John
1Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.
6Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.
9Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10Dā yana duniyar ma ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'arsa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.
14Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
15Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, “‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.” 16Dukanmu kuwa daga falalarsa muka samu, alheri kan alheri. 17Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. 18Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.
(Mat 3.1-12; Mar 1.1-8; Luka 3.1-18)
19Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne. 20Sai ya faɗi gaskiya, bai yi mūsu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” 21Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.” 22Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?” 23Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, “‘Ku gyara wa Ubangiji tafarki,” yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”
24Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su. 25Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, 27shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in kwance ba.” 28An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma. 1.29 “Ga Ɗan Rago na Allah” “Ga Ɗan Rago na Allah”
29Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya! 30Wannan shi ne wanda na ce, “‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.” 31Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.” 32Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kasance a kansa. 33Dā kam, ban san shi ba, shi dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, “‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.” 34Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa, wannan Ɗan Allah ne.”
35Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. 36Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!” 37Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suke bi Yesu. 38Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato, Malam ke nan, ina kake da zama?” 39Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. 40Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. 41Sai ya fara nemo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato, shafaffe. 42Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato, kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato, Bitrus.
43Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.” 44Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato, Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” 46Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.” 47Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!” 48Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.” 49Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!” 50Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma.” 51Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”
1A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana nan, 2aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3Da ruwan inabi ya gaza, mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.” 5Sai mahaifiyar Yesu ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” 6A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce tana cin wajen tulu shida shida. 7Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal. 8Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai. 9Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango, 10ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”
11Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.
(Mat 21.12-13; Mar 11.15-17; Luka 19.45-46)
13Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima. 14A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma 'yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu. 15Sai ya tufka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu. 16Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.” 17Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.” 18Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?” 19Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.” 20Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba'in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?” 21Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne. 22Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.
23To, sa'ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu'ujizan da ya yi. 24Yesu bai amince da su ba, 25domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.
1To, akwai wani Bafarisiye, sunansa Nikodimu, wani shugaban Yahudawa. 2Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.” 3Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” 4Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin mahaifiyarsa ta sāke haifo shi?” 5Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta wurin ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba. 6Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne. 7Kada ka yi mamaki domin na ce maka, “‘Dole a sāke haifarku.” 8Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta ba. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.” 9Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?” 10Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba? 11Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu. 12In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama? 13Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum (da yake Sama). 14Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.
16“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami. 17Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa. 18Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne. 20Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu. 21Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa, da taimakon Allah ne aka yi su.”
22Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma. 23Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma. 24Domin a sa'an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
25Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawwara a kan maganar tsarkakewa. 26Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.” 27Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama. 28Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba. 29Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron maganarsa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika. 30Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.
31“Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa. 32Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa. 33Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne. 34Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba. 35Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa. 36Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”
1To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya 2(ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne), 3sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili. 4Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya. 5Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu. 6Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa.
7Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.” 8Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci. 9Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa). 10Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, “‘Ba ni ruwa in sha,” ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.” 11Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai? 12Ashe, ka fi ubanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da 'yayansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?” 13Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa. 14Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.” 15Macen ta ce masa, “Ya Shugaba, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan in ɗiba.”
16Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.” 17Sai macen ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji, 18don kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” 19Macen ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne. 20Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada.” 21Sai Yesu ya ce da ita, “Mace, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima, 22Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake. 23Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” 25Sai macen ta ce masa, “Na san Almasihu yana zuwa, (wanda ake kira Kristi). Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.” 26Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganar nan da ke.”
27Ya gama magana ke nan sai almajiransa suka iso. Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” ko, “Don me kake magana da ita?” 28Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane, 29“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?” 30Sai suka fito daga garin suka nufo shi.
31Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Malam, ci abinci.” 32Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.” 33Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?” 34Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi. 36Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, “‘Wani da shuka, wani da girbi.” 38Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”
39Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40Da samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan. 41Saboda maganarsa kuma waɗansu da yawa suka gaskata. 42Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”
43Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili. 44Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa, annabi ba shi da girma a garinsu. 45Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.
46Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani basarake wanda ɗansa ba shi da lafiya. 47Da jin cewa, Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa. 48Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” 49Sai basaraken nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.” 50Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa. 51Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka ya warke.” 52Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya da rana zazzaɓin ya sake shi.” 53Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka. 54Wannan kuwa ita ce mu'ujiza ta biyu da Yesu ya yi a Galili, bayan komowarsa daga Yahudiya.
1Bayan haka sai Yesu ya tafi Urushalima domin idin Yahudawa.
2A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar. 3A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu.[Suna jira a motsa ruwan. 4Don lokaci lokaci wani mala'ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.] 5A nan kuwa akwai wani mutum da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya. 6Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?” 7Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai saka ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.” 8Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi!” 9Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiyarsa. Ran nan kuwa Asabar ce. 10Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.” 11Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.” 12Suka tambaye shi, “Wanne mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?” 13Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da suke wurin. 14Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.” 15Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi. 16Saboda haka, Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar. 17Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.” 18Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.
19Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi. 20Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi. 21Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa. 22Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan, 23domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan. 24Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.
25“Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci yana zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu. 26Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai. 27Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne. 28Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji muryarsa, 29su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.
30“Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 31In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce. 32Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi a kaina tabbatacciya ce. 33Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya. 34Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan. 36Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni. 37Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa. 38Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ba. 39Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai. 41Ba na karɓar girma wurin mutane. 42Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci. 43Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa. 44Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa? 45Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta. 47In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”
(Mat 14.13-21; Mar 6.30-44; Luka 9.10-17)
1Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato, Tekun Tibariya. 2Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya. 3Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4To, Idin Ƙetarewa wato, idin Yahudawa, ya gabato. 5Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?” 6Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi. 7Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.” 8Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa, 9“Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?” 10Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzauna, su wajen dubu biyar. 11Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su. 12Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya lalace.” 13Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu. 14Da jama'a suka ga mu'ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya!”
15Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yayi su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa a kan dutsen shi kaɗai.
(Mat 14.22-27; Mar 6.45-52)
16Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa teku. 17Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna. 18Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa. 19Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita. 20Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.” 21Sa'an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.
22Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi. 23Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya. 24Sa'ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?” 26Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi. 27Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato, Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.” 28Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?” 29Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah yake so, wato, ku gaskata da wanda ya aiko.” 30Sai suka ce masa, “To, wace mu'ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi? 31Kakannin kakanninmu sun ci manna a jeji, yadda yake a rubuce cewa, “‘Ya ba su gurasa daga Sama su ci.” 32Sa'an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama. 33Ai, Gurasar Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai.” 34Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!”
35Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. 36Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan. 38Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe. 40Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”
41Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasar da ya sauko daga Sama.” 42Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda mahaifiyarsa da mahaifinsa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, “‘Na sauko ne daga sama?” 43Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku. 44Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 45A rubuce yake cikin littafan annabawa cewa, “‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.” To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni. 46Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban. 47Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami. 48Ni ne Gurasa mai ba da rai. 49Kakannin kakanninku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu. 50Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu. 51Ni ne Gurasar rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”
52Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?” 53Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku. 54Duk wanda yake cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 55Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika. 56Duk wanda yake cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa. 57Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. 58Wannan shi ne Gurasar da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.” 59Wannan kuwa a majami'a ya faɗa, sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.
60Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?” 61Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe? 62Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā? 63Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai. 64Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi. 65Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”
66Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba. 67Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?” 68Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami. 69Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.” 70Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.” 71Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.
1Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi. 2Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato. 3Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi. 4Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.” 5Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba. 6Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne. 7Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne. 8Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.” 9Da ya faɗa musu haka, ya dakata a ƙasar Galili.
10Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba. 11Yahudawa suna ta nemansa a wurin idin suna cewa, “Ina yake ne?” 12Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu suna cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma suna cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.” 13Amma ba wanda ya yi maganarsa a fili don tsoron Yahudawa.
14Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar. 15Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?” 16Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce. 17Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwar nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa. 18Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. 19Ashe, ba Musa ne ya ba ku Shari'a ba? Duk da haka ba mai kiyaye Shari'ar a cikinku. Don me kuke neman kashe ni?” 20Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?” 21Yesu ya amsa musu ya ce, “Aiki ɗaya kawai na yi, dukanku kuwa kuna mamakinsa. 22Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma. 23To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari'ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar? 24Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.” 7.25 Wannan Almasihu Ne? Wannan Almasihu Ne>
25Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba? 26Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu? 27Wannan kam, mun san daga inda yake, amma sa'ad da Almasihu ya zo ba wanda zai san daga inda yake.” 28Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba. 29Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.” 30Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna. 31Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa'ad da Almasihu ya zo, zai yi mu'ujizai fiye da na mutumin nan?”
32Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi. 33Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa'an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. 34Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba. Inda nake kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 35Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman? 36Me kuma yake nufi da cewa, “‘Za ku neme ni amma ba za ku same ni ba?” da kuma cewa, “‘Inda nake ba za ku iya zuwa ba?”
37A ranar ƙarshe ta idin, wato, babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha. 38Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda nassi ya ce, “‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.” 39To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.
40Da jin maganar nan waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.” 41Waɗansu kuwa suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma waɗansu suka ce, “Me? Ashe, Almasihu daga ƙasar Galili zai fito? 42Nassi ba cewa, ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?” 43Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa. 44Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.
45Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?” 46Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!” 47Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne? 48Ashe, akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi? 49Amma wannan taro da ba su san Attaura ba, ai, la'anannu ne.” 50Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, ya ce musu, 51“Ashe, shari'armu takan hukunta mutum tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da yake ciki?” 52Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.” [
53Sai kowa ya tafi gida.
1Yesu kuwa ya hau Dutsen Zaitun. 2Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu. 3Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka, 4suka ce masa, “Malam, matar nan an kama ta ne, suna cikin yin zina. 5To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?” 6Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa. 7Da suka dinga tambayarsa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.” 8Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa. 9Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar a tsaye a wurin. 10Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?” 11Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”]
12Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,” 13Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka kake wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.” 14Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni. 15Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa. 16Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, domin ba ni kaɗai nake ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne. 17A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa, shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. 18Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.” 19Saboda haka suka ce masa, “Ina Uban naka yake?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana, ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.” 20Ya faɗi wannan magana ne a baitulmalin Haikali, lokacin da yake koyarwa a wurin. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
21Sai ya ƙara ce musu, “Zan yi tafiya, za ku kuwa neme ni, amma za ku mutu da zunubinku. Inda za ni kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 22Saboda haka sai Yahudawa suka ce, “Wato, zai kashe kansa ke nan da ya ce, “‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba?” 23Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyar nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne. 24Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Domin in ba ku gaskata ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.” 25Sai suka ce masa, “Kai wane ne?” Yesu ya ce musu, “Daidai yadda na gaya muku. 26Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.” 27Ba su gane maganar Uba yake yi musu ba. 28Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa. 29Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.” 30Sa'ad da Yesu yake faɗar haka, mutane da yawa suka gaskata da shi.
31Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne. 32Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.” 33Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?”
34Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne. 35Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa. 36In kuwa Ɗan ya 'yanta ku, za ku 'yantu, 'yantuwar gaske. 37Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku. 38Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uban.”
39Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi. 40Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba. 41Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato, Allah.” 42Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni. 43Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne. 44Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni. 46A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni? 47Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”
48Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.” 49Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi. 50Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari'a. 51Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.” 52Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa, kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada. 53Wato, ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?” 54Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku. 55Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye maganarsa. 56Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.” 57Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, ashe ka ga Ibrahim!” 58Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.” 59Don haka suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fita daga Haikalin.
1Yesu yana wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho. 2Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?” 3Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa. 4Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki. 5Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.” 6Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon, 7ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” (wato, aikakke). Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani. 8Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?” 9Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!” 10Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?” 11Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, “‘Je ka Siluwam ka wanke ido.” Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.” 12Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
13Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā. 14To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido. 15Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.” 16Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu. 17Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”
18Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin, 19suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa, an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?” 20Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi. 21Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” 22Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa, kowa ya amsa, cewa, shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a. 23Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.” 25Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.” 26Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?” 27Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne. 29Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.” 30Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido! 31Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi. 32Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba. 33Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.” 34Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.
35Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?” 36Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?” 37Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.” 38Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada. 39Yesu ya ce, “Na shigo duniyar nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.” 40Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato, mu ma makafi ne?” 41Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.
1“Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani wuri, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne. 3Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa, yakan kama sunan nasa tumakin, ya kai su waje. 4Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin suna biye da shi, domin sun san muryarsa. 5Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.” 6Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.
7Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba. 9Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo. 10Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace. 11Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin. 12Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran. 13Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin. 14Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni, 15kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin. 16Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle ne in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda. 17Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma. 18Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”
19Saboda maganar nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa. 20Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?” 21Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”
22Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima, 23damuna ce kuma, Yesu kuwa yana zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali, 24sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.” 25Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata. 26Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina. 27Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na. 28Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su hallaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban. 30Ni da Uba ɗaya muke.”
31Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi. 32Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?” 33Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.” 34Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, “‘Na ce ku alloli ne?” 35To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi), 36kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, “‘Sāɓo kake,” domin na ce, “‘Ni Ɗan Allah ne?” 37In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.” 39Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.
40Sa'an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can, 41mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.
1Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta. 2Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta. 3To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunar nan ba shi da lafiya.” 4Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
5Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru. 6To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu. 7Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.” 8Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?” 9Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyar nan. 10Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!” 11Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” 12Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.” 13Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne. 14Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu. 15Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.” 16Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”
17Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari. 18Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu. 19Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu. 20Da jin Yesu yana zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida. 21Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba. 22Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.” 23Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.” 24Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.” 25Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. 26Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?” 27Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, wanda yake zuwa cikin duniya.”
28Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwarta Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.” 29Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa. 30Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi. 31Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta'aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can. 32Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.” 33Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya. 34Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.” 35Sai Yesu ya yi kuka. 36Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!” 37Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”
38Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin. 39Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, 'yar'uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” 40Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?” 41Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama'ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.” 43Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!” 44Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuskarsa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”
(Mat 26.1-5; Mar 14.1-2; Luka 22.1-2)
45Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi. 46Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka? 48In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama'armu.” 49Amma ɗayansu, mai suna Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekarar nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba. 50Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk al'umma ta hallaka.” 51Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekarar nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a, 52ba ma saboda al'umma kaɗai ba, har ma yă tattaro 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina su zama ɗaya. 53Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi.
54Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.
55Ana nan, Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauyuka suka tafi Urushalima su tsarkake kansa kafin idin. 56Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali, suna ce wa juna, “Me kuka gani? Zai zo idin kuwa?” 57Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa, idan kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.
(Mat 26.6-13; Mar 14.3-9)
1Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Betanya inda Li'azaru yake, wanda Yesu ya tasa daga matattu. 2Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li'azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi. 3Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man. 4Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato, wanda zai bāshe shi, ya ce, 5“Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba talakawa kuɗin?” 6Ya faɗi haka fa, ba don yana kula da talakawa ba, a'a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da ke ciki. 7Sai Yesu ya ce, “A ƙyale ta, dā ma ta ajiye shi domin tanadin ranar jana'izata. 8Ai, kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”
9Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba domin Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li'azaru wanda ya tasa daga matattu. 10Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li'azaru, shi ma, 11domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.
(Mat 21.1-11; Mar 11.1-11; Luka 19.28-40)
12Kashegari babban taron da suka zo idi, da suka ji Yesu yana zuwa Urushalima, 13suka ɗaɗɗauko gazarin dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila!” 14Da Yesu ya sami wani aholaki sai ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa, 15“Kada ki ji tsoro, yake 'yar Sihiyona, Ga sarkinki yana zuwa a kan aholakin jaki!” 16Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi.
17Taron da suke tare da shi sa'ad da ya kira Li'azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka. 18Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu'ujizan nan. 19Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”
20To, a cikin waɗanda suka zo idin yin sujada akwai waɗansu Helenawa. 21Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Betsaida ta ƙasar Galili, suka roƙe shi suka ce, “Maigida, muna bukatar mu gana da Yesu.” 22Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu. 23Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. 24Lalle hakika, ina gaya muku, in ba an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa. 25Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyar nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami. 26Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”
27“Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, “‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci?” A'a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci. 28Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,” 29Da taron da suke tsaya a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala'ika ne ya yi masa magana.” 30Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan murya ba, sai dominku. 31Yanzu ne za a yi wa duniyar nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyar nan. 32Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.” 33Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi. 34Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa, Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?” 35Yesu ya ce musu, “Haske yana tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske yana tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba. 36Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.”
Ba Yesu ya faɗi haka, sa'an nan ya tafi ya ɓuya musu. 37Amma ko da yake ya sha yin mu'ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba, 38domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu? Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?” 39Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa, 40“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciyarsu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.” 41Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa. 42Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a. 43Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.
44Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni. 45Wanda kuma yake dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. 46Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu. 47Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya. 48Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe. 49Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi. 50Na kuma san umarnin nan nasa rai ne madawwami. Domin haka, abin da nake faɗa ina faɗa ne daidai yadda Uba ya faɗa mini.”
1Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai bar wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa. 2Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi. 3Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko mayani ya yi ɗamara da shi. 5Sa'an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafewa da mayanin. 6Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu kam, ba ka san abin da nake yi ba, amma daga baya za ka fahimta.” 8Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai ba, har ma da hannuwana da kaina!” 10Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.” 11Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”
12Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake. 14Tun da yake ni da nake Ubangijinku, kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, kuma wajibi ne ku wanke wa juna. 15Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku 16Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne. 18Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, “‘Wanda muke ci tare ya tasar mini.” 19Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”
(Mat 26.20-25; Mar 14.17-21; Luka 22.21-23)
21Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.” 22Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa ko da wa yake. 23Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu. 24Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?” 25Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne shi?” 26Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti. 27Da karɓar 'yar lomar nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.” 28Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba talakawa wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu. 30Shi kuwa da karɓar 'yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.
31Bayan da ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa. 32Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi. 33Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, “‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,” haka nake faɗa muku yanzu. 34Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” 13.36 Bitrus zai Yi Mūsun Sanin Yesu Bitrus zai Yi Mūsun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35; Mar 14.27-31; Luka 22.31-34)
36Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.” 38Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
1“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2A gidan Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ba ne, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ta yaya za mu san hanyar?” 6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”
8Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus! Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, “‘Nuna mana Uban?” 10Wato, ba ka gaskata cikin Uba nake ba, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa. 11Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma a cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan su kansu.
12“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan. 14Kome kuke roƙo da sunana, zan yi shi.”
15“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. 17Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.
18“Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20A ran nan ne fa za ku sani, ni a cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24Wanda ba ya ƙaunata, ba zai kiyaye maganata ba. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.
25“Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26Amma Mai Taimako, wato, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada ku ji tsoro. 28Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyar nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”
1“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi. 2Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa. 3Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku. 4Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko yana haɗe da itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina. 5Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba. 6Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone. 7In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku. 8Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka, kuma zaku tabbata almajiraina. 9Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku. 10In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini. 11Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.
12“Wannan fa shi ne umarnina, cewa, ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato, mutum yă ba da ransa saboda aminansa. 14Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. 15Nan gaba, ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.
18“In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu, da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka. 25An yi wannan kuwa domin a cika maganar da take a rubuce a cikin Shari'arsu cewa, “‘Sun ƙi ni ba dalili.” 26Amma sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato, Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaida ni. 27Ku ma shaida ne, domin tun farko kuke tare da ni.
1“Na faɗa muku waɗannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe. 2Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma yana zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi. 3Za su yi haka ne kuwa, domin ba su san Uba ko ni ba. 4Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”
“Ban faɗa muku abubuwan tun da farko ba, domin ina tare da ku. 5Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, “‘Ina za ka?” 6Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku. 7Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai Taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8Sa'ad da kuwa ya zo zai kā da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9Wato, a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba, 10a kan adalci kuwa, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba, 11a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
12“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba. 13Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku. 14Zai ɗaukaka ni, domin zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku. 15Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”
16“Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.” 17Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, “‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni?” da kuma cewa, “‘Domin za ni wurin Uba?” 18Suka ce, “Me yake nufi da, “‘Bayan ɗan lokaci kaɗan” ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗi ba.” 19Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato, kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, “‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni?” 20Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya. 22Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku. 23A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana. 24Har yanzu dai, ba ku roƙi komi cikin sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”
25“Duk waɗannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari. 26A ran nan za ku yi roƙo a cikin sunana. Ban kuwa ce muku zan roƙar muku Uba ba, 27domin shi Uban kansa na ƙaunarku, domin kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba. 30Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32To, lokaci yana zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba yana tare da ni. 33Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”
1Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka, 2tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko. 4Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi. 5Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga zatinka da ɗaukakar nan da nake da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.
6“Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka. 7Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake. 8Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni. 9Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙar wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne. 10Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu. 11Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke. 12Duk sa'ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya hallaka, sai dai hallakakken nan, domin Nassi ya cika. 13Amma a yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya. 18Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya. 19Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.
20“Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙar wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta wurin maganarsu, 21domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa, kai ne ka aiko ni. 22Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya, 23ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni. 24Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba. 25Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka, waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni. 26Na sanar da su sunanka, zan kuma ci gaba da sanar masu, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance a cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”
(Mat 26.47-56; Mar 14.43-50; Luka 22.47-53)
1Bayan da Yesu ya yi maganar nan, ya fita, shi da almajiransa zuwa hayin Rafin Kidron, inda wani lambu yake, ya kuma shiga da almajiransa. 2Yahuza ma wanda ya bāshe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can. 3Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jinyoyi, da makamai, 4Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa kuke nema?” 5Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuza kuwa da ya bāshe shi yana tsaye tare da su. 6Da Yesu ya ce musu, “Ni ne,” suka ja da baya da baya, har suka fāɗi. 7Sai ya sāke tambayarsu, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” 8Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku, ni ne. In kuwa ni kuke nema, ku bar waɗannan su tafi.” 9Wannan kuwa domin a cika maganar da ya yi ne cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban yar da ko ɗaya ba.” 10Bitrus kuwa da yake yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus. 11Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”
(Mat 26.57-58; Mar 14.53-54; Luka 22.54)
12Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi, 13suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafa ne, wanda yake shi ne babban firist a shekarar nan. 14Kayafa kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawara, cewa, ya fiye musu mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a. 18.15 Bitrus ya Yi Mūsun Sanin Yesu Bitrus ya Yi Mūsun Sanin Yesu
(Mat 26.69-70; Mar 14.66-68; Luka 22.55-57)
15Sai Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har gidan firist ɗin tare da Yesu, 16Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da yake sananne ga babban firist ya fita, ya yi magana da wanda yake jiran ƙofa, sa'an nan ya shigo da Bitrus. 17Baranyar da yake jiran ƙofar kuwa ta ce wa Bitrus, “Anya! Kai ma ba a cikin almajiran mutumin nan kake ba?” Ya ce, “A'a, ba na ciki.” 18To, barori da dogaran Haikali kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye, suna jin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin wutar.
(Mat 26.59-66; Mar 14.55-64; Luka 22.66-71)
19Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwarsa. 20Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba. 21Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.” 22Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” 23Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?” 24Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist. 18.25 Bitrus ya Sāke Mūsun Sanin Yesu Bitrus ya Sāke Mūsun Sanin Yesu
(Mat 26.71-75; Mar 14.69-72; Luka 22.58-62)
25To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba a cikin almajiransa kake ba?” Sai ya yi mūsu ya ce, “A'a, ba na ciki.” 26Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato, dangin wanda Bitrus ya fille wa kunne, ya ce, “Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?” 27Sai Bitrus ya sāke yin mūsu. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.
(Mat 27.1-2,11-14; Mar 15.1-5; Luka 23.1-5)
28Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa. 29Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?” 30Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.” 31Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.” 32Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” 34Yesu ya amsa ya ce, “Wato, wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?” 35Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama'arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?” 36Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyar nan ba ne. Da mulkina na duniyar nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.” 37Sai Bilatus ya ce masa, “Wato, ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.” 38Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne, shi gaskiya?”
(Mat 27.15-31; Mar 15.6-20; Luka 23.13-25) Bayan da ya faɗi haka, ya sāke fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba. 39Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku mutum ɗaya. To, kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 40Sai suka sāke ɗaukar kururuwa suna cewa, “A'a, ba wannan ba, sai dai Barabbas!” Barabbas ɗin nan kuwa ɗan fashi ne.
1Sa'an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala. 2Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan shunayya. 3Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa. 4Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.” 5Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan shunayya. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!” 6Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.” 7Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Shari'ar nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.” 8Da Bilatus ya ji maganar nan sai ya ƙara tsorata. 9Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka sani ba ni ne da ikon sakinka, ko gicciye ka?” 11Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”
12A kan wannan Bilatus ya nema ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.” 13Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata. 14Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!” 15Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.” 16Sa'an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.
(Mat 27.32-44; Mar 15.21-32; Luka 23.26-43)
17Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota. 18Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya. 19Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.” 20Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci. 21Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta “‘Sarkin Yahudawa,” sai dai ka rubuta, “‘A faɗarsa shi ne Sarkin Yahudawa.” 22Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta na rubuta ke nan.”
23Bayan soja sun gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta. 24Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri'a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa, “Suka rarraba tufafina a tsakaninsu, suka jefa kuri'a akan rigata”
25Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da mahaifiyarsa, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye. 26Da Yesu ya ga mahaifiyarsa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa mahaifiyarsa, “Iya, ga ɗanki nan!” 27Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
(Mat 27.45-56; Mar 15.33-41; Luka 23.44-49)
28Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa. 30Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.
31Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan. 32Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi. 33Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya rasu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano. 35Wanda ya gani ɗin kuwa shi ya ba da shaida kan haka, shaidarsa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya yake faɗa, domin ku ma ku ba da gaskiya. 36Wannan kuwa don a cika Nassi ne cewa, “Ko ƙashinsa ɗaya ba za a karya ba.” 37Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
(Mat 27.57-61; Mar 15.42-47; Luka 23.50-56)
38Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu. 39Nikodimu kuma, wanda zuwansa na farko wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al'ul a gauraye, wajen awo ɗari. 40Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lilin game da kayan ƙanshin nan, bisa ga al'adar Yahudawa ta jana'iza. 41A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa a ciki ba. 42Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka sa Yesu a nan.
(Mat 28.1-10; Mar 16.1-8; Luka 24.1-12)
1To, a ranar farko ta mako, Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kawar da dutsen daga kabarin. 2Sai ta yiwo gudu wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.” 3Sai Bitrus da almajirin nan suka fita suka doshi kabarin. 4Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin. 5Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba. 6Sa'an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye, 7mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya. 8Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya. 9Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa, lalle ne yă tashi daga matattu. 10Sai almajiran suka koma gida.
(Mar 16.9-11)
11Maryamu kuwa tana tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa, ta leƙa kabarin, 12sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu. 13Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.” 14Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba. 15Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.” 16Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato, Malam. 17Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.” 18Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce wa almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
(Mat 28.16-20; Mar 16.14-18; Luka 24.36-49)
19A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, ƙofofin ɗakin da almajiran suke ciki yana kulle sabo da tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salama a gare ku!” 20Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farin ciki da ganin Ubangiji. 21Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama a gare ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.” 22Da ya faɗi haka ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”
24Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa'ad da Yesu ya zo. 25Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”
26Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama a gare ku.” 27Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.” 28Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina da kuma Allahna!” 29Sai Yesu ya ce masa, “Wato, saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”
30Yesu ya yi waɗansu mu'ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba. 31Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.
1Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa. 2Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare, 3Sai Bitrus ya ce musu, “Za ni sū.” Suka ce masa, “Mu ma mā tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama kome ba.
4Gari yana wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba. 5Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A'a.” 6Ya ce musu, “Ku jefa taru dama da jirgin za ku samu.” Suka jefa, har suka kāsa jawo shi don yawan kifin. 7Sai almajirin nan da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ubangiji ne fa!” Da Bitrus ya ji, ashe, Ubangiji ne sai ya yi ɗamara da taguwarsa, don a tuɓe yake, ya fāɗa tekun. 8Sauran almajirai kuwa suka zo a cikin ƙaramin jirgi, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, kamar misalin kamu ɗari biyu ne.
9Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi, da kuma gurasa. 10Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi daga cikin waɗanda kuka kama yanzu.” 11Sai Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba. 12Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Daga cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin tambayarsa ko shi wane ne, domin sun sani Ubangiji ne. 13Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin. 14Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.
15Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon 'ya'yan tumakina.” 16Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.” 17Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina. 18Lalle hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka kakan yi wa kanka ɗamara, ka tafi inda ka nufa, amma in ka tsufa, za ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.” 19(Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”
20Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato, wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?” 21Da Bitrus ya gan shi, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?” 22Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!” 23Saboda haka maganar nan ta bazu cikin 'yan'uwa, cewa, almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce masa ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki?”
24Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan al'amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaidarsa tabbatacciya ce.
25Akwai waɗansu ayyuka kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta ko wannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.