Micah
1Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.
2Dukanku ku ji, ku al'ummai! Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan abin da yake cikinki. Bari Ubangiji Allah Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama shaida a kanku.
3Ga shi, Ubangiji yana fitowa daga wurin zamansa, Zai sauko, ya taka kan tsawawan duwatsun duniya.
4Duwatsu za su narke a ƙarƙashinsa, Kwaruruka za su tsattsage kamar kakin zuma a gaban wuta, Kamar ruwa yana gangarowa daga tsauni.
5Duk wannan kuwa saboda laifin Yakubu ne, Da laifin Isra'ila. Mene ne laifin Yakubu? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Samariya ba? Mene ne kuma laifin Yahuza? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Urushalima ba>
6“Domin haka zan mai da Samariya jujin kufai a karkara, Wurin dasa kurangar inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari, In tone harsashin gininta.
7Za a farfashe dukan siffofinta na zubi, Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta, Zan lalatar da gumakanta duka, Gama ta wurin karuwanci ta samo su, Ga karuwanci kuma za su koma.”
8Mika ya ce, “Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka, Zan tuɓe, in yi tafiya huntu. Zan yi kuka kamar diloli, In yi baƙin ciki kamar jiminai.
9Gama raunin Samariya, ba ya warkuwa, Gama ya kai Yahuza, Ya kuma kai ƙofar jama'ata a Urushalima.”
10Kada a faɗe shi a Gat, Sam, kada a yi kuka. Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.
11Ku mazaunan Shafir, ku wuce abinku da tsiraici da kunya. Mazaunan Za'anan ba su tsira ba. Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zai tumɓuke harasashin gininki.”
12Mutanen Marot sun ƙosa su ga alheri, Amma masifa ta zo ƙofar Urushalima daga wurin Ubangiji.
13Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wa dawakai karusai, Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, Gama an iske laifofin Isra'ila cikinku.
14Domin haka sai ku ba Moreshet-gat guzuri, Mutanen Akzib za su yaudari sarakunan Isra'ila.
15Ku mazaunan Maresha, Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi, Darajar Isra'ila za ta shiga Adullam.
16Ku aske kanku saboda ƙaunatattun 'ya'yanku. Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar ungulu, Gama 'ya'yanku za su tafi bautar talala.
1Taku ta ƙare, ku masu shirya mugunta, Masu tsara mugunta a gadajensu! Sa'ad da gari ya waye, sai su aikata ta, Domin ikon aikatawa yana hannunsu.
2Sukan yi ƙyashin gonaki da gidaje, sai su ƙwace. Sukan zalunci mutum, su ƙwace gidansa da gādonsa.
3Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.
4A wannan rana za su yi karin magana a kanku, Za su yi kuka da baƙin ciki mai zafi, Su ce, “An lalatar da mu sarai! Ya sāke rabon mutanena, Ya kawar da shi daga gare ni! Ya ba da gonakinmu ga waɗanda suka ci mu da yaƙi.”
5Don haka ba za ku sami wanda zai sa muku ma'auni A taron jama'ar Ubangiji ba.
6“Kada su yi wa'azi,” amma sun yi wa'azi. “Idan ba su yi wa'azi a kan abubuwan nan ba, Raini ba zai ƙare ba.
7Daidai ne a faɗi haka, ya jama'ar Yakubu? “‘Ruhun Ubangiji ya yi rashin haƙuri ne? Waɗannan ayyukansa ne?” “Ashe, maganata ba takan amfana wanda yake tafiya daidai ba?”
8Ubangiji ya amsa ya ce, “Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar maƙiyi, Kukan tuɓe rigar masu wucewa da salama, masu komawa da yaƙi.
9Kukan kori matan mutanena Daga gidajensu masu kyau, Kukan kawar da darajata har abada daga wurin 'ya'yansu.
10Ku tashi, ku tafi, Gama nan ba wurin hutawa ba ne, Saboda ƙazantarku wadda take kawo muguwar hallaka.
11“Idan mutum ya tashi yana iskanci, yana faɗar ƙarya, ya ce, “‘Zan yi muku wa'azi game da ruwan inabi da abin sa maye,” To, shi ne zai zama mai wa'azin mutanen nan!
12“Hakika zan tattara ku duka, ya Yakubu, Zan tattara ringin Isra'ila. Zan haɗa su tare kamar tumaki a garke, Kamar garken tumaki a makiyaya Za su zama taron jama'a mai hayaniya.
13“Wanda zai huda garu, shi zai yi musu jagora, Za su fita ƙofar, su wuce, su fice ta cikinta. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma yana kan gaba.”
1Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya ku shugabannin mutanen Yakubu, Da ku sarakunan Isra'ila. Ya kamata ku san shari'a.
2Amma kuna ƙin nagarta, kuna ƙaunar mugunta, Kuna feɗe mutanena, Kuna kuma fizge naman jikinsu daga ƙasusuwansu.
3Kuna cin naman mutanena, kuna feɗe fatar jikinsu, Kuna kakkarya ƙasusuwansu, Kuna yanyanka su gunduwa gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya.”
4Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji, Amma Ubangiji ba zai amsa musu ba. Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan lokaci, Saboda mugayen ayyukansu.
5Ga abin da Ubangiji ya ce a kan annabawan da suka bi da mutanensa a karkace, Waɗanda suke cewa, “Salama,” sa'ad da suke da abinci, Amma sukan kai yaƙin shahada Ga wanda bai ba su abin sawa a baka ba.
6Saboda haka kome zai zama dare da duhu, ba wahayi ko duba. Rana za ta fāɗi a kan annabawa, Yini zai zama musu duhu baƙi ƙirin.
7Masu gani za su sha kunya, Masu duba kuwa za su ruɗe, Dukansu za su rufe bakinsu, Gama ba amsa daga wurin Allah.
8Amma ni ina cike da iko, Da Ruhun Ubangiji, Da shari'a da ƙarfin hali, Don in sanar wa Yakubu da laifinsa, Isra'ila kuma da zunubinsa.
9Ku ji wannan, ya ku shugabannin jama'ar Yakubu, Da ku sarakunan mutanen Isra'ila, Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya, Kuna karkatar da dukan gaskiya.
10Kuna gina Sihiyona da jini, Kuna kuwa gina Urushalima da zalunci.
11Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”
12Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.
(Ish 2.1-4)
1Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake Zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, Zai fi tuddai tsayi, Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.
2Al'umman duniya za su zo, su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila, Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.” Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.
3Zai shara'anta tsakanin al'umman duniya masu yawa, Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Māsunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace. Al'umma ba za ta ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.
4Kowa zai zauna gindin kurangar inabinsa da gindin ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi, Gama Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗa.
5Ko da yake al'ummai suna bin gumakansu, Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.
6Ubangiji ya ce, “A waccan rana zan tattara guragu, Da waɗanda aka kora, Da waɗanda na wahalshe su.
7Zan sa guragu su wanzu, Korarru kuwa su zama al'umma mai ƙarfi, Ni, Ubangiji, zan yi mulkinsu a Sihiyona har abada.
8“Ke kuma hasumiyar garken tumaki, tudun Sihiyona, Mulki na dā zai komo wurinki, Wato sarautar Urushalima.”
9Yanzu, me ya sa kike kuka da ƙarfi? Ba sarki a cikinki ne? Mashawarcinki ya hallaka ne, Da azaba ta auka miki kamar ta mace mai naƙuda>
10Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, ke Sihiyona, Kamar mace mai naƙuda, Gama yanzu za ki fita daga cikin birni, Ki zauna a karkara, Za ki tafi Babila, daga can za a cece ki. Daga can Ubangiji zai cece ki daga hannun maƙiyanki.
11Yanzu al'ummai sun taru suna gāba da ke, suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, Bari mu zura mata ido.”
12Amma ba su san nufin Ubangiji ba, Ba su gane shirinsa ba, Gama ya tara su ne kamar dammunan da za a kai masussuka.
13“Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka! Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe, kofatanki kuwa tagulla, Za ki ragargaje al'ummai da yawa.” Za ki ba Ubangijin dukan duniya dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya.
1Ki tattara sojojinki, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ila da sanda.
2“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”
3Domin haka zai yashe su, Sai lokacin da wadda take naƙuda ta haihu. Sa'an nan sauran 'yan'uwansa Za su komo wurin mutanen Isra'ila.
4Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da ƙarfin Ubangiji, Da ɗaukakar sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuwa zauna lafiya, Gama zai zama mai girma cikin duniya duka.
5Zai zama salamarmu.
6Za su mallaki ƙasar Assuriya da takobi, Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da zararren takobi, Zai cece mu daga hannun Ba'assuriye, Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmu yaƙi, Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.
7Sa'an nan ringin Yakubu zai zamar wa mutane Kamar raɓa daga wurin Ubangiji, Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire, Wanda ba ya jinkiri ko ya jira mutane.
8Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su.
9Za a ƙarfafa hannunka a kan maƙiyanka, Za a datse maƙiyanka duka.
10“A wannan rana, ni Ubangiji na ce, Zan kashe dawakanku, in hallaka karusanku.
11Zan shafe biranen ƙasarku, In rushe garunku.
12Zan kawar da maita daga ƙasarku, Ba za ku ƙara samun bokaye ba.
13Zan sassare siffofinku da ginshiƙanku, Ba za ku ƙara sunkuya wa aikin hannuwanku ba.
14Zan tumɓuke gumakan nan Ashtarot daga cikinku, Zan hallaka biranenku.
15Da fushi da hasala zan yi sakayya A kan al'umman da ba su yi biyayya ba.”
1“Ku ji abin da ni Ubangiji nake cewa, Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu, Ku bar tuddai su ji muryarku.
2“Ku duwatsu da madawwaman tussan duniya, Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yi muku. Gama Ubangiji, yana da magana gāba da mutanensa, Zai tuhumi Isra'ila.
3“Ya ku jama'ata, me na yi muku? Wace irin fitina nake yi muku? Ku amsa mini!
4Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu.
5Ya ku jama'ata, ku tuna Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla, Da yadda Bal'amu ɗan Beyor ya amsa masa, Da abin da ya faru daga Shittim, har zuwa Gilgal, Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.”
6Da me zan zo gaban Ubangiji, In sunkuyar da kaina a gaban Allah na Sama? Ko in zo gabansa da maraƙi bana ɗaya domin yin hadaya ta ƙonawa>
7Ubangiji zai yi murna da raguna dubbai Ko kuwa da kogunan mai dubbai? Zan ba da ɗan farina ne don laifina? Ko kuwa zan ba da 'ya'yana saboda zunubina>
8Ya kai mutum, ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau. Abin da Ubangiji yake so gare ka, shi ne Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri, Ka bi Allah da tawali'u.
9Ubangiji yana kira ga birnin. Hikima ce ƙwarai a ji tsoron sunanka. “Ki ji ya kabila, wa ya sa miki lokacinki>
10Ba zan manta da dukiya ta mugunta a gidan mugu ba, Ba kuwa zan manta da bugaggen mudun awo ba.
11Zan kuɓutar da mutum mai ma'auni na cuta Da ma'aunin ƙarya>
12Attajiran birnin sun cika zalunci, Mazaunansa kuwa maƙaryata ne, Harshensu na yaudara ne.
13Domin haka zan buge ku da ciwo, In maishe ku kufai saboda zunubanka.
14Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba, Yunwa za ta kasance a cikinku, Za ku tanada, amma ba zai tanadu ba, Abin da kuma kuka tanada zan bai wa takobi.
15Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba. Za ku matse 'ya'yan zaitun, amma ba za ku shafa mansa ba, Za ku kuma matse 'ya'yan inabi, amma ba za ku sha ruwansa ba.
16Domin kun kiyaye dokokin Omri, Kun bi halin gidan Ahab, Kun kuma bi shawarwarinsu. Domin haka zan maishe ku kufai, In mai da ku abin dariya, Za ku sha raini a wurin mutanena.”
1Tawa ta ƙare, gama na zama kamar lokacin da aka gama tattara amfanin gona, Kamar lokacin da aka gama kalar 'ya'yan inabi, Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci, Ba kuma 'ya'yan ɓaure da suka harba wanda raina yake so.
2Mutanen kirki sun ƙare a duniya, Ba nagarta a cikin mutane. Dukansu suna kwanto don su zub da jini. Kowa yana farautar ɗan'uwansa da tarko.
3Sun himmantu su aikata abin da yake mugu da hannuwansu. Sarki da alƙali suna nema a ba su hanci, Babban mutum kuma yana faɗar son zuciyarsa, Da haka sukan karkatar da zance.
4Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake, Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen ƙaya yake. Ranar da kuka sa mai tsaro, A ran nan za a aukar muku da hukunci. Yanzu ruɗewarku ta zo,
5Kada ka dogara ga maƙwabcinka, Kada kuma ka amince da abokinka. Ka kuma kame bakinka daga matarka Wadda take kwance tare da kai.
6Gama ɗa yana raina mahaifi, 'Ya kuma tana tayar wa mahaifiyarta, Matar ɗa kuma tana gāba da surukarta, Mutanen gidan mutum su ne maƙiyansa.
7Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji, Zan jira ceton Allahna, Allahna zai ji ni.
8Ya maƙiyina, kada ka yi murna a kaina, Gama sa'ad da na fāɗi, zan tashi kuma. Sa'ad da na zauna cikin duhu, Ubangiji zai haskaka ni.
9Zan ɗauka fushin Ubangiji ne, Gama na yi masa zunubi, Sai lokacin da ya ji da'awata, Har ya yanke mini shari'a. Zai kawo ni zuwa wurin haske, Zan kuwa ga cetonsa.
10Sa'an nan maƙiyina wanda yake ce mini, “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, ya kuma ji kunya. Idanuna za su gan shi lokacin da aka tattake shi Kamar taɓo a titi.
11Za a faɗaɗa iyakarka A ranar da za a gina garunka.
12A waccan rana mutane za su zo wurinka, Daga Assuriya har zuwa Masar, Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis, Daga teku zuwa teku, daga dutse zuwa dutse.
13Duniya kuwa za ta zama kufai, Saboda mazaunan da suke cikinta, Saboda hakkin ayyukansu.
14Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.
15“Zan nuna muku abubuwa masu banmamaki, Kamar a kwanakin da kuka fito ƙasar Masar.”
16Al'umman duniya za su gani, Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka. Za su sa hannuwansu a baka, Kunnuwansu za su kurmance.
17Za su lashi ƙura kamar maciji da abubuwa masu rarrafe, Za su fito da rawar jiki daga wurin maɓuyarsu, Da tsoro za su juyo wurin Ubangiji Allahnmu, Za su ji tsoronka.
18Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne.
19Zai sāke jin juyayinmu, Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin ƙafafunsa. Za ka jefar da zunubanmu a cikin zurfin teku.
20Za ka nuna wa Yakubu aminci, Ga Ibrahim kuma madawwamiyar ƙauna, Kamar yadda ka rantse wa kakanninmu Tun a zamanin dā.