Joel

Yowel

1

Ɓarnar Fāra

1Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.

2Ku dattawa, ku kasa kunne, Bari kowa da kowa da ke cikin Yahuza, ya kasa kunne. Wani abu mai kamar wannan ya taɓa faruwa a lokacinku, Ko a lokacin kakanninku>

3Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa, 'Ya'yanku kuma su faɗa wa 'ya'yansu, 'Ya'yansu kuma su faɗa wa tsara mai zuwa.

4Abin da ɗango ya bari fara ta ci, Abin da fara ta bari burduduwa ta ci.

5Ku farka, ku yi ta kuka, ku bugaggu, Ku yi kuka, ku mashayan ruwan inabi, An lalatar da 'ya'yan inabin Da ake yin sabon ruwan inabi da su.

6Rundunar ta aukar wa ƙasarmu, Tana da ƙarfi, ba ta kuma ƙidayuwa, Haƙoranta suna da kaifi kamar na zaki.

7Ta lalatar da kurangar inabinmu, Ta cinye itatuwan ɓaurenmu. Ta gaigaye ɓawo duka, Saboda haka rassan sun zama fari fat.

8Ya jama'a, ku yi kuka Kamar yarinyar da ke makokin rasuwar saurayinta.

9Ba hatsi ko ruwan inabin Da za a yi hadaya da su cikin Haikalin. Firistoci masu miƙa wa Ubangiji hadaya suna makoki.

10Ba kome a gonaki, Ƙasa tana makoki, Domin an lalatar da hatsin, 'Ya'yan inabi sun bushe, Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.

11Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki, Ku yi kuka, ku da kuke lura da gonakin inabi, Gama alkama, da sha'ir, Da dukan amfanin gonaki sun lalace.

12Kurangar inabi ta bushe, Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi, Rumman, da dabino, da gawasa, Da dukan itatuwan gonaki sun bushe. Murna ta ƙare a wurin mutane.

13Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a bagaden Ubangiji, Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka! Ku shiga Haikali, ku kwana, Kuna saye da tufafin makoki, Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za a yi hadaya da su, A cikin Haikalin Allahnku.

14Ku sa a yi azumi, Ku kira muhimmin taro. Ku tara dattawa da dukan mutanen ƙasar A Haikalin Ubangiji Allahnku, Ku yi kuka ga Ubangiji.

15Taku ta ƙare a wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.

16An lalatar da amfanin gonaki a kan idonmu, Ba murna a Haikalin Allahnmu.

17Itatuwa sun mutu a busasshiyar ƙasa, Ba hatsin da za a adana a rumbu, Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.

18Dabbobi suna nishi! Garkunan shanu sun ruɗe Domin ba su da makiyaya. Garkunan tumaki da awaki kuma suna shan azaba.

19Ina kuka a gare ka, ya Ubangiji, Domin ciyayi da itatuwa sun bushe, Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.

20Har ma namomin jeji suna kuka a gare ka, Domin rafuffuka sun bushe, Ciyayi kuma sun bushe, Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.

2

Fāra ta Zama musu Alamar Ranar Ubangiji

1Ku busa ƙaho, ku yi gangami, A cikin Sihiyona, tsattsarkan dutsen Allah! Duk mutanen ƙasar za su yi rawar jiki, Domin ranar Ubangiji tana zuwa, ta yi kusa.

2Za ta zama rana ce mai duhu dulum, Ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Runduna mai ƙarfi tana tasowa, Kamar ketowar hasken safiya bisa tsaunuka. Faufau ba a taɓa ganin irinta ba, Ba kuwa za a sāke ganin irinta ba.

3Tana cinye shuke-shuke kamar wuta, Ƙasa kamar gonar Adnin take kafin ta zo, Amma a bayanta ta zama hamada, Ba abin da ya tsere mata.

4Kamar doki take, Tana gudu kamar dokin yaƙi.

5Motsin tsallenta a kan duwatsu kamar Motsin karusa ne. Kamar kuma amon wutar da ke cin tattaka. Kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgar yaƙi.

6Da zuwanta mutane sukan firgita, Dukan fuskoki sukan ɓaci.

7Takan auka kamar mayaƙa, Takan hau garu kamar sojoji, Takan yi tafiya, Kowa ta miƙe sosai inda ta sa gaba, Ba ta kaucewa.

8Ba ta hawan hanyar juna, Kowa tana bin hanyarta. Takan kutsa cikin abokan gāba, ba a iya tsai da ita.

9Takan ruga cikin birni, Takan hau garu a guje, Takan hau gidaje, Takan shiga ta tagogi kamar ɓarawo.

10Duniya takan girgiza saboda ita, Sammai sukan yi rawar jiki. Rana da wata sukan duhunta, Taurari kuwa sukan daina haskakawa.

11Ubangiji yakan umarci rundunarsa, Rundunarsa mai cika umarninsa babba ce, mai ƙarfi, Gama ranar Ubangiji babba ce mai banrazana. Wa zai iya daurewa da ita>

Jinƙan Ubangiji

12“Koyanzu,” in ji Ubangiji, “Ku juyo wurina da zuciya ɗaya, Da azumi, da kuka, da makoki,

13Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci.

14Wa ya sani ko Ubangiji Allahnmu zai sāke nufinsa, Ya sa mana albarka, Har mu miƙa masa hadaya ta gari da ta sha>

15Ku busa ƙaho a Sihiyona, Ku sa a yi azumi, Ku kira muhimmin taro.

16Ku tattara jama'a wuri ɗaya, Ku tsarkake taron jama'a, Ku tattara dattawa da yara, Har da jarirai masu shan mama. Ku sa ango ya fito daga cikin turakarsa, Amarya kuma ta fito daga cikin ɗakinta.

17Sai firistoci masu hidimar Ubangiji, Su yi kuka a tsakanin shirayi da bagade, Su ce, “Ya Ubangiji, ka ceci jama'arka, Kada ka bar gādonka ya zama abin zargi Da abin ba'a a tsakiyar al'ummai. Don kada al'ummai su ce, “‘Ina Allahnsu?”

18Sai Ubangiji ya ji kishin ƙasarsa, Ya kuma ji ƙan mutanensa.

19Sa'an nan ya ce musu, “Ga shi, zan ba ku hatsi da ruwan inabi, da mai, Za ku ƙoshi. Ba zan sa ku ƙara zama abin zargi ga al'ummai ba.

20Zan kawar muku da waɗanda suka zo daga arewa, Zan kori waɗansunsu zuwa cikin hamada. Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikin Tekun Gishiri, Zan kori sahunsu na baya, zuwa cikin Bahar Rum. Gawawwakinsu za su yi ɗoyi. Zan yi musu haka saboda dukan abin da suka yi muku.”

21Kada ki ji tsoro, ya ƙasa, Ki yi farin ciki, ki yi murna, Gama Ubangiji ne ya yi waɗannan manyan al'amura.

22Kada ku ji tsoro, ku dabbobin saura, Gama wuraren kiwo a jeji sun yi kore shar. Itatuwa suna ta yin 'ya'ya, Itacen ɓaure da kurangar inabi suna ta yin 'ya'ya sosai.

23Ya ku mutanen Sihiyona, ku yi murna, Ku yi farin ciki da Ubangiji Allahnku, Gama ya ba ku ruwan farko Domin shaidar gafarar da ya yi muku, Ya kwararo muku da ruwan farko da na ƙarshe da yawa kamar dā.

24Masussukai za su cika da hatsi, Wuraren matse ruwan inabi za su malala da ruwan inabi.

25“Zan mayar muku da abin da kuka yi hasararsa A shekarun da fara ta cinye amfaninku, Wato ɗango da fara mai gaigayewa, da mai cinyewa, Su ne babbar rundunata wadda na aiko muku.

26Yanzu za ku ci abinci a wadace ku ƙoshi, Za ku yabi sunan Ubangiji Allahnku, Wanda ya yi muku abubuwa masu banmamaki, Ba kuma za a ƙara kunyatar da mutanena ba.

27Ku mutanen Isra'ila, za ku sani ina cikinku, Ni ne kuwa Ubangiji Allahnku, ba wani kuma, Ba kuma za a ƙara kunyatar da mutanena ba.”

Za a Ba da Ruhun Allah

28“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.

29A lokacin zan zubo Ruhuna, Har a kan barori mata da maza.

30“Zan yi faɗakarwa a kan wannan rana A sararin sama da a duniya. Za a ga jini, da wuta, da murtukewar hayaƙi,

31Rana za ta duhunta, Wata zai zama ja wur kamar jini, Kafin isowar babbar ranan nan mai bantsoro ta Ubangiji.

32Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, Akwai waɗanda ke a Dutsen Sihiyona da Urushalima Da za su tsira, Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su tsira.”

3

Shari'ar Al'ummai

1“A wannan lokaci zan mayar wa Yahuza da Urushalima da wadatarsu.

2Zan tattara dukan al'ummai, In kai su kwarin Yehoshafat. A can zan yi musu shari'a A kan dukan abin da suka yi wa jama'ata. Sun warwatsa Isra'ilawa a sauran ƙasashe, Suka rarraba ƙasata.

3Sun jefa kuri'a a kan mutanena, Sun sayar da yara, mata da maza, zuwa bauta Don su biya karuwai da ruwan inabi.

4“Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa. 5Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku. 6Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa. 7Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu. 8Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”

9Ku sanar wa al'ummai da wannan, Su yi shirin yaƙi, Su kira mayaƙa! Su tattaro sojoji, su zo!

10Su bubbuge allunan garmunansu, Su yi takuba da su. Su ƙera māsu da wuƙaƙen da ake yi wa itatuwa aski. Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumi ne!”

11Su gaggauta, su zo su al'ummai da ke kewaye, Su tattaru a kwarin. “Ya Ubangiji, ka saukar da rundunarka mai ƙarfi.”

12“Sai al'ummai su yi shiri, Su zo kwarin Yehoshafat, Gama a can zan zauna in shara'anta al'umman da ke kewaye,

13Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi. Su shiga su tattaka, Gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika. Manyan randuna sun cika suna tumbatsa, Gama muguntarsu da yawa take.”

14Dubun dubbai suna cikin kwarin da za a yanke shari'a! Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa a kwarin yanke shari'a.

15Rana da wata sun yi duhu, Taurari kuma ba su haskakawa.

Ceton Yahuza

16Ubangiji yana magana da ƙarfi daga Sihiyona, Yana tsawa daga Urushalima, Sammai da duniya sun girgiza. Amma Ubangiji shi ne mafakar jama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.

17“Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda ke zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.

18“A wannan lokaci tsaunuka za su rufu da kurangar inabi, Tuddai za su cika da shanu, Dukan rafuffukan Yahuza za su gudano da ruwa, Maɓuɓɓuga za ta gudano daga Haikalin Ubangiji, Ta shayar da kwarin Shittim.

19“Masar za ta zama hamada, Edom kuma za ta zama kufai, Saboda kama-karya da suka yi wa mutanen Yahuza, Saboda sun zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu,

20Za a zauna a Yahuza da Urushalima dukan tsararraki har abada.

21Zan sāka alhakin jininsu, Ba zan kuɓutar da mai laifi ba, Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”