Luke

BISHARA TA HANNUN
Luka

1

Gabatarwa

1Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da suka tabbata a cikinmu, 2daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al'amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana, 3da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas, 4domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.

An Yi Faɗin Haihuwar Yahaya Maibaftisma

5A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu. 6Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. 7Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

8Ana nan, wata rana Zakariya yana a kan hidimarsa ta firist, a kan ƙungiyarsu, 9bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare. 10A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama'a suna waje, suna addu'a, 11sai wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare. 12Da Zakariya ya gan shi ya firgita, tsoro ya kama shi. 13Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya. 14Za ka yi murna da farin ciki, Mutane da yawa kuma za su yi farin ciki da haihuwarsa. 15Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji, Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki Tun yana cikin mahaifiyarsa. 16Zai kuma juyo da Isra'ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu. 17Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, domin ya same su a shirye.” 18Sai Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwana biyu.” 19Sai mala'ikan ya amsa ya ce, “Ni ne Jibra'ilu da nake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir. 20To, ga shi, za ka babance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al'amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.” 21Jama'a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali. 22Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana. 23Sa'ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, ya koma gida.

24Bayan kwanakin nan mata tasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa, 25“Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rahama, domin yă kawar mini da wulakanci a wurin mutane.”

An Yi Faɗin Haihuwar Yesu

26A wata na shida Allah ya aiko mala'ika Jibra'ilu zuwa wani gari a ƙasar Galili, mai suna Nazarat, 27gun wata budurwa da aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu. 28Sai mala'ikan ya je wurinta, ya ce, “Salama a gare ki, yake zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!” 29Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce. 30Mala'ikan kuma ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. 31Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haife ɗa, ki kuma raɗa masa suna Yesu. 32Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda, 33Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada, Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” 34Sai Maryamu ta ce wa mala'ikan, “T ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?” 35Mala'ikan ya amsa mata ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. 36Ga shi kuma, 'yar'uwarki Alisabatu ma ta yi cikin ɗa namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shaida, ita da ake ce wa bakararriya. 37Ba wata faɗar Allah da za ta kāsa cika.” 38Sai Maryamu ta ce, “To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zama mini yadda ka faɗa.” Sai mala'ikan ya tashi daga gare ta.

Maryamu ta Ziyarci Alisabatu

39A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza. 40Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu. 41Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki, 42har ta tā da murya da ƙarfi, ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne! 43Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da mahaifiyar Ubangijina za ta zo gare ni? 44Domin kuwa da jin muryarki ta gaisuwa a kunnena, sai jaririn ya motsa da ƙarfi a cikina domin farin ciki. 45Albarka tā tabbata ga wadda ta gaskata, domin za a cika abubuwan da Ubangiji ya aiko a faɗa mata.”

Waƙar Maryamu

46Sai Maryamu ta ce, “Zuciyata tana ɗaukaka shi, Ubangiji, 47Allah Mai Cetona, da shi ruhuna yake ta farin ciki, 48Domin fa shi ya dubi ƙasƙancin baiwarsa. Ga shi, jama'a ta dukan zamanai na nan gaba, za su ce mini mai albarka ce nan gaba. 49Domin fa shi da yake Mai Iko, Manyan al'amura ya yi mini, Sunansa labudda Mai Tsarki ne. 50Daga zamanai ya zuwa wani zamani, Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa. 51Manyan ayyuka da ya yi, Masu girmankai, su da dabarbarunsu ya warwatsa. 52Ya fiffitar da sarakuna a sarauta, Ya ɗaukaka ƙasƙantattu. 53Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri, Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi. 54Ya taimaka wa baransa Isra'ila, Domin yana tunawa da jinƙansa. 55Ya cika faɗarsa ga kakanninmu, Ga Ibrahim da zuciyarsa, har abada.” 56Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa'an nan ta koma gida.

Haihuwar Yahaya Maibaftisma

57To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji. 58Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya yi ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki. 59Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan mahaifinsa, Zakariya, 60amma mahaifiyarsa ta ce, “A'a, Yahaya za a sa masa.” 61Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan'uwanku mai suna haka.” 62Sai suka alamta wa mahaifinsa, suna neman sunan da yake so a sa masa. 63Sai ya nema a ba shi allo, sa'an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki. 64Nan da nan ya sami baki, kwaɗon harshensa ya saku, ya fara magana, yana yabon Allah. 65Sai tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Aka yi ta baza labarin duk waɗannan al'amura ko'ina a dukan ƙasa mai duwatsu ta Yahudiya. 66Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.

Waƙar Zakariya

67Sai aka cika mahaifinsa Zakariya da Ruhu Mai Tsarki, ya yi annabci, ya ce, 68“Ubangiji Allahn Isra'ila, A gare shi ne lalle yabo yake tabbata, Domin ya kula, ya yi wa jama'arsa fansa. 69Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu, Daga zuriyar baransa Dawuda. 70Yadda tun tuni ya faɗa ta bakunan Annabawa nasa tsarkakan nan, 71Yă cece mu daga abokan gābanmu, Har ma daga dukan maƙiyanmu. 72Domin nuna jinƙai ne ga kakanninmu, Yă tuna da alkawarinsa mai tsarkin nan. 73Shi ne rantsuwar nan wadda ya yi wa ubanmu Ibrahim, 74Domin yana cetonmu daga abokan gābanmu, Mu bauta masa ba da jin tsoro ba, 75Sai dai da tsarki da adalci a gabansa, Dukan iyakar kwanakin nan namu. 76Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki, Gama za ka riga Ubangiji gaba, Domin ka shisshirya hanyoyinsa, 77Kă sanar da ceto ga jama'arsa, Wato ta samun gafarar zunubansu, 78Saboda tsananin jinƙai na Allahnmu, Daga Sama hasken asubahi zai ɓullo mana, Daga can Sama ne fa zai keto mana, 79Domin yă haskaka na zaune cikin duhu, Da waɗanda suke zaune a bakin mutuwa, Domin ya bishe mu a hanyar salama.” 80Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Isra'ila.

2

Haihuwar Yesu

(Mat 1.18-25)

1A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa. 2Wannan ita ce ƙidaya ta fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya. 3Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi. 4Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa), 5don a rubuta shi, duka da Maryamu wadda yake tashin, wadda take kuma da ciki. 6Sa'ad da suke a can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi. 7Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani kwamin dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.

Makiyaya da Mala'iku

8A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin, suna tsaron garken tumakinsu da daddare. 9Sai ga wani mala'ikan Ubangiji a tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, har suka tsorata gaya, 10Sai mala'ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. 11Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji. 12Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri a rufe da zanen goyo, kwance a kwamin dabbobi.” 13Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa, 14“Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, a can cikin Sama mafi ɗaukaka. A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”

15Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.” 16Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn a kwance cikin kwamin dabbobi. 17Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu a game da wannan ɗan yaro. 18Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu. 19Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana bimbini a zuci. 20Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

Kaciyar Yesu

21Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka raɗa masa suna Yesu, wato sunan da mala'ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.

Miƙa Yesu a Haikali

22Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji 23(kamar dai yadda yake a rubuce a Shari'ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce tsattsarka ne shi na Ubangiji,”) 24su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu.”

25To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26Ruhu Mai Tsarki kuwa ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji. 27Ruhu yana iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka'idar Shari'ar ta ce, 28sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce, 29“Yanzu kam, ya Mamallaki, Sai ka sallami bawanka lafiya, Bisa ga abin da ka faɗa, 30Don na ga cetonka zahiri, 31Da ka shirya a gaban kabilai duka, 32Haske mai bayyana wa alummai hanyarka, Da kuma ɗaukakar jama'arka Isra'ila.”

33Mahaifiyarsa da mahaifinsa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa a game da shi, 34Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu mahaifiyar Yesu, “Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin fāɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa a cikin Isra'ila, Zai kuma zama alama wadda ake kushenta, 35Domin tunanin zukata da yawa su bayyana. I, ke ma, takobi zai zarta zuciyarki.”

36Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, 'yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukarta na budurci, 37da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi. 38Nan tāke ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.

Komawa Nazarat

39Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat. 40Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.

Saurayi Yesu ya Shiga Haikali

41To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa. 42Da Yesu ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin idi. 43Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba. 44Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani. 45Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa. 46Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin yana zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi. 47Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajiin irin fahimtarsa da amsoshinsa. 48Da suka gan shi suka yi mamaki, sai mahaifiyarsa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.” 49Sai ya ce musu, “Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha'anin Ubana ba?” 50Amma ba su fahimci maganar da ya yi musu ba. 51Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuwa tana riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.

52Yesu kuwa ya yi ta ƙaruwa da hikima, da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da mutane.

3

Wa'azin Yahaya Maibaftisma

(Mat 3.1-12; Mar 1.1-8; Yah 1.19-28)

1A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya, 2a zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, Maganar Allah ta zaike wa Yahaya ɗan Zakariya a jeji. 3Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa'azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu, 4yadda yake a rubuce a Littafin Annabi Ishaya cewa, “Muryar mai kira a jeji tana cewa, Ku shirya wa Ubangiji tarfarki, Ku miƙe hanyoyinsa, 5Za a cike kowane kwari, Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su. Za a miƙe karkatattun wurare, Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba. 6Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”

7Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da suke zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi aikin da nuna tubarku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan. 9Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”

10Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?” 11Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.” 12Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?” 13Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.” 14Waɗansu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”

15Da yake mutane duk sun zaƙu, kowa yana wuswasi a ransa a game da Yahaya, ko watakila shi ne Almasihu, 16sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɗaurin takalminsa ma ban isa in kwance ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 17Ƙwaryar shiƙarsa tana hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkama ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar mutuwa.”

18Ta haka, da waɗansu gargaɗi masu yawa, Yahaya ya yi wa jama'a bishara. 19Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan'uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi, 20sai ya ƙara da kulle Yahaya a kurkuku.

An Yi wa Yesu Baftisma

(Mat 3.13-17; Mar 1.9-11)

21To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre, 22Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata siffa, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”

Asalin mutuntakar Yesu

(Mat 1.1-17)

23Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli, 24Heli ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu, 25Yusufu ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Azaliya, Azaliya ɗan Najaya, 26Najaya ɗan Ma'ata, Ma'ata ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Shimeya, Shimeya ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yahuza, 27Yahuza ɗan Yowana, Yowana ɗan Refaya, Refaya ɗan Zarubabel, Zarubabel ɗan Shayaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri, 28Niri ɗan Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kosama, Kosama ɗan Almadama, Almadama ɗan Er, 29Er ɗan Yosi, Yosi ɗan Eliyezer, Eliyezar ɗan Yorima, Yorima ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, 30Lawi ɗan Saminu, Saminu ɗan Yahuza, Yahuza ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yonana, Yonana ɗan Eliyakim, 31Eliyakim ɗan Malaya, Malaya ɗan Mainana, Mainana ɗan Matata, Matata ɗan Natan, Natan ɗan Dawuda, 32Dawuda ɗan Yesse, Yesse ɗan Obida, Obida ɗan Bo'aza, Bo'aza ɗan Salmon, Salmon ɗan Nashon, 33Nashon ɗan Amminadab, Amminadab ɗan Aram, Aram ɗan Hesruna, Hesruna ɗan Feresa, Feresa ɗan Yahuza, 34Yahuza ɗan Yakubu, Yakubu ɗan Ishaku, Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ɗan Tera, Yera ɗan Nahor, 35Nahor ɗan Serug, Serug ɗan Reyu, Reyu ɗan Feleg, Feleg ɗan Eber, Eber ɗan Shela, 36Shela ɗan Kenan, Kenan ɗan Arfakshad, Arfakshad ɗan Shem, Shem ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamek, 37Lamek ɗan Metusela, Metusela ɗan Anuhu, Anuhu ɗan Yared, Yared ɗan Mahalel, Mahalel ɗan Kenan, 38Kenan ɗan Enosh, Enosh ɗan Shitu, Shitu ɗan Adamu, Adamu kuma na Allah.

4

Shaiɗan ya Gwada Yesu

(Mat 4.1-11; Mar 1.12-13)

1Yesu kuma cike da Ruhu Mai Tsarki sai ya dawo daga Kogin Urdun. Ruhu yana iza shi zuwa jeji, 2har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa. 3Iblis ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama gurasa,” 4Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, “‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.” 5Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido. 6Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama. 7In kuwa za ka yi mini sujada, duk za su zama naka.” 8Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa, “‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai za ka bauta wa.” 9Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan, 10don a rubuce yake cewa, “‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni a game da kai, su kiyaye ka,” 11da kuma “‘Za su tallafe ka, Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.” 12Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, “‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.” 13Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.

Yesu ya Fara Hidima a Galili

(Mat 4.12-17; Mar 1.14-15)

14Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen. 15Ya yi ta koyarwa a majami'unsu, duk ana girmama shi.

An Ƙi Yesu a Nazarat

(Mat 13.53-58; Mar 6.1-6)

16Ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami'a a ran Asabar kamar yadda ya saba yi. Sai ya miƙe domin ya yi karatu. 17Aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta cewa, 18“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne, 19In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.” 20Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke a cikin majami'a suka zuba masa ido. 21Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.” 22Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?” 23Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganar nan, “‘Likita, warkar da kanka.” Za ku kuma ce mini, “‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnaham, ka yi a nan garinku mana.” 24Ya ce kuma, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da yake yardajje a garinsu. 25Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar. 26Duk da haka ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata gwauruwa, kaɗai a Zarifat ta ƙasar Sidon. 27A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra'ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na'aman, mutumin Suriya, kaɗai.”

28Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami'a suka husata ƙwarai. 29Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa. 30Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa

Mai Baƙin Aljan

(Mar 1.21-28)

31Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu a ran Asabar. 32Suka yi mamakin koyarwarsa domin maganarsa da hakikancewa take. 33A majami'ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce, 34“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.” 35Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba. 36Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.” 37Labarinsa duk ya bazu ko'ina a kewayen ƙasar.

Yesu ya Warkar da Surukar Bitrus

(Mat 8.14-15; Mar 1.29-31)

38Sai ya tashi daga majami'a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita. 39Sai ya tsaya a kanta, ya tsawata wa zazzaɓin, ya kuwa sake ta. Nan take ta tashi ta yi musu hidima.

Yesu ya Warkar da Mutane da yawa da Maraice

(Mat 8.16-17; Mar 1.32-34)

40A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su. 41Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don su sani shi ne Almasihu.

Yesu ya Tafi Yin Wa'azi

(Mar 1.35-39)

42Da gari ya waye ya fita, ya tafi wani wurin a inda ba kowa. Sai taro masu yawa suka yi ta nemansa, suka je wurinsa. Sonsu ne su tsaishe shi, don kada ya tashi daga gare su. 43Amma ya ce musu, “Lalle ne in yi wa sauran garuruwa bisharar Mulkin Allah, domin saboda wannan nufi ne aka aiko ni.” 44Sai ya yi ta yin wa'azi a majami'un ƙasar Galili.

5

An Kama Kifi Jingim

(Mat 4.18-22; Mar 1.16-20)

1Wata rana taro suna matsarsa domin su ji Maganar Allah, shi kuwa yana tsaye a bakin Tekun Janisarata, 2sai ya hangi ƙananan jirage biyu a bakin tekun, masuntan kuwa sun fita daga cikinsu, suna wankin tarunsu. 3Sai ya shiga ɗaya jirgin, wanda yake na Bitrus, ya roƙe shi ya ɗan zakuɗa da jirgin daga bakin gaci. Sai ya zauna ya yi ta koya wa taro masu yawa daga jirgin. 4Da ya gama magana, ya ce wa Bitrus, “Zakuɗa da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunku, ku janyo kifi.” 5Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama kome ba, amma tun da ka yi magana zan saki tarun.” 6Da suka yi haka kuwa, suka kamo kifi jingim, har ma tarunsu suka fara kecewa. 7Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar za su nutse. 8Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.” 9Domin shi da waɗanda ke tare da shi duka, mamaki ya kama su saboda kifin nan da duka janyo, 10haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.” 11Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.

Yesu ya Warkar da Kuturu

(Mat 8.1-4; Mar 1.40-45)

12Wata rana Yesu yana ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.” 13Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi. 14Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 15Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu. 16Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu'a.

Yesu ya Warkar da Shanyayye

(Mat 9.1-8; Mar 2.1-12)

17Wata rana yana koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan. 18Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu. 19Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu. 20Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.” 21Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?” 22Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku? 23Wanne ya fi sauƙi, a ce, “‘An gafarta maka zunubanka,” ko kuwa a ce, “‘Tashi, ka yi tafiya?” 24Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya,” sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.” 25Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah. 26Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga abubuwan al'ajabi!”

Kiran Lawi

(Mat 9.9-13; Mar 2.13-17)

27Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” 28Sai ya bar kome duka, ya tashi ya bi shi.

29Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su. 30Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya. 32Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”

Tambaya a kan Azumi

(Mat 9.14-17; Mar 2.18-22)

33Sai suka ce masa, “Almajiran Yahaya suna azumi a kai a kai, suna kuma addu'a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.” 34Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su? 35Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.” 36Ya kuma yi musu misali, ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. In ma an yi, ai, sai ya kece sabuwar tufar, sabon ƙyallen kuma ba za dace da tsohuwar tufar ba. 37Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace. 38Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. 39Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabin bayan ya sha tsohon, don ya ce, “‘Ai, tsohon yana da kyau.”

6

Almajirai suna Zagar Alkama a Ran Asabar

(Mat 12.1-8; Mar 2.23-28)

1Wata rana a ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci. 2Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Don me kuke yin abin da bai halatta a yi ba a ran Asabar?” 3Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4Yadda ya shiga masujadar Allah, ya ɗauki keɓaɓɓiyar gurasar nan ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa, wadda ba ta halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai?” 5Sai ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”

Mai Shanyayyen Hannu

(Mat 12.9-14; Mar 3.1-6)

6A wata Asabar kuma ya shiga majami'a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye. 7Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 8Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan a tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin. 9Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?” 10Sai ya duddube su dūke, ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Da ya miƙa, hannunsa kuwa sai ya koma lafiyayye. 11Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.

Yesu ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu

(Mat 10.1-4; Mar 3.13-19)

12A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah. 13Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni. 14Su na Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas, 15da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti, 16da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.

Yesu ya yi wa Mutane Masu Yawa Hidima

(Mat 4.23-25)

17Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da suke bakun bahar, waɗanda su zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu. 18Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su. 19Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

Albarka da La'ana

(Mat 5.1-12)

20Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce, “Albarka tā tabbata a gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.

21“Albarka tā tabbata a gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da ku. “Albarka tā tabbata gare ku, ku da ke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.

22“Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kama ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum. 23Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.

24“Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta'aziyya.

25“Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.

26“Kaitonku in kowa yana yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”

Ƙaunar Magabta

(Mat 5.38-48; 7.12)

27“Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri. 28Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a. 29Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma. 30Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi. 31Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.

32“In masoyanku kawai kuke ƙauna wace lada ce da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu. 33In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wace lada ce da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi. 34In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wace lada ce da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai. 35Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladarku kuma za ta yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye. 36Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”

Kada ku Ɗora wa Kowa Laifi

(Mat 7.1-5)

37“Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku. 38Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a aunamuku.”

39Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba? 40Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa. 41Don me kake duban ɗan hakin da ke a idon ɗan'awanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ku kula ba? 42Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, “‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,” alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”

Akan Gane Itace ta 'Ya'yansa

(Mat 7.16-20; 12.33-35)

43“Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan 'ya'ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan 'ya'ya. 44Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya. 45Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”

Kafa Harsashin Gini Iri Biyu

(Mat 7.24-27)

46“Don me kuke kirana, “‘Ubangiji, Ubangiji,” ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku? 47Duk mai zuwa wurina, yake yin maganata, yake kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa. 48Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci. 49Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”

7

Yesu ya Warkar da Bawan Wani Jarumi

(Mat 8.5-13)

1Bayan da Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama'a, ya shiga Kafarnahum. 2To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangidansa ke jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa. 3Da jarumin ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu shugabannin Yahudawa wurinsa, su roƙe shi ya zo ya warkar da bawansa. 4Da suka isa wurin Yesu sai suka roƙe shi ƙwarai suka ce, “Ai, ya cancanci a yi masa haka, 5don yana ƙaunar jama'armu, shi ne ma ya gina mana majami'armu.” 6Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai jarumin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahalar da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba. 7Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke. 8Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, “‘Je ka,” sai ya je, wani kuwa in ce masa, “‘Zo,” sai ya zo, in ce wa bawana, “‘Yi abu kaza,” sai ya yi.” 9Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.” 10Da waɗanda aka aika suka koma gidan, suka sami bawan garau.

Yesu ya Tā da Ɗan Gwauruwa

11Ba da daɗewa ba, Yesu ya tafi wani gari, mai suna Nayin, almajiransa da kuma babban taro suka tafi da shi. 12Ya kusaci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ama ɗauke da shi, shi kaɗai ne wajen mahaifiyarsa, gwauruwa. Mutanen gari da yawa sun rako ta. 13Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.” 14Sa'an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.” 15Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga mahaifiyarsa. 16Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.” 17Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.

'Yan Saƙo daga Yahaya Maibaftisma

(Mat 11.2-19)

18Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan. 19Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya cewa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 20Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu a gare ka, yana tambaya, cewa, “‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 21Nan tāke Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani. 22Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka gani. Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara. 23Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”

24Bayan da jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa? 25To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke. 26To, kallon me kuka ya yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa. 27Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa, “‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.” 28Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.” 29Da duk jama'a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya. 30Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.

31“To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su? 32Kamar yara suke da suke zaune a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba, Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.” 33Ga shi, Yahaya Maibaftisma ya zo, ba ya cin gurasa, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, “‘Ai, yana da iska.” 34Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, kuna kuma cewa, “‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!” 35Duk da haka hikimar Allah, ta dukkan aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”

Yesu a Gidan Saminu Bafarisiye

36Wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga gidan Bafarisiyen, ya ƙishingiɗa wurin cin abincin. 37Sai ga wata matar garin, mai zunubi, da ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, ta kawo wani ɗan tandu na man ƙanshi, 38ta tsaya a bayansa a wajen ƙafafunsa, tana kuka. Sai hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, ta goge su da gashinta, ta yi ta sumbantarsu, ta shafa musu man ƙanshin. 39To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da take taɓa shi, don mai zunubi ce.” 40Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.” 41Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. 42Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?” 43Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.” 44Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matar nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta. 45Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar ƙafafuna ba. 46Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna. 47Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake yi.” 48Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.” 49Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?” 50Sai Yesu ya ce matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”

8

Waɗansu Mata sun Tafi tare da Yesu

1Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Su goma sha biyun nan kuwa suna tare da shi, 2da waɗansu mata da aka raba su da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. A cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai, 3da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.

Misali da Mai Shuka

(Mat 13.1-9; Mar 4.1-9)

4Da jama'a masu yawa suka taru, mutane suna ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce. 5“Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su. 6Waɗansu kuma suka fāɗi a kan dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don ba danshi. 7Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su. 8Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Ma'anar Misalin

(Mat 13.10-17; Mar 4.10-12)

9Sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin. 10Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, za su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, za su ji, amma ba za su fahimta ba.

Yesu ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka

(Mat 13.18-23; Mar 4.13-20)

11“To, misalin irin shi ne, Maganar Allah. 12Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa'an nan iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto. 13Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe. 14Waɗanda suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya suka sarƙe su, har su kāsa yin amfani. 15Waɗanda suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.

Fitila a Rufe da Masaki

(Mar 4.21-25)

16“Ba mai kunna fitila ya rufe da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A'a, sai dai ya ɗora ta a a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken. 17Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba sai tonu ya zama bayyananne ba. 18Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”

Mahaifiyar Yesu da 'Yan'uwansa

(Mat 12.46-50; Mar 3.31-35)

19Mahaifiyarsa da 'yan'uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro. 20Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.” 21Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma 'yan'uwana.”

Yesu ya Tsawata wa Hadiri

(Mat 8.23-27; Mar 4.35-41)

22Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi. 23Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Hadiri mai iska ya taso a tekun, jirginsu ya tasar wa cika da ruwa, har suna cikin hatsari. 24Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, za mu hallaka!” Sai ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit. 25Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

Warkar da Mai Aljan na Garasinawa

(Mat 8.28-34; Mar 5.1-20)

26Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda ke hannun riga da ƙasar Galili. 27Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta. 28Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya fāɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.” 29Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji. 30Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa. 31Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahallaka.

32A, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade ne kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu. 33Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shiga aladun. Garken kuwa suka rungungunta ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka hallaka a ruwa.

34Da 'yan kiwon aladun nan suka ga abin da ya faru, suka gudu, suka ba da labari a birni da ƙauye. 35Sai jama'a suka fiffito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, a zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata. 36Waɗanda aka yi abin a gaban idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan. 37Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma. 38Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce, 39“Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko'ina a cikin birnin yana sanar da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.

Warkar da 'Yar Yayirus da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu

(Mat 9.18-26; Mar 5.21-43)

40To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne. 41Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami'a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa. 42Yana da 'ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa. Yana tafiya, taro masu yawa na matsarsa, 43sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita. 44Ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar jininta ta tsaya. 45Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi mūsu, sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka ce, “Maigida, ai, taro masu yawa ne suke tutturarka, suna matsarka.” 46Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, domin na ji wani iko ya fita daga gare ni.” 47Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama'a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take. 48Sai ya ce mata, “Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami'ar, ya ce, “Ai, 'yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.” 50Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami'ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.” 51Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma mahaifin yarinyar da mahaifiyarta, 52Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.” 53Sai suka yi masa dariyar raina, don sun sani ta mutu. 54Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.” 55Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci. 56Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

9

Yesu ya Aiki Goma Sha Biyun Nan

(Mat 10.5-15; Mar 6.7-13)

1Sai ya tara goma sha biyun nan ya ba su iko da izini kan dukan aljannu, su kuma warkar da cuce-cuce, 2ya kuma aike su su yi wa'azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. 3Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ka ɗauki taguwa biyu. 4Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi. 5Duk waɗanda ba su yi na'am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” 6Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko'ina.

Mutuwar Yahaya Maibaftisma

(Mat 14.1-12; Mar 6.14-29)

7To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu. 8Waɗansu kuwa suka ce Iliya ne ya bayyana. Waɗansu kuma suka ce ɗaya daga annabawan dā ne ya tashi. 9Sai Hirudus ya ce, “Yahaya kam na fille masa kai. Wa ke nan kuma da nake jin irin waɗannan abubuwa a game da shi?” Sai ya nemi ganinsa.

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

(Mat 14.13-21; Mar 6.30-44; Yah 6.1-14)

10Da manzanni suka dawo, suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari mai suna Betsaida. 11Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa. 12Da rana ta fara sunkuyawa, goma sha biyun suka matso, suka ce masa, “Sai ka sallami taron, su shiga ƙauyuka da karkara na kurkusa, su sauka, su nemi abinci, don inda muke ba mutane.” 13Amma ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai, abin da muke da shi bai fi gurasa biyar da kifi biyu ba, sai dai in za mu je mu sayo wa dukkan jama'ar nan abinci ne.” 14Maza sun kai wajen dubu biyar. Sai ya ce wa almajiransa, “Ku ce musu su zazzauna ƙungiya, kowace ƙungiya misali hamsin hamsin.” 15Haka kuwa suka yi, suka sa dukkansu su zazzauna. 16Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a. 17Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashe ragowar gutsattsarin, kwando goma sha biyu.

Hurcin Bitrus a kan Yesu

(Mat 9.18-26; Mar 5.21-43)

18Wata rana yana addu'a shi kaɗai, almajiransa kuwa suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane suke cewa nake?” 19Suka amsa suka ce, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.” 20Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Almasihu na Allah.”

Yesu ya Faɗi irin Mutuwar da zai Yi

(Mat 16.20-28; Mar 8.30ū9.1)

21Sai ya kwaɓe su matuƙa kada su gaya wa kowa wannan magana. 22Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana uku kuma a tashe shi.”

23Sai ya ce wa dukansu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, yă bi ni. 24Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, tattalinsa yake yi. 25Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka a kan hasarar ransa, ko a bakin ransa? 26Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa'ad da ya zo da ɗaukakarsa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala'iku tsarkaka. 27Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu a tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Mulkin Allah.”

Sākewar Kamanninsa

(Mat 17.1-8; Mar 9.2-8)

28Bayan misalin kwana takwas da yin maganar nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu'a. 29Yana yin addu'a, sai kamanninsa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido. 30Sai ga mutum biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya. 31Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙaunarsa ne, wadda yake gabannin yi a Urushalima. 32Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi. 33Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba. 34Yana faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su suka tsorata. 35Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙuanataccena. Ku saurare shi!” 36Bayan muryar ta yi magana, sai ga Yesu shi kaɗai. Suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

Yesu ya Warkar da Yaro Mai Farfadiya

(Mat 17.14-21; Mar 9.14-29)

37Kashegari da suka gangaro daga kan dutsen, wani babban taro ya tarye shi. 38Sai ga wani daga cikin taron ya yi kira, ya ce, “Malam, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ne ke nan gare ni. 39Ga shi, aljan yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai. 40Na kuwa roƙi almajiranka su fitar da shi, amma sun kasa.” 41Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗan naka.” 42Yana zuwa, sai aljanin ya buge shi ƙwarai, jikinsa yana rawa. Amma Yesu ya tsawata wa baƙin aljanin, ya warkar da yaron, ya kuma mayar wa mahaifinsa da shi. 43Duk aka yi mamakin girman ikon Allah.

Yesu ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

(Mat 17.22-23; Mar 9.30-32) Tun dukansu suna mamakin duk abubuwan da yake yi, sai ya ce wa almajiransa, 44“Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.” 45Amma ba su fahimci maganar nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana. 9.46 Wane ne Mafi Girma? Wane ne Mafi Girma?

(Mat 18.1-5; Mar 9.33-37)

46Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu. 47Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi. 48Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ka karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”

Wanda ba ya Gāba da ku, Naku Ne

(Mar 9.38-40)

49Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.” 50Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

Samariyawan wani Ƙauye sun Ƙi Karɓar Yesu

51Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima. 52Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa sa shisshirya masa. 53Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take. 54Da almajiransa Yakubu da Yahaya ga haka suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?” 55Amma ya juya, ya tsawata musu. 56Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.

Masu Cewa za su Bi Yesu

(Mat 8.19-22)

57Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.” 58Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da shekunansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.” 59Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.” 60Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.” 61Wani kuma ya ce, “Ya Ubangiji, zan bi ka, amma ka bar ni tukuna in ji wa mutanen gida bankwana.” 62Yesu ya ce masa “Wanda ya fara huɗa da keken noma, yana duban baya, bai dace da Mulkin Allah ba.”

10

Yesu ya Aiki Saba'in Ɗin

1Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi. 2Ya ce musu, “Girbin yana da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi. 3To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai. 4Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya. 5Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, “‘Salama a gare ku mutanen gidan nan!” 6In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku. 7Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma'aikaci ya cancanci ladarsa. Kada ku riƙa sāke masauki. 8Duk garin da kuka shiga, in an yi na'am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku. 9Ku warkar da marasa lafiya da ke cikinsa, ku kuma ce musu, “‘Mulkin Allah ya kusato ku.” 10Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na'am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa, 11“‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.” 12Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”

Tsawata wa Garuruwan da ba su Tuba Ba

(Mat 11.20-24)

13“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizar da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka. 14Amma a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku. 15Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.

16“Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”

Komowar Saba'in Ɗin

17Sai kuma saba'in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!” 18Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya. 19Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma yi rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan. 20Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu suna yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”

Yesu ya Yi Farin Ciki

(Mat 11.25-27; Mar 13.16-17)

21A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri. 22Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”

23Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani. 24Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

Basamariyen da ya Nuna Jinƙai

25Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?” 26Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?” 27Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.” 28Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”

29Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan'uwa nawa?” 30Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai 'yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah. 31Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 32Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 33Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi, 34ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa'an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa. 35Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, “‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.” 36To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan'uwa ga wanda 'yan fashin suka faɗa wa?” 37Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”

Yesu ya Ziyarci Marta da Maryamu

38Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta saukar da shi a gidanta. 39Tana kuwa da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron maganarsa. 40Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ku kula ba, 'yar'uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.” 41Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe ya ke, kina kuma damuwa kan abu da yawa. 42Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”

11

Koyarwar Yesu a kan Addu'a

(Mat 6.9-15; 7.7-11)

1Wata rana Yesu yana addu'a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu'a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.” 2Sai ya ce musu, “In kuna addu'a ku ce, “‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki, Mulkinka yă zo, 3Ka ba mu abincin yau da na kullum. 4Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi. Kada ka kai mu wurin jaraba.”

5Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, “‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana, 6ga shi, wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi,” 7sa'an nan aminin ya amsa masa daga ciki ya ce, “‘Kada ka dame ni, ai, an kulle ƙofa, da ni da 'ya'yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.” 8Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata. 9Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku. 10Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa. 11Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi[gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji? 12Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama? 13To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”

Yesu da Ba'alzabul

(Mat 12.22-30; Mar 3.20-27)

14Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. 15Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.” 16Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama. 17Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje. 18In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu. 19In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. 20Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan. 21In ƙaƙƙarfan mutum ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayan gidansa lafiya suke. 22In kuwa wanda ya fi shi ƙarfi ya fāɗa masa, ya kuma rinjaye shi, sai ya ƙwace duk makaman da ya dogara da su, ya kuma rarraba kayansa ganima, 23Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.”

Komawar Baƙin Aljan

(Mat 12.43-45)

24“Baƙin aljan, in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa, yana neman hutawa. In ya rasa, sai ya ce, “‘Zan koma gidana da na fito.” 25Sa'ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce, 26Daga nan sai ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum kuwa ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa.”

Tabbatacciyar Albarka

27Yana faɗar haka, sai wata mace a taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Albarka tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.” 28Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”

'Yan Zamani Mugaye suna Neman Alama

(Mat 12.38-42; Mar 8.12)

29Da taro ya riƙa ƙaruwa a wurinsa, sai ya fara cewa, “Wannan zamani mugun zamani ne. Suna neman ganin wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu sai dai ta Yunusa. 30Wato, kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Nineba, haka kuma, Ɗan Mutum zai zamar wa zamanin nan. 31A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan. 32A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan su kā da su. Don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.”

Fitilar Jiki

(Mat 5.15; 6.22-23)

33“Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken. 34Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu. 35Saboda haka, sai ka lura ko hasken da yake a gare ka duhu ne. 36In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda yake da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka maka.”

Yesu ya Fallashi Farisiyawa da Masanan Attaura

(Mat 23.1-36; Mar 12.38-40; Luka 20.45-47)

37Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin. 38Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba. 39Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki a cike kuke da zalunci da mugunta. 40Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba? 41Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.

42“Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na'ana'a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba. 43Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami'u, da kuma gaisuwa a kasuwa. 44Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”

45Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.” 46Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu! 47Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe. 48Wato, ku shaida ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku, ga shi, su ne fa suka kashe su, ku kuwa har kuka gina musu gubbobin! 49Shi ya sa hikimar Allah ta ce, “‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,” 50don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani, 51wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe a tsakanin bagadin hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi a kan mutanen wannan zamani. 52Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”

53Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa, 54suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.

12

Faɗaka a kan Makirci

1Sa'an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci. 2Ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. 3Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a lolloki, za a yi shelarsa daga kan soraye

Wanda za a Ji Tsoro

(Mat 10.28-31)

4“Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi. 5Amma zan gaya muku wanda za ku ji tsoro. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku tsorata! 6Ashe, ba gwara biyar ne kobo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba. 7Kai! Ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”

Bayyana Yarda da Almasihu a gaban Mutane

(Mat 10.32-33; 12.32)

8“Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala'ikun Allah. 9Wanda kuwa ya yi mūsun sanina a gaban mutane, za a yi mūsun saninsa a gaban mala'ikun Allah. 10Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11Sa'ad da suka kai ku a gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa, 12domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”

Misali na Mai Arziki Marar Azanci

13Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan'uwana ya raba gādo da ni.” 14Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?” 15Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.” 16Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai. 17Sai ya ce a ransa, “‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.” 18Ya kuma ce, “‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. 19Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali na.” ” 20Amma Allah ya ce masa, “‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?” 21Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”

Damuwa da Alhini

(Mat 6.25-34)

22Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku, a game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura. 23Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!” 25Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? 26To, in ba za ku iya yin ƙaramin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa da sauran? 27Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 28To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle fa ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini. 30Ai, al'umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu. 31Ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.

Tara Dukiya a Sama

(Mat 6.19-21)

32“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku yana jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin. 33Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya mara yankewa ke nan a Sama, a inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta, 34don kuwa a inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Bayin da suke a Faɗake

35“Ku yi ɗamara, fitilunku suna kunne. 36Ku dai zama kamar mutane masu jiran Ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa. 37Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda Ubangijinsu da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sa'an nan ya bi ta kan kowannensu yana yi masa hidima. 38In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne. 39Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida. 40Ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.”

Amintaccen Bawa ko Marar Aminci

(Mat 24.45-51)

41Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?” 42Ubangiji ya ce, “Wane ne amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangidansa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 43Albarka tā tabbata ga bawan da, in ubangidansa ya dawo, zai samu yana yin haka. 44Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa. 45In kuwa bawan nan ya ce a ransa, “‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,” sa'an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa, 46ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a lokacin kuma da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da marasa riƙon amana. 47Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangidansa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin dūka, 48Wanda kuwa bai san ubangidansa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”

Yesu ya Kawo Rabuwa

(Mat 10.34-36)

49“Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru! 50Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita! 51Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A'a, ina gaya muku, sai dai rabuwa. 52Anan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku suna gāba da biyu, biyu kuma suna gāba da uku. 53Ta haka, za su rabu. Mahaifi yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da mahaifinsa, mahaifiya tana gāba da 'yarta, 'yar kuma tana gāba da mahaifiyarta, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da surukarta.”

Gane Yanayin Lokatai

(Mat 16.1-4; Mar 8.11-13)

54Ya kuma ce wa taron, “In kun ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, “‘Za a yi ruwa.” Sai kuwa a yi. 55In kuwa kun ga iskar kudu tana busowa, kukan ce, “‘Za a yi matsanancin zafi.” Sai kuwa a yi. 56Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”

Yi Jiyayya da Mai Ƙararka

(Mat 5.25-26)

57“Me ya sa ku da kanku ma ba kwa iya rarrabewa da abin da yake daidai? 58Misali, in kuna tafiya zuwa gaban shari'a da mai ƙararku, sai ka yi ƙoƙari ka yi jiyayya da shi tun a hanya, don kada ya ja ku zuwa gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa wa ɗan doka, ɗan doka kuma ya jefa ka a kurkuku. 59Ina gaya maka, lalle ba za ka fita ba, sai ka biya duka, ba sauran ko anini.”

13

Tuba ko Hallaka

1Anan take waɗansu da suke a wurin suke ba shi labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi na hadaya. 2Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawa zunubi ne, don sun sha wannan azaba? 3Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu. 4Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu.”

Misali na Ɓaure Marar 'Ya'ya

6Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba. 7Sai ya ce wa mai kula da garkar, “‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman 'ya'yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?” 8Sai ya amsa masa ya ce, “‘Ubangidana, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki. 9In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.”

Warkar da Tanƙwararriyar Mace a Ran Asabar

10Wata rana yana koyarwa a wata majami'a a ran Asabar, 11sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa. 12Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!” 13Sai ya ɗora mata hannu, a nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah. 14Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar a ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba a ran Asabar ba.” 15Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa a ran Asabar? 16Ashe, bai kamata matar nan 'yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?” 17Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al'ajabi da yake yi.

Misali na Ƙwayar Mastad

(Mat 13.31-32; Mar 4.30-32)

18Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi? 19Kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa, ta kuma girma ta zama itace, har tsuntsaye suka yi sheƙarsu a rassanta.”

Misali na Yisti

(Mat 13.33)

20Ya sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah? 21Kamar yisti yake wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya gama da yistin.”

Ƙunƙuntar Ƙofa

(Mat 7.13-14,21-23)

22Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima. 23Sai wani ya ce masa, “Ya Ubangiji, waɗanda za su sami ceto kam, kaɗan ne?” Sai ya ce musu, 24“Ku yi famar shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba su iya ba. 25In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, “‘Ya Ubangiji, buɗe mana,” sai ya amsa muku ya ce, “‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.” 26Sa'an nan za ku fara cewa, “‘Ai, mun ci mun sha a gabanka, har ka koyar a kan hanyoyinmu.” 27Shi kuwa sai ya ce, “‘Ina dai gaya muku, ku kam, ban san daga inda kuke ba. Ku tafi daga wurina, dukanku ku masu aikata mugunta!” 28Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon haƙora. 29Za a zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, a zauna cin abinci a Mulkin Allah. 30Ga shi fa, waɗansu da suke na ƙarshe za su zama na farko, waɗansu kuwa da suke na farko za su koma na ƙarshe.”

Yesu ya Ji Juyayin Urushalima

(Mat 23.37-39)

31Anan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.” 32Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, “‘Ka ga, a yau ina fitar da aljannu, ina warkarwa, a gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina. 33Duk da haka, lalle ne in ci gaba da tafiyata yau, da gobe, da kuma jibi, don kuwa bai dace a kashe annabi ba, in ba a Urushalima ba.”

34“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne nake so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 35Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! Ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai a ran da kuka ce, “‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.”

14

Warkar da Mai Ciwon Fara

1Wata rana Asabar, ya shiga gidan wani shugaba Farisiyawa garin cin abinci, mutane kuwa suna haƙwansa. 2Sai ga wani mai ciwon fara a gabansa. 3Yesu ya amsa ya ce wa masanan Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar a ran Asabar ko kuwa babu?” 4Sai suka yi shiru, Yesu kuwa ya riƙe shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi. 5Sa'an nan ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa a rijiya a ran Asabar, ba zai fitar da shi nan da nan ba?” 6Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.

Aya ga Waɗanda aka Gayyato Biki da Mai Gayyar

7To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce, 8“In an gayyace ka zuwa biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja, 9wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, “‘Ba mutumin nan wuri.” Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci. 10Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, “‘Aboki, hawo nan mana.” Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare. 11Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”

12Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanta kawai, ko 'yan'uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka. 13Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da masukai, da guragu, da makafi, 14za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka a ranar tashin masu adalci.”

Misali na Babban Biki

15Da jin haka, sai ɗaya daga cikin abokan cin abincin ya ce masa, “Albarka tā tabbata ga wanda zai ci abinci a Mulkin Allah.” 16Amma ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa. 17Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa ya ce wa waɗanda aka gayyata, “‘Ku zo, duk an shirya kome,” 18Sai dukansu baki ɗaya suka fara kawo hanzari. Na farko ya ce masa, “‘Na sayi gona, lalle ne in je in gano ta. Ina roƙonka ka ɗauke mini,” 19Sai wani ya ce, “‘Na sayi shanun noma guda goma, za ni in gwada su. Ina roƙonka ka ɗauke mini.” 20Wani kuma ya ce, “‘Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.” 21Bawan ya dawo ya ba ubangidansa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce wa bawansa, “‘Fita maza, ka bi hanyoyin birni da kwararo-kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.” 22Sai bawan ya ce, “‘Ya ubangida, abin da ka umarta duk an gama, amma har yanzu da sauran wuri.” 23Sai ubangidan biki ya ce wa bawan, “‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. 24Ina gaya muku, ba ko ɗaya daga cikin mutanen da na gayyata a dā da zai ɗanɗana bikina ba.”

Wuyar Zama Almajiri

25To, taro masu yawan gaske suna bin sa. Sai ya juya ya ce musu, 26“Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da mahaifinsa, da mahaifiyarsa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa maza da mata, har ma da ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28Misali, in wani daga cikinku yana son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin? 29Kada ya zamana bayan da ya sa harsashin ginin, yă kasa gamawa, har duk waɗanda suka gani, su fara yi masa ba'a, 30su riƙa cewa, “‘A! Ka ga mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa gamawa!”

31“Ko kuwa wane sarki ne, in za shi yaƙi da wani sarki, da fari ba ya zauna ya yi shawara, ya ga ko shi mai mutum dubu goma zai iya karawa da mai dubu ashirin ba? 32In kuwa ba zai iya ba, to, tun wancan yana nesa, sai ya aiki jakadu, su tambayo sharuɗan amana. 33Haka ma, kowannenku in bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.”

Sānannen Gishiri

(Mat 5.13; Mar 9.50)

34“Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? 35Ba shi da wani amfani a gona, ko a taki, sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji.”

15

Misali na Ɓatacciyar Tunkiya

(Mat 18.12-14)

1To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi. 2Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa. “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”

3Sai ya ba su wannan misali ya ce. 4“In waninku yana da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓata, har ya same ta ba? 5In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki. 6In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, “‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.” 7Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da a kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”

Misali na Ɓataccen Kuɗi

8“Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba? 9In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, “‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.” 10Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”

Misali na Ɓataccen Ɗa

11Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza. 12Sai ƙaramin ya ce wa mahaifinsa, “‘Baba, ba ni rabona na gādo.” Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa. 13Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a. 14Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara. 15Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade. 16Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu 17Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, “‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin mahaifina da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana! 18Zan tashi, in tafi gun mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. 19Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ” 20Sai ya tashi, ya taho wurin mahaifinsa. Amma tun yana daga nesa, sai mahaifinsa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa. 21Sai kuma ɗan ya ce masa, “‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.” 22Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, “‘Maza ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma, 23a kuma kawo kiwataccen ɗan maraƙin nan, a yanka, mu ci, mu yi murna. 24Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.” Sai suka yi ta farin ciki.

25“A sa'an nan kuwa, babban ɗansa yana gona. Yana dawowa, ya yi kusa da gida ke nan, sai ya ji ana kaɗe-kaɗe da raye-raye. 26Sai ya kira wani baran gidan, ya tambayi dalilin wannan abu. 27Shi kuwa ya ce masa, “‘Ai, ɗan'uwanka ne ya dawo, tsohonku ya yanka kiwataccen ɗan maraƙin nan saboda ya sadu da shi lafiya ƙalau.” 28Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Mahaifinsa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa. 29Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, “‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina. 30Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!” 31Sai mahaifin ya ce masa, “‘Ya ɗana, ai, kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne. 32Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.”

16

Misali na Wakili Marar Gaskiya

1Ya kuma ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki da yake da wakili. Sai aka sari wakilin a wurinsa a kan yana fallasar masa da dukiya. 2Sai ya kira shi ya ce masa, “‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.” 3Sai wakilin ya ce a ransa, “‘Ƙaƙa zan yi, da yake maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi, ba ni da ƙarfin noma, in yi roƙo kuwa, ina jin kunya. 4Yau wa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.” 5Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, “‘Nawa maigida yake bin ka?” 6Ya ce, “‘Garwa ɗari ta mai.” Sai ya ce masa, “‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,” 7Ya kuma ce wa wani, “‘Kai fa, nawa ake bin ka?” Sai ya ce, “‘Buhu ɗari na alkama.” Ya ce masa, “‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.” 8Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo. 9Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa'ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.

10“Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12In kuma ba ku yi aminci da kayan wani ba, wa zai ba ku halaliyarku? 13Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

Shari'a da Mulkin Allah

14Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki. 15Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.

16“Attaura da litattafin annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki. 17Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

(Mat 19.1-12; Mar 10.1-12)

18“Kowa ya saki matarsa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”

Mai Arziki da Li'azaru

19“An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana. 20An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne. 21Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa. 22Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa. 24Sai ya yi kira ya ce, “‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko da Li'azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.” 25Amma ibraham ya ce, “‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma a yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba. 26Banda wannan ma duka, a tsakaninmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda suke son ƙetarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro zuwa wurinmu daga can.” 27Sai mai arzikin ya ce, “‘To, ina roƙonka, Baba, ka aika shi zuwa gidan mahaifina, 28don ina da 'yan'uwa biyar maza, ya je ya yi musu gargaɗi, kada su ma su zo wurin azabar nan.” 29Amma Ibrahim ya ce, “‘Ai, suna da littattafan Musa da na annabawa, su saurare su mana.” 30Sai ya ce, “‘A'a, Baba Ibrahim, in dai wani daga cikin matattu ya je wurinsu sa tuba.” 31Ibrahim ya ce masa, “‘In dai har ba su saurari littattafan Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.”

17

Sanadodin Yin Zunubi

(Mat 18.6-7; 21-22; Mar 9.42)

1Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu! 2Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku. 3Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi. 4Ko ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, sa'an nan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, “‘Na tuba,” sai ka yafe shi.”

Ƙara Mana Bangaskiya

5Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.” 6Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, “‘Ka ciru, ka dasu a cikin teku,” sai kuwa ya bi umarninku.”

Wajibin Bawa

7“Misali, wane ne a cikinku in yana da bawa mai yi masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce, “‘Maza, zo ka zauna, ka ci abinci?” 8Ashe, ba ce masa zai yi, “‘Shirya mini jibi, ka kuma yi ɗamara, ka yi mini hidima, har in gama ci da sha, daga baya kai kuma ka ci ka sha,” ba? 9Yā gode wa bawan nan don ya bi umarni? 10Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, “‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibinmu kurum.”

Yesu ya Warkar da Kutare Goma

11Wata rana yana tafiya Urushalima, sai ya bi iyakar ƙasar Samariya da Galili. 12Yana shiga wani ƙauye ke nan, sai waɗansu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa. 13Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu,” 14Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka. 15Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi, 16ya fāɗi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne. 17Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran? 18Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah, sai baƙon nan kaɗai?” 19Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”

Bayyanar Mulkin Allah

(Mat 24.23-28; 36-41)

20Da Farisiyawa suka tambaye shi lokacin bayyanar Mulkin Allah, ya amsa musu ya ce, “Ai, bayyanar Mulkin Allah ba ganinta ake yi da ido ba. 21Ba kuwa za a ce, “‘A! Ga shi nan,” ko kuwa, “‘Ga shi can,” ba. Ai, Mulkin Allah a tsakaninku yake.”

22Ya kuma ce wa almajiran, “Lokaci yana zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. 23Za su ce muku, “‘A! ga shi nan,” ko kuwa, “‘Ga shi can!” Kada ku je, kada ku bi su. 24Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, haka ma, Ɗan Mutum zai zama a ranar bayyanarsa. 25Amma lalle sai ya sha wuya iri iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi. 26Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Ɗan Mutum. 27Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka. 28Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine, 29amma a ranar da Lutu ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka. 30Haka kuma zai zama a ranar bayyanar Ɗan Mutum. 31A ran nan fa wanda yake a kan soro, kayansa kuma suna a cikin gida, kada ya sauko garin ɗaukarsu. Haka kuma wanda yake gona, kada ya juyo. 32Ku tuna fa da matar Lutu. 33Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi. 34Ina gaya muku, a wannan dare za a ga mutum biyu a gado ɗaya, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 35Za a ga mata biyu suna niƙa tare, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.[ 36Za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.”] 37Sai suka amsa suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “A inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.”

18

Misali na wadda Mijinta ya Mutu da Alƙali

1Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai. 2Ya ce, “A wani gari an yi wani alƙali marar tsoron Allah, marar kula da mutane. 3A garin nan kuwa da wata gwauruwa, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, “‘Ka shiga a tsakanina da abokin gābana.” 4Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, “‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane, 5amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.” 6Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa! 7Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne? 8Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”

Misali na Bafarisiye da Mai Karɓar Haraji

9Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, cewa su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce, 10“Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu'a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji. 11Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, “‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan. 12Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.” 13Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, “‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!” 14Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”

Yesu ya sa wa 'Yan Yara Albarka

(Mat 19.13-15; Mar 10.13-16)

15Waɗansu suka kawo masa 'yan yaransu, domin ya taɓa su. Ganin haka, sai almajiransa suka kwaɓe su. 16Amma Yesu ya kira 'yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne. 17Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

Shugaban Jama'a Mai Arziki

(Mat 19.16-30; Mar 10.17-31)

18Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?” 19Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci, sai Allah kaɗai. 20Kā dai san umarnan nan, “‘Kada ka yi zina. Kada ka yi kisankai. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.” 21Sai ya ce, “Ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.” 22Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.” 23Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske. 24Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah! 25Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?” 27Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”

28Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.” 29Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda Mulkin Allah, 30sa'an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”

Yesu ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

(Mat 20.17-19; Mar 10.32-34)

31Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake a rubuce kuma a game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata. 32Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau. 33Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.” 34Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.

Warkar da Makaho Mai Bara a kusa da Yariko

(Mat 20.29-34; Mar 10.46-52)

35Da ya kusato Yariko, ga wani makaho a zaune a gefen hanya, yana bara. 36Da ya ji taro yana wucewa, sai ya tambaya ko mene ne. 37Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.” 38Sai ya ɗaga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 39Sai waɗanda suke a gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 40Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi, 41“Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!” 42Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43Anan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

19

Yesu da Zakka

1Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin, 2sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma, 3ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne. 4Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi. 5Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.” 6Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna. 7Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!” 8Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.” 9Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da yake shi ma ɗan Ibrahim ne. 10Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”

Misali na Fam Goma

11Da suka ji abubuwan nan, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, gama yana kusa da Urushalima, suna kuma tsammani Mulkin Allah zai bayyana nan da nan. 12Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo. 13Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda guda, ya kuma ce musu, “‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.” 14Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu. 15Ana nan, da ya samo sarantar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribar da suka ci a wajen jujjuyawar. 16Sai na farko ya zo a gabansa, ya ce, “‘Ya ubangida, fam ɗinka ya jawo fam goma.” 17Sai shi kuma ya ce masa, “‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.” 18Sai na biyun ya zo, ya ce, “‘Ya ubangida, fam ɗinka ya jawo fam biyar.” 19Shi kuma ya ce masa, “‘Kai ma na ba ka mulkin gari biyar.” 20Wani kuma ya zo, ya ce, “‘Ya ubangida, ga fam ɗinka nan! Dā ma a mayani na ƙulle shi, na ajiye. 21Domin ina tsoronka, don kai mutum ne mai tsanani, son banza a gare ka, kakan girbi abin da ba kai ka shuka ba.” 22Sai ya ce masa “‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba? 23To, in haka ne, don me ba ka ajiye kuɗin nawa a banki ba, da dawowata in ƙarɓa, har da riba?” 24Sai ya ce wa na tsaitsaye a wurin, “‘Ku karɓe fam ɗin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.” 25Suka ce masa, “‘Ya Ubangiji, ai, yana da fam goma.” 26“‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai a karɓe masa. 27Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.”

Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu

(Mat 21.1-11; Mar 11.1-11; Yah 12.12-19)

28Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima. 29Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu, 30ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake a gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 31Kowa ya tambaye ku, “‘Don me kuke kwance shi?” ku ce, “‘Ubangiji ne yake bukatarsa.” 32Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu. 33Suna a cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?” 34Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.” 35Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu. 36Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya. 37Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani. 38Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!” 39Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Malam, ka kwaɓi almajirinka mana!” 40Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”

41Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka, 42ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku. 43Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe, 44su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”

Yesu ya Tsabtace Haikali

(Mat 21.12-17; Mar 11.15-19; Yah 12.13-22)

45Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa, 46ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, “‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu'a.” Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”

47Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi. 48Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.

20

Ana Shakkar Izinin Yesu

(Mat 21.23-27; Mar 11.27-33)

1Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso, 2suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?” 3Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini, 4baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” 5Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, “‘Daga Sama take,” sai ya ce, “‘To, don me ba ku gaskata shi ba?” 6In kuwa muka ce, “‘Ta mutum ce,” sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.” 7Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba. 8Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

Misali na Manoman da suka Yi Ijarar Garkar Inabi

(Mat 21.33-46; Mar 12.1-12)

9Sai ya shiga ba jama'a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe. 10Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi. 11Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu wofi. 12Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi. 13Sai mai garkar ya ce, “‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.” 14Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, “‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.” 15Sai suka jefa shi a bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangidan garkar nan zai yi da su? 16Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!” 17Amma ya dube su, ya ce, “Wannan da yake a rubuce fa cewa, “‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini?” 18Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje, amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

Biyan Haraji ga Kaisar

(Mat 22.15-22; Mar 12.13-17)

19Anan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama'a. 20Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi. 21Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. 22Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?” 23Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu, 24“Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.” 25Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” 26Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana a gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.

Tambaya a kan Tashin Matattu

(Mat 22.23-33; Mar 12.18-27)

27Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu), 28suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya. 29To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba. 30Na biyun, 31da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa. 32Daga baya kuma ita matar ta mutu. 33To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”

34Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa. 35Amma waɗanda aka ga sun cancanci samun shiga wancan zamani da kuma tashin nan daga matattu, ba za su yi aure ko aurarwa ba. 36Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala'iku, 'ya'yan Allah ne kuwa, da yake 'ya'yan tashin matattu ne. 37A game da tashin matattu kuwa, ai, Musa ma ya faɗa, a labarin kurmin, a inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, da Allahn ishaku, da Allahn Yakubu. 38Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.” 39Sai waɗansu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Malam, ka faɗi daidai.” 40Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

(Mat 22.41-46; Mar 12.35-37)

41Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne? 42Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a damana, 43Sai na sa ka take maƙiyanka.” ” 44Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

Yesu ya Fallashi Malaman Attaura

(Mat 23.1-36; Mar 12.38-40; Luka 11.37-54)

45Ya ce wa almajiransa a gaban dukan jama'a, 46“Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki. 47Su ne masu cin kayan gwauraye mata, masu yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

21

Sadaka wadda aka Saka

(Mar 12.41-44)

1Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali. 2Sai ya ga wata matalauciya gwauruwa ta saka rabin kobo biyu a ciki. 3Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da matalauciyar gwauruwar nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka. 4Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”

Yesu ya Faɗi irin Rushewar da za ta Sami Haikali

(Mat 24.1-2; Mar 13.1-2)

5Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce, 6“In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan'uwansa da ba a baje shi ba.”

Alamu da Tsanance-tsanance

(Mat 24.3-14; Mar 13.3-13)

7Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?” 8Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, “‘Lokaci ya yi kusa.” To, kada ku bi su. 9In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”

10Sa'an nan ya ce musu, “Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. 11Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al'amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama. 12Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami'u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana. 13Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida. 14Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba. 15Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba. 16Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku. 17Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. 18Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo. 19Jurewarku ce za ta fisshe ku.”

Yesu ya Faɗi irin Ribɗewa da za ta Sami Urushalima

(Mat 24.15-28; Mar 13.14-23)

20“Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta. 21Sa'an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni. 22Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake a rubuce. 23Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama'ar nan. 24Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”

Komowar Ɗan Mutum

(Mat 24.29-31; Mar 13.24-27)

25“Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al'ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa. 26Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al'amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 27A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa. 28Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

(Mat 24.32-35; Mar 13.28-31)

29Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa, 30da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan. 31Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan al'amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato. 32Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku. 33Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Gargaɗi a Zauna a Faɗake

34“Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranar nan ta mamaye ku kamar tarko. 35Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa. 36Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”

37Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun. 38Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.

22

An Ƙulla Shawara gāba da Yesu

(Mat 26.1-5,14-16; Mar 14.1-2,10-11; Yah 11.45-53)

1To, idin abinci marar yisti, wanda ake ce da shi Idin Ƙetarewa, ya gabato. 2Sai manyan firistoci da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama'a.

3Sai Shaiɗan ya shiga a cikin Yahuza, wanda ake kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan. 4Sai ya tafi ya yi shawara da manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali a kan yadda zai bāshe shi a gare su. 5Sai suka yi murna, suka kuma yi alkawarin ba shi kuɗi. 6Shi kuwa ya yarda, ya kuma nemi hanyar bāshe shi a gare su a bayan idon jama'a.

Yesu ya Ci Jibin Ƙetarewa tare da Almajiransa

(Mat 26.17-25; Mar 14.12-21; Yah 13.21-30)

7Sai rana idin abinci marar yisti ta zo, wato, rana da ake yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa. 8Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.” 9Suka ce masa, “A ina kake so mu shirya?” 10Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum a ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga. 11Ku ce wa maigidan, “‘Malam ya ce, ina masaukin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?” 12Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.” 13Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

Cin Jibin Ubangiji

(Mat 26.26-30; Mar 14.22-26; 1 Kor 11.23-26)

14Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi. 15Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya. 16Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.” 17Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha. 18Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.” 19Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.” 20Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku. 21Amma ga shi, mai bāshe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni. 22Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!” 23Sai suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka. 22.24 Mūsu a kan Ko wane ne Babba Mūsu a kan Ko wane ne Babba

24Sai mūsu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu. 25Sai ya ce musu, “Sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, mahukuntansu kuma sukan nema a ce da su, “‘Mataimakan jama'a.” 26Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima. 27Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.

28“Ku ne kuka tsaya a gare ni a gwaje-gwajen da na sha. 29Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko, 30ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila. 22.31 Bitrus zai yi Mūsun Sanin Yesu Bitrus zai yi Mūsun Sanin Yesu

(Mat 26.31-35; Mar 14.27-31; Yah 13.36-38)

31“Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu. 32Ni kuwa na yi maka addu'a, kada bangaskiyarka ta kāsa. Kai kuma, bayan da ka juyo, sai ka ƙarfafa 'yan'uwanka.” 33Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye nake in bi ka har cikin kurkuku, ko kuma Lahira.” 34Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”

Jakar Kuɗi, Burgami da Takobi

35Ya kuma ce musu, “Sa'ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.” 36Ya ce musu, “Amma a yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sayar da mayafinsa ya saya. 37Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, “‘An lasafta shi a cikin masu laifi.” Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.” 38Sai suka ce, “Ya Ubangiji, ai ga takuba biyu.” Ya ce musu, “Ya isa.”

Yesu ya yi Addu'a a Gatsemani

(Mat 26.36-46; Mar 14.32-42)

39Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba yi. Almajiransa kuwa suka bi shi. 40Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.” 41Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu'a. 42Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi”[ 43Sai wani mala'ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi. 44Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.] 45Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki. 46Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”

An Ba da Yesu, an Kama Shi

(Mat 26.47-56; Mar 14.43-50; Yah 18.2-11)

47Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama'a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake yi musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi. 48Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?” 49Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?” 50Sai ɗayansu ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. 51Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi. 52Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi? 53Sa'ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.” 22.54 Bitrus ya yi Mūsun Sanin Yesu Bitrus ya yi Mūsun Sanin Yesu

(Mat 26.57-58,69-75; Mar 14.53-54,66-72; Yah 18.12-18,25-27)

54Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi a cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa. 55Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu. 56Sai wata baranya ta gan shi a zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai, mutumin nan ma, tare da shi yake.” 57Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.” 58Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.” 59Bayan wajen sa'a guda sai wani ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi yake, don Bagalile ne.” 60Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Anan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara. 61Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.” 62Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

An Yi wa Yesu Ba'a, an Duke Shi

(Mat 26.67-68; Mar 14.65)

63Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi tayi masa ba'a, suna dūkansa. 64Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?” 65Suka kuma yi tayi masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.

Yesu a gaban 'Yan Majalisa

(Mat 26.59-66; Mar 14.55-64; Yah 18.19-24)

66Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama'a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce, 67“To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba. 68In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba. 69Amma a nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna a dama na Allah Mai iko.” 70Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.” 71Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”

23

Yesu a gaban Bilatus

(Mat 27.1-2,11-14; Mar 15.1-5; Yah 18.28-38)

1Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi a gaban Bilatus. 2Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.” 3Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.” 4Bilatus ya ce wa manyan firistoci da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.” 5Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama'a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”

Yesu a gaban Hirudus

6Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne. 7Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin. 8Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu'ujiza da Yesu zai yi. 9Sai ya yi tayi masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba. 10Manyan firistoci da malaman Attaura suna nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun. 11Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus. 12A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.

An Hukunta wa Yesu Mutuwa

(Mat 27.15-26; Mar 15.6-15; Yah 18.39ū19.16)

13Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama'a, 14ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, cewa yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba. 15Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba. 16Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”[ 17A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]

18Amma duk suka ɗauki ihu gaba ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakar mana Barabbas!” 19(Barabbas shi ne wani mutum da aka jefa a kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai.) 20Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, don yana so ya saki Yesu. 21Amma suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” 22Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.” 23Amma suka yi ta matsa lamba, suna ɗaga murya, suna cewa a gicciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye. 24Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata. 25Ya kuwa sakar musu wanda suka roƙa, wato, wanda aka jefa a kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu, su yi masa abin da suke so.

An Gicciye Yesu

(Mat 27.32-44; Mar 15.21-32; Yah 19.17-27)

26Suna tafiya da Yesu ke nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu. 27Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da waɗansu mata da suke kuka, suke kuma gunji saboda shi. 28Amma Yesu ya juya zuwa gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma 'ya'yanku, 29don lokaci yana zuwa da za ku ce, “‘Albarka tā tabbata ga matar bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.” 30Sa'an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, “‘Ku faɗo a kanmu,” su kuma ce da tsaunuka, “‘Ku binne mu.” 31In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”

32Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi. 33Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, a nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun. 34Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kari'a a kansu. 35Mutane da suke a tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!” 36Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami, 37suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!” 38Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”

39Sai ɗaya daga cikin masu laifin, da aka gicciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin, ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanku mana, duk da mu!” 40Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsaron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa? 41Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.” 42Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, a sa'ad da ka shiga sarautarka.” 43Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”

Mutuwar Yesu

(Mat 27.45-56; Mar 15.33-41; Yah 19.28-30)

44To, a wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 45Hasken rana ya dushe. Labulen da yake a cikin Haikali ya tsage gida biyu. 46Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika. 47Sa'ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!” 48Sa'ad da duk taro masu yawa, waɗanda suka zo kallo suka ga abin da ya faru, suka koma, suna bugun ƙirjinsu. 49Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.

Jana'izar Yesu

(Mat 27.57-61; Mar 15.42-47; Yah 19.38-42)

50To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Arimatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗan majalisa ne, nagari ne, adali kuma. 51Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah. 52Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 53Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 54Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso. 55Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa. 56Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa. Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.

24

Tashin Yesu daga Matattu

(Mat 28.1-10; Mar 16.1-8; Yah 20.1-10)

1A ranar farko ta mako kuwa, da asussuba, suka je wurin kabarin da kayan ƙanshi da suka shirya. 2Sai suka tarar an mirgine dutsen daga kabarin. 3Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji ba. 4Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye a kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali. 5Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu a ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu? 6Ai, ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili 7cewa, “‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi.” 8Sai suka tuna da maganarsa. 9Da suka dawo daga kabarin suka shaida wa goma sha ɗayan nan, da kuma duk sauransu, dukan waɗannan abubuwa. 10To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa. 11Su kuwa sai maganar nan ta zama musu kamar zance ne kawai, suka ƙi gaskatawa. 12Amma Bitrus ya tashi, ya doshi kabarin da gudu. Ya duƙa, ya leƙa a ciki, ya ga likkafanin lilin a ajiye a waje ɗaya. Sai ya koma gida yana al'ajabin abin da ya auku.

Almajirai Biyu a Hanyar Imuwasu

(Mar 16.12-13)

13A ran nan kuma sai ga waɗansu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imuwasu, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne. 14Suna ta zance da juna a kan dukan al'amuran da suka faru. 15Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare. 16Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba. 17Yesu ya ce musu, “Wace magana ce kuke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna baƙin ciki. 18Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a 'yan kwanakin nan ba?” 19Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “A game da Yesu Banazare ne, wanda yake annabi mai manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana a gaban Allah da dukan mutane, 20da kuma yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa gicciye shi. 21Dā kuwa muna bege shi ne zai fanshi Isra'ila. Hakika kuma, bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abu. 22Har wa yau kuma, waɗansu mata na cikinmu, sun ba mu al'ajabi. Don sun je kabarin da sassafe, 23da ba su sami jikinsa ba, suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi, sun ga mala'ikun da suka ce yana da rai. 24Waɗansunsu da suke tare da mu kuma, suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.” 25Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa! 26Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?” 27Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.

28Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba, 29suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurinmu, ai, magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu. 30Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su. 31Idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu. 32Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba, sa'ad da yake a hanya, yana bayyana mana Littattafai?”

33Anan take, suka tashi suka koma Urushalima, suka sami sha ɗayan nan tare gu ɗaya, da kuma waɗanda suke tare da su, 34suna cewa, “Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!” 35Su kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi a wajen gutsura gurasa.

Yesu ya Bayyana ga Almajiransa

(Mat 28.16-20; Mar 16.14-18; Yah 20.19-23; A. M. 1.6-8)

36Suna a cikin faɗar waɗannan abubuwa, sai ga Yesu da kansa a tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama a gare ku!” 37Amma suka firgita, tsoro ya kama su, suka zaci fatalwa suke gani. 38Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku? 39Ku dubi hannuwana da ƙafafuna, ai, ni ne da kaina. Ku taɓa ni, ku ji, don fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.” 40Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa. 41Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?” 42Sai suka ba shi wata tsokar gasasshen kifi. 43Ya kuwa karɓa, ya ci a gabansu.

44Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake a rubuce, a game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.” 45Sa'an nan ya wayar da hankalinsu su fahimci Littattafai, 46ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu, 47a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya alkawarta. Amma ku dakata a birni tukuna, har a yi muku baiwar iko daga Sama.”

An Ɗauke Yesu zuwa Sama

(Mar 16.19-20; A. M. 1.9-11)

50Sai ya kai su a waje har jikin Betanya. Ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka. 51Yana sa musu albarka ke nan, sai ya rabu da su, aka ɗauke shi zuwa sama. 52Su kuwa suka yi masa sujada, suka koma Urushalima, suna matuƙar farin ciki. 53Ko yaushe kuma suna a Haikali suna yabon Allah.