haikalin da ake kira da sunana. 16Amma sai kuka sāke tunaninku, kuka ɓata sunana sa'ad da kowannenku ya komo da bayinsa, mata da maza, waɗanda kuka 'yantar, don su zauna yadda suke so. Ga shi kuma, kun komo da su su zama bayinku. 17Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. 18Mutanen da suka keta alkawarina, ba su kuma kiyaye maganar alkawarin da suka yi a gabana ba, sa'ad da suka raba ɗan maraƙi kashi biyu, suka bi ta tsakiyarsa, 19wato manyan fādawan Yahuza, da na Urushalima, da 'yan majalisa, da firistoci da dukan jama'ar ƙasa, waɗanda suka bi ta tsakanin rababben ɗan maraƙin, 20zan bashe su a hannun abokan gabansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsaye da namomin jeji. 21Zadakiya, Sarkin Yahuza kuwa, da sarakunansa, zan bashe su a hannun abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, wato sojojin Sarkin Babila, waɗanda suka tashi suka bar ku. 22Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”

35

Biyayyar Rekabawa

1A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya ke mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya, 2“Ka tafi gidan Rekabawa, ka yi magana da su, ka kawo su a Haikalin Ubangiji, cikin ɗayan ɗakunan, sa'an nan ka ba su ruwan inabi su sha.” 3Sai na ɗauki Yazaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da 'yan'uwansa, da dukan 'ya'yansa maza da dukan iyalin gidan Rekabawa. 4Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin 'ya'yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma'aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa. 5Sa'an nan na sa tuluna cike da ruwan inabi, da ƙoƙuna a gaban Rekabawa, sai na ce musu, “Ku sha ruwan inabi!”

6Sai suka amsa, suka ce, “Ba za mu sha ruwan inabi ba, gama Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya umarce mu cewa, “‘Ko ku, ko 'ya'yanku, ba za ku sha ruwan inabi ba har abada, 7ba kuma za ku gina ɗaki ba, ba kuwa za ku yi shuka ba, ba za ku yi dashe ba, ba za ku yi gonar inabi ba. Za ku zaune cikin alfarwai dukan kwanakin ranku, domin ku yi tsawon rai a ƙasar baƙuncinku.” 8Mu kuma muka yi biyayya da umarnin da Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya yi mana, cewa kada mu sha ruwan inabi, mu da matanmu, da 'ya'yanmu mata da maza, 9kada kuma mu gina wa kanmu gidajen zama. Ba mu da gonar inabi, ko gona ko iri. 10Amma a alfarwai muke zamanmu. Mun yi biyayya da dukan abin da Yonadab kakanmu ya umarce mu. 11Amma sa'ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, “‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.” Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”

12Sa'an nan Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce, 13“Haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa, ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima cewa, “‘Ba za ku karɓi umarnina, ku kasa kunne ga maganata ba?” 14Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa 'ya'yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba. 15Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba. 16'Ya'yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama'an nan ba su yi mini biyayya ba. 17Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.”

18Sai Irmiya ya ce wa Rekabawa, “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, “‘Tun da ya ke kun kiyaye dukan abin da Yonadab kakanku ya umarce ku, 19saboda haka Yonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa magaji wanda zai tsaya a gabana ba.”

36

An Ƙone Littafi

1A sa'ad da Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, yana shekara huɗu da sarauta, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce, 2“Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra'ila, da Yahuza, da dukan al'ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau. 3Mai yiwuwa ne idan mutanen Yahuza suka ji dukan masifar da na yi niyya in aukar musu da ita, za su bar mugayen ayyukansu don in gafarta musu muguntarsu da zunubinsu.”

4Sai Irmiya ya kirawo Baruk ɗan Neriya. Baruk kuwa ya rubuta maganar da Irmiya ya faɗa masa a takarda, wato dukan maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. 5Sai Irmiya ya umarci Baruk, ya ce, “An hana ni zuwa Haikali, 6saboda haka kai za ka tafi. A ranar azumi za ka karanta wa mutane maganar Ubangiji, wadda ke a takardar da ka rubuta ta wurin shibtar da na yi maka. Ka karanta ta a cikin Haikali, a gaban mutanen Yahuza waɗanda suka fito daga biranensu. 7Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.” 8Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya umarce shi. Ya karanta takardan nan ta maganar Ubangiji a Haikalin Ubangiji.

9A watan tara a shekara ta biyar ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, sai dukan jama'ar Urushalima da dukan jama'ar da suka zo Urushalima daga biranen Yahuza suka yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji. 10Sai Baruk ya karanta maganar Irmiya wadda ke a takardar, kowa yana ji, a cikin Haikali a ɗakin Gemariya ɗan Shafan, magatakarda. Ɗakinsa yana a shirayi na bisa a hanyar shiga Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11Sa'ad da Mikaiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji da ke a littafin, 12sai ya gangara gidan sarki, ya shiga ɗakin magatakarda, inda dukan shugabanni suke zaune, wato Elishama magatakarda, da Delaiya ɗan Shemaiya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemariya ɗan Shafan, da Zadakiya ɗan Hananiya, da dukan sarakuna. 13Sai Mikaiya ya faɗa musu dukan maganar da ya ji sa'ad da Baruk ya karanta littafin a kunnuwan jama'a. 14Sai dukan sarakunan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya faɗa wa Baruk ya kawo littafin nan da ya karanta wa jama'a. Sai Baruk ɗan Neriya ya ɗauki littafin ya je wurinsu. 15Suka ce masa ya zauna, ya karanta musu littafin. Baruk kuwa ya karanta musu. 16Da suka ji dukan maganar, suka dubi juna a firgice, suka ce wa Baruk, “Ai, sai mu faɗa wa sarki wannan magana.” 17Suka kuma tambayi Baruk, suka ce, “Ka faɗa mana yadda ka yi ka rubuta wannan magana. Ya yi maka shibta ne?”

18Sai Baruk ya ce musu, “Ya yi mini shibtar dukan wannan magana ne, na kuwa rubuta su da tawada a takarda.”

19Sarakunan kuwa suka ce wa Baruk, “Ka tafi, da kai da Irmiya ku ɓuya kada ku bari kowa ya san wurin da kuke.”

20Suka tafi zauren sarki bayan sun ajiye littafin a ɗakin Elishama, magatakarda, suka sanar da sarki dukan abin da ke cikin littafin. 21Sarki ya aiki Yehudi ya je ya kawo littafin. Sai ya je ya ɗauko littafin daga ɗakin Elishama magatakarda. Yehudi kuwa ya karanta wa sarki tare da dukan sarakunan da suke tsaye kewaye da sarkin. 22A watan tara ne, sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, ga wuta tana ci cikin kasko a gabansa. 23Da Yehudi ya karanta sakin layi uku ko huɗu sai sarki ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da ke ci a kasko, da haka ya ƙone littafin duka. 24Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki. 25Ko da ya ke Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su. 26Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!

27Bayan da sarki ya ƙone littafin da Baruk ya rubuta ta wurin shibtar da Irmiya ya yi masa, sai Ubangiji ya yi wa Irmiya magana, ya ce, 28ya ɗauki wata takarda ya rubuta dukan maganar da ke cikin littafin da Yehoyakim Sarkin Yahuza, ya ƙone. 29Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, “‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?” 30Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami māgaji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi. 31Zan hukunta shi, shi da zuriyarsa, da barorinsa saboda muguntarsu. Zan kawo dukan masifar da na hurta a kansu, da a kan mazaunan Urushalima, da a kan mutanen Yahuza, amma sun ƙi ji.”

32Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da ke a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.

37

An Sa Irmiya a Kurkuku

1Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim. 2Amma shi da barorinsa, da mutanen ƙasar, ba wanda ya kasa kunne ga maganar Ubangiji wadda ya yi musu ta bakin annabi Irmiya.

3Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.” 4A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna. 5Rundunar sojojin Fir'auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.

6Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce, 7“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, “‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar. 8Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta. 9Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo. 10Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda ke yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.”

11Da rundunar sojojin Kaldiyawa ta janye daga Urushalima saboda zuwan rundunar sojojin Fir'auna, 12sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi. 13A sa'ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”

14Sai Irmiya ya ce, “Ƙarya ce, ni ba gudu zuwa wurin Kaldiyawa nake yi ba.” Amma Irija bai yarda ba, sai ya kai shi wurin shugabanni. 15Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku. 16Irmiya ya yi kwanaki da yawa can cikin kurkukun.

Zadakiya ya Nemi Shawara ga Irmiya

17Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?” Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.” 18Sai kuma ya tambayi sarki Zadakiya ya ce, “Wane laifi na yi maka, ko barorinka, ko wannan jama'a da ka sa ni a kurkuku? 19Ina annabawanku waɗanda suka yi maka annabci cewa, “‘Sarkin Babila ba zai kawo wa ƙasarku yaƙi ba?” 20Yanzu ya maigirma sarki, ina roƙonka ka ji wannan roƙo da nake yi maka, kada ka mai da ni a gidan Jonatan magatakarda, domin kada in mutu a can.”

21Sai sarki Zadakiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a gidan waƙafi. Aka riƙa ba shi malmalar abinci daga unguwar masu tuya kowace rana, har lokacin da abinci ya ƙare duka a birnin. Haka kuwa Irmiya ya zauna a gidan waƙafi.

38

An Fitar da Irmiya daga Rijiya Marar Ruwa

1Shefatiya ɗan Mattan, da Gedaliya ɗan Fashur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da Fashur ɗan Malkiya, suka ji maganar da Irmiya ke faɗa wa dukan mutane cewa, 2“Ubangiji ya ce wanda ya zauna a wannan birni zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma wanda ya fita ya je wurin Kaldiyawa zai rayu, zai sami ransa kamar ganimar yaƙi. 3Gama Ubangiji ya ce, hakika za a ba da wannan birni a hannun rundunar sojojin Sarkin Babila su ci shi.”

4Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”

5Sarki Zadakiya ya ce, “Ai, ga shi nan a hannunku, gama sarki ba zai yi abin da ba ku so ba.” 6Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda ke gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.

7Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda ke a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu. 8Sai Ebed-melek ya fita, ya tafi gaban sarki, ya ce masa, 9“Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.” 10Sa'an nan sarki ya umarci Ebedmelek, mutumin Habasha, ya tafi da mutum talatin su tsamo annabi Irmiya daga cikin rijiyar kafin ya mutu. 11Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar. 12Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa. 13Suka jawo Irmiya da igiyoyi, suka fito da shi daga rijiya. Irmiya kuwa ya zauna a gidan waƙafi.

Zadakiya ya Nemi Shawarar Irmiya

14Sarki Zadakiya ya aika a kirawo annabi Irmiya. Ya tafi ya sadu da Irmiya a ƙofa ta uku ta Haikalin Ubangiji. Sarki kuwa ya ce wa Irmiya, “Zan yi maka tambaya, kada kuwa ka ɓoye mini kome.”

15Irmiya kuwa ya ce wa Zadakiya, “Idan na faɗa maka gaskiya za ka kashe ni, idan kuma na ba ka shawara, ba za ka karɓi shawarata ba.”

16Sarki Zadakiya ya rantse wa Irmiya a ɓoye, ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda ke ba mu rai, ba zan kashe ka ko in bashe ka a hannun waɗannan mutane da ke neman ranka ba.”

17Irmiya ya ce wa Zadakiya, “Haka Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, idan ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila, za ka tsira, ba kuwa za a ƙone birnin da wuta ba, kai da gidanka za ku tsira. 18Amma idan ba ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila ba, to, za a ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa, za su ƙone shi da wuta. Kai kuma ba za ka tsira daga hannunsu ba.”

19Sarki Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawa waɗanda suka gudu zuwa wurin Kaldiyawa. Kila a bashe ni a hannunsu, su ci mutuncina.”

20Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira. 21Amma idan ka ƙi miƙa wuya, to, ga abin da Ubangiji ya nuna mini a wahayi. 22Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa, “‘Aminanka sun ruɗe ka, Sun rinjaye ka. Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutse cikin laka, Sai suka rabu da kai.”

23“Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”

24Sai Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan magana, kai kuwa ba za a kashe ka ba. 25Idan sarakuna suka ji, wai na yi magana da kai, in suka zo wurinka, suka ce, “‘Ka faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da abin da sarki ya faɗa maka, kada ka ɓoye mana kome mu kuwa ba za mu kashe ka ba.” 26Sai ka ce musu, “‘Na roƙi sarki da ladabi don kada ya mai da ni a gidan Jonatan, don kada in mutu a can.” 27Dukan sarakuna suka tafi wurin Irmiya suka tambaye shi. Shi kuwa ya amsa musu yadda sarki ya umarce shi. Sai suka daina magana da shi, tun da ya ke ba wanda ya ji maganar da ya yi da sarki. 28Irmiya kuwa ya yi zamansa a gidan waƙafi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi.

39

Faɗuwar Urushalima

(2 Sar 24.20ū25.21; 2 Tar 36.17-21; Irm 52.3-30)

1A watan goma a na shekara ta tara ta sarautar sarki Zadikiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, da dukan sojojinsa suka zo, suka kewaye Urushalima da yaƙi. 2A rana ta tara ga watan huɗu, a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya, sai aka huda garun birnin.

3Sa'an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.

4Sa'ad da Zadakiya, Sarkin Yahuza, da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu, suka fita daga birnin da dare, ta hanyar gonar sarki a ƙofar da ke a tsakanin garu biyu. Suka nufi zuwa wajen Araba. 5Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci. 6Sarkin Babila ya kashe 'ya'yan Zadakiya, maza, a Ribla a kan idon Zadakiya. Ya kashe dukan shugabannin Yahuza. 7Ya kuma ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babila. 8Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima. 9Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa. 10Amma ya bar matalauta waɗanda ba su da kome a ƙasar. Ya ba su gonakin inabi da waɗansu gonaki a ran nan.

Nebukadnezzar ya Lura da Irmiya

11Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce, 12“Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.” 13Sai Nebuzaradan shugaban matsara, da Nebushazban, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan shugabannin Sarkin Babila, 14suka aika aka kawo Irmiya daga gidan waƙafi, suka ba da Irmiya amana ga Gedaliya, ɗan Ahikam ɗan Shafan, don ya kai shi gida. Da haka Irmiya ya zauna tare da mutane.

Ebed-melek yana Sa Zuciya ga Kuɓuta

15Ubangiji ya yi magana da Irmiya a lokacin da aka kulle shi a gidan waƙafi, ya ce, 16“Ka tafi ka faɗa wa Ebedmelek mutumin Habasha, cewa Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, “‘Zan sa masifa, ba alheri ba, ta auko wa wannan birni. Wannan kuwa zai faru a kan idanunka a wannan rana. 17Amma a ranan nan, ni Ubangiji zan cece ka, ba za a ba da kai a hannun mutanen da kake jin tsoronsu ba. 18Gama hakika zan cece ka, ba za ka mutu ta takobi ba. Za ka sami ranka kamar ganimar yaƙi, domin ka dogara gare ni, ni Ubangiji na faɗa.”

40

Irmiya da waɗanda suka Ragu sun Zauna tare da Gedaliya

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya bayan da Nebuzaradan shugaban matsara ya sake shi daga Rama, sa'ad da ya yi masa ƙuƙumi tare da waɗanda aka kwaso daga Urushalima da Yahuza, za su Babila.

2Shugaban matsara ya ware Irmiya, sa'an nan ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ne ya hurta wannan masifa a kan wurin nan. 3Ga shi kuwa, ya yi kamar yadda ya faɗa, domin kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, don haka wannan masifa ta auko muku. 4Yau na kwance ƙuƙumin da ke a wuyanka, idan ka ga ya fi maka kyau, ka zo mu tafi tare zuwa Babila, to, sai ka zo, zan lura da kai da kyau, amma idan ba ka ga haka ya yi maka daidai ba, to, kada ka bi ni. Ga dukan ƙasa shimfiɗe a gabanka, ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.”

5Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa'an nan ya sallame shi. 6Irmiya kuwa ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa, ya zauna tare da shi da mutanen da suka ragu a ƙasar.

7Sa'ad da shugabannin sojoji waɗanda ke a karkarar Yahudiya tare da mutanensu, suka ji labari Sarkin Babila ya sa Gedaliya ɗan Ahikam ya zama mai mulkin ƙasar, a kan matalauta, wato mata da maza, da yara na ƙasar, waɗanda ba a kwashe su zuwa bautar talala a Babila ba, 8sai shugabannin, wato Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan da Jonatan, 'ya'yan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, da 'ya'yan Efai, mutumin Netofa, da Yazaniya ɗan mutumin Ma'aka suka tafi tare da mutanensu zuwa wurin Gedaliya a Mizfa. 9Gedaliya ɗan Ahikam, jikan shafan ya rantse musu da mutanensu, ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Kaldiyawa, ku yi zamanku a ƙasar, ku bauta wa Sarkin Babila, za ku kuwa zauna lafiya. 10Amma ni zan zauna a Mizfa, in zama wakilinku a wurin Kaldiyawa waɗanda za su zo wurinmu. Ku tattara inabi, da 'ya'yan itatuwa na kaka, da man zaitun, ku tanada su a gidajenku, ku zauna a garuruwan da kuka ci.” 11Haka kuma Yahudawan da ke a Mowab, da Ammon, da Edom, da kuma sauran ƙasashe suka ji, cewa Sarkin Babila ya bar waɗansu mutane a Yahuza, ya kuma shugabantar da Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan a kansu, 12sai dukan Yahudawa suka koma daga inda aka kora su zuwa ƙasar Yahuza. Suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Suka tattara ruwan inabi da 'ya'yan itatuwa na kaka da yawa.

Maƙarƙashiyar Isma'ilu gāba da Gedaliya

13Yohenan ɗan Kareya kuwa, tare da dukan shugabannin sojojin da ke cikin sansani a karkara, suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. 14Suka ce masa, “Ko ka sani Ba'alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba. 15Sai Yohenan ɗan Kareya ya yi magana da Gedaliya a Mizfa a asirce ya ce, “Ka bar ni in tafi in kashe Isma'ilu ɗan Netaniya, ba wanda zai sani. Don me shi zai kashe ka, ya watsa dukan Yahudawan da ke tare da kai, har sauran Yahudawan da suka ragu su halaka.”

16Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohenan ɗan Kareya, “Kada ka kuskura ka yi wannan abu, gama ƙarya ce kake yi wa Isma'ilu.”

41

1A watan bakwai sai Isma'ilu ɗan Netaniya, ɗan Elishama, na cikin zuriyar sarauta, ɗaya daga cikin ma'aikatan sarki, ya zo a wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa tare da mutum goma. Sa'ad da suke cin abinci tare a Mizfa, 2Isma'ilu ɗan Netaniya, da mutanen nan goma da ke tare da shi, suka tashi suka sare Gedaliya ɗan Ahikam ɗan shafan, da takobi, suka kashe shi, wato Gedaliya wanda Sarkin Babila ya naɗa ya zama mai mulkin ƙasar. 3Isma'ilu kuma ya kashe dukan Yahudawa da ke tare da Gedaliya a Mizfa da waɗansu sojojin Kaldiyawa da ke a wurin.

4Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani, 5sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji. 6Sai Isma'ilu ɗan Netaniya ya fito daga cikin Mizfa yana kuka, don ya tarye su. Da ya sadu da su, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam!” 7Sa'ad da suka shiga birnin, sai Isma'ila ɗan Nataniya da mutanen da ke tare da shi suka kashe su, suka jefa su a wata rijiya.

8Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma'ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha'ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba. 9Rijiyar da Isma'ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba'asha Sarkin Isra'ila. Isma'ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe. 10Sai Isma'ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da ke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama'ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma'ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.

11Amma sa'ad da Yohenan ɗan Kareya, tare da dukan shugabannin sojoji da ke tare da shi suka ji irin wannan mugun aiki wanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya yi, 12sai suka kwashe mutanensu duka, suka tafi su yi yaƙi da Isma'ilu ɗan Netaniya. Suka iske shi a babban tafkin da ke a Gibeyon. 13Sa'ad da dukan jama'ar da Isma'ilu ya kwashe suka ga Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji tare da shi, sai suka yi murna. 14Dukan mutanen nan da Isma'ilu ya kwashe su ganima daga Mizfa, suka juya, suka koma wurin Yohenan ɗan Kareya. 15Amma Isma'ilu ɗan Netaniya tare da mutum takwas suka tsere suka gudu zuwa wurin Ammonawa.

16Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da ke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon. 17Suka fa tafi suka zauna a wurin Kimham kusa da Baitalami. Suna nufin su tafi Masar, 18don gudun Kaldiyawa, gama suna jin tsoronsu, domin Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam wanda Sarkin Babila ya naɗa shi mai mulkin ƙasa.

42

Jawabin Irmiya ga Yohenan

1Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama'a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo, 2suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka. 3Ka yi mana addu'a domin Ubangiji Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.”

4Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”

5Sa'an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba. 6Ko magari ne ko mugu ne, za mu yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu wanda muka aike ka wurinsa, gama zai zama alheri a gare mu idan mun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu.”

7Bayan kwana goma sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya. 8Sai Irmiya ya kira Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda ke tare da shi, da dukan jama'a tun daga ƙarami har zuwa babba. 9Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda kuka aike ni da koke-kokenku wurinsa ya ce, 10“‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku. 11Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,” in ji Ubangiji, “‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa. 12Zan yi muku jinƙai in sa sarkin ya ji ƙanku, ya bar ku ku zauna a ƙasarku.”

13“Amma idan kuka ce ba za ku zauna a wannan ƙasa ba, kuka ƙi yin biyayya da muryar Ubangiji Allahnku, 14kuna cewa, “‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.” 15To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, “‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can, 16to, takobin nan da kuke jin tsoro, zai ci muku can a ƙasar Masar, yunwan nan kuma da kuke jin tsoro za ta bi ku zuwa Masar ta tsananta muku, a can za ku mutu. 17Duk waɗanda suka sa gaba zuwa Masar domin su zauna can, da takobi, da yunwa, da annoba su ne ajalinsu. Ba wanda zai ragu, ba wanda zai tsira daga masifar da zan aukar musu.”

18“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.”

19“Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, “‘Kada ku tafi Masar.” Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau, 20cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, “‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.” 21A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba. 22Domin haka yanzu fa ku sani takobi, da yunwa, da annoba, su ne ajalinku a wurin can da kuke sha'awar ku zauna.”

43

Tafiya zuwa Masar

1Sa'ad da Irmiya ya gama faɗa wa dukan jama'a maganar da Ubangiji Allahnsu ya aiko musu da ita, 2sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan 'yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba! 3Amma Baruk ɗan Neriya shi ne ya sa ka faɗi wannan magana gāba da mu, don ka bashe mu a hannun Kaldiyawa domin su kashe mu, ko kuwa su kai mu bauta a Babila.” 4Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama'a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba. 5Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al'ummai, inda aka kora su, 6mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya. 7Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.

8Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce, 9“Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir'auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza, 10ka kuma ce musu, “‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin. 11Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi. 12Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya. 13Zai kuma farfashe al'amudan duwatsu na On a ƙasar Masar. Zai ƙone gidajen gumakan Masar da wuta.”

44

Jawabin Ubangiji zuwa ga Yahudawan da ke Masar

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan dukan Yahudawan da ke zaune a ƙasar Masar, a garin Migdol, da Tafanes, da Memfis, da dukan ƙasar Fatros, ya ce, 2“Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda ke zaune a cikinsu, 3domin mutanen da ke cikinsu sun aikata mugayen abubuwa da suka tsokane ni. Sun miƙa wa gumaka hadayu, suka kuma bauta musu, ko da ya ke su, ko ku, ko kakanninku, ba ku san su ba. 4Na yi ta aika muku da dukan bayina annabawa waɗanda suka faɗa muku kada ku aikata wannan mugun abin banƙyama. 5Amma ba su kasa kunne ba, ba su kuwa ji ba, da za su juyo daga mugayen ayyukansu na miƙa wa gumaka hadayu. 6Saboda haka fushina ya yi zafi a kan garuruwan Yahuza da titunan Urushalima, don haka a yanzu sun lalace, suka zama kufai.

7“Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu? 8Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la'ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya. 9Ko kun manta da mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakunan Yahuza da na matansu, da naku, da na matanku, waɗanda suka aikata a ƙasar Yahuza da kan titunan Urushalima? 10Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.

11“Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka. 12Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la'antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya. 13Zan hukunta dukan waɗanda ke zaune a Masar kamar yadda na hukunta wa Urushalima da takobi, da yunwa, da annoba. 14Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”

15Sai dukan mazan da suka sani matansu sun miƙa wa gumaka hadayu, da dukan matan da ke tsaye a wurin, da dukan Yahudawan da ke zaune a Fatros, babban taron jama'a, suka ce wa Irmiya, 16“Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba! 17Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala. 18Amma tun da muka daina miƙa wa sarauniyar sama hadayu, da hadayu na sha, ba mu da kome, sai dai takobi da yunwa suke kashe mu.”

19Mata kuma suka ce, “Sa'ad da muka toya waina ga siffar sarauniyar sama, muka miƙa mata hadayu, da hadayu na sha, ai, mazanmu sun goyi bayan abin da muka yi.”

20Sa'an nan Irmiya ya ce wa dukan mutane, mata da maza, waɗanda suka ba shi irin amsan nan, ya ce, 21“A kan turaren da ku da kakanninku, da sarakunanku, da shugabanninku, da mutanen ƙasar, kuka ƙona a garuruwan Yahuza da a titunan Urushalima, kuna tsammani Ubangiji bai san su ba, ko kuna tsammani ya manta? 22Ubangiji ba zai yarda da mugayen ayyukanku ba, da ƙazantarku da kuka aikata, don haka ƙasarku a yau ta zama kufai ba mai zama a cikinta. Ta zama abin ƙyama da la'ana. 23Saboda kun ƙona turare, kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, ba ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da sharuɗansa ba, shi ya sa wannan masifa ta auko muku a yau.”

24Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane duk da mata, “Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da ke a Masar. 25Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “‘Ku da matanku kun faɗa da bakinku, kun kuma aikata da hannuwanku, cewa za ku aikata wa'adodin da kuka yi na ƙona turare, da miƙa hadayu na sha ga sarauniyar sama.” To, sai ku tabbatar da wa'adodinku, ku cika su! 26Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da ke zaune a ƙasar Masar. “‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da ke ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.” 27Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda ke a ƙasar Masar. 28“‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa. 29Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika. 30Zan kuma ba da Fir'auna Hofra, Sarkin Masar, a hannun abokan gabansa, da waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zadakiya, Sarkin Yahuza, a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila wanda ya zama abokin gābansa, ya kuwa nemi ransa.”

45

Jawabin Irmiya ga Baruk

1A shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Baruk ɗan Neriya ya rubuta abin da Irmiya ya faɗa masa. 2“Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce maka, kai Baruk, 3kai ka ce, “‘Kaitona, gama Ubangiji ya ƙara baƙin ciki a kan wahalaina, na gaji da nishina, ba ni da hutu!”

4“Sai ka faɗa wa Baruk cewa, “‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum. 5Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan 'yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.”

46

Annabci a kan Masar

1Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma. 2Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda ke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.

3Masarawa suka yi ihu, suka ce, “Ku shirya kutufani da garkuwa, Ku matso zuwa wurin yaƙi!

4Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, ku hau! Ku tsaya a wurarenku da kwalkwali a ka! Ku wasa māsunku! Ku sa kayan yaƙi!”

5Ubangiji ya yi tambaya ya ce, “Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, An ci sojojinsu, suna gudu, Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a kowane sashi.”

6Masu saurin gudu ba za su tsere ba, Hakanan kuma jarumi, A arewa a gefen Kogin Yufiretis, Sun yi tuntuɓe, sun fādi.

7Wanene wannan mai tashi kamar Kogin Nilu, Kamar kogunan da ruwansu ke ambaliya>

8Masar tana tashi kamar Nilu, Kamar kogunan da ruwansu ke ambaliya. Masar ta ce, “Zan tashi, in rufe duniya, Zan hallaka birane da mazauna cikinsu.”

9Ku haura, ku dawakai, Ku yi sukuwar hauka, ku karusai! Bari sojoji su fito, Mutanen Habasha da Fut masu riƙon garkuwoyi, Da mutanen Lud, waɗanda suka iya riƙon baka.

10Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai Runduna ce, Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama wa maƙiyansa. Takobi zai ci, ya ƙoshi, Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna zai hallaka maƙiyansa, A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.

11Ku mutanen Masar, ku haura zuwa Gileyad Don ku samo ganye! A banza kuke morar magunguna, Ba za ku warke ba.

12Kunyarku ta kai cikin sauran al'umma, Kukanku kuma ya cika duniya. Soja na faɗuwa bisa kan soja. Dukansu biyu sun faɗi tare.

13Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.

14“Ku yi shelarsa cikin garuruwan Masar, Cikin Migdol, da Memfis, da Tafanes, Ku ce, “‘Ku tsaya, ku yi shiri, Gama takobi yana cin waɗanda ke kewaye da ku!”

15Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi, Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba? Domin Ubangiji ya tunkuɗe shi ƙasa!

16Sun yi ta fāɗuwa, Suna faɗuwa a kan juna, Sai suka ce, “‘Mu tashi mu koma wurin mutanenmu, Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu daga takobin azzalumi!”

17“Ku ba Fir'auna Sarkin Masar sabon suna, “‘Mai yawan surutu, wanda bai rifci zarafi ba!”

18Ni wanda sunana Ubangiji Mai Runduna Sarki ne, Na rantse da raina, wani zai ɓullo, Kamar Tabor a cikin tsaunuka, Ko kuwa kamar Karmel a bakin teku.

19Ya ku mazaunan Masar, Ku shirya kayanku don zuwa bauta, Gama Memfis za ta lalace, ta zama kufai, Ba mai zama a ciki.

20“Masar kyakkyawar karsana ce, Amma bobuwa daga arewa ta aukar mata!

21Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa ne, masu yawan kitse, Sun ba da baya, sun gudu, ba su tsaya ba, Domin ranar masifarsu ta zo, Lokacin halakarsu ya yi.

22Masar tana gudu, tana huci kamar maciji, Gama abokan gābanta suna zuwa da ƙarfi, Za su faɗo mata da gatura kamar masu saran itatuwa.

23Ni Ubangiji na ce, za su sari kurminta, Ko da ya ke ba su ƙirguwa, Gama suna da yawa kamar fara, Ba su lasaftuwa.

24Za a kunyatar da mutanen Masar, An bashe su a hannun mutanen arewa.”

25Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda ke dogara gare shi. 26Zan bashe su a hannun waɗanda ke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.

27“Ya bawana Yakubu, kada ka ji tsoro, Kada ka firgita, ya Isra'ila. Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa da rai kwance, Ba wanda zai razanar da shi.

28Ni Ubangiji na ce, Kada ka ji tsoro, ya bawana Yakubu, Gama ina tare da kai. Zan hallaka dukan sauran al'umma sarai inda na kora ka. Amma ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hukunta ka yadda ya kamata, Ba zan bar ka ba hukunci ba.”

47

Jawabin Ubangiji a kan Filistiyawa

1Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa. 2Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da ke ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da ke cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.

3Da jin takawar kofatan dawakai, Da amon karusai da ƙafafun karusai, Ubanni ba su juya, su dubi 'ya'yansu ba, Domin hannuwansu sun yi laƙwas,

4Domin lokacin hallaka dukan Filistiyawa ya yi. Za a datse wa Taya da Sidon kowane taimakon da ya ragu, Gama Ubangiji zai hallaka Filistiyawa Waɗanda ke baƙin teku na Kaftor.

5Baƙin ciki zalla ya sami Gaza, Ashkelon ta lalace. Ya ƙattin mutane, yaushe za ku daina tsattsage kanku>

6Ya takobin Ubangiji, yaushe za ka huta? Sai ka koma ƙubenka, Ka huta, ka yi shiru!

7Ƙaƙa zai huta, tun da ni Ubangiji ne na umarce shi? Ni Ubangiji na umarce shi ya yi yaƙi da Ashkelon Da mazauna a bakin teku.”

48

Jawabin Ubangiji a kan Mowab

1Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa a kan Mowab, “Kaiton Nebo, gama ta lalace! An kunyatar da Kiriyatayim, an ci ta da yaƙi, An kunyatar da kagararta, an rushe ta.

2Darajar Mowab ta ƙare. Ana shirya mata maƙarƙashiya a Heshbon, “‘Bari mu je mu ɓata ta daga zaman al'umma!” Ke kuma Madmen za ki yi shiru, Takobi zai runtume ki.

3Muryar kuka daga Horonayim tana cewa, “‘Risɓewa da babbar halaka!”

4“An hallakar da Mowab, Ƙanananta suna kuka.

5Gama a hawan Luhit, za su hau da kuka, Gama a gangaren Horonayim, Suna jin kukan wahalar halaka.

6Ku gudu don ku tserar da rayukanku, Ku gudu kamar jakin jeji.

7“Kun dogara ga ƙarfinku da wadatarku, Amma yanzu za a ci ku da yaƙi, Kemosh zai tafi bauta Tare da firistocinsa da shugabanninsa.

8Mai hallakarwa zai shiga kowane gari, Don haka ba garin da zai tsira. Kwari da tudu za su lalace, Ni Ubangiji na faɗa.

9Ku ba Mowab fikafikai, Gama za ta tashi ta gudu, Garuruwanta za su zama kango, Ba mazauna cikinsu.

10“La'ananne ne shi wanda ke yin aikin Ubangiji da ha'inci, La'ananne ne shi kuma wanda ya hana wa takobinsa jini.

11“Tun daga ƙuruciya Mowab tana zama lami lafiya, Hankali kwance, Ba a jujjuya ta daga tulu zuwa tulu ba, Ba a taɓa kai ta bauta ba, Domin haka daɗin ɗanɗanonta bai rabu da ita ba, Ƙanshinta kuma bai sāke ba.”

12Ubangiji ya ce, “Domin haka kwanaki suna zuwa, sa'ad da zai aika da mutane su tuntsurar da tuluna, su zubar da ruwan inabi, su farfasa tulunanta. 13Sa'an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra'ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.

14“Don me kake cewa, “‘Mu jarumawa ne, mayaƙan gaske?”

15Mai hallaka Mowab da garuruwanta ya taho, Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sun gangara mayanka, Ni sarki, mai suna Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.

16Masifar Mowab ta kusato, Halakarta kuma tana gaggabtowa.

17“Ku yi makoki dominta, ku da ke kewaye da ita, Dukanku da kuka san sunanta, ku ce, “‘Ƙaƙa sandan sarauta mai iko Da sanda mai daraja ya karye?”

18Ku da ke zaune a Dibon, Ku sauka daga wurin zamanku mai daraja, Ku zauna a busasshiyar ƙasa, Gama mai hallaka Mowab ya zo ya yi gab da ku. Ya riga ya rushe kagararku.

19Ku mazaunan Arower, Ku tsaya a kan hanya, ku jira, Ku tambayi wanda yake gudu Da wanda ke tserewa, Abin da ya faru.

20An kunyatar da Mowab, ta rushe. Ku yi kuka dominta, Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab ta halaka.

21“Hukunci ya auka kan garuruwan da ke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat, 22da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim, 23da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon, 24da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa. 25An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.

26“Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya. 27Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.

28“Ku mazaunan Mowab, ku bar garuruwanku, Ku tafi, ku zauna a kogwanni, Ku zama kamar kurciya wadda ke yin sheƙarta a bakin kwazazzabo.

29Mun ji labarin girmankan Mowab, da ɗaukaka kanta, Da alfarmarta, da izgilinta, Tana da girmankai ƙwarai.

30Ni Ubangiji na san Mowab tana da girmankai, Alfarmarta ta banza ce, Ayyukanta kuma na banza ne.

31Don haka zan yi kuka saboda Mowab duka, Zan kuma yi baƙin ciki saboda mutanen Kir-heres.

32Zan yi kuka saboda kurangar inabin Sibma Fiye da yadda zan yi kuka saboda mutanen Yazar. Rassanku sun haye teku har sun kai Yazar, Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan 'ya'yan itatuwanku da damuna Da kan amfanin inabinku.

33An ɗauke farin ciki da murna daga ƙasa mai albarka ta Mowab, Na hana ruwan inabi malala daga wurin matsewarsa, Ba wanda ke matse shi, yana ihu na murna, Ihun da ake yi ba na murna ba ne.

34“Mutanen Heshbon da na Eleyale suna kururuwa ana iya jin kururuwansu a Yahaza. Ana iya jinta kuma a Zowar, da Horonayim, da Eglat-shelishiya. Har ma ruwan Nimra ya ƙafe. 35Zan hana mutanen Mowab miƙa hadayu na ƙonawa a tuddai, da miƙa wa gumakansu sadaka, ni Ubangiji na faɗa.

36“Zuciyata tana makoki domin Mowab da Kir-heres kamar wanda ke kukan makoki da sarewa saboda wadatarsu ta ƙare. 37Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki. 38Ba abin da ake yi a bisa kan soraye da dandali na Mowab sai baƙin ciki, gama na farfashe Mowab kamar tulun da ba a so, ni Ubangiji na faɗa. 39An farfashe Mowab, ta yi kuka, ta kunyata! Ta zama abin dariya da abin tsoro ga waɗanda ke kewaye da ita.

40“Ni Ubangiji na ce, Wani zai yi firiya da sauri kamar gaggafa, Zai shimfiɗa fikafikansa a kan Mowab.

41Za a ci garuruwa da kagarai da yaƙi, A wannan rana zukatan sojojin Mowab Za su zama kamar zuciyar macen da ke naƙuda.

42Za a hallaka Mowab daga zaman al'umma, Domin ta tayar wa Ubangiji.

43Tsoro, da rami, da tarko suna jiranku, Ya mazaunan Mowab, Ni Ubangiji na faɗa.

44Wanda ya guje wa tsoro, Zai fāɗa a rami, Wanda kuma ya fito daga cikin rami, Tarko zai kama shi. Gama na sa wa Mowab lokacin da zan hukunta ta, Ni Ubangiji na faɗa.

45“A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yan gudun hijira suna tsaye ba ƙarfi. Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon, Harshen wuta kuma ya fito daga Sihon, Ta ƙone goshin Mowab da ƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.

46Kaitonku, ya Mowabawa! Mutanen Kemosh sun lalace, An kai 'ya'yanku mata da maza cikin bauta.

47“Amma zan komar da mutanen Mowab nan gaba, Ni Ubangiji na faɗa.” Wannan shi ne hukuncin Mowab.

49

Jawabin Ubangiji a kan Ammonawa

1Wannan shi ne abin da Ubangiji ya faɗa akan Ammonawa, “Isra'ila ba shi da 'ya'ya ne? Ko kuwa ba shi da māgada ne? Me ya sa waɗanda ke bautar Milkom suka mallaki inda Gad ke zama, Suka zauna a garuruwanta>

2Domin haka lokaci yana zuwa, Sa'ad da zan sa mutanen garin Rabba ta Ammon su ji busar yaƙi. Rabba za ta zama kufai, Za a ƙone ƙauyukanta da wuta, Sa'an nan Isra'ila zai mallaki waɗanda suka mallake shi. Ni Ubangiji na faɗa.

3“Ki yi kuka, ya Heshbon, gama Ai ta zama kufai! Ku yi kuka, ku mutanen Rabba, ku sa tufafin makoki. Ku yi gudu, kuna kai da kawowa a cikin garuka, Gama za a kai Milkom bauta tare da firistocinsa da wakilansa.

4Me ya sa kuke taƙama da ƙarfinku, Ƙarfinku da ke ƙarewa, ku mutane marasa aminci? Kun dogara ga dukiyarku, Kuna cewa, “‘Wanene zai iya gāba da mu?”

5Ga shi, zan kawo muku razana daga waɗanda ke kewaye da ku, Za a kore ku, kowane mutum zai kama gabansa, Ba wanda zai tattara 'yan gudun hijira. Ni Ubangiji Allah Mai Runduna na faɗa.

6“Amma daga baya zan sa Ammonawa su wadata kuma, Ni Ubangiji na faɗa.”

Jawabin Ubangiji a kan Edom

7Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa a kan Edom, “Ba hikima kuma a cikin Teman? Shawara ta lalace a wurin masu basira? Hikima ta lalace ne>

8Ku mazaunan Dedan, ku juya, ku gudu, Ku ɓuya cikin zurfafa, Gama zan kawo masifa a kan Isuwa A lokacin da zan hukunta shi,

9Idan masu tsinkar 'ya'yan inabi sun zo wurinka Ba za su rage abin kala ba? Idan kuma ɓarayi sun zo da dare, Za su ɗauki iyakacin abin da suke so kurum.

10Amma na tsiraita Isuwa sarai, Na buɗe wuraren ɓuyarsa, Har bai iya ɓoye kansa ba, An hallakar da mutanen Isuwa Tare da 'yan'uwansa da maƙwabtansa, Ba wanda ya ragu.

11Ka bar marayunka, ni zan rayar da su. Matanka da mazansu sun mutu, Sai su dogara gare ni.”

12Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi! 13Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”

14Irmiya ya ce, “Na karɓi saƙo daga wurin Ubangiji. An aiki jakada a cikin al'ummai cewa, “‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gāba da ita, Ku tasar mata da yaƙi!”

15Gama ga shi, zan maishe ki ƙanƙanuwa cikin al'ummai, Abar raini a wurin mutane.

16Tsoronki da ake ji da girmankanki sun ruɗe ki, Ke da kike zaune a kogon dutse, a kan tsauni, Ko da ya ke kin yi gidanki can sama kamar gaggafa, Duk da haka zan komar da ke ƙasa, Ni Ubangiji na faɗa.”

17Ubangiji ya ce, “Edom za ta lalace, duk wanda ya bi ta wurin zai gigice, ya yi tsaki saboda dukan masifunta. 18Abin da zai faru ga Edom zai zama daidai da abin da ya faru ga Saduma, da Gwamrata, da biranen da ke kusa da su, a lokacin da aka kaɓantar da su. Ba wanda zai zauna cikinta, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a cikinta, ni Ubangiji na faɗa. 19Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa ke kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni? 20Domin haka, ku ji shirin da ni Ubangiji na yi wa Edom, da abin da nake nufin yi wa mazaunan Teman. Hakika za a tafi da su, har da ƙanana na garken tumaki, zan kuma sa wurin kiwonsu ya zama ƙeƙuwa saboda su. 21Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza, za a kuma ji muryar kukansu har a Bahar Maliya. 22Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da ke naƙuda.”

Jawabin Ubangiji a kan Dimashƙu

23Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu, “Hamat da Arfad sun gigice, Domin sun ji mugun labari, sun narke saboda yawan damuwa, Ba za su iya natsuwa ba.

24Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi, Ta juya, ta gudu, Tsoro ya kama ta, Azaba da baƙin ciki sun kama ta kamar na naƙuda.

25Ƙaƙa aka manta da sanannen birni, Birnin da ke cike da murna>

26A waccan rana samarinta za su fāɗi a dandalinta. Za a hallaka sojojinta duka, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

27Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu, Za ta kuwa cinye fādodin Ben-hadad.”

Jawabin Ubangiji a kan Kedar da Hazor

28Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi, “Ku tashi zuwa Kedar, Ku hallaka mutanen gabas.

29Za a kwashe alfarwansu da garkunansu, Da labulan alfarwansu, da dukan kayansu. Za a kuma tafi da raƙumansu, Za a gaya musu cewa, “‘Razana ta kewaye ku!”

30“Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwa nesa, Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji na faɗa, Gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya shirya muku maƙarƙashiya, Ya ƙulla mugun nufi game da ku.

31Ku tashi ku fāɗa wa al'ummar da ke zama lami lafiya, Waɗanda ba su da ƙofofi ko ƙyamare, Suna zama su kaɗai.

32“Za a washe raƙumansu da garkunan shanunsu ganima, Zan watsar da masu yin kwaskwas ko'ina, Zan kuma kawo musu masifu daga kowace fuska, Ni Ubangiji na faɗa.

33Hazor za ta zama kufai har abada, wurin zaman diloli, Ba wanda zai zauna a ciki, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”

Jawabin Ubangiji a kan Elam

34Maganar da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Elam a farkon sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza.

35Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan karya bakan Elam, inda ƙarfinta yake.

36Zan sa iska ta hura a kan Elam daga kusurwoyi huɗu na samaniya. Za ta watsar da mutane ko'ina, Har ba ƙasar da za a rasa mutumin Elam a ciki.

37Zan sa mutanen Elam su ji tsoron maƙiyansu waɗanda ke neman ransu. Da zafin fushina zan kawo musu masifa, In sa a runtume su da takobi, Har in ƙare su duka, Ni Ubangiji na faɗa.

38Zan kafa gadon sarautata a Elam, Zan hallaka sarkinta da shugabanninta.

39Amma daga baya zan sa Elam kuma ta wadata. Ni Ubangiji na faɗa.”

50

Jawabin Ubangiji a kan Babila

1Jawabin da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Babila da ƙasar Kaldiyawa ke nan,

2“Ku ba da labari ga sauran al'umma, ku yi shela, Ku ta da tuta, ku yi shela, Kada ku ɓuya, amma ku ce, “‘An ci Babila da yaƙi, An kunyatar da Bel, An kunyatar da siffofinta, Merodak ya rushe, Gumakanta kuma sun ragargaje!”

3“Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”

4Ubangiji ya ce, “Sa'ad da lokacin nan ya yi, mutanen Isra'ila da na Yahuza za su zo tare, suna kuka, suna nemana, ni Ubangiji Allahnsu. 5Za su tambayi hanyar Sihiyona, sa'an nan su bi ta, suna cewa, “‘Bari mu haɗa kanmu don mu yi madawwamin alkawari da Ubangiji, alkawari wanda ba za a manta da shi ba.”

6“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.

7Duk waɗanda suka same su, sun cinye su. Maƙiyansu suka ce, “‘Ba mu yi laifi ba,” Gama sun yi wa Ubangiji laifi, wanda yake tushen gaskiya, Ubangiji wanda kakanninsu suka dogara gare shi.

8“Ku gudu daga cikin Babila, Ku fita kuma daga cikin ƙasar Kaldiyawa, Ku zama kamar bunsurai waɗanda ke ja gaban garke.

9Ga shi, zan kuta manyan ƙasashe daga arewa Su faɗa wa Babila da yaƙi. Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, su cinye ta. Kibansu kamar na gwanayen mayaƙa ne Waɗanda ba su komowa banza.

10Za a washe Kaldiyawa, Waɗanda suka washe su kuwa za su ƙoshi, Ni Ubangiji na faɗa.

11“Saboda kuna murna, kuna farin ciki, Ku da kuka washe gādona, Saboda kuma kuna tsalle kamar karsana a cikin ciyawa, Kuna haniniya kamar ingarmu,

12Domin haka za a kunyatar da Babila sosai, inda kuka fito. Za ta zama ta baya duka a cikin sauran al'umma, Za ta zama hamada, busasshiyar ƙasa.

13Saboda fushin Ubangiji, ba wanda zai zauna a cikinta, Za ta zama kufai, Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai ji tsoro, Zai kuma yi tsaki saboda lalacewarta.

14“Dukanku 'yan baka, ku ja dāga, ku kewaye Babila, Ku harbe ta, kada ku rage kibanku, Gama ta yi wa Ubangiji zunubi.

15Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi! Ta ba da gari, Ginshiƙanta sun fāɗi. An rushe garunta, Gama wannan sakayya ce ta Ubangiji. Ku sāka mata, ku yi mata kamar yadda ta yi.

16Ku datse wa Babila mai shuka, Da mai yanka da lauje a lokacin girbi. Saboda takobin azzalumi, Kowa zai koma wurin mutanensa, Kowa kuma zai gudu zuwa ƙasarsa.”

17“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne ke gaigayi ƙasusuwansu. 18Saboda haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, zan yi wa Sarkin Babila da ƙasarsa hukunci, kamar yadda na hukunta Sarkin Assuriya. 19Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad. 20Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.

21“Ku haura ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da mazaunan Fekod. Ku kashe, ku hallaka su sarai, Ku aikata dukan abin da na umarce ku, Ni Ubangiji na faɗa.

22Hargowar yaƙi tana cikin ƙasar, Da kuma babbar hallakarwa!

23Ga yadda aka karya gudumar dukan duniya! Ga yadda Babila ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma!

24Na kafa miki tarko, ya kuwa kama ki, ya Babila, Ke kuwa ba ki sani ba. An same ki, an kama, Domin kin yi gāba da ni.”

25Ubangiji ya buɗe taskar makamansa, Ya fito da makaman hasalarsa, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana da aikin da zai yi a ƙasar Kaldiyawa.

26Ku zo, ku fāɗa mata daga kowane sashi. Ku buɗe rumbunanta, Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi, Ku hallakar da ita ɗungum, Kada wani abu nata ya ragu.

27Ku kashe dukan bijimanta, a kai su mayanka! Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare, Lokacin hukuncinsu ya yi.

28Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar Babila, Don su faɗa cikin Sihiyona, Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin Haikalinsa.

29“Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila.

30Domin haka samarinta za su fāɗi a tituna. Za a hallaka sojojinta duka a wannan rana, Ni Ubangiji na faɗa.

31“Ga shi, ina gaba da ke, ke Babila, mai girmankai. Gama ranar da zan hukunta ki, ta zo, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

32Mai girmankai za ta yi tuntuɓe ta fāɗi, Ba kuwa wanda zai tashe ta, Zan ƙone garuruwanta da wuta, Zan kuma hallaka dukan abin da ke kewaye da ita.

33“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, An danne mutanen Isra'ila da na Yahuza, Duk waɗanda suka kama su bayi sun riƙe su da ƙarfi. Sun ƙi su sake su.

34Mai fansarsu mai ƙarfi ne, Ubangiji Mai Runduna ne sunansa. Hakika zai tsaya musu don ya kawo wa duniya salama, Amma zai kawo wa mazaunan Babila fitina.

35Ni Ubangiji na ce, Akwai takobi a kan Kaldiyawa, Da a kan mazaunan Babila, Da a kan ma'aikatanta da masu hikimarta,

36Akwai takobi a kan masu sihiri Don su zama wawaye. Akwai takobi a kan jarumawanta Don a hallaka su.

37Akwai takobi a kan mahayan dawakanta, da a kan karusanta, Da a kan sojojin da ta yi ijara da su Don su zama kamar mata, Akwai takobi a kan dukan dukiyarta domin a washe ta.

38Fari zai sa ruwanta ya ƙafe, Gama ƙasa tana cike da gumaka waɗanda suka ɗauke hankalin mutane.

39“Domin haka namomin jeji da diloli za su zauna a Babila, Haka kuma jiminai. Ba za a ƙara samun mazauna a cikinta ba har dukan zamanai.

40Abin da ya faru da Saduma da Gwamrata, Da biranen da ke kewaye da su, Shi ne zai faru da Babila. Ba mutumin da zai zauna cikinta.

41“Ga mutane suna zuwa daga arewa, Babbar al'umma da sarakuna Suna tahowa daga wurare masu nisa na duniya.

42Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi. Amonsu yana kama da rurin teku, Suna shirya don yin yaƙi da ke, ya Babila.

43Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda.

44“Ni Ubangiji ina zuwa kamar zakin da ke fitowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya. Nan da nan zan sa su gudu daga gare ta. Sa'an nan zan naɗa mata wanda na zaɓa. Wa ke kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Wane shugaba zai yi gāba da ni? 45Saboda haka ku ji shirin da Ubangiji ya yi gāba da Babila, da nufin ya yi gaba da ƙasar Kaldiyawa. Hakika za a tafi da ƙananansu, garke zai zama kango. 46Duniya za ta girgiza sa'ad da ta ji an ci Babila da yaƙi. Za a ji kukanta cikin sauran al'umma.”

51

Hukuncin Ubangiji a kan Babila

1Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan kawo iskar ɓarna a kan Babila Da mazaunan Kaldiya.

2Zan aika da masu casawa zuwa Babila, za su casa ta, Su bar ƙasarta kango. Za su kewaye ta a kowane sashi A wannan ranar masifa.

3Kada ku bar maharbi ya yi harbi da bakansa, Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa, Kada ku rage samarinta, Ku hallaka dukan sojojinta.

4Za su fāɗi matattu a ƙasar Kaldiyawa, Za a sassoke su a titunansu.”

5Allah na Isra'ila da Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, bai yashe su ba, Ko da ya ke sun yi wa Mai Tsarki na Isra'ila zunubi.

6Ku gudu daga cikin Babila, Bari kowa ya ceci ransa, Kada a hallaka ku tare da ita, Gama a wannan lokaci Ubangiji zai sāka mata, Zai sāka mata bisa ga alhakinta.

7Babila ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, Ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashen duniya sun sha ruwan inabinta, suka haukace.

8Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, ta kakkarye, Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani domin azabar da take sha, watakila ta warke.

9Mun ba Babila magani, amma ba ta warke ba. Bari mu ƙyale ta, kowannenmu ya koma garinsu, Gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo har samaniya.

10Ubangiji ya baratar da mu a fili, Bari mu tafi mu yi shelar aikin Ubangiji Allahnmu a cikin Sihiyona.

11Ku wasa kibau, ku cika kwaruruwanku! Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan Mediyawa, Domin yana niyyar hallaka Babila. Gama Ubangiji zai yi ramuwa saboda Haikalinsa.

12Ku ta da tuta don a faɗa wa garun Babila, Ku ƙarfafa matsara, Ku sa su su yi tsaro, Ku kuma sa 'yan kwanto! Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwa aikata Abin da ya faɗa a kan mazaunan Babila.

13Ƙarshenki ya zo, Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa, Mai yawan dukiya. Ajalinki ya auka.

14Ubangiji Mai Runduna ya rantse da zatinsa, ya ce, “Hakika zan cika Babila da mutane kamar fāra, Za su kuwa raira waƙar nasara a kanta.”

15Ubangiji ne ya halicci ƙasa da ikonsa, Ya kafa duniya da hikimarsa, Ya kuma shimfiɗa sammai da fahiminsa.

16Bisa ga umarninsa ruwan da ke samaniya yakan yi ruri, Yakan sa gajimare su tashi daga ƙarshen duniya, Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin ruwan sama, Yakan sa iska ta haura daga cikin taskokinsa.

17Kowane ɗan adam wawa ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya kuma zai sha kunya daga wurin gumakansa, Gama siffofinsa na ƙarya ne, ba numfashi a cikinsu.

18Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwa ne kawai, Za su lalace a lokacin da za a hukunta su.

19Amma wanda ke wajen Yakubu ba haka yake ba, Domin shi ne ya halicci dukan abu, Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne, Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.

20Ubangiji ya ce, “Kai ne guduma da kayan yaƙina, Da kai ne na farfasa ƙasashen duniya, Da kai ne na hallaka mulkoki.

21Da kai ne na karya doki da mahayinsa,

22Da kai ne na farfasa karusa da mahayinsa. Da kai ne na kakkarya mace da namiji, Da kai ne na kakkarya tsoho da saurayi, Da kai ne na kakkarya saurayi da budurwa,

23Da kai ne na kakkarya makiyayi da garkensa, Da kai ne na kakkarya manoma da dawakan nomansa, Da kai ne na kakkarya masu mulki da shugabanni.”

24Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.

25Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse mai hallakarwa, Wanda ya hallaka duniya duka. Zan miƙa hannuna gāba da kai, Zan mirgino da ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, Zan maishe ka ƙonannen dutse.

26Ba za a sami dutsen yin kusurwa, ko na kafa harsashen gini a cikinka ba, Amma za ka zama marar amfani har abada.”

27Ku ta da tuta a duniya, Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho, Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita, Ku kirawo mulkokin Ararat, da na Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita. Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai shugabanci yaƙin da za a yi da ita, Ku kawo dawakai kamar fāra.

28Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita, Sarakunan Mediyawa, da masu mulkinsu, da shugabanninsu, Da kowace ƙasar da ke ƙarƙashin mulkinsu.

29Duniya ta girgiza, tana makyarkyata saboda azaba, Gama nufin Ubangiji na gāba da Babila ya tabbata, Nufinsa na mai da ƙasar Babila kufai, inda ba kowa.

30Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata, An sa wa wuraren zamanta wuta, An karya ƙyamaren ƙofofin garinta.

31Maguji yana biye da maguji a guje, Jakada yana biye da jakada, Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewa an ci birninsa a kowane gefe.

32An ƙwace mashigai An ƙone fadamu da wuta, Sojoji sun gigice.

33Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, “Mutanen Babila sun zama kamar daɓen masussuka A lokacin da ake sussuka, Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”

34Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya cinye Urushalima, Ya ragargaza ta, Ya maishe ta kufai, Ya haɗiye ta kamar yadda dodon ruwa yakan yi, Ya cika cikinsa da kayan marmarinta, Ya tatse ta sarai.

35Bari mutanen Sihiyona su ce, “Allah ya sa muguntar da mutanen Babila suka yi mana ta koma kansu!” Bari kuma mutanen Urushalima su ce, “Allah ya sa hakkin jininmu ya koma kan Kaldiyawa!”

36Ubangiji ya ce, “Zan tsaya muku, Zan ɗaukar muku fansa, Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu su ƙafe.

37Babila za ta zama tarin juji, wurin zaman diloli, Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.

38Mutanen Babila za su yi ruri kamar zakuna, Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.

39Sa'ad da suke cike da haɗama zan yi musu biki, In sa su sha, su yi maye, su yi murna. Za su shiga barcin da ba za su farka ba.

40Zan kai su mayanka kamar 'yan raguna, da raguna, da bunsurai.

41“An ci Babila, Ita wadda duniya duka ke yabo an cinye ta da yaƙi, Ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma!

42Teku ta malalo a kan Babila, Raƙuman ruwa masu hauka sun rufe ta.

43Garuruwanta sun zama abin ƙyama, Ta zama hamada, inda ba ruwa, Ƙasar da ba mazauna, Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.

44Zan hukunta Bel, gunkin Babila, Zan sa ya yi aman abin da ya haɗiye, Ƙasashen duniya ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Garun Babila ya rushe!”

45“Ku fito daga cikinta, ya jama'ata, Kowa ya tsere da ransa daga zafin fushin Ubangiji.

46Kada zuciyarku ta yi suwu, Kada kuma ku ji tsoro saboda labarin da ake ji a ƙasar, Labari na wannan shekara dabam, na wancan kuma dabam, A kan hargitsin da ke a ƙasar, Mai mulki ya tasar wa mai mulki.

47Saboda haka kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila, Za a kunyatar da dukan ƙasar Babila, Dukan matattunta za su faɗi a tsakiyarta.

48Sa'an nan sama da duniya, da dukan abin da ke cikinsu, Za su raira waƙar farin ciki, Domin masu hallakarwa daga arewa da za su auko mata, Ni Ubangiji na faɗa.”

49Babila za ta fāɗi, Saboda mutanen Isra'ila da dukan mutanen duniya waɗanda ta kashe.

50Ku waɗanda kuka tsere wa takobi! Ku gudu! Kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a can nesa inda kuke, Ku kuma yi ta tunawa da Urushalima.

51Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana, Kunya ta rufe mu, Gama baƙi sun shiga tsarkakan wurare na Haikalin Ubangiji.

52“Domin haka kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila, da dukan ƙasarta, Waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.

53Ko da Babila za ta hau samaniya, Ta gina kagara mai ƙarfi a can, Duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta, Ni Ubangiji na faɗa.”

54Ku ji muryar kuka daga Babila, Da hargowar babbar hallakarwa daga ƙasar Kaldiyawa!

55Gama Ubangiji yana lalatar da Babila, Yana kuma sa ta kame bakinta na alfarma, Sojoji suna kutsawa kamar raƙuman ruwa, Suna ta da muryoyinsu.

56Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila, An kama sojojinta, An kuma kakkarya bakunansu, Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya, Zai yi sakayya sosai.

57“Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta, Da masu mulkinta, da shugabanninta, Da sojojinta su sha su yi maye. Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna.

58“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, Za a baje garun nan na Babila mai fāɗi Za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta. Mutane sun wahalar da kansu a banza. Sauran al'umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”

59Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi. 60Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila. 61Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan. 62Ka kuma ce, “‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.” 63Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis. 64Sa'an nan ka ce, “‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.” Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.

52

Mulkin Zadakiya

(2 Sar 24.18-20; 2 Tar 36.11-16)

1Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, wanda ke zauna a Libna. 2Sarki Zadakiya ya aikata abin da ke mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehoyakim ya yi. 3Al'amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra'ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala.

Faɗuwar Urushalima

(2 Sar 25.1-7; Irm 39.1-7) Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila. 4A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina garu kewaye da ita. 5An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zadakiya. 6A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci. 7Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da ke tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawa ke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba. 8Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi. 9Da aka kama Zadakiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babila ya yanke masa shari'a. 10Ya kuwa kashe 'ya'yan Zadakiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuza a Ribla. 11Sa'an nan ya ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babila inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.

Yahuza ya Je Zaman Talala

(2 Sar 25.8-21; 2 Tar 36.17-21; Irm 39.8-10)

12A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima. 13Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da ke Urushalima. 14Sojojin Kaldiyawa da ke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan garun Urushalima. 15Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila. 16Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.

17Kaldiyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda ke a Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babila. 18Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar Haikali. 19Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da ke na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe. 20Tagullar da sarki Sulemanu ya yi waɗannan abubuwa da ita, wato ginshiƙai biyu, da kwatarniyar tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda ke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna. 21Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma taƙi huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki. 22A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman. 23Akwai siffofin rumman tasa'in da shida da ake gani a gyaffan. Dukan siffofin rumman da ke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.

24Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda ke biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su. 25Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai 'yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su. 26Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babila a Ribla, 27Sarkin Babila kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Haka aka tafi da mutanen Yahuza bautar talala. 28Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa dubu uku da ashirin da uku (3,023). 29A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima ɗari takwas da talatin da biyu. 30A shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa kuma, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa ɗari bakwai da arba'in da biyar. Jimillarsu duka kuwa dubu huɗu da ɗari shida ne (4,600).

An saki Yekoniya an ba shi Girma a Babila

(2 Sar 25.27-30)

31A shekarar da Ewil-merodak ya zama Sarkin Babila, sai ya nuna wa Yekoniya Sarkin Yahuza alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yekoniya bauta. 32Ewil-merodak ya nuna wa Yekoniya alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babila tare da shi. 33Yekoniya ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa. 34Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarki, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.