Job
1Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. 2Yana da 'ya'ya bakwai maza, uku mata. 3Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.
4'Ya'yansa maza sukan yi liyafa bi da bi a gidajen junansu, inda su duka sukan taru koyaushe, sukan gayyaci 'yan'uwan nan nasu mata su halarci liyafar. 5A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, ya miƙa hadayu don ya tsarkake 'ya'yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin 'ya'yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.
6Sa'ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaiɗan ma ya zo tare da su. 7Sai Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Kai fa me kake yi?” Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko'ina a duniya.”
8Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”
9Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada? 10Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasar nan. 11Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili ya zage ka ƙiri ƙiri.”
12Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.
13Wata rana 'ya'yan Ayuba suna shagali a gidan wansu, 14sai ga jakada ya zo wurin Ayuba a guje, ya ce, “Muna huɗar gona da shanu, jakuna suna kiwo a makiyayar da take kusa da wurin, 15sai Sabiyawa suka auka musu farat ɗaya, suka sace su duka, suka kuma karkashe duk barorinka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”
16Kafin ya gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Tsawa ta kashe tumaki da makiyayansu duka, ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”
17Kafin ya gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa suka auka mana, suka kwashe raƙuma duka, suka kuma karkashe barorinka duka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”
18Kafin ya gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Sa'ad da 'ya'yanka suke liyafa a gidan wansu, 19sai hadiri ya taso daga hamada, ya rushe gidan, ya kashe 'ya'yanka duka, ni kaɗai na tsira na zo in faɗa maka.”
20Sai Ayuba ya tashi, ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki. Ya aske kansa, ya fāɗi ƙasa, 21ya ce, “Ban shigo duniya da kome ba, ba kuma zan fita cikinta da kome ba. Ubangiji ya bayar, shi ne kuma ya karɓe, yabo ya tabbata ga sunansa.” 22Ko da yake waɗannan al'amura duka sun faru, duk da haka Ayuba bai sa wa Allah laifi ba.
1Sa'ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta sāke yi, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su. 2Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ina ka fito?” Sai Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, ko'ina a duniya.”
3Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. Kai ka sa na yardar maka ka far masa, ba tare da wani dalili ba. Amma duk da haka Ayuba yana nan da amincinsa kamar yadda yake.”
4Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Mutum ya iya rabuwa da dukan abin da yake da shi don ya ceci ransa. 5Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai ya fito fili ya zage ka.”
6Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”
7Sa'an nan Shaiɗan ya rabu da Ubangiji, ya je ya sa ƙuraje su fito ko'ina a jikin Ayuba. 8Ayuba ya je ya zauna kusa da juji ya ɗauki tsingaro ya yi ta sosa ƙurajen. 9Sai matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana da amincin nan naka? Don me ba za ka zagi Allah ka mutu ba?”
10Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na'am da shi, to, me zai sa sa'ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.
11Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi. 12Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu. 13Sa'an nan suka zauna a ƙasa tare da shi, har kwana bakwai, amma ba wanda ya ce uffan, saboda ganin irin yawan wahalar da yake sha.
1Ayuba ya yi magana ya la'anci ranar da aka haife shi. 2Ya ce, “Ya Ubangiji, ka la'anci ranar nan da aka haife ni.
3Ka la'anci daren nan da aka yi cikina.
4Ka mai da ranar nan ta zama duhu, ya Allah. Kada a ƙara tunawa da wannan rana, Kada haske ya ƙara haskakata.
5Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin. Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.
6Ka shafe wannan dare daga cikin shekara, Kada kuma a ƙara lasafta shi.
7Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.
8Ka faɗa wa masu sihiri su la'anci wannan rana, Su waɗanda suke umartar dodon ruwa.
9Ka hana gamzaki haskakawa, Kada ka bar daren nan ya sa zuciya ga wayewar gari,
10Ka la'anci daren nan da aka haife ni, Da ya jefa ni a baƙin ciki da wahala.
11“Da ma na mutu tun a cikin cikin uwata, Ko kuwa da haihuwata in mutu.
12Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta, Ta shayar da ni kuma da mamanta>
13Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,
14Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulki Waɗanda suka sāke gina fādodi na dā,
15Da ina ta sharar barcina kamar shugabanni Waɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa,
16In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu.
17Mugaye za su daina muguntarsu a kabari, Ma'aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta,
18Har 'yan sarƙa ma za su ji daɗin salama, Su huta daga tsautawa da umarnai masu tsanani.
19Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne, Bayi ma sun sami 'yanci.
20“Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa? Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki>
21Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa, Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.
22Ba su da farin ciki, sai sun mutu an binne su tukuna.
23Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba, Ya kalmashe su kowane gefe.
24A maimakon cin abinci, sai baƙin ciki nake yi, Ba kuma zan daina yin nishi ba,
25Dukan abin da nake jin tsoro ko fargaba ya faru.
26Ba ni da salama, ba ni da hutawa, Wahala ba za ta taɓa ƙarewa ba.”
1Elifaz ya yi magana.
2“Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana? Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba.
3Ka koya wa mutane da yawa, Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.
4Idan wani ya yi tuntuɓe, Ya gaji, ya rasa ƙarfi, Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa, Har ya iya tsayawa kyam.
5Yanzu naka lokacin wahala ya zo, Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,
6Kana yi wa Allah sujada, Ba wani laifi a zamanka, Ya kamata ka amince ka sa zuciya.
7“Yanzu fa sai ka yi tunani. Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.
8Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta, Suna shuka mugunta, Suka kuwa girbe mugunta.
9A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.
10Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki, Amma Allah yakan sa su yi tsit, Ya kakkarya haƙoransu.
11Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci, Hakanan za su mutu, 'ya'yansu kuwa su warwatse duka.
12“Wata rana wani saƙo ya zo a hankali, Har da ƙyar nake iya ji,
13Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.
14Na yi rawar jiki ina makyarkyata, Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro.
15Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata, Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba.
16Na ga wani abu can yana tsaye, Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne, Ina cikin wannan hali sai na ji murya,
17Ta ce, “‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah? Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa>
18Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai, Yakan sami laifi a wurin mala'ikunsa.
19Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa, Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.
20Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.
21Duk abin da ya mallaka an ɗauke, Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.”
1“Ka yi kira, ya Ayuba, ka gani, ko wani zai amsa! Akwai wani mala'ika da za ka juya zuwa gare shi>
2Ba shi da amfani ka dami kanka Har ka mutu, saboda tsarguwa, gama wannan wawanci ne, Da aikin rashin hankali.
3Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya, Amma nan da nan sai na la'anci gidajensu.
4Ko kaɗan, 'ya'yansu maza ba za su taɓa zama lafiya ba. Ba wanda zai tsaya musu a ɗakin shari'a.
5Mayunwata za su ci amfanin gonar wawa, Har da hatsin da yake girma cikin ƙayayuwa, Waɗanda suke jin ƙishirwa za su ji ƙyashin dukiyarsa.
6Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa, Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa.
7Ai, an haifi mutum domin wahala ne, Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta yake tashi.
8“In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah, In kai ƙarata a wurinsa.
9Ba za mu iya fahimtar manyan abubuwa da yake yi ba, Al'ajabansa kuwa ba su da iyaka.
10Yakan aiko da ruwan sama, Ya shayar da gonaki.
11I, Allah ne yake ɗaukaka masu tawali'u, Shi yake kuɓutar da dukan waɗanda suke makoki.
12Yakan birkitar da shirye-shiryen masu wayo.
13Yakan sa wa masu wayo tarko cikin dabarunsu, Har ba za su yi nasara a dukan abin da suke yi ba.
14Da rana sukan yi karo da duhu, Ko da tsakar rana ma lalube suke kamar ana duhu.
15Amma Allah yakan ceci matalauta daga mutuwa, Yakan kuma ceci masu bukata daga zalunci.
16Yakan sa matalauta su sa zuciya, Ya sa mugaye su yi shiru.
17“Mai farin ciki ne mutumin da Allah ya hora, Kada ka tsargu sa'ad da ya tsauta maka.
18Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka, Ciwon da ya ji maka da hannunsa, Da hannunsa yakan warkar.
19Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai, Ba muguntar da za ta taɓa ka.
20Yakan kiyaye ka da rai a lokacin yunwa, A yaƙi kuma yakan tsare ka daga mutuwa.
21Allah yakan kuɓutar da kai daga ƙarairayi da ɓata suna, Yakan cece ka daga hallaka.
22Aikin kama-karya da yunwa za su zama abin dariya a gare ka, Ba kuwa za ka ji tsoron namomin jeji ba.
23Ba za a sami duwatsu a gonakin da kake nomawa ba, Mugayen namomin jeji ba za su far maka ba.
24Sa'an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka, A sa'ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya.
25'Ya'yanka za su yi yawa kamar ciyawa, Kamar yadda alkama take a lokacin kakarta.
26Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.
27Kai, Ayuba, mun koyi wannan don mun daɗe muna nazari, Gaskiya ce, don haka ka yarda da wannan.”
1Ayuba ya amsa.
2“In da za a auna wahalata da ɓacin raina da ma'auni,
3Da sun fi yashin teku nauyi. Kada ka yi mamaki da maganganun da nake yi.
4Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau, Dafinsu kuwa ya ratsa jikina. Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.
5“Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya, In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.
6Amma wane ne zai iya cin abinci ba gishiri? Akwai daɗin ɗanɗano ga farin ruwan ƙwai>
7Ba na jin marmarin cin abinci irin haka, Kowane irin abu da na ci yakan sa mini cuta.
8“Me ya sa Allah ya ƙi ba ni abin da nake roƙo? Me ya sa ya ƙi yin abin da nake so>
9Da ma ya ci gaba kawai ya kashe ni, Ko ya sake ikonsa ya datse ni!
10Da na san zai yi haka, da sai in yi tsalle don murna, Da ba zan kula da tsananin azabar da nake ciki ba. Ba taɓa yin gāba da umarnan Allah ba.
11Wane ƙarfi ne nake da shi na rayuwa? Wane sa zuciya kuma nake da ita, tun da na tabbata mutuwa zan yi>
12Da dutse aka yi ni? Ko da tagulla aka yi jikina>
13Ba ni da sauran ƙarfi da zan ceci kaina, Ba inda zan juya in nemi taimako.
14“A cikin irin wannan wahala Ina bukatar amintattun abokai, Ko da na rabu da Allah, ko 'ina tare da shi.
15Amma ku abokaina, kun ruɗe ni, Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani. 16-17Rafin yana cike da iska mai laima da ƙanƙara, Amma lokacin zafi sai su ɓace, Kwacciyar rafin, sai ta bushe ba kome.
18Ayari sukan ɓata garin neman ruwa, Su yi ta gilo, har su marmace a hamada.
19Ayari daga Sheba da Tema suka yi ta nema,
20Amma sa zuciyarsu ta ƙare a gefen busassun rafuffuka,
21Kamar rafuffukan nan kuke a gare ni, Kun ga abin da ya same ni, kun gigita.
22Na roƙe ku ku ba ni kyauta ne? Ko kuwa na roƙe ku ku ba wani rashawa domina>
23Ko kuma na roƙe ku ku cece ni daga maƙiyi ko azzalumi ne>
24“To, sai ku koya mini, ku bayyana mini laifofina, Zan yi shiru in kasa kunne gare ku.
25Kila muhawara mai ma'ana ta rinjaye ni, Amma yanzu duk maganar shirme kuke yi.
26Kuna so ku amsa maganganuna? Don me? Mutumin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba wata maganar da zai yi in ba shirme ba.
27Kukan jefa wa bayi da marayu kuri'a, Kukan arzuta kanku daga abokanku na kurkusa.
28Ku dubi fuskata, Lalle ba zan faɗi ƙarya ba.
29Kai, kun zaƙe, ku daina aikata rashin adalci, Kada ku sa mini laifi, nake da gaskiya.
30Amma duk da haka kuna tsammani ƙarya nake yi. Kuna tsammani ba zan iya rarrabe tsakanin gaskiya da ƙarya ba.”
1“Kamar kamen soja na tilas, Haka zaman 'yan adam take, Kamar zaman mai aikin bauta.
2Kamar bawa ne wanda yake sa zuciya ga inuwa mai sanyi, Kamar ma'aikaci wanda yake sa zuciya ga lokacin biya.
3Wata da watanni ina ta aikin banza, Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini.
4Sa'ad da na kwanta barci, sai daren ya daɗa tsawo In yi ta jujjuyawa duk dare, in ƙosa gari ya waye.
5Jikina cike yake da tsutsotsi, Ƙuraje duka sun rufe shi, Daga miyakuna mugunya tana ta zuba.
6Kwanakina sun wuce ba sa zuciya, Sun wuce da sauri kamar ƙoshiyar saƙa.
7“Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai, Farin cikina ya riga ya ƙare.
8Kuna ganina yanzu, amma ba za ku sāke ganina ba. Idan kuka neme ni, za ku tarar ba na nan.
9Kamar girgijen da yake bajewa ya tafi, Hakanan mutum yake mutuwa.
10Ba kuwa zai ƙara komowa ba, Mutanen da suka san shi, duka za su manta da shi.
11A'a, ko kaɗan ba zan yi shiru ba! Haushi nake ji, zuciyata ta ɓaci, Dole ne in yi magana.
12“Ya Ubangiji, don me ka sa ni a waƙafi? Kana tsammani ni dodon ruwa ne>
13Na kwanta ina ƙoƙari in huta, Ina neman taimako don azabar da nake sha.
14Amma kai kana firgita ni da mafarkai, Kana aiko mini da wahayi da ganegane,
15Har nakan fi so a rataye ni, Gara in mutu da in rayu a wannan hali.
16Na fid da zuciya. Na gaji da rayuwa. Ku rabu da ni. Rayuwa ba ta da wata ma'ana.
17“Ya Ubangiji, me ya sa mutum yake da daraja haka a gare ka? Me ya sa kake lura da abin da yake yi>
18Kakan dube shi kowace safiya. Kana jarraba shi a kowane daƙiƙa.
19Ba za ka ko ɗan kawar da kai ba, Don in samu in haɗiye yau>
20Ko na yi zunubi ina ruwanka, Kai mai ɗaure mutane? Me ya sa ka maishe ni abin bārata? Ni wani babban kaya mai nauyi ne a gare ka>
21Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”
1Sai Bildad ya yi magana.
2“Ka gama maganganunka marasa kan gado duka>
3Allah bai taɓa yin danniya ba, Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.
4Lalle 'ya'yanka sun yi wa Allah zunubi, Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta.
5Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki.
6Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka, Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.
7Duk hasarar dukiyar nan da ka yi, ba kome ba ne In aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba.
8“Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā. Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya.
9Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai, Ba mu san kome ba, Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.
10Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka, Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.
11“Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa, Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama.
12In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa, Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.
13Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke, Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.
14Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.
15Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su? Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa>
16“Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana, Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka.
17Saiwoyinsu sukan nannaɗe duwatsu, Su riƙe kowane dutse da ƙarfi.
18Amma idan aka tumɓuke su, Ba wanda zai taɓa cewa sun kasance a wurin.
19Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan, Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu.
20“Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba, Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba.
21Zai sāke barinka ka yi dariya ka ƙyalƙyata kamar dā, Ka kuma yi sowa da murna matuƙa.
22Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya, Za a shafe gidajen mugaye.”
1Ayuba ya amsa.
2“Ai, na taɓa jin waɗannan duka, Amma ta ƙaƙa mutum zai yi jayayya da Allah har ya yi nasara>
3Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi? Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.
4Allah mai hikima ne, mai iko, Ba wanda zai iya ja in ja da shi.
5Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya, Ya hallaka su da fushinsa,
6Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya, Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.
7Allah yana da iko ya hana rana fitowa, Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.
8Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai, Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su.
9Allah ya rataye taurari a sararin sama, Wato su mafarauci da kare da zomo, Da kaza da 'ya'yanta da taurarin kudu.
10Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi. Ayyukan al'ajabansa ba su da iyaka.
11“Allah yana wucewa kusa da ni, Amma ba na ganinsa.
12Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi, Ba wanda yake tambayarsa cewa, “‘Me kake yi?”
13“Allah ba zai huce fushinsa ba. Ya murƙushe maƙiyansa waɗanda suka taimaki dodon ruwan nan da ake kira Rahab, wanda ya tayar masa.
14To, ƙaƙa zan yi in samo kalmomin da zan amsa wa Allah>
15Ko da yake ba ni da laifi, Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan, In roƙi Allah ya yi mini jinƙai, Shi da yake alƙalina.
16Amma duk da haka ko ya yardar mini in yi magana ma, Ban yi tsammani zai saurare ni ba.
17Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni, Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.
18Ya hana ni in ko shaƙata, Ina jin haushin dukan abin da yake yi mini.
19In gwada ƙarfi ne? To, a iya gwada wa Allah ƙarfi? In kai shi ƙara ne? Wa zai sa shi ya je>
20Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni, A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne. Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi.
21Ba ni da laifin kome, amma ba na ƙara damuwa. Na gaji da rayuwa.
22Don haka ban damu da kome ba. Da marar laifin da mai laifin duk, Allah zai hallaka mu.
23Sa'ad da marar laifi ya mutu farat ɗaya, Allah yakan yi dariya.
24Allah ya ba da duniya ga mugaye, Ya makantar da dukan alƙalai, Idan ba Allah ne ya yi hakanan ba, to, wa ya yi>
25“Kwanakina suna shuɗewa da sauri, ba mai kyau ko ɗaya.
26Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri, Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura.
27Idan an yi murmushi, Ina ƙoƙari in manta da azabata,
28Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni, Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi.
29Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne, To, me zai sa in damu>
30Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina.
31Allah ya jefa ni a kwatami, Har tufafina ma suna jin kunyata.
32Da a ce Allah mutum ne, Da sai in mayar masa da magana, Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a.
33Amma ga shi, ba wanda zai shiga tsakaninmu, Ba wanda zai shara'anta tsakanina da Allah.
34Ka daina hukunta ni, ya Allah! Ka daina razanar da ni.
35Ba na jin tsoro, Zan yi magana, domin na san zuciyata.”
1“Na gaji da rayuwa, Ku ji ina fama da baƙin ciki.
2Kada ka hukunta ni, ya Allah. Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.
3Daidai ne a gare ka ka yi mugunta? Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi? Sa'an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye>
4Yadda mutane suke duban abu, haka kake duba>
5Kai ma ranka gajere ne kamar namu>
6In haka ne, me ya sa kake bin diddigin dukan laifofina, Kana farautar dukan abin da na yi>
7Ka sani, ba ni da laifi, Kakuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.
8“Da ikonka ne ka yi ni, ka siffata ni, Yanzu kuma da ikon nan naka ne za ka hallaka ni.
9Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni. Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura>
10Kai ne ka ba mahaifina ƙarfin da zai haife ni, Kai ne ka sa na yi firma a cikin cikin mahaifiyata.
11Kai ne ka siffata jikina da ƙasusuwa da jijiyoyi, Ka rufe ƙasusuwan da nama, naman kuma ka rufe da fata.
12Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna, Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.
13Amma yanzu na sani, Dukan lokacin nan kana da wani nufi a ɓoye game da ni.
14Jira kake ka ga ko zan yi zunubi, Don ka ƙi gafarta mini.
15Da cewa na yi zunubi, na shiga uku ke nan a wurinka. Amma sa'ad da na yi abin kirki ba na samun yabo. Ina baƙin ciki ƙwarai, kunya ta rufe ni.
16Da zan ci nasara a kan kowane abu, Da sai ka yi ta farautata kamar zaki, Kana aikata al'ajabai don ka cuce ni.
17A koyaushe kakan karɓi shaida gāba da ni, Fushinka sai gaba gaba yake yi a kaina, Kakan yi mini farmaki a koyaushe.
18“Ya Allah, me ya sa ka bari aka haife ni? Da ma na mutu tun kafin wani ya gan ni!
19Da a ce daga cikin cikin mahaifiyata an wuce da ni zuwa kabari Da ya fi mini kyau bisa ga kasancewata.
20Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai! Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.
21An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau, Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,
22Ƙasa mai duhu, da inuwoyi da ɗimuwa Inda ko haske ma kansa duhu ne.”
1Zofar ya amsa.
2“Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu? Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai>
3Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka>
4Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne, Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.
5Da ma Allah zai amsa maka, Ya yi magana gāba da kai,
6Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa. Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam. Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.
7“Kana iya gane matuƙa da iyakar Girman Allah da na ikonsa>
8Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba, Amma ga shi, yana can nesa da kai, Allah ya san lahira, Amma kai ba ka sani ba.
9Fāɗin girman Allah ya fi duniya Ya kuma fi teku fāɗi.
10Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari'a, Wa zai iya hana shi>
11Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani, Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.
12Idan dakikan mutane sa yi hikima, To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.
13“Ayuba, ka shirya zuciyarka, Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.
14Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.
15Sa'an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya, Da ƙarfi da rashin tsoro.
16Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka, Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.
17Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana. Kwanakin ranka mafiya duhu Za su yi haske kamar ketowar alfijir.
18Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya, Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.
19Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba, Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.
20Amma mugaye za su dudduba ko'ina da fid da zuciya, Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta. Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.”
1Ayuba ya amsa.
2“Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a, Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.
3Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi, Ban ga yadda ka fi ni ba. Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.
4Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
5Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya. Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.
6Amma ɓarayi da marasa tsoron Allah suna zaune cikin salama, Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.
7“Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani, Suna da abu mai yawa da za su koya maka.
8Ka roƙi talikan da suke a duniya, da a cikin teku, hikimar da suke da ita.
9Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.
10Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa. Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.
11Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci, Hakanan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi. 12-13“Tsofaffi suna da hikima, Amma Allah yana da hikima da iko. Tsofaffi suna da tsinkaya, Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.
14Sa'ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa? Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku>
15Akan yi fari sa'ad da Allah ya hana ruwan sama, Rigyawa takan zo sa'ad da ya kwararo ruwa.
16Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yake Da macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.
17Yakan mai da hikimar masu mulki wauta, Yakan mai da shugabanni marasa tunani.
18Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.
19Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.
20Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su. Yakan kawar da hikimar tsofaffi.
21Yakan kunyatar da masu iko, Ya hana wa masu mulki ƙarfi.
22Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.
23Yakan sa sauran al'ummai su yi ƙarfi su ƙasaita, Sa'an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.
24Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye, Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,
25Su yi ta lalube cikin duhu, su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.”
1-2 “Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa, Na gane da shi sarai. Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani. Ba ku fi ni da kome ba.
3Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba, Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.
4Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi. Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.
5Kada ku faɗi kome, Wani sai ya ce kuna da hikima!
6“Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.
7Me ya sa kuke yin ƙarya? Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah>
8Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba? Kuna goyon bayan Allah? Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ko gaban shari'a>
9Da Allah ya bincike ku sosai, Zai iske wani abin kirki ne a cikinku? Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane>
10Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku, Duk da haka zai tsauta muku,
11Ikonsa kuwa zai razana ku.
12Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.
13“Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana. Duk abin da zai faru, ya faru.
14A shirye nake in yi kasai da raina.
15Na fid da zuciya ɗungum. To, in Allah ya kashe ni, sai me? Zan faɗa masa ƙarata.
16Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni, Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah.
17Sai a saurari bayanin da zan yi.
18A shirye nake in faɗi ƙarata, Domin na sani ina da gaskiya.
19“Ya Allah, za ka yi ƙarata? Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu.
20Ina da abu biyu da zan yi maka roƙo, Ka yarda da su, sa'an nan ba zan yi ƙoƙari in ɓoye ba.
21Wato ka daina hukuncin da kake yi mini, Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni.
22“Ka fara yin magana, ya Allah, ni kuwa zan amsa. Ko kuma ka bari in yi magana, sa'an nan ka amsa mini.
23Kuskure da laifi guda nawa na yi? Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su>
24Me ya sa kake guduna? Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi>
25Ƙoƙari kake ka firgita ni? Ni ba wani abu ba ne, ganye ne kawai, Ka fāɗa wa tattaka da yaƙi ne kawai.
26Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina, Har da laifofin da na yi na ƙuruciya.
27Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi, Kakan lura da kowace takawata, Har kana bin diddigin sawayena.
28Saboda wannan na zama abin kallo, ni kuwa kamar ragargazajjen itace ne, ko diddigaggiyar riga.”
1“Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.
2Sukan yi firma su bushe nan da nan kamar furanni, Sukan shuɗe kamar inuwa.
3Na ma isa ka dube ni ne, ya Allah? Ko ka gabatar da ni a gabanka, Ka yi mini shari'a>
4Ba wani abu tsarkakakke Da zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.
5Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can, An ƙayyade yawan watannin da zai yi, Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.
6Ka kawar da fuska daga gare shi, ka rabu da shi, Ka bar shi ya ji daɗin kwanakinsa na fama da aiki idan zai iya.
7“Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare, Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.
8Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa, Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,
9In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.
10Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan, Ya mutu, a ina yake a lokacin nan>
11“Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu, Har tekuna kuma su ƙafe.
12Amma matattu ba za su tashi ba daɗai, Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan. Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.
13“Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira, Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce, Sa'an nan ka lokacin da za ka tuna da ni!
14Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma? Amma zan jira lokaci mafi kyau, In jira sai lokacin wahala ya wuce.
15Sa'an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa, Za ka yi murna da ni, ni talikinka.
16Sa'an nan za ka lura da kowace takawata Amma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.
17Za ka soke zunubaina ka kawar da su, Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.
18“Lokaci na zuwa sa'ad da duwatsu za su fāɗi, Har ma za a kawar da duwatsun bakin teku.
19Ruwa zai zozaye duwatsu, su ragu, Ruwan sama mai ƙarfi zai kwashe jigawa, Kai ma ka bar mutane, ba su da sauran sa zuciya ko kaɗan.
20Ka fi ƙarfin mutum, ka kore shi har abada, Fuskarsa ta rikiɗe sa'ad da ya mutu.
21'Ya'yansa maza za su sami girma, amma sam, ba zai sani ba, Sam, ba wanda zai faɗa masa sa'ad da aka kunyatar da su.
22Ciwon jikinsa da ɓacin zuciyarsa kaɗai yake ji.”
1Elifaz ya yi magana.
2“Surutai, Ayuba! Surutai!
3Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka, Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma'ana.
4Kana karya jama'a, kana hana su jin tsoron Allah, Kana hana su yin addu'a gare shi.
5Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu, Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.
6Ba na bukata in kā da kai, Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.
7“Kana tsammani kai ne mutumin da aka haifa na farko? Sa'ad da Allah ya yi duwatsu kana nan>
8Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi? Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane>
9Ba wani abu da ka sani da mu ba mu sani ba.
10Daga wurin mutanen da suka yi furfura muka koyi hikimarmu. Mun koyi hikimarmu daga mutane waɗanda aka haife su Tun kafin a haifi mahaifinka.
11“Allah yana ta'azantar da kai, Me ya sa har yanzu ka ƙi kulawa da shi? Mun yi magana a madadinsa a natse da lafazi mai daɗi.
12Amma ka ta da hankalinka, Kana ta zazzare mana ido da fushi.
13Fushi kake yi da Allah, kana ƙinsa.
14Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai? Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah>
15Me ya sa Allah bai sakar wa mala'ikunsa kome ba? Har su ma ba tsarkaka suke a gare shi ba.
16Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa, Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.
17“Yanzu ka saurara, ya Ayuba, ga abin da na sani.
18Mutane masu hikima sun koya mini gaskiya Wadda suka koya daga wurin kakanninsu, Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.
19Ƙasaru 'yantacciya ce daga baƙi Ba wanda zai raba su da Allah.
20“Mugun mutum mai zaluntar sauran mutane Zai kasance da wahala muddin ransa.
21Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa. 'Yan fashi za su fāɗa masa Sa'ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.
22Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba, Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.
23Yana ta yawon neman abinci, yana ta cewa, “‘Ina yake?” Ya sani baƙin ciki ne yake jiransa a nan gaba. Kamar sarki mai iko,
24Haka masifa take shirin fāɗa masa.
25“Wannan shi ne ƙaddarar mutum, Wanda ya nuna wa Allah yatsa, Ya kuwa raina Mai Iko Dukka.
26Wannan mutum mai girmankai ne, ɗan tawaye.
27Ya ɗauki garkuwarsa kamar ɗan yaƙi, Ya ruga don ya yi yaƙi da Allah.
28Shi ne mutumin da ya ci birane da yaƙi, Ya ƙwace gidajen waɗanda suka tsere, Amma yaƙi ne zai hallaka birane da gidaje.
29Arzikinsa ba zai daɗe ba, Duk abin da ya mallaka ba zai daɗe ba. Har inuwarsa ma za ta shuɗe,
30Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba. Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa, Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.
31Idan wauta tasa ta kai shi ga dogara ga mugunta, To, mugunta ce kaɗai zai samu.
32Kafin kwanakinsa su cika zai bushe, Zai bushe kamar reshe, ba zai ƙara yin ganye ba.
33Zai ama kamar itacen inabi Wanda 'ya'yansa suka kakkaɓe tun kafin su nuna, Kamar itacen zaitun wanda bai taɓa yin 'ya'ya ba.
34Marasa tsoron Allah ba za su sami zuriya ba, Wuta za ta cinye gidajen da aka gina da dukiyar rashawa.
35Waɗannan su ne irin mutanen da suke shirya tarzoma, su aikata mugunta. Kullum zuciyarsu cike take da ruɗarwa.”
1Ayuba ya yi magana.
2“Ai, na taɓa jin magana irin wannan, Ta'aziyyar da kake yi azaba ce kawai.
3Ka dinga yin magana ke nan har abada? A kullum maganarka ita ce dahir>
4In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka, Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu. Da sai in kaɗa kaina da hikima, In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.
5Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa, In yi ta yi maka maganar ta'azantarwa.
6“Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka, Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.
7Ka gajiyar da ni, ya Allah, Ka shafe iyalina.
8Ka kama ni, kai maƙiyina ne. Na zama daga fata sai ƙasusuwa, Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.
9Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa, Yana dubana da ƙiyayya.
10Mutane sun buɗe baki don su haɗiye ni Suna kewaye ni suna ta marina.
11Allah ya bashe ni ha mugaye.
12Dā ina zamana da salama, Allah Allah ya maƙare ni, Ya fyaɗa ni ƙasa ya ragargaza ni. Allah ya maishe ni abin bārata.
13Ya harbe ni da kibau daga kowane gefe. Kiban sun ratsa jikina sun yi mini rauni, Duk da haka bai nuna tausayi ba!
14Ya yi ta yi mini rauni a kai a kai, Ya fāɗa mini kamar soja da ƙiyayya ta haukata.
15“Ina makoki saye da tsummoki, Ina zaune cikin ƙura a kunyace.
16Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur, Idanuna kuma suka yi luhuluhu.
17Amma ban yi wani aikin kama-karya ba, Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.
18“Duniya, kada ki ɓoye laifofin da aka yi mini! Kada ki yi shiru da roƙon da nake yi na neman adalci!
19Akwai wani a Sama Wanda zai tsaya mini ya goyi bayana.
20Ina so Allah ya ga hawayena, Ya kuma ji addu'ata.
21“Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina, Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
22Yanzu shekaruna wucewa suke yi, Ina bin hanyar da ba a komawa.”
1“Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi, Ba abin da ya rage mini sai kabari.
2Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba'a.
3Ni amintacce ne, ya Allah, ka yarda da maganata. Ba wanda zai goyi bayan abin da nake faɗa.
4Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah, Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.
5A karin maganar mutanen dā an ce, “‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi, 'Ya'yansa sā sha wahala!”
6Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina. Da mutane suka ji, Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.
7Baƙin cikina ya kusa makantar da ni, Hannuwana da ƙafafuna sun rame, sun zama kamar kyauro.
8Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana. Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.
9Har su ma da suke cewa su mutanen kirki ne Suna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.
10Amma da a ce dukansu za su zo su tsaya a gabana, Da ba zan sami mai hikima ko ɗaya daga cikinsu ba.
11“Kwanakina sun ƙare, shirye-shiryena sun kāsa, Ba ni da sauran sa zuciya.
12Amma abokaina sun ce dare shi ne hasken rana, Sun kuma ce haske yana kusa, Ko da yake ina cikin duhu.
13Ba ni da sauran sa zuciya, Gidana yana lahira, Inda zan kwanta in yi ta barci cikin duhu.
14Zan ce kabari shi ne mahaifina, Tsutsotsin da suke cinye ni su ne mahaifiyata, da 'yan'uwana mata.
15Ina ne zan sa zuciyata? Wane ne ya ga inda zan sa ta>
16Akwai wanda ya yi shiri a binne shi tare da ni, Mu tafi tare da shi zuwa lahira?”
1Bildad ya amsa.
2“Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru? Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.
3Me ya sa kake tsammani mu dakikai ne kamar shanu>
4Cutar kanka kake yi saboda fushin da kake ji. Duniya za ta ƙare ne sabili da kai? Za a kawar da duwatsu sabili da kai>
5“Za a kashe hasken mugun mutum, Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.
6Fitilar da take cikin alfarwarsa ba za ta ba da haske ba.
7A dā gagau yake tafiya, amma yanzu ɗingishi yake yi, Shawararsa ta kāshe shi.
8Yana tafiya, sai ya fāɗa cikin tarko. Tarkon ya kama ƙafafunsa.
9Tarko ya kama diddigensa ya riƙe shi,
10An binne masa tarko a ƙasa, An kafa masa tarko a hanyarsa.
11“Kewaye da shi duka razana tana jiransa, Duk inda ya nufa tana biye da shi,
12Dā attajiri ne, amma yanzu ya talauce, Kusa da shi bala'i na tsaye yana jiransa.
13Mummunan ciwo ya bazu ko'ina a jikinsa, Yana sa hannuwansa da ƙafafunsa su ruɓe,
14Dā yana zaune lafiya, Sai razana ta tatike shi, Ta jawo shi zuwa ga Sarkin Mutuwa.
15Yanzu kowa zai iya zama a alfarwarsa, Bayan da an karkashe ƙwayoyin cuta da farar wuta.
16Saiwoyinsa da rassansa suka yi yaushi suka bushe.
17Sunansa ya ƙare a gida da a jeji, Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
18Za a kore shi daga ƙasar masu rai, Za a kore shi daga haske zuwa duhu.
19Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.
20Daga gabas zuwa yamma, duk wanda ya ji labarin ƙaddarar da ta same shi, Zai yi makyarkyata, ya yi rawar jiki don tsoro.
21Wannan ita ce ƙaddarar mugaye, Wannan ita ce ƙaddarar mutane waɗanda ba su damu da kome na Allah ba.”
1Ayuba ya amsa.
2“Me ya sa kuke azabta ni da maganganu>
3A kowane lokaci kuna wulakanta ni, Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.
4Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne, Da me ya cuce ku>
5Tsammani kuke kun fi ni ne, Kuna ɗauka cewa wahalar da nake sha Ta tabbatar ni mai laifi ne.
6Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini, Ya kafa tarko don ya kama ni.
7Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba, Amma ba wanda ya kasa kunne. Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.
8Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa, Ya rufe hanyata da duhu,
9Gama ya kwashe dukiyata duka, Ya ɓata mini suna.
10Ya mammangare ni, Ya tumɓuke sa zuciyata, Ya bar ni in yi yaushi, in mutu.
11Allah ya zaburo mini da fushi, Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.
12Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini, Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto.
13“Yan'uwana sun yashe ni, Na zama baƙo ga idon sanina.
14Dangina da abokaina sun tafi.
15Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni. Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa.
16Sa'ad da na kira barana, ba ya amsawa, Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni.
17Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina, 'Yan'uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.
18'Yan yara sukan raina ni su yi mini dariya sa'ad da suka gan ni.
19Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama, Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana.
20Fatar jikina ta saki, ba ƙarfi, Da ƙyar na kuɓuta.
21Ku abokaina ne! Ku ji tausayina! Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa.
22Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi? Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba>
23“Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa, Ya rubuta shi a littafi!
24Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse, Ya rubuta su don su tabbata har abada!
25Amma na sani akwai wani a Samaniya Wanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.
26Ko da yake ciwo ya riga ya cinye fatata, A wannan jiki zan ga Allah.
27Zan gan shi ido da ido, Ba kuwa zai zama baƙo a gare ni ba. “Zuciyata ta karai saboda ku mutane kun ce,
28“‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?” Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini.
29Amma yanzu, sai ku ji tsoron takobi, Ku ji tsoron takobin da yake kawo hasalar Allah a kan zunubi. Don haka za ku sani akwai wani mai yin shari'a.”
1Zofar ya amsa.
2“Ayuba, ka ɓata mini rai, Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.
3Abin da ka faɗa raini ne, Amma na san yadda zan ba ka amsa.
4“Hakika ka sani tun daga zamanin dā, Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,
5Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.
6Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama. Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.
7Amma zai shuɗe kamar ƙura. Waɗanda dā suka san shi, Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.
8Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare, Ba kuwa zai a ƙara ganinsa ba.
9Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.
10Tilas 'ya'yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta, Tilas hannuwansa subiya dukiyar da ya ƙwace.
11Ko da yake gagau yake, ma'aikaci ne kuma sa'ad da yake yaro, Duk da haka ba da jimawa ba, zai zama ƙura. 12-13Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai, Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.
14Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci, Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.
15Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba, Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.
16Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake, Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.
17Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba, Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.
18Tilas ya rabu da dukan abin da ya yi wahalarsa. Ba dama ya mori dukiyarsa,
19Saboda zalunci da rashin kula da matalauta, Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.
20“Har abada ba zai kai ga samun abin da yake wahala ba.
21Sa'ad da ya ci ba zai yi saura ba, Gama yanzu dukiyarsa ta ƙare.
22A lokacin da yake gaɓar samunsa, Baƙin ciki mai nauyin gaske zai ragargaza shi.
23Bari ya ci duk irin abin da yake so! Allah zaihukunta shi da hasala da fushi.
24Lokacin da yake ƙoƙari ya kuɓuta daga takobin baƙin ƙarfe, Za a harbe shi da bakan tagulla ya fāɗi warwar.
25Kibiya za ya kafe a jikinsa Tsininta zai yi ta ɗiɗɗiga da jini, Razana ta kama zuciyarsa.
26Aka hallaka dukan abin da ya tattara, Wutar da ba hannun mutum ya kunna ba Ta ƙone shi, shi da iyalinsa duka.
27Samaniya ta bayyana zunubin wannan mutum, Duniya kuma ta ba da shaida gāba da shi.
28Dukan dukiyarsa za a hallaka ta a rigyawar fushin Allah.
29“Wannan ita ce ƙaddarar mugaye, Wadda Allah ya ƙayyade musu.”
1Ayuba ya amsa.
2“Ku kasa kunne ya abin da nake faɗa, Wannan ita ce ta'aziyyar da nake nema a gare ku.
3Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
4“Ba da 'yan adam nake faɗa ba, Ina da isasshen hanzarin da za sa in yi fushi.
5Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru, Ku firgita, ku yi shiru ba>
6Sa'ad da na tuna da abin da ya same ni, Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata in rawar jiki.
7Me ya sa Allah yake barin mugaye Har su tsufa su kuma yi arziki>
8'Ya'yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.
9Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala'i ba, Ba su taɓa zama a razane ba.
10Hakika shanunsu suna ta hayayyafa, Suna haihuwa ba wahala.
11'Ya'yansu suna guje-guje, Suna tsalle kamar 'yan raguna,
12Suna rawa ana kaɗa garaya, Ana busa sarewa.
13Suka yi zamansu da salama, Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.
14Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum, Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.
15Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah, Ko a yi addu'a gare shi domin samun wata fa'ida.
16Sukan ce ta wurin ƙarfinsu ne suka yi nasara, Amma ban yarda da irin tunaninsu ba.
17“An taɓa kashe hasken mugun mutum? Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu? Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,
18Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa? Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa>
19“Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa. A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi. Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.
20Bari dai a hukunta masu zunubi Su kuma ga hasalar Allah.
21Bayan rasuwar mutum, Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi>
22Mutum zai iya koya wa Allah? Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka>
23“Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu, Suna cikin farin ciki da jin daɗi,
24Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.
25Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba. Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.
26Amma duk abu guda ne su, mutuwa za su yi, a binne, Tsutsotsi su lulluɓe su duka.
27“Na san irin tunaninku na hassada,
28Kuna ta tambaya, “‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu, Wato mutumin da yake aikata mugunta?”
29“Ashe, ba ku yi magana da matafiya ba? Ba ku kuma san rahoton da suka kawo ba>
30A ranar da Allah ya yi fushi, ya yi hukunci, A kullum mugun na kaɗai yakan kuɓuta.
31Ba wanda zai fito fili ya zargi mugun, Ko ya mayar masa da martani.
32Sa'ad da aka ɗauke shi zuwa hurumi, A inda ake tsaron kabarinsa,
33Dubban mutane sukan tafi wurin jana'izarsa, Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali.
34“Amma ku, ƙoƙari kuke yi ku ta'azantar da ni da maganganun banza. Duk abinda kuka faɗa ƙarya ne!”
1Elifaz ya yi magana.
2“Akwai wani mutum, ko mafi hikima, Wanda zai amfani Allah>
3Gaskiyar da kake yi za ta amfani Allah? Ko kuwa abin kirki da kake yi zai taimake shi>
4Ai, ba don tsoron Allah da kake yi ba ne, Ya sa wannan tsautawa da jarrabawa suka same ka.
5Ko kusa ba haka ba ne, Amma saboda zunubi mai yawa da ka yi ne. Saboda kuma dukan muguntar da ka aikata.
6Don ka sa ɗan'uwanka ya biya ka bashin da kake binsa, Ka ƙwace tufafinsa, ka bar shi huntu.
7Ka hana wa waɗanda suke ji ƙishi ruwan sha, Ka hana waɗanda suke jin yunwa abinci.
8Ka mori ikonka da matsayinka, Don ka mallaki dukan ƙasar.
9Ba ƙin taimako kaɗai ka yi ba, Amma har marayu ma ka yi musu ƙwace, ka wulakanta su.
10Don haka ne yanzu akwai ramummuka ko'ina kewaye da kai, Tsoro ya kama ka nan da nan.
11An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, Rigyawa ta sha kanka.
12“Ashe, ba a can saman sammai Allah yake zaune ba? Sai ya sunkuya ya dubi taurari, ko da yake suna can sama ne.
13Duk da haka ka ce, “‘Allah bai san kome ba. Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari'a?”
14Kana tsammani gizagizai masu duhu sun hana shi gani, A lokacin da yake tafiya a kan iyakar da ke tsakanin duniya da sararin sama.
15“Ka ɗauka a ranka ka bi gurbin da mugaye suke bi kullum>
16Kafin ma su kai ga kwanakinsu, Sai rigyawa ta shafe su.
17Su ne mutanen da suka ƙi Allah, Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,
18Ko da yake Allah ne ya arzuta su. Ba na iya gane tunanin mugaye.
19Mutanen kirki suna murna, Marasa laifi kuma suna dariya Sa'ad da suka ga ana hukunta mugaye.
20Duk abin da mugu ya mallaka ya hallaka, Wuta kuwa ta lashe kowane abu da ya ragu.
21“Yanzu fa, Ayuba, sai ka yi sulhu da Allah, Ka daina ɗaukarsa kamar maƙiyinka, In ka yi haka, to, za ka sami albarka.
22Ka karɓi koyarwar da yake yi, Ka riƙe kalmominsa a zuciyarka.
23Hakika sai ka yi tawali'u, ka koma wurin Allah, Ka kawar da dukan muguntar da ake yi a gidanka.
24Ka jefar da zinariyarka, zinariyarka mafi kyau, Ka jefar da ita kamar dutse ko ƙura.
25Bari Allah Mai Iko Dukka ya zama zinariyarka, Ya zama azurfa, wadda aka tula dominka.
26Sa'an nan za ka dogara ga Allah kullayaumin, Ka kuma tarar shi ne asalin farin cikinka.
27Sa'ad da ka yi addu'a zai amsa maka, Za ka kuwa kiyaye alkawaran da ka yi.
28Za ka yi nasara a kowane abu da za ka yi, Haske kuma zai haskaka hanyarka.
29Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai, Yakan ceci mai tawali'u.
30Zai ceci wanda yake da laifi, Idan abin da kake yi daidai ne.”
1Ayuba ya amsa.
2“Duk da haka zan yi tawaye in yi wa Allah gunaguni, In dinga yin nishi.
3Da ma na san inda zan same shi, In kuma san yadda zan kai wurinsa,
4Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.
5Ina so in san irin amsar da zai mayar mini, Ina kuma so in san yadda zai amsa mini.
6Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni? A'a, zai saurara in na yi magana.
7Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina, Zai tabbatar da amincina duka.
8“Na nemi Allah a gaba, amma ban same shi a can ba, Ban kuwa same shi a baya ba sa'ad da na neme shi.
9Allah ya tafi wurin aiki a dama, Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba.
10Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.
11Da aminci ina bin hanyar da ya zaɓa, Ban kuwa taɓa kaucewa daga wannan gefe zuwa wancan ba.
12A kullum ina aikata abin da Allah ya umarta, Ina bin nufinsa, ba nufin kaina ba.
13“Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi, Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata.
14Zai tabbatar da abin da ya shirya domina, Wannan ma ɗaya daga cikin shiryeshiryen da ya yi ne.
15Don haka in rawar jiki a gabansa saboda tsoro.
16Allah Mai Iko Dukka ya lalatar da ƙarfin halina. Allah ne ya tsorata ni,
17Amma ban damu da damu ba, Ko da yake duhu ya dunɗe idanuna.”
1“Me ya sa Allah bai tsai da ranar da zai yi shari'a ba? Me ya sa ba ya tsai da ranar adalci ga Waɗanda suka bauta masa>
2Mugaye sukan ci iyaka, Don su ƙara yawan gonarsu. Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.
3Sukan saci jakunan marayu, Su kama san gwauruwa, Su ce sai ta biya basusuwanta.
4Sukan hana matalauta samun halaliyarsu, Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.
5Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji, Haka matalauta suke, Ba inda za su iya samo wa 'ya'yansu abinci.
6Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba, Su tattara 'ya'yan inabi daga gonakin mugaye.
7Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa, Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.
8Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda ka kwararowa daga kan duwatsu. Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.
9“Mugaye sukan bautar da yara marayu, Sukan kama 'ya'ya matalauta a bakin bashin da suke bi.
10Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura. Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.
11Suna matse mai daga 'ya'yan zaitun. Suna kuma matse ruwan inabi daga 'ya'yan inabi, Amma su kansu suna fama da ƙishi.
12Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni da Waɗanda suke baƙin mutuwa a birni, Amma Allah bai kula da addu'o'insu ba.
13“Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske, Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.
14Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci, Da dare kuma ya yi fashi.
15Mazinaci yakan jira sai da magariba, Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.
16Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje, Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.
17Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su, Sun saba da razanar duhu.
18“Rigyawa takan ci mugun mutum, Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la'anar Allah. Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.
19Kamar dusar ƙanƙara take a lokacin zafi da a lokacin fari, Haka mai zunubi yakan shuɗe daga ƙasar masu rai.
20Ba wanda zai tuna da shi, mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba. Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai. Za a sare mugunta kamar itace.
21Haka yake samun wanda ya wulakanta gwauraye. Bai kuma nuna alheri ga matan da ba su haihu ba.
22Allah, da ikonsa, yakan hallaka masu ƙarfi, Allah yakan aikata, sai mugun mutum ya mutu.
23Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya, Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.
24Mugun mutum yakan ci nasara ɗan lokaci, Daga nan sai ya yi yaushi kamar tsiro, Ya yi yaushi kamar karan dawa da aka yanke.
25Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne? Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”
1Bildad ya amsa.
2“Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa, A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.
3Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima? Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba>
4Akwai wanda ya isa ya zama adali, Ko mai tsarki a gaban Allah>
5Hasken wata ba haske ba ne a gare shi, Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.
6To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”
1Ayuba ya amsa.
2“Kai ne mai taimakon marar ƙarfi, Kai ne mai ceton rarrauna!
3Kai ne kake ba marar hikima shawara, Kai kake sanar da ilimi mai ma'ana a wadace!
4Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka? Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana>
5“Lahira tana rawa, Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro.
6Lahira tsirara take a gaban Allah, Haka kuma Hallaka take a gaban Allah.
7Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum, Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.
8Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa, Girgijen kuwa bai kece ba.
9Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa.
10Ya shata da'ira a kan fuskar teku, A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.
11Ginshiƙan samaniya sun girgiza, Sun firgita saboda tsautawarsa.
12Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku, Da saninsa ya hallaka dodon ruwan nan, wato Rahab.
13Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi garau, Ikonsa ne kuma ya sha zarar macijin nan mai gudu.
14Amma waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin al'amuransa. Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa. Amma wa zai iya fahimtar ikon tsawarsa?”
1Ayuba ya amsa.
2“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.
3Muddin ina numfashi, Ruhun Allah kuma yana cikin hancina
4Bakina ba zai faɗi ƙarya ba, Harshen kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.
5Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai, Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.
6Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba, Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.
7“Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum, Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.
8Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah? Sa'ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa>
9Allah kuwa zai ji kukansa sa'ad da wahala ta same shi>
10Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci>
11“Zan koya muku zancen ikon Allah, Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.
12Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku, Me ya sa kuka zama wawaye>
13“Wannan shi ne rabon mugaye daga wurin Allah, Gādo ne kuma wanda azzalumai za su karɓa daga wurin Mai Iko Dukka.
14Idan 'ya'yansu sun riɓaɓɓanya za su zama rabon takobi, Zuriyarsu kuwa ba za su sami isasshen abinci ba.
15Waɗanda suka tsira, annoba za ta kashe su, Matansu ba za su yi makokin mutuwarsu ba.
16Koda yake sun tsibe azurfa kamar turɓaya, Sun tara tufafi kamar ƙasa,
17Za su tara, amma adalai za su sa, Marasa laifi ne za su raba azurfar.
18Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo, Kamar bukkar mai tsaro.
19Attajirai za su kwanta, amma daga wannan shi ke nan, Za su buɗe ido su ga dukiyar nan ba ta.
20Razana za ta auka musu kamar rigyawa. Da dare iska za ta tafi da su.
21Iskar gabas za ta fauce su su tafi, Ta share su ta raba su da wurin zamansu.
22Za ta murɗe su ba tausayi, Hakika za su yi ƙoƙari su tsere daga ikonsa, Sai su yi ƙundumbala.
23Kowa zai tafa hannu ya yi musu tsaki har su tashi daga wurin da suke.”
1“Hakika akwai ma'adinai na azurfa, Da wuraren da ake tace zinariya.
2Mutane sukan haƙo baƙin ƙarfe daga ƙasa, Sukan narkar da tagulla daga dutse.
3Mutane sukan kawar da duhu, Sukan kuma bincike zuzzurfar iyaka, Sukan haƙo duwatsun da suke cikin duhu, duhu baƙi ƙirin.
4Sukan haƙa loto a fadama nesa da mutane, Sukan kafa abin lilo su yi ta lilo nesa da mutane.
5“Daga cikin ƙasa ake samun abinci, Amma a ƙarƙashinta yakan zama kamar wuta.
6Akwai duwatsu masu daraja cikin duwatsunta, Akwai zinariya a ƙurarta.
7Tsuntsu mai cin nama bai san wannan hanya ba. Shaho ma bai gan ta ba.
8Namomin jeji ba su taɓa bin hanyar ba, Ko zaki ma bai taɓa binta ba.
9“Mutane sun iya sarrafa ƙanƙarar dutse, Suna kuma iya tumɓuke tushen duwatsu.
10Sukan haƙa magudanar ruwa cikin duwatsu, Idanunsu sukan ga kowane abu mai daraja.
11Sukan datse rafuffuka su hana su gudu, Su binciko abin da yake ɓoye, ya fito sarari.
12Amma ina, a ina za a iya samun hikima? A ina za a samo haziƙanci>
13Mutane ba su san darajar hikima ba, Ba a samunta a ƙasar masu rai.
14Zurfafa sun ce, “‘Ba ta a cikinmu,” Tekuna kuma sun ce, “‘Ba ta tare da mu.”
15Ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba. Azurfa ba za ta iya biyan tamaninta ba.
16Ko zinariyar Ofir, ko onis, Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.
17Ba daidai take da zinariya ko madubi ba, Ba za a iya musayarta da kayayyakin da aka yi da zinariya tsantsa ba.
18Kada ma a ko ambaci murjani, Da duwatsu masu walƙiya. Gama tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai mafiya daraja duka.
19Ba za a daidaita tamaninta da na duwatsun tofaz na Habasha ba. Tamaninta ya fi na zinariya tsantsa.
20“To, daga in a hikima ta fito? A wane wuri kuma haziƙanci yake>
21Ba talikin da ya iya ganinta, Ko tsuntsun da yake tashi sama.
22Hallaka da Mutuwa sun ce, “‘Da kunnuwanmu mun ji ƙishinƙishin a kanta.”
23“Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta, Ya san inda hikima take,
24Saboda yana ganin duniya ɗungum, Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.
25Sa'ad da Allah ya sa iska ta hura, Ya yi wa tekuna iyaka.
26Sa'ad da ya ba da umarni ga ruwan sama, Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,
27Shi ya san hikimar, shi ya sanar, Ya tabbatar da ita, ya bincike ta sarai.
28“Allah ya ce wa mutane, “‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima, Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.”
1Ayuba ya ci gaba da magana.
2Da ma ina cikin lokacin da ya wuce ne, Lokacin da Allah yake lura da ni,
3Sa'ad da fitilarsa take haskaka mini, Ta wurin haskensa kuma nake tafiya da duhu,
4Kwanakin da nake gaɓar raina, Lokacin da ni'imar Allah take kan gidana,
5Sa'ad da Mai Iko Dukka take tare da ni, 'Ya'yana duka kuma suka kewaye ni,
6Sa'ad da aka wanke ƙafafuna da madara, Duwatsu kama suna ɓulɓulo mini da rafuffukan mai!
7A sa'ad da nakan tafi kofar birni, In shirya wurin zamana a dandali,
8Da samari sun gan ni, sai su kawar da jiki, Tsofaffi kuma su miƙe tsaye,
9Sarakuna sun yi shiru sun kame bakinsu.
10Manyan mutane sukan yi shiru, harshensu ya liƙe a dasashi.
11Waɗanda suka ji labarina sukan sa mini albarka, Waɗanda suka gan ni sukan yi na'am da ni.
12Domin sa'ad da matalauta suka yi kuka, ni nake cetonsu, Nakan taimaki marayu waɗanda ba su da mai taimako.
13Waɗanda suke bakin mutuwa sukan sa mini albarka, Na taimaki gwaurayen da mazansu suka mutu, Su raira waƙa don murna.
14Adalci shi ne suturata, Gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.
16Ni mahaifi ne ga matalauta, Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.
17Nakan karya muƙamuƙin marar adalci, In sa ya saki ganimar da ya kama.
18“Da na zaci zan mutu cikin sutura, Kwanakina kuma suriɓaɓɓanya, su yi yawa kamar yashi,
19Saiwoyina a shimfiɗe suke cikin ruwa, Dukan dare raɓa na sauka a kan rassana.
20Darajata garau take a gare ni, Bakana kullum sabo yake a hannuna.
21Mutane sukan kasa kunne su jira, su yi shiru Sa'ad da nake ba da shawara.
22Bayan na gama magana ba wanda zai ƙara wata magana. Maganata takan shige su.
23Suna jirana kamar yadda ake jiran ruwan sama, Da baki buɗe, kamar yadda ake jiran ruwan bazara.
24Nakan yi musu murmushi sa'ad da suka fid da zuciya, Ba su yi watsi da fara'ata ba.
25Nakan zaɓar musu hanyar da za su bi, Ina zaune kamar sarki a tsakanin mayaƙansu, Kamar mai ta'azantar da masu makoki.”
1“Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini, Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.
2Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari>
3Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame, Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.
4Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci, Sukan ci doyar jeji.
5Aka kore su daga cikin mutane, Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,
6Sai a kwazazzabai suke zama Da a ramummuka da kogwannin duwatsu.
7Suka yi ta kuka a jeji, Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.
8Mutane ne marasa hankali marasa suna! Aka kore su daga ƙasar.
9“Yanzu na zama abin waƙa gare su, Abin ba'a kuma a gare su.
10Suna ƙyamata, guduna suke yi, Da ganina, sai su tofa mini yau.
11Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙanta ni, Saboda haka sun raba ni da zuriyata,
12A hannun dama 'yan tā da zaune tsaye sun taso mini, Sun runtume ni, sun tura ni a hanyarsu ta hallakarwa.
13Sun datse hanyata, Sun jawo mini bala'i, Ba kuwa wanda ya hana su.
14Sun kutsa kamar waɗanda suka karya doka, Sun auka mini da dukan ƙarfinsu kamar yadda suka yi nufi.
15Sun firgita ni, Sun kori darajata kamar da iska, Wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.
16“Yanzu zuciyata ta narke Kwanakin wahala sun same ni.
17Da dare ƙasusuwana karkaɗuwa suke, Azaba tana ta gaigayata ba hutawa.
18An yi mini kamun kama-karya, An ci wuyan rigata.
19Allah ya jefar da ni cikin laka, Na zama kamar ƙura ko toka,
20“Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba, Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.
21Ka zama mugu a gare ni, Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.
22Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ni in hau ta, Ka yi ta shillo da ni cikin rugugin hadiri.
23Hakika na sani za ka kai ni ga mutuwa, Gidan da aka ƙaddara wa kowane mai rai.
24“Ashe, wanda yake gab da gagarumar hallaka, Ba zai miƙa hannu ya roƙi taimako a masifar da yake sha ba>
25Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba? Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba>
26Amma sa'ad da na sa zuciya ga alheri, sai ga mugunta, Sa'ad da nake jiran haske, sai ga duhu ya zo.
27Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya, Kwanakin wahala sun auko mini.
28Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba, Na tsaya a gaban taron jama'a, ina roƙon taimako.
29“Na zama ɗan'uwan dila, Na kuma zama aminin jiminai.
30Fatata ta takura, ta zama baƙa, Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,
31Saboda haka garayata ta zama ta makoki, Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”
1“Na yi alkawari da idanuna, Me zai sa in ƙyafaci budurwa>
2Wane rabo zan samu daga wurin Allah a Sama? Wane gādo kuma zan samu daga wurin Mai Iko Dukka a can samaniya>
3Yakan aika da masifa da lalacewa Ga waɗanda suke aikata abin da ba daidai ba.
4Allah ya san dukan abin da nake yi, Yana ƙididdige dukan takawata.
5“Idan ina tafiya da rashin gaskiya, Ina hanzari don in aikata yaudara,
6Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai, Zai kuwa san mutuncina.
7Idan dai na kauce daga hanya, Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna, Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,
8To, bari in shuka, wani ya ci amfanin, Bari a tumɓuke amfanin gonata.
9“Idan na yi sha'awar wata mace, Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10To, bari matata ta yi wa wani abinci, Bari waɗansu su kwana da ita.
11Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai, Wanda alƙalai ne za su hukunta.
12Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka, Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
13“Idan a ce ban kasa kunne ga kukan barorina mata da maza ba, Sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,
14To, wace amsa zan ba Allah sa'ad da ya tashi don ya hukuntar? Me zan iya faɗa sa'ad da Allah ya zo yi mini shari'a>
15Ashe, shi wanda ya halicce ni a cikin mahaifa, Ba shi ne ya halicce su ba? Shi wanda ya siffata mu a cikin mahaifa>
16“Ban taɓa ƙin taimakon matalauta ba, Ban kuma taɓa sa gwauruwar da mijinta ya mutu ta yi kuka ba,
17Kokuwa in bar marayu da yunwa sa'ad da nake cin abincina,
18Tun suna yara nake goyonsu, Ina lura da su kamar 'ya'yan cikina.
19“Amma idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura, Ko wani matalauci matar abin rufa,
20Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba, Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,
21Ko na ɗaga hannuna don in cuci maraya, Don na ga ina da kafar kuɓuta,
22To, ka sa kafaɗuna su ɓaɓɓalle daga inda suke. Ka kakkarya gwiwoyin hannuna.
23Gama bala'i daga wurin Allah ya razanar da ni, Saboda ɗaukakarsa ba zan iya yin kome ba.
24“Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,
25Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya, Ko saboda abin da na mallaka ne,
26Idan ga hasken rana nake zuba ido, Ko ga hasken farin wata ne,
27Zuciyata ta jarabtu ke nan a asirce, Ni da kaina ina sumbatar hannuna,
28Wannan ma zai zama laifi ne wanda alƙalai za su hukunta, Gama na zama munafukin Allah Mai Iko Dukka ke nan.
29“Idan na yi murna saboda wahala ta sami maƙiyana, Ko na yi fariya saboda mugun abu ya same shi,
30Ban yi zunubi da bakina ba, Ban nemi ran wani ta wurin la'anta shi ba.
31Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce, Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.
32Ban bar baƙi su kwana a titi ba, Ƙofar gidana a buɗe take ga matafiya.
33Idan na ɓoye laifofina a zuciyata,
34Ko na tsaya shiru saboda tsoron taron jama'a, Saboda kuma baƙar maganar mutane ta razanar da ni,
35Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni, Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa, Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini. “Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,
36Hakika da sai in ɗauke ta a kafaɗata, In kuwa naɗa ta a kaina kamar rawani.
37Da na ba Allah dukan lissafin abin da na taɓa yi, In tinƙare shi kamar ni basarauce ne.
38“Idan ƙasata tana kuka da ni, Ita da kunyoyinta,
39Ko na ci amfaninta ban biya ba, Ko na yi sanadin mutuwar mai ita,
40Ka sa ƙayayuwa su tsiro maimakon alkama, Tsire-tsire marasa amfani kuma maimakon sha'ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.
1Mutanen nan uku sun daina ba Ayuba amsa, saboda yana ganin kansa adali ne. 2Sai Elihu, ɗan Barakel, mutumin Buz, daga cikin iyalin Arama, ya husata, yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, bai bari Allah ya baratar da shi ba. 3Yana kuma fushi da abokan nan uku na Ayuba, domin sun rasa amsar da za su ba Ayuba, ko da yake sun hurta Ayuba ne yake da laifi. 4Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka. 5Sa'ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da wata amsa da za su ba Ayuba, sai ya yi fushi.
6Elihu ɗan Barakel, mutumin Buz, ya fara magana, ya ce, “A shekaru dai ni yaro ne ku kuwa manya ne, Don haka ina jin nauyi, Ina kuma jin tsoro in faɗa muku ra'ayina.
7Na ce wa kaina, “‘Ya kamata kwanaki su yi magana, Yawan shekaru kuma su koyar da hikima.”
8Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum, Yakan ba mutane basira.
9Ba tsofaffi ne masu wayo ba, Ba kuma masu yawan shekaru kaɗai suke gane abin da yake daidai ba.
10Don haka na ce ku kasa kunne gare ni, Bari in faɗa muku nawa ra'ayi.
11“Ga shi, na dakata na ji maganarku, Na kasa kunne ga maganarku ta hikima, Tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa.
12Na kasa kunne gare ku sosai, Amma ko ɗaya ba wanda ya kā da Ayuba. Ba kuma wanda ya ba shi amsar tambayarsa.
13Ku lura kada ku ce kuna da hikima, Allah ne kaɗai yake da iko ya kā da shi, ba mutum ba.
14Ba da ni Ayuba yake magana ba, Saboda haka ba zan amsa masa da irin amsarku ba.
15“Abin ya cika musu ciki, ba su ƙara amsawa ba, Wato ba su da ta cewa.
16Ni kuma sai in tsaya don ba su ce kome ba? Sun tsaya kurum, don ba su da ta cewa>
17A'a, ni kuma zan ba da tawa amsa, In kuma faɗi ra'ayina.
18Cike nake da magana, Ruhun da ka cikina ya iza ni.
19Ga zuciya tana kama da ruwan inabin da ba shi da mafitar iska, Kamar sabuwar salkar ruwan inabi wadda take shirin fashewa.
20Tilas in yi magana don in huce, Dole in ba da amsa.
21Ba zan yi wa kowa son zuciya ba, Ko kuma in yi wa wani fādanci.
22Gama ni ban iya fādanci ba, Idan na yi haka kuwa Mahaliccina zai kashe ni nan da nan.”
1“Amma yanzu, kai Ayuba, ka yarda ka ji maganata, Ka kasa kunne ga dukan abin da zan faɗa.
2Ga shi, na buɗe baki in yi magana.
3Maganar da zan hurta ainihin gaskiya da take a zuciyata ce, Abin da zan faɗa kuma dahir ne.
4Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
5“Ka amsa mini, in ka iya, Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
6Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah, Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.
7Don haka kada ka razana saboda ni, Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.
8“Hakika na ji maganar da ka yi, Na kuwa ji amon maganganunka,
9Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi, Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.
10Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,
11Ya saka ka a turu, Yana duban dukan al'amuranka.
12“Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa, Gama Allah ya fi kowane mutum girma.
13Me ya sa kake yi wa Allah gunaguni, Cewa ba ya karɓar maganarka ko ɗaya>
14Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne, I, har sau biyu, duk da haka mutum ba ya lura.
15Yakan sanar a mafarkai ko a wahayi Sa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su, A sa'ad da suke barci a gadajensu.
16Yakan buɗe kunnuwan mutane, Ya tsorata su da faɗakarwarsa,
17Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi, Ya kuma kawar musu da girmankai.
18Yakan hana su zuwa kabari, Ya hana ransu hallaka da takobi.
19“Akan hori mutum da cuta mai zafi a gadonsa, Ya yi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa,
20Ransa yana ƙyamar abinci, Yana ƙyamarsa kome daɗinsa kuwa.
21Yakan rame ƙangayau, ƙasusuwansa duk a waje.
22Yana gab da shiga kabari, Ransa yana hannun mala'ikun mutuwa.
23“Da a ce akwai wani mala'ika mai sulhuntawa a tsakani, Ko da ɗaya daga cikin dubu ne wanda zai faɗa wa mutum,
24Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce, “‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari, Na sami abin da zai fanshe shi!”
25Naman jikinsa zai koma kamar na saurayi, Zai komo kamar lokacin da yake gaɓar ƙarfinsa.
26Sa'an nan ne mutum zai yi addu'a ga Allah, ya karɓe shi, Ya zo gabansa da murna, Allah zai komar wa mutum da adalcinsa.
27Zai raira waƙa a gaban jama'a, ya ce, “‘Na yi zunubi. Ban yi daidai ba, Amma ba a sa ni in biya ba.
28Allah ya fanshe ni daga gangarawa zuwa kabari, Raina kuwa zai ga haske.”
29“Ga shi kuwa, Allah ya yi dukan waɗannan abubuwa sau biyu, har ma sau uku ga mutum,
30Don ya komo da ran mutum daga kabari, Domin a haskaka shi da hasken rai.
31“Haba Ayuba, ka kula fa, ka kasa kunne, Ga abin da nake faɗa, Ka yi shiru, zan yi magana.
32Amma idan kana da ta cewa, to, amsa, Yi magana, gama ina so in kuɓutar da kai.
33In kuwa ba haka ba, sai ka yi shiru, Ka kasa kunne gare ni, Zan kuwa koya maka hikima.”
1Elihu ya ci gaba.
2“Ku mutane masu hikima, ku ji maganata, Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.
3Kunne yake rarrabewa da magana, Kamar yadda harshe yake rarrabewa da ɗanɗanar abinci.
4Bari mu zaɓi abin da yake daidai, Bari kuma mu daidaita abin da yake mai kyau tsakanin junanmu.
5Gama Ayuba ya ce, “‘Ni marar laifi ne, Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.
6Duk da rashin laifina an ɗauke ni a maƙaryaci, Raunina ba ya warkuwa ko da yake ba ni da laifin kome.”
7“Wane irin mutum ne kai, Ayuba, Da kake shan raini kamar yadda kake shan ruwa,
8Wanda yake cuɗanya da ƙungiyar masu aikata laifi, Kana yawo tare da mugaye>
9Gama ka ce, “‘Bai amfana wa mutum kome ba Ya yi murna da Allah.”
10“Saboda haka ku kasa kunne gare ni, ku da kuke haziƙai, Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne, A wurin Mai Iko Dukka ba kuskure,
11Gama bisa ga aikin mutum yake sāka masa, Yana sa aniyarsa ta bi shi.
12Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba, Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.
13Wa ya shugabantar da shi a kan duniya? Wa ya mallakar masa da duniya duka>
14Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,
15Da duk mai rai ya hallaka, Mutum kuma ya koma ƙura.
16“Idan kai haziƙi ne, to, ji wannan, Kasa kunne ga abin da zan faɗa.
17Da Allah maƙiyin adalci ne, da ya yi mallaka? Ka iya sa wa Adali, Mai Iko Dukka laifi>
18Ka iya sa wa Allah laifi, Shi da ya ce, “‘Sarki marar amfani ne, Hakimai kuma mugaye?”
19Ba ya nuna sonkai ga sarakuna, Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta, Gama shi ya halicce su duka.
20Sukan mutu nan da nan, Da tsakar dare manya da ƙanana sukan shuɗe farat ɗaya, An kawar da su ba da hannun mutum ba.
21“Gama yana ganin al'amuran mutum, Yana kuma ganin dukan manufarsa.
22Ba wani duhu, ko duhu baƙi ƙirin Inda masu aikata mugunta za su ɓuya.
23Ba ajiyayyen lokacin da ya ajiye wa kowane mutum Da zai je shari'a a gaban Allah.
24Yakan ragargaza ƙarfafa ba tare da wani bincike ba, Ya sa waɗansu a madadinsu.
25Saboda sanin ayyukansu, Yakan kaɓantar da su da dare ya ragargaza su,
26Yakan buge su a gaban mutane saboda muguntarsu,
27Don sun daina binsa, ba su kula da ko ɗaya Daga cikin umarnansa ba.
28Suka sa matalauta su yi kuka ga Allah, Ya kuwa ji kukan waɗanda ake tsananta wa.
29Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi? Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa, Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum>
30Bai kamata marar tsoron Allah ya yi mulki ba, Don kada ya tura jama'a cikin tarko.
31“Akwai wanda zai ce wa Allah, “‘Ni horarre ne, Ba zan ƙara yin laifi ba>
32Ka koya mini abin da ban sani ba, Idan na yi laifi, ba zan ƙara yi ba.”
33Zai kuɓutar domin ya gamshe ka saboda ka ƙi yarda? Tilas kai za ka zaɓa, ba ni ba, Saboda haka sai ka hurta abin da ka sani.
34“Haziƙan mutane da mutum mai hikima da suka ji ni za su ce,
35“‘Ayuba yakan yi magana ne ba tare da sanin abin da yake yi ba, Maganarsa ba ta mai hangen nesa ba ce.
36Da ma a gwada Ayuba har ƙarshe, Saboda amsar da yake bayarwa ta mugaye.
37Gama ya ƙara zunubinsa da tayarwa, Yana tafa hannunsa a tsakaninmu, Yana yawaita maganganunsa gāba da Allah.”
1Elihu kuwa ya yi magana.
2“Ayuba, ba daidai ba ne, ka ce, Ba ka yi laifi a gaban Allah ba,
3Ka kuwa ce, “‘Wace riba na ci? Wane fifiko nake da shi fiye da idan na yi zunubi?”
4Zan ba ka amsa, kai da abokanka.
5Ka duba sama, Ka dubi gizagizai waɗanda suke can sama da kai.
6Idan ka yi zunubi, da me ka cuci Allah? Idan ka aikata laifofi da yawa, wace cuta ka yi masa>
7Idan kai adali ne da me ka ƙara masa, Ko kuwa me ya samu daga gare ka>
8Muguntarka ta shafi mutum ne kamarka, Haka kuma adalcinka ya shafi ɗan adam ne kawai.
9“Saboda yawan zalunci, jama'a sukan yi kuka, Suka nemi taimako, saboda matsin masu ƙarfi.
10Amma ba su juyo wurin Allah Mahaliccinsu ba, Wanda yakan sa a raira wanda da dare,
11Wanda yake koya mana fiye da namomin jeji da suke a duniya, Wanda ya sa muka fi tsuntsayen sama hikima.
12Suka yi kira don taimako, amma Allah bai amsa ba, Saboda suna da girmankan mugaye.
13Hakika Allah bai ji holoƙon kukansu ba, Allah Mai Iko Dukka kuwa bai kula da shi ba.
14“Ayuba, kai wane ne da za ka ce ba ka gan shi ba? Da kake cewa ƙararka tana gabansa, Jiransa kake yi>
15Yanzu fa saboda bai yi hukunci da fushinsa ba, Kamar kuma bai kula da laifi ba,
16Ayuba, maganarka marar ma'ana ce, Ka yi ta maganganu marasa hikima.”
1Elihu ya ci gaba da magana.
2“Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka, Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah.
3Zan tattaro ilimina daga nesa, In bayyana adalcin Mahaliccina.
4Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba, Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.
5“Ga shi kuwa, Allah Mai Girma, ba ya raina kowa, Shi mai girma ne, mai cikakkiyar basira.
6Ba ya rayar da masu laifi, Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu.
7Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya, Yakan kafa su har abada tare da sarakuna, A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.
8Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi, Da kuma igiyar wahala,
9Sa'an nan yakan sanar da su aikinsu Da laifofin da suke yi na ganganci.
10Yakan sa su saurari koyarwa, Da umarnai, cewa su juya, su bar mugunta.
11Idan suka kasa kunne suka bauta masa, Za su cika kwanakinsu da wadata, Shekarunsu kuma da jin daɗi.
12Amma idan ba su kasa kunne ba, Za a hallaka su da takobi, Su mutu jahilai.
13“Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu, Suna tanada wa kansu fushi, Ba su neman taimako sa'ad da ya ɗaure su.
14Sukan yi mutuwar ƙuruciya, Sukan ƙare kwanakinsu da kunya.
15Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani, Ta wurin tsananin da suke sha, Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.
16Allah ya tsamo ka daga cikin wahala, Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi, Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur.
17“Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye, Amma hukunci da adalci sun kama ka.
18Ka lura kada ka bar hasalarka ta sa ka raina Allah, Kada kuma ka bar wahalar da kake sha ta sa ka ɓata da mai fansarka.
19Kukanka ya iya raba ka da wahala, Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi>
20Kada ka ƙosa dare ya yi, Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse, Kowa ya kama gabansa.
21Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta, Gama saboda haka kake shan wannan tsanani, Don a tsare ka daga aikata mugunta.
22“Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa, Wa ya iya koyarwa kamarsa>
23Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi, Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure>
24“Ka tuna ka girmama aikinsa, Wanda mutane suke yabo.
25Dukan mutane sun ga ayyukansa, Sun hango shi daga nesa.
26Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne, Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba, Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27“Allah yakan sa ruwa ya zama tururi, Ya maishe shi ruwan sama,
28Wanda yakan kwararo daga sama, Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.
29Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama, Da tsawar da ake yi a cikinsu>
30Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi, Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu. Zurfin teku yana nan da duhunsa.
31Gama ta haka yakan shara'anta mutane, Yakan ba da abinci a yalwace.
32Ya cika hannunsa da walƙiya, Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.
33Tsawarta tana nuna kasancewar Allah, Ko shanu sun san da zuwan hadiri.”
1“Saboda wannan zuciyata takan kaɗu, Kamar ta yi tsalle daga inda take.
2Ku kasa kunne ga tsawar muryarsa, Ku saurara ga maganarsa mai ƙarfi.
3Yakan sako ta a ƙarƙashin samaniya duka, Walƙiyarsa takan zagaya dukan kusurwoyin duniya.
4Bayan walƙiyar akan ji rugugin muryarsa, Ya yi tsawa da muryarsa ta ɗaukaka, Ko da yake an ji muryarsa bai dakatar da tsawar ba.
5Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce, Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.
6Yakan umarci dusar ƙanƙara ta fāɗo bisa duniya, Yayyafi da ruwan sama kuwa su yi ƙarfi.
7Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa, Domin dukan mutane su san aikinsa.
8Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu, Su yi zamansu a ciki.
9Guguwa takan taso daga inda take, Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.
10Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara, Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.
11Yakan cika girgije mai duhu da ruwa, Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.
12Sukan yi ta kewayawa ta yadda ya bishe su, Don su cika dukan abin da ya umarce su a duniya da ake zaune a ciki.
13Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya, Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.
14“Ka ji wannan, ya Ayuba, Tsaya ka tuna da ayyukan Allah masu banmamaki.
15Koka san yadda Allah yakan ba su umarni, Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka>
16Ko kuma ka san yadda gizagizai suke tsaye daram a sararin sama? Ayyukan banmamaki na Allah, cikakken masani!
17Ko ka san abin da yake sa ka jin gumi Sa'ad da iskar kudu take hurowa>
18Ka iya yin yadda ya yi, Kamar yadda ya shimfiɗa sararin sama daram, Kamar narkakken madubi>
19Ka koya mana abin da za mu faɗa masa, Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.
20A iya faɗa masa, cewa zan yi magana? Mutum ya taɓa so a haɗiye shi da rai>
21“A yanzu dai mutane ba su iya duban haske, Sa'ad da yake haskakawa a sararin sama, Bayan da iska ta hura ta share gizagizai sarai.
22Daga arewa wani haske kamar na zinariya ya fito mai banmamaki, Allah yana saye da ɗaukaka mai bantsoro.
23Mai Iko Dukka, ya fi ƙarfin ganewarmu, Shi mai girma ne, da iko, da gaskiya, Da yalwataccen adalci, Ba ya garari.
24Saboda haka mutane suke tsoronsa, Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”
1Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.
2“Wane ne wannan da yake ɓāta shawara Da maganganu marasa ma'ana>
3Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji, Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
4A ina kaka sa'ad da na aza harsashin gina duniya? Faɗa mini idan ka sani.
5Wane ne ya zayyana kusurwoyinta? Hakika ka sani. Wane ne kuma ya auna ta>
6A kan me aka kafa tushenta? Wa ya aza dutsen kan kusurwarta>
7Sa'ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare, Sai mala'iku duka suka yi sowa saboda murna.
8“Wa ya yi wa teku iyaka Sa'ad da ta tumbatso daga zurfafa>
9Sa'ad da na suturta ta da gizagizai, Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.
10Na sa mata iyakoki, Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,
11Na ce mata, “‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan, Ba za ki wuce ba. Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.”
12“Ayuba, a dukan kwanakinka Ka taɓa umartar wayewar gari, Ko ka sa alfijir ya keto>
13Da gari ya waye, Ka kawar da muguntar da ake yi da dare>
14Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi, Yakan rine kamar riga.
15Akan hana wa mugaye haske, Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.
16“Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku? Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku>
17An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa? Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin>
18Ko ka san iyakar fāɗin duniya? Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.
19“Ina hanya zuwa wurin da haske yake? A ina kuma duhu yake>
20Ka san iyakarsa ko mafarinsa>
21Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka, Shekarunka kuwa suna da yawa.
22“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara? Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara>
23Na adana su ne don lokacin wahala, Domin ranar faɗa da ta yaƙi.
24Ina hanya zuwa inda rana take fitowa, Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko'ina>
25“Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi? Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi>
26Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane, Da a cikin hamada inda ba kowa,
27Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa, Har ta tsiro da ciyayi>
28“Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa>
29Wace ce mahaifiyar ƙanƙara? Wace ce kuma ta haifi jaura>
30Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse, Teku ta daskare.
31“Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta? Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo>
32Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu>
33Ka san ka'idodin sammai? Ko ka iya faɗar yadda suka danganta da duniya>
34“Kana iya yi wa gizagizai tsawa, Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka>
35Ka iya aikar walƙiyoyi su tafi, Sa'an nan su ce maka, “‘Ga mu mun zo?”
36Wa ya sa hikima a gizagizai, Ko kuma wa ya ba da ganewa ga kāsashi>
37Akwai mai hikimar da zai iya ƙidaya gizagizai? Ko kuwa wa zai iya karkato da salkunan ruwan sammai,
38Sa'ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam>
39“Ka iya farauto wa zakoki abinci? Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki,
40Sa'ad da suke fako a kogwanninsu, Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu>
41Wa yake tanada wa hankaka abincinsa, Sa'ad da 'ya'yansa suke kuka ga Allah, Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?”
1“Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa? Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa>
2Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin haihuwarsu>
3Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu, Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu>
4'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura, Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.
5“Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so? Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,
6Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa, Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa>
7Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a, Ba ruwansa da tsawar masu kora.
8Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa, A can yake neman kowane ɗanyen abu.
9“Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki? Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka>
10Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya? Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka>
11Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa? Za ka kuma bar masa aikinka>
12Ka gaskata zai komo, Ya kawo maka hatsi a masussukarka>
13“Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma! Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.
14Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta, Ta bar ƙasa ta ɗumama su.
15Takan manta wani ya iya taka su su fashe, Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.
16Takan yi wa 'ya'yanta mugunta, Sai ka ce ba nata ba ne, Ko da yake ta sha wahala a banza, Duk da haka ba ta damu ba.
17Gama Allah bai ba ta hikima ba, Bai kuwa ba ta fahimi ba.
18Amma sa'ad da ta sheƙa a guje, Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.
19“Kai ka yi wa doki ƙarfinsa? Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza>
20Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango? Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro.
21Yakan yi nishi a fadama, Yana murna saboda ƙarfinsa, A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.
22Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba. Ba ya da baya ga takobi,
23Kibau na ta shillo a kansa, Māsu suna ta gilmawa a gabansa.
24Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa, Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.
25Sa'ad da aka busa ƙaho yana ce, “‘Madalla.” Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu.
26“Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi, Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu>
27Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi sama Ta yi sheƙarta can ƙwanƙoli>
28A kan dutse take zaune, a can take gidanta, Cikin ruƙuƙin duwatsu.
29Daga can takan tsinkayi abincinta Idanunta sukan hango shi tun daga nesa.
30'Yayanta sukan tsotsi jini, A inda kisassu suke, can take.”
1Ubangiji ya yi wa Ayuba magana.
2“Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka? Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”
3Ayuba ya amsa wa Ubangiji ya ce,
4“Ai, ni ba a bakin kome nake ba, Wace amsa zan ba ka? Na rufe bakina na yi gam.
5Ai, na riga na yi magana sau ɗaya, har ma sau biyu, Ba zan amsa ba, ba zan ƙara cewa kome ba.”
6Sa'an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba daga cikin guguwa, ya ce,
7“Tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji, Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
8Kai kanka za ka sa mini laifi? Za ka kā da ni don kai ka barata>
9Kana da ƙarfi kamar na Allah? Kana iya tsawa da murya kamar tasa>
10“Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka, Ka yafa daraja da maƙami.
11Ka kwararar da rigyawar fushinka, Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.
12Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi, Ka tattake mugaye a inda suke.
13Dukansu ka binne su a ƙasa, Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.
14Sa'an nan ni kaina kuma zan sanar da kai, Cewa da hannun damanka za ka yi nasara.
15“Ga dorina wanda ni na halicce ta, Kamar yadda na halicce ka, Tana cin ciyawa kamar sa.
16Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta, Ikonta yana cikin tsakar cikinta.
17Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al'ul, Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya
18Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.
19“Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah, Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi!
20Gama duwatsu suke ba ta abinci, A inda dukan namomin jeji suke wasa.
21Takan kwanta a inuwar ƙaddaji, Ta ɓuya a cikin iwa, da a fadama.
22Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce, Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
23Ga shi, ba ta jin tsoron tumbatsar kogi, A natse take, ko da ta bakinta rigyawar Urdun take wucewa.
24Akwai wanda zai iya kama ta da ƙugiya, Ko ya sa mata asirka?”
1“Ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kama kifi? Ko kuma ka iya zarge harshensa da igiya>
2Ka iya sa wa hancinsa asirka? Ko ka iya huda muƙamuƙinsa da ƙugiya>
3Zai ta yi maka godo? Zai yi maka magana da tattausar murya>
4Zai ƙulla alkawari da kai, Cewa zai zama baranka har abada>
5Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata>
6'Yan kasuwa za su saye shi? Za su karkasa shi ga fatake>
7Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna? Kokuwa kansa da māsu>
8In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!
9Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi, Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.
10Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi. Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana>
11Wa ya ba ni har da zan biya shi? Dukan abin da yake cikin duniyar nan nawa ne.
12“Ba zan yi shiru a kan zancen gaɓoɓinsa ba, Ko babban ƙarfinsa, ko kyan ƙirarsa.
13Wa zai iya yaga babbar rigarsa? Kokuwa ya kware sulkensa da aka ninka biyu>
14Wa zai iya buɗe leɓunansa? Gama haƙoransa masu bantsoro ne.
15An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne, An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.
16Suna haɗe da juna gam, Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.
17Sun manne da juna har ba su rabuwa.
18Atishawarsa takan walƙata walƙiya, Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.
19Harsunan wuta kamar jiniya suna fitowa daga bakinsa, Tartsatsin wuta suna ta fitowa.
20Hayaƙi na fita daga hancins Kamar tururi daga tukunya mai tafasa, Ko bāgar da ta kama wuta.
21Numfashinsa yakan kunna gawayi, Harshen wuta yana fita daga bakinsa.
22A wuyansa ƙarfi yake zaune, Razana tana rausaya a gabansa.
23Namansa yana ninke, manne da juna, Gama ba ya motsi.
24Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse, Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.
25Sa'ad da ya miƙe tsaye, ƙarfafa sukan tsorata, Su yi ta tutturmushe juna.
26Ko an sare shi da takobi, Ko an nashe shi da māshi ko hargi, ko an jefe shi, Ba sa yi masa kome.
27Kamar ciyawa baƙin ƙarfe yake a gare shi, Tagulla ma kamar ruɓaɓɓen itace take.
28Kibiya ba za ta sa ya gudu ba, Jifar majajjawa a gare shi kamar jifa da tushiyoyi ce.
29A gare shi kulake kamar tushiyoyi ne, Kwaranniyar karugga takan ba shi dariya.
30Kaifin ƙamborin cikinsa kamar tsingaro ne. Yana jan ciki a cikin laka kamar lular ƙarfe.
31Yakansa zurfafa su tafasa kamar tukunya, Teku kuwa kamar kwalabar man shafawarsa.
32Idan yana wucewa sai a ga hasken dārewar ruwa, Yakansa zurfafa su yi kumfa.
33A duniya ba kamarsa, Taliki ne wanda ba shi da tsoro.
34Yakan dubi kowane abu da yake mai alfarma, Shi sarki ne a bisa dukan masu girmankai.”
1Ayuba ya amsa wa Ubangiji.
2“Na sani kai kake da ikon yin dukan abu, Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.
3Wane ne wannan marar ilimi da zai ɓoye shawara? Saboda haka na hurta abin da ban gane ba, Abubuwa waɗanda ban gane ba suna banmamaki ƙwarai.
4Ka ce, “‘Kasa kunne, zan yi magana da kai, Zan yi maka tambaya, ka ba ni amsa.”
5Dā jin labarinka nake, Amma yanzu na gan ka ido da ido.
6Saboda haka na ga ni ba kome ba ne, Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”
7Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni, kamar yadda bawana Ayuba ya yi ba. 8Yanzu fa, sai ku kama bijimai bakwai da raguna bakwai, ku kai wa Ayuba, ku miƙa su hadaya ta ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi addu'a dominku, ni kuwa zan amsa addu'arsa don kada in sāka muku bisa ga wautarku. Gama ba ku faɗi gaskiya game da ni kamar yadda bawana Ayuba ya yi ba.”
9Sai Elifaz mutumin Teman, da Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na'ama suka tafi suka yi kamar yadda Ubangiji ya faɗa musu, Ubangiji kuwa ya karɓi addu'ar Ayuba.
10Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa'ad da ya yi addu'a domin abokansa, sai Ubangiji ya mayar masa da riɓin abin da yake da shi dā. 11Sa'an nan dukan 'yan'uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta'azantar da shi, saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi 'yan kuɗi da zoben zinariya.
12Ubangiji ya sa wa wannan zamani na Ayuba albarka, har fiye da na farko. An ba shi tumaki dubu goma sha huɗu (14,000), da raƙuma dubu shida (6,000), da takarkari dubu biyu (2,000), da jakai mata dubu ɗaya (1,000). 13Ya kuma haifi 'ya'ya maza bakwai, mata uku. 14Ya raɗa wa ta farin suna Yemima, da ta biyun Keziya, da ta ukun Keren-Haffuk. 15Duk ƙasar ba 'yan mata kyawawa kamar 'ya'yan Ayuba. Mahaifinsu kuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu maza.
16Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba'in bayan wannan, ya ga 'ya'yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu. 17Sa'an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.