Mark
(Mat 3.1-12; Luka 3.1-9,15-17; Yah 1.19-28)
1Farkon bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan. 2Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa, “Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya. 3Muryar mai kira a jeji tana cewa, Ku shirya wa Ubangiji tafarki, Ku miƙe hanyoyinsa.”
4Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa'azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu. 5Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun. 6Yahaya kuwa yana sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma. 7Ya yi wa'azi ya ce, “Wani yana zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko takalminsa ma ban isa in sunkuya in kwance ba. 8Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”
(Mat 3.13-17; Luka 3.21-22)
9Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun. 10Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya. 11Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”
(Mat 4.1-11; Luka 4.1-13)
12Nan da nan sai Ruhu ya iza shi jeji. 13Yana jeji har kwana arba'in, Shaiɗan yana gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala'iku kuma suna yi masa hidima.
(Mat 4.12-17; Luka 4.14-15)
14To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah, 15yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”
(Mat 4.18-22; Luka 5.1-11)
16Yana wucewa ta bakin Tekun Galili, sai ya ga Bitrus da Andarawas ɗan'uwansa, suna jefa taru a teku, don su masunta ne. 17Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” 18Nan da nan kuwa suka bar tarunansu suka bi shi. 19Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taru. 20Nan da nan da ya kira su, suka bar mahaifinsu Zabadi a cikin jirgin tare da ma'aikata, suka bi shi.
(Luka 4.31-37)
21Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar ne kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa. 22Sun yi mamakin koyarwarsa, domin yana koya musu da Iko, ba kamar malaman Attaura ba. 23Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami'arsu, yana ihu, 24yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai tsarkin nan ne na Allah.” 25Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! fita daga cikinsa!” 26Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa yana rawa, ya yi ihu, ya fita daga cikinsa. 27Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!” 28Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.
(Mat 8.14-15; Luka 4.38-49)
29Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya. 30Surukar Bitrus kuwa tana kwance tana zazzaɓi, nan da nan suka ba shi labarinta. 31Sai ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.
(Mat 8.16-17; Luka 4.40-41)
32Da magariba, bayan fāɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu. 33Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan. 34Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri iri, ya kuma fitar wa mutane aljannu da yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.
(Luka 4.42-44)
35Da assussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can. 36Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi. 37Da suka same shi, suka ce masa, “Duk ana nemanka.” 38Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa'azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito.” 39Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane da aljannu.
(Mat 8.1-4; Luka 5.12-16)
40Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni.” 41Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.” 42Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka. 43Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan, 44bayan ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 45Amma ya tafi, ya shiga sanar da maganar, yana baza labarin al'amarin ko'ina, har ya zamana Yesu bai ƙara shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko'ina.
(Mat 9.1-8; Luka 5.17-26)
1Bayan 'yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida. 2Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa'azin Maganar Allah. 3Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi. 4Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayyen yake kwance a kai. 5Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.” 6To, waɗansu malaman Attaura suna nan zaune, suna ta waswasi a zuciyarsu, 7suna cewa, “Don me mutumin nan yake faɗar haka? Ai, sāɓo yake yi! Wa yake da ikon gafarta zunubi in banda Allah kaɗai?” 8Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Don me kuke a waswasi haka a zuciyarku? 9Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, “‘An gafarta maka zunubanka”, ko kuwa a ce, “‘Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya?” 10Amma don ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya”ūsai ya ce wa shanyayyenū 11“Na ce maka, tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.” 12Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a kan idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”
(Mat 9.9-13; Luka 5.27-32)
13Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu. 14Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
15Wata rana Yesu yana cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne; 16da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci tare da masu zunubi da masu karɓar haraji, sai suka ce wa almajiransa, “Don me yake ci yake sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 17Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”
(Mat 9.14-17; Luka 5.33-39)
18To, almajiran Yahaya da na Farisiyawa suna azumi, sai aka zo aka ce masa, “Don me almajiran Yahaya da na Farisiyawa suke azumi, amma naka almajirai ba sa yi?” 19Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango za su yi azumi tun ango yana tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba. 20Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi. 21Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa. 22Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai ruwan inabin ya fasa salkunan, a kuma yi hasararsa da ta salkunan. Sabon ruwan inabi, ai sai sababbin salkuna.”
(Mat 12.1-8; Luka 6.1-5)
23Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara zagar alkamar. 24Farisiyawa suka ce masa, “Duba! Don me suke yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba?” 25Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa'ad da ya matsu da yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 26Yadda ya shiga masujadar Allah a zamanin Abiyata babban firist, ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai, har ma ya ba abokan tafiyarsa?” 27Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba. 28Saboda haka Ɗan Mutum shi ne Ubangijin har ma da na ranar Asabar.”
(Mat 12.9-14; Luka 6.6-11)
1Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. 2Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 3Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.” 4Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru. 5Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 6Da Farisiyawa suka fita, nan da nan sai suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.
7Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya, 8da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi. 9Don gudun kada taron ya marmatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda, 10saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta suna dannowa wurinsa domin su taɓa shi. 11Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.” 12Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.
(Mat 10.1-4; Luka 6.12-16)
13Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa. 14Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi domin ya riƙa aikensu suna wa'azi. 15Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu. 16Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus, 17da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato, 'ya'yan tsawa. 18Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane, 19da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi.
(Mat 12.22-32; Luka 11.14-23) Sa'an nan ya shiga wani gida. 20Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci. 21Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.” 22Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.” 23Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan? 24Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba. 25Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba. 26Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewarsa ce ta zo. 27Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.
28“Hakika, ina gaya muku, za a gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane sāɓon da suka hurta, 29amma fa, duk wanda ya sāɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.” 30Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”
(Mat 12.46-50; Luka 8.19-21)
31Sa'an nan mahaifiyarsa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa ya je. 32Taro kuwa yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.” 33Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?” 34Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana! 35Ai, kowa ya yi abin da Allah ke so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata.”
(Mat 13.1-9; Luka 8.4-8)
1Ya kuma fara koyarwa a bakin teku ke nan, sai babban taro ya haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi a tekun, ya kuwa zauna a ciki. Duk taron kuwa yana kan tudu a bakin tekun. 2Sai ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A cikin koyarwarsa har ya ce musu, 3“Ku saurara! Wani mai shuka ya tafi shuka. 4Yana cikin yafa iri, sai waɗansu ƙwayoyi suka fāɗa a hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5Waɗansu kuma suka fāɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa. 6Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe. 7Waɗansu kuma suka fāɗa cikin ƙaya, sai ƙayar ta tashi ta sarƙe su, ba su yi tsaba ba. 8Waɗansu kuma suka fāɗa a ƙasa mai kyau, suka yi yabanya, suka girma, suka yi tsaba, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.” 9Sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
(Mat 13.10-17; Luka 8.9-10)
10Da suka kaɗaita, masu binsa da su goma sha biyun nan suka tambaye shi ma'anar misalan. 11Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali, 12don gani da ido kam, za su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, za su ji, amma ba za su fahimta ba, don dai kada su juyo a yafe musu.”
(Mat 13.18-23; Luka 8.11-15)
13Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misali ba? Ƙaƙa za ku fahimci sauran ke nan? 14Mai shukan nan fa Maganar Allah yake shukawa. 15Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciyarsu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu. 16Haka kuma waɗanda aka shuka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farin ciki. 17Su kam ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe. 18Waɗansu kuma su ne kwatancin waɗanda suka fāɗa cikin ƙaya, su ne waɗanda suke jin Maganar, 19amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani. 20Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”
(Luka 8.16-18)
21Sai ya ce musu, “Shin, ana kawo fitila don a rufe ta da masaki, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado ne, ba don a ɗora ta a kan maɗorinta ba? 22Ba abin da yake ɓoye, sai domin a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da yake asirce, sai domin a bayyana shi a gaba. 23In da mai kunnen ji, yă ji.” 24Sai ya ce musu, “Ku ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. 25Domin mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.”
26Ya ce kuma, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a ƙasa. 27A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma, bai kuwa san ta yadda aka yi ba. 28Ƙasa da kanta takan ba da amfani, tsiro shi na farko, sa'an nan kai, sai kuma ƙwaƙƙwarar ƙwaya a kan. 29Sa'ad da amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato, kaka ta yi ke nan.”
(Mat 13.31-32; Luka 13.18-19)
30Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31Kamar ƙwayar mastad yake, wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi ƙanƙantar ƙwayoyi a duniya, 32duk da haka in an shuka ta, sai ta girma ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”
(Mat 13.34-35)
33Da misalai da yawa irin waɗannan Yesu ya yi musu Maganar Allah, daidai gwargwadon ganewarsu. 34Ba ya faɗa musu kome sai da misali, amma a keɓe yakan bayyana wa almajiransa kome.
(Mat 8.23-27; Luka 8.22-25)
35A ran nan da maraice ya ce musu, “Mu haye can ƙetare.” 36Da suka bar taron, suka tafi da shi yadda yake a cikin jirgin, waɗansu jirage kuma suna tare da shi. 37Sai babban hadari mai iska ya taso, raƙuman ruwa kuma suna ta fantsama cikin jirgin, har jirgin ya tasar wa cika da ruwa. 38Yesu kuwa yana daga ƙarshen baya na jirgin a kan matashi, yana barci. Sai suka tashe shi, suka ce masa, “Malam, za mu hallaka ba ka kula ba ko?” 39Sai ya farka, ya tsawata wa iskar, ya kuma ce wa ruwan tekun, “Natsu! Ka yi shiru!” Sai iskar ta kwanta, wurin duk ya yi tsit. 40Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?” 41Sai suka tsorata, matuƙar tsoro, suka ce wa juna, “Wa ke nan kuma, wanda har iska da ruwan teku ma suke yi masa biyayya?”
(Mat 8.28-34; Luka 8.26-39)
1Suka iso hayin teku a ƙasar Garasinawa. 2Da saukarsa daga jirgin, sai ga wani mai baƙin aljan daga makabarta ya tarye shi. 3Shi kuwa makabarta ce mazauninsa. Ba mai iya ɗaure shi kuma, ko da sarƙa ma. 4Don dā an sha ɗaure shi da mari da sarƙa, amma ya tsintsinka sarƙar, ya gutsuntsuna marin, har ma ba mai iya bi da shi. 5Kullum kuwa dare da rana yana cikin makabarta, da kan duwatsu, yana ta ihu, yana kukkuje jikinsa da duwatsu. 6Da dai ya hango Yesu, sai ya sheƙo a guje ya fāɗi a gabansa, 7ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.” 8Ya faɗi haka ne domin Yesu ya ce masa, “Rabu da mutumin nan, kai wannan baƙin aljan!” 9Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli, don muna da yawa.” 10Sai ya roƙi Yesu da gaske kada ya kore su daga ƙasar. 11To, wurin nan kuwa akwai wani babban garken alade suna kiwo a gangaren dutsen. 12Aljannun nan suka roƙe shi suke ce, “Tura mu wajen aladun nan, mu shiga cikinsu.” 13Ya kuwa yardar musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shiga aladun. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugunguta ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka hallaka a ruwa.
14Daga nan sai 'yan kiwon aladun suka gudu, suka ba da labari birni da ƙauye. Jama'a suka zo su ga abin da ya auku. 15Da suka zo wurin Yesu suka ga mai aljannun nan a zaune, sanye da tufa, cikin hankalinsa kuma, wato, mai aljannun nan masu yawa a dā, sai suka tsorata. 16Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka farfaɗi abin da ya gudana ga mai aljannun da kuma aladun. 17Sai suka fara roƙon Yesu ya bar musu ƙasarsu. 18Yana shiga jirgi ke nan, sai mai aljannun nan a dā ya roƙe shi izinin zama a gunsa. 19Amma Yesu bai yardar masa ba, ya ce masa, “Tafi gida wurin 'yan'uwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.” 20Sai ya tafi, ya shiga baza labari a Dikafolis na irin manyan abubuwan da Yesu ya yi masa. Duk mutane kuwa suka yi al'ajabi.
(Mat 9.18-26; Luka 8.40-56)
21Da Yesu ya sāke haye ƙetare cikin jirgi, sai babban taro ya kewaye shi. Shi kuwa yana bakin tekun. 22Sai ga wani daga cikin shugabannin majami'a, mai suna Yayirus. Da ganin Yesu kuwa sai ya fāɗi a gabansa, 23ya roƙe shi da gaske, yana cewa, “Ƙaramar 'yata tana bakin mutuwa. Idan za ka yarda ka zo ka ɗora mata hannu, sai ta warke ta rayu.” 24Sai suka tafi tare. Babban taro kuwa yana biye da shi, suna matsarsa.
25Sai ga wata mace wadda ta yi shekara goma sha biyu tana zub da jini, 26ta kuma sha wahala ƙwarai da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi. 27Da ta ji labarin Yesu, ta raɓo ta bayansa cikin taron, ta taɓa mayafinsa. 28Don tā ce a ranta, “Ko da tufarsa ma na taɓa, sai in warke.” 29Nan take zubar jininta ta tsaya, ta kuma ji a jikinta an warkar da cutarta. 30Nan da nan kuwa da Yesu ya ji wani iko ya fita daga gare shi, sai ya waiwaya a cikin taron, ya ce, “Wa ya taɓa tufata?” 31Sai almajiransa suka ce masa, “Kana ganin taro yana matsarka, ka ce, wa ya taɓa ka?” 32Sai Yesu ya juya domin ya ga wadda ta yi haka. 33Matar kuwa da ta san abin da aka yi mata, sai ta zo a tsorace, tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta faɗa masa ƙashin gaskiya. 34Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”
35Yana cikin magana, sai ga waɗansu daga gidan shugaban majami'a suka ce, “Ai, 'yarka ta rasu, me kuma za ka wahalar da Malamin?” 36Amma Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, ya ce wa shugaban majami'a, “Kada ka ji tsoro, ka ba da gaskiya kawai.” 37Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yahaya ɗan'uwan Yakubu. 38Da suka isa gidan shugaban majami'a, ya ji ana hayaniya, ana kuka, ana kururuwa ba ji ba gani. 39Da shigarsa sai ya ce musu, “Don me kuke hayaniya kuna kuka haka? Ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” 40Sai suka yi masa dariyar raini. Shi kuma bayan ya fitar da su duka waje, sai ya ɗauki mahaifin yarinyar, da mahaifiyarta, da kuma waɗanda suke tare da shi, ya shiga inda yarinyar take. 41Ya rike hannunta, ya ce mata, “Talita ƙumi,” wato, “Ke yarinya, ina ce miki, tashi.” 42Nan take yarinyar ta tashi ta yi tafiya, domin 'yar shekara goma sha biyu ce. Nan da nan kuwa mamaki ya kama su. 43Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.
(Mat 13.53-58; Luka 4.16-30)
1Ya tashi daga nan ya koma garinsu, almajiransa kuwa suka bi shi.
2Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa! 3Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi. 4Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin 'yan'uwansa, da kuma gidansu.” 5Bai ko iya yin wata mu'ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkar da su. 6Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu. Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
(Mat 10.5-15; Luka 9.1-6)
7Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu. 8Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai, 9amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu. 10Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi. 11Duk inda aka ƙi yin na'am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ka tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.” 12Haka fa, suka fita, suna wa'azi don mutane su tuba. 13Suka fitar da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkar da su.
(Mat 14.1-12; Luka 9.7-9)
14Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tāsa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.” 15Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.” 16Amma da Hirudus ya ji haka, sai ya ce, “Yahaya, wanda na fille wa kai, shi ne aka tāsa.” 17Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura. 18Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, “Bai halatta ka ƙwace matar ɗan'uwanka ba.” 19Hirudiya kuwa tana riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba, 20don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake yana murna da jinsa. 21Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki. 22Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Ki roƙe ni kome, sai in ba ki.” 23Ya kuma rantse mata, ya ce, “Kome kika roƙe ni zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.” 24Ta fita, ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.” 25Nan da nan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa, ta roƙe shi, ta ce, “Ina so yanzu yanzu ka ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi.” 26Sai sarki ya yi baƙin ciki matuƙa, amma saboda rantsuwar da ya yi da kuma kunyar baƙinsa, ba ya so ya hana ta. 27Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi umarni a kawo kan Yahaya. Dogarin ya tafi ya fille wa Yahaya kai a kurkuku, 28ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa ta ba mahaifiyarta. 29Da almajiran Yahaya suka ji labari, sai suka zo suka ɗauki gangar jikinsa, suka sa ta a kabari.
(Mat 14.13-21; Luka 9.10-17; Yah 6.1-14)
30Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar. 31Ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita a wurin da ba kowa, ku ɗan huta.” Domin mutane da yawa suna ta kaiwa da kawowa, ko damar cin abinci ma, manzannin ba su samu ba. 32Sai suka tafi cikin jirgi wurin da ba kowa, su kaɗai. 33Ashe, mutane da yawa sun ga tafiyarsu, sun kuwa shaida su, suka fa dunguma ta tudu daga garuruwa duka, suka riga su zuwa. 34Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa. 35Kusan fāɗuwar rana sai almajiransa suka zo gare shi, suka ce masa, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta kusa faɗuwa. 36Sai ka sallame su, su shiga karkara da ƙauyuka na kurkusa, su saya wa kansu abinci.” 37Amma ya amsa musu ya ce, “Ku ku ba su abinci mana.” Sai suka ce masa, “Wato, mu je mu sayo gurasa ta dinari metan, mu ba su su ci?” 38Ya ce musu, “Gurasa nawa ke gare ku? Ku je ku dubo.” Da suka binciko suka ce, “Ai, biyar ne, da kifi biyu.” 39Sa'an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna ƙungiya ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40Haka suka zauna jeri jeri, waɗansu ɗari ɗari, waɗansu hamsin hamsin. 41Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu. 42Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, 43har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin gurasar da na kifin. 44Waɗanda suka ci gurasar nan kuwa maza dubu biyar ne.
(Mat 14.22-27; Yah 6.16-21)
45Nan da nan ya sa almajiransa su shiga jirgi su riga shi hayewa zuwa Betsaida, kafin ya sallami taron. 46Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse domin ya yi addu'a. 47Da magariba ta yi, jirgin yana tsakiyar teku, Yesu kuwa yana nan a kan tudu shi kaɗai. 48Da ya ga suna fama da tuƙi, gama iska tana gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare, sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su, 49amma da suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka zaci fatalwa ce, suka yi kururuwa, 50domin duk sun gan shi, sun kuwa firgita. Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, ni ne, kada ku ji tsoro.” 51Sa'an nan ya shiga jirgi wurinsu, iska kuma ta kwanta. Sai mamaki ya kama su ƙwarai, 52don ba su fahimci al'amarin gurasar nan ba, saboda zuciyarsu ta taurare.
(Mat 14.34-36)
53Da suka haye, suka isa ƙasar Janisarata, suka ɗaure jirgin a gaɓa. 54Da fitarsu daga jirgin sai mutane suka shaida shi. 55Suka gama ƙasar da gudu, suka fara ɗaɗɗauko marasa lafiya a kan shimfiɗunsu zuwa duk inda suka ji yake. 56Duk inda ya shiga kuma, birni ko ƙauye ko karkara, sukan kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi ya yarda su taɓa ko ma da gezar mayafinsa. Iyakar waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
(Mat 15.1-9)
1To, da Farisiyawa suka taru a wurinsa tare da waɗansu daga cikin malaman Attaura da suka zo daga Urushalima, 2suka lura waɗansu almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsarki, wato, marasa wanki. 3Domin Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci sai sun wanke hannu sarai tukuna, saboda bin al'adun shugabanninsu. 4In sun komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma waɗansu al'adu da yawa da suka gada suke kiyayewa, kamar su wankin ƙore, da tuluna, da daro. 5Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka tambaye shi, “Don me almajiranka ba sa bin al'adun shugabanni, sai su riƙa cin abinci da hannuwa marasa tsabta?” 6Sai ya ce masu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa, “‘Al'umman nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni. 7A banza suke bauta mini, Domin ƙa'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.” 8Kuna yar da umarnin Allah, kuna riƙe da al'adun mutane.”
9Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al'adunku! 10Domin Musa ya ce, “‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,” da kuma, “‘Wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, sai lalle a kashe shi.” 11Amma ku kukan ce, “‘In mutum ya ce wa ubansa ko mahaifiyarsa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ” (wato, an sadaukar), 12shi ke nan fa, ba saura ku bar shi ya yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa aikin kome. 13Ta haka kuke banzanta Maganar Allah ta wajen al'adunku. Kun kuwa cika yin irin waɗannan abubuwa.”
(Mat 15.10-20)
14Sai ya sāke kiran jama'a, ya ce musu, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta. 15Ba abin da yake shiga mutum daga waje ya ƙazanta shi, sai abin da yake fita, yake ƙazantar da shi.[ 16Duk mai kunnen ji, yă ji.”] 17Bayan rabuwarsa da taron, da ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin. 18Ya ce musu, “Ashe, ku ma ba ku da fahimta ne? Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum daga waje, ba yadda zai ƙazanta shi, 19tun da yake ba zuciyarsa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci. 20Ya kuma ce, “Abin da yake fita daga cikin mutum yake ƙazantar da shi. 21Don daga ciki ne, wato, daga zuciyar mutum, mugayen tunani suke fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina, 22da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta. 23Duk waɗannan mugayen abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kuwa ƙazantar da mutum.”
(Mat 15.21-28)
24Daga nan kuma ya tashi ya tafi wajajen Taya da Sidon. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa ya sani ba, amma ba ya ɓoyuwa. 25Nan da nan sai wata mace, wadda karamar 'yarta take da baƙin aljan ta ji labarinsa, ta zo ta fāɗi a gabansa. 26Matar kuwa Baheleniya ce, asalinta kuma Basurofinikiya ce. Sai ta roƙe shi ya fitar wa 'yarta da aljanin. 27Yesu ya ce mata, “Bari 'ya'ya su ƙoshi tukuna, domin bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.” 28Amma ta amsa masa ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.” 29Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da 'yarki.” 30Sai ta koma gida ta iske 'yarta a kwance a gado, aljanin kuwa ya riga ya rabu da ita.
31Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis. 32Suka kawo masa wani kurma kuma bebe, suka roƙe shi don ya ɗora masa hannu. 33Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsotsinsa a kunnuwan kurma, ya tofar da yau, ya kuma taɓa harshen beben. 34Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato, “Buɗu!” 35Sai aka buɗe kunnuwansa, aka saki kwaɗon harshensa, ya kuma yi magana sosai. 36Yesu ya kwaɓe su kada su fada wa kowa, amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin. 37Suka yi mamaki gaba da kima, suka ce, “Kai, ya yi kome da kyau! Har kurma ma ya sa ya ji, bebe kuma ya yi magana.”
(Mat 15.32-38)
1A lokacin nan da wani taro mai yawan gaske ya sāke haɗuwa, ba su kuwa da abinci, sai ya kira almajiransa, ya ce musu, 2“Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci. 3In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai, za su kasa a hanya, ga shi kuwa, waɗansunsu sun fito nesa.” 4Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za a iya samun gurasar da za ta ciyar da mutanen nan a jeji haka?” 5Sai ya tambaye su, “Gurasa nawa ke gare ku?” Suka ce, “Bakwai.” 6Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki gurasar nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiransa su kai wa taron, suka kuwa kakkai musu. 7Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan. Da ya yi wa Allah godiya, sai ya ce su ma a kai musu. 8Suka ci, suka ƙoshi, har suka ɗauki ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai. 9Mutanen kuwa sun yi wajen dubu huɗu. Sai ya sallame su. 10Nan da nan kuwa sai ya shiga jirgi tare da almajiransa, ya tafi ƙasar Dalmanuta.
(Mat 16.1-4; Luka 12.54-56)
11Farisiyawa suka zo suka fara muhawwara da shi, suna nema ya nuna musu wata alama daga sama, don su gwada shi. 12Sai ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, ya ce, “Don me mutanen zamanin nan suke neman ganin alama? Hakika, ina gaya muku, ba wata alamar da za a nuna wa mutanen wannan zamani.” 13Daga nan ya bar su, ya sāke shiga jirgi, ya haye wancan ƙetaren.
(Mat 16.5-12)
14Sun kuwa manta, ba su kawo gurasa ba, sai guda ɗaya kawai ke gare su a jirgin. 15Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.” 16Suka yi magana da juna a kan ba su da gurasa. 17Da yake Yesu ya gane haka, sai ya ce musu, “Don me kuke zancen ba ku da gurasa? Ashe, har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahimta ba? Zuciyarku a taurare take? 18Kuna da idanu, ba kwa gani ne? Kuna da kunnuwa, ba kwa ji ne? Ba kwa kuma tunawa? 19Da na gutsuttsura wa mutum dubu biyar gurasar nan biyar, kwando nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Sha biyu.” 20“To, gurasa bakwai da na gutsuttsura wa mutum dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.” 21Sai ya ce musu, “To, har yanzu ba ku fahimta ba?”
22Suka iso Betsaida. Aka kawo masa wani makaho, aka roƙe shi ya taɓa shi. 23Ya kama hannun makahon, ya kai shi bayan gari. Da ya tofa yau a idanunsa, ya ɗora masa hannu, sai ya tambaye shi cewa, “Kana iya ganin wani abu?” 24Sai makahon ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane kam, amma kamar itatuwa nake ganinsu, suna yawo.” 25Sai ya sāke ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido ƙwar, ya warke, ya ga kome garau. 26Sai Yesu ya sallame shi ya koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”
(Mat 16.13-20; Luka 9.18-21)
27Yesu ya tashi, da shi da almajiransa, ya shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa, nake?” 28Suka ce masa, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, wani daga cikin annabawa.” 29Sai ya tambaye su, “Amma ku fa, wa kuke cewa, nake?” Bitrus ya amsa masa ya ce, “Kai ne Almasihu.” 30Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.
(Mat 16.21-28; Luka 9.22-27)
31Ya fara koya musu, cewa, lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai. 32Ya kuwa faɗi wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawatar masa. 33Amma da Yesu ya waiwaya ya ga almajiransa, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Kai yi nesa da ni, Shaiɗan! Ba ka tattalin al'amuran Allah sai na mutane.”
34Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni. 35Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, saboda bishara kuma, tattalinsa yake yi. 36Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? 37Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa? 38Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi, sa'ad da ya zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'iku.”
1Sai ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah ya bayyana da iko.”
(Mat 17.1-13; Luka 9.28-36)
2Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, 3tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya wanke su haka a duniya. 4Sai Iliya da Musa suka bayyana a gare su, suna magana da Yesu. 5Sai Bitrus ya ka da baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” 6Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske. 7Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.” 8Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.
9Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu tukuna. 10Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna ko mece ce ma'anar tashi daga matattu. 11Suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya yă fara zuwa?” 12Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa, zai sha wuya iri iri, a kuma wulakanta shi? 13Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa yake a rubuce.”
(Mat 17.14-21; Luka 9.37-43)
14To, da suka komo wurin almajiran, sai suka ga babban taro ya kewaye su, malaman Attaura kuma suna muhawwara da su. 15Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ɗungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16Ya tambaye su, “Muhawwarar me kuke yi da su?” 17Sai ɗaya daga cikin taron ya amsa masa ya ce, “Malam, ga shi, na kawo maka ɗana, don yana da beben aljan. 18Duk inda ya hau shi, sai ya doka shi har ƙasa, bakinsa yana kumfa, yana tsukun haƙoransa, yana sandarewa. Na kuma yi wa almajiranka magana su fitar da shi, suka kasa.” 19Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marasa bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.” 20Suka kawo masa yaron. Da aljanin ya gan shi, nan da nan sai ya buge yaron, jikinsa na rawa, ya fāɗi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa. 21Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Mahaifin ya ce, “Tun yana ƙarami. 22Ya kuwa sha jefa shi a wuta da kuma ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.” 23Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.” 24Nan da nan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!” 25Da Yesu ya ga taro yana ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.” 26Bayan da aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi yaron da gaske, jikinsa yana rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu!” 27Amma Yesu ya kama hannunsa ya tashe shi, ya kuwa tashi tsaye. 28Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a keɓe suka ce, “Me ya sa mu muka kāsa fitar da shi?” 29Sai ya ce musu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”
(Mat 17.22-23; Luka 9.43-45)
30Sai suka tashi daga nan, suka ratsa ƙasar Galili, bai kuwa so kowa ya sani ba, 31domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.” 32Amma fa ba su fahimci ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa. 9.33 Wane ne Mafi Girma? Wane ne Mafi Girma>
(Mat 18.1-5; Luka 9.46-48)
33Suka zo Kafarnahum. Da ya shiga gida sai ya tambaye su, “Muhawwarar me kuka yi a hanya?” 34Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawwarar ko wane ne babbansu. 35Sai ya zauna, ya kira goma sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa yake son ya zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, baran kowa kuma.” 36Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, ya rungume shi, ya ce musu, 37“Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
(Luka 9.49-50)
38Sai Yahaya ya ce masa, “Malam, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.” 39Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ai, ba wanda zai yi wata mu'ujiza da sunana, sa'an nan, nan da nan ya kushe mini. 40Ai, duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne. 41Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moɗa guda saboda ku na Almasihu ne, hakika ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.
(Mat 18.7-9; Luka 17.1-2)
42“Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku. 43In kuwa hannunka yana sa ka laifi, to, yake shi. Zai fiye maka ka shiga rai da dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa.[ 44A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.] 45In kuwa ƙafarka tana sa ka laifi, to yanke ta. Zai fiye maka ka shiga rai da gurguntaka, da a jefa ka Gidan Wuta da ƙafa biyu.[ 46A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.] 47In kuma idonka yana sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi. Zai fiye maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu. 48A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta. 49Da wuta za a tsarkake kowa, kamar yadda ake tsarkake abu da gishiri. 50Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sāne, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yizaman lafiya da juna.”
(Mat 19.1-12; Luka 16.18)
1Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.
2Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutum ya saki matarsa?” 3Sai ya amsa musu ya ce, “Me Musa ya umarce ku?” 4Suka ce, “Musa ya ba da izini a rubuta takardar kisan aure, a kuma saki matar.” 5Yesu ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya rubuta muku wannan umarni. 6Amma tun farkon halitta “‘Allah ya halicce su, namiji da tamata.” 7“‘Don haka fa sai mutum yă bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa. 8Haka su biyun nan su zama jiki guda.” Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. 9Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”
10A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana. 11Sai ya ce musu, “Kowa ya saki matarsa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun. 12In kuma matar ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”
(Mat 19.13-15; Luka 18.15-17)
13Suna kawo masa waɗansu yara ƙanana domin ya taɓa su, sai almajiransa suka kwaɓe su. 14Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne. 15Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.” 16Sai Yesu ya rungume su, yana ɗora musu hannu, yana sa musu albarka.
(Mat 19.16-30; Luka 18.18-30)
17Ya fara tafiya ke nan, sai ga wani ya sheƙo a guje, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?” 18Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci sai Allah kaɗai. 19Ka dai san umarnan nan, “‘Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Kada ka yi zamba. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.” 20Sai ya ce masa, “Malam, ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.” 21Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba talakawa, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.” 22Da jin wannan magana sai gabansa ya fāɗi, ya tafi yana da baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.
23Daga nan sai Yesu ya duddubi almajiransa, ya ce musu, “Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!” 24Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ya ku 'ya'yana, da ƙyar ne kamar me a shiga Mulkin Allah! 25Zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce masa, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?” 27Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.” 28Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai, ga shi, mu mun bar kome, mun bi ka.” 29Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko 'yan'uwansa mata, ko 'yan'uwansa maza, ko mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ko 'ya'yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara, 30sa'an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da 'yan'uwa mata, da 'yan'uwa maza, da uwaye, da 'ya'ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami. 31Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”
(Mat 20.17-19; Luka 18.31-34)
32Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa yana tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da ke biye kuma suka tsorata. Ya sāke keɓe goma sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi. 33Ya ce, “Ga shi, za mu Urushalima, za a ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga al'ummai. 34Za su yi masa ba'a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”
(Mat 20.20-28)
35Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.” 36Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?” 37Suka ce masa, “Ka yardar mana, ranar ɗaukakarka, mu zauna ɗaya a damanka, ɗaya a hagun.” 38Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?” 39Suka ce masa, “Ma iya.” Sai Yesu ya ce musu, “Ƙoƙon da ni zan sha, da shi za ku sha, baftismar da za a yi mini kuwa, da ita za a yi muku. 40Amma zama a damana, ko a haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.” 41Da almajiran nan goma suka ji haka, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya. 42Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gāsa musu iko. 43Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda yake son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 44Wanda duk kuma ke so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawan kowa. 45Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
(Mat 20.29-34; Luka 18.35-43)
46Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho yana bara, sunansa Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya. 47Da ya ji dai Yesu Banazare ne, sai ya fara ɗaga murya yana cewa, “Ya Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 48Waɗansu da yawa suka kwaɓe shi, cewa, ya yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai tausayina!” 49Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kirawo shi.” Sai suka kirawo makahon suka ce masa, “Albishirinka! Taso, yana kiranka.” 50Sai ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu. 51Yesu ya ce masa, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Malam, in sami gani!” 52Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, suka tafi.
(Mat 21.1-11; Luka 19.28-40; Yah 12.12-19)
1Da suka kusato Urushalima, da Betafaji, da Betanya, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 3Kowa ya ce muku, “‘Don me kuke haka?” ku ce, “‘Ubangiji ne yake bukatarsa, Zai kuma komo da shi nan da nan.” 4Sai suka tafi, suka tarar da aholakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5Sai waɗanda suke tsaitsaye a gun suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?” 6Suka faɗa musu abin da Yesu ya ce. Su kuwa suka ƙyale su suka tafi. 7Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau. 8Sai mutane da yawa suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka baza rassan da suka kakkaryo a saura. 9Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! 10Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dawuda! Hosanna ga Allah!”
11Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Da dai ya dudduba kome, da yake magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun nan.
(Mat 21.18-19)
12Kashegari, da suka tashi daga Betanya, ya ji yunwa. 13Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami 'ya'ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan ɓaure ba ne. 14Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin 'ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa suna ji.
(Mat 21.12-17; Luka 19.45-48; Yah 2.13-22)
15Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai, 16ya kuma hana kowa ya ratsa Haikalin ɗauke da wani abu. 17Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, “‘Za a kira masujadata ɗakin addu'a na dukkan al'ummai?” Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.” 18Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ji wannan magana, sai suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama'a suna mamaki da koyarwarsa. 19Kowace yamma kuwa Yesu yakan fita gari.
(Mat 21.20-22)
20Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa. 21Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la'anta ya bushe!” 22Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce wa dutsen nan, “‘Ka ciru, ka fāɗa teku,” bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi. 24Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa, samamme ne, za ku kuwa samu. 25Koyaushe kuka tsaya yin addu'a, in akwai wanda kuke jin haushinsa, ku yafe masa, domin Ubanku da yake Sama shi ma yă yafe muku laifofinku.[ 26Amma in ba kwa yafewa, haka Ubanku da yake Sama ma, ba zai yafe muku laifofinku ba.”]
(Mat 21.23-27; Luka 20.1-8)
27Suka koma Urushalima. Yana zagawa cikin Haikalin sai manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, 28suka ce masa, “Da wane izini kake yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka izinin yin haka?” 29Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan. 30To, baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce? Ku ba ni amsa.” 31Sai suka yi muhawwara da juna, suka ce, “In muka ce, “‘Daga Sama take,” sai ya ce, “‘To, don me ba ku gaskata shi ba?” 32Ma kuwa ce, “‘Ta mutum ce?” Suna kuwa jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa, Yahaya annabi ne. 33Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
(Mat 21.33-46; Luka 20.9-19)
1Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma ijarar garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa. 2Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar. 3Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannu banza. 4Sai ya sāke aika musu wani bawan. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi. 5Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu. 6Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, “‘Sā ga girman ɗana.” 7Amma manoman nan suka ce wa juna, “‘Ai, wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon yă zama namu.” 8Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge. 9To, me ubangijin garkar nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar. 10Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba? cewa, “‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. 11Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.”
12Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi misalin, amma suna jin tsoron jama'a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi.
(Mat 22.15-22; Luka 20.20-26)
13Suka aiko masa da waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin maganarsa. 14Da suka zo, suka ce masa, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, domin ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. Shin, dai dai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa? 15Mu biya, ko kada mu biya?” Shi kuwa da ya gane makircinsu, ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku kawo mini dinari in gani.” 16Suka kawo masa. Ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.” 17Sai Yesu ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.
(Mat 22.23-33; Luka 20.27-40)
18Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce, 19“Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa, idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya. 20To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba. 21Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka. 22Haka dai duk bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu. 23To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”
24Sai Yesu ya ce musu, “Ba saboda wannan ne ya sa kuka ɓata ba? Wato, don ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 25Domin in an tashi daga matattu, ba a aure, ba a aurarwa, amma kamar mala'ikun da suke Sama ake. 26Game da tashin matattu kuma, ashe, ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa, “‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu?” 27Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Kun ɓata da gaske.”
(Mat 22.34-40; Luka 10.25-28)
28Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawwara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wane umarni ne mafi girma duka?” 29Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, “‘Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.” 31Mabiyinsa shi ne, “‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.” Ba fa sauran wani umarni da ya fi waɗannan girma.” 32Sai malamin Attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka Malam, Ubangiji ɗaya ne, ba kuwa wani sai shi. 33A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan'uwa kamar kai, ai, ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.” 34Da Yesu ya ga ya yi masa magana da fasaha, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da Mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.
(Mat 22.41-46; Luka 20.41-44)
35Sa'ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne? 36Domin Dawuda da kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, Zauna a damana, Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.” 37Dawuda da kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.
(Mat 23.1-36; Luka 11.37-54; 20.45-47)
38A koyarwarsa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishe su a kasuwa, 39da kuma mafifitan mazaunai a majami'u, da mazaunan alfarma a wurin biki. 40Su ne masu ƙwace mallakar mata gwauraye, da yin doguwar addu'a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”
(Luka 21.1-4)
41Sai ya zauna gaban baitulmalin Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kuɗi a ciki. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi masu tsoka. 42Sai ga wata gwauruwa ta zo, ta zuba rabin kobo biyu a ciki, wato, kobo ke nan. 43Sai ya kira almajiransa, ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, abin da matalauciyar gwauruwar nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran duka. 44Su duk sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk abin da take da shi, duk ma da kuɗinta na abinci.”
(Mat 24.1-2; Luka 21.5-6)
1Yesu na fita daga Haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam, dubi irin duwatsun nan da gine-ginen nan!” 2Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga manyan gine-ginen nan? Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa, da ba za a baje shi ba.”
(Mat 24.3-14; Luka 21.7-19)
3Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake fuskantar Haikalin sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce. 4“Gaya mana yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin sukuwa?” 5Sai Yesu ya fara ce musu, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku. 6Mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa. 7In kuma kun jin labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna. 8Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi ta raurawar ƙasa a wurare dabam dabam, da kuma yunwa. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.
9“Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu. 10Amma lalle sai an fara yi wa dukan al'ummai bishara. 11Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne. 12Ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su. 13Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai tsira.”
(Mat 24.15-28; Luka 21.20-24)
14“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin sāɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu. 15Wanda yake kan soro kuma kada ya sauko ya shiga gida garin ɗaukar wani abu. 16Wanda yake gona kuma kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa. 17Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! 18Ku yi addu'a kada abin nan ya auku da damuna. 19A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittar da Allah ya yi, har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada. 20Da ba don Ubangiji ya taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan da ya zaɓa, sai ya taƙaita kwanakin. 21To, a lokacin nan kowa ya ce muku, “‘Kun ga, ga Almasihu nan!” ko, “‘Kun ga, ga shi can!” kada ku yarda. 22Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma, in zai yiwu. 23Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.”
(Mat 24.29-31; Luka 21.25-28)
24“Amma lokacin nan, wato, bayan tsabar wahalar nan, za a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. 25Taurari za su riƙa fāɗowa daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 26A sa'an nan ne za a ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da ɗaukaka. 27Sa'an nan zai aiko mala'ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga iyakar duniya har ya zuwa iyakar sama.”
(Mat 24.32-35; Luka 21.29-33)
28“Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan. 29Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan abubuwa suna aukuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake, 30Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku. 31Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
(Mat 24.36-44; Luka 17.26-30,34-36)
32“Amma fa wannan rana ko wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da suke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 33Ku kula, ku zauna a faɗake, kuna addu'a, domin ba ku san sa'ar da lokacin zai yi ba. 34Kamar mutum ne mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta barorinsa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai jiran ƙofa ya zauna a faɗake. 35To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne, 36kada ya zo kwaram, ya samu kuna barci. 37Abin kuwa da na gaya muku, ina gaya wa kowa ne, shi ne ku zauna a faɗake.”
(Mat 26.1-5; Luka 22.1-2; Yah 11.45-53)
1Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da idin abinci marar yisti, sai manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi, 2don sun ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kaɗa jama'a su ta da hargitsi.”
(Mat 26.6-13; Yah 12.1-8)
3Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tandu na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa tandun, ta tsiyaye masa man a kā. 4Waɗansu kuwa da suka ji haushi, suka ce wa juna, “Mene ne na ɓata mai haka? 5Da ma an sayar da shi fiye da dinari ɗari uku, an ba talakawa!” Sai suka hasala da ita, suna gunaguni. 6Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa. 7Kullum kuna tare da talakawa, koyaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba. 8Ta yi iyakacin ƙoƙarinta. Ta shafe jikina da mai gabannin jana'izata. 9Hakika kuwa ina gaya muku, duk inda za a yi bishara a duniya duka, abin da matar nan ta yi, za a riƙa faɗarsa domin tunawa da ita.”
(Mat 26.14-16; Luka 22.3-6)
10Sai Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, ya je wurin manyan firistoci don ya bāshe shi a gare su. 11Da suka ji haka suka yi murna, har suka yi alkawarin su ba shi kuɗi. Shi kuwa ya riƙa neman hanyar bāshe shi.
(Mat 26.17-25; Luka 22.7-14,21-23; Yah 13.21-30)
12A ranar farko ta idin abinci marar yisti, wato, ranar da aka saba yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa, sai almajiransa suka ce masa, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin cin Idin Ƙetarewa?” 13Sai ya aiki almajiransa biyu, ya ce musu, “Ku shiga gari, can za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa, ku bi shi. 14Duk gidan da ya shiga, ku ce wa maigidan, “‘In ji Malam, ina masaukin da zai ci Idin Ƙetarewa da almajiransa?” 15Shi kuwa zai nuna muku wani babban soro bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.” 16Sai almajiran suka tashi, suka shiga gari, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Idin Ƙetarewa.
17Da magariba ta yi, sai ya zo tare da goma sha biyun nan. 18Suna cin abinci ke nan, sai Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni, wanda kuwa muke ci tare.” 19Suka fara baƙin ciki, suna ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne?” 20Sai ya ce musu, “Ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne dai, wanda kuwa muke ci tare. 21Ga shi, Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kuwa, kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”
(Mat 26.26-30; Luka 22.15-20; 1 Kor 11.23-26)
22Suna cikin cin abinci, sai ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Ungo, wannan jikina ne.” 23Sai ya ɗauki ƙoƙo kuma, bayan ya yi godiya ga Allah, ya ba su, dukkansu kuwa suka shassha. 24Sa'an nan ya ce musu, “Wannan jinina ne na tabbatar da alkawari, wanda za a bayar saboda mutane da yawa. 25Hakika, ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da zan sha wani sabo a Mulkin Allah.” 26Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun. 14.27 Bitrus zai Yi Mūsun Sanin Yesu Bitrus zai Yi Mūsun Sanin Yesu
(Mat 26.31-35; Luka 22.31-34; Yah 13.36-38)
27Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe ne, domin a rubuce yake cewa, “‘Zan bugi makiyayi, tumaki kuwa su fasu.” 28Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.” 29Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe, ni kam, ba zan yi ba.” 30Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” 31Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi yana cewa, “Ko da za a kashe ni tare da kai, ba zan yi mūsun saninka ba.” Dukansu ma haka suka ce.
(Mat 26.36-46; Luka 22.39-46)
32Sai suka isa wani wuri, da ake kira Getsamani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan sa'ad da nake yin addu'a.” 33Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai. 34Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar zan mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake.” 35Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi addu'a ko ya yiwu a ɗauke masa wannan lokacin. 36Sa'an nan ya ce, “Ya Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.” 37Ya komo ya samu suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Bitrus, barci kake yi? Ashe, ba za ka iya zama a faɗake ko da sa'a ɗaya ba? 38Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a kada ku fāɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.” 39Sai ya sāke komawa, ya yi addu'a, yana maimaita maganar dā. 40Har wa yau kuma ya sāke dawowa, ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido ƙwarai, suka kuwa rasa abin da za su ce masa. 41Ya sāke komowa zuwa na uku, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka. Lokaci ya yi. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi. 42Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bāshe ni ɗin nan ya matso!”
(Mat 26.47-56; Luka 22.47-53; Yah 18.3-12)
43Nan da nan, kafin ya rufe baki, sai ga Yahuza, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, da taron mutane riƙe da takuba da kulake, waɗanda manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabanni suka turo. 44To, mai bāshe shi ɗin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi, ku tafi da shi a rirriƙe.” 45Da zuwansa kuwa ya zo wurin Yesu, ya ce masa, “Ya Rabbi!” sai ya yi ta sumbantarsa. 46Su kuwa suka danƙe Yesu, suka kama shi. 47Amma ɗaya daga cikin na tsaye, ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne. 48Sai Yesu ya ce musu, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? 49Kowace rana ina tare da ku a Haikalin ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Amma an yi haka ne fa domin a cika Littattafai.” 50Daga nan sai duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansa.
51Sai wani saurayi, daga shi sai mayafi, ya bi shi. Suka kai masa cafka, 52shi kuwa ya bar musu mayafin, ya gudu huntu.
(Mat 26.57-68; Luka 22.54-55,63-71; Yah 18.13-14,19-24)
53Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. Duk manyan firistoci da shugabanni da malaman Attaura suka taru a wurinsa. 54Bitrus kuma ya bi shi daga nesa nesa, har cikin gidan babban firist ɗin, ya zauna cikin dogaran Haikali, yana jin wuta. 55To, manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi, amma ba su samu ba. 56Da yawa kam, sun yi masa shaidar zur, amma bakinsu bai zo ɗaya ba. 57Daga baya kuma waɗansu suka taso, suka yi masa shaidar zur suka ce, 58“Mun ji ya ce, zai rushe Haikalin nan da mutane suka gina, ya gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba.” 59Duk da haka dai shaidarsu ba ta zo ɗaya ba. 60Sai babban firist ya miƙe a tsakiyarsu ya tambayi Yesu ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?” 61Amma ya yi shiru abinsa, bai amsa da kome ba. Sai babban firist ɗin ya sāke tambayarsa, “To, ashe, kai ɗin nan ne Almasihu Ɗan Maɗaukaki?” 62Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum zaune dama ga Mai Iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.” 63Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Wace shaida kuma za mu nema? 64Kun dai ji sāɓon da ya yi! Me kuka gani?” Duk suka yanke masa shari'a a kan ya cancanci kisa. 65Waɗansu ma suka fara tattofa masa yau, suka ɗaure masa idanu, suka bubbuge shi, suna ce masa, “Yi annabci!” Dogaran Haikali kuma suka yi ta marinsa. 14.66 Bitrus ya Yi Mūsun Sanin Yesu Bitrus ya Yi Mūsun Sanin Yesu
(Mat 26.69-75; Luka 22.56-62; Yah 18.15-18,25-27)
66Bitrus kuwa yana ƙasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo. 67Da ta ga Bitrus yana jin wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Banazaren nan Yesu!” 68Amma ya mūsa ya ce, “Ni ban ma san abin da kike faɗa ba, balle in fahimta.” Sai ya fito zaure. Zakara kuwa ya yi cara. 69Sai baranyar ta gan shi, ta sāke ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma nasu ne.” 70Amma ya sāke musawa. Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don Bagalile ne kai.” 71Sai ya fara la'antar kansa, yana ta rantserantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan da kuke faɗa ba.” 72Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.
(Mat 27.1-2,11-14; Luka 23.1-5; Yah 18.28-38)
1Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus. 2Bilatus ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗa.” 3Sai manyan firistoci suka yi ta kai ƙararsa a kan abubuwa da yawa. 4Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba ka da wata amsa? Dubi yawan maganganu da suke ba da shaida a kanka!” 5Yesu dai har yanzu bai yi wata magana ba, har Bilatus ya yi mamaki.
(Mat 27.15-26; Luka 23.13-25; Yah 18.39ū19.16)
6To, a lokacin idi kuwa Bilatus ya saba sakar musu kowane ɗan sarƙa guda da suka roƙa. 7Akwai wani mai suna Barabbas da yake ɗaure, tare da waɗansu 'yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen. 8Jama'a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi. 9Sai ya amsa musu, ya ce, “Wato, kuna so ne in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 10Don ya gane, saboda hassada ne manyan firistoci suka bāshe shi. 11Amma manyan firistocin suka zuga jama'a, gwamma ya sakar musu Barabbas. 12Sai Bilatus ya sāke ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da wanda kuke kira Sarkin Yahudawa?” 13Sai suka sāke yin ihu suka ce, “A gicciye shi!” 14Bilatus ya ce musu, “Ta wane hali? Wane mugun abu ne ya yi?” Amma su, sai ƙara ɗaga murya suke yi, suna cewa, “A gicciye shi!” 15Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama'a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.
(Mat 27.27-31; Yah 19.2-3)
16Sai soja suka tafi da shi cikin fāda, wato, fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja. 17Suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura, suka kuma yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a kā. 18Sai suka fara gaishe shi, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” 19Suka riƙa ƙwala masa sanda a ka, suna tattofa masa yau, sa'an nan suka durƙusa, kamar suna masa ladabi. 20Da suka gama yi masa ba'a haka, suka yaye masa alkyabba mai ruwan jar garura, suka sa masa nasa tufafi, suka kai shi waje don su gicciye shi.
(Mat 27.32-44; Luka 23.26-43; Yah 19.17-27)
21Sai ga wani mai wucewa, sunansa Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu. 22Suka kai Yesu wani wuri da ake kira Golgota, wato, wurin ƙoƙon kai. 23Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha. 24Sa'an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri'a a kansu, su ga abin da kowa zai samu. 25Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi. 26Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato, “Sarkin Yahudawa.” 27Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun.[ 28Wannan shi ne cikar Nassin nan da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.”] 29Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! Kai da za ka rushe Haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, 30to, sauko daga gicciyen, ka ceci kanka mana!” 31Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura suka riƙa yi masa ba'a a junansu suna cewa, “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kāsa ceton kansa, 32Almasihun nan, Sarkin Isra'ila, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka gicciye tare da shi su ma suka zazzage shi.
(Mat 27.45-56; Luka 23.44-49; Yah 19.28-30)
33Da rana tsaka, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 34Da karfe ukun, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāna?” wato, “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?” 35Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, suka ce, “Kun ji yana kiran Iliya.” 36Sai ɗayansu ya yiwo gudu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.” 37Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, kāna ya cika. 38Sa'an nan labulen Haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. 39Sa'ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”
40Akwai kuma waɗansu mata da suke hange daga nesa, a cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu mahaifiyar Yakubu ƙarami da Yusufu, da kuma Salome, 41su ne waɗanda suka biyo shi, sa'ad da yake ƙasar Galili, suna yi masa hidima, da kuma mata da yawa da suka rako shi Urushalima.
(Mat 27.57-61; Luka 23.50-56; Yah 19.38-42)
42Da maraice lis, da yake ranar shiri ce, wato, gobe Asabar, 43Yusufu mutumin Arimatiya ya zo, wani ɗan majalisa mai mutunci, wanda shi ma yake sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 44Bilatus ya yi mamaki ko ya mutu. Sai ya kira jarumi ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa. 45Da ya san haka daga bakin jarumi ɗin sai ya bai wa Yusufu jikin. 46Sai Yusufu ya sayi likkafanin lilin. Da ya sauko da Yesu, ya sa shi a likkafanin lilin ɗin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, ya kuma mirgina wani dutse a bakin kabarin. 47Maryamu Magadaliya da Maryamu mahaifiyar Yusufu sun ga inda aka sa shi.
(Mat 28.1-10; Luka 24.1-12; Yah 20.1-10)
1Da Asabar ta wuce, Maryamu Magadaliya, da Maryamu mahaifiyar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, domin su je su shafa masa. 2A ranar farko ta mako, da assussuba suka tafi kabarin, da fitowar rana sai suka isa. 3Suna ce wa juna, “Wa zai mirgine mana dutsen nan daga bakin kabarin?” 4Da suka ɗaga kai, suka ga, ashe, an mirgine dutsen waje ɗaya, ga shi kuwa, ƙato ne ƙwarai. 5Suna shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, sanye da farar riga. Sai suka firgita. 6Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi! 7Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.” 8Sai suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna tsoro. [
(Yah 20.11-18)
9Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai. 10Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa waɗanda dā suke tare da shi, ta tarar suna baƙin ciki, suna kuka. 11Amma da suka ji yana da rai, har ma ta gan shi, sai suka ƙi gaskatawa.
(Luka 24.13-35)
12Bayan haka ya bayyana da wata kama ga waɗansu biyu daga cikinsu, sa'ad da suke tafiya ƙauye. 13Suka koma suka gaya wa sauran, su ma kuwa ba su gaskata su ba.
(Mat 28.16-20; Luka 24.36-49; Yah 20.19-23; A. M. 1.6-8)
14Daga baya ya bayyana ga goma sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurin kansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba. 15Sai ya ce musu, “Ku tafi ko'ina a duniya, ku yi wa dukkan 'yan adam bishara. 16Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi. 17Za a ga waɗannan mu'ujizai wurin masu ba da gaskiya, wato, da sunana za su fitar da aljannu, za su yi magana da waɗansu baƙin harsuna, 18za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan, za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”
(Luka 24.50-53; A. M. 1.9-11)
19To, bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna dama ga Allah. 20Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]