Malachi

Malakai

1

Ubangiji yana Ƙaunar Yakubu

1Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya ba Malakai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila.

2Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunarku.” Amma ku kuka amsa kuka ce, “Ta yaya kake ƙaunarmu?” Ubangiji ya amsa, ya ce, “Ashe, Isuwa da Yakubu ba 'yan'uwan juna ba ne? Amma zuriyar Yakubu nake ƙauna. 3Na ƙi Isuwa da zuriyarsa, na hallaka ƙasarsa ta kan tudu, wurin zamansa kuwa na ba namomin jeji.”

4Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.” Sa'an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, Ƙasar mugaye, da al'ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.”

5“Da idanunku za ku ga wannan, za ku kuwa ce, Allah mai girma ne yake a ƙasar da ba ta Isra'ila ba ce!”

Ubangiji ya Tsauta wa Firistoci

6Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, “‘Ƙaƙa muka raina ka?” 7Yadda kuka yi ke nan. Kun miƙa haramtacciyar hadaya ta abinci a kan bagadena, sa'an nan kuna cewa, “‘Ta ƙaƙa muka raina ka?” To, zan faɗa muku, don kun ƙazantar da bagadena. 8Sa'ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa'ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

9To, firistoci ku gwada, ku roƙi Allah domin ya yi mana alheri. Ai, ba zai amsa addu'arku ba, wannan kuwa laifinku ne. Ubangiji Mai Runduna ya faɗa. 10“Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna. 11“Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna. 12“Amma ku kun raina ni da yake kuka ce bagadena ba kome ba ne, kuna raina abincin da kuke ajiyewa a kai. 13Kuka kuma ce, “‘Mun gaji da wannan irin abu fa!” Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku? 14La'ananne ne macucin da yake da lafiyayyun dabbobi da ya alkawarta zai ba ni daga cikin garkensa ya kuwa miƙa mini hadaya ta haramtacciyar dabba. Gama ni babban Sarki ne, dukan al'ummai kuwa suna jin tsoron sunana, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

2

1“Yanzu firistoci, ga umarni dominku. 2Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 3Ga shi, zan tsauta wa 'ya 'yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa'an nan zan kore ku daga gabana. 4Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

5“Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai. 6Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta. 7Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.

8“Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 9Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”

Rashin Amincin Isra'ilawa

10Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu? 11Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra'ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka. 12Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna.

13Ga kuma abin da kuke yi. Kuna cika bagaden Ubangiji da hawaye, da kuka, da kururuwa domin ba zai ƙara karɓar hadayun da kuke kawo masa ba. 14Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka. 15Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so 'ya'yanmu su zama 'yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.

16“Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce ina ƙin kisan aure, ina ƙinsa sa'ad da waninku ya yi wa matarsa hakanan. Domin haka sai ku kula da kanku kada ku keta alkawari, mutum ya zama mai aminci ga matarsa.”

Ranar Hukunci ta Gabato

17Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”

3

1A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”

2Amma wa zai iya jurewa da ranar zuwansa? Wa kuma zai tsira sa'ad da ya bayyana? Zai zama kamar wutar da take narka ƙarfe, kamar kuma sabulu salo. 3Zai zo ya yi hukunci kamar wanda yake tace azurfa, ya tsarkake ta. Zai tsarkake firistoci, ya tace su kamar yadda ake yi wa azurfa da zinariya. A sa'an nan ne za su kawo wa Ubangiji hadayun da suka dace. 4Sa'an nan kuma Ubangiji zai yarda da hadayun mutanen Yahuza da na Urushalima kamar yadda yake a zamanin dā.

5Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”

Ba da Zaka

6“Ni ne Ubangiji, ba na sākewa, domin haka ku zuriyar Yakubu, ba ku ƙāre ɗungum ba. 7Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, “‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?” 8Mutum zai iya zambatar Allah? Amma ku kuna zambatata, kuna kuwa cewa, “‘Ta ƙaƙa muka zambace ka?” A wajen al'amarin zaka da hadayu, kuke zambatata. 9Dukanku la'antattu ne gama al'ummar duka zamba take yi mini! 10Ku kawo dukkan zaka a ɗakin ajiyata domin abinci ya samu a cikin Haikalina. Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske. 11Ba zan bar ƙwari su lalatar da amfanin gonaki ba. Kurangar inabinku za ta cika da 'ya'ya, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 12Sa'an nan jama'ar dukan al'ummai za su ce ku masu farin ciki ne, gama ƙasarku za ta yi daɗin zama.”

Bambancin Adalai da Mugaye

13“Kun faɗi mugun abu a kaina,” in ji Ubangiji, “Amma kun ce, “‘Me muka ce a kanka?” 14Kun ce, “‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna. 15A ganinmu masu girmankai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suke yi ba, amma sukan jarraba Allah da mugayen ayyukansu su kuwa zauna lafiya.”

16Sa'an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi. 17“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, za su zama mutanena na ainihi, a ranar da na aikata. Zan ji ƙansu kamar yadda mahaifi yakan ji ƙan ɗansa wanda yake masa hidima. 18Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”