Joshua
1Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki, 2“Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'ar nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa. 3Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa. 4Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku. 5Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba. 6Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu. 7Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da hakanan za ka arzuta cikin dukan harkokinka. 8Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara. 9Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”
10Sai Joshuwa ya umarci shugabannin jama'a, ya ce, 11“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, “‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.”
12Joshuwa kuma ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, 13“Ku tuna da maganar da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku da ita, ya ce, “‘Ubangiji Allahnku zai hutar da ku, zai kuma ba ku wannan ƙasa.” 14Da matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobinku, za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a wannan hayin Urdun, amma jarumawanku su haye tare da 'yan'uwanku da shirin yaƙi domin su taimake su, 15har lokacin da Ubangiji ya hutar da 'yan'uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa'an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.”
16Su kuwa suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Iyakar abin da ka umarce mu za mu yi, duk inda ka aike mu kuma za mu tafi. 17Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya a kowane abu hakanan za mu yi maka biyayya, Ubangiji Allahnka dai ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance tare da Musa. 18Duk wanda ya ƙi bin umarninka, bai kuwa yi biyayya da maganarka da dukan irin abin da ka umarce shi ba, za a kashe shi. Kai dai ka dāge, ka yi ƙarfin hali.”
1Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.
2Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da dad dare domin su bincike ƙasar.”
3Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, “Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka.”
4Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba, 5da maraice kuma, sa'ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu.” 6Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin. 7Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin.
8Amma kafin 'yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin, 9ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya ba ku ƙasar, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku. 10Gama mun ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Bahar Maliya ya ƙafe a gabanku a sa'ad da kuka fito daga Masar, da irin abin da kuka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon da Og, waɗanda kuka hallakar da su sarai. 11Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa. 12Yanzu fa, ku rantse mini da Ubangiji, kamar yadda na yi muku alheri, haka ku kuma za ku yi wa gidan mahaifina, ku ba ni tabbatacciyar alama. 13Ku ceci mahaifina, da mahaifiyata, da 'yan'uwana mata da maza, da dukan abin da yake nasu, ku ceci rayukanmu daga mutuwa.”
14Mutanen kuwa suka ce mata, “Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al'amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa'ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”
15Sa'an nan ta zurarar da su da igiya ta taga, gama gidanta yana haɗe da garun birnin ne. 16Sai ta ce musu, “Tafi cikin tsaunuka domin kada masu bin sawun su same ku, ku ɓuya a wurin kwana uku, har masu bin sawun su komo, sa'an nan ku kama hanyarku.”
17Mutanen suka ce mata, “Za mu kuɓuta daga rantsuwarki wadda kika rantsar da mu. 18A lokacin da za mu shigo ƙasar, sai ki ɗaura wannan jan kirtani a tagar da kika zurarar da mu, ki kuma kawo mahaifinki, da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki, da dukan iyalin gidan mahaifinki a gidanki. 19Idan waninku ya fita daga ƙofar gidanki zuwa kan titi, to, alhakin jininsa yana bisa kansa, mu kuwa sai mu kuɓuta. Amma idan aka sa wa wani hannu wanda yake cikin gida tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu. 20Amma idan kika tone al'amarin nan namu, to za mu kuɓuta daga rantsuwar da kika rantsar da mu.”
21Sai ta ce, “Bisa ga maganarku ya zama haka.” Sa'an nan ta sallame su, suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan kirtanin a tagar.
22Sai suka tafi, suka shiga tsaunuka, suka yi zamansu a can kwana uku har masu bin sawun suka koma, gama masu bin sawun suka yi ta nema ko'ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba. 23Mutanen nan biyu suka sauko daga tsaunuka, suka haye zuwa wurin Joshuwa ɗan Nun, suka faɗa masa dukan abin da ya same su. 24Suka kuma ce masa, “Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu.”
1Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye. 2Bayan kwana uku sai shugabannin jama'a suka bibiya zango, 3suna umartar jama'ar suna cewa, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi, 4domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.”
5Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku.” 6Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama'ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama'a.
7Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai. 8Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, “‘Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.”
9Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.” 10Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku. 11Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun. 12Yanzu fa, ku ɗauki mutum goma sha biyu daga kabilanku, wato mutum ɗaya daga kowace kabila. 13A sa'ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda.” 14-15(Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe, 16sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama'a kuwa suka haye daura da Yariko. 17A sa'ad da Isra'ilawa duka suke tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa.
1Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, 2“Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama'a, wato mutum ɗaya na kowace kabila. 3Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.” 4Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra'ilawa, mutum guda na kowace kabila.
5Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila. 6Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana 'ya'yanku za su tambaye ku, su ce, “‘Ina ma'anar waɗannan duwatsu a gare ku?” 7Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, “‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.” Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”
8Sai Isra'ilawa suka yi yadda Joshuwa ya umarta, suka ɗauki duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun bisa ga yawan kabilansu kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Joshuwa, suka haye da su zuwa inda suka sauka, a can suka ajiye su. 9Joshuwa kuma ya kafa duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun, a wurin da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya, duwatsun suna nan har wa yau. 10Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama'a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi. Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye. 11Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar. 12Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su. 13Mutum wajen dubu arba'in ne (40,000), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko. 14A ranar nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.
15Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, 16“Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.” 17Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun. 18Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.
19Rana ta goma ga watan ɗaya jama'a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko. 20Joshuwa ya kafa duwatsun nan goma sha biyu da suka ɗauko daga Urdun a Gilgal. 21Sai ya ce wa Isra'ilawa, “Sa'ad da wata rana 'ya'yanku suka tambayi ubanninsu ma'anar duwatsun nan, 22sa'an nan za ku sanar da 'ya'yanku cewa Isra'ilawa sun haye Urdun da ƙafa a kan sandararriyar ƙasa! 23Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya ƙafe, har kuka haye kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa Bahar Maliya ta ƙafe har muka haye, 24domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”
1Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.
2A lokacin kuwa Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu, ka yi wa mazajen Isra'ila kaciya.” 3Sai Joshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa mutanen kaciya a Gibeyat-ha'aralot, wato dutsen kaciya.
8Da aka gama yi wa al'ummar duka kaciya, sai suka zauna a zango har suka warke. 9Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “A wannan rana na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka, har wa yau ake kiran sunan wurin Gilgal, wato a kawar.
10Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko. 11A kashegarin idin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, waina marar yisti da busasshiyar tsaba. 12Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, mannar ta yanke, mutanen Isra'ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan'ana.
13Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”
14Sai mutumin ya ce, “A'a, gama na zo ne kamar sarkin yaƙin rundunar Ubangiji.” Sai Joshuwa ya sunkuyar da kansa, ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada, ya ce masa, “Wace magana ce Ubangiji yake faɗa wa bawansa?”
15Sarkin yaƙin rundunar Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Cire takalmanka da suke a ƙafafunka, gama wurin da kake tsaye tsattsarka ne.” Haka kuwa Joshuwa ya yi.
1Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra'ilawa. 2Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka. 3Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida. 4Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni. 5Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.” 6Joshuwa ɗan Nun kuwa ya kirawo firistoci, ya ce musu, “Ɗauki akwatin alkawarin, sa'an nan firistoci bakwai su ɗauki ƙaho bakwai na raguna su wuce a gaban akwatin alkawarin Ubangiji.” 7Ya kuma ce wa jama'a, “Ku wuce, ku zaga birnin, masu makamai kuma su wuce a gaban akwatin Ubangiji.”
8Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama'a, firistoci bakwai da suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su. 9Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, 'yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni. 10Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, “Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa'an nan za ku yi ihu.” 11Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa'an nan suka koma zango, suka kwana.
12Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji. 13Firistoci bakwai ɗin da suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna, suka wuce gaban akwatin Ubangiji suna ta busawa, masu makamai suna tafe a gabansu, 'yan tsaron baya suna biye da akwatin Ubangiji, ana ta busa ƙahoni. 14A rana ta biyu kuma suka zaga birnin sau ɗaya, sa'an nan suka koma zango. Haka suka yi ta yi har kwana shida.
15A rana ta bakwai kuwa suka tashi da sassafe, suka yi sammako, suka zaga birnin yadda suka saba yi har sau bakwai. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai. 16A zagawa ta bakwai, sa'ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin. 17Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwar nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika. 18Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa. 19Amma dukan azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe keɓaɓɓu ne ga Ubangiji. Za a shigar da su cikin taskar masujadar Ubangiji.” 20Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin. 21Sa'an nan suka hallakar da dukan abin da yake a cikin birnin, da mata da maza, yara da tsofaffi, da shanu da tumaki, da jakai.
22Sa'an nan Joshuwa ya ce wa mutum biyu ɗin nan da suka leƙo asirin ƙasar, “Tafi gidan karuwar, ku fitar da ita, da dukan waɗanda suke nata kamar yadda kuka rantse mata.” 23Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra'ilawa. 24Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji. 25Amma Joshuwa ya bar Rahab da rai, da ita da iyalin mahaifinta, da dukan waɗanda suke nata. Rahab ta yi zamanta wurin Isra'ilawa har wa yau domin ta ɓoye manzannin da Joshuwa ya aika don su leƙo asirin Yariko.
26A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce, “La'ananne ne mutum a gaban Ubangiji Wanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko. A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa, A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa.”
27Ubangiji yana tare da Joshuwa, ya kuwa yi suna cikin dukan ƙasar.
1Amma Isra'ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
2Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.
3Da suka komo wurin Joshuwa, sai suka ce masa, “Kada dukan mutane su tafi, amma a bar mutum wajen dubu biyu ko uku su tafi su bugi Ai, kada a sa dukan mutane su sha wahalar zuwa can, domin su kima ne.” 4Sai mutum wajen dubu uku daga cikin jama'a suka tafi, amma mutanen Ai suka kore su. 5Mutanen Ai suka kashe mutum wajen talatin da shida daga cikin Isra'ilawa, suka runtume su tun daga ƙofar garin har zuwa Shebarim, suka yi ta karkashe su har zuwa gangaren. Zukatan mutanen Isra'ila kuwa suka narke, suka zama kamar ruwa.
6Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu. 7Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'ar nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun. 8Ya Ubangiji, me zan ce bayan da Isra'ilawa sun ba da baya ga abokan gābansu? 9Gama Kan'aniyawa da dukan mazaunan ƙasar za su ji labari, su kewaye mu, su shafe sunanmu daga duniya, to, me za ka yi don sunanka mai girma?”
10Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Tashi, don me ka fāɗi rubda ciki? 11Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya. 12Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku. 13Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, “‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku. 14Da safe kuwa za a gabatar da ku kabila kabila, zai zama kuwa kabilar da Ubangiji ya ware, za a gabatar da ita iyali iyali, iyalin da Ubangiji ya ware kuma, za a gabatar da su gida gida, gidan kuma da Ubangiji ya ware, za a gabatar da su mutum mutum. 15Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.”
16Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza. 17Ya gabatar da iyalan Yahuza, aka ware iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera gida gida, aka ware gidan Zebdi. 18Ya gabatar da iyalin gidansa mutum mutum, aka ware Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza. 19Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”
20Akan kuwa ya amsa wa Joshuwa, ya ce, “A gaskiya kam, na yi wa Ubangiji, Allah na Isra'ila zunubi. Ga abin da na yi. 21A cikin kayan ganimar na ga wata kyakkyawar alkyabba irin ta Shinar, da shekel dari biyu na azurfa, da sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai na yi ƙyashi, na kwashe su, ga su a binne a ƙasa a alfarwata da azurfa a ƙarƙashi.”
22Joshuwa ya aika da manzanni, suka sheƙa a guje zuwa alfarwar, suka tarar da abubuwan a binne cikin alfarwarsa da azurfa a ƙarƙashi. 23Sai suka kwaso suka kawo wa Joshuwa da dukan Isra'ilawa, suka ajiye su a gaban Ubangiji. 24Joshuwa kuwa tare da dukan Isra'ilawa suka ɗauki Akan, ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da sandan zinariya, da 'ya'yansa mata da maza, da shanunsa, da jakunansa, da tumakinsa, da alfarwarsa, da dukan abin da yake da shi, suka kawo su a Kwarin Akor. 25Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra'ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta. 26Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa'an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.
1Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka. 2Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”
3Joshuwa kuwa tare da dukan mayaƙa suka yi shirin tashi zuwa Ai. Sai Joshuwa ya zaɓi jarumawa ƙarfafa dubu talatin (30,000), ya aike su da dad dare. 4Ya umarce su, ya ce, “Ku tafi, ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birni da yawa, amma dukanku ku kasance da shiri sosai. 5Da ni da dukan mutanen da suke tare da ni za mu je kusa da birnin. Sa'ad da za su fito don su yi karo da mu kamar dā, za mu gudu daga gare su. 6Za su kuwa fito su bi mu. Mu kuwa za mu janye su nesa da birnin, gama za su ce, “‘Suna gudunmu kamar dā.” Haka fa, za mu gudu daga gare su. 7Ku kuwa ku tashi daga kwanto, ku ci birnin, gama Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku. 8A sa'ad da kuka ci birnin, ku sa wa birnin wuta yadda Ubangiji ya ce. Ku lura fa, da abin da na umarce ku.” 9Sai Joshuwa ya sallame su, suka tafi inda za su yi kwanto. Suka yi fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma shi ya kwana tare da jama'a.
10Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe ya tattara mutanen, ya tafi tare da shugabannin Isra'ilawa, suka wuce gaba, suka bi da mutane zuwa Ai. 11Dukan mayaƙan da suke tare da shi, suka tafi kusa da birnin, suka kafa sansaninsu arewacin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari. 12Ya kuma zaɓi mutum wajen dubu biyar (5,000) ya sa su yi kwanto tsakanin Betel da Ai, yamma da birnin. 13Mutanensu suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na 'yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Joshuwa ya kwana a kwarin. 14A sa'ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra'ilawa, amma bai san akwai 'yan kwanto a bayan birnin ba. 15Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji. 16Saboda haka aka kira dukan mutanen da suke cikin birnin, su fafare su. Da suka fafari Joshuwa, sai aka janye su nesa da birnin. 17Ba namijin da ya ragu cikin Ai da bai fita ya fafari Isra'ilawa ba, suka bar birnin a buɗe, suka fafari Isra'ilawa.
18Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka miƙa mashin da yake hannunka wajen Ai, gama zan ba da ita a hannunka.” Sai Joshuwa ya miƙa mashin da yake hannunsa wajen birnin. Nan da nan da ya ɗaga hannunsa 19'yan kwanto suka tashi da sauri daga maɓoyansu, suka shiga birnin, suka ci shi, suka yi sauri, suka cuna wa birnin wuta. 20Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu. 21Sa'ad da Joshuwa da dukan Isra'ilawa suka ga 'yan kwanto sun ci birnin, da kuma hayaƙi ya murtuke bisa, suka juya kan mutanen Ai, suka ɗibge su. 22Sauran Isra'ilawa kuwa suka fito daga cikin birnin suka fāɗa musu. Har ya zama suna tsakiyar Isra'ilawa gaba da baya. Isra'ilawa suka karkashe su, har ba wanda ya tsira ko ya tsere. 23Amma suka kama Sarkin Ai da rai, suka kai shi wurin Joshuwa.
24Sa'ad da Isra'ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra'ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta. 25A wannan rana aka ƙarasa mutanen Ai duka, mata da maza. Jimillarsu ta kai mutum dubu goma sha biyu (12,000). 26Joshuwa bai janye hannunsa da riƙon mashin ba, sai da ya hallaka mazaunan Ai sarai. 27Dabbobi da kayayyaki na birnin kaɗai Isra'ilawa suka kwashe ganima bisa ga faɗar Ubangiji zuwa ga Joshuwa. 28Haka fa Joshuwa ya ƙone Ai, ya maishe ta tsibin kufai har abada. Tana nan haka har wa yau. 29Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa'ad da rana yake faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau.
(M. Sh 27.1-26)
30Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra'ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal. 31Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra'ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama. 32A nan, a idon Isra'ilawa, Joshuwa ya kafa dokokin Musa a bisa duwatsun. 33Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka. 34Bayan haka ya karanta dukan zantuttukan shari'a, da na albarka da na la'ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin Attaura. 35Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.
1Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari, 2sai suka tattaru, suka haɗa kansu domin su yaƙi Joshuwa da Isra'ilawa.
3Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai, 4sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki. 5Suka kuma sa tsofaffin takalma waɗanda suka sha gyara, da tsofaffin tufafi. Dukan guzurinsu ya bushe, ya yi fumfuna. 6Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”
7Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”
8Su kuwa suka ce wa Joshuwa, “Mu bayinka ne.” Joshuwa kuwa ya ce musu, “Su wane ne ku? Daga ina kuka zo kuma?”
9Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar, 10da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot. 11Dattawanmu da dukan mazaunan ƙasarmu suka ce mana mu ɗauki guzuri a hannunmu don tafiya, mu tafi taryarku, mu ce muku, “‘Mu bayinku ne, yanzu dai sai ku yi mana alkawari.” 12Wannan abinci, da ɗuminsa muka ɗauko shi daga gidajenmu a ranar da muka fito zuwa gare ku, amma ga shi, yanzu ya bushe ya yi fumfuna. 13Waɗannan salkunan ruwan inabi kuma da muka cika sababbi ne, amma ga shi, sun kyakkece, waɗannan tufafinmu kuma da takalmanmu sun tsufa saboda tsawon hanya!” 14Sai Isra'ilawa suka ɗiba daga cikin guzurin Hiwiyawa, amma ba su nemi shawara wurin Ubangiji ba. 15Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama'a kuma suka rantse musu.
16Amma a rana ta uku bayan da suka yi alkawari da su, suka ji cewa, su maƙwabtansu ne, suna zaune a cikinsu. 17Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim. 18Amma Isra'ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama'a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila. Dukan jama'a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin. 19Amma shugabanni suka ce wa dukan jama'a, “Mun riga mun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, don haka yanzu ba shi yiwuwa mu taɓa su. 20Abin da za mu yi musu ke nan, a bar su da rai saboda rantsuwar da muka rantse musu don kada mu jawo wa kanmu fushin Ubangiji!” 21Suka ƙara da cewa, “A bar su da rai domin su zama masu sarar mana itace, da masu ɗebo mana ruwa.”
22Joshuwa kuwa ya kirawo su, ya ce musu, “Me ya sa kuka ruɗe mu da cewa, “‘Muna nesa da ku ƙwarai,” ga shi kuwa, a tsakiyarmu kuke zaune? 23Yanzu fa ku la'anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.”
24Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka. 25Yanzu dai muna a hannunka, ka yi yadda ka ga ya yi maka kyau.” 26Haka kuwa ya yi musu, ya cece su daga hannun Isra'ilawa, har ba su kashe su ba. 27Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama'a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.
1Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra'ilawa, har suna zama cikinsu. 2Sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne. 3Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce, 4“Ku zo, ku taimake ni, mu yaƙi Gibeyon, gama ta yi amana da Joshuwa da Isra'ilawa.” 5Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.
6Gibeyonawa dai suka aika zuwa wurin Joshuwa a zango cikin Gilgal cewa, “Kada ka yar da bayinka. Ka zo wurinmu da sauri, ka cece mu, ka taimake mu, gama dukan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu.”
7Sai Joshuwa ya tashi daga Gilgal da dukan mayaƙa, da dukan jarumawa tare da shi. 8Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.” 9Sai Joshuwa ya tafi ya auka musu ba labari, gama daga Gilgal ya bi dare zuwa can. 10Ubangiji kuwa ya sa suka gigice a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa suka kashe su da yawa a Gibeyon, suka runtume su ta hanyar haurawa zuwa Ber-horon. Suka yi ta karkashe su har zuwa Azeka da Makkeda. 11Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.
12Sa'an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra'ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce, “Ke rana, ki tsaya a Gibeyon, Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”
13Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, Har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu. Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda. 14Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.
15Sa'an nan Joshuwa ya koma zango a Gilgal tare da dukan Isra'ilawa.
16Waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda. 17Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.”
18Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa'an nan ku sa mutane su yi tsaronsu. 19Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a Hannunku.” 20Joshuwa da jama'ar Isra'ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu. 21Sa'an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra'ilawa.
22Sa'an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.” 23Suka yi hakanan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon. 24Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu. 25Sai Joshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, gama haka Ubangiji zai yi da dukan abokan gābanku waɗanda za ku yi yaƙi da su.” 26Sa'an nan Joshuwa ya buga su, ya kashe su, ya kuma rataye kowane ɗayansu a bisa itace. Suka yini a rataye har maraice. 27Amma sa'ad da rana take faɗuwa, Joshuwa ya umarta, aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan, aka jefa su cikin kogon inda suka ɓuya. Sa'an nan suka rufe bakin kogon da manyan duwatsu. Har wa yau suna nan.
28A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da Yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.
29Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra'ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna. 30Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.
31Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra'ilawa duka, zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata. 32Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra'ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna.
33Horam, Sarkin Gezer kuwa, ya kawo wa Lakish gudunmawa, Joshuwa kuwa ya buge shi tare da mutanensa, har ba wanda ya ragu.
34Joshuwa kuma ya zarce tare da dukan Isra'ilawa daga Lakish zuwa Eglon, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata. 35A ran nan suka cinye ta, suka buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi. Ya hallakar da su a wannan rana kamar yadda ya yi wa Lakish.
36Joshuwa kuma ya haura tare da dukan Isra'ilawa daga Eglon zuwa Hebron, suka auka mata. 37Suka cinye ta, suka buge ta, da sarkinta, da garuruwanta, da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.
38Sai Joshuwa ya juya tare da dukan Isra'ilawa zuwa Debir, ya auka mata. 39Ya cinye ta da yaƙi, da sarkinta, da garuruwanta. Ya buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Kamar yadda ya yi wa Hebron, da Libna da sarkinta, haka kuma ya yi wa Debir da sarkinta. 40Hakanan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta. 41Joshuwa kuma ya cinye su da yaƙi tun daga Kadesh-barneya har zuwa Gaza, da dukan ƙasar Goshen har zuwa Gibeyon. 42Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi yaƙi domin Isra'ilawa. 43Sa'an nan Joshuwa ya komo tare da dukan Isra'ilawa zuwa zango a Gilgal.
1Sa'ad da Yabin Sarkin Hazor ya ji labari, ya aika wa Yobab, Sarkin Madon, da Sarkin Shimron, da Sarkin Akshaf, 2da sarakunan da suke arewacin ƙasar tuddai, da cikin Araba a kudancin Kinneret, da cikin filayen kwari, da cikin Dor a yamma. 3Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa. 4Sai suka fita tare da dukan mayaƙansu, babbar runduna mai yawa kamar yashi a bakin teku, da dawakai, da karusai da yawa ƙwarai. 5Da sarakunan nan duka suka haɗa ƙarfinsu, sai suka je suka kafa sansaninsu a wuri ɗaya a bakin ruwayen Merom domin su yi yaƙi da Isra'ilawa.
6Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra'ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.” 7Sai Joshuwa, tare da dukan mayaƙansa, suka je suka mame su, suka auka musu a bakin ruwayen Merom. 8Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf. 9Joshuwa kuwa ya yi musu kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, ya daddatse agaran dawakansu, ya kuma ƙone karusansu.
10A wannan lokaci Joshuwa ya koma da baya ya ci Hazor, ya kashe sarkinta da takobi, gama a lokacin Hazor ita ce masarautar mulkokin nan. 11Suka kashe dukan waɗanda suke cikinta da takobi, suka hallakar da su ƙaƙaf, ba wanda ya ragu. Joshuwa kuwa ya ƙone Hazor. 12Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta. 13Amma mutanen Isra'ila ba su ƙone ko ɗaya daga cikin biranen da suke bisa tuddai ba, sai Hazor kaɗai Joshuwa ya ƙone. 14Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba. 15Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.
16Ta haka kuwa Joshuwa ya ci ƙasar nan duka, da ƙasar tuddai, da Negeb duka, da dukan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Araba, da ƙasar tuddai ta Isra'ila da filayen kwarinta, 17tun daga Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa wajen Seyir, har zuwa Ba'al-gad a kwarin Lebanon, a gindin Dutsen Harmon. Ya kama sarakunan wuraren nan, ya buge su ya kashe su. 18Joshuwa ya daɗe yana yaƙi da su. 19Ba wani birnin da ya yi amana da Isra'ilawa, sai dai Hiwiyawa da suke zaune a Gibeyon. Saura duka kuwa, an ci su da yaƙi. 20Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra'ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
21A wannan lokaci kuwa Joshuwa ya tafi ya hallaka Anakawa, wato gwarzayen nan da suke ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da dukan ƙasar tuddai ta Yahuza, da dukan ƙasar tuddai ta Isra'ilawa. Joshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu. 22Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra'ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu. 23Hakanan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.
1Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas, 2Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa, 3daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga, 4da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai. 5Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon. 6Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra'ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa'an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.
7Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba'al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra'ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu, 8da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 9Sunayen sarakunan su ne, Sarkin Yariko, da Sarkin Ai, da yake kusa da Betel, 10da Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, 11da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, 12da Sarkin Eglon, da Sarkin Gezer, 13da Sarkin Debir, da Sarkin Geder, 14da Sarkin Horma, da Sarkin Arad, 15da Sarkin Libna, da Sarkin Adullam, 16da Sarkin Makkeda, da Sarkin Betel, 17da Sarkin Taffuwa, da Sarkin Hefer, 18da Sarkin Afek, da Sarkin Lasharon, 19da Sarkin Madon, da Sarkin Hazor, 20da Sarkin Shimron-meron, da Sarkin Akshaf, 21da Sarkin Ta'anak, da Sarkin Magiddo, 22da Sarkin Kedesh, da Sarkin Yakneyam a Karmel, 23da Sarkin Dor a bakin teku, da Sarkin Goyim na Gilgal, 24da Sarkin Tirza. Sarakuna talatin da ɗaya ke nan.
1Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa. 2Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa, 3daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai sarakuna biyar na Filistiyawa da suke a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa, 4da dukan ƙasar Kan'aniyawa a wajen kudu, da Meyara ta Sidoniyawa, zuwa Afek, har zuwa iyakar Amoriyawa, 5da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba'al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat, 6da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka. 7Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”
8Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan, 9daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon, 10da dukan biranen Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, har zuwa iyakar Amoriyawa, 11da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka, 12da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su. 13Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau.
14Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.
15Musa ya riga ya ba Ra'ubainawa nasu gādo bisa ga iyalansu. 16Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba, 17da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba'al, da Ba'al-mayon, 18da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat, 19da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin, 20da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot. 21Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar. 22Jama'ar Isra'ila kuma suka kashe Bal'amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi. 23Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama'ar Ra'ubainu. Wannan shi ne gādon Ra'ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu.
24Musa kuma ya ba Gadawa gādo bisa ga iyalansu. 25Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba, 26daga Heshbon zuwa Ramat-mizfe, da Betonim, daga Mahanayim zuwa karkarar Debir, 27da a kwarin Ber-aram, da Betnimra, da Sukkot, da Zafon, da kuma ragowar mulkin Sihon, Sarkin Heshbon. Kogin Urdun ne iyakar yankin ƙasarsu har zuwa wutsiyar Tekun Kinneret, a gabashin hayin Urdun. 28Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu.
29Musa kuma ya ba rabin jama'ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu. 30Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan, 31da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.
32Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun daura da Yariko. 33Amma Musa bai ba Lawiyawa gādon yankin ƙasa ba. Ya faɗa musu Ubangiji Allah na Isra'ila, shi ne rabon gādonsu.
1Waɗannan su ne karkasuwar gādon da Isra'ilawa suka karɓa a ƙasar Kan'ana, wanda Ele'azara, firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra'ila suka ba su. 2Kabilar nan tara da rabi sun karɓi nasu rabon gādo ta hanyar jefa kuri'a, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 3Gama Musa ya riga ya ba kabilar nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba. 4Jama'ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu. 5Jama'ar Isra'ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri'a.
6Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina. 7Ina da shekara arba'in sa'ad da Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barneya don in leƙi asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda yake a zuciyata. 8Amma 'yan'uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama'ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci. 9Musa kuwa ya rantse a wannan rana ya ce, “‘Hakika duk inda ƙafafunka suka taka a ƙasar nan zai zama gādonka, kai da 'ya'yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahnka sosai!” 10Ga shi kuwa, Ubangiji ya kiyaye ni har wa yau, kamar yadda ya faɗa, shekara arba'in da biyar ke nan, tun lokacin da Ubangiji ya faɗa wa Musa wannan magana, a lokacin da Isra'ilawa suke yawo a jeji. Ga shi yau ni mai shekara tamanin da biyar ne. 11Ga shi kuwa, har wa yau ina da ƙarfi kamar ran da Musa ya aike ni. Kamar yadda ƙarfina yake a dā, haka yake a yanzu domin yaƙi, da kuma kai da kawowa. 12Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranar nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
13Joshuwa ya sa wa Kalibu, ɗan Yefunne, albarka. Ya ba shi Hebron ta zama gādonsa. 14Domin haka Hebron ta zama gādon Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, har wa yau, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila sosai. 15A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.
1Rabon da aka ba jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu ya yi kudu, a iyakar Edom zuwa jejin Zin, can kudu nesa. 2Iyakarsu wajen kudu ta miƙa tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga wajen gaɓar da ta fuskanci kudu. 3Ta milla kudanci hawan Akrabbim, ta zarce zuwa Zin, ta haura kudu da Kadesh-barneya, ta wajen Hesruna har zuwa Addar. Sai ta karkata zuwa Karka. 4Ta zarce zuwa Azemon, ta bi ta rafin Masar zuwa inda ya gangara a teku. Wannan ita ce iyakar mutanen Yahuza wajen kudu. 5Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri zuwa bakin Urdun. Wajen arewa kuwa ta miƙa daga bakin teku a inda Kogin Urdun ya gangara a tekun. 6Iyakar ta bi zuwa Ber-hogla, ta zarce zuwa arewa da Bet-araba, ta haura zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu. 7Daga kwarin Akor ta wuce zuwa Debir ta yi wajen arewa, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal wadda take daura da hawan Adummim wanda yake kudancin gefen kwarin. Sai ta zarce zuwa ruwan En-shemesh, ta ƙare a En-rogel. 8Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa. 9Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim. 10Ta kuma kewaye kudancin Ba'ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna. 11Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa'an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba'ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa'an nan ta gangara a teku. 12Bakin Bahar Rum, ita ce iyaka a wajen yamma. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.
(L. Mah 1.11-15)
13Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyatarba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak. 14Daga can sai Kalibu ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak. 15Daga can kuma ya tafi ya fāɗa wa mazaunan Debir, dā sunan Debir Kiriyat-sefer ne. 16Kalibu ya ce, “Duk wanda ya bugi Kiriyat-sefer, har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.” 17Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa aure. 18Da ta zo wurinsa, ya zuga ta ta roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”
19Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.
20Wannan shi ne gādon jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu. 21Biranen jama'ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur, 22da Kina, da Dimona, da Adada, 23da Kedesh, da Hazor, da Yitnan, 24da Zif, da Telem, da Beyalot, 25da Hazor-hadatta, da Kiriyot-hesruna, wato Hazor, 26da Amam, da Shema, da Molada, 27da Hazar-gadda, da Heshmon, da Bet-felet, 28da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba, da Biziyotaya, 29da Ba'ala, da Abarim, da Ezem, 30da Eltola, da Kesil, da Horma, 31da Ziklag, da Madmanna, da Sansanna, 32da Labayot, da Shilhim, da Ayin, da Rimmon. Birane ashirin da tara ke nan da ƙauyukansu.
33Na filayen kwarin kuwa, su ne Eshtawol, da Zora, da Ashna, 34da Zanowa, da En-ganim, da Taffuwa, da Enayim, 35da Yarmut, da Adullam, da Soko, da Azeka, 36da Shayarim, da Aditayim, da Gedera, da Gederotayim. Birane goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.
37Da kuma Zenan, da Hadasha, da Migdal-gad, 38da Dileyan, da Mizfa, da Yokteyel, 39da Lakish, da Bozkat, da Eglon, 40da Kabbon, da Lahmam, da Kitlish, 41da Gederot, da Bet-dagon, da Na'ama, da Makkeda, birane goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
42Da kuma Libna, da Eter, da Ashan, 43da Yifta, da Ashna, da Nezib, 44da Kaila, da Akzib, da Maresha, birane tara ke nan da ƙauyukansu.
45Da kuma Ekron da garuruwanta da ƙauyukanta. 46Daga Ekron zuwa tekun, da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.
47Ashdod da garuruwanta da ƙauyukanta, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta zuwa rafin Masar da Bahar Rum da bakinta.
48Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne Shamir, da Yattir, da Soko, 49da Danna, da Kiriyat-sanna, wato Debir, 50da Anab, da Eshtemowa, da Anim, 51da Goshen, da Holon, da Gilo. Birane goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.
52Da kuma Arab, da Duma, da Eshan, 53da Yanim, da Bet-taffuwa, da Afeka, 54da Hunta, da Kiriyat-arba, wato Hebron, da Ziyor, birane tara ke nan da ƙauyukansu.
55Da kuma Mawon, da Karmel, da Zif, da Yutta, 56da Yezreyel, da Yokdeyam, da Zanowa, 57da Kayin, da Gebeya, da Timna, birane goma ke nan da ƙauyukansu.
58Halhul, da Bet-zur, da Gedor, 59da Ma'arat, da Bet-anot da Eltekon, birane shida ke nan da ƙauyukansu.
60Da kuma Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, da Rabba, birane biyu ke nan da ƙauyukansu.
61Biranen da suke a jeji kuwa su ne Bet-araba, da Middin, da Sekaka, 62da Nibshan, da Birnin Gishiri, da En-gedi, birane shida ke nan da ƙauyukansu.
63Amma jama'ar Yahuza ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zaune a Urushalima ba, don haka Yebusiyawa suka yi zamansu da jama'ar Yahuza cikin Urushalima har wa yau.
1Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel. 2Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa'an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa. 3Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa'an nan ya gangara a teku.
4A nan ne jama'ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo.
5Karkarar jama'ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu. 6Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta'anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa. 7Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa'an nan ta gangara a Urdun. 8Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa'an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu, 9tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama'ar Manassa. 10Amma ba su kori Kan'aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan'aniyawa suka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan'aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.
1Aka ba kabilar Manassa, ɗan farin Yusufu, nata rabon gādo. Makir ƙan farin Manassa, uban Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan domin shi jarumi ne. 2Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manassa nasu rabon gādo bisa ga iyalansu, wato Abiyezer, da Helek, da Asriyel, da Shekem, da Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne 'ya'yan Manassa, maza, bisa ga iyalansu.
3Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ƙan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 4Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji. 5Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun, 6domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad.
7Yankin ƙasar Manassa ya kai daga Ashiru zuwa Mikmetat wadda take gabas da Shekem. Iyakar kuma ta miƙa kudu zuwa mazaunan Entaffuwa. 8Ƙasar Taffuwa tana hannun mutanen Manassa, amma mutanen Ifraimu ne suke da garin Taffuwa wanda yake iyakar yankin Manassa. 9Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum. 10Ƙasar wajen kudu ta Ifraimu ce, ta wajen arewa kuwa ta Manassa. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Mutanen Ashiru suna wajen arewa, mutanen Issaka kuwa wajen gabas. 11A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat. 12Amma mutanen Manassa ba su iya su mallaki waɗannan birane ba, don haka Kan'aniyawa suka yi zamansu a wuraren. 13Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi sai suka tilasta su su yi musu aikin dole, amma ba su iya korarsu ba.
14Kabilan Yusufu suka ce wa Joshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo guda ɗaya? Ga shi kuwa, muna da jama'a mai yawa, gama Ubangiji ya sa mana albarka.”
15Joshuwa kuwa ya amsa musu, ya ce, “Idan ku babbar jama'a ce, har ƙasar tuddai ta Ifraimu ta kāsa muku, to, sai ku shiga jeji ku sheme wa kanku wuri a ƙasar Ferizziyawa da ta Refayawa.”
16Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”
17Joshuwa kuma ya ce wa jama'ar gidan Yusufu, wato kabilar Ifraimu da ta Manassa, “Ku babbar jama'a ce, ga shi kuma, kuna da ƙarfi, ba kashi ɗaya kaɗai za ku samu ba, 18amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan'aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”
1Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.
2Har yanzu akwai sauran kabila bakwai na Isra'ila waɗanda ba su sami gādonsu ba tukuna. 3Sai Joshuwa ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku? 4Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa'an nan su komo wurina. 5Sai su raba ƙasar kashi bakwai. Kabilar Yahuza za ta ci gaba da zama a yankin ƙasarta a wajen kudu, mutanen gidan Yusufu kuwa su zauna a yankin ƙasarsu a wajen arewa. 6Ku auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sa'an nan ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji Allahnmu. 7Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.”
8Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa'an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji a nan Shilo.” 9Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa'an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo. 10Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.
11Kuri'ar kabilar Biliyaminu bisa ga iyalanta ta fito. Yankin ƙasar da ya faɗo mata ke nan, ya zama a tsakanin yankin ƙasar kabilar Yahuza da na jama'ar Yusufu. 12A wajen arewa iyakar ta tashi daga Urdun, ta bi ta tsaunin da yake arewa da Yariko, ta kuma haura tudu wajen yamma, har zuwa hamadar Bet-awen inda ta ƙare. 13Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari. 14Daga nan iyakar ta nausa ta nufi yammacin kudancin dutse da yake kudu, daura da Bet-horon, sa'an nan ta tsaya a Kiriyatba'al, wato Kiriyat-yeyarim, birnin Yahuza. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma. 15A wajen kudu kuwa iyakar ta fara daga karkarar Kiriyat-yeyarim, daga can ta miƙa zuwa Efron a maɓuɓɓugar ruwan Neftowa. 16Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel. 17Sai ta nausa ta yi wajen arewa zuwa En-shemesh, sa'an nan ta tafi Gelilot wanda yake daura da hawan Adummim. Daga nan ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu. 18Sai ta wuce ta yi arewa daura da gefen Bet-araba, daga nan ta gangara zuwa Araba. 19Ta kuma zarce zuwa arewa daura da gefen Bet-hogla, ta tsaya a arewacin gaɓar Tekun Gishiri a ƙarshen Urdun wajen kudu. 20Kogin Urdun shi ne iyakar a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Biliyaminu suka gāda.
21Biranen iyalan kabilar Biliyaminu ke nan Yariko, da Bet-hogla, da Emekkeziz, 22da Bet-araba, da Zemarayim, da Betel, 23da Awwim, da Fara, da Ofra, 24da Kefar-ammoni, da Ofni, da Geba. Birane goma sha biyu ke nan tare da ƙauyukansu. 25Akwai kuma Gibeyon, da Rama, da Biyerot, 26da Mizfa, da Kefira, da Moza, 27da Rekem, da Irfeyel, da Tarala, 28da Zela, da Elef, da Yebus, wato Urushalima, da Gebeya, da Kiriyat. Birane goma sha huɗu ke nan tare da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon mutanen Biliyaminu bisa ga iyalansu.
1Kuri'a ta biyu ta faɗa kan kabilar Saminu bisa ga iyalanta. Nasu rabon gādon yana tsakiyar rabon gādon kabilar Yahuza. 2Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada, 3da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem, 4da Eltola, da Betul, da Horma, 5da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa, 6da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu. 7Akwai kuma Ayin, da Rimmon, da Eter, da Ashan. Garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu, 8da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba'alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu. 9Gādon kabilar Saminu yana cikin yankin ƙasar rabon kabilar Yahuza domin rabon kabilar Yahuza ya yi mata yawa, don haka kabilar Saminu ta sami gādo daga cikin tsakiyar gādon kabilar Yahuza.
10Kuri'a ta uku ta faɗa a kan kabilar Zabaluna bisa ga iyalanta. Yankin ƙasar gādonsu ya kai har Sarid. 11Iyakar ta hau wajen yamma zuwa Marala, ta kai Dabbeshet da rafin da yake gabas da Yakneyam. 12Daga Sarid, ta nufi wajen gabas zuwa iyakar Kislotabar, sa'an nan ta bi ta Daberat da Yafiya. 13Daga can ta miƙa wajen gabas zuwa Gat-hefer da Et-kazin, har zuwa Rimmon inda ta nausa zuwa Neya. 14Daga wajen arewa iyakar ta juya zuwa Hannaton, sa'an nan ta faɗa a kwarin Iftahel. 15Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna. 16Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin gādon mutanen Zabaluna bisa ga iyalansu.
17Kuri'a ta huɗu ta faɗo a kan kabilar Issaka bisa ga iyalanta. 18Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem, 19da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat, 20da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez, 21da Remet da En-ganim, da En-hadda, da Bet-fazzez. 22Iyakar kuma ta bi ta Tabor, da Shahazuma, da Bet-shemesh. Sa'an nan ta gangara a Kogin Urdun. Akwai garuruwa goma sha shida da ƙauyukansu. 23Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.
24Kuri'a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta. 25Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf, 26da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat. 27Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul, 28da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba. 29Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa'an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib, 30da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu. 31Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar da kabilar Ashiru ta gāda bisa ga iyalanta.
32Kuri'a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta. 33Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za'anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa'an nan ta tsaya a Kogin Urdun. 34Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa'an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun. 35Garuruwan da suke da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret, 36da Adama, da Rama, da Hazor, 37da Kedesh, da Edirai, da En-hazor, 38da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu. 39Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon gādon kabilar Naftali da iyalanta.
40Kuri'a ta bakwai ta faɗo a kan kabilar Dan bisa ga iyalanta. 41Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh, 42da Shalim, da Ayalon, da Itla, 43da Elon, da Timna, da Ekron, 44da Elteki, da Gebbeton, da Ba'alat, 45da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon, 46da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa. 47Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan. 48Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.
49Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu. 50Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki.
51Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama'ar Isra'ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri'a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.
(L. Ƙid 35.6-34; M. Sh 4.41-43; 19.1-13)
1Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, 2“Ka faɗa wa jama'ar Isra'ila, su keɓe biranen mafaka waɗanda na faɗa wa Musa ya faɗa muku. 3Domin idan wani mutum ya yi kisankai ba da niyya ba, ba kuma da saninsa ba, sai ya tsere zuwa can. Biranen za su zama muku mafaka daga mai bin hakkin jini. 4Wanda ya yi kisankan sai ya tsere zuwa ɗaya daga cikin biranen, ya tsaya a bakin ƙofar birnin, ya bayyana wa dattawan garin abin da ya same shi. In sun ji, sai su shigar da shi a birnin, su ba shi wurin zama, ya zauna tare da su. 5Idan mai bin hakkin jinin ya bi shi, ba za su ba shi wanda ya yi kisankan ba, domin bai kashe maƙwabcinsa da gangan ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu dā ma. 6Zai yi zamansa a birnin har lokacin da aka gabatar da shi gaban dattawa don shari'a, sai kuma bayan rasuwar babban firist na lokacin, sa'an nan wanda ya yi kisankan zai iya komawa garinsu da gidansa daga inda ya tsere.”
7Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza. 8A hayin Urdun, gabas da Yariko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ra'ubainu, da Ramot cikin Gileyad ta kabilar Gad, da Golan cikin Bashan ta kabilar Manassa. 9Waɗannan su ne biranen mafaka da aka keɓe domin dukan Isra'ilawa, da baƙin da suke baƙuntaka cikinsu. Don duk wanda ya yi kisankai ba da niyya ba zai iya tserewa zuwa can don kada ya mutu ta hannun mai bin hakkin jini. Zai zauna a can har lokacin da za a gabatar da shi a gaban taron jama'a.
(1 Tar 6.54-81)
1Shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa suka zo wurin Ele'azara, firist, da wurin Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan jama'ar Isra'ila. 2Suka yi magana da su a Shilo a ƙasar Kan'ana, suka ce musu, “Ubangiji ya umarta ta bakin Musa a ba mu biranen zama da wuraren kiwo domin dabbobinmu.” 3Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.
4Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.
5Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa.
6Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.
7Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna.
8Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.
9Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata. 10Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko. 11Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak. 12Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.
13Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata, 14da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata, 15da Holon tare da wuraren kiwo nata, da Debir tare da wuraren kiwo nata, 16da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu. 17Daga cikin kabilar Biliyaminu aka ba su birane huɗu, wato Gibeyon tare da wuraren kiwo nata, da Geba tare da wuraren kiwo nata, 18da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata. 19Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu. 20-22Aka ba sauran Kohatiyawa na iyalan Lawiyawa birane huɗu daga kabilar Ifraimu. Aka ba su Shekem tare da wuraren kiwo nata, a ƙasar tuddai ta Ifraimu, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Gezer tare da wuraren kiwo nata, da Yokmeyam tare da wuraren kiwo nata, da Bet-horon tare da wuraren kiwo nata.
27Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata.
41Jimillar biranen da wuraren kiwo nasu da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama'ar Isra'ila guda arba'in da takwas ne. 42Kowane birni yana da wuraren kiwo nasa kewaye da shi.
43Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra'ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki. 44Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko'ina kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin abokan gābansu da ya iya ta da kai da su, gama Ubangiji ya ba da abokan gābansu duka a hannunsu. 45Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra'ila.
1Sa'an nan Joshuwa ya kira mutanen kabilar Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa. 2Ya ce musu, “Kun aikata dukan abin da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku, kun kuma yi biyayya da dukan abin da na umarce ku. 3Ba ku yar da 'yan'uwanku dukan waɗannan yawan kwanaki, har wa yau ba. Amma kuka kiyaye umarnin Ubangiji Allahnku sosai. 4Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba 'yan'uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun. 5Sai dai ku kiyaye umarnai da dokokin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa, ku kiyaye dokokinsa, ku manne masa, ku bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku.” 6To, Joshuwa ya sa musu albarka, sa'an nan ya sallame su, suka koma gida.
7Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka, 8ya ce musu, “Ku koma gidajenku da wadata mai yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa, da zinariya, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da tufafi masu yawa. Ku raba da 'yan'uwanku ganimar da kuka kwaso daga abokan gabanku.” 9Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka koma gida. Suka yi bankwana da sauran 'yan'uwansu Isra'ilawa a Shilo ta ƙasar Kan'ana. Suka koma ƙasar Gileyad, ƙasar da suka gāda bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Musa.
10Sa'ad da suka kai Gelilot, kusa da Urdun, a gefen da yake wajen ƙasar Kan'ana, suka gina babban bagade a wurin. 11Sauran Isra'ilawa kuwa suka ji labari cewa, “Ga shi, Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa sun gina bagade a Gelilot a kan iyakar ƙasar Kan'ana, a wajen hayinsu na yammacin Urdun.” 12Da Isra'ilawa suka ji haka sai dukansu suka tattaru a Shilo don su kai musu yaƙi.
13Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad. 14Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra'ila. 15Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu, 16“In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, “‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?” Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade. 17Zunubin da aka yi a Feyor, ashe, bai ishe mu ba, har annoba ta wahalar da taron jama'ar Ubangiji? Ga shi, har yanzu ma ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba. 18Za ku kuma daina bin Ubangiji ne yau? Idan kuka tayar masa yau, gobe zai yi fushi da dukan jama'ar Isra'ila. 19Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji inda alfarwa ta sujada take, ku sami abin mallaka a tsakaninmu, amma kada ku tayar wa Ubangiji, ku kuma tayar mana ta wurin gina wa kanku wani bagade dabam da bagaden Allahnmu. 20Lokacin da Akan, ɗan Zera, ya yi rashin aminci cikin abubuwan da aka haramta, ai, dukan Isra'ilawa aka hukunta. Ba shi kaɗai ya hallaka don zunubinsa ba.”
21Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka amsa wa shugabannin iyalan Isra'ilawa suka ce, 22“Allah Maɗaukaki, Allah Ubangiji ya sani, bari Isra'ilawa kuma da kansu su sani. Idan tayarwa ce, ko kuwa mun yi wa Ubangiji rashin aminci ne, to, kada ku bar mu da rai yau. 23Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana. 24Saboda gudun gaba ne muka yi haka, domin kada wata rana 'ya'yanku su ce wa 'ya'yanmu, “‘Ba ruwanku da Ubangiji, Allah na Isra'ila. 25Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra'ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.” To, da haka 'ya'yanku su hana 'ya'yanmu yi wa Ubangiji sujada. 26Don haka muka ce, “‘Bari mu gina bagade, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, 27amma domin ya zama shaida tsakaninmu da ku, da tsakanin zuriyarmu da taku, don mu ci gaba da bautar Ubangiji da hadayunmu na ƙonawa, da na sadaka, da na salama.” 'Ya'yanku kuma ba za su ce wa 'ya'yanmu, “‘Ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.” 28Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, “‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.” 29Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”
30Sa'ad da Finehas, firist, da shugabannin jama'a, wato shugabannin iyalan Isra'ila, suka ji maganar da Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai. 31Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.”
32Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, da shugabannin suka komo daga wurin Ra'ubainawa da Gadawa a ƙasar Gileyad, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mutanen Isra'ila, suka ba su rahoton abin da suka ji. 33Mutanen Isra'ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra'ubainawa da Gadawa suke zaune ba. 34Ra'ubainawa da Gadawa suka sa wa bagaden suna Shaida, domin in ji su, “Shi shaida ne a tsakaninmu, cewa Ubangiji shi ne Allah.”
1An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra'ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa. 2Sai Joshuwa ya kira Isra'ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa, 3kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al'ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku. 4Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al'umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma. 5Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Ka ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku. 6Domin haka sai ku yi ƙarfin hali ƙwarai, ku riƙe, ku aikata dukan abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, kada ku kauce dama ko hagu, 7domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da suke zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu. 8Amma ku manne wa Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi har wa yau. 9Gama Ubangiji ya kori manyan al'ummai ƙarfafa daga gabanku, har wa yau ba mutumin da ya isa ya yi hamayya da ku. 10Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku. 11Ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku. 12Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al'umman nan da suke tare da ku, har kuka yi aurayya da juna, 13to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasar nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
14“A yanzu ina gaba da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi, ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba. 15Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, hakanan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasar nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku. 16Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”
1Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra'ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra'ila. Suka hallara a gaban Allah. 2Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, “‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka. 3Sai na ɗauki kakanku Ibrahim daga wancan hayin Kogi, na kawo shi ƙasar Kan'ana, na sa zuriyarsa ta yawaita. Na ba shi Ishaku. 4Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar. 5Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku. 6Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku. 7A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa. 8Sa'an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu. 9Haka kuma Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya tashi ya yi yaƙi da Isra'ila, har ya gayyaci Bal'amu, ɗan Beyor, ya zo ya la'anta ku. 10Amma ban saurari Bal'amu ba, saboda haka ya sa muku albarka, ta haka na cece ku daga hannunsa. 11Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku. 12Na kuma aiki zirnako a gabanku, waɗanda suka kori sarakunan nan biyu na Amoriyawa daga gabanku. Ba takobinku, ko bakanku ya kore su ba. 13Na ba ku ƙasar da ba ku yi wahala a kanta ba, da biranen da ba ku gina ba, ga shi, kuna zaune a ciki, kuna kuma cin 'ya'yan inabi, da na zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba.”
14“To fa, ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da sahihanci da aminci, ku yi watsi da gumakan da kakanninku suka bauta wa a hayin Kogin Yufiretis, da cikin Masar. 15Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”
16Jama'a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka. 17Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al'umman da muka ratsa. 18Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar, domin haka za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.”
19Amma Joshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, gama shi Allah mai tsarki ne, mai kishi kuma, ba kuwa zai gafarta laifofinku da zunubanku ba. 20Idan kun rabu da Ubangiji, kun bauta wa gumaka, sai ya juyo ya wulakanta ku, ya hallaka ku, ko da yake ya riga ya nuna muku alheri.”
21Jama'a kuwa suka ce wa Joshuwa, “A'a, mu dai za mu bauta wa Ubangiji ne.”
22Joshuwa kuma ya ce wa mutanen, “Ku ne shaidun kanku da kanku, kun zaɓi Ubangiji don ku bauta masa.” Sai suka ce, “I, mu ne shaidu.”
23Joshuwa ya ce, “To, ku kawar da gumakan da suke cikinku, ku sa zuciyarku ga Ubangiji, Allah na Isra'ila.”
24Jama'a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.” 25A wannan rana, Joshuwa ya yi alkawari da jama'a a Shekem, ya kafa musu dokoki da ka'idodi. 26Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari'ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji. 27Sai ya ce wa jama'a, “Wannan dutse shi ne shaida a kanmu, gama ya ji dukan abin da Ubangiji ya faɗa mana, domin haka zai zama shaida a kanku, don kada ku yi wa Allahnku ƙarya.” 28Joshuwa kuwa ya sallami jama'ar, kowane mutum ya koma wurin gādonsa.
(L. Mah 2.6-10)
29Bayan waɗannan al'amura, sai Joshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya rasu yana da shekara ɗari da goma da haihuwa. 30Suka binne shi a ƙasar gādonsa a Timnat-sera wadda take cikin karkarar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash.
31Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji a dukan zamanin Joshuwa, da dukan zamanin dattawan da suka wanzu bayansa, waɗanda suka san dukan ayyukan da Ubangiji ya aikata domin Isra'ilawa.
32Kasusuwan Yusufu, waɗanda jama'ar Isra'ila suka kawo daga Masar, an binne su a Shekem a yankin ƙasar da Yakubu ya saya a bakin azurfa ɗari daga wurin 'ya'yan Hamor mahaifin Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusufu.
33Ele'azara, ɗan Haruna kuma ya rasu, aka binne shi a Gebeya a garin ɗansa, Finehas, wanda aka ba shi a ƙasar tuddai ta Ifraimu.