LITTAFI NA FARI NA
MAKABAWA1. Iskandari Sarkin Helenawa
1 Iskandari ɗan Filibus na Makidoniya wanda ya fito daga kasar Kittim, ya gaji ubansa, ya zama Sarkin Helenawa. Sai ya ci nasarar Dariyus, sarkin mutanen Farisa da na Mediya, ya kwace masa sarauta. 2 Ya yi yaƙe‑yaƙe, ya ci birane masu yawa, ya kashe sarakunan duk gun da ya je. 3 Mulkinsa ya game dukan duniya, ya mai da ƙasashe masu yawa ganima. A dukan duniya ba mai iya tayar masa, sai ya zama mai girmankai, yana fariya. 4 Yana da sojoji masu ɗumbun yawa, ya mallaki ƙasashe, da kabilai, da sarakuna, duk suna biya masa haraji.
5 Bayan haka sai rashin lafiya ya kama shi, ya gane mutuwa zai yi, 6 sai ya kira manyan jarumawansa, waɗanda ya girma tare da su, ya raba musu mulkinsa tun yana da rai. 7 Shekarunsa goma sha biyu a sarauta lokacin da ya rasu.
8 Sai kowane jarumi ya soma mulkin jihar da aka ba shi. 9 Kowa ya sami yancin kai, yayansu kuma suka gāje su, suka daɗe a sarauta, suna ɓata duniya.
Sarki Antiyaku Efifanesa ya Tsananci Yahudawa
10 Sai wani jikansu, ɗan baya, mai suna Antiyaku Efifanesa, ɗan sarki Antiyaku wanda dā shi kamamme ne a Roma, ya zama sarki a shekara ta ɗari da talatin da bakwai, ta mulkin Helenawa.
11 A lokacin nan waɗansu Israilawa masu keta sharia sun ruɗi mutane da yawa, suna ce musu, Ku, mu je, mu yi yarjejeniya da sauran alumma da ke kewaye da mu, gama tun da muka rabu da su wahala na biye da mu. 12 Wannan shawara kuwa ta faranta wa mutane zuciya, 13 sai waɗansu daga cikinsu suka hanzarta zuwa gun sarki. Ya yarje musu su bi aladun da sauran alumma ke bi. 14 Sai Israilawan nan suka gina wurin yin wasa tsirara a Urushalima, kamar yadda dai sauran alumma ke yi, 15 suka kuma riƙa ɓoye kaciyarsu, suka manta da yarjejeniyarsu da Allah. Suka haɗa kai da sauran alumma, suka mai da kansu mamugunta.
16 Lokacin da Antiyaku ya ga mulkinsa ya ƙarfafa, sai ya ɗauri niyya ya ci sarautar Masar, don ya mallaki ƙasar Masar da ƙasarsa ta Asiya baki ɗaya. 17 Sai ya kai wa Masar hari da gawurtattun mayaƙa na sojojin doki, da giwaye, da jiragen ruwa, 18 domin ya yaƙi Talomi, Sarkin Masar. Sai Talomi ya gudu, ya bar ƙasassu da raunannu masu yawa. 19 Antiyaku ya ci manyan birane na Masar, ya washe duk ƙasar.
20 Bayan ya ci Masar da yaƙi, Antiyaku ya dawo a shekarar Helenawa ta ɗari da arbain da uku (169 B.C.). Sai ya nufi ƙasar Israila, ya shiga Urushalima da gawurtattun mayaka. 21 Ya shiga Haikalin Allah kai tsaye, ya ɗauke bagaden zinariya inda ake ƙona turare, da maɗorin fitilu, da dai dukan kayan ibada, 22 da teburin gurasar ajiyewa, da kwanoni, da ƙoƙuna, da farantan zinariya na ƙona turare, da labule, da zobba, da adon zinariya na fuskar Haikalin Allah. Ya dai kwashe kome da kome 23 na azurfa da zinariya, da dukan kaya masu tsada, da ɓoyayyiyar dukiya wadda ya tono, 24 ya tafi da su ƙasarsa, yana kashe mutane, yana taƙama.
25 Israilawa suka yi kuka da baƙin ciki duk inda suke,
26 Sarakuna da dattawa suka yi gunaguni.
Yan mata da samari suka rame,
Kyan mata duk ya dushe.
27 Kowane ango ya yi makoki,
Kowace amarya ta yi kuka a ɗakinta.
Har ƙasa ma ta yi girgiza
Kamar tana jin tausayin abin da ya faru,
Tana jin kunya saboda jikokin Yakubu.29 Bayan shekara biyu sarki Antiyaku ya aika da jarumin Misiya zuwa biranen Yahudiya. Shi kuwa ya tafi da gawurtattun mayaƙan ijara, ya gangara har Urushalima da su. 30 Ya ruɗi mutanen birnin da daɗin baki, har suka yarda da shi. Amma ya auka wa birnin da bazata, ya yi kacakaca da shi, ya karkashe mutane da yawa. 31 Ya washe garin, ya cinna masa wuta, ya bubbugi gidaje da garu, 32 ya kama mata da yara, har da shanu. 33 Sai ya gina hasumiyoyi da garu mai ƙarfin gaske kewaye da ɓarin da ake ce da shi Birnin Dawuda, ya mai da shi kagararsa. 34 Can ya ajiye shaiɗanum sojojinsa, suka yi ta tsaron kansu a wurin. 35 Suka tattara makamai, da abinci, da ganimar da suka kwace daga birnin Urushalima, sai suka zama ƙadangaren bakin tulu ga mutanen garin.
36 Wannan kagara ta zama gun kwanto na yan gāba na Wuri Mai Tsarki,
Maƙiyin Israilawa kuma na kullayaumin.
37 Aka zubar da jinin bayin Allah kewaye da Wuri Mai Tsarki, har cikinsa ma.
Saboda haka, mutanen Urushalima suka bar garin,
Garin ya zama masaukin baƙi,
Wanda yayansa ba su taɗa sani ba,
Suka bar shi ɗungurungun.
39 Wuri Mai Tsarki ya zama ba kowa, sai ka ce jeji.
Bukukuwan da aka saba yi suka zama baƙin ciki.
Ranakun ibadarsa suka zama abin kunya,
Darajarsa ta zama abin raini.
40 Sai da rashin darajar garin ya kasa darajarsa,
Ɗaukakarsa ta faɗi ba nauyi.An Hana Bin Addini
41 Sai sarki ya yi wasiƙa zuwa ga dukan gundumomin da yake riƙo, ya ce su zama alumma ɗaya, 42 kowannensu kuma ya watsar da aladunsa. Dukan sauran alumma, suka yarda da wannan umarni na sarki. 43 Har ma waɗansu Israilawa da yawa, suka yi ɗokin bin wannan addini nasa, sai suka soma yi wa gumaka hadayu, suna keta dokar hutun Asabar.
44 Sarkin kuwa ya aika da wasiƙu zuwa Urushalima da sauran biranen Yahudiya, ya ba su umarnin bin aladu waɗanda ba nasu ba, 45 ya hana yin ƙonannun hadayu da sadaka, da hadayun zub da ruwa a Wuri Mai Tsarki, ya ce musu su yi kunnen shege da Asabarasabar da ranakun bukukuwansu, 46 su ƙasƙantar da Wuri Mai Tsarki da firistoci. Sai ya ce su gina bagadai da gidajen tsafi, su siffata gumaka, 47 su yi layyar alade da sauran ƙazamun dabbobi, 48 kada kuma su yi wa yayansu kaciya, su ƙazantu da kowane irin abin ƙyama, 49 domin su mance da Attaura, su kuma mūsa dukan dokokinta. 50 Duk wanda bai bi umarnin sarki ba kuma, a kashe shi.
51 Da irin waɗannan maganganu ne, ya yi wa waɗanda yake riƙonsu wasiƙu. Ya zaɓi shugabanni masu duba mutanen. Ya kuma umarci biranen Yahudiya su miƙa hadayun tsafi bi da bi. 52 Mutane da yawa waɗanda suka watsar da Shariar Musa suka bi shugabannin, suka aikata mugunta a ƙasar. 53 Fitinan nan ta tilasta wa Israilawa gudun hijira.
54 Ran goma sha biyar ga watan Kisle a shekarar Helenawa ta ɗari da arbain da biyar (167 B.C.), sai sarkin ya gina babban abin ƙyama, mafificin mugunta, wato gunki bisa bagaden hadayun ƙonawa na Haikalin. Aka kuma giggina bagadan tsafi a biranen Yahudiya da ke kewaye da Urushalima, 55 aka ƙona turaren tsafi a bakin ƙofofi da a tituna. 56 Dukan littattafan Attaura da suka gani kuma suka yayyage su, suka ƙone.
57 Wanda duk aka gani da littafin yarjejeniyar, ko aka ga yana bin dokokin Attaura, sai sarki ya yi masa hukuncin kisa. 58 Aka yi ta yi wa Israilawan da aka kama a cikin birane haka kowane wata. 59 Ran ashirin da biyar ga kowane wata arnan nan suka yi hadaya bisa bagaden da aka gina a kan bagaden ƙonawa. 60 Bisa ga tasu doka ana kashe duk matan da aka yi wa yayansu kaciya, 61 ana rataye yayan a wuyan iyayensu, ana kashe duk mutanen gida, duk da wanzaman da suka yi kaciya. 62 Duk da haka, mutane da yawa suka ƙeƙasa kasa, suka ƙi cin abincin da ba shi da tsabta. 63 Suka zaɓi mutuwa kada a ƙazanta su ta wurin cin abincin, ko kuma su saɓa wa tsattsarkar yarjejeniya. Sai kuwa aka kashe su. 64 Fushi mai bantsoro ya auko wa Israilawa.
2. Mattatiyas da Tayansa
1 A lokacin nan Mattatiyas ɗan Yahaya, ɗan Saminu, firist na gidan Yowariba, ya tashi daga Urushalima, ya koma Modayan da zama. 2 Yana da yaya biyar, Yahaya, wanda aka ce da shi Gaddi, 3 da Saminu, wanda aka ce da shi Tasai, 4 da Yahuza, mai suna Makabi, 5 da Eleazara, wanda aka ce da shi Abarana, da Jonatan, mai suna Afusa. 6 Mattatiyas ya ga saɓon da ake yi wa mutanen Yahudiya da Urushalima, 7 sai ya ce, Kaito! Don me aka haife ni in ga halakar alummata da ta tsattsarkan birni, in zauna nan kuma a lokacin da za a sallama wa maƙiya shi, a ba baƙi Wuri Mai Tsarki?
8 Haikalin Urushalima ya zama kamar mutumin da aka ci wa mutunci,
9 An ɗauke kayan adonta, ya zama ganima.
An kashe jariranta a hanyoyinta,
Takobin maƙiya kuma ya kashe samarinta.
10 Wace kabila ce ba ta kutsa kai ƙasarta ba?
Ko kuma wadda ba ta taɓa ganimarta ba?
11 An ƙwace mata duk kayan adonta,
Yancinta na dā ya koma bauta.
12 Dubi Wuri Mai Tsarki, mai shaawa da ɗaukaka,
Yadda aka mai da shi banza.
Sauran alumma sun ƙazantar da shi.
Ina amfanin rayuwarmu?14 Sai Mattatiyas da yayansa suka yage tufafinsu, suka sa tsummoki suka yi kukan baƙin ciki mai tsanani.
Sun Ƙi yin Layya a Modayin
15 Jarumawan sarki waɗanda ke kula da matsa wa barin addinin Yahudawa sun shiga birnin Modayin domin mutanen garin nan su yanka layya. 16 Israilawa da yawa suka bi su, amma Mattatiyas da yayansa suka ware waje daya. 17 Sai jarumawan sarki suka ce wa Mattatiyas, Kai shugaba ne, mai mutunci, mai girma a wannan birni, kana da yaya da dangi masu goyon bayanka. 18 Zo yanzu, ka zama na farkon da zai bi umarnin sarki a nan, kamar yadda sauran alumma da mutanen Yahudiya, da waɗanda aka bari a Urushalima, suka yi. Saan nan za a mai da ku, kai da yayanka yan majalisar sarki, a kuma arzuta ku da zinariya, da azurfa, da kyauta iri iri, mai yawan gaske. 19 Amma Mattatiyas ya ba da amsa da kakkausar murya, ya ce, Ko da ya ke sauran alumma da sarki ke mallaka sun yarda da umarninsa, kowannensu ya daina bin addinin kakanninsa, 20 ni da yayana, da dangina, za mu riƙe yarjejeniyar da Allah ya yi da kakanninmu. 21 Allah ya ƙara taya mu mu bi Shariar Musa da dokokinsa. 22 Ba za mu bi umarnin sarki ba, domin kada mu bauɗe ko kadan, ga bin addininmu.
23 Da Mattatiyas ya gama waɗannan maganganu, sai wani Bayahude ya matso gaba a fuskar kowa don ya yanka layya a bagaden nan wanda yake a Modayin, bisa ga umarnin sarki. 24 Da ganin haka, sai ran Mattatiyas ya ɓaci da gaske, ya ji zafin fushinsa na son aikata adalci, sai ya zabura, ya kashe Bayahuden nan a kan bagaden. 25 Duk a lokaci ɗaya ne kuma, ya kashe jakadan sarki wanda ke tilasta wa mutane su yi hadayar, ya kuma yamutse bagaden. 26 Ta haka ya nuna tsananin himma ga Sharia, kamar dai yadda Finehas ya yi da Zimri ɗan Salu.
27 Sai Mattatiyas ya shiga gari, yana kūwwa, yana cewa, Wanda duk ke bin Shariar, yana goyon bayan yarjejeniya, ya fito ya bi ni. 28 Sai ya tsere da yayansa zuwa tsaunuka, suka bar dukan dukiyarsu a garin. 29 Sai waɗansu da yawa masu neman adalci da gaskiya suka shiga hamada, suka zauna a can, 30 su da yayansu, da matansu, da dabbobinsu, saboda masifun da suka auko musu.
31 Sai labarin nan ya iso gun jarumawan sarki da ƙungiyar sojan da ke Urushalima a sansanin Birnin Dawuda, cewa mutanen da suka ƙi bin umarnin sarki sun ɓuya a hamada. 32 Sai wata ƙungiyar soja ta bi su. Da ta tsinkaye su, sai suka sauka, suka yi shirin kai musu hari a ranar Asabar. 33 Sai sojoji suka ce musu, Ɓuyan nan ya isa haka. Ku fito, ku yi abin da sarki ya umarce ku, za a ceci rayukanku.
34 Sai Yahudawan suka amsa, suka ce, Ba za mu fito ba, ba kuma za mu bi umarnin sarki ba, har mu saɓa wa hutun Asabar. 35 Sai maƙiyan suka kai musu harin gaggawa. 36 Amma Yahudawan ba su yi musu wata tsayayya ba. Ko daga hannu ba su yi ba, ba su ma kankange kogon ɓuyarsu ba, 37 domin sun ce, Bari mu mutu a rashin laifinmu. Sama da ƙasa ne shaidunmu, kun hallaka mu ba da laifinmu ba. 38 Sai jarumawa da sojoji suka kai musu hari ran Asabar, suka kashe su duka, da matansu, da yayansu, da dabbobinsu, wajen mutum dubu ɗaya suka mutu.
Ayyukan Mattatiyas da Magoya Bayansa
Mattatiyas da abokansa, da jin haka, 39 sai suka yi wa yanuwansu makokin gaske. 40 Sai suka ce wa junansu, In muka ƙyale su kamar yadda danginmu suka yi, ba mu yaƙi mutanen sarki domin rayukanmu da aladunmu ba, hallaka mu za su yi daga duniya. 41 A ran nan sai suka yanke wata shawara, suka ce, Za mu yaƙi duk mutumin da ya kawo mana hari a ranar Asabar, don kada su kashe mu, kamar yadda suka kashe danginmu a kogonsu na ɓoyewa.
42 Sai suka haɗu da wata kungiyar Israilawa wadda aka ce da su Hasidiyawa, gogaggun mayaƙa ne, dukansu mabiyan Shariar Musa. 43 Duk waɗanda suke guje wa tsananin sarkin, sai suka yi haɗin gwiwa da su, suka yi musu gudunmawa. 44 Sai Mattatiyas da abokansa suka haɗa kungiyar mayaƙa, suka kashe masu keta haddin Shariar Musa, suka kuma nuna wa dukan masu yin saɓo kishin zucinsu. Sai sauran Yahudawan nan masu keta haddin sharia, waɗanda suka gudu daga gun Mattatiyas, suka koma gun mutanen sarki domin su tsira. 45 Mattatiyas da abokansa suka yi ta zagawa koina a ƙasar Israila, suna yamutse bagadan arna, 46 suna kuma tilasta a yi wa dukan yara marasa kaciya kaciya. 47 Suka kori masu girmankai, aikinsu kuma ya yi ta ci gaba. 48 Suka ceci sharia daga hannun sauran alumma da sarakunansu, ba su bar masu laifi su rinjiaya ba.
Wasiyyar Mattatiyas da Mutuwarsa
49 Da kwanakin Mattatiyas suka kusa karewa, sai ya ce wa yayansa, Masu girmankai da hassada sun ƙarfafa, lokacin ne kuma na tsanani da wulakanci mai tsanani. 50 To, yayana, ku nuna himma ga sharia, ku kuma ba da rayukanku domin yarjejeniyar da Allah ya yi da kakanninmu.
51 Ku tuna da ayyukan da kakanni suka aikata a nasu zamani,
Ku za ku sami ɗaukaka da sūna madawwami.
52 Ko ba ku ga amincin Ibrahim ba, lokacin da aka jarabce shi,
Har kuma aka mai da wannan aminci nasa abin samun karɓuwa ga Allah?
53 A cikin tsanani ne ma Yusufu ya kiyaye doka,
Har ya zama hakimin ƙasar Masar.
54 Finehas, kakanmu ma, saboda tsananin himmarsa ne,
Aka yi masa alkawarin madawwamin firistanci.
55 Joshuwa kuwa saboda cika aikin nan ne da aka ba shi,
Ya zama alƙalin Israilawa.
56 Kalibu kuma, domin shaidan nan mai kyau
Da ya bayar a gaban jamaar Israila,
Aka raba gādon kasar da shi.
57 Dawuda kuwa, da ya ke shi mai jinƙai ne,
Sai ya gaji gadon sarauta ta har abada.
58 Iliya, shi kuma saboda tsananin himmarsa a kan sharia,
Sai aka ɗauke shi zuwa samaniya.
59 Hananiya, da Azariya, da Mishayel saboda bangaskiyarsu ne,
Aka cece su daga ƙunar wuta.
60 Daniyel ma, domin rashin laifinsa ne,
Aka kare shi daga bakin zakoki.
61 Ku duba fa, daga zamani, har dai zuwa wani zamani,
Duk wanda ya amince da Allah ba ya rasa taimako,
62 Don haka, kada ku ji tsoron kurarin mai zunubi,
Domin darajarsa za ta shuɗe, ya zama abincin tsutsotsi.
63 In shi ne yau, ai, ba shi ne gobe ba,
Domin zai zama toka ya bi iska,
Shirye‑shiryensa kuma su bi ruwa.
64 Ku yi ƙarfin zuciya, yayana,
Ku kiyaye haddin bin sharia,
Domin ta wurinta ne za ku sami daraja.65 Ku lura kuma da ɗanuwanku Saminu. Na sani shi mai hikima ne wajen shawara, ku saurare shi kullayaumin, zai zama babbanku. 66 Yahuza Makabi gawurtaccen jarumi ne tun yana saurayi, shi zai shugabanci rundunarku a yaƙi da sauran alumma. 67 Ku kuma tara duk waɗanda suke bin sharia, ku kuma rama laifin da ake yi wa alummarku sarai. 68 Ku rama abin da sauran alumma suka yi muku, ku rika bin dokokin sharia.
69 Da Mattatiyas ya gama sa wa yayansa albarka, sai ya bi kakanninsa. 70 A shekara ta ɗari da arbain da shida ne ya mutu (166 B.C.). Aka rufe shi a kabarin kakanninsa a Modayin. Duk Israilawa suka yi matuƙar baƙin ciki a kan wannan rashi da suka yi.
3. Yahuza Makabi
1 Sai Yahuza, mai suna Makabi, ya zama shugaba a matsayin ubansa. 2 Dukan yanuwansa da magoya bayan mahaifinsa suka taru, suka bi Yahuza, suka tsare ƙasarsu ta Israila da farin ciki.
3 Yahuza ya baza darajar alummarsa koina,
Ya shiga sulkensa kamar wani toron giwa.
Ya saɓi makaman yaƙi,
Ya kuma yi shirin yaƙi, ya tsare sansaninsu.
4 In ya husata, sai ka ce zaki,
Ko ɗan zaki mai ƙugi, yana neman abin da zai ci.
5 Ya fatattaki masu keta sharia, yana farautarsu
Waɗanda ke damun mutanensa, ya ƙone garuruwansu.
6 Masu keta sharia nesa suke yi da shi, don ba ya wasa,
Dukan mugaye na gigicewa.
A shugabancinsa ne Israilawa suka sami yanci,
7 Ya tsanantar sarakuna da dama.
Amma ayyukansa sun sa yayan Yakubu farin ciki,
Za a kuma riƙa sa masa albarka har abada.
8 Ya yi ta zaga biranen Yahudiya,
Yana korar masu saɓon Allah daga ƙasar.
Ta haka ya hutar da Israilawa daga wahala.
9 Sunansa kuma ya shahara koina a duniya,
Sai ya tattara duk waɗanda ke bakin halaka a gu ɗaya.Nasarar Yahuza ta Farko
10 Sai wani jarumin sarki, mai suna Afaloni, ya tattara babbar runduna ta Samariyawa da ta sauran alumma domin ya yaƙi Israilawa. 11 Da Yahuza ya ji wannan labari, sai ya fito domin ya kara da Afaloni. Sai ya ci nasara, ya kashe Afaloni da waɗansu da dama daga cikin mayaƙansa, sai sauran mayaƙan Afaloni suka ce, Kai, a mai da iri gida. 12 Sai mutanen Yahuza suka kwashe kayansu, Yahuza kuwa ya ɗauki takobin Afaloni, ya yi ta yaƙi da shi a dukan kwanakinsa.
13 Sarona, shugaban askarawan sarki a yankin Suriya, ya ji labari Yahuza ya tara jamaar mayaƙa waɗanda suka amince da shi, ya kuma shirya su don yaƙi. 14 Sai Sarona ya ce, Zan yi wa kaina suna, in sami daraja a mulkin sarki ta cin nasara da Yahuza da mabiyansa, tun da ya ke sun raina umarnin sarki. 15 Sai kuma wata ƙakƙarfar ƙungiyar masu saɓon Allah na Israilawa ta bi shi don su yi wa Israilawa masu kirki ramawar gayya. 16 Da Sarona ya kai kusa da gangaran nan ta Bet‑horon, sai Yahuza ya tarye shi da ɗan taron sojoji. 17 Amma lokacin da sojojin Yahuza suka ga askarawan Sarona sun dosa kansu, sai suka ce wa Yahuza, Ta yaya mu da ba mu da yawa za mu iya yin yaƙi da wannan runduna ta gogaggun soja? Ba kuma wani mai kataɓus a cikinmu, domin ba mu ci kome ba yau.
18 Sai Yahuza ya amsa ya ce, Ai, wannan abu ne mai sauƙi a gun Allah, mutane kaɗan su ci masu yawa, domin duk ɗaya ne ga Allah ya taimaki mutane kaɗan ko masu yawa. 19 Ba yawan sojoji ke kawo cin nasara a yaƙi ba, amma taimako daga gun Allah yake. 20 Abokan gabanmu sun auka mana da girmankai da saɓon shariarmu, domin su hallaka mu, da matanmu, da yayanmu, su kuma kwashe kayanmu, 21 amma muna faɗa domin rayukanmu da aladunmu. 22 Allah ne zai murƙushe mana su. Don haka kada ku ji tsoronsu.
23 Da Yahuza ya gama yin jawabin nan, sai ya auka wa askarawan Sarona, ya cinye su. 24 Ya kore su daga gangaran nan ta Bet‑horon zuwa karkara. Ɗari takwas ne suka mutu daga cikin askarawan Sarona, sauran kuma suka tsira, suka shiga ƙasar Filistiyawa. 25 Aka soma jin tsoron Yahuza da yanuwansa, sai tsoro ya girgiza duk sauran alumma da ke kewaye da su. 26 Labarin Yahuza ya kai har kunnen sarki, kowace kabila kuma ta yi ta hira a kan Yahuza da yaƙe‑yaƙensa.
Antiyaku ya Naɗa Lisiyas Wakili
27 Waɗannan labaru suka ɓata wa sarki Antiyaku rai, har ya tara dukan sojojin mulkinsa, ya haɗa ƙungiya ƙaƙƙarfa. 28 Sai ya karɓi kuɗi a baitulmali, ya ba askarawansa albashin shekara ɗaya. Ya ce su zama shiryayyu, yaƙi na nan tafe ko yau ko gobe. 29 Saan nan ya ga kuɗin baitulmalin sun ƙare, kuɗin lardi kuma sun ragu domin rashin jituwa da balain da sarki ya kawo wa ƙasar, tun da ya ke ya hana waɗansu dokoki masu inganci na zamanin dā. 30 Sai ya fara jin tsoro kuɗi ba za su ishe shi kashewa ba, da kuma na kyauta mai yawa da yake bayarwa fiye da yadda sarakunan dā suka saba yi. 31 Da abin ya cuɗe masa, sai ya ƙudura zuwa yankunan Farisa, ya sara musu haraji, ya sami kuɗi masu tsoka. 32 Sai ya danƙa dukan shaanin sarauta gun Lisiyas, wani ɗan sarki, domin ya kula da jamaa tun daga gabar kogin Yufiretis har zuwa iyakar Masar, 33 ya kuma kula da ɗansa har ya dawo. 34 Ya bar wa Lisiyas rabin sojojin da waɗansu giwaye, ya ba shi umarnai a kan duk abubuwan da zai yi, tun ba game da mutanen Yahudiya da Urushalima ba. 35 Ya ce wa Lisiyas ya aika da askarawa su murƙushe Israilawa da dai duk mutanen da suka ragu a Urushalima, domin a mance da wanzuwarsu a wurin, 36 a saukar da baƙi koina a yankunansu, a rarraba ƙasa tasu.
37 Sai Sarki Antiyaku ya tashi daga Antakiya, babban birninsa, da rabin askarawan da suka ragu, a shekara ta ɗari da arbain da bakwai (165 B.C.), ya haye kogin Yufiretis, ya biyo ta lardunan ciki.
Lisiyas ya Aika da Runduna zuwa Yahudiya
38 Sai Lisiyas ya zaɓi Talomi, ɗan Dorimanesa, da Nikanar, da Gorgiyus manyan yan majalisar sarki, 39 ya hada su da sojojin ƙafa dubu arbain, da sojojin doki dubu bakwai, su shiga ƙasar Yahudiya, su hallaka ta bisa ga umarnin sarki. 40 Sai suka tashi da mayaƙansu duka, suka kai kusa da Imuwasu ta karkara, sai suka kafa sansaninsu a wurin. 41 Da yan kasuwa na jihar suka ji labarin zuwansa, sai suka kawo zinariya da azurfa mai yawa da gigar, suka tafi sansanin domin su sayi bayi, Israilawa. Kungiyoyin askarawa daga Suriya da na Filistiya suka haɗu da sojojin Lisiyas.
42 Yahuza da yanuwansa suka ga alamari yana shirin kai ga dokar ta ɓaci, suka kuma ga askarawa sun kafa sansaninsu gab da Israilawa, Yahuza da yanuwansa a sane suke kuma da umarnin nan na sarki a kan a yi wa Israilawa mugun kisa. 43 Sai suka ce wa junansu, Bari mu kāre mutanenmu kada a hallaka su. Mu yi yaƙi dominsu da Wuri Mai Tsarki.
44 Sai Yahuza ya tara mutanensa, su yi shirin yaƙi, su kuma yi addua, su roki jinƙai da rahama na Allah.
45 An bar Urushalima ba mutane, kamar jejin Allah,
Duk cikin yayanta ba mai shiga, balle fita.
An tattake Wuri Mai Tsarki,
Baƙi sun kwace sansaninta,
Ta zama masaukin sauran alumma.
Ba wata sauran murna gun jikokin Yakubu.
Ba a jin ƙarar mabusa, balle ta garaya.Yahudawa sun yi Shiri a Mizfa
46 Bayan da Yahudawan nan suka taru, sai suka nufi Mizfa, garin nan da ke kusa da Urushalima, da ya ke Mizfa da wuri ne na adduar Israilawa. 47 Ran nan suka yi azumi, suka sa tsummoki, suka yi hurwa da toka, suka yayyage tufafinsu. 48 Sai kuma suka yi ta buɗe Littafin Attaura domin su gane abin da ya kamata su yi, kamar yadda sauran alumma ke neman nasiha gun gumakansu a halin ƙaƙa naka yi. 49 Suka kuma kawo tufafin firistoci da tumun fari da za su miƙa, da ushirin dukiya, suka kuma zo da Nazarawa waɗanda kwanakin rantsuwarsu ta ɗaukar alkawari suka cika. 50 Sai suka ta da muryarsu ga Allah da ƙarfin gaske, suka ce, Me za mu yi da waɗannan Nazarawa, ina kuma za mu kai su? 51 Gama an tattake Wuri Mai Tsarki, an yi saɓo a ciki, firistocinku suna kukan shan ƙaskanci. 52 Ka duba kuma, sauran alumma sun haɗu domin su hallaka mu, ka kuma san abin da suke nufin yi da mu. 53 Ta yaya za mu iya ja in ja da su, in ba ka tashi ka taimake mu ba? 54 Sai suka busa algaitu, suka ƙwala ihu.
55 Bayan haka, sai Yahuza ya zabar wa mutanensa shugabanni, wato shugaban da zai umarci mutum dubu, da wanda zai umarci ɗari, da wanda zai umarci hamsin ko goma. 56 Ya ce wa maginan gidaje, da angaye, da masu shukar itacen inabi, da matsorata, kowannensu ya koma gida, kamar yadda sharia ta ce. 57 Sai askarawan suka nufi Imuwasu, suka kafa sansaninsu kudancin wurin. 58 Yahuza ya ce, Ku yi ɗamara, ku nuna halin jarumi. Ku yi shiri tun da sassafe ku yi yaƙi da waɗannan alummai da suka tayar mana domin su hallaka mu, duk da Wuri Mai Tsarki. 59 Gara mu mutu a fagen fama da mu ga lalacewar alummarmu da ta Wuri Mai Tsarki. 60 Ai, ƙaddarar Allah ta riga fata.
4. Yaki a Imuwasu
1 Sai Gorgiyus ya bi dare da sojojin ƙafa dubu biyar, da dubu ɗaya na doki, 2 domin su kai wa Yahudawa hari ba zato ba tsammani. Waɗansu mutane ne daga sansanin Birnin Dawuda suke nuna masa hanya. 3 Da Yahuza ya ji wannan labari, sai shi da sojojinsa suka fita domin su kara da rundunar sarki a Imuwasu, 4 lokacin da askarawan sarki suka yi ɗaya ɗaya a bayan sansaninsu. 5 Da dare ya tsalla, sai Gorgiyus ya shiga sansanin Yahuza, bai iske kowa ba, sai ya yi ta nemansu a bisa tsaunuka, yana cewa, Waɗannan mutane sun guje mana.
6 Da gari ya waye, sai Yahuza ya mamaye karkarar da sojoji dubu uku, amma ba su da makamai yadda suke bukata. 7 Sai suka ga rundunar sauran alumma, jarumawa na cikin sulke, ga su kuma gogaggu wajen yaƙi, sojojin doki kuma na kewaye da su. 8 Sai Yahuza ya ce wa mutanensa, Kada yawansu ya tsorata ku. 9 Ku tuna da yadda aka tsirar da kakanninmu a Bahar Maliya, lokacin da Firauna, sarkin Masar, ya angazo musu askarawansa. 10 Amma yanzu bari mu roƙi Allah ya ji tausayinmu, ya tuna da yarjejeniyar da ya yi da kakanninmu, ya murƙushe waɗannan sojoji a gabanmu yau, 11 domin alummai su sani, lalle akwai wani Mai Ceto mai tserar da Israilawa.
12 Da mayakan sauran alumma suka ta da kansu, suka ga Yahudawa sun kwararo su, 13 sai suka fito daga sansani domin a gabza. Sai mutanen Yahuza suka busa ƙaho. 14 Suka soma yaƙi. Aka murƙushe mutanen sauran alumma, suka ruga zuwa karkara, 15 takuba kuma suka kintsa waɗanda aka bari baya. Aka kora su zuwa Gazara, har ma zuwa karkarar Edom, da Azotus, da Yamamya. Abokan gāban dai, nan take suka rasa mutum dubu uku.
16 Yahuza da askarawansa suka koma da baya, suka ƙyale su. 17 Sai Yahuza ya ce wa askarawansa, Kada ku nemi ganima, domin da sauran yaƙi. 18 Gorgiyus da ƙungiyarsa suna kusa da mu cikin tsaunuka. Mu tasar wa abokan gabanmu, mu yaƙe su, bayan haka sai ku kwashi ganima yadda kuka ga dama.
19 Kafin Yahuza ya rufe baki, sai wata yar ƙungiyar abokan gāba ta fito daga tsaunin. 20 Sai ƙungiyar ta ga an karkashe rundunarsu, an kuma ƙone sansaninsu, domin sun ga hayaƙin da ya nuna musu abin da ya faru. 21 Da suka ga wannan, tsoro ya kama su ƙwarai. Lokacin da suka ga rundunar Yahuza a karkara, har ma sun ƙosa don a buga, 22 suka gudu, suka shiga ƙasar Filistiya.
23 Da Yahuza da mayaƙansa suka isa sansanin, suka yi ta kwasar ganima ta zinariya da azurfa mai yawa, da tufafi masu daraja, da dukiya mai yawa. 24 Lokacin da Yahudawa suke dawowa, sai suka yi ta raira waƙoki ga Allah,
Kaunarsa tabbatacciya ce.
25 A wannan rana ce Israilawa suka sami babbar kuɓuta.
Nasara bisa Lisiyas
26 Sai askarawan sauran alumma da suka tsira suka zo, suka faɗa wa Lisiyas duk abin da ya faru. 27 Labarin ya gigita shi, ya kuma ba shi tsoro, domin abubuwa ba su faru a ƙasar Israila kamar yadda ya nufa ba, ko kamar yadda sarki ya umarta.
28 Bayan shekara ɗaya, sai Lisiyas ya kwashe sojojin ƙafa dubu sittin, da sojojin doki dubu biyar, nufinsa ya cinye Yahudawa. 29 Sai suka kutsa cikin Edom, suka yi sansani a birnin Bet‑zur. Ta nan ne Yahuza da askarawansa dubu goma suka yi karo da su. 30 Da Yahuza ya ga ƙarfin abokan gaba, sai ya yi addua. Ga adduarsa.
Yabo ya tabbata gare ka, ya Mai Ceton Israilawa, mai ragargaje ƙarfin zakaran yan Filistiyawa ta hannun baranka Dawuda, ka kuma ba da sansaninsu a hannun Jonatan ɗan Saul tare da mai ɗaukar sulkensa. 31 Haka ma yanzu ka ba da rundunar abokan gāba a hannun mutanenka Israilawa. Ka sa abokan gābanmu su ji kunya, da sojojinsu na ƙafa, da na doki. 32 Ka ba su tsoro, ka kawar da jaruntakarsu ta barance. Ka sa su su yi makyarkyata, su halaka. 11 Ka kashe su da takobin waɗanda ke ƙaunarka, domin duk waɗanda suka san sunanka su yabe ka da waƙoƙi.
34 Da ƙungiyoyin nan biyu suka kara, sai mutum dubu biyar na Lisiyas suka halaka a wajen ba ta kāshin. 35 Lokacin da Lisiyas ya ga gazarwar nasa askarawa da ƙarfin zuciya na Yahum, ya ga dai jarumawan nan na Yahuza, ko wuta aka ce su fāɗa, za su faɗa, sai Lisiyas ya ranta ciki na kare zuwa Antakiya. Can ne ya kwaso sojojin haya domin ya sāke auka wa kasar Yahudiya da ƙungiya mai yawan gaske.
Tsarkakewar Haikalin Allah
36 Sai Yahuza da yanuwansa suka ce, Da ya ke yanzu mun cinye abokan gābanmu da yaƙi, sai mu tashi, mu share Wuri Mai Tsarki, mu tsarkake shi. 37 Sai duk askarawan suka hallara gu ɗaya, suka tashi zuwa tsaunin Sihiyona. 38 A can ne suka ga Wuri Mai Tsarki ya zama jeji, bagade ya ƙazantu, ƙyamaren ƙofofi sun ƙone, haki ya fito a fadodinta kamar dai yadda zai fito a kurmi ko bisa tsauni, ɗakunan firistoci sun lalace. 39 Sai suka yage tufafinsu, suka yi baƙin ciki mai tsanani, suna yin hurwa, 40 suka durƙusa, goshinsu a ƙasa. Lokacin da aka busa kakaki kuwa, sai suka fashe da kuka ga Allah.
41 Sai Yahuza ya ba mutanensa umarni suka kara da askarawan da ke a kagara lokacin da yake share Wuri Mai Tsarki. 42 Ya kuma zaɓi firistoci marasa laifi waɗanda ke girmama sharia, 43 suka taya shi tsabtace Wuri Mai Tsarki, suka kuma ɗauke gunkin arna, suka jefar da shi a juji. 44 Suka yi mushawara a kan abin da za a yi da bagaden ƙona hadaya da aka ƙazanta. 45 Suka yi tunani kuma, cewa abin da ya fi, shi ne a yamutse shi kurum, domin kada ya kawo musu zargi, saboda sauran alumma sun ƙazanta shi. Sai suka yamutse bagaden ƙona hadayar, 46 suka ajiye duwatsun a wuri mai dacewa bisa tsaunin Haikalin Allah, suna jiran wani annabi ya fito, ya gaya musu abin da za su yi da su. 47 Sai suka ɗauki duwatsu waɗanda ba a feƙe ba, kamar yadda sharia ta nuna, suka gina sabon bagaden hadaya kamar na dā. 48 Suka kuma gyara Wuri Mai Tsarki da sauran wuraren Haikalin Allah, suka share fadodin. 49 Suka yi sababbin tukwanen ibada, suka kuma kawo maɗdorin fitilu, da bagaden ƙona turare, da tebur cikin Haikalin Allah. 50 Sai suka ƙona turare a kan bagaden, suka kunna fitilu bisa maɗorinsu, sai haske ya cika Wuri Mai Tsarki na Allah. 51 Sai suka aza gurasa bisa teburin, suka kuma ɗaɗɗaura labule. Ta haka suka gama dukan aikin da suka yi niyyar yi.
52 Da sassafe ran ashirin da biyar ga watan tara, wato Kisle, a shekara ta ɗari da arbain da takwas (164 B.C.), 53 sai suka tashi, suka miƙa sadakoki, kamar yadda sharia ta nuna, bisa sabon bagaden ƙona hadaya wanda suka gina. 54 A ranar da sauran alumma suka ƙazanta wurin ne, aka sāke tsarkake shi da waƙe‑waƙe da kiɗe‑kiɗe da bushe‑bushe. 55 Duk mutanen suka durƙusa, suka yi sujada da yabo zuwa ga wanda ya ba su nasara.
56 Sai suka yi idin tsarkake bagaden har kwana takwas, suna miƙa hadayun ƙonawa, da na farin ciki, da hadayun godiya, da na yabon Allah saboda cetonsu da ya yi. 57 Suka yi wa gaban Haikalin Allah ado da zobban zinariya da ƙananan garkuwoyi, suka gyara ƙofofin da ɗakunan firistoci, suka sa musu ƙyamare. 58 Sai mutane suka yi murna ƙwarai da gaske, da ya ke yanzu an kawar da ƙazantar da sauran alumma suka yi. 59 Sai Yahuza da yanuwansa da dukan sauran jamaar Israilawa suka zartar a yi idin tsarkakewar bagade tare da jin daɗi da murna kowace shekara, har kwana takwas, daga ran ashirin da biyar ga kowane watan Kisle.
60 A lokacin suka gina garu mai tsamo, da hasumiyoyi masu ƙarfi kewaye da tsaunin Sihiyona, domin su hana sauran alumma shigowa, su taka shi, kamar yadda suka yi da. 61 Yahuza kuma ya ajiye rundunar sojoji a birnin don a tsare shi. Ya kuma ƙarfafa ƙauyen Bet‑zur, domin jamaa su sami matsara mai fuskantar Edom.
5. Ramuwar Gaya ga Abokan Gāba
1 Da sauran alumma waɗanda ke kewaye da Israilawa suka ji labari yadda aka sāke gina bagade, an kuma tsarkake Wuri Mai Tsarki kamar dā, sai suka yi fushi. 2 Saboda haka, sai suka yi shirin hallaka Israilawan da ke wurinsu, suka fara tsananta musu har da kisa. 3 Sai Yahuza ya kai wa kabilar Isuwa hari wajen Akarɓatana a ƙasar Edom, domin sun tare Israilawa. Ya yi nasara bisa gare su, ya washe musu kaya. 4 Ya kuma tuna da ƙetar kabilar Biyana, waɗanda suka zama abin bantsoro ga mutane, suna sari‑ka‑noƙe bisa hanyoyi. 5 Ya yi musu kullen dole a hasumiyoyin da ya kewaye da yaƙi. Ya alkawarta zai hallaka su, sai ya ƙone hasumiyoyinsu, duk da mutanen da ke ciki, ƙurmus. 6 Sai ya ketare zuwa ga Ammonawa, inda ya sami gawurtacciyar runduna ta sojoji da farar hula. Timoti na shugabancinsu. 7 Ya yi yaƙe‑yaƙe da su, ya kore su, ya karkashe su. 8 Bayan ya cinye birnin Yazar da ƙauyukansu, sai ya koma ƙasar Yahudiya.
An Ceci Yahudawan Galili
9 Sauran alumman da ke a jihar Gileyad suka taru domin su kai wa Israilawa hari, su kuma hallaka su a ƙasarsu. Sai Israilawan nan suka gudu zuwa matserar da ke Daterna. 10 Suka aika wa Yahuza da yanuwansa wasiƙa, suka ce, Sauran alumman da ke kewaye da mu sun haɗa kai domin su hallaka mu, 11 a shirye suke kuma su zo su ci matseran nan inda muke zaune. Timoti shi ne shugaba na wannan runduna. 12 Maza, ku zo, ku cece mu daga gare su, gama suna nan, suna ta yi mana kisan gilla. 13 Duk an kashe danginmu waɗanda ke wajen Tobiyawa. Sauran alumma sun tafi da matansu da yayansu da kayansu. An kashe mutane kimmanin dubu daya.
14 Yahuza da yanuwansa ke karanta wannan wasiƙa ke nan, sai waɗansu manzanni masu yagaggun riguna suka iso daga ƙasar Galili, suka kawo wani mugun saƙo, cewa mutanen biranen Talamayas, da Taya, da Sidon, da dukan sauran alumma na Galili sun haɗa kai domin su hallaka su. 15 Lokacin da Yahuza da jamaarsa suka ji haka, sai suka kira taron gaggawa don su shawarta abin da za su yi wanda zai amfani danginsu waɗanda abokan gāiba suka kai wa hari.
17 Sai Yahuza ya ce wa ɗanuwansa Saminu, Ka zaɓi mutane, ka je ka ceci danginka a ƙasar Galili. Ni da danuwana Jonatan kuma, za mu je Gileyad.
18 Amma Yahuza ya bar Yusufu ɗan Zakadya, da Azariya, shugaban jamaa, a Yahudiya tare da sauran runduna domin su tsare jihar Yahudiya. 19 Ya umarce su, ya ce, Ku lura da jamaarmu, amma kada ku takali wata alumma da yaƙi sai mun dawo. 20 Aka ba Saminu mutane dubu uku, suka tafi ƙasar Galili, aka kuma ba Yahuza mutane dubu takwas, suka tafi ƙasar Gileyad.
21 Saminu ya shiga ƙasar Galili, ya yi yaƙe‑yaƙe da sauran alumma. Ya buge musu guwai, 22 ya kuma kore su har ya zuwa ƙofar Talamayas. Aka kashe kamar mutum dubu uku na sauran alumma, ya kwashe kayansu. 23 Ya kuma dawo da Yahudawan da ke a ƙasar Galili da birnin Arabata, duk da matansu da yayansu da dukan abin da ke gare su, ya kawo su jihar Yahudiya tare da farin ciki mai yawa.
An Ceci Yahudawa a Gileyad
24 Yahuza Makabi da ƙanensa Jonatan suka haye kogin Urdun, suka yi tafiya kwana uku cikin hamada. 25 Can ne suka sadu da waɗansu Nabatawa, waɗanda suka marabce su, suka gaya musu duk abin da ya faru da Yahudawan da ke ƙasar Gileyad cewa, 26 An ɗure da dama daga cikinsu a biranen Bozka, da Basor da ke kusa da Alema, da Kasfa, da Makadi, da Kamayim. Duk waɗannan manyan mafaku ne. 27 An kuma ɗaure waɗansunsu a waɗansu birane a ƙasar Gileyad. Abokan gāban Yahudawa suna niyyar kai wa mafakan nan na Yahudawa hari gobe, su hallaka mutanen duk gaba daya.
28 Da jin haka, nan take sai Yahuza ya sāke hanyar rundunarsa, ya wuce hamada zuwa birnin Bozara, ya ci birnin. Ya kashe duk mazan da ke a garin, ya kwashe dukiyarsu, ya ƙone birnin. 29 Daganan suka tashi, suka bi dare, suka nufi mafakar da ke Daterna. 30 Da gari ya waye, ya hangi abokan gāba hululu, suna hawan tsaunuka, suna ta kai wa Yahudawan da ke ciki hari. 31 Da Yahuza ya ga an soma ja in ja, duk wuri kuma ya ruɗe da hayaniyar mutane da ƙarar kakaki, 32 sai ya ce wa askarawansa, Ku yi wa danginmu faɗan gani yau!
33 Sai Yahuza ya doshi abokan gāban da runduna uku, masu busa kakaki, da masu yin addua, ya yi magana da kakkausar murya. 34 Da abokan gāba suka gane, ashe, Yahuza Makabi ne, sai suka ja da baya. Ya yi musu ƙazamin kisa a ranan nan, na wajen mutane dubu takwas. 35 Sai ya nufi birnin Alema, ya kai hari ya cinye shi, ya kashe duk mazan da ke garin, ya kwashe dukiyarsu, ya ƙone birnin. 36 Daganan kuma ya ci gaba, ya cinye Kasfa, da Makadi, da Basor, da dai sauran biranen nan na Gileyad.
37 Bayan waɗannan alamura, sai Timoti ya tattara wata runduna, ya yi sansani da ke fuskantar ƙauyen ƙafoni, wanda ke hayin rafi. 38 Yahuza ya aika da magewaya zuwa sansanin Timoti. Sai suka kawo masa wannan labari, suka ce, Dukan sauran alumman da ke kewaye da mu sun goyi bayan Timoti, sun yi babban haɗin gwiwa. 39 Sun kuma yi ijarar da sojoji na Larabawa, sun yi sansani a hayin rafin da ke gabanka, sun yi shirin kai maka hari. Sai Yahuza ya fita domin ya riga su.
40 Da Yahuza da rundunarsa suka doshi rafin, sai Timoti ya ce wa jarumawan rundunarsa, In ya fara haye zuwa gunmu, ba za mu iya i masa ba, zai yi nasararmu. 41 Amma in ya ji tsoro, ya yi sansam a waccan gaɓar, za mu haye, mu je gunsa, za mu kuwa yi nasara.
42 Amma lokacin da Yahuza ya isa rafin, ya zaunar da shugabannin jamaarsa a gaɓa, sai ya ce musu, Kada ku yarda wani ya kafa tanti, amma ku yi ta kai hare‑hare. 43 Shi ne ya fara ƙetarewa ya kai hari, duk jamaa na baya. Ya lallasa sauran alumma duka, har suka watsar da makamansu, suka gudu zuwa mafakar ɗakin gunkin nan a Karnayim. 44 Sai Yahudawa suka cinye birnin nan, suka ƙone mafakar da duk waɗanda ke cikinta. Ta haka ne aka rinjayi Kamayim, garin kuwa bai sāke yin wani tawaye ba.
45 Saan nan ya tattara dukan Israilawa, manya da ƙanana, waɗanda ke a ƙasar Gileyad, duk da matansu da yayansu da kayansu, babban taron jamaa, domin su koma kasar Yahudiya. 46 Da suka isa birnin Efron, wata babbar mafaka ce a hanya, sai suka ga Ialle ba shi yiwuwa su bauɗe ta dama ko hagun, tilas ne su bi ta ciki. 47 Amma mutanen da ke birnin suka rufe ƙofofi, suka danne su da duwatsu. 48 Sai Yahuza ya aika musu da saƙon sulhu, ya ce, Muna so mu bi ta garinku zuwa namu. Ba wanda zai taɓa ku, wucewa kurum za mu yi. Amma suka ƙi buɗdewa.
49 Sai Yahuza ya sa aka fada wa askarawan da ke a sansaninsa, ya ce kowa ya kai hari daga inda yake. 50 Bayan da mutanensa suka gama shiri, suna jiran a ce musu, Ku yi, Yahuza ya ce su auka wa birnin. Suka yini suka kwana suna yaƙi, sai da suka cinye birnin. 51 Suka kashe duk mazan da ke cikin garin, suka rushe shi, suka kwashe kayan da ke ciki, suka bi suka wuce ta kan gawawwakin da aka kashe.
52 Saan nan suka haye kogin Urdun zuwa ga babbar karkarar da ke fuskantar birnin Bet‑sheyan. 53 A tafiyarsu Yahuza yana tattara mutanen da suka ɓace daga cikin jamaa, yana ƙarfafa su duka, sai ya isa ƙasar Yahudiya. 54 Suka hau tsaunin Sihiyona da murna da farin ciki, suka miƙa hadayun ƙonawa domin ba wanda ya mutu daga cikinsu, kowa ya dawo lami lafiya.
An cinye Yusufu da Azariya
55 Lokacin da Yahuza da Jonatan ke ƙasar Gileyad, Saminu kuma, wansu, yana ƙasar Galili kusa da Talamayas, 56 Yusufu ɗan Zakariya, da Azariya, shugabannin runduna, suka ji labarin jaruntakar da yanuwansu suka yi, 57 sai suka ce, Bari mu ma mu yi wa kanmu suna, mu yaƙi sauran alumman da ke kewaye da mu.
58 Sai suka ba sojojinsu umarni, su ci birnin Yamaniya. 59 Amma Gorgiyus da mutanensa suka fito daga birnin domin a kara. 60 Sai aka fi ƙarfin Yusufu da Azariya, aka kore su har zuwa kan iyakar Yahudiya. Yahudawa kuma kamar dubu biyu ne suka mutu ran nan. 61 Mutane suka yi ƙazamin rashin katari, domin ba su yi biyayya ga Yahuza da yanuwansa ba, suna tsammani za su aikata jaruntaka. 62 Gama ba su da dangantaka da sashin nan da Allah ya zaɓa su zama macetan Israilawa. 63 Yahuza da yanuwansa duk sun fi kowa shahara kan jaruntaka koina a Israila da sauran alumma, 64 mutane suna yabonsu, suna kuma haɗa gwiwa da su.
65 Saan nan Yahuza da yanuwansa suka fita, suka kai wa kabilar Isuwa hari a ƙasar Edom wadda ke kudancin Yahudiya. Ya cinye birnin Hebron da ƙauyukansa, ya kuma rushe mafakansa, ya ƙone hasumiyoyin da ke kewaye da shi. 66 Saan nan ya nufi ƙasar Filistiya, ya wuce ta birnin Marisa. 67 A lokacin nan waɗansu firistoci sun mutu cikin yaƙi, don sun fita ba tare da shiri ba, suna neman daraja domin kansu. 68 Saan nan Yahuza ya juya zuwa ga birnin Azotus a ƙasar Filistiyawa. Ya ragargaje bagadansu, ya ƙone gumakansu. Bayan ya mai da biranensu ganima, sai ya koma ƙasar Yahudiya.
6. An Ci Antiyaku na Huɗu, da Mutuwarsa
1 Lokacin da sarki Antiyaku ke wuce Iardunan gabas, sai ya ji labarin wani birni, mai suna Alimaisa a ƙasar Farisa, shi birnin sananne ne, saboda azurfarsa da zinariyarsa, 2 ɗakin gumakansa kuma mai yawan dukiya ne, yana cike da hulunan kwano, da sulkuna, da makamai, dukansu na zinariya, waɗanda Iskandari ɗan Filibus, Sarkin Makidoniya, wanda ya zama Sarkin Helenawa na fari, ya bari can. 3 Sabili da haka ne, ya tafi don ya ci birnin, ya kwashe kayan da ke ciki. Amma ya kasa domin mutanen birnin sun gane shirye‑shiryensa. 4 Suka kuma tasar masa da yaƙi. Sai ya ja da baya, ya komo Babila da baƙin ciki.
5 Lokacin da yake a ƙasar Farisa, manzo ya zo da labari, cewa rundunar da aka aika a ƙasar Yahudiya, an kore ta, 6 Lisiyas kuma ya fara shiga da gawurtaciyyar runduna wadda Israilawa suka kora, Israilawa kuma sun ƙarfafa da makamai, da mutane, da kuma kayan ganima, waɗanda suka karɓa daga rundunar da suka hallaka, 7 sai kuma suka ragargaje gumaka masu banƙyama waɗanda Lisiyas ya gina bisa bagaden da ke a Urushalima, suka kuma gina garu kewaye da Wuri Mai Tsarki kamar yadda yake dā, aka ma gina garu kewaye da birninsa Bet‑zur.
8 Da sarki ya ji labarin nan, sai ya yi fargaba, ya yi makyarkyata ta tsoro. Sai rashin lafiya na baƙin ciki ya kama shi, har an hana shi cika nufinsa, ya tafi ya maƙare gado. 9 A bisa gadon nan ne ya yi kwana da kwanaki, yana baƙin ciki, domin ya san lalle mutuwa zai yi.
10 Sai ya kira yan majalisarsa, ya ce musu, Kwana nake ba barci, domin ina yin zuIumi mai yawa. 11 Sai na ce wa kaina, Yau na shiga uku, raina ya ɓaci. 12 Ko da ya ke dā ina da sanyin hali da farin jini ga jamaata, yanzu na tuna da mugayen abubuwan da na aikata a Urushalima, lokacin da na kwashe dukan tukwanen ibada na zinariya da azurfa da ke a Haikalin Allah, na kuma sa aka hallaka mutanen Yahudiya. 13 Na sani don haka ne wahalolin nan suka auka mini, ga shi kuma, yanzu zan mutu da matuƙar baƙin ciki a ƙasar waje.
14 Sai ya kirawo Filibus, ɗan majalisarsa, ya miƙa masa ragamar mulkin. 15 Ya ba shi rawaninsa, da rigarsa, da zobensa mai hatimi, domin ya yi renon ɗansa Antiyaku, ya kuma hore shi har ya zama sarki. 16 Sarki Antiyaku ya mutu a ƙasar Farisa a shekara ta ɗari da arbain da tara (164 B.C.).
A Zamanin Sarki Antiyaku Yahuza ya Yaƙi Kagarar Urushalima
17 Da Lisiyas ya ji labari sarki ya rasu, sai ya naɗa Yarima Antiyaku sarki, wanda ya yi ta reno tun yana karami, ya kuma ba shi suna Yufatari.
18 Sojojin Antiyaku da ke a kagarar Urushalima, sai suka riƙa kewaye Israilawa da yaƙi a Wuri Mai Tsarki, suna nema su raunata su, su ƙarfafa sauran alumma. 19 Amma Yahuza ya yi shirin hallaka sojan, ya kira dukan jamaarsa, ya ce su kewaye kagarar. 20 A shekarar ta ɗari da hamsin ne, suka taru, suka kai wa kagarar hari. Saboda haka ya shirya waɗansu irin majajjawa masu watsi da manyan duwatsu, da waɗansu irin makamai. 21 Daga cikin waɗanda aka kewaye, waɗansu sun tsira da taimakon waɗansu Israilawa masu saɓo.
22 Sai suka je inda sarki yake, suka ce, Sai yaushe ne za ka zartar da hukunci, ka kuma rama wa danginmu abin da aka yi musu? 23 Mun yarda mu bauta wa mahaifinka, mu kuma bi umarnansa da dokokinsa. 24 Duk da haka, waɗansu mutane da kake mulki sun tayar mana, suna kashe duk wanda suka samu daga cikinmu, suna mai da gidajenmu ganima. 24 Suna faɗa mana su yi mana ƙwace, ba mu kadai ba, amma kowa ma a ƙasar. 25 Ga shi, yanzu sun kewaye kagarar Urushalima da yaƙi domin su ci ta, sun kuma ƙarfafa Wuri Mai Tsarki, da birnin Bet‑zur. 26 In ba ka yi sauri ka hana su ba, za su yi abin da ya fi haka muni, ba kuma za ka iya tsai da su ba.
Sauran Alumma sun Yaƙi Yahuza
28 Da sarki ya ji haka, sai ya yi fushi, ya kira dukan yan majalisarsa da jarumawan rundunarsa da shugabannin sojojin doki. 29 Sojojin ijara kuwa daga ƙasashen waje da na tsibiran teku suka zo domin su taimake shi. 30 Rundunarsa ta kunshi sojan ƙafa dubu ɗari, da sojan doki dubu ashirin, da giwaye talatin da biyu waɗanda aka hora musamman domin yaƙi. 31 Sai suka wuce ƙasar Edom, suka yi sansam kusa da birnin Bet‑zur. Suka yi kwanaki da dama suna harbin birnin, suna shirya wani irin tsani‑tsani na hawan garu, amma da suka gama, sai mutanen birnin suka fita, su ƙone su, don tsananin jaruntaka.
32 Saan nan Yahuza ya tashi daga kagarar Urushalima, ya mai da sansaninsa zuwa Bet‑zakariya, kusa da inda sansanin sarki yake. 33 Sai sarki ya tashi goshin asuba, ya tafi da rundunarsa da sauri zuwa Bet‑zakariya. Sai rundunar Yahuza da ta abokan gāba suka yi shirin yaƙi, lokacin da ake bushebushe. 34 Sai suka ɗirka wa giwaye giya domin su zama gwari, ba sane sai aiki a yaƙin. 35 Aka rarraba giwayen ga kowace runduna, kowace giwa tana da sojoji dubu masu sulke da hulunan kwano, tare da sojan doki ɗari biyar. 36 Duk sojan nan suka liƙe wa giwarsu, duk inda ta nufa suna biye da ita. 37 Aka ɗora wa kowace giwa wani irin ɗaki mai ƙarfi na itace, aka ɗaure shi da majayai. A kowane ɗaki kuma akwai soja uku da mai riƙon linzamin giwa guda Bahinde. 38 Aka sa sauran sojojin doki a dama da rundunar da hagunta domin su riƙa auka wa abokan gāba da hari, su dawo su fake da sauran runduna.
39 In rana ta haskaka garkuwoyin zinariya da na jan ƙarfe, sai tsaunuka su yi haske, har suna ɗaukar ido kamar madubi. 40 Wani sashi na rundunar sarki ya rufe tsauni, sashi guda kuma na cikin kwari, amma dukansu sun doshi birni a hankali bisa ga shiri. 41 Duk waɗanda suka ji motsin tafiyarsu da rugumin makamansu, sai suka firgita, gama rundunar gagaruma ce, mai ƙarfin gaske.
42 Sai Yahuza da rundunarsa suka taryi abokan gāba domin a kara, sai aka kashe mutane ɗari shida na rundunar sarki. 43 Wani mutum mai suna Eleazara Abarona ya ga wata giwa wadda ta fi saura girma, an daje ta da adon sarauta, sai ya yi tsammani sarki ne a kanta. 44 Ya yi kuru domin ya ceci mutanensa, ya kuma yi wa kansa madawwamin suna. 45 Ya ruga wajenta, ko da ya ke tana tsakiyar runduna, yana kashe mutane dama da hagun, sai mutane suka yi ta kayewa, suna ba shi hanya. 46 Sai ya shiga karkashin giwar, ya soke ta a ciki. Ta faɗi a bisansa, suka yi mutuwar kasko.
47 Da Yahudawa suka ga ƙarfin rundunar sarki da himmar sojojinta, sai suka ja da baya. 48 Sai sashen rundunar sarki ya tafi Urushalima domin ya kai wa birnin hari. Sarki ya kafa sansam kuma a wurare dabam dabam a ƙasar Yahudiya, da kusa da tsaunin Sihiyona. 49 Ya yi sulhi da mutanen birni Betzur, suka fita neman abinci, domin bai isa yadda za su daɗe suna jayayya da shi ba, gama shekaran nan ta bakwai ce ta hutu, ba a shuka. 50 Sai sarki ya shiga garin Bet‑zur, ya ajiye rundunar sojoji can, su tsare wurin. 51 Ya yi kwana da kwanaki yana kewaye da
Wuri Mai Tsarki na Urushalima, yana kafa waɗansu irin makamai masu jefa dutse, da wuta, da kibau. Yahudawa ma suka kafa nasu makamai, suka dade suna yaƙi. I I Amma abincin da ke cikin rumbuna ya ƙare, domin shekara ce ta hutu, gama sauran Yahudawa, wato yan gudun hijira zuwa Yahudiya, suna cinye musu abinci. Soja suka yi ta barin garin, sai kadan ne suka ragu a Wuri Mai Tsarki, sauran kuwa kowa ya yi ta kansa, domin yunwa ta yi tsanam.
An Yi Sulhu
55‑56 Kafin mutuwar sarki Antiyaku na huɗu, ya danƙa wa Filibus ɗansa Antiyaku don ya hore shi a kan shaanin sarauta. Sai Lisiyas ya ji labari Filibus ɗin nan ya dawo daga ƙasar Farisa da Mediya tare da runduna wadda ta bi sarki Antiyaku na huɗu, yana neman karɓar sarauta. 57 Nan da nan Lisiyas ya yi niyya ya bar Urushalima. Ya ce wa sarki, da jarumawan runduna, da sojoji, Ga shi, kullum ƙarfinmu sai raguwa yake yi, abincinmu ya yi mana kaɗan, wurin da muka kewaye kuma mai wuyar kamawa ne, wajibi ne mu kula da harkokin mulki. 58 Saboda haka sai mu yi sulhu da mutanen nan da dukan alummarsu. 59 Sai mu ba su yanci su bi aladunsu kamar dā, gama domin mun hana su bin aladunsu ne suka yi fushi, suka yi duk waɗannan abubuwa.
60 Da sarki da jarumawansa suka yarda da wannan shawara, sai ya aika da shawarar sulhu. Yahudawa kuma suka yarda da ita. 61 Sai sarki da jarumawansa suka yi rantsuwa. Bisa ga kaidodin rantsuwar, sai Yahudawa suka bar kagarar garin. 62 Amma da sarki ya shiga tsaunin Sihiyona, ya ga kuma yadda aka ƙarfafa shi, sai ya yi tuban muzuru, ya koma ya ba da umarnin a rushe garun. 63 Bayan haka ya tashi da sauri, ya koma birnin Antakiya, inda ya iske Filibus ne ya ci birnin. Sai Lisiyas ya yi yaƙi da shi, ya karɓe birnin ƙarfi da yaji.
7. Dimitiriyas na fari ya Ƙwace Mulki
1 A shekara ta ɗari da hamsin da ɗaya (161 B.C.) Dimitiriyas ɗan Saluku ya tashi daga Roma, ya iso da mutane kaɗan a wani birni da ke gaɓar teku, sai ya fara yin sarauta a nan. 2 Da Dimitiriyas ya yi shirin shiga fadar kakanninsa, sai sojoji suka kama Antiyaku na biyar da Lisiyas don a kai su wurin da Dirnitiriyas yake. 3 Da ya ji haka, sai ya ce, Ba na son ganinsu. 4 Sai sojoji suka kashe su, Dimitiriyas ya kwace gādon mulki, ya haye.
Bakadi da Alkima sun Yi wa Israilawa Ɓarna
5 Sai masu saɓo, da yan iska na Israilawa, suka zo gun Dimitiriyas. Alkima ne ya yi musu jagora, domin yana so ya zama babban firist. 6 Sai suka kai wa sarki wannan zargi na Israilawa, suka ce, Yahuza da yanuwansa sun hallaka abokanka, sun kuma kore mu daga ƙasarmu. 7 Yanzu dai, sai ka aika da wanda ka amince da shi, ya je ya ga ɓarna wadda Yahuza ya yi mana da ta ƙasar sarki, don ya ɗauko mana fansa a kansu da duk magoya bayansu.
8 Sai sarki ya zaɓi Bakadi, ɗaya daga cikin yan majalisar sarki, hakiman Yammacin Yufiretis kuma. Shi babban mutum ne a ƙasar, sarki ya amince da shi kuma. 9 Sai sarki ya aika da Bakadi da kuma babban jairin nan Alkima, wanda sarkin ya naɗa babban firist, don su ɗauko Israilawa fansa. 10 Sai suka tashi. Da isarsu ƙasar Yahudiya da babbar runduna, sai suka aika da manzanni waɗanda suka yi hirar daɗin baka ta yin sulhu, gun Yahuza da yanuwansa. 11 Amma Yahuza da yanuwansa, sai suka yi musu shirwa ta gane garin yan ƙosai, domin sun ga babbar runduna tana biye da su. 12 Duk da haka, sai wani taron malamai ya je wurin Alkima da Bakadi, ya nema a yi shirin gaskiya. 13 Wata ƙungiyar Yahudawa ce, da ake kira Hasidiyawa, ta fara nema a yi sulhu, 14 gama ta ce Ga wani firist a nan, jikan Haruna, ya zo tare da rundunar, ba zai cuce mu ba. 15 Firist ɗin nan, Alkima kuwa, ya yi maganar sulhu da su, har ya yi rantsuwa, ya ce, Ba za mu saɓa muku ko abokanku ba. 16 Sai suka amince da abin da ya ce. Amma sai da ya ɗaure sittin daga cikin Hasidiyawan, ba su kuma kwana a ran nan ba, don a cika Nassin:
Sun bar wa tsuntsaye, gawawwakin jamaarka,
Suka bar wa namomin jeji su ci
Gawawwakin bayinka.18 Sai tsoro da firgita suka auka wa dukan Israilawa, har suka ce, Amincinsu ba na gaskiya ba ne. Sun keta yarjejeniya da rantsuwar da suka yi.
19 Saan nan Bakadi ya tashi daga Urushalima ya kafa sansaninsa a ƙauyen Bet‑zaiti. Sai ya sa aka ɗadɗɗaure sojoji masu yawa waɗanda suka yar da shi, ya jefa su a wani ƙaton kududdufi mai zurfi. 20 Ya hannanta wa Alkima lardin Yahudiya, ya ƙara masa sojoji don su taimake shi, shi kuwa ya koma wurin sarki.
21 Alkima ma ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya riƙe matsayinsa na sarautar firistanci. 22 Sai duk waɗanda ke yi wa jamaa tarzoma suka goyi bayansa. Suka mallaki ƙasar Yahudiya, suka guma wa Israilawa baƙin ciki. 23 Da Yahuza ya ga duk masifun da Alkima da mutanensa ke kawo wa Israilawa fiye da yadda sauran alumma suka yi, 24 sai ya yi rangadin ƙasar Yahudiya domin ya hori mutanensa waɗanda suka gudu, sai ya hana su gusa koina. 25 Amma da Alkima ya ga Yahuza da mabiyansa suna ƙara ƙarfi, ya gane kuma ba zai iya hana su yin haka ba, sai ya koma wurin sarki, ya zarge su da laifofi masu tsanani.
Cin Nikanar Jarumin Dimitiriyas
26 Sai sarki ya aika da Nikanar, wani shahararren jaruminsa, wanda ya ƙi jinin Israilawa, ya ba shi umarni ya hallaka jamaa. 27 Da ya iso Urushalima da babbar runduna, sai ya aika wa Yahuza da yanuwansa wannan saƙon ƙarya na salama, inda ya ce, 28 Kada faɗa ya shiga tsakanina da kai. Zan zo da waɗansu yan rakiya kaɗan don mu yi saduwar salama.
29 Sai ya zo wurin Yahuza, suka yi wata gaisuwa mai lalama. Amma abokan gāba sun yi shirin kama Yahuza. 30 Da Yahuza ya gane Nikanar ya zo don ya yaudare shi ne, sai ya ji tsoro, ya ƙi komawa. 31 Da Nikanar ya ga an gane shirinsa, sai ya fita wani ƙauye, mai suna Kafara‑salama, don ya yaƙi Yahuza. 32 Nan take mutane kamar ɗari biyar na rundunar Nikanar suka mutu, sauran suka tsere zuwa Birnin Dawuda a Urushalima.
33 Bayan wannan, sai Nikanar ya tashi zuwa tsaunin Sihiyona. Sai waɗansu firistoci na Wuri Mai Tsarki da waɗansu dattawan jamaa suka fito don su tarye shi da salama, su kuma nuna masa hadayar ƙonawa wadda ake cikin miƙawa, don Allah ya ja zamanin sarki. 34 Amma ya yi musu dariya da baa, ya tofa musu yau don ya kazanta su yadda sai suka sāke yin wanka kafin su yi ibadarsu. Sai ya yi fariya da fushi, 35 ya yi rantsuwa, ya ce, In Yahuza da ƙungiyarsu ba su sallama mini kansu nan da nan ba, da na dawo bayan na yi nasara, zan ƙone Haikalin Allah ɗin nan. Sai ya fita a husace. Amma firistoci, suka tashi, suka shiga Haikalin Allah, suka tsaya a gaban bagade na Wuri Mai Tsarki, suka yi kuka da hawaye, suka ce, 36 Ka zaɓi wannan ɗaki tun dā, ka sa masa sunanka, ya zama ɗakin addua da roƙo don jamaarka. 37 Sai ka juya wa mutumin nan da rundunarsa baya, su haɗu da ajalinsu. Ka tuna da saɓonsu, kada ka bari su ci gaba.
39 Sai Nikanar ya bar Urushalima, ya ƙafa sansaninsa a kauyen Bet-horon, inda ya yi haɗin gwiwa da rundunar Suriyawa. 40 Amma Yahuza ya kafa sansaninsa a ƙauyen Adasa, shi da askarawa dubu uku. A nan ne ya yi wannan addua, ya ce, 41 A zamanin dā, lokacin da sarki Sennakerib ya yi cika baki, sai malaikanka ya fita ya kashe dubu ɗari da tamanin da biyar daga cikin sojansa. 42 Ka hallaka rundunan nan da ke gabanmu a yau, ta haka kowa ya sani Nikanar ba shi da gaskiya lokacin da ya cika baki game da Wurinka Mai Tsarki. Sai ka hukunta shi gwargwadon suɓul da baka da ya yi.
43 Sai runduna biyun nan suka ci karo da juna ran goma sha uku ga watan Adar. Aka cinye rundunar Nikanar, shi ne ma ya fara mutuwa. 44 Da askarawan Nikanar suka ga ya mutu, suka watsar da makamansu, suka gudu. 45 Sai Yahudawa suka yini suna binsu tun daga ƙauyen Adasa har zuwa gab da Gazara, suna busa kakaki, Ku tare mana. 46 Da jin haka, sai mutanen ƙauyukan da ke gaba da su suka fito, duka, ko ɗaya ba wanda ya kai labari.
47 Sai Yahudawa suka kwashe ganima, suka yanke kan Nikanar da hannunsa na dama wanda yake ɗagawa in yana fariya. Aka kai su Urushalima domin a nunnuna. 48 Sai jamaa suka yi ta tsallen farin ciki, suka mai da ranar ta babban idi. 49 Suka ce a riƙa yin wannan idi kowace shekara a ran goma sha uku ga watan Adar. 50 Bayan haka, sai aka yi zaman lafiya a ƙasar Yahudiya kamar na wata daya.
8. Yarjejeniya da Romawa
1 Yahuza yana da labarin halin Romawa, ta bijintarsu a wajen faɗa, da amincinsu gun waɗanda suka goyi bayansu. Sukan ƙulla zumunci da waɗanda suka nemi zumuncin. 2 Yana kuma da labarin yaƙe‑yaƙensu da jaruntakarsu lokacin da suka ci ƙasar Faransai, suka tilasta musu biyan haraji. 3 Har ma suka kwace maadinan zinariya da azurfa na Esbanya, 4 ta wajen hazikancin shirinsu da kuma niyyarsu ne har suka ƙwace ƙasar duka, ko da ya ke tana nesa da tasu. Koina a duniya duk sarkin da ya kai wa Romawa hari, sai su cinye shi, cikin biyu ya zaɓi daya, ko su kashe shi, ko kuma ya biya su haraji a kowace shekara. 5 Filibus, Sarkin Makidoniya, da Barsiyus magajinsa, da sauran waɗanda suka yi wa Romawa karo a yaƙi, sai aka cinye su, aka mallake su. 6 Sai Antiyaku na uku, shahararren sarkin nan na Asiya, ya yaƙe su da giwaye ɗari da ashirin, da sojojin doki, da babbar runduna, amma suka cinye shi. 7 Aka kama shi da rai, aka tilasta masa da magadansa su biya haraji mai ɗumbun yawa, su ba da kamammu 8 da lardunansu mafi kyau na Likiya da Misiya da Lud. Romawa suka kwace su, suka ba sarki Yumanesa su. 9 Da Helenawa suka yi shiri su zo su hallaka Romawa, 10 sai Romawan suka gane, suka aika da shugaba ɗaya ya yaƙe su. Aka raunata mutane da yawa, aka kashe su, sai Romawa suka kama matansu da yayansu, suka kwashe kayansu, suka amshe ƙasarsu, suka yamutse mafakansu, suka mai da su bayi har yau, har ma gobe. 11 Duk sauran ƙasashe da tsibirai waɗanda suka nuna masu ƙarƙo, sai suka hallaka su, suka mai da su bayi. 12 Amma suka ƙulla abuta da abokansu da waɗanda suka dogara gare su. Suka yi nasara bisa sarakuna na kusa da na nesa, da kuma duk waɗanda suka ji labarinsu suka tsorata da su. 13 Hakika duk waɗanda Romawa ke so su zama sarakuna, sun zama sarakuna, duk waɗanda suke so su tuɓe kuma, sun tuɓe. Don haka ake girmama su. 14 Duk da haka, ba wani sarki daga cikinsu wanda ya sa wa kansa rawani ko alkyabba don ya nuna sarauta. 15 Sun gina ɗakin majalisar wakilai, inda mutum ɗari uku da ashirin ke taruwa kowace rana, suna shawarta duk abin da ya shafi alumma da zaman lafiyarsu. 16 Suna zaɓen mutum ɗaya kowace shekara su danƙa masa ragamar mulkinsu, suna binsa sau da ƙafa, ba tare da wata hamayya ba.
17 Saboda haka ne, Yahuza ya zaɓi Yubalima ɗan Yahaya ɗan Akko, da Yason ɗan Eleazara, ya aika da su Roma domin su ƙulla zumunci da Romawa. 18 Ya yi haka ne kuwa domin ya karya mulkin mallakar Helenawa, domin mulkinsu yana mai da Israilawa bayi. 19 Bayan jakadan sun yi wannan tafiya mai nisa zuwa Roma, sai suka shiga majalisar wakilai, suka yi wannan jawabi, suka ce, 20 Yahuza, wanda ake kira Makabi, da yanuwansa, tare da alummar Yahudawa, sun aiko mu gare ku domin mu yi yarjejeniya ta salama da ku, mu yaƙi abokan gabanmu tare, mu kuma zama abokan juna. 21 Sai Romawa suka yarda da hakanan, 22 suka rubuta amsa a kan allunan tagulla, suka aika da su Urushalima domin a ajiye su can, su zama abin tunin salama da juna, da taimakon juna a yaƙi.
23 Ga abin da Romawa suka rubuta, suka ce, Mun ga ya yi kyau alummar Romawa da ta Yahudawa su yi zaman lafiya, su da askarawansu na teku da na kan tudu har abada, su kuma faskari kowane abokin gāba. 24 Amma in aka fara yaƙi da Romawa ko abokansu a koina cikin mulkinsu, 25 alummar Yahudawa za ta taimake su da zuciya guda, iyakar iyawarta, 26 ba kuma za su agaji waɗanda ke yaƙin Romawa ba, da hatsi, ko makamai, ko kuɗi, ko jiragen ruwa. Wannan ne abin da majalisar Roma ta zartar. Yahudawa za su cika wajiban nan, ba tare da wani lada ba. 27 Haka ne kuma, in aka fara yaƙi da alummar Yahudawa, Romawa za su taimake su da zuciya guda, iyakar iyawarsu, 28 ba kuma za su agaji waɗanda suke kai musu hari ba da hatsi, ko makamai, ko kuɗi, ko jiragen ruwa. Haka majalisar Roma ta zartar. Romawa za su cika wajibansu ba tare da munafunci ba. 29 Ta waɗannan kaidodi ne Romawa suka yi yarjejeniya da alummar Yahudawa. 30 In waninsu nan gaba zai so ya ƙara wani abu ko ya rage, zai yi shi yadda zai gami dukansu biyu. Abin da duk suka ƙara ko suka rage kuma zai ingantu.
31 Amma game da cutar da sarki Dimitiriyas ya yi wa Yahudawa, mun rubuta masa cewa, Me ya sa kake tsananta mulkin mallakarka a kan abokanmu da mataimakamnu Yahudawa? 32 In suka sāke kawo ƙararka, za mu yiwo kukan kura, mu da su, mu yaƙe ka ta kan tudu da ta teku.
9. An Kai wa Yahudiya Hari
1 Da Dimitiriyas ya ji Nikanar da rundunarsa sun mutu a bakin dāgā, sai ya aiki Bakadi da Alkima tare da rabin rundunarsa zuwa ƙasar Yahudiya. 2 Sai suka bi hanya zuwa jihar Galili, suka yi sansani kusa da hawa na ƙauyen Arbila, sai suka ci shi, suka kashe mutane da yawa. 3 A wata na fari ga shekara ta ɗari da hamsin da biyu (160 B.C.) suka yi sansani kusa da Urushalima. 4 Sai suka tashi daga Urushalima zuwa ƙauyen Biriya da sojan ƙafa dubu ashirin da sojan doki dubu biyu. 5 Amma Yahuza da zaɓaɓɓun askarawa dubu uku suka yi sansani a ƙauyen Alasa. 6 Da askarawansa suka ga yawan abokan gāba, sai suka yi fargaba, sojoji da yawa daga cikinsu kuma suka gudu daga sansanin, sai soja ɗari takwas ne kawai suka ragu.
7 Da Yahuza ya ga rundunarsa tana raguwa, ana kuma bakin yaƙi, sai ya firgita, domin ba yadda zai yi ya tattara sojansa da suka gudu. 8 Ko da ya ke ransa a ɓace yake, sai ya ce wa sauran, Mu kai wa abokan gābanmu hari, watakila za mu iya i musu.
9 Sai suka yi ƙoƙarin hana shi, suka ce, Ba ma iyawa. Bari mu sulale yanzu, mu dawo da danginmu, saan nan mu yake su. Mun yi kaɗan yanzu.
10 Amma Yahuza ya ce, Abin kunya ne in yi wa abokan gāba gudu. In ajalinmu ya zo, sai mu mutu da mazakuta domin danginmu, kada mu ba jikokinmu kunya.
Mutuwar Yahuza
11 Sai rundunar Bakadi ta tashi daga sansani, ta yi shirin yaƙi. Aka raba sojojin doki sashe biyu, dama da hagun, masu majajjawa da maharban kibiya suna gaban rundunar, saan nan kwararrun jarumawan na biye da su. 12 Bakadi yana sashen dama, sojojin doki kuma sun yi wa rundunar zobe, dama da hagun, sai suka kai hari da bushe‑bushen kakaki. Askarawan Yahuza, su ma suka busa nasu kakaki. 13 Sai ƙasa ta motsa saboda nishin ƙatti da ƙarar makamai, aka yi ta bugi in buga tun safe har zuwa faɗuwar rana. 14 Da Yahuza ya ga Bakadi yana sashen dama na zaɓaɓɓun askarawansa, sai Yahuza da nasa zaɓaɓɓun askarawa 15 suka yi kukan kura zuwa sashen dama na abokan gāba, suka tasa su gaba, har zuwa gangaren tsaunuka. 16 Amma da sashen hagu na abokan gāba suka ga an wartaki sashen dama, sai suka juya, suka bi Yahuza da askarawansa daga baya. 17 Sai aka yi yaƙi mai tsanani inda aka yi kare jini birni jini jeji. 18 Saan nan aka kashe Yahuza, sauran sojansa kuwa suka gudu.
19 Sai Jonatan da Saminu suka ɗauki ƙanensu Yahuza, suka rufe shi a kabarin kakanninsu a kauyen Modayin. 20 Dukan Israilawa suka yi makokin mutuwarsa. Sun yi kwana da kwanaki suna kuka, har ma suka ce, 21 Allah Sarki! Yanzu an kashe jarumin nan, macecin Israilawa. 22 Sauran ayyukan Yahuza da yaƙe‑yaƙensa da jaruntakarsa, da darajarsa ba a rubuta su ba, amma ya yi bijinta ƙwarai da gaske.
Jonatan ya kori Bakadi
23 Bayan mutuwar Yahuza, sai masu keta haddin sharia suka yi ta ɓullowa koina a ƙasar Israilawa, da yan fashi iri iri. 24 A lokacin nan aka yi yunwa koina, sai mutane da dama daga ƙauyuka suka riƙa yin cudanya da yan fashin nan. 25 Sai Bakadi ya zaɓi waɗansu Israilawa masu saɓo, ya mai da su waziransa a kasar. 26 Sai waziran nan suka farauci abokan Yahuza, suka kawo su gun Bakadi, wanda ya wulakanta su, yana yi musu baa. 27 Ba a taɓa ganin irin wannan masifa a ƙasar Israilawa ba, tun zamanin da annabawa suka ƙaura.
28 Sai dukan abokan Yahuza suka taru, suka ce wa Jonatan, Tun da ɗanuwanka Yahuza ya rasu, ba wani kamarsa wanda zai yi wa abokan gābanmu karo, wato su Bakadi da ƙungiyarsa. 29 Shi ya sa muka zaɓe ka yau ka zama sarkinmu da shugaba a matsayinsa, ka kuma yi mana yaƙi. 30 Tun daga lokacin, Jonatan ya yarda da shugabancin, ya zatma a matsayin ɗanuwansa Yahuza.
32 Da Bakadi ya ji wannan labari, sai ya nemi hanyar kashe shi. Amma Jonatan da ɗanuwansa Saminu, da dukan mutanensu suka gane hakanan, sai suka gudu zuwa hamadar Tekowa, suka yi sansani kusa da ruwan Asafar.
35 Sai Jonatan ya aika da ɗanuwansa Yahaya ya raka maƙiyayan da ke kula da dabbobin da ake yanka wa sojoji, zuwa gun abokan Nabatawa, su tambaye su izni su aɗana musu dabbobinsu masu yawa. 36 Amma waɗansu yayan Yambarawa na ƙauyen Medeba suka yi wa Yahaya fashi suka kwashe Yahaya da duk abin da yake da shi. 37 Bayan haka, sai aka kawo wa Jonatan da ɗanuwansa Saminu wannan saƙo, aka ce, Yambarawa suna ta yin babban bikin aure, yan ɗaukar amaryar mutane ne tasasa, suna nan tafe. Ita kuma yar wani attajiri ce na kasar Kanana a ƙauyen Nadabati.
38 Sai Jonatan da Saminu suka tuna yadda aka kashe ɗanuwansu Yahaya, suka hau tsauni, suka ɓoye. 39 Suna ta sauraro, suka hango taro mai hayaniya ɗauke da kayan amarya. Ango da abokansa suka fito taryar amarya da tambura, da sauran kaɗe‑kaɗe, da kaya mai yawa. 40 Sai Yahudawa suka auka musu daga maɓoyinsu, suka yaƙe su, suka raunata da dama daga cikinsu. Sai waɗanda suka tsira suka gudu zuwa wajen tsaunuka, in ana ta kai ba kayan amarya. 41 Ta haka aka kai da bikin aure janaiza, murna ta koma ciki. 42 Bayan Yahudawa sun gama ramuwar gayya don ɗanuwansu Yahaya, sai suka koma fadamar Kogin Urdun.
43 Da Bakadi ya ji haka, sai ya bangazo wata babbar runduna a ran Asabar zuwa gaɓar Urdun. 44 Sai Jonatan ya ce wa mutanensa, Mu tashi yanzu, mu yi yaƙi iyakar iyawarmu, gama yau ba damar gudu kamar jiya ko shekaranjiya. 45 Ga yaƙi gabanmu, a bayawnu kuma akwai ruwan Urdun, da fadama, da kurmi. Ba hanyar tsira. 46 Yanzu dai sai ku kai kukanku ga Allah, ya kiyaye ku daga abokan gābanmu. 47 Da aka buga, kowa ya ɗanɗana kowa, sai Jonatan ya zaro wani irin kolo, ya kai wa Bakadi bugu, amma Bakadi ya goce, ya ja da baya. 48 Da Jonatan ya ga ya ɗan girgiza abokan gāba, sai shi da mutanensa suka faɗa a Kogin Urdun, suka yi iwo zuwa wancan gaci. Amma abokan gāba ba su haye sun bi su ba. 49 A yar karawan nan da aka yi ta ɗan lokaci, sai da aka kashe mutanen Bakadi guda dubu.
50 Da Bakadi ya koma Urushalima, sai ya gina mafakai masu ƙarfi a ƙasar Yahudiya, a Yariko, da Imuwasu, da Bet‑horon, da Betel, da Timna, da Faratoni, da Tafoni, kowacce da garu mai tsawo da ƙofofi masu ƙyamare na dirkokin ƙarfe. 51 A kowace mafaka ya sa kungiya ɗaya don karƙon Israilawa. 52 Ya ƙarfafa birnin Bet‑zur, da Gazara, da kagarar Urushalima, ya kuma cika su da askarawa da abinci. 53 Ya kuma kama yan shugabannin ƙauyuka, ya tsare su a kagarar Urushalima.
54 A shekara ta ɗari da hamsin da uku (159 B.C.), wata na biyu, Alkima ya ba da umarni a buge katangan nan wadda take hana arna shiga fadar Wuri Mai Tsarki, ta haka ya rushe aikin annabawa. Amma da ya fara rushe shi, 53 sai hannuwansa da ƙafafunsa suka kwage. Sai ciwon ya hana shi ci gaba da aikin, ba ya iya buɗe baki, aka innace shi, ya kasa yin magana a kan shaanonin gidansa. 54 Daga ƙarshe ma sai ya mutu da babbar ukuba. 55 Da Bakadi ya ji Alkima ya rasu, sai ya koma gun sarki, ƙasar Yahudiya kuma ta sami zaman lafiya har shekara biyu.
58 Saan nan dukan masu saɓa sharia suka yi shawara, suka ce, Jonatan da abokansa suna zaman lafiya da lumana. Bari mu kirawo Bakadi, ya kama dukansu a hannu dare ɗaya. 59 Sai suka je, suka yi shawara da shi. 60 Da Bakadi ke fitowa da babbar runduna, sai ya aika da wasiƙu daga asiri zuwa ga duk mataimakansa a ƙasar Yahudiya, ya ce musu su kama Jonatan da abokansa. Amma suka kasa, domin an gane maƙarƙashiyarsu. 61 Har ma mutanen Jonatan suka kama wajen mutane hamsin na ƙasar waɗanda ke shugabantar ƙeta, suka kashe su. 62 Sai Jonatan, da Saminu, da abokansu, suka ɓoye cikin birnin Bet‑basi, da ke cikin hamada. Sai suka sake gina gine‑ginen kagaransa waɗanda aka rushe. 63 Da Bakadi ya gane wannan, sai ya tara duk rundunarsa, ya kuma aika wa sauran mutanensa waɗanda ke a ƙasar Yahudiya saƙo. 64 Sai ya zo, ya kafa sansani kusa da birnin Bet‑basi, ya yi tsammuka na hawan garu, da dai sauran makamai irin masu lalata birni. Ya yi kwanaki masu yawa yana yaƙin birnin.
65 Sai Jonatan ya bar ɗanuwansa Saminu a birni, ya fita da yar ƙungiyar mutane zuwa karkara. 66 Sai ya kashe Udamera da danginsa, da Fasironawa a sansaninsu, waɗanda suka nufa su taimaki mutanen Bakadi. 67 Sai Saminu da mutanensa suka fito daga birni, suka ƙone makaman abokan gāba, 68 suka yaƙi Bakadi, suka ci shi. Sai Bakadi ya yi baƙin ciki mai yawa. Saboda shirinsa ya bi ruwa, 69 sai ya yi fushi da masu saɓo waɗanda suka shawarce shi ya kai wa lardin hari. Ya kashe su da dama, sai ya yi niyyar koma wa tasa kasa.
70 Da Jonatan ya ji wannan labari, ya aika da jakadu, su nemi sulhu da Bakadi, su kuma roƙa ya ba kamammu yanci. 71 Sai Bakadi ya yarda da abin da Jonatan ya roƙa, ya yi rantsuwa, ba zai yaƙe shi ba har iyakar ransa. 72 Ya kuma saki kamammun da ya kamo daga ƙasar Yahudiya. Saan nan ya koma gida, bai sake zuwa ƙasar Yahudiya ba.
73 Sai a lokacin nan ne aka daina yaƙi a ƙasar Israila. Jonatan ya zauna a birnin Mikmash, yana mulkin jamaa, yana kuma hallaka Israilawa yan ɓata gari.
10. Tawayen Iskandari Ɗan Antiyaku
1 A shekara ta ɗari da sittin (152 10 B.C.), Iskandari mai suna Afifanesa, ɗan Antiyaku ya zo, ya ci birnin Talamayas. Mutanen garin suka marabce shi, har suka ɗora shi a gadon sarauta.
Dimitiriyas yana Neman Abutar Jonatan
2 Da sarki Dimitriyas ya ji haka, sai ya tara babbar runduna, ya fita ya yake shi. 3 Sai Dimitiriyas ya aika wa Jonatan wasiƙar salama, yana girmama shi, 4 domin yana neman abuta da Jonatan kafin Jonatan ya yi abuta da Iskandari, su taru su sarƙe shi, 5 domin Dimitiriyas yana tsoron Jonatan, zai tuna da dukan ƙetar da ya yi masa, da yanuwansa, da alummarsa.
6 Saboda haka ne Dimitiriyas ya ba Jonatan izni ya tara runduna da makamai kamar shi mataimakinsa yake. Ya kuma yi umarni a saki kamammun da ke a kagarar Urushalima. 7 Sai Jonatan ya tafi Urushalima, ya karanta wa dukan jamaa wasiƙar Dimitiriyas. Sojojin Dimitiriyas masu tsaron kagara, 8 sai suka ji tsoro lokacin da suka ji sarki ya ba Jonatan ikon tara runduna. 9 Amma suka fito da kamammu, suka ba Jonatan, Jonatan ya je ya dandanƙa su a hannun iyayensu. 10 Bayan haka sai Jonatan ya zauna a Urushalima, ya soma gyaran gine‑ginen birni. 11 Ya umarci maaikata su gina garu na tubulan dutse a kewaye da tsaunin Sihiyona, sai suka yi. 12-13 Sai sojan Dimitiriyas da ke a mafakan sauran biranen Yahudiya waɗanda Bakadi ya gina suka ranta ciki na kare, kowa ya koma gidansu. 14 A Bet‑zur kawai ne waɗansu Israilawa suka ragu waɗanda ke jayayya da Jonatan, ba su bin dokokin sharia, suna mai da Bet‑zur tasu mafaka.
Iskandari ya Rubuta Wasiƙa ga Jonatan
15 Da sarki Iskandari ya ji labarin alkawaran da Dimitiriyas ya yi da Jonatan, ya kuma ji labarin yaƙe‑yaƙen Jonatan da yanuwansa, da jaruntakarsu, da kuma wahalolin da suka sha, 16 sai ya ce, Ina za mu sami wani kamar Jonatan? Yanzu sai mu mai da shi abokinmu da mataimakinmu.
17 Sai ya aika wa Jonatan wasiƙa cewa, 18 Daga sarki Iskandari zuwa ga ɗanuwana Jonatan, gaisuwa mai yawa. 19 Bayan haka, mun ji labari kai jarumi ne wanda ya dace da abutarmu. 20 A yau mun naɗa ka babban firist na alummarka, za a kira ka ɗan majalisar sarki. Sai ka kula da jin daɗinmu, ka kuma ƙulla aminci da mu. Iskandari kuma ya aika masa da riga mai tsada da rawanin zinariya.
21 Jonatan ya sa tufafin ibada a wata na bakwai ga shekara ta ɗari da sittin (152 B.C.), a ranar Idin Bukkoki, ya tara runduna da makamai masu yawa.
Dimitiriyas ya Rubuta Wasiƙa ga Jonatan
22 Da Dimitiriyas ya ji wannan, sai ya firgita, ya ce, 23 Don me muka bar Iskandari ya riga mu yin abuta da Yahudawa? Ga shi nan, yanzu ya sami mādāfa. 24 Ni ma zan rubuta wa Yahudawa wasiƙar daɗin baki, in mika musu matsayan daraja da kyauta, domin su taimake ni.
25 Sai ya aika musu da wannan saƙo, ya ce, Gaisuwa mai yawa daga sarki Dimitiriyas ga alummar Yahudawa. 26 Bayan haka, mun ji yadda kuka ƙulla yarjejeniya da mu, kuka riƙa abuta da mu, ba ku kuma koma wurin maƙiyanmu ba. Saboda haka mun yi murna. 27 Sai ku ci gaba da amincewa da mu, mu ma za mu saka muku da alheri a kan abin da kuka yi mana. 28 Za mu ɗauke muku biyan haraji iri iri, za mu kuma yi muku kyauta mai yawa.
29 Yanzu na ɗauke wa dukan Yahudawa nauyin harajin shekara, da harajin gishiri, da kyautar da sarki ke karɓa. 30 Zancen sashi ɗaya daga cikin uku da nake karɓa na hatsi da, da rabin yabanyar itatuwa, daga yau ba zan ƙara karɓar kome ba daga ƙasar Yahudiya, ko daga lardunan nan uku da aka karɓe wa Samariya, aka ba Yahudiya. 31 Ba za a karɓi haraji daga Urushalima da sauran Yahudiya ba, ko daga ushuri da kuɗin fito da mamulkina ke samu. 32 Na ba babban firist na Yahudawa ikona kan kagarar Urushalima. 33 Kowane Bayahude wanda aka kama daga ƙasar Yahudiya, zuwa kowane lardin mulkina, na yanta shi, ba tare da karɓar kuɗi ba, na ma ɗauke musu duk harajinsu, har da jangali. 34 Bari dukan idodi, da ranakun Asabar, da ran amaryar wata, da ranakun ibadar nafila, da kwana uku na jajibirin idodin, da kuma kwana uku na bayansu, su zama ranakun hutu ga kowane Bayahude a ƙasar mulkina. 35 A waɗannan kwanaki ba wani mai ikon tambayar wanda yake bi bashi, ko kuma ya dame shi ta kowace hanya.
36 Bari a zaɓi Yahudawa, dubu talatin, a girka su, a sa su a rundunar sarki, a kuma ba su albashi kamar yadda sauran sojojin sarki ke samu. 37 Sai a ajiye waɗansu a muhimman mafakan sarki, a kuma ba waɗansu matsayan amana a siyasar mulki. Sai a zaɓar musu hakimai daga cikinsu. Su kuma bi nasu dokoki, kamar yadda sarki ya umarta a ƙasar Yahudiya.
38 Sai lardunan nan uku da aka karɓe wa Samariya su zama jihar Yahudiya, don su zama ƙarƙashin mutum daya, su yi wa babban firist biyayya, shi kaɗai. 39 Harajin birnin Talamayas da ƙauyukanta kuwa, na ba Wuri Mai Tsarki na Urushalima kyauta, don duk abin da Ɗakin Sujada zai bukata. 40 Kowace shekara zan ba Wuri Mai Tsarki kuɗin da suka kai jimillar shekel na azurfa dubu goma sha biyar daga kuɗin da sarki ke karɓa daga wurare dabam dabam. 41 Duk kuɗin da suka yi rara kuma, waɗanda hakimai ba su bayar don ibadar Wuri Mai Tsarki ba, kamar yadda suka saba yi dā, sai su bayar. 42 Ba kuma zan sāke karɓar shekel na azurfa dubu biyar daga ribar da Ɗakin Sujada ke samu ba, domin kuɗin nan na firistoci ne waɗanda ke shugabantar sujada. 43 Wanda duk ya yi gudun hijira zuwa Haikalin Allah a Urushalima ko fadodinta saboda kuɗin da sarki ke binsa, ko wani bashi dabam, za a sake shi duk da dukiyar da ya mallaka a mulkina. 44 Sarki zai biya kuɗin gyara gine‑ginen Wuri Mai Tsarki. 45 Sarki ne kuma zai biya kuɗin gina garun Urushalima, da na ƙarfafa shi da na gina garun sauran biranen Yahudiya.
Jonatan ya Goyi Bayan Iskandari, aka ma Kashe Dimitifiyas na Fari
46 Da Jonatan da jamaarsa suka ji an karanta wannan wasiƙa, sai suka ƙi gaskatawa, ba su yarda da ita ba, domin sun tuna da babbar ƙetar da Dimitiriyas ya yi a ƙasar Israilawa, da yadda ya wulakanta su. 47 Saboda haka ne ma, suka zaɓi Iskandari, domin shi ya fara yi musu maganar salama, sai suka zama abokansa na rai da rai.
48 Sai sarki Iskandari ya tara babbar runduna, ya yi sansani kusa da Dimitiriyas. 49 Sai biyunsu suka hakume da faɗa, amma Dimitiriyas ya ga ba dama, sai ya ruga, shi da rundunarsa. Iskandari na biye da shi, yana banke masa sojojinsa. 50 Iskandari ya yi ta fatattakarsu har faɗuwar rana. Ran nan ne aka ga bayan Dimitiriyas.
Yarjejeniya tsakanin Talomi da Iskandari
51 Sai Iskandari ya aika da jakadu zuwa gun Talomi, Sarkin Masar, da wannan saƙo, ya ce, 52 Yanzu ne na komo ga sarautata, na zauna a gadon tsohona, na tabbatar da mulkina ta cin Dimitiriyas, da karɓar mulkin ƙasata, 53 gama na yaƙe shi, na cinye shi da rundubarsa, na kuma mayar wa kaina da sarauta. 54 Saboda haka sai mu ƙulla abuta da junanmu. Ka ba ni yarka in aura. In na zama surukinka, zan ba ku kyautai masu yawa, kai da ita, waɗanda suka cancanta gare ku.
55 Sai sarki Talomi ya amsa, ya ce, Na yi murna da dawowarka ƙasar kakanninka da zamanka bisa gadon sarauta. 56 Zan yi maka abin da ka roƙa, amma sai ka sadu da ni a birnin Talamayas domin mu ga juna, zan kuma zama surukinka kamar yadda ka fada.
57 Sai Talomi ya tashi da yarsa Kiliyafatira daga Masar zuwa Talamayas a shekara ta ɗari da sittin da biyu (151 ko 150 B.C.). 58 Can ne sarki Iskandari ya sadu da shi. Talomi kuma ya ba shi yarsa Kiliyafatira aure. Aka yi babban bikin aure a Talamayas irin na yan sarakai.
59 Sarki Iskandari ya kuma rubuta wa Jonatan ya zo, su sadu. 60 Sai Jonatan ya tafi da kayan sarautarsa zuwa Talamayas, inda ya sadu da waɗannan sarakuna biyu, ya kuma ba su, su da abokansu, azurfa da zinariya da sauran kyautai masu yawa, don haka suka so shi. 61 Waɗansu mugayen Israilawa, masu keta haddin sharia, suka haɗa kai don su tuhumce shi, amma sarki Iskandari bai kula da su ba. 62 Sai ya ba da umarni a cire wa Jonatan rigarsa, a sa masa wata mai tsada. 63 Sarki kuma ya zaunar da shi kusa da shi. Sai ya ce wa alkalansa, Ku tafi da shi ƙofar fada, ku yi shela kada wani ya tuhumce shi a kowane hali, kada ma wani ya dame shi ta kowace hanya.
64 Da matuhumtansa suka ga an girmama shi ta yin shelan nan, da sa masa riga mai daraja da aka yi, sai suka gudu. 65 Sarki kuwa ya girmama shi, ya naɗa shi ɗan majalisarsa, da kuma hakimi da shugaba na lardin. 16 Sai Jonatan ya koma Urushalima da salama da farin ciki da ba sai an faɗa ba.
An Ci Afaloni, Jarumin Dimitiriyas na Biyu
67 A shekara ta ɗari da sittin da biyar (147 B.C.), Dimitiriyas na biyu, ɗan Dimitiriyas na fari, ya fito daga Karita zuwa ƙasar kakanninsa. 68 Da sarki Iskandari ya ji haka, ya damu kwarai, sai ya koma Antakiya. 69 Dimitiriyas na biyu kuwa ya naɗa Afaloni hakimin ƙasar Kilisuriya. Bayan Afaloni ya tara babbar runduna, sai ya kafa sansani kusa da birnin Yamaniya. Daga can ya aika wa Jonatan, babban firist, wannan saƙo.
70 Kai kaɗai ne ka gagare mu. Ana yi mini dariya saboda kai. Don me kake gwada mana ƙarfi a tsaunuka? 71 Idan ka amince wa askarawanka, sai ku sauko karkara, mu gwada ƙarfinmu, mu gani. Har ina da waɗansu askarawa daga birane. 72 Duba, ka gane kowanene ni, ko kuma suwanene mataimakana. An ce ba ku iya i mana, sabili da an kori kakanninku sau biyu daga cikin tasu ƙasa. 73 Yanzu ba za ku iya yin takara da sojojinmu na doki, da kuma runduna kamar wannan a karkara ba, inda ba dutse, ko tsakuwa, ko wurin tsira.
74 Da Jonatan ya ji saƙon Afaloni, sai hankalinsa ya tashi. Ya zaɓi mutane dubu goma, ya tashi daga Urushalima, ɗanuwansa Saminu ya kuma bi shi don ya taimake shi. 75 Sai ya kafa sansani kusa da birnin Yafa, amma mutanen birnin suka hana shi shiga, domin Afaloni yana da ƙungiyar sojoji can. Da Yahudawa suka kewaye birnin don su yaƙe shi, 76 sai tsoro ya kama mutanen birnin, suka buɗe kofofi, Jonatan ya ci Yafa.
77 Da Afaloni ya ji haka, sai ya tara sojan doki dubu uku, da sojan ƙafa ba iyaka. Ya kama hanya zuwa birnin Azotus, sai ka ce zai wuce, gama ko dā ma karkara yake nufin zuwa, domin yana da ɗumbun sojojin doki. 78 Sai Jonatan ya bi shi zuwa birnin Azotus, suka gwabza. 79 Amma Afaloni ya riga ya yi tsimin sojan doki guda dubu, suna ɓoye a baya. 80 Kafin Jonatan ya ankara da yan sari‑ka-noƙen da ke bayansa, an riga an kewaye askarawansa, aka yi ta harbinsu da kibau tun da safe har zuwa yamma. 81 Amma mutanen Jonatan ba su gudu ba, kamar yadda Jonatan ya sa musu a baka. Amma dawakan abokan gaba suka tafke. 82 Da sojan dokin suka gaji tiɓis, sai Saminu ya kai musu hari, ya cinye su, ya kuma sa su yi gudun tilas. 83 Sai suka warwatsu koina a karkara. Abokan gāba suka gudu zuwa Azotus, suka shiga Bet‑dagon, wato ɗakin gunkinsu, domin su ceci kansu. 84 Amma Jonatan ya ƙone garin Azotus, ya kuma mai da shi ganima, duk da ƙauyukansa. Ya kuma ɗirka wa ɗakin Dagon da mutanen da ke cikinsa wuta, ya kashe su duka. 85 Waɗanda aka kashe da takobi ko wuta, kamar mutum dubu takwas ne. 86 Sai Jonatan ya bar wurin, ya kafa sansaninsa a birnin Ashkelon. Mutanen birnin Ashkelon kuwa suka fito, suka tarye shi da shagulgula. 87 Sai shi da mutanensa suka koma Urushalima ɗauke da ganima mai yawa. 88 Da sarki Iskandari ya ji waɗannan alamura, sai ya ƙara wa Jonatan girma. 89 Ya kuma ba shi lambar girma ta zinariya, irin wadda yan sarakai ke sawa. Ya ba shi birnin Ekron da ƙauyukansa kyauta.
11. Yarjejeniya tsakanin Talomi da Dimitiriyas
1 Sarkin Masar ya tara askarawansa masu ɗumbun yawa, da jiragen ruwa masu yawa da nufin ya ci ƙasar da Iskandari ya mallaka, ya haɗa da tasa. 2 Sai ya shiga Suriya da kalmomin salama, mutanen birane ma suka buɗe masa ƙofofinsu, suka marabce shi, kamar yadda sarki Iskandari ya umarce su su yi, domin shi surukinsa ne. 3 Arnma da Talomi ya shiga biranen, sai ya kafa kagara a kowannensu. 4 Da ya isa Azotus, sai aka nunnuna masa ɗakin Dagon, wanda aka ƙone, da kufan birnin da ƙauyukansa, da gawawwakin da Jonatan ya kashe da takobi da wuta a watse koina gefen hanya. 5 Domin a haɗa sarki gāba da Jonatan, sai aka gaggaya masa duk abin da Jonatan ya yi, amma sarkin bai ce kala ba. 6 Sai Jonatan ya ci adonsa irin na sarki, ya tafi Yafa domin ya sadu da sarki. Suka gai da juna, suka kwana can. 7 Sai Jonatan ya raka sarki har zuwa kogin Alutari, daganan ya koma Urushalima.
8 Sai sarki Talomi ya ci biranen gaɓar teku, har Salukiya da ke gab da teku, yana ta ƙulla wa Iskandari maƙarƙashiya. 9 Ya aika wa sarki Dimitiriyas jakadu, yana cewa, Bari mu yi yarjejeniya da juna. In ba ka yata wadda Iskandari ya aura, za ka kuma sarauci ƙasar mahaifinka. 10 Na yi kuskure da na ba Iskandari yata, bugu da ƙari ma, har neman kashe ni ya yi. 11 Amma bisa ga gaskiya, abin da ya sa Talomi ya tuhumci Iskandari, yana kwaɗayin mulkin Iskandari ne. 12 Bayan Talomi ya kwace yarsa, ya ba Dimitiriyas ita, sai ya watsar da Iskandari, ƙiyayyarsu ta fito fili. 13 Sai Talomi ya shiga Antakiya, ya naɗa kansa Sarkin Asiya. Ta haka ne ya mallaki ƙasashe biyu, wato ƙasar Masar da ta Asiya.
Mutuwar Iskandari da ta Talomi
14 A lokacin nan sarki Iskandari yana jihar Kilikiya, domin mutanen jihar sun yi tawaye. 15 Da Iskandari ya ji labarin abin da Talomi ya yi, sai ya koma domin ya yaƙe shi. Talorni kuwa ya fita, ya kara da shi da babbar runduna, sai da suka yi wa Iskandari fata fata. 16 Iskandari ya tsira zuwa Arabiya. Nasarar Talomi ta sami tushenta 17 a lokacin da wani Balarabe mai suna Zabdiyel ya fille wa Iskandari kai, ya aika wa Talomi da shi. 18 Amma bayan kwana uku sai sarki Talomi ya rasu shi ma, mutanen mafakai kuma suka kashe mutanensa. 19 Ta haka ne Dimitiriyas na biyu ya zama sarki a shekara ta ɗari da sittin da bakwai (146 ko 145 B.C.).
Yarjejeniya tsakanin Jonatan da Dimitiriyas
20 A lokacin nan sai Jonatan ya tara mutanen Yahudiya domin su kai wa kagarar Urushalima hari, suka kuma kafa wa kagarar tsaunuka da sauran makamai. 21 Sai waɗansu masu keta haddin sharia, maƙiyan alummarsu, suka tafi gun sarki, suka gaya masa Jonatan ya kewaye kagarar da yaƙi. 22 Da Dimitiriyas ya ji haka, sai ya husata, ya tashi nan da nan zuwa Talamayas. Ya kuma rubuta wa Jonatan wasiƙa, ya yi masa umarni ya daina yaƙin, ya kuma sadu da shi don shawara a Talamayas, ba da jinkiri ba.
23 Da Jonatan ya ji warman, sai ya umarta a ci gaba da yaƙi. Ya kuma zaɓi wadansu dattawa da firistocin Israilawa, ya kutsa kai cikin hatsari, ba ko makami, 24 ya tafi gun sarki a Talamayas, ɗauke da azurfa, da zinariya, da tufafi, da waɗansu irin kayan kyauta dabam dabam, sai sarki ya marabce shi. 25 Ko da ya ke waɗansu masu saɓo na Israilawa sun tuhumci Jonatan da laifofi, 26 sarki ya girmarna shi gaban dukan yan majalisarsa, kamar yadda marigayan sarakuna suka yi. 27 Ya kuma tabbata shi a babban firist, ya mayar masa da dukan darajojin da yake da su da, ya sa shi a manyan shugabannin yan majalisarsa.
28 Sai Jonatan ya roƙi sarki ya ɗauke wa Yahudiya da lardunan nan uku nauyin haraji. Jonatan ya ƙara da alkawarin ba shi talanti ɗari uku maimakonsa. 29 Sarki ya yarda, ya kuma rubuta wa Jonatan wannan wasiƙa a kan alamuran nan.
30 Daga sarki Dimitiriyas zuwa ga ƙanena Jonatan da dukan alurnmar Yahudawa. 31 Gaisuwa mai yawa. Bayan haka, muna aika maka, don ka sani, maganar wasiƙa wadda muka aika wa Lasitanesa, ɗanuwan nan namu, a game da kai.
32 Gaisuwa daga sarki Dimitiriyas zuwa ga wansa Lasitanesa. 33 Bayan haka, saboda zumuncin da Yahudawa suke nuna mana, mun yarda mu yi wa alummarsu alheri, gama su abokanmu ne, masu cika magana. 34 Don haka, mun tabbatar musu da mulkinsu a kan ƙasar Yahudiya da kuma lardunan nan uku na Afarema, da Ludda, da Ramatayim. Dā mun karɓe su da ƙauyukansu daga Samariya, mun haɗa su da Yahudiya, domin mun ji daɗin mutanen da suka miƙa wa Allah hadayu dominmu a Urushalima, maimakon harajin da dā sarki yake karɓa daga wajensu kowace shekara na amfanin ƙasa, da yabanyar itatuwa. 35 Daga yau mun ɗauke musu biyan sauran abubuwa da suka wajabta su ba mu, kamar harajin ushiri, da harajin shekara, da harajin gishiri, da harajin da sarki ke karɓa don kansa. 36 Daga yanzu ba za a sāke tā da ko ɗaya daga cikin sharuɗan nan ba. 37 Ka tabbata ka yi fassarar wannan wasiƙa, ka ba Jonatan ita, domin a nuna fassara a fili bisa tsaunin Sihiyona.
Maƙarƙashiyar Tariho
38 Da sarki Dimitiriyas na biyu ya ga duk ƙasarsa ta zauna lafiya, ba shi kuma da maƙiya, sai ya sallami dukan askarawansa, amma banda sojojin ijara na tsibiran waje. Shi ya sa duk askarawan da suka yi wa waɗanda ya gāda aiki suka ƙi shi. 39 Da wani mutum, mai suna Tariho, wanda ke mabiyin Iskandari a dā, ya ga dukan askarawa suna gunaguni da Dimitiriyas sai ya tafl gun wani Balarabe, mai suna Almalakawi, wanda ya ke renon Antiyaku ɗan Iskandari. 40 Tariho ya dinga matsa wa Almalakawi ya ba shi ɗan, domin ya naɗa dan ya gaji ubansa. A yan kwanakin da Tariho ya yi gun Almalakawi, ya gaya masa duk abin da Dimitiriyas ya yi, da kuma yadda askarawansa suka ƙi shi.
Jonatan ya Taimaki Dimitiriyas
41 A lokacin nan sai Jonatan ya roƙi sarki Dimitiriyas ya janye askarawansa daga kagarar Urushalima da sauran mafakai, domin suna damun Israilawa. 42 Sai Dimitiriyas ya amsa wa Jonatan, ya ce, Ba haka kaɗai zan yi maka da alummarka ba, amma zan ba ka babban girma, kai da alummarka, a lokacin da ya kamata. 43 Amma ka yi mini wannan alheri, ka aiko da askarawa su yi mini yaƙi, gama duk askarawana sun yi tawaye.
44 Sai Jonatan ya aika masa da kwararrun askarawa dubu uku a Antakiya. Da suka isa wurin sarki, ya yi murna da zuwansu, 45 gama mutanen birni wajen dubu dari da ashirin, sun taru a ƙofar fada don su kashe shi. 46 Amma da sarki ya laɓe a fada, sai yan tawayen suka ci muhimman wurare na birnin, suka kuma kewaye fadar da yaki. 47 Sai Yahudawa suka goyi bayan sarki Dimitiriyas, suka taimake shi ta wurin watsuwa koina a birnin. Ran nan Yahudawa suka kashe yan tawayen kimmanin mutane dubu ɗari a birnin. 48 Suka kuma ƙone birnin bayan sun kwashe ganima mai yawa ta yan tawayen. Ta haka ne suka ceci ran sarki. 49 Da mutanen garin suka ga gari yana a hannun Yahudawa, sai suka karaya suka roƙi sarki da kuka, suka ce: 50 Ka yi mana sulhu, ka hana Yahudawa kai mana hari. Sai mutanen garin suka yar da makamai, aka yi sulhu. 51 Ta haka ne Yahudawa suka sami ɗaukaka wurin sarki da talakawansa, har suka shahara a koina a ƙasar da sarki ya mallaka. Bayan haka suka korna Urushalima ɗauke da ganima mai yawa.
52 Amma da sarki Dimitiriyas ya tabbatar da sarautarsa, ya kuma ga ƙasarsa na zaune lafiya, 53 sai ya karya duk alkawaransa, ya yi watsi da Jonatan. Maimakon ya yi wa Jonatan alheri, kamar yadda Jonatan ya yi masa, sai ya wulakanta shi ƙwarai.
Yarjejeniya tsakanin Jonatan da Antiyaku Ɗan Iskandari
54 Bayan haka Tariho ya kawo yaron nan Antiyaku, aka naɗa shi sarki. 55 Sai dukan askarawan da Dimitiriyas ya sallama suka bi Antiyaku, suka yaƙi Dimitiriyas suka yi masa korar kare. 56 Tariho kuwa ya kama giwaye, ya shiga Antakiya. 57 Sai sarki Antiyaku ya rubuta wa Jonatan wannan wasiƙa.
Na tabbatar da kai babbar firist, na ma naɗa ka sarkin lardunan nan huɗu, ɗaya na Yahudiya da uku na Samariya. Ina so ka zama dan majalisar sarki. 58 Ya ba shi tasoshin zinariya da kayan cin abinci, ya ba shi ikon yin amfani da jemon zinariya, ya kuma sa lamba irin na yan sarakuna. 59 Ya kuma naɗa Saminu, ɗanuwan Jonatan, hakimin lardi tun daga Taya, har zuwa iyakar Masar.
60 Sai Jonatan ya tashi, ya wuce ta ƙasar Falisɗinu, da Lebanon da biranensu. Dukan askarawan Suriya na biye da shi domin su taimake shi. Da ya isa Ashkelon, sai mutanen garin suka tarye shi da shagulgula. 61 Amma da ya tashi zuwa Gaza, mutanen Gaza suka kulle ƙofofinsu. Sai ya kewaye garin da yaƙi, ya ƙone shi, ya mai da ƙauyukan da ke kusa da shi ganima. 62 Sai mutanen Gaza suka roƙa ya yi sulhu da su. Ya kama yayan dattawansu, ya aika da su Urushalima. Sai ya ratsa garuruwa har zuwa Dimashƙu.
Jonatan ya Yaki Dimitiriyas na Biyu
63 Da Jonatan ya ji labarin shugabannin yaƙi na Dimitiriyas sun zo da babbar runduna zuwa birnin Kedesh a ƙasar Galili domin su tuɓe shi, 64 sai ya fita domin ya yaƙe su. Ya bar ɗanuwansa, Saminu, tsaron gida. 65 Sai Saminu ya kewaye birnin Bet-zur, ya yi kwana da kwanaki yana yaƙin wurin, yana hana mutane fitowa. 66 Da suka roƙi sulhu, ya yarda. Ya ce musu, Kowa ya san inda dare ya yi masa, ya mallaka birnin, ya sa wata ƙungiya a ciki.
67 A lokacin nan Jonatan da rundunarsa sun kafa sansani kusa da tekun Galili. Da gari ya waye suka tafi karkarar Hazor. 68 Ba su ankara ba, sai ga rundunar Dimitiriyas gab da su. Sai rundunar ta kai masa hari a karkara, bayan ta ajiye masa yan sari-ka-noƙe a tsaunuka. 69 Saan nan yan sari-ka-noƙen nan suka fito daga maɓoya, suka shiga yaƙi. 70 Dukan mutanen Jonatan suka gudu, ba wanda ya tsaya sai jarumawa Mattatiyas dan Absalom, da Yahuza ɗan Kalfi. 71 Sai Jonatan ya yage tufafinsa, ya yi ta yin hurwa da addua. 72 Sai ya sāke komawa bakin dāgā, aka shiga ɗauki ba daɗi, ya cinye abokan gāba, har suka gudu. 73 Da mutanensa waɗanda da suka gudu suka ga haka, sai suka dawo gunsa, suka taya shi bin abokan gāba, har zuwa sansaninsu na Kedesh. 74 Aka kashe askarawan rundunar Dimitiriyas dubu uku ran nan. Jonatan kuwa ya koma Urushalima.
12. Yahudawa sun Yi Yarjejeniya da Roma da Sufarta
1 Da Jonatan ya ga yin abuta da Roma da waɗansu wurare zai yiwu, sai ya aika da jakadu zuwa Roma domin su tabbatar da zumuncinsa da Romawa. 2 Ya kuma aika da wasiƙu zuwa Sufarta da waɗansu wurare don zumunci ya kahu da gindinsa.
3 Bayan jakadun sun isa Roma, sai suka shiga ɗakin majalisa, suka ce, Babban firist, Jonatan, da alummar Yahudawa sun aiko mu mu tabbatar da abuta da yarjejeniya waɗanda ke tsakaninmu da ku. 4 Sai Romawa suka ba su wasiƙu zuwa ga hakiman wurare dabam dabam, suna roƙonsu su ba jakadun nan amana a tafiyarsu zuwa ƙasar Yahudiya.
5 Ga wasiƙar da Jonatan ya rubuta wa Sufartawa. Ya ce, 6 Daga Jonatan, babban firist da majalisar alummar Yahudawa, da firistoci, da dukan sauran jamaa, zuwa ga yanuwansu Sufartawa. Gaisuwa mai yawa. 7 Bayan haka, muna aiko muku fassarar wasiƙar da marigayin sarkinku Ariyus ya taɓa yi wa Oniyas, marigayin babban firist, wadda ta ce mu yanuwan juna ne. 8 Oniyas ya marabci jakadunku, ya kuma karɓi wasiƙar da ta nuna abuta da taimakon juna ga yaƙi. 9 Ko da ya ke ba mu bukatar wasiƙu irin waɗannan, tun da littattafamnu masu tsarki ke ƙarfafa mana zuciya, 10 muna so mu aika muku da roƙonmu na sabunta abutarmu da dangantakarmu, don kada mu rabu da ku sam sam, gama an daɗe rabonku da aika mana da jakada. 11 Mu ma, ai, ba mu mance da ku ba a duk lokacin da muke yi wa Allah hadayu da adduoi na ranakun idodinmu da waɗansu ranaku, domin ya kamata yanuwa sun tuna da juna. 12 Muna murna da shahararku kwarai da gaske. 13 Amma masifu da yaƙe-yaƙe da yawa sun same mu, sarakunan da ke kewaye da mu kuma sun auko mana. 14 Lokacin yaƙe‑yaken nan ba mu so mu dame ku da yawan neman taimako, ku da sauran mataimakanmu. 15 Da taimakon Allah, mun tsira daga maƙiyanmu, su kuwa an ƙasƙanta su. 16 Saboda haka ne, muka zaɓi Numini ɗan Antiyaku, da Antifata ɗan Yason, muka aika da su zuwa ga Romawa, domin su tabbatar da yarjejeniyarmu ta dā ta abuta da taimakon juna a yaƙi. 17 Mun umarce su kuma, su je wurinku, su gai da ku, su kuma ba ku wasiƙarmu ta sabunta dangantakar. 18 Don haka, sai ku ba mu amsa game da wannan alamari.
19 Ga wasiƙar da aka aika wa Oniyas, 20 Daga Ariyus, Sarkin Sufartawa, zuwa ga Oniyas, babban firist na Yahudawa. Gaisuwa mai yawa. 21 Bayan haka, ina so in sanar da ku cewa mun sami wata takarda wadda ta ce Sufartawa da Yahudawa yanuwa ne, gama su biyu jikokin Ibrahim ne. 22 Tun da ya ke mun gane haka, yanzu don Allah ku rubuto mana, ku ba mu labarin abin da kuke ciki. 23 Mu yanzu, muna sanar da ku, cewa shanumnu da kayanmu duk naku ne, naku kuma namu ne. Saboda wannan, mun ba da umarni a gaya muku hakanan.
An Kori Dimitiriyas
24 Da Jonatan ya ji labarin shugabannin yaƙi na Dimitiriyas sun komo da rundunar da ta fi ta dā yawa, domin su kai masa hari, 25 sai ya tashi daga Urushalima, ya tafi ƙasar Hamat, domin ya yaƙe su kafin su shiga jiharsa. 26 Sai magewaya waɗanda ya aika zuwa sansaninsu suka dawo, suka ba da labari abokan gāba sun yi shirin kai wa Yahudawa hari a daren nan. 27 Saboda haka ne, da faɗuwar rana Jonatan ya umarci askarawansa, kada su saki jiki, kada ma su saki makamansu, amma su kasance da shirin yaƙi a kowane lokaci na dare. Ya kuma sa masu tsaro kewaye da sansanin. 27 Da abokan gaba suka ji labari Jonatan da askarawansa sun yi shirin yaƙi, suka firgita ƙwarai. Sai suka hura wutar jin dumi, suka ja da baya. 29 Amma da ya ke Jonatan da askarawansa suna hangen wuta, ba su san abin da ya kasance ba, har zuwa safe. 30 Saan nan Jonatan ya bi su, amma bai ci musu ba, domin sun riga sun haye kogin Alutari.
31 Sai Jonatan ya ratse, ya yaƙi waɗansu Larabawa masu suna Zabadawa, ya ci su, ya kuma ƙwace kayansu. 32 Sai ya ratsa ta Dimashƙu, ya keta dukan jihar.
33 Saminu kuma ya tashi, ya tafi har garin Ashkelon da mafakan da ke kewaye da shi. Sai ya koma Yafa, ya ci garin, 34 domin ya gane mutanensa suna niyyar ba da mafakan nan ga mataimakan Dimitiriyas. Ya bar ƙungiya a cikinsa, su tsare shi.
35 Da Jonatan ya dawo, ya tara dattawan alumma, suka yi shiri domin su gina mafakai a ƙasar Yahudiya, 36 su ƙara tsawon garun Urushalima, su kuma gina bango tsakanin kagara da birnin, ya bambanta kagarar da birnin, domin kada sojojin Dimitiriyas da ke a kagara su fito, su yi saye da sayarwa da mutanen gari. 37 Sai mutanen suka taru su gyara birnin, gama ɓarin gabas na garu ya zagce, ya faɗa cikin kwari. Suka kuma gyara wani sabon gari mai suna Kafinata. 38 Sai kuma Saminu ya gina birnin Adida a lardin Shafala, ya ƙarfafa garunsa da ƙyamare masu dirkokin ƙarfe.
An Kama Jonatan
39 Tariho ya nema ya zama Sarkin Asiya, ya tuɓe sarki Antiyaku. 40 Amma yana tsoron Jonatan zai hana shi, ya yaƙe shi. Sai ya tafi birnin Betsheyan, yana nufi ya kama Jonatan, ya kashe shi. 41 Sai Jonatan ya tafi ya yaƙe shi da zaɓaɓɓun askarawa dubu arbain, ya isa har Bet‑sheyan. 42 Amma da Tariho ya ga Jonatan ya iso da babbar runduna, sai ya ji tsoro ya yaƙe shi. 43 Maimakon haka, sai ya marabce shi, har ya yi ta sassada shi da dukan abokansa, ya ƙara masa kyauta. Ya kuma umarci abokansa da askarawan nan nasa, ya ce, Ku bi shi sau da ƙafa, kamar yadda kuke yi mini. 44 Sai ya ce wa Jonatan, Saboda me kake wahala da askarawanka? Ga shi, ba cikin yaƙi muke ba. 45 Sai ka zaɓi waɗansu askarawa su zauna da kai, amma ka sallami sauran su tafi gida, saan nan ka zo mu tafi Talamayas. Zan ba ka birnin duk da waɗansu mafakai tare da ƙungiyoyinsu da jarumawansu, in ƙyale ka can, in koma gida. Abin da ya kawo ni gunka ke nan.
46 Sai Jonatan ya yarda da man da aka shafa masa a baka, ya bi abin da aka ce masa, ya sallami askarawansa, suka koma Yahudiya. 47 Amma ya zaɓi askarawa dubu uku, daga cikinsu ya aiki dubu biyu zuwa Galili, ya ce sauran dubu ɗaya su raka shi. 48 Da fa aka shigar da Jonatan birnin Talamayas, sai mutanen birnin suka rurrufe ƙofolin garun, suka kama shi. Duk waɗanda suka shiga tare da shi, sai suka shassharɓa su da takuba.
49 Sai Tariho ya aika da sojan ƙafa da na doki zuwa Galili da babbar karkarar Bet‑sheyan domin su kashe dukan askarawan Jonatan. 50 Amma da mutanen Jonatan suka ji an kama Jonatan, an kashe yan rakiyarsa, sai suka ƙarfafa wa juna gwiwa, suka fita don a kara da su. 51 Da sojojin Tariho suka ga Yahudawa sun yi shirin yaƙin tsai da rai, sai suka ja da baya. 52 Ta haka ne waɗannan sauran mutane na Jonatan suka koma Yahudiya lami lafiya. Sai suka yi wa Jonatan da mutanensa makoki, suka ji tsoro kwarai. Dukan Israilawa suka yi kuka mai yawa.
53 Sai dukan alumman da ke kewaye da Israilawa suka nema su hallaka su. Suka ce, Tun da ya ke yanzu ba su da shugaba mai taimakonsu, sai mu yaƙe su, mu kawar da su, ba ma za a ƙara tunawa da su a duniya ba.
13. Saminu Shugaban Yahudawa
1 Da Saminu ya ji labarin Tariho yana tara babbar runduna domin ya shiga ƙasar Yahudiya ya yamutse ta, 2 ya kuma ga jamaa na jin tsoro da firgita, sai ya tashi zuwa Urushalima. A can ne ya tara jamaa, 3 ya yi musu gargaɗi, ya ce, Kun sani abin da ni, da yanuwana, da dangina, muka yi saboda Attaura da Wuri Mai Tsarki, kun sani kuma yaƙe‑yaƙe da masifun da suka shafe mu. 4 Saboda haka ne ma, duk yanuwana suka ba da ransu domin jamaarmu ta Israilawa, ni kaɗai na ragu. 5 Ba ni kuwa da niyyar tserewa a lokacin masifa, domin ban fi yanuwana daraja ba. 6 Maimakon haka, zan yi wa alummata da Wuri Mai Tsarki ramuwar gayya, da kuma matanku da yayanku, gama duk sauran alumma sun haɗa kai, sun ƙi jininmu, domin su hallaka mu.
7 Da jamaa suka ji wannan jawabi, duk suka ji wani sabon ƙarfi ya zo musu. 8 Da kakkausar murya suka ce, Kai ne shugabanmu maimakon yanuwanka Yahuza da Jonatan. 9 Sai ka shugabanci yaƙe‑yaƙenmu, za mu yi duk abin da ka ce mana mu yi. 10 Saminu ya tara duk majiya ƙarfi, ya sa su su gama gyaran garun Urualima, su ƙarfafa ta ta kowane ɓari. 11 Sai ya tura Jonatan ɗan Absalom zuwa Yafa da babbar runduna, sai Jonatan ya kori mutanen birnin, shi kuwa ya zauna can.
Ruɗi da Yaudarar Tariho
12 Sai Tariho ya tashi daga Talamayas da babbar runduna domin ya kai wa Yahudiya hari, yana tafe da Jonatan bawan yaƙi. 13 Saminu ma ya kafa sansaninsa a Adida, kusa da karkara. 14 Da Tariho ya ji labarin Saminu ya gāji ƙanensa Jonatan, yana kuma nufin ya yaƙe shi, sai ya aika da jakadu zuwa gare shi, da wannan saƙo, ya ce, 15 Mun tsare ƙanenka Jonatan a kan kuɗin da baitulmalin sarki ya biyo shi game da sarauta iri iri da ya yi, bai biya ba. 16 Don haka, sai ku aiko mana da talanti na azurfa ɗari da yayansa biyu don mu tsare su, mu tabbatar da Jonatan, in an sake shi, ba zai yi mana tawaye ba, saan nan za mu sake shi.
17 Ko da ya ke Saminu ya sani, ruɗinsa kawai Tariho yake yi, ya ba da umarni a ba da kuɗin da yaran, domin tsoron jamaa, kada su ce 18 Jonatan ya mutu domin Saminu ya ƙi aika wa Tariho kuɗin da yaran. 19 Sai ya aika da yaran da talanti ɗari, amma Tariho ya ƙi cika alkawarinsa na sakin Jonatan. 20 Daga baya sai ya kai wa ƙasar hari, ya yamutse ta. Askarawansa suka bi ta hanyar zuwa Adora, amma Saminu da rundunarsa suka yi ta binsu gindi gindi duk inda suka nufa. 21 Sai mutanen kagarar Urushalima suka tura manzanni gun Tariho, suna gargaɗinsa ya zo wurinsu ta hanyar hamada, ya kuma aika musu da guzuri. 22 Ko da Tariho ya riga ya shirya dukan sojansa na doki don su yi asubanci, amma ga shi, aka yi ruwan ƙankara a daren nan, ta daskare dukan fuskar ƙasa, har suka kasa tafiya. Sai ya bi ta wata hanya dabam zuwa Gileyad. 23 Lokacin da ya yi kusa da ƙauyen Baskama, ya sa aka kashe Jonatan, aka kuma rufe shi can. 24 Sai Tariho ya koma ƙasarsa.
Kushewar Jonatan
25 Sai Saminu ya aiki waɗansu su tafi su tono gawar ƙanensa Jonatan. Suka kawo masa, ya kuma rufe shi a Modayin, garin kakanninsa. 26 Dukan Israilawa suka yi makokinsa kwana da kwanaki. 27 Sai Saminu ya gina hasumiya da gogaggun duwatsu bisa kusheyin mahaifinsa da na yanuwansa don a tuna da su, hasumiyar mai tsawo ce, ana hangenta daga nesa. 28 Ya kuma gina waɗansu irin dala guda bakwai a jere don mahaifinsa da mahaifiyarsa da yanuwansa huɗu. 29 Kusa da dala-dalan nan ya gina ginshiƙan dutse, a bisansu ne ya sassaƙa siffofin garkuwoyi da jiragen ruwa don su zama abin tuni, har ma ga matafiya a jiragen teku ɗin. 30 Gine‑ginen nan waɗanda ya yi a Modayin suna nan kyam har kwanan gobe.
Yarjejeniya tsakanin Saminu da Dimitiriyas
31‑32 Sai Tariho ya hainci sarki Antiyaku. Ya kashe shi ya kwace masa sarautar Asiya. Ta haka ne ya kawo wa ƙasar masifa mai yawa. 33 Saminu ya karfafa mafakan da ke Yahudiya, yana kara wa ƙarfin mafakan hasumiyoyi masu tsawo da garuka masu faɗi da ƙyamare masu dirkokin ƙarfe. Ya kuma cika mafakan da abinci. 34 Saminu kuma ya aika da jakadu zuwa ga sarki Dimitiriyas yana roƙonsa ya ɗauke wa ƙasar nauyin haraji, gama Tariho lalata kasar kurum ya yi. 35 Sai sarki Dimitiriyas ya amsa masa da wannan wasiƙa.
36 Daga sarki Dimitiriyas zuwa ga Saminu, babban firist, da kuma ɗan majalisar sarakuna, da dattawa, da sauran alummar Yahudawa. Gaisuwa mai yawa. 37 Bayan haka, mun sami zinariya da reshen zaitun waɗanda ka aiko mana. Mun yarda mu yi sulhu da ku, mu kuma faɗa wa hakiminmu ya ɗauke muku nauyin haraji. 38 Duk abin da muka tabbatar muku dā, hakanan zai zama, mafakai kuma da kuka gina za su yi zamanku. 39 Mun yafe muku dukan kasawarku ta harajin da sarki ke karɓa, wanda ba ku biya ba, ba za a kara karɓar wani haraji dabam a Urushalima ba. 40 Waɗanda suka cancanci su yi mana wani aiki, za mu ɗauke su. Tsakanimnu da ku sai girma da arziki.
41 Ta haka ne, a shekara ta ɗari da sabain (142 ko 141 B.C.), an ɗauke mulkin mallakar sauran alumma daga ƙasar Israilawa. 42 Daganan kowa, in zai rubuta kwanan wata a littafin kwangila ko tarihi, sai ya rubuta, A shekara ta fari ga sarautar Saminu, babban firist, hakimi da shugaban Yahudawa.
An Ci Birnin Gazara da Kagarar Urushalima
43 A lokacin nan Saminu da askarawansa suka kewaye Gazara da yaƙi. Sai ya gina tsanin hawan garu, ya jingina shi da garun, sai ya hau, ya ci ɗaya daga cikin hasumiyoyinta. 44 Mutanen da suka ci hasumiyar, sai suka yi ta kutsa kai cikin birni, sun tā da hargitsi mai yawa. 45 Sai mutanen garin, duk da matansu da yayansu, suka hahhau garu, suka kece tufafinsu, suka yi kuwwa, suna roƙon Saminu ya yi sulhu, suna cewa, 46 Kada ka saka mana gwargwadon laifofinmu, amma gwargwadon jinƙanka.
47 Sai Saminu ya yi musu sulhu, bai hallaka su ba. Amma ya ce musu su fita daga birnin, ya kuma tsabtace gidajen da gumaka ke ciki. Ya shiga birnin, ana ta raira waƙoƙi da yabo. 41 Bayan ya kawar da duk ƙazaman abubuwa, sai ya zatmar da masu bin sharia a wurin. Ya ƙarfafa garun birnin, ya kuma gina wa kansa gida.
49 Da aka hana sojoffin da ke zaune a kagarar Urushalima fita zuwa kasuwa su sayo abinci, sai suka sha wahalar yunwa mai tsanani. Mutane da dama daga cikinsu kuma, yunwa ta yi ta kisansu. 50 Suka roƙi sulhu wurin Saminu, sai ya yarda. Amma ya kore su daga kagarar, ya kuma tsabtace ta, domin dā, da ƙazaman abubuwa a ciki. 51 Ran ashirin da uku ga watan biyu, a shekara ta ɗari da sabain da ɗaya (141 B.C.), sai Yahudawa suka shiga kagarar, suna ihu don murna, suna kaɗa rassan dabino, suna kuma yin kaɗe-kaɗe iri iri da waƙoƙin yabo, domin an i wa ƙadangarun bakin tulunan nan da ke damun alummar Israilawa, waɗanda suka gaje kagarar Urushalima. 52 Sai Saminu ya umarci a riƙa tunawa da wannan rana ta murna a kowace shekara. Ya kuma ƙarfafa garun da ke kewaye da tsaunin Haikalin Allah, wanda ke gefen kagarar. A nan ne Saminu da abokansa suka zauna. 53 Tun da Samirm ya ga ɗansa Yahaya ya kawo ƙarfi, sai ya mai da shi shugaban dukan askarawansa, ya ajiye shi a Gazara.
14. An kama Dimitiriyas
1 A shekara ta ɗari da sabain da biyu (140 B.C.) ne sarki Dimitiriyas ya harhada sojansa, ya gangara zuwa Mediya neman taimako domin ya kara da Tariho. 2 Da Arsaka, sarkin mutanen Farisa da na Mediya, ya ji har Dimitiriyas ya shigar masa ƙasa, sai ya aika da wani jaruminsa domin ya kamo shi, ya kawo shi da rai. 3 Sai jarumin nan ya tafi, ya auka wa Dimitiriyas ya kamo shi, ya kai wa sarki Arsaka shi a hannu, Arsaka kuwa ya jefa shi a kurkuku.
Yabon Saminu
4 Sai ƙasar ta zauna lami Iafiya a zamanin Saminu,
Ya nemi zaman lafiya na mutanen kabilarsa.
Su kuma suka yi naam da irin mulkinsa
Da darajarsa dukan kwanakin sarautarsa.
5 Babbar bijintarsa ita ce yadda ya ƙwace Yafa,
Ya mai da ita tashar jiragen ruwansa ga masu zuwa tsibiran teku.
6 Ya faɗaɗa gundumomin jamaarsa,
Ya mallaki kasar tangaran, har ba sauran ɓata gari.
7 Ya kama bayin yaƙi masu ɗumbun yawa,
Ya mallaki Gazara, da Bet‑zur, da kagarar Urushalima.
Ya kawar da abubuwan da ke mugaye daga cikin kagarar,
Ba kuwa wanda ya iya fafatawa da shi.
8 Sai Israilawa suka yi ta nomansu rai kwance,
Ƙasar kuwa ta yi amfanin gaske,
Itatuwan karkara kuma suka yi yayan gaske.
9 Sai dattawan garin suka yi ta zamansu gefen hanya, suna holewa,
A kowane loto, ba hirar da suke yi, sai ta ci gaba da suka samu,
Matasa masu ƙarfi, sai suka yi ta sa tufatin taka tsaran nan nasu na aikin soja.
10 Sai ya yi ta hangaza wa garin abinci,
Ya kuma aɗana shi da kaya irin na tsaro,
Sai da kwarjininsa ya sanu ga dukan duniya.
11 Ya kawo zaman lafiya a ƙasar,
Israilawa suka zama da babban farm ciki.
12 Kowa ya yi zamansa ba ƙishi, ba yunwa,
Ba kuma wanda zai gigita su.
13 Ai, ko maƙiyi ɗaya ba a bari a ƙasar ba,
Balle ya auka musu da yaƙi.
Sarakunan zamanin ma, ai, niƙe su, aka yi.
14 Sai ya yi ta ƙarfafa mutanensa waɗanda ke tagwarai,
Ya dukufa kan a kiyaye Attaurar Musa,
Ya wartaki kowane jairi da maƙetaci
15 Ya kuma yi wa Haikalin ɗaukaka sabuwa,
Ya arzuta shi da sababbin kayayyaƙin ibada.Saminu ya Yi Yarjejeniya da Roma da Sufarta
16 Da labarin ya iso Roma da Sufarta, cewa Jonatan ya rasu, sai mutane suka yi gayan baƙin ciki. 17 Amma da dai suka ji labarin Saminu, ɗanuwan nan nasa, ya gaje shi a kan shaanin firistoci, shi ne kuma uban ƙasar duka, da biranenta, 18 sai suka rubuta masa wasiƙu a kan allunan tagulla, domin su sāke sabunta yarjejeniya ta abuta, da taimakon juna a yaƙi, da irin matuƙar goyon bayan nan nasu waɗanda suka nunnuna wa yanuwansa, su Yahuza da Jonatan. 19 Aka kuwa karanta wa babban taro wasiƙun nan a Urushalima.
20 Ga wadda Sufartawa suka rubuta, su ma suka ce, Daga sarakuna da ƙusoshin garin Sufarta zuwa ga Saminu, babban firist, da dattawa, da sauran firistoci, da jamaa dai duka, ta yanuwansu Yahudawa ga baki daya. Muna yi muku barka da war haka. 21 Bayan haka, muna sanar muku, cewa jakadunku da kuka aiko mana sun sanar mana da irin bangirma da darajar da kuke da su, mun kuma yi matuƙar murna da wannan ziyara da suka yi mana. 22 Game da saƙon da suka kawo mana, mun sa an rubuta shi a littafin ayyukan majalisarmu kamar haka, cewa: Numini ɗan Antiyaku, da Antifata ɗan Yason, jakadun Yahudawa, sun zo gunmu don su sake sabunta abokantakarsu da mu. 23 Jamaa kuma ta karɓe su da hannu bibbiyu da matuƙar bangirma, har ma an rubuta jawabinsu a littafin da mulki ke sa manyan alamuranta, domin ya zama abin tuni ga mutanen Sufarta. An kuma aika wa babban firist Saminu da fassarar sanarwan nan.
24 Da aka yi haka, sai Saminu ya aiki Numini Roma ɗauke da wata babbar garkuwa ta zinariya, wadda kuɗinta suka kai jaka ɗari, don ya nuna yardarsa da yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
Yahudawa sun Girmama Saminu
25 Da Yahudawa suka ji abin da Saminu ya aikata, sai suka ce, Wane irin alheri ne za mu nuna wa Saminu da yayansa? 26 Ya zama ɗanuwa a gare mu, shi da dukan yanuwan nan nasa, sun tsaya tsayin daka, sun ragargaje magabtan IsraIlawa. Saboda haka, sai suka yi wani rubutu a kan allunan tagulla, suka ɗora su a waɗansu dirkoki can kan tsaunin Sihiyona.
27 Ga abin da suka rubuta, suka ce, A ranar goma sha takwas ga watan Alul a shekara ta ɗari da sabain da biyu ne (140 B.C.), wadda take shekara ta uku da shigar Saminu a sarauta ta babban firist da shugaban Israilawa, 28 a babban taron firistoci, da hakimai, da dattawa aka yi wannan sanarwa cewa: 29 A lokacin da ƙasar ta yi ta yawan hargitsi, ai, Saminu ne, ɗan Mattatiyas, wanda yake ɗan kabilar Yowariba, shi da yanuwansa suka sai da rai, suka kuma kare alummarsu daga shan wahala da keta haddin sharia da Wuri Mai Tsarki nasu. Ta haka ne suka jawo wa alummarsu babbar daraja. 30 Bayan Jonatan ya haɗa kan alummarsa, har ya zama babban firistinsu, sai ya bi kakanninsa lahira. 31 Da maƙiyansu suka yi shirin kai musu hari domin su sakwarkwata musu garuruwa, su ɓata musu Wuri Mai Tsarki, 32 sai Saminu ya sha ɗamara domin ya yi wa dangi faɗan gani. Ya yi ta angazar da tasa duniya wajen ba sojan alummarsa makamai da albashi. 33 Ya sa aka yi gine‑ginen tsaro a garuruwan Yahudiya, tun ba na Bet‑zur ba wadda take a kan iyakar Yahudiya, a inda abokan gāba suka tara makamansu dā, ya sa rundunar sojan Yahudawa a gun. 34 Ya kuma sa aka ƙarfafa garin Yafa, wadda take a bakin gaɓar teku, da Gazara, da ke kan iyakar Azotus, gun da abokan gāba suka mamaye dā can. Ya zaunar da Yahudawa a waɗannan birane, har ya biya musu kowace irin bukata domin su dogara, su miƙe. 35 Da jamaa suka gane amincin Saminu da darajar da yake nufin kawo musu, sai suka naɗa shi shugabansu da babban firistinsu saboda dukan irin ayyukan bijinta da ya riga ya yi, tare da nuna adalci da aminci ga alummar, da kuma ƙoƙarin ɗaukaka mutanensa da ya yi.
36 A ƙarkashin jagorancinsa ne suka yi ta tasa ƙyeyar sauran alumma, arna, gaba daga ƙasar, tun ba daga birnin Dawuda a Urushalima ba, inda suka gina wa kansu kagara domin su riƙa fita a kai a kai, suna ƙazanta Wuri Mai Tsarki da kewayensa. 37 Sai ya zaunar da sojan Yahudawa a kagaran nan, ya ma ƙarfafa gine‑ginensa don kare birnin, da dai duk ƙasar gaba ɗaya. Ya kuma kara tsawon garun Urushalima. 38 Saboda yin haka, sai sarki Dimitiriyas ya naɗa shi babban firist, 39 ya mai da shi ɗaya daga cikin yan majalisarsa, ya ba shi babban girma dai, 40 gama Dimitiriyas ya ji Romawa suna kiran Yahudawa abokansu, da mataimaka a yaƙi, da dangi, sun kuma yi wa jakadun Saminu babban marhabun.
41 Saboda haka, alummar Yahudawa da firistocinsu suka zartar da Saminu ya zama shugabansu da babban firist, har wani annabi macancanci ya zo, su ji abin da zai ce. 42 Suka ce shi ne ma babban shugaba ɗinsu, don ya kula da duk ibadar da ake yi a haikali da aikin jamaa na gayya, ya lura da ƙasa da kayan fadanta da mafakanta, 43 kowa kuma ya yi ta yi masa biyayya dole. Dukan kwangilar da za a rubuta a ƙasar sai da sunansa, sai ya rika sa tufafin sarakuna, masu adon zinariya. 44 Ba wani a cikin jamaa, ko firist, wanda yake da iko ya kashe ko ɗaya daga cikin kaidodin nan, ko ya ƙi bin umarnan Saminu, ko ya kira wata taruwar shawara a dukan ƙasar, sai da iznin Saminu, ba ma wani mai damar sa tufafin nan irin na sarakuna masu adon zinariya. 45 Duk wanda ya yi wani gigi, ko ƙin bin wata daga cikin kaidodin nan, sai a hukunta shi nan da nan.
46 Sai dukan mutane suka yarda Saminu ya yi sarautar jamaa a bisa ga waɗannan kaidodi. 47 Saminu ya yarda, ya kuma zama babban firist, da shugaba, da sarki na alummar Yahudawa, da firistocinsu. Ta haka ya zama shugaban ƙasar baki ɗaya, ba mai ce masa aa.
48 Jamaar Yahudawa suka umarci a rubuta wannan zance nasu a kan allunan tagulla, a lilliƙa su a wani muhimmin wuri a fadodin Haikali, 49 a kuma kai juyi guda, a ajiye wa Saminu da yayansa a baitulmali.
15. Wasiƙar Sarki Antiyaku na Bakwai
1 Antiyaku, ɗan sarki Dimitiriyas na biyu, ya aika da wasiƙa daga tsibiran teku zuwa ga babban firist da sarkin nan na Yahudawa, da dai sauran alummarsa ga baki ɗaya, 2 sai ya yi rubutu kamar haka,
Daga hannun sarki Antiyaku zuwa ga Saminu babban firist, sarki kuma, da shi da alummar Yahudawa, gaisuwa mai yawan gaske zuwa gare ku. 3 Tun da ya ke waɗansu sun yi shiga hanci da ƙudundune, sun karɓe mana ragamar mulkin da muka gāda kaka da kakanni, ni ina son sāke ƙwato shi, in mayar da shi a zaman lafiya, kamar yadda yake dā. Yanzu ma har na ɗibi sojan ijara masu ɗumbun yawa, na cika jiragenmu na ruwa, na yaƙi da su, 4 ina so in yi kukkutsa a ƙasar da sojojin nan, in yi ramuwar gayya a kan waɗanda suka hargitsa ƙasata, suka sakwarkwata garuruwa masu yawa na mulkina.
5 Don haka, ni ma yanzu na ɗauke maka duk iyakar harajin da waɗanda suka riga ni yin mulki suka ɗauke maka, na ba ka duk sauran abubuwan da suka alkawarta a yi maka, ni ma ko guda ba zan yar ba. 6 Ni, yanzu na ba ka iznin buga naku irin kuɗin kashewa masu hatiminka, da kai da alummarka za ku yi amfani da su a kasarka. 7 Na sallama maka Urushalima da Wuri Mai Tsarki. Dukan makaman da ka tara, da mafakan da ka gina, waɗanda suke a hannunka yanzu, na hannanta maka su. 8 Dukan kuɗin da ba ka biya baitulmali ɗin sarki ba, na yanzu da zuwa gaba, zan yafe maka su, ba sauran ka sāke biyansu nan gaba. 9 In har muka sāke samun ƙwace ƙasarmu, duk kai za mu ɗora wa girman, kai da alummarka, da Haikalin, domin dukan duniya ta san darajarka.
10 A shekara ta ɗari da sabain da huɗu (138 B.C.), sai Antiyaku ya yayi soja, ya auka wa ƙasan nan ta kakanninsa da yaƙi. Dukan sojojin mulkin da ke can suka kuwa goyi bayansa, sai kaɗan ne suka zauna gun Tariho. 11 Antiyaku ya wawari mai son fizgen mulkin, wanda aka wawara ya gudu zuwa birnin Dor a gaɓar teku, 12 da ya gane, ba shi da saa, har ma sojansa suna yi masa shewar dila, 13 sai Antiyaku ya kakkafa sansani gab da Dor, tare da sojan ƙafa kimmanin dubu ɗari da dubu ashirin, da dubu takwas na sojan doki. 14 Ya kewaye garin a lokacin da jiragen ruwansu na yaƙi ke harhaɗe gu ɗaya a teku. Aka yi wa birnin zobe ta ruwa da ta kan tudu, aka yi wa yan garin ƙofar rago, ba mai shiga, ba mai fita.
Saminu ya Sabunta Yarjejeniya da Roma
15 A lokacin nan sai Numini da sauran abokan tafiyarsa suka shigo daga Roma ɗauke da wasiƙun da aka rubuto wa sarakuna da larduna dabam dabam, wasiƙun da suka ƙunshi kalmomin da aka faɗa:
16 Daga hannun Lukiyus, shugaban yan majalisar Romawa, zuwa ga sarki Talomi na Masar, gaisuwa mai yawan gaske. 17 Waɗansu jakadu na Yahudawa sun zo mana nan bisa ga yarjejeniyar amincin da taimakon juna a yaƙi da ke tsakaninmu, domin mu sāke sabunta yarjejeniyar. Jakadun nan babban firist, Saminu, da dai duk jamaar Yahudawa ga baki ɗaya ne suka aiko su. 18 Sun kawo garkuwa ta zinariya waddu kuɗinta suka kai jaka ɗari. 19 Saboda haka mu ma muka yi niyyar rubuto wa sarakuna na ƙasashe dabam dabam, muna ja musu kunne a kan kada su dami jamaar Yahudawa, ko kuma su kai wa garuruwansu da karkararsu wani hari, kada ma su yi haɗin gwiwa da masu yaƙinsu ko kadan. 20 Mun ma shawarta, mun kuma yi naam da garkuwar da suka kawo mana. 21 In har waɗansu yan iska suka kuskura, suka zo gudun ɓuya nan gunku, ku hannanta wa Saminu firist, ya hore su bisa ga kaidar shariar Yahudawa.
22 Shugaban yan majalisar Romawa ya aika da fassarar irin wasiƙar gun sarki Dimitiriyas, da Atalus, da Ariyarati, da Arsaka, 23 da dai sauran lardunan, har da Sambasami da Sufarta, da Dilo, da Mindu, da Sikayona, da Kariya, da Samus, da Bamfiliya, da Likiya, da Halikanasus, da Rodusa, da Faseli, da Kos, da Sida, da Aradi, da Gotina, da Nidus, da Kubrus, da Kurani. 24 Har suka ba babban firist Saminu nasa shi ma.
Antiyaku ya Nuna wa Saminu Ƙiyayya
25 Amma a lokacin da Antiyaku ya yi wa garin Dor zobe, sai ya yi ta kai wa garin hari, ya ƙirƙiro waɗansu irin kayan faɗa kuma, ya tsare Tariho da su, ya hana shi shiga ko fita. 26 Sai Saminu ya aika wa Antiyaku da gogaggun sojoji dubu biyu, domin su taimake shi a gun faɗan, har ma ya aika da zinariya, da azurfa, da dai sauran kayan agaji masu yawan gaske. 27 Amma sai Antiyaku ya ƙeƙasa ƙasa, ya ƙi karɓa, maimakon haka ma, sai ya sassoke dukan yarjejeniyan nan da suka yi, shi da Saminu, ya ma sauya wa Saminu ɗin fuska gaba ɗaya.
28 Har ma Antiyaku ya aiki Atanobi, ɗaya daga cikin yan majalisarsa, don ya yi magana da Saminu ya ce masa, Don me yanzu ka mamaye Yafa, da Gazara, da kagaran nan na Urushalima, wato garuruwan da ke ƙarƙashin nawa mulki? 29 Ka bi su, ka sakwarkwace, kana yi wa mutanen garuruwan nan cin mutunci, ka ma ƙwace waɗansu gundumomi da dama waɗanda ke nawa. 30 To, yanzu dai kuwa, ka mayar mini da wuraren da ka amsa, waɗanda ba su a ƙasar Yahudiya. 31 Ko kuma ka biya jaka dubu ɗari biyar saboda biranen da ka rurrushe, da kuma kuɗin harajinsu su ma, jaka dubu ɗari biyar. In ba haka ba, to, za mu iso, mu yaƙe ka.
32 Lokacin da Atanobi, ɗayan nan daga cikin yan majalisar sarki, ya je Urushalima, ya ga Saminu da dukan darajar gidansa, ga dai kwanonin zinariya da na azurfa, da sauran wadata tsabarta, sai kawai ya dimauce don mamaki.
Da ya isar da saƙon sarki, 33 sai Saminu ya ce masa, Ai, ba wata baƙuwar ƙasa da muka ƙwace, ba mu ma yi wa wani baƙo fashi ba, amma mun nemi hakkin da kakanninmu suka bar mana gddo, wanda magabtanmu suka ƙwace mana ƙarfi da yaji. 34 Ga shi, koyanzu mun fara tasawa, muna kuma neman hakkin da kaka da kakanni suka bar mana. 35 A game da garuruwan Yafa da Gazara, waɗanda kake nema, su ne suka yi wa jamaarmu babban lahani, har aka sami damar ɓata mana gari. Amma su, a shirye muke domin mu saye su, ko sun kai jaka dubu dari.
36 Ba tare da ce wa Saminu i, ko aa ba, sai manzon nan ya husata, ya koma, ya faɗi abin da Saminu ya ce wa sarkin, da dukan cika baki da ya yi yana hurzarwa, da kuma girma da daraja da ya gani na Saminu. Da dai manzon ya gama faɗar jawabin, sai sarkin ya fāɗi, ya suma don fushi.
Yahaya Ɗan Saminu ya Ci Kandabayu, Jarumin Antiyaku
37 Sai Tariho ya shiga jirgin ruwa, ya ruga zuwa Artasiya. 38 Sarki Antiyaku ya naɗa Kandabayu shugaban sojan da ke a gaɓar teku, ya dangaza masa sojojin ƙafa da na doki. 39 Ya ce masa ya tafi da sojojin, su tunkari Yahudiya. Ya ƙara da cewa, a ƙarfafa birnin Kidron, a kuma ƙarfafa ƙofofinsa, don su yaƙi Yahudawa daga can. Sarkin kuwa shi sai ya fafari Tariho. 40 Da Kandabayu ya iso Yamaniya, ya yi ta wulakanta jamaa, yana kai wa Yahudiya hare‑hare, yana mai da Yahudawan da ya kama bayin yaƙi, ko ya kashe su. 41 Kamar dai yadda sarki ya umarce shi da yi, ya ƙarfafa Kidron, ya ajiye waɗansu askarawan doki da na kafa a garin, domin su tsare hanyoyin Yahudiya.
16.
1 Sai Yahaya ya zarce daga Gazara, ya gaya wa ubansa, Saminu, cewa ga abin da Kandabayu ke ta yi. 2 Da jin haka, Saminu ya kira yayansa biyu, Yahuza da Yahaya, ya ce musu, Kun ga ni da yanuwana da gidan ubana mun yaƙi dukan abokan gāban Israilawa, tun muna cikin ƙuruciyarmu har zuwa yanzu. Ai, mun kwaci Israilawa sau da yawa. 3 Amma kaito, ga shi, yanzu na tsufa. Duk da haka na gode wa Allah da yake kun balaga. Ku gāji matsayina da na yanuwana, ku fita ku yi wa alummarmu faɗan gaske. Allah kuma ya taimake ku.
4 Saan nan Yahaya ya zaɓi soja dubu ashirin na ƙafa da na doki daga cikin dukan ƙasar, ya aika da su su yaƙi Kandabayu. Suka yi zango a Modayin. 5 Daganan suka yi sammako, suka shiga karkara, har suka tarar da wani tukunkunjin soja na ƙafa da na doki, da kuma wani rafi a tsakaninsu. 6 Sai Yahaya ya fuskance su, shi da mutanensa. Da dai ya ga mutanensa sun ji tsoron haye rafin, sai shi ya fara hayewa. Da mutanensa suka ga ya haye, sai suka ce, Ai, mu ma za mu haye. Suka haye, suka bi shi. 7 Ya raba sojansa na ƙafa kashi biyu, ya sa dawakai a tsakiyarsu, gama sojan doki na abokan gāba sun fi bakin bunu yawa. 8 Da aka busa kakakin yaƙi, sai aka yi wa Kandabayu korar kare, shi da nasa mayaƙa. Aka kashe mutane da dama, sauran suka ce, Kai ar, mu mai da iri gida mana. Sai suka gudu zuwa mafakarsu. 9 A loton nan ne aka sami yi wa Yahuza, ɗanuwan Yahaya, rauni. Amma Yahaya ya fafari su Kandabayu, sai da ya kai su birnin nan na Kidron, gun nan da Kandabayu ya ƙarfafa dā. 10 Suna gudu, yana bi, har da suka kai hasumiyoyin nan na karkarar Azotus. Yahaya kuwa ya ƙone hasumiyoyin ƙurmus. Abokan gāba dai nan take sun yi rashin soja fiye da dubu biyu. Yahaya kuwa ya dawo lami lafiya, ya shiga gidansa a Yahudiya.
An kashe Saminu da Yayansa Biyu
11 Talomi ɗan Abubi ne aka zaɓa shugaban sojan karkarar Yariko. Ya mallaki azurfa da zinariya da yawa, 12 shi babban firist ne kuma. 13 Sai kishin zuci ya zabure shi, ya bukaci zama sarkin dukan ƙasar. Daganan ya yi ta neman zarafin kashe Saminu da yayansa. 14 Saminu wanda ke kaiwa da komowa yana kula da shaanin mulki, a loton ya iso Urushalima tare da yayansa Mattatiyas da Yahuza, a shekara ta ɗari da sabain da bakwai (134 B.C.), a watan goma sha ɗaya, watan nan da ake kira Shabati. 15 Sai Talomi ɗan Abubin nan ya yi musu marabar hainci a wata yar mafaka da ake kira Doku, wadda shi kansa ya gina, inda ya shirya musu ƙasaitacciyar liyafa, amma ya ɓoye dakarunsa a lungunan ɗakin liyafar. 16 Da Saminu da yayansa suka sha, suka yi tatil, sai Talomi ya yi zabura ya miƙe shi da jamaarsa, kowannensu ya saɓi makami, suka yiwo wa Saminu cida gaba ɗaya, suka kashe shi, shi da yayan nan nasa guda biyu, da waɗansu daga na bayansa. 17 Sai ya aikata babban abin kunya, ya saka alheri da mugun abu.
18 Saan nan Talomi ya rubuto labarin alamarin da ya faru, ya aika wa sarki, yana roƙa a ba shi sojoji, a kuma hannanta masa mulkin ƙasar. 19 Sai ya aiki waɗansu jamaa zuwa Gazara ya ce su yanka Yahaya, a kuma sanar da shugabannin sojan ƙasar duka su zo su karbi azurfa da zinariya da kyautai masu yawa, 20 ya ma aiki waɗansu, ya ce su gaji Urushalima da tsaunin Wuri Mai Tsarki.
Yahaya Ɗan Saminu ya Gaji Ragamar Mulki
21 Amma har wani ya riga Talomi ya sanar da Yahaya a Gazara cewa, ai, mahaifinsa da yanuwansa sun halaka, suka ƙara da cewa, Yanzu ma kai kaɗai ne ka ragu na waɗanda Talomi zai kashe, zai kuwa kashe ka in ka yi sakaci. 22 Da Yahaya ya ji haka, mutane suka zo kama shi, sai shi ya same su, ya kashe, gama ya riga ya san shirinsu tun kafin su iso.
23 Ai, sauran ayyukan Yahaya, da yaƙin da ya yi, da jaruntakarsa da ya yi, yadda ya sāke ginin garun garin, da dai sauran ayyukan da ya yi, 24 duk, ai, suna nan a rubuce a littafin tarihinsa na babban firist, tun daga ran da ya hau karagar mahaifinsa a babban firist.
* * * * *
* * *
*