Matthew
(Luka 3.23-38)
1Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.
2Ibraham ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuza da 'yan'uwansa, 3Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (mahaifiyarsu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram, 4Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, 5Salmon ya haifi Bo'aza (mahaifiyarsa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse, 6Yesse ya haifi sarki Dawuda. Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda mahaifiyarsa dā matar Uriya ce), 7Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa, 8Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Azariya, 9Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya, 10Hezekiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya. 11Yosiya ya haifi Yekoniya da 'yan'uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.
12Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel, 13Zarubabel ya haifi Abihudu, Abihudu ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azuro, 14Azuro ya haifi Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu, 15Aliyudu ya haifi Ele'azara, Ele'azara ya haifi Matana, Matana ya haifi Yakubu, 16Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.
17Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.
(Luka 2.1-7)
18Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki. 19Yusufu mijinta kuwa da yake shi mutumin kirki ne, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama'a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce. 20Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne. 21Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,
23“Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, Za a kuma sa masa suna Immanuwel.”
(Ma'anar Immanuwel kuwa itace Allah yana tare da mu.) 24Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala'ikan Ubangiji, ya ɗauki matarsa, 25amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.
1Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, 2“Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.” 3Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. 4Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama'a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu. 5Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,
6“‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.”
7Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana. 8Sa'an nan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” 9Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan yake. 10Da suka ga tauraron sai suka yi matuƙar farin ciki. 11Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da mahaifiyarsa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwa tare da zinariya, da lubban, da mur. 12Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
13Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.” 14Yusufu kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa da daddare, ya tafi Masar, 15ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”
16Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan. 17A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa,
18“An ji wata murya a Rama, Ta kuka da baƙin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta. Ba za ta ta'azantu ba, don ba su.”
19Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce, 20“Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi ƙasar Isra'ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.” 21Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ya zo ƙasar Isra'ila. 22Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili. 23Sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”
(Mar 1.1-8; Luka 3.1-9; Yah 1.19-28)
1A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya, 2yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.” 3Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar mai kira a jeji yana cewa, “‘Ku shirya wa Ubangiji tafarki, Ku miƙe hanyoyinsa.”
4Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma. 5Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa, 6yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.
7Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi aikin da zai nuna tubarku. 9Kada kuwa ku ɗauka a ranku cewa, Ibrahim ne ubanku, domin ina gaya muku, Allah yana da ikon ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan. 10Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.
11“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 12Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar bituwa.”
(Mar 1.9-11; Luka 3.12-22)
13A lokacin nan ne Yesu ya zo daga ƙasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. 14Yahaya kuwa ya so ya hana shi, ya ce, “Ni da nake bukatar kai ka yi mini baftisma, ka zo gare ni?” 15Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa. 16Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan da ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dāre, ya ga Ruhun Allah yana saukowa da kamar kurciya, har ya sauka a kansa. 17Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.”
(Mar 1.12-13; Luka 4.1-13)
1Sa'an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi. 2Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi. 3Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” 4Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, “‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba, Sai dai da kowace maganar da ke fitowa daga wurin Allah.”
5Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, 6ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa, “‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,” da kuma “‘Za su tallafe ka, Don kada ka buga kafarka a dutse.”
7Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, “‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.” 8Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu. 9Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.” 10Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! Domin a rubuce yake cewa, “‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.”
11Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.
(Mar 1.14-15; Luka 4.14-15)
12To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili. 13Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali, 14domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,
15“Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali, Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun, Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,
16Mazaunan duhu sun ga babban haske, Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta, Haske ya keto musu.”
17Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”
(Mar 1.16-20; Luka 5.1-11)
18Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne. 19Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” 20Nan da nan, sai suka bar tarunsu, suka bi shi. 21Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su. 22Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.
(Luka 6.17-19)
23Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane. 24Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. 25Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.
(Mat 5ū7)
1Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa. 2Sai ya buɗe baki ya koya musu.
(Luka 6.20-23)
3“Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.
4“Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.
5“Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.
6“Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.
7“Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.
8“Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.
9“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.
10“Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.
11“Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni. 12Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”
(Mar 9.50; Luka 14.34-35)
13“Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.
14“Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa. 15Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske. 16To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”
17“Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in ciccika su. 18Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome. 19Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama. 20Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”
(Luka 12.57-59)
21“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, “‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.” 22Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, “‘Kai wofi!” Hakkinsa shiga Gidan Wuta. 23Saboda haka, in kana cikin miƙa hadayarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan'uwanka yana da wata magana game da kai, 24sai ka dakatar da hadayarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa hadayarka. 25Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku. 26Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini a kanka.”
27“Kun dai ji an faɗa, “‘Kada ka yi zina.” 28Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha'awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita. 29In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta. 30In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”
(Mat 19.9; Mar 10.11-12; Luka 16.18)
31“An kuma ce, “‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.” 32Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”
33“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, “‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa'adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.” 34Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah, 35ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki. 36Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba. 37Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan “‘I” ko “‘A'a” kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”
(Luka 6.29-30)
38“Kun dai ji an faɗa, “‘Sakayyar ido, ido ce, sakayyar haƙori kuma haƙori ce.” 39Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. 40In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma. 41In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma. 42Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”
(Luka 6.27-28,32-36)
43“Kun dai ji an faɗa, “‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.” 44Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a, 45domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci. 46In masoyanku kawai kuke ƙauna, wace lada ce da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba? 48Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama yake cikakke.”
1“Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.
2“Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma a kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan. 3Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi, 4domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”
(Luka 11.2-4)
5“In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanyoyi don dai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu. 6Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanka wanda yake ɓoye, Ubanka kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.
7“In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu. 8Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi. 9Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka, “‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama, A kiyaye sunanka da tsarki.
10Mulkinka yă zo, A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.
11Ka ba mu abincinmu na yau.
12Ka gafarta mana laifofinmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.
13Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.”
14Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku. 15In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”
16“In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, don dai mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan. 17Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska, 18don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”
(Luka 12.33-34)
19“Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma ke fasawa suke yi sata. 20Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa su yi sata. 21Domin kuwa inda dukiyarka take, a can zuciyarka ma take.”
(Luka 11.34-36)
22“Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske. 23In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”
(Luka 16.13)
24“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”
(Luka 12.22-31)
25“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba? 26Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama yana ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba? 27Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa? 28To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, 29duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 30To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a wuta, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 31Don haka kada ku damu, cewa, “‘Me za mu ci?” ko, “‘Me za mu sha?” ko kuwa, “‘Me za mu sa?” 32Ai, al'ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka. 33Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.
34“Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Dawainiyar yau ma ta isa, wahala.”
(Luka 6.37-38,41-42)
1“Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku. 2Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku. 3Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba? 4Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanku, “‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,” alhali kuwa da gungume naka ido? 5Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.
6“Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”
(Luka 11.9-13)
7“Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku. 8Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa. 9To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse? 10Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? 11To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa? 12Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”
(Luka 13.24)
13“Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa. 14Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”
(Luka 6.43-44)
15“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa. 16Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan 'ya'ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. 18Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan 'ya'ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan 'ya'ya. 19Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. 20Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”
(Luka 13.25-27)
21“Ba duk mai ce mini, “‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,” ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so. 22A ranar nan da yawa za su ce mini, “‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?” 23Sa'an nan zan ce musu, “‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.”
(Luka 6.47-49)
24“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā. 25Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne. 26Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi. 27Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”
(Mar 1.22)
28Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, 29domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.
(Mar 1.40-45; Luka 5.12-16)
1Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi. 2Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” 3Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke. 4Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”
(Luka 7.1-10)
5Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi, 6ya ce, “Ya Ubangiji, yarona yana kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.” 7Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.” 8Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke. 9Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, “‘Je ka,” sai ya je, wani kuwa in ce masa, “‘Zo,” sai ya zo, in ce wa bawana, “‘Yi abu kaza,” sai ya yi.” 10Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba. 11Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin Sama, 12'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.” 13Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.
(Mar 1.29-31; Luka 4.38-39)
14Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzaɓi. 15Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.
(Mar 1.32-34; Luka 4.40-41)
16Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”
(Luka 9.57-62)
18To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan hayi. 19Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” 20Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.” 21Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.” 22Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu.”
(Mar 4.35-41; Luka 8.22-25)
23Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. 24Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci. 25Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” 26Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit! 27Mutanen suka yi al'ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”
(Mar 5.1-20; Luka 8.26-39)
28Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya. 29Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” 30Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken aladu suna kiwo. 31Sai aljannun suka roƙe shi, suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” 32Ya ce musu, “To, ku je.” Sai suka fita, suka shiga aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka hallaka a ruwa. 33Masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun. 34Sai ga duk jama'ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.
(Mar 2.1-12; Luka 5.17-26)
1Da ya shiga jirgi, ya haye ya je garinsu. 2Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.” 3Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!” 4Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? 5Wanne ya fi sauƙi, a ce, “‘An gafarta maka zunubanka,” ko kuwa a ce, “‘Tashi ka yi tafiya?” 6Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya”ūsai ya ce wa shanyayyenū“Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.” 7Shi kuwa ya tashi ya tafi gida. 8Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.
(Mar 2.13-17; Luka 5.27-32)
9Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
10Sa'ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. 11Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 12Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. 13Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, “‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.” Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”
(Mar 2.18-22; Luka 5.33-39)
14Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, “Don me mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma naka almajiran ba sa yi?” 15Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi. 16Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa. 17Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”
(Mar 5.21-43; Luka 8.40-56)
18Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama'a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu 'yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.” 19Sai Yesu ya tashi, ya bi shi tare da almajiransa. 20Ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa, 21domin ta ce a ranta, “Ko da mayafinsa ma na taɓa, sai in warke.” 22Sai Yesu ya juya, yā gan ta, ya ce, “'Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.
23Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya, 24sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini. 25Amma da aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi. 26Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.
27Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka yi mana jinƙai.” 28Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!” 29Sa'an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.” 30Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.” 31Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk ƙasar.
32Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan. 33Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba.” 34Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”
35Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi. 37Sai ya ce wa almajiransa, “Girbin yana da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. 38Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin ya turo masu girbi, su yi masa girbi.”
(Mar 3.13-19; Luka 6.12-16)
1Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, 3da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, 4da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
(Mar 6.7-13; Luka 9.1-6)
5Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila, 7kuna wa'azi, kuna cewa, “‘Mulkin Sama ya kusato.” 8Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta. 9Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku, 10kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa. 11Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi. 12In za ku shiga gidan ku ce, “‘Salama a gare ku.” 13In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku. 14Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku. 15Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”
(Mar 13.9-13; Luka 12.11-12; Luka 21.12-19)
16“Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi. 17Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu. 18Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma. 19A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin. 20Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21'Dan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su. 22Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai sami ceto. 23In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.
24“Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa. 25Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”
(Luka 12.2-7)
26“Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta. 29Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. 30Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. 31Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
(Luka 12.8-9)
32“Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da ke cikin Sama. 33Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubana da yake cikin Sama.”
(Luka 12.51-53; 14.26-27)
34“Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A'a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35Domin na zo ne in haɗa mutum da mahaifinsa gāba, 'ya da mahaifiyarta, matar ɗa kuma da surukarta. 36Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37Wanda duk ya fi son mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”
(Mar 9.41)
40“Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni. 41Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali. 42Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”
(Luka 7.18-35)
1Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.
2To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa, 3su ce masa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 4Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji, da abin da kuka gani. 5Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara. 6Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”
7Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa? 8To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke. 9To, don me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa. 10Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa, “‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.”
11Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi. 12Tun daga zamanin Yahaya Maibaftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan riske shi. 13Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya. 14In kuma za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15Duk mai kunnen ji, yă ji.
16“To, da me zan kwatanta zamanin nan? Kamar yara ne da suke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa,
17“‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba, Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba!”
18“Ga shi, Yahaya ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, “‘Ai, yana da iska.” 19Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, “‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!” Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”
(Luka 10.13-15)
20Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al'ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba. 21“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka. 22Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku. 23Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau. 24Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”
(Luka 10.21-22)
25A wanna lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. 26Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri. 27Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa. 28Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku. 29Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai. 30Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”
(Mar 2.23-28; Luka 6.1-5)
1A lokacin nan a ran Asabar, Yesu yana ratsa gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci. 2Amma da Farisiyawa suka ga haka, suka ce masa, “Ka ga! Almajiranka suna yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba.” 3Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai? 5Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a Attaura ba, yadda a ran Asabar, firistoci a Haikalin sukan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa? 6Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan. 7Da kun san ma'anar wannan cewa, “‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba,” da ba ku ga laifin marasa laifi ba. 8Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”
(Mar 3.1-6; Luka 6.6-11)
9Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu. 10Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne. 11Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba? 12Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.” 13Sa'an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan. 14Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.
15Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka. 16Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi. 17Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,
18“Ga barana wanda na zaɓa! Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.
19Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba, Ba kuma wanda zai ji muryarsa a hanya.
20Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba, Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai bice ta ba, Har ya sa gaskiya ta ci nasara.
21Al'ummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.”
(Mar 3.19-30; Luka 11.14-23)
22Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljan, ya kuwa warkar da shi, har beben ya yi magana, ya kuma sami gani. 23Mutane duk suka yi al'ajabi, suka ce, “Shin, ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?” 24Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu ne kawai, wannan yake fitar da aljannu.” 25Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu a kan gāba, da zai ɗore. 26In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yā rabu a kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore? 27In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alƙalanku. 28Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan. 29Yaya za a iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum a washe kayansa, in ba an fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin ba? Sa'an nan ne za a iya washe gidansa. 30Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
31“Don haka ina gaya muku, za ā gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhun, ba za a gafarta masa ba. 32Kowa ya aibata Ɗan Mutum, za ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”
(Luka 6.43-45)
33“Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, ta 'ya'yansa ake gane shi. 34Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa. 35Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. 36Ina dai gaya muku, a Ranar Shari'a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi. 37Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”
(Mar 8.12; Luka 11.29-32)
38Waɗansu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Malam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.” 39Sai ya amsa musu ya ce, “'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama! Amma ba wata alama da za a nuna musu sai dai ta Annabi Yunusa. 40Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa. 41A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan. 42A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ji hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.
(Luka 11.24-26)
43“Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa don neman hutu, amma ba ya samu. 44Sa'an nan sai ya ce, “‘Zan koma gidana da na fito.” Sa'ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce. 45Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zama wa wannan mugun zamani.”
(Mar 3.31-35; Luka 8.19-21)
46Yana cikin magana da taro, sai ga mahaifiyarsa da 'yan'uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi. 47Wani ya ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.” 48Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa, ya ce, “Wace ce tsohuwata, su wane ne kuma 'yan'uwana?” 49Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa, ya ce, “Ga tsohuwata da 'yan'uwana nan! 50Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan'uwana, shi ne 'yar'uwata, shi ne kuma tsohuwata.”
(Mar 4.1-9; Luka 8.4-8)
1A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a gabar teku. 2Taro masu yawan gaske suka haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi, ya zauna. Duk taron kuwa suka tsaya a bakin gaci.
3Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya je shuka. 4Yana cikin yafe iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su. 5Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa. 6Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe. 7Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su. 8Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi ƙwaya, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin. 9Duk mai kunnen ji, yă ji.”
(Mar 4.10-12; Luka 8.9-10)
10Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake yi musu magana da misalai?” 11Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarje muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba. 12Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 13Shi ya sa nake yi musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta. 14Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa, “‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau, Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,
15Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.”
16Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji. 17Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.
(Mar 4.13-20; Luka 8.11-15)
18“To, ga ma'anar misalin mai shukar nan. 19Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya. 20Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki. 21Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe. 22Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani. 23Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”
24Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa. 25Sa'ad da mutane suke barci, sai magabcinsa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa. 26Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana. 27Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, “‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?” 28Sai ya ce musu, “‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.” Bayin suka ce masa, “‘To, kana so mu je mu ciccire mu tara ta?” 29Amma ya ce, “‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma. 30Ku bari su kasance tare har zuwa lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.”
(Mar 4.30-32; Luka 13.18-19)
31Ya kawo musu wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa. 32Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”
(Luka 13.20-21)
33Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”
(Mar 4.33-34)
34Yesu ya gaya wa taro duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya faɗa musu kome sai da misali. 35Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Zan yi magana da misalai, Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”
36Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.” 37Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum. 38Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne. 39Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne. 40Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya. 41Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa, 42su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora. 43Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”
44“Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana cikin murnarsa, sai ya je yă sayar da dukan mallakarsa, ya sayi gonar.”
45“Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja. 46Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallakarsa, ya saye shi.”
47“Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri. 48Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar. 49Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci, 50su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”
51“Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.” 52Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”
(Mar 6.1-6; Luka 4.16-30)
53Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan. 54Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami'arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu'ujizan nan? 55Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Mahaifiyarsa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba? 56'Yan'uwansa mata ba duk tare da mu suke ba? To a ina ne mutumin nan ya sami waɗannan abu duka?” 57Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsa da kuma a gidansu.” 58Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.
(Mar 6.14-29; Luka 9.7-9)
1A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu. 2Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.” 3Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus. 4Don dā ma Yahaya ya ce masa bai halatta ya aure ta ba. 5Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama'a, don sun ɗauka shi annabi ne. 6To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus, 7har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta roƙa. 8Amma da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.” 9Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma kunyar baƙinsa, ya yi umarni a ba ta. 10Ya aika aka fille wa Yahaya kai a kurkuku, 11aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta. 12Almajiransa suka zo suka ɗauki gangar jikin, suka binne, suka kuma je suka gaya wa Yesu.
(Mar 6.30-34; Luka 9.10-17; Yah 6.1-14)
13Da Yesu ya ji haka sai ya tashi daga nan, ya shiga jirgi zuwa wani wuri inda ba kowa, domin ya kaɗaita. Amma da taron jama'a suka ji haka, suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa. 14Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu. 15Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.” 16Yesu ya ce, “Ba lalle su tafi ba. Ku ku ba su abinci mana.” 17Sai suka ce masa, “Ai, gurasa biyar da kifi biyu kawai muke da su a nan.” 18Sai ya ce, “Ku kawo mini su.” 19Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a. 20Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu. 21Waɗanda suka ci kuwa misalin maza dubu biyar ne banda mata da yara.
(Mar 6.45-52; Yah 6.16-21)
22Sai ya sa almajiransa suka shiga jirgi su riga shi hayewa kafin ya sallami taron. 23Bayan ya sallami taron, ya hau dutse shi kaɗai domin ya yi addu'a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai. 24Sa'an nan kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa suna mangararsa, gama iska tana gāba da su. 25Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun. 26Sa'ad da kuwa almajiran suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka firgita suka ce, “Fatalwa ce!” Suka yi kururuwa don tsoro. 27Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, Ni ne, kada ku ji tsoro.”
28Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka a kan ruwan.” 29Ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya nufi gun Yesu. 30Amma da ya ga iska ta yi ƙarfi sai ya ji tsoro. Da ya fara nutsewa sai ya yi kururuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!” 31Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?” 32Da shigarsu jirgin iska ta kwanta. 33Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”
(Mar 6.53-56)
34Da suka haye, suka sauka a ƙasar Janisarata. 35Da mutanen garin suka shaida shi, sai suka aika ko'ina a duk karkarar, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, 36suka roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma, iyakar waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.
(Mar 7.1-13)
1Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce, 2“Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.” 3Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku? 4Domin Allah ya yi umarni ya ce, “‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,” kuma “‘Wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa lalle a kashe shi.” 5Amma ku kukan ce, “‘Kowa ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama mahaifinsa ba ke nan.” 6Wato, saboda al'adunku kun mai da Maganar Allah banza. 7Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,
8“‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni.
9A banza suke bauta mini, Don ka'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.”
(Mar 7.14-23)
10Ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahimta. 11Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.” 12Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganar nan?” 13Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da yake Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi. 14Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.” 15Amma Bitrus ya ce masa, “A yi mana fassarar misalin nan.” 16Yesu ya ce, “Ku ma, ashe, har yanzu ba ku fahimta ba? 17Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice? 18Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum. 19Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke. 20Waɗannan suke ƙazantar da mutum. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazantar da mutum.”
(Mar 7.24-30)
21Yesu ya tashi daga nan, ya tafi zuwa ƙasar Taya da Sidon. 22Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mani jinƙai. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.” 23Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.” 24Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.” 25Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!” 26Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.” 27Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.” 28Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'yarta ta warke.
29Yesu ya tashi daga nan, ya bi ta bakin Tekun Galili. Sai ya hau dutse ya zauna a can. 30Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa, ya kuwa warkar da su. 31Har jama'ar suka yi ta al'ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu suna tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra'ila.
(Mar 8.1-10)
32Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.” 33Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?” 34Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa ke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.” 35Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. 36Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma suna, bai wa jama'a. 37Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai. 38Waɗanda suka ci kuwa maza dubu huɗu ne, banda mata da yara. 39Da ya sallami taron ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.
(Mar 8.11-13; Luka 12.54-56)
1Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi. 2Ya amsa musu ya ce, “In magariba ta yi, kuka ga sama ta yi ja, kukan ce, “‘Aha, gari zai yi sarari.” 3Da safe kuma in kun ga sama ta yi ja, ta kuma gama gari, kukan ce, “‘Yau kam, za a yi hadiri.” Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba kwa iya gane alamun zamanin nan. 4'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu, sai dai ta Yunusa.” Sai ya bar su ya tafi.
(Mar 8.14-21)
5Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe, sun manta ba su kawo gurasa ba. 6Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.” 7Sai suka yi magana da juna suka ce, “Ba mu kawo gurasa ba fa!” 8Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba? 9Ashe, har yanzu ba ku gane ba? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka ɗauka? 10Ko kuma gurasan nan bakwai na mutum dubu huɗu, manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? 11Yaya kuka kasa ganewa? Ba zancen gurasa na yi ba, sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.” 12Sa'an nan ne fa suka fahimta cewa, ba ce musu ya yi, su yi hankali da yistin gurasa ba, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.
(Mar 8.27-30; Luka 9.18-21)
13To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke cewa, Ɗan Mutum yake?” 14Sai suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa Iliya, waɗansu kuma Irmiya, ko kuwa ɗaya daga cikin annabawa.” 15Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa, nake?” 16Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.” 17Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama. 18Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba. 19Zan ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome ka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.” 20Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.
(Mar 8.31ū9.1; Luka 9.22-27)
21Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi. 22Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!” 23Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”
24Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni. 25Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. 26Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa? 27Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa. 28Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”
(Mar 9.2-13; Luka 9.28-36)
1Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da ɗan'uwansa Yahaya, ya kai su a kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske. 3Ga shi, Musa da Iliya sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu. 4Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin. In kana so, sai in kafa bukkoki uku a nan, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” 5Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.” 6Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su. 7Sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Da suka ɗaga kai ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai.
9Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.” 10Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya ya riga zuwa?” 11Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa. 12Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.” 13Sa'an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.
(Mar 9.14-29; Luka 9.37-43)
14Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce, 15“Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa. 16Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” 17Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.” 18Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke. 19Sa'an nan almajiran suka zo wurin Yesu a keɓe, suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?” 20Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, “‘Kawu daga nan, ka koma can!” sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.[ 21Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a da azumi.”]
(Mar 9.30-32; Luka 9.43-45)
22Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, 23za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.
24Da suka zo Kafarnahum masu karɓar rabin shekel na gudunmawar Haikali suka je wurin Bitrus, suka ce, “Malaminku yana ba da gudunmawar?” 25Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?” 26Sa'ad da kuma ya ce, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, 'ya'yan an ɗauke musu ke nan. 27Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.” 18.1 Wane ne Mafi Girma? Wane ne Mafi Girma>
(Mar 9.33-37; Luka 9.46-48)
1A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?” 2Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, 3ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba. 4Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.
5“Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa. 6Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”
(Mar 9.42-48; Luka 17.1-2)
7“Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin! 8In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu. 9In kuwa idonka yana sa ka laifi, to ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.”
(Luka 15.3-7)
10“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.[ 11Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.] 12To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa'in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba? 13In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa'in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba. 14Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”
(Luka 17.3)
15“In ɗan'uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan'uwanka ke nan. 16In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. 17In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”
18“Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne. 19Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi. 20Gama kuwa inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”
21Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?” 22Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har saba'in.
23“Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da take hannun bayinsa. 24Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi. 25Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da matarsa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin. 26Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, “‘Ya ubangida, ka yi mini haƙuri, zan biya ka tsaf.” 27Saboda tausayin bawan nan ubangidansa ya sake shi, ya yafe masa bashin. 28Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, “‘Biya ni abin da nake binka.” 29Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, “‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.” 30Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin. 31Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana. 32Sai ubangidansa ya kira shi, ya ce masa, “‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni, 33ashe, bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?” 34Ubangidansa ya yi fushi, ya ba da shi ga masu azabtarwa har yā biya duk bashin da ake binsa. 35Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”
(Mar 10.1-12; Luka 16.18)
1To, da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya bar ƙasar Galili, ya shiga ta Yahudiya, wadda take ƙetaren Kogin Urdun. 2Taro mai yawan gaske suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.
3Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa su gwada shi, suka ce, “Halal ne mutum ya saki matarsa a kan kowane dalili?” 4Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karantawa ba, cewa, wanda ya halicce su tun farko, dā ma ya yi su, namiji da tamata?” 5Ya kuma ce, “Don haka fa sai mutum ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa. Haka su biyun nan su zama jiki guda. 6Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.” 7Sai suka ce masa, “To, don me Musa ya yi umarni a ba da takardar kisan aure, a kuma saki matar?” 8Ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya yardar muku ku saki matanku, amma ba haka yake ba tun farko. 9Ina kuma gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”
10Sai almajiran suka ce masa, “In ko haka tsakanin mutum da matarsa yake, ashe ma, rashin yin aure ya fi amfani.” 11Amma ya ce musu, “Ba duk mutum ne zai iya ɗaukar maganar nan ba, sai dai waɗanda aka yardar wa. 12Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”
(Mar 10.13-16; Luka 18.15-17)
13Sa'an nan aka kawo masa yara ƙanana domin ya ɗora musu hannu, ya yi musu addu'a, amma almajiran suka kwaɓe su. 14Yesu kuwa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Sama na irinsu ne.” 15Sai ya ɗora musu hannu ya yi tafiyarsa.
(Mar 10.17-31; Luka 18.18-20)
16Sai ga wani ya matso wurinsa, ya ce, “Malam, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?” 17Sai ya ce masa, “Don me kake tambayata a kan abin da yake nagari? Ai, Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami wannan rai, to, ka kiyaye umarnan nan.” 18Sai ya ce masa, “Waɗanne?” Yesu ya ce, “Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. 19Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.” 20Saurayin ya ce masa, “Ai, duk na kiyaye waɗannan, me kuma ya rage mini?” 21Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa talakawa, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.” 22Da saurayin nan ya ji haka, sai ya tafi, yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.
23Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Hakika, ina gaya muku, da wuya mai arziki ya sami shiga Mulkin Sama. 24Har wa yau ina gaya muku, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 25Da almajiran suka ji haka, sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?” 26Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.” 27Sai Bitrus ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi mun bar kome, mun bi ka. Me za mu samu ke nan?” 28Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila. 29Kowa ya bar gidaje, ko 'yan'uwa maza, ko 'yan'uwa mata, ko mahaifi, ko mahaifiya, ko 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami. 30Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”
1“Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi. 2Da ya yi lada da su a kan dinari guda a yini, sai ya tura su garkarsa. 3Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza a bakin kasuwa. 4Sai ya ce musu, “‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.” Sai suka tafi. 5Da ya sāke fita wajen tsakar rana, da kuma ƙarfe biyu na rana, ya sāke yin haka dai. 6Wajen ƙarfe huɗu na yamma kuma ya fita ya sami waɗansu a tsaitsaye, ya ce musu, “‘Don me kuke zaman banza yini zubur?” 7Sai suka ce masa, “‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.” Ya ce musu, “‘Ku ma ku tafi garkata.” 8Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, “‘Kirawo ma'aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.” 9Da waɗanda aka ɗauka wajen ƙarfe hudu na yamma suka zo, sai ko wannensu ya sami dinari guda. 10To, da na farkon suka zo suka zaci za su sami fiye da haka. Amma su ma aka ba ko wannensu dinari guda. 11Da suka karɓa sai suka yi ta yi wa maigidan gunaguni, 12suna cewa, “‘Na bayan nan, ai, aikin sa'a guda kawai suka yi, ka kuwa daidaita mu, mu da muka yini zubur muna shan wahala da zafin rana.” 13Sai ya amsa wa ɗayansu ya ce, “‘Abokina, ai, ban cuce ka ba. Ashe, ba mu yi fada da kai a kan dinari guda ba? 14Sai ka karɓi halalinka ka tafi. Ni ne na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15Ashe, ba ni da ikon yin abin da na ga dama da abin da ke mallakata? Ko kuwa kana jin haushin alherina ne?” 16Saboda haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su koma na ƙarshe.”
(Mar 10.32-34; Luka 18.31-34)
17Yesu na tafiya Urushalima, ya ɗauki almajiran nan goma sha biyu waje ɗaya. Suna tafiya ke nan sai ya ce musu, 18“To, ga shi, za mu Urushalima, za a kuma ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, 19su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”
(Mar 10.35-45)
20Sa'an nan mahaifiyar 'ya'yan Zabadi ta matso wurinsa tare da 'ya'yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu. 21Sai ya ce mata, “Me kike bukata?” Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan 'ya'yana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.” 22Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya shan ƙoƙon da ni zan sha?” Suka ce masa, “Ma iya.” 23Sai ya ce musu, “Lalle kwa sha ƙoƙona, amma zama a damana da haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda Ubana ya riga ya shirya wa ne.” 24Da almajiran nan goma suka ji haka, sai suka ji haushin 'yan'uwan nan biyu. 25Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. 26Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 27Wanda duk kuma yake so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku, 28kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
(Mar 10.46-52; Luka 18.35-43)
29Suna fita daga Yariko ke nan, sai wani babban taro ya bi shi. 30Ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne yake wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!” 31Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!” 32Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?” 33Suka ce masa, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!” 34Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.
(Mar 11.1-11; Luka 19.28-40; Yah 12.12-19)
1Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su. 3Kowa ya yi muku magana, ku ce, “‘Ubangiji ne yake bukatarsu,” zai kuwa aiko da su nan da nan.” 4An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,
5“Ku ce wa 'yar Sihiyona, Ga Sarkinki yana zuwa gare ki, Mai tawali'u ne, Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”
6Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu. 7Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa masu mayafansu, ya hau. 8Yawancin jama'a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya. 9Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!” 10Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?” 11Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”
(Mar 11.15-19; Luka 19.45-48; Yah 2.13-22)
12Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai. 13Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, “‘Za a kira gidana ɗakin addu'a,” amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
14Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su. 15Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi. 16Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, “‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka?”
17Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.
(Mar 11.12-14,20-24)
18Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa. 19Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe. 20Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?” 21Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, “‘Ka ciru, ka faɗa teku,” sai kuwa ya auku. 22Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”
(Mar 11.27-33; Luka 20.1-8)
23Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?” 24Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan. 25To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, “‘Daga Sama take,” sai ya ce mana, “‘To, don me ba ku gaskata shi ba?” 26In kuwa muka ce, “‘Ta mutum ce,” ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.” 27Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
28“To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, “‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.” 29Sai ya ce, “‘Na ƙi.” Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi. 30Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, “‘To, za ni, baba,” amma bai je ba. 31To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da mahaifinsu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah. 32Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
(Mar 12.1-12; Luka 20.9-19)
33“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma ijarar garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa. 34Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar. 35Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya. 36Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka. 37Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, “‘Sā ga girman ɗana.” 38Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, “‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.” 39Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. 40To, sa'ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?” 41Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma ijararta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”
42Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.”
43Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari. 44Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake. 46Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama'a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.
1Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce, 2“Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki. 3Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa. 4Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, “‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ” 5Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gonarsa, wani kuma cinikinsa. 6Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulakanta su, suka kashe su. 7Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus. 8Sa'an nan ya ce wa bayinsa, “‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.” 10Sai bayin suka yi ta bin hanyoyin garin, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11“Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba. 12Sai ya ce masa, “‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?” Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13Sai sarki ya ce wa barorinsa, “‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon hakora.” 14Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
(Mar 12.13-17; Luka 20.20-26)
15Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa. 16Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai. 17To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 18Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai! 19Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. 20Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” 21Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” 22Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.
(Mar 12.18-27; Luka 20.27-40)
23A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya, 24suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, “‘In mutum ya rasu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan'uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.” 25To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa. 26Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin. 27Bayansu duka sai matar ta rasu. 28To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 30Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala'ikun da suke Sama ake. 31Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa, 32“‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.” 33Da jama'a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
(Mar 12.28-34; Luka 10.25-28)
34Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru. 35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce, 36“Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?” 37Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. 38Wannan shi ne babban umarni na farko. 39Na biyu kuma kamarsa yake, “‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.” 40A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”
(Mar 12.35-37; Luka 20.41-44)
41Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya, 42ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.” 43Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,
44“‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, Zauna a damana, Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.”
45Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?” 46Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.
(Mar 12.38-40; Luka 11.37-54; 20.45-47)
1Sa'an nan Yesu ya yi wa jama'a da almajiransa magana, ya ce, 2“Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa. 3Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa. 4Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi. 5Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa. 6Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u, 7a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su “‘Malam.” 8Amma ku kam, kada a ce muku “‘Malam,” domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne. 9Kada ku kira kowa “‘Uba” a duniya, domin Uba ɗaya ne ke gare ku, wanda yake cikin Sama. 10Kada kuma a kira ku “‘Shugabanni,” domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu. 11Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku. 12Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.
13“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga.[ 14Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan mata gwauraye, kukan yi doguwar addu'a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.] 15Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.
16“Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, “‘Kowa ya rantse da Haikalin, ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.” 17Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18Kukan ce, “‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.” 19Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar? 20Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa. 21Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa. 22Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.
23“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba. 24Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!
25“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari. 26Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.
27“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri. 28Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.
29“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai. 30Kuna cewa, “‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.” 31Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa. 32To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku! 33Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta? 34Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba. 35Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya. 36Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”
(Luka 13.34-35)
37“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 38Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! 39Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, “‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.”
(Mar 13.1-2; Luka 21.5-6)
1Yesu ya fita Haikalin, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gine-ginen Haikalin. 2Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”
(Mar 13.3-13; Luka 21.7-19)
3Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?” 4Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku, 5domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa. 6Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna. 7Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabam dabam. 8Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.
9“Sa'an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al'ummai za su ƙi ku saboda sunana. 10A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna. 11Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa. 12Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi. 13Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu. 14Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”
(Mar 13.14-23; Luka 21.20-24)
15“Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta), 16to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu. 17Wanda yake kan soro, kada ya sauko garin ɗaukar kayan da yake a gidansa. 18Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa. 19Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! 20Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar. 21A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada. 22Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin. 23A sa'an nan kowa ya ce muku, “‘Kun ga, ga Almasihu nan!” ko, “‘Ga shi can!” kada ku yarda. 24Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu. 25To, na dai gaya muku tun da wuri. 26Saboda haka in sun ce da ku, “‘Ga shi can a jeji,” kada ku fita. In kuwa sun ce, “‘Yana can cikin lolloki,” kada ku yarda. 27Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗan Mutum za ta zama. 28Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.
(Mar 13.24-27; Luka 21.25-28)
29“Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama. 30A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa. 31Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”
(Mar 13.28-31; Luka 21.29-33)
32“Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan. 33Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake. 34Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku. 35Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
(Mar 13.32-37; Luka 17.26-30,34-36)
36“Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da suke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama. 38Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, 39ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama. 40A sa'an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 41Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 42To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba. 43Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida. 44Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”
(Luka 12.41-48)
45“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 46Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka. 47Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa. 48Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, “‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,” 49sa'an nan ya soma dūkan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya, 50ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da zai zata ba, a kuma lokacin da bai sani ba, 51yă faffasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon hakora.”
1“Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango. 2Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima. 3Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba. 4Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu. 5Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su. 6Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, “‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!” 7Duk budurwan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu. 8Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, “‘Ku zuba mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!” 9Amma masu hikimar suka amsa suka ce, “‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.” 10Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa. 11Daga baya sai waɗancan budurwai ma suka iso, suka ce, “‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!” 12Sai ya amsa ya ce, “‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.” 13Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”
14“Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa. 15Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi. 16Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri. 17Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri. 18Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangidansa. 19To, da aka daɗe sai ubangidan bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su. 20Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, “‘Ya ubangida, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.” 21Sai ubangidansa ya ce masa, “‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.” 22Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, “‘Ya ubangida, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.” 23Sai ubangidansa ya ce masa, “‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.” 24Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, “‘Ya ubangida, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne. 25Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!” 26Sai ubangidansa ya amsa masa ya ce, “‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne? 27Ya kamata ka sa kuɗina a ma'aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba! 28Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan. 29Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. 30Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon hakora.”
31“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa. 32Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki. 33Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa. 34Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, “‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya. 35Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni. 36Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.” 37Sa'an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, “‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai? 38A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai? 39Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?” 40Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, “‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.” 41Sa'an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, “‘Ku rabu da ni, la'anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala'ikunsa. 42Don na ji yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba. 43Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.” 44Sa'an nan su ma za su amsa su ce, “‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?” 45Sa'an nan zai amsa musu ya ce, “‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.” 46Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”
(Mar 14.1-2; Luka 22.1-2; Yah 11.45-53)
1Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa, 2“Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”
3Sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa. 4Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi. 5Amma suka ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kada jama'a su yi hargitsi.”
(Mar 14.3-9; Yah 12.1-8)
6To, sa'ad da Yesu yake a Betanya a gidan Saminu kuturu, 7sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tandu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a kā, a lokacin da yake cin abinci. 8Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! 9Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba talakawa!” 10Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa. 11Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba. 12Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne domin tanadin jana'izata. 13Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
(Mar 14.10-11; Luka 22.3-6)
14Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci, 15ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi. 16Tun daga lokacin nan ne ya riƙa neman hanyar da zai bashe shi.
(Mar 14.12-21; Luka 22.7-14,21-23; Yah 13.21-30)
17To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?” 18Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, “‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.” 19Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.
20Da maraice ya yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu. 21Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22Sai suka yi baƙin ciki gaya, suka fara ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne, ya Ubangiji?” 23Sai ya amsa ya ce, “Wanda muke ci a ƙwarya ɗaya, shi ne zai bashe ni. 24Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.” 25Sai Yahuza da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi, kai ma ka faɗa.”
(Mar 14.22-26; Luka 22.15-20; 1 Kor 11.23-26)
26Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.” 27Sai ya ɗauki ƙoƙo kuma, bayan da ya yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha. 28Wannan jinina ne na tabbatar da alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu. 29Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”
30Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.
(Mar 14.27-31; Luka 22.31-34; Yah 13.36-38)
31Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, “‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.” 32Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.” 33Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.” 34Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.” 35Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.
(Mar 14.32-42; Luka 22.39-46)
36Sa'an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu'a.” 37Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. 38Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.” 39Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.” 40Ya komo wurin almajiran, ya ga suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da na sa'a ɗaya ba? 41Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.” 42Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.” 43Har yanzu dai ya dawo ya ga suna barci, don duk barci ya cika musu ido. 44Har wa yau ya sāke barinsu, ya koma ya yi addu'a ta uku, yana maimaita maganar dā. 45Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi, kuna hutawa? To, ga shi, lokaci ya yi kusa. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi. 46Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni nan, ya matso!”
(Mar 14.43-50; Luka 22.47-53; Yah 18.3-12)
47Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su. 48To, mai bashe shi ɗin ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.” 49Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “A gaishe ka, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa. 50Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Suka matso suka kama Yesu, suka danƙe shi. 51Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne. 52Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka a kubensa. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa. 53Kuna tsammani ba ni da iko in roƙi Ubana nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala'iku goma sha biyu? 54To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?” 55Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. 56Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
(Mar 14.53-65; Luka 22.54-55,63-71; Yah 18.13-14,19-24)
57Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Attaura da shugabanni suke tare. 58Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin. 59To, sai manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi. 60Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso, 61suka ce, “Wannan ya ce, zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.” 62Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan ke yi a kanka fa?” 63Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.” 64Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.” 65Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi! 66Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!” 67Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi, 68suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”
(Mar 14.66-72; Luka 22.56-62; Yah 18.15-18,25-27)
69To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!” 70Amma ya yi musu a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike nufi ba.” 71Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!” 72Sai ya sāke yin musu har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.” 73Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.” 74Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara. 75Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.
(Mar 15.1; Luka 23.1-2; Yah 18.28-32)
1Da gari ya waye sai duk manyan firistoci da shugabannin jama'a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi. 2Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga mai mulki Bilatus.
(A. M. 1.18-20)
3Sa'ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan, 4ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!” 5Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa. 6Amma manyan firistoci suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitulmalin Haikali ba, don kuɗin ladan kisankai ne.” 7Sai suka yi shawara, suka sayi filin maginin tukwane da kuɗin don makabartar baƙi. 8Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan filin jini. 9Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra'ilawa suka yi wa kima, 10suka sayi filin maginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umurce ni.”
(Mar 15.2-5; Luka 23.3-5; Yah 18.33-38)
11To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.” 12Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba. 13Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?” 14Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai.
(Mar 15.6-15; Luka 23.13-25; Yah 18.39ū19.16)
15To, a lokacin idi kuwa mai mulki ya saba sakar wa jama'a kowane ɗaurarre guda da suka so. 16A lokacin kuwa da wani shahararren ɗan sarƙa, mai suna Barabbas. 17Da suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sakar muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake kira Almasihu?” 18Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi. 19Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai matarsa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkin da na yi a game da shi.” 20To, sai manyan firistoci da shugabanni suka rarrashi jama'a su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi. 21Sai mai mulki ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sakar muku?” Sai suka ce, “Barabbas.” 22Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!” 23Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”
24Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.” 25Sai duk jama'a suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa a wuyarmu, mu da 'ya'yanmu!” 26Sa'an nan ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.
(Mar 15.16-20; Yah 19.2-3)
27Sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan ƙungiyar soja a kansa. 28Sai suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar alkyabba. 29Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” 30Suka tattofa masa yau, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka. 31Da suka gama yi masa ba'a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafi, suka tafi da shi domin su gicciye shi.
(Mar 15.21-32; Luka 23.26-43; Yah 19.17-27)
32Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.
33Da suka isa wurin da ake kira Golgota, wato, wurin ƙoƙwan kai, 34suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha. 35Da suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu ta jefa kuri'a. 36Suka zauna a nan suna tsaronsa. 37A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.” 38Sai kuma aka gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun. 39Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, 40suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!” 41Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa yi masa ba'a, suna cewa, 42“Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa. Ai, Sarkin Isra'ila ne, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mā gaskata da shi. 43Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce shi Ɗan Allah ne.” 44Har 'yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan.
(Mar 15.33-41; Luka 23.44-49; Yah 19.28-30)
45To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 46Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” 47Da waɗansu ɗa suke tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan na kiran Iliya ne.” 48Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha. 49Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya ceci shi.” 50Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa'an nan ya săki ransa.
51Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage. 52Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suke barci kuma suka tashi. 53Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa. 54Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
55Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima. 56A cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu mahaifiyar Yakubu da Yusufu, da kuma mahaifiyar 'ya'yan Zabadi.
(Mar 15.42-47; Luka 23.50-56; Yah 19.38-42)
57Maraice lis sai wani mai arziki ya zo, mutumin Arimatiya, mai suna Yusufu, shi ma almajirin Yesu ne. 58Ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya yi umarni a ba shi. 59Yusufu ya ɗauki jikin, ya sa shi a likkafanin lilin mai tsabta, 60ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi. 61Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.
62Kashegari, wato, bayan ranar shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus, 63suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu. 64Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.” 65Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗibi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku.” 66Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka buga wa dutsen nan hatimi, suka kuma sa sojan tsaro.
(Mar 16.1-8; Luka 24.1-12; Yah 20.1-10)
1To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin. 2Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai. 3Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar alli. 4Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu. 5Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye. 6Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi. 7Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.” 8Sai suka tashi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farin ciki, suka ruga a guje domin su kai wa almajiransa labari. 9Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama a gare ku!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”
11Suna tafiya ke nan, sai waɗansu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan firistoci labarin da ya auku. 12Su kuwa da suka taru da shugabannin jama'a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka, 13suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci. 14In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.” 15Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.
(Mar 16.14-18; Luka 24.36-49; Yah 20.19-23)
16To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su. 17Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa. 19Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, 20kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har ya zuwa matuƙar zamani.”