Leviticus
(L. Fir 6.8-13)
1Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce 2ya ba Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki. 3Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji. 4Sai ya ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya ta ƙonawar, za a karɓa masa, a kuwa yi masa gafara. 5Sa'an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi. 6Sai mai hadayar ya feɗe dabbar, ya yanyanka ta gunduwa-gunduwa. 7Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza, firistoci, za su hura wuta a bisa bagaden, su jera itace daidai a wutar. 8Su ɗibiya gunduwoyin, da kan, da kitsen bisa itacen da yake cikin wutar da take a kan bagaden. 9Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya ƙone duka a kan bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
10Idan hadayarsa ta ƙonawa daga cikin garken tumaki ko kuwa na awaki ne, sai ya ba da namiji marar lahani. 11Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden. 12Mai hadayar kuma zai yanyanka shi gunduwa-gunduwa, da kansa, da kitsensa. Firist zai jera su a bisa itacen da yake cikin wutar da take a bagaden. 13Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya miƙa duka, ya ƙone a bisa bagaden, gama hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
14Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai. 15Firist ɗin zai kawo tsuntsun a bagaden, ya murɗe wuyan tsuntsun, sa'an nan ya ƙone kan a bisa bagaden. Za a tsiyaye jini a gefen bagaden. 16Amma zai ɗauki kururun da gashin ya zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka. 17Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, ya ƙone shi, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
(L. Fir 6.14-23)
1A sa'ad da mutum ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, sai ya kawo gari mai laushi, ya zuba masa mai da lubban. 2Zai kuma kawo hadayarsa a wurin 'ya'yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 3Ragowar garin hadayar kuwa, zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadaya ce ta ƙonawa mafi tsarki ga Ubangiji.
4Sa'ad da aka kawo hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, sai a yi shi da gari mai laushi marar yisti kwaɓaɓɓe da mai, a shafa masa mai, a toya, ko kuwa a soya ƙosai.
5Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai. 6Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan.
7Idan kuma hadayar ta gari ce wadda aka dafa cikin tukunya, ita kuma, sai a yi ta da gari mai laushi da mai. 8Za a kawo hadaya ta gari da aka yi da abubuwan nan ga Ubangiji. Sa'ad da aka kai wa firist, sai ya kawo ta a bagaden. 9Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 10Ragowar hadayar garin zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza, gama hadayar ƙonawa ce mafi tsarki ga Ubangiji.
11A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba. 12Amma a iya kawo su kamar hadayar nunan fari ga Ubangiji, sai dai ba za a ƙona su a kan bagade ba, kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi. 13Sai a sa gishiri a kowace hadaya ta gari, kada a rasa sa gishirin alkawarin Allah a hadaya ta gari. A sa gishiri a dukan hadayu. 14Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza. 15Za a zuba masa mai, a barbaɗa masa lubban, gama hadaya ce ta gari. 16Firist kuwa zai ƙone wani kashi daga cikin ɓarzajjen hatsin a gauraye da man, da dukan lubban don tunawa, gama hadaya ce ta ƙonawa ga Ubangiji.
(L. Fir 7.11-21)
1Idan mutum zai kawo hadayarsa ta salama daga garken shanu, sai ya kawo mace ko namiji marar lahani ga Ubangiji. 2Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi. 3Daga hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsen da yake rufe da kayan ciki, da wanda yake bisana, 4da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare ƙodojin. 5'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
6Idan kuwa hadayarsa ta salama ga Ubangiji daga garken tumaki, ko na awaki ce, sai ya ba da dabbar, mace ko namiji, marar lahani. 7Idan ɗan rago ne ya bayar don hadaya, sai ya miƙa shi a gaban Ubangiji. 8Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi. 9Daga cikin hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsensa da wutsiyarsa duka mai kitse. Zai yanke ta gab da ƙashin gadon baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki kuwa, da wanda yake bisansa, 10da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare da ƙodojin. 11Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.
12Idan ya kawo akuya don hadayarsa, sai ya miƙa ta a gaban Ubangiji. 13Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi. 14Sa'an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa, 15da ƙodoji biyu, da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama don a miƙa su hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. 16Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne. 17Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.
(L. Fir 6.25-30)
1Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 2ya faɗa wa mutanen Isra'ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka'idodin nan.
3Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama'a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata. 4Zai kawo ɗan bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, ya ɗibiya hannunsa a kan kan bijimin, ya yanka shi a gaban Ubangiji. 5Shi kuma keɓaɓɓen firist ɗin ya ɗibi jinin bijimin ya kai shi a alfarwa ta sujada. 6Ya tsoma yatsansa cikin jinin, ya yayyafa jinin sau bakwai a gaban Ubangiji a wajen labulen Wuri Mai Tsarki. 7Zai kuma ɗiba daga cikin jinin, ya sa a bisa zankayen bagaden ƙona turaren da suke cikin alfarwar a gaban Ubangiji. Sauran jinin bijimin kuwa zai zuba shi a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada. 8Zai ɗebe dukan kitsen ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi, da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa, 9da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama. 10Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin ya ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya. 11Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da tarosonsa, 12da sauran bijimin duka zai kai su waje bayan zango a wuri mai tsabta inda ake zubar da toka, nan zai ƙone su da wuta a inda ake zubar da tokar.
13Idan taron jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi. 14Amma sa'ad da zunubin da suka aikata ya sanu, taron jama'a za su ba da ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi. Za a kawo shi a gaban alfarwa ta sujada. 15Sai dattawan jama'a su ɗibiya hannunsu a kan kan bijimin a gaban Ubangiji, sa'an nan a yanka bijimin a gaban Ubangiji. 16Sai keɓaɓɓen firist ya ɗibi jinin bijimin, ya kai cikin alfarwa ta sujada. 17Sa'an nan ya tsoma yatsansa a cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen. 18Sai ya ɗiba daga cikin jinin ya shafa wa zankayen bagaden da suke cikin alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, sauran jinin kuwa sai ya zuba a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada. 19Zai kwashe kitsensa duka, ya ƙone shi bisa bagaden. 20Sai ya yi da ɗan bijimin kamar yadda ya yi da ɗan bijimi na hadaya don zunubin firist. Ta haka firist zai yi kafara domin jama'a, za a kuwa gafarta musu. 21Zai kai bijimin a bayan zango, ya ƙone shi kamar yadda ya yi da na farin, gama hadaya ce don zunubin taron jama'ar.
22Idan shugaba ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. 23Idan aka sanar da shi zunubin da ya yi, sai ya kawo bunsuru marar lahani don yin hadaya. 24Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi. 25Sai firist ya ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden. 26Firist ɗin zai ƙona kitsen duka a bisa bagaden kamar yadda akan yi da kitsen hadaya ta salama, ta haka firist zai yi kafara domin zunubin shugaban, za a kuwa gafarta masa.
27In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. 28Sa'ad da aka sanar da shi zunubin da ya aikata, sai ya kawo akuya marar lahani don yin hadaya saboda zunubinsa. 29Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa. 30Firist zai ɗibi jinin da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona kadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden. 31Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
32Idan kuwa daga cikin 'yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo 'yar tunkiya marar lahani. 33Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa. 34Sai firist ya ɗibi jinin abin yin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden. 35Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi masa kafara saboda zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta masa.
(L. Fir 7.1-7)
1Laifi ne idan mutum ya aikata kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. Idan mutum ya ji ana shelar neman mai laifi, amma ya ƙi fitowa ya ba da shaida, ko da yake ya gani, ko kuma ya san abin da ya faru, ya yi laifi, alhaki yana kansa.
2Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abu da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba.
3Ko kuma idan ya taɓa kowace irin ƙazantar mutum wadda akan ƙazantu da ita, ba da saninsa ba, amma in daga baya ya sani, to, laifi ya kama shi.
4Ko kuma idan mutum ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa, cewa, zai yi mugunta, ko nagarta, ko kowace irin rantsuwa ta garaje da mutane sukan yi, to, laifi ya kama shi bayan da ya gane da rantsuwarsa.
5In mutum ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan laifofi, sai ya hurta laifin da ya yi. 6Ya kuma kawo hadaya ga Ubangiji don laifin da ya yi. Sai ya kawo 'yar tunkiya ko akuya domin hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara don laifin mutumin.
7Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa. 8Zai kawo su wurin firist. Da fari firist zai miƙa hadaya don laifi. Zai karye wuyanta, amma ba zai tsinke kan ba. 9Zai yayyafa jinin hadaya don laifi a gefen bagaden, sauran jinin kuwa zai tsiyaye a gindin bagade, gama hadaya ce don laifi. 10Sa'an nan zai miƙa ta biyun don hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka ƙayyade. Firist ɗin zai yi kafara saboda laifin da mutumin ya yi, za a kuwa gafarta masa.
11Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi. 12Zai kai wa firist garin, firist zai ɗibi garin cike da tafin hannunsa, wannan shi ne kashi na tunawa. Zai ƙone shi bisa bagaden kamar hadaya na ƙonawa ga Ubangiji, gama hadaya ce don laifi. 13Ta haka firist zai yi kafara don laifin da mutumin ya aikata daga cikin abubuwan nan, za a kuwa gafarta masa. Sauran garin zai zama na firist kamar yadda yakan zama nasa a hadaya ta gari.
14Sai Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan. 15Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi. 16Zai kuma biya diyya saboda abu mai tsarki da ya yi laifi a kansa. Zai kuma ƙara humushi a kai, sa'an nan ya ba firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa.
17Idan wani ya yi laifi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, laifi ya kama shi ko da bai sani ba. Alhakin laifin yana kansa. 18Sai ya kai wa firist rago marar lahani daga cikin garke. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa. 19Hadaya ce don laifi, gama ya yi wa Ubangiji laifi.
1Ubangiji kuma ya ba Musa ka'idodin nan. 2Idan wani mutum ya yi laifi na cin amana gāba da Ubangiji, wato, ya yaudari maƙwabcinsa a kan ajiya, ko jingina, ko ƙwace, ko ya zalunce shi, 3ko ya yi tsintuwa, amma ya yi mūsu har ya rantse da ƙarya, duk dai irin abubuwan da akan aikata na laifi, 4sa'ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta, 5ko kowane abu da ya rantse a kansa da ƙarya. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har ya ƙara da humushin tamanin abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa. 6Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi. 7Firist kuwa zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.
(L. Fir 1.1-17)
8Ubangiji kuma ya umarci Musa, 9ya ba Haruna da 'ya'yansa maza ka'idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe. 10Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa. 11Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa'an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta. 12Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta. 13Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.
(L. Fir 2.1-16)
14Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. 'Ya'yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden. 15Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa. 16Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada. 17Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi. 18Kowane ɗa namiji cikin 'ya'yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka.
19Sai Ubangiji ya ba Musa waɗannan ka'idodi, 20domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice. 21Za a shirya shi da mai a kwanon tuya. A kwaɓa shi sosai, a toya shi dunƙule dunƙule kamar hadaya ta gari, sa'an nan a kawo shi a miƙa shi don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 22Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada. 23Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.
(L. Fir 4.1-35)
24Sai Ubangiji ya umarci Musa 25ya ba Haruna da 'ya'yansa maza waɗannan ka'idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki. 26Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada. 27Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki. 28Sai a fasa tukunyar ƙasa wadda aka dafa naman a ciki, amma in a cikin tukunyar tagulla aka dafa, sai a kankare ta a ɗauraye da ruwa. 29Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki. 30Amma ba za a ci naman hadaya don zunubi ba wanda aka shigar da jininsa a alfarwa ta sujada domin yin kafara a Wuri Mai Tsarki. Sai a ƙone shi da wuta.
(L. Fir 5.1—6.7)
1Waɗannan su ne ka'idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka. 2Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa. 3Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, 4da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama wadda za a cire tare da ƙodojin. 5Firist zai ƙone su a bisa bagaden, gama hadaya ce da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, hadaya ce don laifi. 6Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.
7Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka'idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu. 8Firist kuma wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ta wani mutum, zai ɗauki fatar abin da aka yi hadayar da shi. 9Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya. 10Kowace hadaya ta gari kuma wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, za ta zama rabon 'ya'yan Haruna, maza duka, kowa da kowa.
(L. Fir 3.1-17)
11Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta salama wadda za a miƙa wa Ubangiji. 12Idan domin godiya mutum ya miƙa hadaya, sai ya miƙa ta tare da abinci marar yisti, wadda aka kwaɓa da mai, da wadda aka shafa wa mai, da kuma ƙosai. 13Tare da hadayarsa ta salama don godiya, sai ya kawo dunƙulen abincin da aka sa masa yisti. 14Daga cikin wannan zai miƙa waina ɗaya daga kowace hadaya don hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist wanda ya yayyafa jinin hadaya ta salama. 15Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe.
16Amma idan hadayarsa ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu. 17Amma idan ba a cinye naman hadayar ba har ya kai kwana uku, kada a ci, sai a ƙone shi da wuta. 18Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa'idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi. 19Kada a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki, sai a ƙone shi da wuta. Duk wanda yake da tsarki zai iya cin nama. 20Amma wanda ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji lokacin da ba shi da tsarki, za a raba shi da mutenensa. 21Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.
22Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 23ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya. 24Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci. 25Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa. 26Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka. 27Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.
28Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka'idodi 29don mutanen Isra'ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama. 30Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji. 31Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza. 32Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama. 33Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama. 34Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa. 35Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da 'ya'yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji. 36Ubangiji ya umarci Isra'ilawa su ba firistoci wannan a ranar da aka keɓe su. Wannan hakkinsu ne a dukan zamanansu.
37Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama. 38Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a Dutsen Sina'i, can cikin hamada, a ranar da ya faɗa wa Isra'ilawa su kawo hadayunsu gare shi.
(Fit 29.1-37)
1Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti. 3Ka kuma tattara jama'a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”
4Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama'ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada. 5Musa ya faɗa wa taron jama'ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”
6Sai Musa ya fito da Haruna da 'ya'yansa maza, ya yi musu wanka. 7Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta. 8Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen. 9Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
10Sai Musa ya ɗauki man keɓewa ya shafa wa alfarwa ta sujada da dukan abin da yake cikinta, da haka ya tsarkake su. 11Ya yayyafa wa bagaden mai sau bakwai, ya kuma shafa wa bagaden da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, don ya tsarkake su. 12Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya keɓe shi. 13Sai Musa kuma ya kawo 'ya'yan Haruna, maza, ya sa musu zilaiku, ya ɗaura musu ɗamaru, ya sa musu huluna kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
14Sa'an nan ya kawo bijimi na yin hadaya don zunubi, Haruna da 'ya'yansa maza, suka ɗibiya hannuwansu a kan kan bijimin. 15Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa. 16Sai ya ɗauki dukan kitsen da yake bisa kayan ciki da matsarmama, da ƙodoji biyu da kitsensu, ya ƙone su bisa bagaden. 17Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
18Sa'an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon. 19Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa. 20Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen. 21Sa'ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
22Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon. 23Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama. 24Sai aka kawo 'ya'yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa'an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden. 25Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama. 26Daga cikin kwandon abinci marar yisti da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama. 27Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na 'ya'yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji. 28Sa'an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 29Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
30Sa'an nan Musa ya ɗiba daga cikin man keɓewa da jinin da yake bisa bagaden, ya yayyafa wa Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu. Da haka ya tsarkake Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu.
31Sai Musa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar alfarwa ta sujada, ku ci shi a wurin, da abincin da yake a cikin kwandon hadayar keɓewa, kamar yadda Ubangiji ya umarta, cewa, Haruna da 'ya'yansa maza za su ci shi. 32Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su. 33Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai. 34Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku. 35A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.” 36Sai Haruna da 'ya'yansa maza suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
1A kan rana ta takwas, Musa ya kirawo Haruna, da 'ya'yansa maza, da dattawan Isra'ila. 2Sai ya ce wa Haruna, “Kawo ɗan maraƙi marar lahani na yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ka miƙa su ga Ubangiji. 3Ka faɗa wa Isra'ilawa su ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa, 4da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.”
5Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama'a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji. 6Musa kuma ya ce, “Ubangiji ya umarce ku ku yi dukan wanna, domin ɗaukakar Ubangiji za ta bayyana gare ku.” 7Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama'a. Ka kuma kawo hadayar jama'a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
8Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. 9'Ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa a cikin jinin, ya shafa a zankayen bagaden, ya kuma zuba jinin a gindin bagaden. 10Amma kitsen, da ƙadojin, da kitsen da yake rufe da hanta na hadaya don zunubi, ya ƙone su a bisa bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 11Naman da fatar kuwa ya ƙone su a bayan zangon.
12Haruna ya yanka hadaya ta ƙonawa, 'ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa a bagaden da kewayensa. 13Suka kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa gunduwa tare da kan, sai ya ƙone su bisa bagaden. 14Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa'an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden.
15Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin. 16Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa, ya yi kamar yadda aka faɗa. 17Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗibi garin cike da tafin hannunsa, ya ƙone shi a bisa bagaden tare da hadaya ta ƙonawa ta safiya. 18Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama'ar. 'Ya'yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa. 19Suka cire kitsen bijimin, da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji, da matsarmama. 20Sai Haruna ya aza kitsen a bisa ƙirjin dabbobin ya ƙone kitsen a bisa bagaden. 21Amma ya yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin da cinyoyi na dama ga Ubangiji, kamar yadda Musa ya umarta.
22Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama'a, ya sa musu albarka sa'an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama. 23Musa da Haruna suka shiga alfarwa ta sujada. Da suka fita, sai suka sa wa jama'a albarka. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana ga jama'a duka. 24Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.
1'Ya'yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa ko wannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. 2Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji. 3Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma'anar abin da Ubangiji yake cewa, “‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama'ata.” Haruna kuwa ya yi tsit.
4Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan 'ya'ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin 'yan'uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.” 5Sai suka zo, suka kama rigunan matattun suka ɗauke su zuwa bayan zango kamar yadda Musa ya faɗa.
6Musa kuma ya ce wa Haruna, da 'ya'yansa maza, wato, Ele'azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama'a duka, amma 'yan'uwanku, wato, dukan Isra'ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone. 7Kada kuwa ku fita daga cikin alfarwa ta sujada don kada ku mutu, gama an shafa muku man keɓewa na Ubangiji.” Sai suka yi yadda Musa ya faɗa.
8Ubangiji kuma ya yi magana da Haruna ya ce, 9“Kada kai da 'ya'yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa'ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku. 10Sai ku bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki, da tsakanin abin da yake halal da abin da yake haram. 11Ku kuma koya wa mutanen Isra'ila dukan dokokin da Ubangiji ya ba su ta hannun Musa.”
12Musa kuwa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda suka ragu, wato, Ele'azara da Itamar, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji, ku ci ba tare da yisti ba a gefen bagaden, gama tsattsarka ne. 13Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni. 14Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da 'ya'yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra'ilwa. 15Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na 'ya'yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
16Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele'azara da Itamar, 'ya'yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce, 17“Don me ba ku ci hadaya don zunubi a wuri mai tsarki ba, da yake tsattsarkan abu ne wanda aka ba ku domin ku kawar da laifin taron jama'a, domin kuma ku yi kafara dominsu a gaban Ubangiji? 18Ga shi, ba a shigar da jinin can cikin Wuri Mai Tsarki ba. Ga shi kuwa, ya kamata ku ci kamar yadda na umarta amma ba ku yi ba.”
19Sai Haruna ya ce wa Musa, “Ga shi, yau suka miƙa hadayarsu don zunubi, da ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?” 20Da Musa ya ji wannan, sai ya yi na'am da shi.
(M. Sh 14.3-21)
1Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi 2domin Isra'ilawa. Za ku ci kowace irin dabbar da take a duniya, 3wadda take da rababben kofato, wadda kuma take yin tuƙa. 4Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku. 5Rema tana tuƙa, amma ba ta da rababben kofato, haram ce a gare ku. 6Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku. 7Alade yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, haram ne a gare ku. 8Ba za ku ci namansu ba, ba kuwa za ku taɓa mushensu ba, gama haram ne a gare ku.
9Kwa iya cin waɗannan abubuwa da suke cikin ruwa, kowane abu da yake da ƙege da kamɓori da yake cikin tekuna ko koguna. 10Amma kowace irin halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, abar ƙyama ce a gare ku. 11Namansu kuma zai zama abin ƙyama a gare ku, ba za ku ci ba. Mushensu kuma abin ƙyama ne. 12Kowane irin abu da yake cikin ruwa da ba shi da ƙege da kamɓori, abin ƙyama ne a gare ku.
13Za ku ji ƙyamar waɗannan irin tsuntsaye, ba za ku ci su ba, gama abin ƙyama ne su, wato, gaggafa, da mikiya, da ungulun kwakwa, 14da shirwa, da buga zabi, da irinsu, 15da kowane irin hankaka, 16da jimina, da mujiya, da shaho, da irinsu, 17da ƙururu, da babba da jaka, da zarɓe, 18da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu, 19da shamuwa, da jinjimi da irinsa, da burtu, da jemage.
20Dukan ƙwarin da yake da fikafikai ƙazantattu ne, 21sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. 22Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu. 23Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
24Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har faɗuwar rana. 25Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice. 26Kowace dabba wadda ba ta da rababben kofato, ba ta kuma tuƙa, haram ce a gare ku. Duk wanda ya taɓa su zai ƙazantu. 27Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice. 28Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.
29Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, 30da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. 31Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice. 32Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka. 33Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon. 34Kowane irin abinci da yake cikinsa kuma da yake da ruwa a cikinsa, zai haramtu. Kowane irin abin sha da yake cikinsa kuma, zai haramtu. 35Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai, zai haramtu, ko randa ce, ko murhu, sai a farfasa, sun ƙazantu, haram ne a gare ku. 36Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu. 37Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba. 38Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku.
39Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice. 40Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.
41Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba, 42duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa. 43Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa. 44Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne. 45Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.
46Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu. 47Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.
1Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan domin jama'ar Isra'ila. 2Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta. 3A kan rana ta takwas za a yi wa jaririn kaciya. 4Sa'an nan kuma sai ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana talatin da uku. A lokacin ba za ta taɓa kowane tsattsarkan abu ba, ba za ta shiga wurin yin sujada ba, har kwanakin tsarkakewarta su cike. 5Amma idan 'ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida.
6Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko 'ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi. 7Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ta haifi ɗa ko 'ya.
8Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.
1Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi. 2Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci. 3Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne. 4Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai. 5A rana ta bakwai firist zai ƙara dudduba shi, in ya ga cutar ba ta yaɗu a fatar jikin mutumin ba, sai ya sāke kulle shi waɗansu kwana bakwai kuma. 6A rana ta bakwai sai firist ya sāke dubansa, idan ciwon ya dushe, cutar kuma ba ta yaɗuwa a fatar jikin mutumin, firist zai hurta, cewa, mutumin tsattsarka ne, ɓamɓaroki ne kawai, sai ya wanke tufafinsa. 7Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar jikin mutumin bayan da ya nuna kansa ga firist don tsarkakewa, sai ya sāke zuwa gaban firist. 8Firist zai duba shi, idan ɓamɓaroki ya yaɗu a fatar, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba ɓamɓaroki ba ne, kuturta ce.
9Sa'ad da cutar kuturta ta kama mutum, sai a kai shi wurin firist. 10Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin, 11to, kuturta ce da ta daɗe a fatar jikinsa. Firist kuwa zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba za a kulle shi ba, gama ya tabbata marar tsarki ne. 12Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist, 13firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka. 14Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki. 15Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce. 16Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist. 17Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka.
18Amma idan akwai wanda yake da ƙurjin da ya warke, 19idan kuma akwai tabo jaja-jaja, da fari-farin tabo, sai a nuna wa firist. 20Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin. 21Amma idan firist ya dudduba shi ya ga gashin wurin bai yi fari ba, zurfin ƙurjin kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, sai firist ɗin ya kulle shi kwana bakwai. 22Amma idan ƙurjin ya bazu a fatar jikin, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce. 23Amma idan tabon ya tsaya wuri ɗaya, bai bazu ba, tabon miki ke nan, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.
24Ko kuma idan mutum ya ƙuna a fatar jiki, naman wurin ƙunar kuwa ya yi tabo jaja-jaja, da fari-fari, ko fari, 25sai firist ya dudduba shi, in gashin wurin tabo ya zarce fatar, to, kuturta ce ta faso a cikin ƙunar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce. 26Amma idan firist ya dudduba tabon, ya ga gashin tabon bai zama fari ba, zurfin tabon kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, firist zai kulle shi kwana bakwai. 27A kan rana ta bakwai, zai sāke dubansa, idan tabon yana bazuwa cikin fatar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce. 28Amma idan tabon ya tsaya a wuri ɗaya, bai bazu a fatar jikin ba, ya kuma dushe, to, kumburi ne na ƙunar, firist zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, gama tabon ƙuna ne.
29Sa'ad da mace ko namiji na da cuta a kai, ko a gemu, 30sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne. 31Amma idan firist ya duba mikin, ya ga zurfinsa bai zarce fatar ba, ba kuma baƙin gashi a ciki, sai firist ya kulle mai miki har kwana bakwai. 32A rana ta bakwai kuma firist zai duba cutar, idan mikin bai bazu ba, babu kuma rawayan gashi a cikinsa, zurfin mikin kuwa bai zarce fatar ba, 33zai aske kansa, amma ba zai aske mikin ba, sai firist ya sāke kulle mai mikin har waɗansu kwana bakwai. 34A rana ta bakwai firist zai dudduba mikin, idan mikin bai bazu ba, zurfinsa kuma bai zarce fatar ba, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya tsarkaka ke nan. 35Amma idan mikin ya bazu bayan tsarkakewarsa, 36sai firist ya dudduba shi, idan mikin ya bazu a fatar, ba lalle ne ya nemi rawayan gashi ba, shi mutumin marar tsarki ne. 37Amma idan a ganinsa mikin bai yaɗu ba, baƙin gashi ya tsiro ya kuma yi tsawo a wurin, mikin ya warke ke nan, mutumin ya tsarkaka, firist kuwa zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.
38Idan a fatar jikin mace ko namiji akwai fararen tabbai, 39sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne.
40Idan gashin kan mutum ya zube, ya zama mai sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne. 41Idan gashin goshin mutum ya zube, ya yi sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne. 42Idan a sanƙon ko a gaban goshi akwai tabon cuta jaja-jaja da fari-fari, to, kuturta ce ta faso a sanƙonsa ko gaban goshinsa. 43Firist kuwa zai dudduba shi, idan an ga kumburin jaja-jaja da fari-fari ne a sanƙon kansa, ko a gabansa kamar alamar kuturta a fata jikinsa, 44to, kuturu ne shi, marar tsarki. Firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta tana kansa.
45Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa'an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.” 46Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.
47Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin, 48ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata, 49idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist. 50Firist zai dudduba cutar, ya ajiye abin da yake da cutar har kwana bakwai. 51A rana ta bakwai ɗin zai sāke dudduba cutar, idan cutar ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a fatar, komenene za a yi da fata, wannan cuta muguwar kuturta ce, abin zai zama marar tsarki. 52Zai ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko waɗari na ulu ko na lilin, ko abin da dai aka yi da fata wanda yake da cutar, gama muguwar kuturta ce.
53Amma idan firist ya dudduba ya ga cutar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a abin da aka yi da fata ba, 54sai firist ya umarta a wanke abin da yake da cutar, ya sāke ajiye shi har kwana bakwai kuma. 55Firist kuma zai sāke duban abin da yake da cutar bayan da aka wanke shi, idan ya ga launin cutar bai sāke ba, ko da cutar ba ta yaɗu ba, abin ya zama marar tsarki ne nan, sai a ƙone shi da wuta, ko tabon cutar yana cikin abin ne, ko a waje. 56Amma idan firist ɗin ya duba ya ga tabon ya dushe bayan da aka wanke shi, sai ya kece wurin daga fatar, ko tariyar zaren, ko waɗarin. 57Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar. 58Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abu da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa'ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.
59Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.
1Ubangiji ya ba Musa 2waɗannan ka'idodi da za a bi a ranar tsarkakewar mai kuturta. Sai a kawo shi ga firist. 3Firist ɗin zai fita zuwa bayan zango ya dudduba shi. Idan kuturun ya warke daga cutar kuturtar, 4firist ɗin zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya domin aikin tsarkakewa. 5Sai firist ya umarta a yanka tsuntsu ɗaya a kaskon da yake cike da ruwa mai gudu. 6Ya kuma ɗauki ɗayan tsuntsu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon. 7Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa'an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura. 8Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai. 9A kan rana ta bakwai zai aske dukan gashin kansa, da gemunsa, da gashin girarsa, da duk gashin jikinsa. Sai kuma ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka.
10A rana ta takwas zai kawo 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai. 11Firist ɗin da zai tsarkake mutumin zai kawo wanda za a tsarkake da waɗannan abubuwa a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 12Firist ɗin zai ɗauki ɗan rago ɗaya ya miƙa shi hadaya don diyyar laifi, da rabin moɗa na mai, ya miƙa su don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. 13Sa'an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki. 14Firist zai ɗibi jinin hadaya don laifi ya shafa a leɓatun kunnen dama, da bisa babban yatsan hannun dama, da na ƙafar dama na wanda za a tsarkake ɗin. 15Firist kuwa zai ɗibi man, ya zuba shi a tafin hannunsa na hagu. 16Ya kuma tsoma yatsan hannunsa na dama a cikin man da ka a tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa man da yatsansa sau bakwai a gaban Ubangiji. 17Sauran man da ya ragu a tafin hannunsa, sai ya shafa shi a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da bisa babban yatsan hannunsa na dama, da na ƙafar dama. Wato, za a shafa man a inda aka shafa jinin hadaya don laifin. 18Sauran man kuma da ya ragu cikin tafin hannunsa, firist ɗin zai shafa a kan wanda za a tsarkake. Firist zai yi kafara dominsa gaban Ubangiji.
19Sai firist ya miƙa hadaya don zunubi domin ya yi kafara, don rashin tsarkin mutumin. Daga baya ya yanka hadaya ta ƙonawa. 20Firist kuma zai miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a bisa bagaden. Da haka zai yi kafara dominsa, shi kuwa zai tsarkaka.
21Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai, 22da kuma kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. 23A rana ta takwas zai kawo su wurin firist don tsarkakewarsa a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji. 24Sai firist ya ɗauki ɗan rago da man zaitun, ya miƙa su hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. 25Sa'an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama. 26Firist ɗin kuma zai ɗibi man ya zuba cikin tafin hannunsa na hagu. 27Sai ya yayyafa man da yake cikin tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Ubangiji da yatsansa na hannun dama. 28Ya kuma shafa man da ya ragu cikin hannunsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da a babban yatsan hannun damansa, da kuma a babban yatsan ƙafar damansa, a inda aka shafa jinin hadaya don laifin. 29Sauran man da yake cikin tafin hannunsa zai zuba a bisa wanda ake tsarkakewar, ya yi kafara dominsa a gaban Ubangiji. 30Sai mutumin ya ba da kurciyoyi, ko 'yan tattabarai yadda ya iya, 31ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa tare da hadaya ta gari. Firist ɗin kuma zai yi kafara a gaban Ubangiji domin wanda ake tsarkakewar. 32Wannan ita ce doka a kan mai ciwon kuturta wanda ba shi da isasshen abin bayarwa don yin hadayun tsarkakewarsa.
33Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 34“Sa'ad da kuka shiga ƙasar Kan'ana wadda nake ba ku ku mallaka, zan sa kuturta ta yaɗu a gidajenku.” Sa'an nan Ubangiji ya ba su waɗannan ka'idodi. 35Mutumin da ya ga kuturta a gidansa, tilas ye je ya faɗa wa firist. 36Firist kuwa ya umarta a fitar da dukan abin da yake cikin gidan kafin ya tafi ya dudduba tabo, domin kada kome da yake cikin gidan ya ƙazantu. Bayan haka sai firist ya shiga, ya duba gidan. 37Zai dudduba tabon, idan akwai alamar tabon a bangayen gida kore-kore, ko jaja-jaja, idan an ga tabon ya yi zurfi cikin bangon, 38sai firist ɗin ya fita daga cikin gidan zuwa ƙofa, ya rufe gidan har kwana bakwai. 39A kan rana ta bakwai, sai firist ɗin ya komo, ya duba. Idan tabon ya yaɗu a jikin bangayen gidan, 40sai ya umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar, a zuba a wuri marar tsarki can bayan birnin, 41ya sa a kankare jikin gidan duka. Shafen da suka kankare kuwa, sai su zubar da shi a wuri marar tsarki can bayan birnin. 42Sa'an nan sai su kwaso waɗansu duwatsu, su sa su a wuraren da suka ciccire waɗancan. Sai a kawo laka a shafe gidan.
43Idan cutar ta sāke ɓulla a cikin gidan bayan da aka ciccire duwatsun, aka kuma kankare gidan, aka yi masa shafe, 44sai firist ya je ya duba, idan cutar ya yaɗu a gidan, to, muguwar kuturta ce, gidan marar tsarki ne. 45Sai a rushe gidan, a kwashe duwatsun gidan, da katakansa, da shafensa duka a zubar bayan birni a wuri marar tsarki. 46Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice. 47Wanda kuma ya kwana cikin gidan, sai ya wanke tufafinsa, haka kuma wanda ya ci abinci cikin gidan, zai wanke tufafinsa.
48Amma idan firist ɗin ya zo, ya dudduba, ya ga tabon bai yaɗu a gidan ba, bayan da an yi wa gidan shafe, sai firist ya hurta, cewa, gidan tsattsarka ne domin tabon ya warke. 49Don tsarkakewar gidan, sai maigida ya kawo 'yan tsuntsaye biyu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya. 50Sai a yanka tsuntsu ɗaya a kasko cike da ruwa mai gudu. 51Zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini, da ɗayan tsuntsu mai ran, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon, ya yayyafa wa gidan sau bakwai. 52Da haka zai tsarkake gidan da jini tsuntsun, da ruwa mai gudu, da tsuntsu mai ran, da itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini. 53Sa'an nan ya saki tsuntsu mai ran daga birni ya tafi saura. Ta haka zai yi kafara domin gidan, gidan kuwa zai tsarkaka.
54Waɗannan su ne dokoki a kan cuce-cucen da akan ɗauka, da 55kuturta a tufafi ko a jikin gida, 56da kumburi, da ɓamɓaroki, ko tabo, 57don a tabbatar lokacin da suke tsarkakakku da lokacin da ba su da tsarki.
1Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi 2domin jama'ar Isra'ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al'aurarsa, ƙazantacce ne. 3Ko al'aurar tana ɗiga ko ta daina shi dai ƙazantacce ne. 4Kowane gado da mai ɗigan ya kwanta a kai ya ƙazantu, da kowane abu da ya zauna a kai ya ƙazantu. 5Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 6Duk wanda kuma ya zauna a kan kowane abu da mai ɗigar ya zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 7Wanda kuma ya taɓa jikin mai ɗigar, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 8Idan mai ɗigar yo tofar da yau a kan wanda yake da tsabta, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 9Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu. 10Duk wanda ya taɓa kowane abu da yake ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har maraice, duk kuma wanda ya ɗauki wannan abu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 11Duk wanda kuma mai ɗigar ya taɓa da hannunsa da bai wanke ba, sai wanda aka taɓa ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 12Kaskon da mai ɗigar ya taɓa, sai a fasa shi, amma idan akushi ne sai a wanke shi da ruwa.
13Sa'ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka. 14A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist. 15Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.
16Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 17Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 18Idan mutum ya kwana da mace, sai su yi wanka da ruwa, sun ƙazantu har maraice.
19Sa'ad da mace take haila irin ta ka'ida, za ta ƙazantu har kwana bakwai, duk wanda ya taɓa ta kuwa zai ƙazantu har maraice. 20Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu. 21Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 22Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abu da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 23Ko gado ne, ko kuma kowane abu da ta zauna a kai, sa'ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice. 24Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu.
25Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka'ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta. 26Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abu da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta. 27Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice. 28Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka. 29A rana ta takwas sai ta kawo 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. 30Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta.
31Ta haka za ka tsarkake jama'ar Isra'ila daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da alfarwata wadda take tsakiyarsu.
32Waɗannan su ne ka'idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙazantacce ne. 33Haka kuma wadda take haila, da kowane namiji ko mace, da take ɗiga, da namijin da ya kwana da mace marar tsarki.
1Sai Ubangiji ya yi magana da Musa bayan rasuwar 'ya'yan Haruna, maza biyu, sa'ad da suka hura wuta marar tsarki a gaban Ubangiji, suka mutu. 2Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin. 3Amma sai Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki bayan da ya kawo ɗan bijimi domin yin hadaya don zunubi, da rago don yin hadaya ta ƙonawa.”
4Sa'an nan Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa'an nan ya sa su.
5Zai karɓi bunsuru biyu daga taron jama'ar Isra'ila domin yin hadaya don zunubi, da rago ɗaya don yin hadaya ta ƙonawa. 6Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa. 7Zai kuma kawo bunsuran nan biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 8Sa'an nan ya jefa kuri'a kan bunsuran nan biyu. Kuri'a ɗaya don Ubangiji, ɗaya kuma domin Azazel. 9A wanda kuri'ar Ubangiji ta faɗa a kansa, sai Haruna ya miƙa shi hadaya don zunubi ga Ubangiji. 10Amma a wanda kuri'ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel.
11Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa. 12Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagaden da yake a gaban Ubangiji, ya kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshi, ya shigar da shi bayan labulen. 13Zai zuba turaren a wuta a gaban Ubangiji, domin hayaƙi ya tunnuke ya rufe murfi wanda yake a kan akwatin alkawari, don kada ya mutu. 14Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.
15Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin. 16Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra'ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu. 17Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita. 18Sa'an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye. 19Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama'ar Isra'ila.
20A sa'ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai. 21Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi. 22Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.
23Sa'an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa'ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan. 24Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa'an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama'a, domin ya yi kafara don kansa da jama'a. 25Zai ƙone kitsen hadaya don zunubi a bisa bagaden. 26Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango. 27Bijimin da bunsurun da aka yi hadaya don zunubi da su, waɗanda aka yi kafara da jininsu a Wuri Mafi Tsarki, sai a kai su bayan zangon, a ƙone fatunsu, da namansu, da tarosonsu. 28Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon.
29Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu. 30Gama a wannan rana za a yi kafara dominsu, domin a tsarkake su daga dukan zunubansu, su zama tsarkakakku a gaban Ubangiji. 31Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada. 32Firist kuma da aka naɗa ya zama firist a madadin mahaifinsa, zai yi kafara yana saye da tufafin lilin masu tsarki. 33Zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden. Sa'an nan kuma ya yi kafara domin firistocin, da dukan taron jama'ar. 34Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama'ar Isra'ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara. Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
1Ubangiji ya umarce Musa, 2ya faɗa wa Haruna da 'ya'yansa maza, da dukan mutanen Isra'ila waɗannan ka'idodi. 3Idan Ba'isra'ile ya yanka sa, ko ɗan rago, ko akuya a cikin zango, ko a bayan zango, 4bai kuwa kawo shi a ƙofar alfarwa ta sujada don ya miƙa shi sadaka ga Ubangiji a gaban alfarwa ta sujada ba, alhakin jinin da ya zubar yana bisa kansa, za a fitar da wannan mutum daga cikin jama'arsa. 5Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji. 6Sai firist ya yayyafa jinin a kan bagaden Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. Zai ƙone kitsen don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. 7Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.
8Kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka, 9amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.
10Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a. 11Gama ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa. 12Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, kada wani daga cikinsu, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, ya ci jini.
13Idan kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya tafi farauta, ya kama nama, ko tsuntsu da ake ci, sai ya zub da jininsa, ya rufe da ƙasa. 14Gama ran dukan nama yana cikin jininsa, saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, faufau ba za su ci jinin kowace dabba ba, gama ran kowace dabba yana cikin jininta. Duk wanda kuwa ya ci shi, za a raba shi da jama'a.
15Duk wanda ya ci mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, ko shi Ba'isra'ile ne, ko baƙo ne, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, ya ƙazantu har maraice, sa'an nan zai tsarkaka. 16Amma idan bai wanke su ba, bai kuwa yi wanka ba, alhakinsa yana kansa.
1Ubangiji kuma ya ce wa Musa 2ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku. 3Kada ku yi kamar yadda suke yi a kasar Masar inda kuka fito. Kada ma ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan'ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu. 4Amma ku bi ka'idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 5Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka'idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”
6Ubangiji ya ba da waɗannan ka'idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci 'yar'uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.” 7Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa. 8Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce. 9Kada ya kwana da 'yar'uwansa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam. 10Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi. 11Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce. 12Kada ya kwana da bābarsa gama 'yar'uwar mahaifinsa ce. 13Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce. 14Kada ya kwana da matar ɗan'uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce. 15Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce. 16Kada ya kwana da matar ɗan'uwansa, gama ita matar ɗan'uwansa ce. 17In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa. 18Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.
19Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki. 20Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa. 21Kada ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne. 22Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan. 23Kada wani ko wata su kwana da dabba don kada su wofintar da kansu.
24Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al'umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu. 25Har ƙasar ma ta ƙazantu, don haka Ubangiji ya hukunta muguntarta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta. 26Amma su sai su kiyaye dokokin Ubangiji da ka'idodinsa. Kada su aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa na banƙyama, ko haifaffe na gida, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu. 27Gama mazaunan ƙasar da suka riga su, sun aikata dukan abubuwa masu banƙyaman nan, don haka ƙasar ta ƙazantu. 28Kada kuma ƙasar ta amayar da su idan sun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da al'ummar da ta riga su zama a cikinta. 29Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama'a.
30Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
1Ubangiji ya ce wa Musa 2ya faɗa wa dukan taron jama'ar Isra'ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne. 3Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.
4“Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
5“Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku. 6A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta, 7gama ta zama abar ƙyama, idan aka ci ta a rana ta uku, ba za ta zama abar karɓa ba. 8Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama'a.
9“Sa'ad da kuke girbin amfanin ƙasarku, kada ku girbe gefen gonakinku, kada kuma ku yi kala bayan da kuka gama girbi. 10Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara 'ya'yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku.
11“Kada ku yi sata, ko ku cuci wani, ko ku yi ƙarya. 12Kada ku yi alkawari da sunana idan dai ba ku da niyyar cika shi, wannan zai jawo wa sunana ƙasƙanci. Ni ne Ubangiji Allahnku.
13“Kada ku zalunci kowa ko ku yi masa ƙwace. Kada kuma ku bar lokacin biyan hakkin ma'aikaci ya kai har gobe. 14Kada ku zagi kurma, kada kuma ku sa wa makaho abin tuntuɓe, amma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Ni ne Ubangiji.
15“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci. 16Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa'ad da wani yake cikin shari'ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji.
17“Kada wani ya riƙe ɗan'uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi. 18Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko yo yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.
19“Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu.
20“Idan mutum ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda kuma wani yake tashinta, tun ba a fanshe ta ba, ko kuwa ba a 'yanta ta ba, sai a bincike, amma ba za a kashe su ba, domin ita ba 'yantacciya ba ce. 21Amma ya kawo rago na yin hadaya don laifinsa ga Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. 22Sai firist ya yi kafara da ragon hadaya don laifi saboda laifin mutumin a gaban Ubangiji. Za a kuwa gafarta masa zunubin da ya yi.
23“Sa'ad da kuka shiga ƙasar, kuka dasa itatuwa iri iri masu ba da 'ya'ya na ci, 'ya'yan itatuwan za su zama ƙazantattu a gare ku har shekara uku. A cikin shekarun nan uku ba za ku ci su ba. 24A shekara ta huɗu 'ya'yan itatuwan za su tsarkaka. Hadaya ce ta yabo ga Ubangiji. 25Amma a shekara ta biyar, sai ku ci 'ya'yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku.
26“Kada ku ci kowane abu da jininsa, kada kuma ku yi duba, ko sihiri. 27Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu, 28ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji.
29“Kada ku ƙasƙantar da 'ya'yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata. 30Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji.
31“Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
32“Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.
33“Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi. 34Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
35“Kada ku cuci wani wajen yin amfani da kowane irin ma'auni na ƙarya, wato, awon tsawo, ko na nauyi, ko na ruwa. 36Sai ma'auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon abin da yake ruwa ruwa, su zama na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. 37Sai ku kiyaye, ku aikata dokokina da umarnaina duka. Ni ne Ubangiji.”
1Ubangiji ya faɗa wa Musa, 2ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu. 3Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki. 4Idan kuwa mutanen ƙasar ba su kashe mutumin nan, wanda ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa ba, 5ni kaina zan yi gāba da mutumin nan da iyalinsa, da waɗanda suka yarda suka bi Molek tare da shi. Ba zan ƙara ce da su mutanena ba.
6“Duk wanda yake sha'ani da masu mabiya, ko da bokaye zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa. 7Sai ku kiyaye kanku da tsarki, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 8Ku kuma kiyaye dokokina, ku aikata su, gama ni ne Ubangiji wanda yakeɓe ku.
9“Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.
10“Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar. 11Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu. 12Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu. 13Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu. 14Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku. 15Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar. 16In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.
17“Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu. 18Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.
19“Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi. 20Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa. 21Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa.
22“Sai fa ku kiyaye dokokina duka, da ka'idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. 23Kada ku bi al'adun waɗannan al'ummai, waɗanda nake kora a gabanku, gama sun aikata waɗannan al'amura, don haka nake ƙyamarsu. 24Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai. 25Domin haka sai ku bambanta tsakanin halattattun dabbobi da haramtattun dabbobi, da tsakanin haramtattun tsuntsaye da halattattun tsuntsaye. Kada ku ƙazantar da kanku da haramtattun dabbobi, ko da tsuntsaye, ko da kowane abu mai rarrafe bisa ƙasa, waɗanda na ware su, su zama haramtattu a gare ku. 26Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa.
27“Namiji ko mace da ke da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”
1Ubangiji kuma ya umarce Musa, ya faɗa wa 'ya'yan Haruna, maza, firistoci cewa, “Kada ko wannensu ya ƙazantar da kansa ta wurin gawar mutanensa, 2sai dai gawar iyalinsa na kurkusa, wato, gawar mahaifiyarsa, da ta mahaifinsa, da ta ɗansa, da ta 'yarsa, da ta ɗan'uwansa, 3da ta 'yar'uwarsa, budurwa, da take kusa da shi, wadda ba ta yi aure ba tukuna. Saboda su ya iya ƙazantar da kansa. 4Kada ya ƙazantar da kansa saboda dangantakar aure cikin mutanensa.
5“Kada su aske kansu ƙwal, ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsaga jikinsu. 6Sai su kasance da tsarki, kada su ƙasƙantar da sunana domin su ne masu kawo hadaya ta ci, masu ƙone hadayu da wuta gare ni, don haka sai su kasance da tsarki. 7Kada firist ya auri karuwa, ko wadda mijinta ya sake ta, gama shi tsattsarka ne gare ni. 8Dole jama'a su gan su da tsarki, gama suna miƙa hadaya ta ci gare ni. Ni ne Ubangiji, ni mai tsarki ne, na kuwa tsarkake mutanena. 9'Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta.
10“Firist wanda yake babba cikin 'yan'uwansa da aka zuba masa man keɓewa, aka kuma keɓe shi ya riƙa sa tufafin firist, kada ya bar gashin kansa buzu-buzu, ko kuwa ya kyakketa tufafinsa. 11Kada ya kusaci gawa, ko gawar mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa don kada ya ƙazantu. 12An keɓe shi domina, kada ya ƙazantar da kansa, kada kuwa ya ɓata alfarwa ta sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. 13Sai ya auri budurwa. 14Kada ya auri mace wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, ko karuwa, amma ya auri budurwa daga cikin kabilarsa, 15domin kada ya ƙazantar da 'ya'yansa waɗanda ya kamata su zama tsarkakakku. Ni ne Ubangiji, na kuwa keɓe shi ya zama babban firist.”
16Sai Ubangiji ya umarce Musa 17ya faɗa wa Haruna cewa, “Kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani ya kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni har abada. 18Duk mutumin da yake da lahani na makanta, ko gurguntaka, ka rauni a fuska, ko gaɓar da ta fi wata, 19ko tauyayye a ƙafa ko a hannu, 20ko mai ƙusumbi, ko wada, ko mai lahani a ido, ko cuta mai sa ƙaiƙayi, ko kirci, ko dandaƙaƙƙe, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ba. 21Duk mutumin da yake cikin zuriyar Haruna firist, wanda yake da lahani, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni ba. 22Amma zai iya ci daga cikin tsattsarkan abincin da aka miƙa mini, da abinci mafi tsarki. 23Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.”
24Haka nan kuwa Musa ya faɗa wa Haruna, da 'ya'yan Haruna, maza, da dukan Isra'ilawa.
1Ubangiji kuma ya umarci Musa 2ya faɗa wa Haruna, da shi da 'ya'yansa cewa, “Ku lura da tsarkakakkun abubuwa waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, don kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Ni ne Ubangiji. 3Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji.
4“Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga, 5da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta, 6duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna. 7To, sa'ad da rana ta faɗi mutumin zai tsarkaka, bayan wannan ya iya cin tsarkakakkun abubuwan nan, gama ko dā ma abincinsa ne. 8Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.
9“Domin haka sai su kiyaye umarnaina don kada su yi zunubi su mutu ta wurin karya tsarkakakkun ka'idodina. Ni ne Ubangiji, ni na sa su tsarkaka.
10“Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake zama tare da su ne, ko kuwa an ɗauke shi yana yi musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba. 11Amma idan firist ya sayi bawa da kuɗinsa, bawan ya zama dukiyarsa, bawan zai iya ci, haifaffun gidansa kuma za su iya cin tsattsarkan abincin. 12Idan kuwa 'yar firist ta auri wani wanda ba firist ba, to, kada ta ci daga cikin tsarkakakkun hadayu. 13Amma idan 'yar firist ɗin gwauruwa ce, ko sakakkiya, ba ta kuma da ɗa, ta kuwa koma gidan mahaifinta, sai ta ci daga cikin abincin mahaifinta kamar cikin kwanakin ƙuruciyarta. Amma wani dabam ba zai ci ba.
14“Idan kuwa har wani mutum dabam ya ci daga cikin tsarkakakken abin ba da saninsa ba, to, sai ya maido abin ga firist, da ƙarin humushin tamanin abin. 15Firist ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun abubuwan nan da jama'ar Isra'ila suke miƙawa ba, 16da zai bar mutumin da bai cancanta ya ci ba, wannan zai jawo masa hukunci. Ni ne Ubangiji. Ni na tsarkake hadayun.”
17Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 18ya yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza, da dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Sa'ad da duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune a Isra'ila, ya kawo hadaya ta ƙonawa, ko ta wa'adi ce, ko ta yardar rai, dole ne dabbar ta zama marar lahani. 19Dabbar ta kasance namiji marar lahani idan ana so ta karɓu. 20Kada ku yi hadaya da abin da yake da lahani, gama Ubangiji ba zai karɓa ba. 21Idan kuwa wani ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji don cika wa'adi, ko don hadaya ta yardar rai, daga cikin garken shanu, ko na tumaki, da na awaki, sai ya zama cikakke, marar lahani, don ya karɓu. 22Dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko mai gundumi, ko mai ɗiga, ko mai susa, ko mai kirci, kada ku miƙa wa Ubangiji, kada kuma ku yi hadaya ta ƙonawa a bagaden Ubangiji da su. 23Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa'adi ba, ba za a karɓa ba. 24Kowace dabba kuma da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa, ba za ku miƙa ta hadaya ga Ubangiji ba, ba kuwa za ku yi hadaya da ita a ƙasarku ba.
25“Ba kuma za ku karɓi irin dabbobin nan daga hannun baƙo don ku miƙa su hadaya ga Ubangiji ba, marasa tsarki ne tun da yake suna da lahani, ba za a karɓa ba.”
26Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce, 27“Sa'ad da kuma aka haifi ɗan maraƙi, ko ɗan rago, ko ɗan akuya, zai yi kwana bakwai tare da uwarsa. A rana ta takwas zuwa gaba, sai a karɓe shi don yin hadaya ta ƙonewa ga Ubangiji. 28Ba za ku yanka uwar dabbar tare da ɗanta rana ɗaya ba, ko uwar saniya ce, ko ta tunkiya ce. 29Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓa. 30A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji.
31“Ku yi biyayya da umarnina. Ni ne Ubangiji. 32Kada ku jawo wa sunana mar tsarki ƙasƙanci, amma sai mutanen Isra'ila su gane, ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji na kuwa tsarkake ku, 33na kuma fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”
1Ubangiji ya ba Musa 2waɗannan ka'idodi domin ƙayyadaddun idodi sa'a da Isra'ilawa za su taru domin yin sujada. 3Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce. 4Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.
(L. Ƙid 28.16-25)
5Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji. 6Sa'an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai. 7Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba. 8A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.
9Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 10lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu. 11Firist ɗin zai kaɗa damin hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, don a karɓe su. Firist zai kaɗa hadayar a kashegarin Asabar. 12A ranar da suka miƙa hadaya ta kaɗawa, za su kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da ɗan rago bana ɗaya marar lahani. 13Tare da wannan hadaya kuma, za su miƙa hadaya ta gari, humushi biyu na garwar gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Za su kuma miƙa hadaya ta sha da ruwan inabi kwalaba ɗaya. 14Kada su ci sabon hatsin, wanda aka tuma, ko ɗanyensa, ko wanda aka yi gurasa da shi sai sun kawo hadayarsu ta sabon hatsi ga Allah. Za su kiyaye wannan ka'ida, da su da dukan zuriyarsu, har dukan zamanai masu zuwa.
(L. Ƙid 28.26-31)
15Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji. 16Kwana hamsin za su ƙirga zuwe kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa'an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji. 17Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji. 18Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 19Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama. 20Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da 'yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist. 21A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.
22Sa'ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.
(L. Ƙid 29.1-6)
23Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 24ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada. 25Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
(L. Ƙid 29.7-11)
26Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 27rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji. 28Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu. 29Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama'ar Allah ba. 30Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi. 31Wannan ka'ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke. 32Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.
(L. Ƙid 29.12-40)
33Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa, 34a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji. 35Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba. 36A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.
37Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta. 38Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa'adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji.
39A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, bayan da sun gama tattara amfanin gonakinsu, sai su yi idi ga Ubangiji har kwana bakwai. Rana ta fari, da rana ta takwas za su zama muhimman ranakun hutawa. 40A ranar sai su ɗibi 'ya'yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa'an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai. 41Za su yi idin nan ga Ubangiji har kwana bakwai. Wannan ka'ida ce a gare su har abada. 42Za su zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Duk 'yan ƙasa waɗanda suke Isra'ilawa za su zauna cikin bukkoki. 43Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra'ilawa su zauna cikin bukkoki, sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.
44Haka kuwa Musa ya sanar wa mutanen Isra'ila da ƙayyadaddun idodin Ubangiji.
(Fit 27.20-21)
1Ubangiji kuma ya ce wa Musa 2ya umarce Isra'ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum. 3Za a ajiye ta a gaban labulen shaida a alfarwa ta sujada. Kullum Haruna zai riƙa lura da ita daga maraice har safiya a gaban Ubangiji. Wannan zai zama muku farilla har abada a dukan zamananku. 4Kullum sai ya shirya fitilun a bisa alkuki na zinariya tsantsa a gaban Ubangiji.
5Ɗauki lallausan gari a toya gurasa goma sha biyu. A ki kowace gurasa da humushi biyu na garwar gari. 6A ajiye su bisa tebur na zinariya tsantsa jeri biyu, shida a kowane jeri. 7Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji. 8Kullum a kowace ranar Asabar, Haruna zai kintsa su a gaban Ubangiji domin Isra'ilawa saboda madawwamin alkawarin. 9Wannan abinci zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza, za su ci a wuri mai tsarki, tun da yake a gare shi rabo ne mai tsarki daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. Wannan farilla ce har abada.
10Ɗan wata mace Ba'isra'iliya wanda mahaifinsa Bamasare ne, ya fita, ya yi faɗa da wani Ba'isra'ile a cikin zangon. 11Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwar Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan. 12Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi.
13Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 14“Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu. 15Sa'an nan ka faɗa wa Isra'ilawa, cewa, duk wanda ya saɓi Allah zai ɗauki alhakin zunubinsa, 16za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.
17“Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi. 18Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.
19“Idan mutum ya yi wa wani rauni, kowane irin rauni ne ya yi masa, shi kuma haka za a yi masa. 20Idan ya karya masa ƙashi ne, sai a karya nasa ƙashin, idan ya cire wa wani ido, sai a ƙwaƙule nasa, idan haƙori ya ɓalle, sai a ɓalle nasa. Duk irin raunin da ya ji wa wani haka za a yi masa. 21Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi. 22Irin shari'ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”
23Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.
1Ubangiji kuwa ya yi wa Musa magana a kan Dutsen Sina'i, ya ce 2ya faɗa wa Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, ƙasar za ta kiyaye shekara ta bakwai ga Ubangiji. 3Shekara shida za su yi, suna ta noman gonakinsu, suna kuma ta aske gonakin inabinsu, suna tattara amfaninsu. 4Amma shekara ta bakwai ta Ubangiji ce, shekara ce ta hutawa ga ƙasar. Kada su nomi gonakinsu, ko kuwa su aske inabinsu. 5Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar. 6A shekarar nan ɗin ƙasar za ta tanada musu abinci, da su da bayinsu mata, da maza, da barorinsu na ijara, da baƙon da yake zaune tare da su, 7har da dabbobinsu na gida da na jeji. Duk albarkar da ƙasar za ta bayar, za ta zama abinci.
8Sai su ƙidaya shekara bakwai har sau bakwai. Shekarar nan bakwai sau bakwai su ne shekara arba'in da tara a gare su. 9A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka. 10Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa. 11Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara 'ya'yan inabin da ba su yi wa aski ba. 12Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar.
13Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa. 14In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna. 15Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. 16Idan shekarun sun ragu da yawa kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, sai ka saya da tsada. Idan kuwa shekarun sun ragu kima ne, sai ka saya da araha, gama yana sayar maka bisa ga yawan shekarun da za ka mora ne. 17Kada ku cuci juna fa, amma ku ji tsoron Allahnku, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”
18“Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka'idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya. 19Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.
20“Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba, 21ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku. 22Sa'ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”
23“Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.
24“Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka. 25Idan ɗan'uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan'uwansa ya jinginar. 26Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa, 27to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa'an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa. 28Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa.
29“Haka nan kuma idan mutum ya jinginar da gida a cikin birni mai garu, yana da izini ya fanshi abinsa a ƙarshen shekara guda. 30Idan kuwa bai fanshi gidan a ƙarshen shekara guda ba, sai gidan nan da yake cikin birni mai garu ya zama mallakar wanda ya karɓi jinginar, da na zuriyarsa duka har abada. Ba za a mayar wa maigidan da gidan a shekara ta hamsin ta murna ba. 31Amma gidajen da suke cikin ƙauyuka da ba su cikin garu, sai a lasafta su daidai da gonakin da suke cikin ƙasar, ana iya fansarsu, za a kuma mayar wa masu su a shekara ta hamsin ta murna. 32Amma a kan biranen Lawiyawa, da gidajen da suke cikin biranen da suka mallaka, Lawiyawa suna da izini su fanshe su a kowane lokaci. 33Amma idan wani daga cikin Lawiyawa bai fanshi gidansa ba, a shekara ta hamsin ta murna sai a mayar masa da gidan nan na cikin birnin da suka mallaka, gama gidajen da suke cikin biranen Lawiyawa su ne nasu rabo a cikin Isra'ilawa. 34Ba za a jinginar da hurumin biranensu ba, gama wannan shi ne abin mallakarsu har abada.”
35“Idan ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce, ya kasa riƙon kansa, sai ka riƙe shi kamar baƙon da yake baƙunci a wurinka. 36Kada ka ba shi rance da ruwa, amma ka ji tsoron Allah ka bar ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya zauna tare da kai. 37Kada ka ranta masa kuɗi da ruwa, kada kuma ka ba shi abinci don sumun riba. 38Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fanshe ku daga ƙasar Masar don in ba ku ƙasar Kan'ana, in zama Allahnku.”
39“Idan kuwa ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce har ya sayar da kansa gare ka, to, kada ka bautar da shi kamar bawa. 40Amma ya zauna tare da kai kamar bara na ijara, ko kuwa kamar wanda yake baƙunci. Sai ya yi aiki tare da kai har shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. 41Sa'an nan shi da iyalinsa su rabu da kai, ya koma wurin danginsa da mahallin kakanninsa. 42Gama su bayina ne, waɗanda na fanshe su daga ƙasar Masar, ba za a sayar da su kamar yadda ake sayar da bayi ba. 43Kada ka mallake shi da tsanani, amma ka ji tsoron Allahnka. 44Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al'ummar da take kewaye da ku. 45Kwa iya sayen bayi daga baƙin da suke baƙunci a wurinku, su da iyalinsu waɗanda aka haifa a ƙasarku. Kwa iya sayensu su zama dukiyarku. 46Kwa iya barinsu ga 'ya'yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma 'yan'uwanku, Isra'ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba.
47“Idan baƙo ne ko mai aikin ijara da yake zaune tare da ku ya arzuta, ɗan'uwanku kuwa wanda yake kusa da shi ya talauce, har ya sayar da kansa ga baƙon, ko mai aikin ijarar da yake tare da ku, ko kuwa ga wani daga cikin iyalin baƙon, 48bayan da ya sayar da kansa ana iya fansarsa. Wani daga cikin 'yan'uwansa ya iya fansarsa. 49Ko kawunsa, ko ɗan kawunsa, ko wani daga cikin danginsa na kusa ya iya fansarsa. Idan kuma shi kansa ya arzuta ya iya fansar kansa. 50Sai ya sa wanda ya saye shi ya lasafta tun daga shekarar da ya sayar da kansa, har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Ƙuɗin da za a fanshe shi zai zama daidai da yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta murna. Sai a ɗauke shi kamar bara na ijara. 51Idan shekarun sun ragu da yawa, sai ya fanshi kansa bisa ga adadin kuɗin da aka saye shi. 52Amma idan shekarun sun ragu kaɗan kafin shekara ta hamsin ta murna, sai ya lasafta, ya biya don fansarsa bisa ga yawan shekarun. 53Sai baƙon ya mai da shi kamar bara mai aikin ijara, shekara a kan shekara. Amma kada ya tsananta masa. 54Idan ba a fanshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, sai a shekara ta hamsin ta murna, a sake shi, shi da 'ya'yansa. 55Gama a gare ni Isra'ilawa bayi ne waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
(M. Sh 7.12-24; 28.1-14)
1Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 2Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji.
3“Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, 4sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu. 5Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.
6“Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba. 7Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku. 8Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi. 9Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina. 10Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da sūnā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo. 11Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba. 12Zan yi tafiya tare daku, in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena. 13Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”
(M. Sh 28.15-68)
14“Amma idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, to, za ku sha hukunci. 15Idan kuma kuka yi watsi da dokokina, ba ku kuwa kula da ka'idodina ba, har kuka ƙi kiyaye umarnaina, kuka karya alkawarina, 16to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci. 17Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.
18“Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku. 19Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla. 20Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.
21“Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku. 22Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.
23“Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini, 24sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku. 25Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku. 26Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.
27“Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini, 28sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku. 29Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza. 30Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku. 31Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba. 32Ni zan lalatar da ƙasar har maƙiyanku da suke zaune a ciki za su yi mamaki. 33Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace. 34Sa'an nan ƙasar za ta ji daɗin hutunta muddin tana zaune kango. Sa'ad da kuke a ƙasar maƙiyanku, ƙasar za ta huta, taji daɗin hutunta. 35Muddin tana zaune kufai za ta sami hutawa, hutawa asabatan da ba ta samu ba a lokacin da kuke zaune cikinta.
36“Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za sukuwa fāɗi. 37Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba. 38Za ku mutu a cikin al'ummai. Ƙasar maƙiyanku za ta haɗiye ku. 39Sauranku da kuka ragu za ku lalace a ƙasashen maƙiyanku saboda muguntarku da ta kakanninku, za ku lalace kamarsu.
40“Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini, 41haka kuma ni na tayar musu, na kai su ƙasar maƙiyansu. Amma idan sun ƙasƙantar da kangararriyar zuciyarsu, suka tuba, suka bar muguntarsu, 42sa'an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar. 43Amma za su fita daga ƙasar, ƙasar kuwa za ta ji daɗin hutunta muddin ba su ciki, tana zaman kango. Amma za su tuba saboda sun ƙi kula da ka'idodina, suka yi watsi da dokokina. 44Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu. 45Amma saboda su zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al'ummai domin in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.”
46Waɗannan su ne dokoki, da ka'idodi, da umarnai waɗanda Ubangiji ya yi tsakaninsa da Isra'ilawa ta hannun Musa a bisa Dutsen Sina'i.
1Ubangiji ya ba Musa 2waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan an ba da mutum ga Ubangiji don cikar babban wa'adi za a iya fansarsa ta wurin biya waɗannan kuɗi.
8Idan mutumin ya cika talauci har ya kasa biyan tamanin da aka kimanta, sai ya kawo mutumin da aka yi wa'adi a kansa a gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamaninsa daidai da ƙarfin wanda ya yi wa'adin.
9Idan kuwa dabba ce irin wadda mutane kan miƙa hadaya ga Ubangiji, dukan irin wannan da mutum yakan bayar ga Ubangiji zai zama tsattsarka. 10Ba zai musaya shi da wani abu ba, ba zai musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau ba. Idan kuwa ya musaya dabba da dabba, sai duka biyu, abar da aka musaya, da wadda aka musayar, za su zama tsarkakakku. 11Idan kuwa dabbar marar tsarki ce, irin wadda ba a miƙa ta hadaya ga Ubangiji, sai mutumin ya kai dabbar a wurin firist. 12Firist ɗin zai kimanta tamanin dabbar daidai darajarta, kamar yadda firist ya kimanta, haka zai zama. 13Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta.
14Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama. 15Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.
16Idan mutum ya keɓe wa Ubangiji wani sashi daga cikin gonarsa ta gādo, sai ka kimanta tamanin gonar daidai da yawan irin da zai rafa. Gonar da za a yafa iri wajen garwa ashirin na sha'ir tamaninta zai zama wajen shekel hamsin. 17Idan ya keɓe gonarsa daga shekara ta hamsin ta murna, ba za a rage kome daga cikin tamanin gonar da aka kimanta ba. 18Amma idan ya keɓe ta bayan shekara ta hamsin ta murna, sai firist ya kimanta yawan kuɗin bisa ga yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. Sai a rage kuɗin tamanin gonar. 19Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa. 20Amma idan ba ya so ya fanshi gonar, ko kuwa ya riga ya sayar wa wani da gonar, faufau, ba zai sāke fansarta ba. 21Sa'ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta.
22Idan kuwa ya keɓe wa Ubangiji gonar da ya saya, wadda ba ta gādo ba, 23sai firist ya kimanta tamaninta har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Shi mutumin zai ba da yawan abin da aka kimanta a ranar, abu mai tsarki ne ga Ubangiji. 24A cikin shekara ta hamsin ta murna, sai a mayar da gonar ga wanda aka saye ta a hannunsa, wanda gonarsa ce ta gādo.
25Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.
26Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne. 27Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta.
28Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji. 29Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi.
30Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na 'ya'yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji. 31Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin. 32Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce. 33Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.
34Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sina'i saboda isra'ilawa.