LITTAFI NA BIYU NA
MAKABAWA

1. Wasiƙa ta fari wajen Shekara ta 124 kafin zuwan Almasihu, zuwa ga Yahudawan Masar

1 Yahudawan Masar, gaisuwa mai yawan gaske, daga yanuwanku Yahudawan Urushalima da na sauran ƙasar Yahudiya.  Muna fata kuna zaman ci gaba da kuma jin daɗi. 2 Allah ya sa muku albarka, ya cika alkawarin nan da ya yi da Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu, bayin nan nasa. Amin. 3 Allah ya sa ku bauta masa, ku bi nufinsa da aniya da farin rai. 4 Allah ya sa ku bi shariunsa da kaidodinsa, ya kuma ba ku salama. 5 Allah ya ji adduoinku, ku sulhuntu, ya raba ku da tsaka mai wuya. 6 Muna nan, muna ta yi maku adduoi.

7 A zamanin da Dimitiriyas ke a kan gadon sarauta, a shekara ta ɗari da sittin da tara, mun taɓa rubuta muku wata wasiƙa, inda muka yi magana a kan cin mutuncin nan da aka yi mana ta wurin Yason a loton da shi da abokansa suka lalata ƙasa mai tsarki, suka yi wa shugabanninta tawaye, 8 suka ƙone ƙyauren Ɗakin Sujada, suka kuma zubar da jinin adalai. Da muka roƙi Ubangiji, ya kuma amsa mana, muka yi wa Allah hadaya tare da sadakar garin alkama, muka kunna fitilu, muka kintsa gurasa curi curi. 9 Muna so ku yi idin nan na tsarkake Haikalin Allah a watan nan na Kisle.

10 Mun hatimci wannan wasiƙa a shekara ta ɗari da tamanin da takwas.

Wata Wasiƙa, ta Shekara ta 164 kafin Almasihu a kan Idin Tsarkake Haikalin

Daga mutanen Urushalima, da na Yahudiya, da yan majalisa, da shugaba Yahuza, zuwa ga Aristobulus, malamin mai girma, sarki Talomi, wanda kuma ke da dangantaka da shafaffun firistocin nan. Kai da Yahudawan da ke zaune a Masar, gaisuwa mai yawa gare ku da fatan alheri.

11 Tun da ya ke Allah ya dube mu da rahama a kan babban zaluncin da aka shirya yi mana, mun yi masa matuƙar godiya da ya ɗora mu a bisa sarki Antiyaku na huɗu. 12 Gama Allah ne ya koro waɗanda suka kai wa birni mai tsarki hari. 13 Domin kuwa a lokacin da shugaban yaƙinsu da jamaarsa masu taurin zuciya suka isa ƙasar Farisa, sai aka hallaka su da shugaba nasu a gidan gunkin nan Naniya, ta munafuncin da sarakunan tsafi suka yi. 14 Gama Antiyaku da yan majalisarsa sun gangaro garin da nufi ya auri Naniya, ya gaji dukiyar da ke a gidan ibadarta. 15 Da sarakunan tsafi na Naniya suka baza waɗannan kaya, Antiyaku ya shiga gidan ibadar, shi da waɗansu mabiyansa. Da dai ya shiga wurin, sai sarakunan tsafi suka kulle ƙofofin. 16 Kana suka buɗe rufin gidan, suka jibga musu duwatsu a kā, suka kashe su, wato shi da mabiyansa. Suka yanyanka su, suka fiffille musu kawuna, suka watsar a waje. 17 Albarka ta tabbata ga Allahnmu, wanda ya sa marasa binsa su ɗanɗana kuɗarsu.

18 Da ya ke za mu yi bikin tsarkake Haikalin Allah ran ashirin da biyar ga watan nan na Kisle, mun ga ya kamata mu gaya muku, domin ku ma ku yi Idin Bukkoki da kuma na wuta wadda ta bayyana a lokacin da Nehemiya, wanda ya sake gina Haikalin Allah da bagadensa, yake miƙa hadaya. 19 Gama lokacin da aka kori kakanninmu zuwa ƙasar Farisa, firistocin ɗin kirki na lokacin, sun ɗibi wutar daga kan bagaden, sun ɓoye ta a wata tsohuwar rijiya marar ruwa, har ba wanda ya san inda take. 20 Da aka yi yan shekaru, da ikon Allah, sai Nehemiya, wanda Sarkin Farisa ya amince wa, ya aiki jikokin firistocin da suka ɓoye wutan nan su tono ta. 21 Amma suka ce mana ba su sami wutar ba, sai wani ruwa mai kamar taɓo. Sai Nehemiya ya umarci su, su ɗebo taɓon nan kaɗan, su kawo. Da aka shirya kayan hadaya tsaf, sai Nehemiya ya umarci firistoci su yayyafa taɓon a itacen duk da abin da ke a kan itacen. 22 Da gama haka, rana ta fara haskakawa, da ya ke dā ta dushe, sai wuta ta kama balbal, sai kowa da kowa ya yi mamaki. 23 Da aka fara gasa naman hadayar, sai firistoci da dukan waɗanda ke tare da su suka fara yin addua gaba ɗaya, Jonatan na faɗa, sauran na amsawa tare de Nehemiya.

24 Ga yadda suka yi addua, suka ce: Ya Ubangiji, Ubangiji Allah Mahaliccin dukan abu, kana da bantsoro, ƙaƙƙarfa ne kai, adali, mai jinkai. Kai kaɗai ne Sarki mai amfanawa. 25 Kai kaɗai ne mai bayarwa, kai kaɗai ne adali, Mai Iko Dukka, Madawwami. Kai ne mai raba Israilawa da kowace tsaka mai wuya. Kai ne ka mai da kakanninmu zaɓaɓɓunka, ka kuma tsarkake su. 26 Ka karɓi wannan hadaya saboda dukan jamaarka Israilawa, ka kāre jamaar da ke abin gādonka, ka kuma tsarkake su. 27 Ka tattara dukanmu da aka warwatsa gu ɗaya, ka sa a yanta bayin da ke bauta wajen sauran alumma, ka dubi waɗanda ake tsanantawa da rahama, ka kuma sa sauran alumma su sani kai ne Allahnmu. 28 Ka hori waɗanda ke matsa mana lamba, suna ci mana mutunci. 29 Ka sa jamaarka su kahu da gindinsu a Wuri Mai Tsarki ɗrin naka kamar dai yadda Musa ya alkawarta.

30 Saan nan sai firistoci suka raira waƙoki. 31 Lokacin da hadayar ta ƙone ƙurmus, sai Nehemiya ya umarci a yayyafa sauran taɓon a kan waɗansu manyan duwatsu. 32 Da yin haka, sai wuta ta kama. Amma hasken harshen wutar da ke a kan bagade ya zarce na wadda ke a kan duwatsu. 33 Da aka ji ɗuriyar haka, har Sarkin Farisawa ma ya ji cewa a wurin da firistocin nan yan gudun hijira suka ɓoye wuta wani ruwa ya bayyana, wanda da shi ne Nehemiya da jamaarsa suka ƙona kayan mika hadaya. 34 Da sarki ya gano gaskiyar alamarin, sai ya sa a kewaye wurin da dami, a mai da shi wuri mai tsarki. 35 Sai sarki ya yi ta samun maƙullan kuɗi a wurin, yana rarraba wa waɗanda yake so ya girmama. 36 Nehemiya da jamaarsa suka kira wurin Nafatari. Maanar wannan kalma ita ce tsarkakewa, amma an fi kiransa Nafata, (wato fetur ko baƙin mai).

2.

1 A takardun tarihi sai muka ga Irmiya ya ba waɗanda aka sa yan bautar talala su ɗan ɗibi wutan nan da muka ambata, su tafi da ita. 2 Ya kuma ba su Shariar Allah, yana ja musu kunne, cewa ko kusa kada su yarda su mance da dokokin Ubangiji, ko kuma su bari tunaninsu ya bauɗe, ya koma a kan gumakan azurfa da zinariya duk da adon nan nasu. 3 Ta irin waɗannan maganganu ya yi musu gargaɗi kada su yarda su bari zuciyarsu ta yi watsi da sharia. 4 A takarda ce kuma aka ga inda, bisa ga wahayi daga wurin Allah, annabi Irmiya ya umarta a bi shi da alfarwar da akwatin alkawari, a loton da zai hau dutsen nan da Musa ya hau domin ya duba ƙasan nan da Allah ya alkawarta wa Israilawa. 5 Da Irmiya ya isa wurin, sai ya iske wani wurin zama na kogon dutse, a can ciki ne ya ajiye alfarwa, da akwatin alkawari, da kuma bagade na ƙona turare. Bayan haka, sai ya rufe ƙofar wurin. 6 Wadansu daga cikin abokan tafiyarsa suka matsa masa su sa wata yar alama ta gane wurin, amma kafin su iso sai wurin ya ɓace musu. 7 Da Irmiya ya gane haka, sai ya yankar musu ƙauna, inda ya ce, 8 Wannan wuri zai kasance a ɓoye sai ran da Ubangiji ya sāke tara jamaarsa, ya nuna musu jinƙai. 9 Saan nan ne Ubangiji zai bayyana waɗannan abubuwa a fili, za a kuma ga ɗaukakar Ubangiji cikin girgije, kamar dai yadda aka nuna a zamanin Musa, da kuma loton da Sulemanu ke yin addua domin Wuri Mai Tsarki ya sami babbar ɗaukaka.

9 Sai an gano yadda Sulemanu, bisa ga hikimarsa, ya miƙa hadaya ta keɓe Wuri Mai Tsarki da kuma kintsuwarsa. 10 Kamar yadda Musa ya yi addua ga Ubangiji wuta kuma ta sauko daga sama, ta lashe kayan hadayar, haka ne Sulemanu, shi ma ya yi addua, wuta kuwa daga sama ta ƙone hadaya ƙurmus. 11 Musa ya taɓa cewa, Saboda ba a ci ba, shi ya sa hadayar da aka yi don zunubi ta ƙone ƙurmus. 12 Sai Sulemanu ya bi gurbin Musa, ya sa aka yi ta idin har kwana takwas.

13 Banda waɗannan abubuwa da muka ce ma, takardun nan da kuma wani littafin tarihi daga hannun Nehemiya sun bayyana yadda Nehemiya ya buɗe wani ɗakin karatu, ya cika shi da littattafai masu tarihin sarakuna, da rubuce‑rubucen annabawa da na sarki Dawuda, da wasiƙun sarakuna a kan yin hadaya. 14 Haka ma Yahuza ya tara irin waɗannan littattafai da aka barbaza a lokacin yaƙi. Ga shi, waɗannan sun fāɗa a hannumnu. 15 In ma kuna bukatar waɗansu daga cikinsu, to, ku aiko wani ya karɓar muku.

16 Mu dai mun takaice muku zancen. Tun da ya ke yanzu za mu yi idin tsarkakewa na Haikalin Allah, muna rubuta muku, muna so ku yi naku idin. 17 Allah ne wanda ya fanshi dukan mutanensa ya kāre dukan abin gādonsu, da mulkinsu, da sarautar firistocinsu, da kuma tsarin ibada, 18 kamar yadda ya alkawarta ta wurin sharia. Mun tabbata zai nuna jinƙansa ba da jinkiri ba, ya harhaɗa mu daga kowace fuska zuwa ga tsattsarkan wurin nan, tun da ya ke ya ƙwato mu daga manyan tsakoki masu wuya, ya kuma tsarkake wurin nan nasa.

Gabatarwa

19 Ga tarihin Yahuza Makabi da na yanuwansa, da na yadda aka tsarkake Haikalin nan mai girma na Allah da bagadensa. 20 Tarihin nan kuma ya ƙunshi yaƙe‑yaƙen da aka yi da sarki Antiyaku Afifanesa da ɗansa Yufatari, 21 da labarin alamun nan daga sama waɗanda suka ƙarfafa zuciyar jarumawan nan masu yaƙi na gaske domin addininsu, ta yadda, ko da ya ke ba su da yawa, duk da haka suka ƙwace ƙasarsu, suka kori bare fata fata, 22 suka sāke gano Wuri Mai Tsarki wanda ke sananne a dukan duniya. Suka yanta birni, suka sāke kafa dokokin da aka kusa mancewa da su. Ubangiji kuwa ya yi ta nuna musu dukan alherinsa. 23 Dukan wannan ya sanu ta littattafan nan biyar na Yason, mutumin Kurani ɗin nan. Muna so mu takaice muku su a littafi guda daya.

24 Tun da ya ke labarun tarihi sun yi yawa, yana da wuya masu niyyar kutsa kansu cikin nazarin tarihin su gane shi duka. 25 Mun nufa mu shirya wa maniyyata abin karantawa mai sauƙi. Masu son haddacewa kuma, mun sawwaƙa musu abubuwan haddata, yadda abin zai amfani kowa. 26 Mu da muka ɗauki nauyin wannan aiki fa, mun ga aiki ne tuƙuru, gama alamari ne mai sa zuffa da hana ido runtsawa har tsakar dare. 27 Muna iya kwatanta wannan aiki da wanda yake niyyar shirya ƙasaitacciyar liyafa, yana burin ya gamsar da kowa da kowa da abin shansa. Haka ne muke farin cikin ɗaukar nauyin wannan aiki don ya amfani jamaa. 28 Duk wanda yake so ya bi alamarin dalla dalla, sai ya karanta littattafan nan biyar da Yason ya wallafa. Mu dai za mu bayyana muku manufar littattafan biyar a taƙaice. 29 Kamar yadda maaunin gida yake kulawa da duk tsarin gida, amma mai shafe yana kulawa da shafen kawai da zai burge jamaa, a ganina haka yake gare mu a kan wannan aikin rubuta tarihi. 30 Nuna wata gwaninta da wani kakalen maragaɗi, da kintsa kome cif cif, wannan duk aikin gwanin mawallatin tarihi ne. 31 Amma wanda ke yin aikin wallafa tarihi, dole ne a ba shi dama yadda ba sai ya faɗi kome dalla dalla ba. 32 Don haka, yanzu bari mu fara ba da labarinmu, ba tare da ƙara wani abu a kan abin da muka ce yanzun nan ba. Ba zai dace ba ko mu faɗa a gabatarwa, mu rage tarihin shi kansa.

3. Labarin Haincin wani Mai Suna Saminu

1 A zamanin dā, birni mai tsarki yana maƙil da jamaa, ana zaman salama, ana kuma bin dokoki yadda ya kamata. Ana yin haka kuwa saboda halin kirkin babban firist Oniyas, mai ƙin mugunta. 2 A loton nan sarakuna ne da kansu suka ɗaukaka Wuri Mai Tsarki, suka kayatar da Haikalin Allah da kayayyaƙi masu mafificiyar daraja. 3 Har Saluku, Sarkin Asiya, ya ba da nasa taimako na kuɗin sayen duk kayan da ake bukata don yin hadayu. 4 Amma wani, mai suna Saminu na kabilar Bilga, da aka naɗa mai kula da Haikalin Allah, sai ya shiga gaba da babban firist Oniyas saboda wata doka ta kasuwar birnin. 5 Da ya ga ba zai iya ja‑in‑ja da Oniyas ba, sai ya tafi gun Afaloni na birnin Tarsus, wanda yake a loton shi ne hakimin Kilisuriya da na Finikiya, 6 ya gaya masa cewa, Ai, baitulmalin ɗin nan na Urushalima, kuɗi kamar su fasa shi. Kuɗin da ake tarawa na sadaka ana kashewa, amma kullum sai ƙaruwa suke yi. Ya ƙara da cewa, Duk wannan duniya tana iya zama mallakarka, in ka so yin haka.

Sarki ya Aika Haliyadoru ya Kwaso Kuɗin Haikalin Allah

7 Sai Afaloni ya je gun sarki, ya gaya masa labarin dukiyar. Daganan sai sarki ya zaɓi wakilinsa, Haliyadoru, ya aike shi, da cewa ya je ya ƙwaƙulo dukiyar ya kawo. 8 Nan da nan Haliyadoru ya shirya, ya fita kamar zai ziyarci biranen Kilisuriya da na Finikiya, amma ainihin manufar tafiyarsa don ya cika umarnin sarki ne. 9 Da ya isa Urushalima bayan an yi masa kyakkyawar maraba, in ji babban firist na Urushalima, sai ya hurta abin da aka gaya masa, ya bayyana wa babban firist daliltin zuwansa birninsu. Ya ce kuma yana so ya tabbatar da gaskiyar alamarin. 10 Sai babban firist ya yi jawabi ya ce, l, akwai yan kuɗin da aka keɓe don gwauraye mata da kuma marayu, 11 da waɗansu yan kayayyaƙi na Hairakanu ɗan nan na Tobiya, yaron nan mai kwarjini. Amma ai, duka dukan kuɗin ba su kai abin da Saminu ya yi tsammani ba, domin ko talanti ɗari na azurfa da ɗari biyu na zinariya kawai. 12 Har ya ƙara da cewa, To, ai, ba ma daidai ba ne a yi wa waɗanda suka amince da amanar Wuri Mai Tsarki cin mutunci, da ya ke dukan duniya gaba ɗayanta tana girmama Haikalin nan na Allah.

13 Amma shi Haliyadoru, saboda umarnin da sarki ya yi masa, sai ya ƙeƙasa ƙasa, ya ƙi, ya ce, Ai, dole ne waɗannan kuɗi su zama mallakar sarki. 14 Da ya shirya ranar yin haka, sai ya shiga maajin kuɗin don ya ƙidaya su.

Hargitsi a Garin

Har duk garin suka firgita ƙwarai. 15 Sai firistoci suka caɓa adonsu na firistoci, suka sunkuya gaban bagade, suka shiga roƙon Allah, domin Allah, wanda ya yi dokar tsare abin da aka tanada, ya kiyaye kuɗin nan don amfanin waɗanda suka tanaje su. 16 Ganin babban firist ma kawai ya isa ya sa mutane su saduda, gama ɗaure fuskarsa ya nuna ɓacin ransa. 17 Da ya ke kuma ya tsorata kwarai har yana rawar jiki, kowa ya gan shi, ya sani yana baƙin ciki matuƙa. 18 Mutane kuwa suka yiwo but daga gidajensu da shirin su yi addua don kada a ci mutuncin Wuri Mai Tsarki. 19 Mata suka taru, suka bi titi titi saye da tsummoki, ba su da ko taguwoyi. Yan matan da ke kulle a gidaje, su ma duk, suka yi daburce, waɗansu zuwa ƙofar gidajensu, waɗansu kuma suka hau katanga, sauran kuwa suna leƙe ta tagogi, 20 dukansu suna ɗaga hannuwa sama, suna roƙon agajin Allah. 21 Abin tausayi ne ganin yadda mutane suka fāɗi koina barkatai, suna addua, da kuma yadda babban firistinsu yake tsananin baƙin ciki.

Allah ya Hori Haliyadoru

22 A lokacin da suke ta roƙon Ubangiji Mai Iko Dukka, ya sa waɗanda aka ajiye wa kuɗin, su iya su mori kuɗin, ba tare da wani lahani ba, 23 Haliyadoru sai kawai ya ƙara dukufa kan abin da ya sa gaba. 24 Amma shi da masu kāre shi suna gabato baitulmalin ɗin ke nan, sai Ubangijin Iyayengiji, Mai Iko Dukka, ya gigita su gaba daya, har suka kurunce, suka faffaɗi wanwar sumammu. 25 Gama kafin ƙyiftawar ido, sai ga wani doki da ya ci ado, da wani mayaƙi mai bantsoro a kai. Dokin nan ya hau kan Haliyadoru, ya kuwa hau shi da ƙafa. An ga mahayin da sulke na zinariya tsantsa. 26 Sai kuma ga samari mayaƙa guda biyu, kowannensu gwarzo banza, masu kyan diri sun ci ado, suka bayyana a gaban Haliyadoru. Sai suka sa Haliyadoru tsaka, suka yi ta tuma suna kwarara masa dūka. 27 Nan take sai Haliyadoru ya fāɗi ƙasa, ya suma. Sai jamaarsa suka kawo gado, suka sa shi a kai. 28 Mutumin da ɗazu ɗazun nan ya kutsa kai cikin baitulmalin don gwada ƙarfi, shi da ɗumbun masu kāre shi, ga shi yanzu, ana ta tallaba, ba yadda yake, tun da ya ke Allah ya gwada masa iko. 29 A loton da Haliyadoru yake a kwance ne, ba ko bakin magana, saboda horon da Allah ya yi masa, 30 Yahudawan suka yabi Ubangiji da ya kāre nasa Wuri Mai Tsarki. Ɗakin nan, wanda da yake cike da tsoro da daburcewa, sai sowa ta keto daga cikinsa, domin an ga Ubangiji ya nuna ikonsa a fili.

31 Sai waɗansu daga cikin jamaar Haliyadoru suka roƙi Oniyas, cewa ya roki Maɗaukaki domin wanda aka bari rai ga Allahn nan ya sami farfadowa. 32 Babban firist kuwa yana jin tsoro kada a zargi Yahudawa, cewa sun yi wa Haliyadoru lahani, sai ya miƙa hadaya nan take domin Haliyadoru ya wartsake. 33 A loton da babban firist ke yin hadayar ta kawar da zunubi ne kuma, sai samari biyu, mayaƙan nan, tufafinsu irin na dā, suka dawo, suka matsi Haliyadoru, suka tsaya kusa da shi, suka ce masa, Ka yi wa Oniyas babban firist godiya, gama saboda shi ne Ubangiji ya farfado da kai. 34 Kai kuma, wanda Allah ya sa ka sha wuya, dole ne ka bayyana wa dukan mutane alherin ikon Allah. Da suka faɗi haka, sai suka ɓace.

Shaidar Haliyadoru

35 Haliyadoru kuma, sai ya miƙa hadaya ga Ubangiji, ya kuma yi wa Allah wanda ya kāre shi alkawari. Sai ya kai wa Oniyas ziyara ta bangirma, kana ya tasa sojojinsa gaba, ya koma gida gun sarki. 36 Gabagaɗi sai ya bayyana wa dukan jamaa ayyukan ikon Allah waɗanda ya gani zahiri. 37 Da sarki ya tambayi Haliyadoru wanda ya kamata a aika da shi Urushalima a wani karo, sai Haliyadoru ya ce, 38 In kana da wani abokin hamayya da mulkin, to, aika da shi. Zai kuwa dawo maka fiɗa fiɗa in ma ba a kashe shi ba, gama akwai ikon Allah ƙwarai a wurin. 39 Wanda ke zaune a can Sama shi ne ke lura da wurin, yana kiyaye shi kuma. Duk kuwa wanda yake da wani nufi na yi wa wurin lahani, sai kawai a ga an yar da shi matacce.

40 Labarin ke nan na abin da ya sami Haliyadoru, da kuma yadda ya yi nesa da taɓa baitulmalin din da ya yi niyyar yi.

4. Oniyas ya Roƙi Sarki ya Hana Saminu Fashi

1 Saminu ɗin da muka yi maganarsa, wanda ya ba da labarin tsabubun dukiyar da ke baitulmali na garinsu, shi ne kuma ya sheƙa wa Oniyas ƙarya, yana cewa, babban firist ne ya yi wa Haliyadoru mugun abu, shi ne kuma tushen duk waɗannan wahaloli. 2 Ta haka Saminu ya mai da wannan mutumin kirki, wanda ba shi da na biyu duk a birnin ga kiyaye sharia Allah, ya zama abokin gāban jamaa. 3 Da alamarin ya ƙara dagulewa, wani magoyin bayan Saminu, har kisan gilla ya riƙa yi wa jamaa. 4 A nan ne, da Oniyas ya ga hatsarin da ke akwai, ya kuma ga yadda Afaloni ɗan Manastu, hakimin Kilisuriya da na Finikiya, ke ta ƙara hura wutar maimakon ya kashe ta, a kan gaibin da Saminu ke kullawa, 5 sai ya tafi gun sarki da kansa don su gana, ba don ya sari mutanen garinsa a gun sarkin ba, amma don ya san abin yi ga lafiyar dukan jamaa baki ɗaya. 6 Da dai ya duba gaba, ya duba baya, ya ga in sarki bai sa baki cikin alamarin ba, ba wata jituwa a ƙasar, gama ba mai hana Saminu haukan da yake yi.

Yason ya sa Yahudawa su Bar Addininsu

7 Lokacin da Saluku ya rasu, Antiyaku mai suna Afifanesa, ya gaji sarautar, sai Yason, ɗanuwan nan na Oniyas, ya ƙwace babban firistanci da gishirin baka. 8 Gama ya taryi sarki cewa, Zan ba ka talanti ɗari uku da sittin na azurfa, zan ma ƙara maka waɗansu guda tamanin daga kuɗin fito da zan samu. 9 Sai ya ci gaba da alkawarta waɗansu talanti ɗari da hamsin, in dai aka ba shi iznin gina wurin nan da zai riƙa yin horon samari matasa a kan karatu da wasani, a kuma ba shi damar mai da mazajen Urushalima su zama kamar haifaffun birnin Antakiya.

10 A lokacin da sarkin ya yardar masa yin haka, sai Yason ya fara koya wa yan garinsu hanyar zama irin ta Helenawa. 11 Ga shi kuma, Yason ya kashe iznin bin aladun gargajiya wanda wani Yahaya ya samo daga wurin sarakunan Helenawa. Shi Yahaya ɗin uban Yubalima ne, wanda daga baya aka aika zuwa Roma don ƙulla yarjejeniya tsakanin Yahudawa da Romawa ta abuta da taimakon juna a yaƙi. Saan nan Yason ya sauya aladunsu na gaskiya na dā, da nasa, waɗanda ba bisa ga shariar ba. 12 Har ya ma kai ga gina wurin yin wasa gab da kagarar Urushalima, inda ya sa samari, yayan ƙusoshin garin, su yi wasa tsirara, sai dai su sa malfa kawai irin ta Helenawa. 13 Da ya ke Yason shi ba mutumin Allah ba ne, ba kuma firist ba, yana ta bin aladun Helenawa da suke bare, har da alamarin ya wuce makaɗi da rawa, 14 sai firistoci suka karaya da yin hidima a kan bagade. Tsakaninsu da Haikalin Allah sai baa, ba kuma ruwansu da miƙa hadaya. Da an buga ƙararrawa, sai su gudu nan da nan, su shiga wasan kwallo, da irin da sharia ta hana musu. 15 Suka raina duk abin da kakanni da iyaye suke girmamawa. Ba wani abin da suke darajantawa in ba na Helenawa ba ne. 16 Amma dukan waɗannan abubuwa kowanne da irin wahalar da yake kawowa. Da ya ke suna yin kishin irin zaman waɗannan mutane, irinta kuma suke son yi, sai Helenawa suka yi ta matsa musu lamba. 17 Ba ƙaramin abu ba ne a saɓa wa dokokin Allah, kamar yadda abin da zai faru da su nan gaba zai nuna.

18 A ranar wasanin cikar shekara biyar a birnin Taya a gaban sarkin garin, 19 sai shegen nan Yason ya aiki dakarun nan yan Urushalima, waɗanda aka mai da su kamar haifaffun birnin Antakiya, su zama jakadunsa a wasanin, su kuma tafi da kuɗi wajen talanti ɗari uku domin su yi wa wani gunki mai suna Harkuli hadaya. Amma su waɗanda suka kai kuɗin ma, sai suka ga bai kamata a kashe kuɗin don hadayar ba, ba daidai ba ne, in ji su. Sai suka shawarta yin wani abu dabam da kuɗin. 20 Maimakon a yi wa Harkuli, ɗan gunkin nan hadaya, sai jakadun nan na Yason suka kashe kuɗin a kan yin waɗansu jiragen ruwa.

21 Da aka aiki Afaloni, ɗan Manastu Masar don ya halarci bikin naɗin Sarki Filamitu na Masar, sai sarki Antiyaku ya ji sarkin nan na Masar ya shiga ƙulle‑ƙullen abin da ba daidai da sonsa ba, sai ya gangara Yafa, kana ya isa Urushalima. 22 Can ne kuwa aka yi masa babbar maraba, in ji Yason da jamaarsa, aka amshe shi da hannu bibbiyu, aka yi masa iso da jiniya da sowa. Da Antiyaku ya ga haka fa, ai, sai ya janye dukan sojansa zuwa Finikiya.

Manalawus ya Ƙwaci Sarautar Yason

23 Bayan shekara uku sai Yason ya aiki Manalawus, ɗanuwan Saminu ɗin nan da muka faɗa, domin ya kai wa sarki kuɗi yadda za a kai ga shirin waɗansu muhimman abubuwa. 24 Amma a lokacin da aka yi masa iso gun sarkin, sai ya yi wa sarkin romon baka, aka naɗa shi firist, bayan ya yi toshin baki na kuɗin da suka wuce na Yason da talanti ɗari uku. 25 Bayan an naɗa shi, sai ya koma gida, bai san kome na shaanin firistanci ba, sai son sarauta kawai da baƙin rai kamar ya haɗiyi kwabo. 26 Saan nan Yason, wanda dā ya yi wa ɗanuwansa wannan irin karmama, sai aka kore shi yanzu, ya yi gudun hijira zuwa kasar Ammonawa.

27 Ko da ya ke Manalawus ya hau gadon sarauta ya harɗe, bai biya kuɗin toshin baki yadda ya alkawarta wa sarki ba. 28 Har ma bayan jarumin nan Sosaratu, mai karɓar haraji, ya yi ta bimbinin Manalawus ya biya waɗannan kuɗi, sai sarki ya tsare Manalawus da jarumin, su biyu gaba ɗaya. 29 Sai Manalawus ya bar ƙanensa Lisimakus wakilinsa a sarautar babban firist, Sosaratu kuwa, sai ya bar Karata, jarumin sojojin Kuburawa a wakilinsa.

An yi wa Oniyas Kisan Gilla

30 Ana cikin yin haka ne, mutanen Tarsus da na Malasa suka shiga yin tawaye domin an ba Antiyakis biranensu tankar sadaka, ga shi kuwa Antiyakis wata kwarkwara ce ta sarki. 31 Sai sarki ya tafi da hanzari don ya tsawata wa jamaa kan haka. Ya bar Andaraniku can a wakilinsa har ya dawo. 32 Saan nan Manalawus ya ga kamar ya taka saa, har ya saci kayan zinariya na cikin Haikalin Allah, ya ba Andaraniku. Ya riga ya sayar da sauran waɗansu kaya a birnin Taya da birane na kewaye. 33 A lokacin da Oniyas ya gane haka, sai ya yi ƙarar Manalawus a gaban jamaa, bayan ya sami wata mafaka a wani wuri mai tsarki, mai suna Dafin, kusa da Antakiya. 34 Saboda haka sai Manalawus ya ware Andaraniku waje ɗaya, ya ce masa, Gara ka kashe Oniyas. Sai Andaraniku ya tafi gun Oniyas, ya cika shi da daɗin baki, ya yi alkawari da shi har da rantsuwa, tare da shan hannun juna, har ya raba shi da Wuri Mai Tsarki. Saan nan ya aikata illar, nan da nan ya sassoke shi.

35 Da fa haka ya faru, ba Yahudawa kaɗai ba, har da sauran kabilai ma, ransu ya dagula kan wannan irin kisan gilla da aka yi na wannan adali. 36 Dawowar sarkin ke da wuya daga Kilikiya, sai Yahudawan birnin suka tarye shi, suka yi masa kukan kisan gillar da aka yi wa Oniyas. Har ma Helenawa suka shiga nuna rashin goyon bayansu a kan mugun abin da aka yi. 37 Sai hankalin Antiyaku ya tashi ƙwarai, ya kuma yi baƙin ciki gaya, ya ji tausayi matuƙa, har ya yi wa mamacin makoki saboda cika gurbi irin nasa yana da wuyar gaske. 38 A husace, nan da nan, sai ya tuɓe alkyabbar Andaraniku, ya yayyage sauran tufafinsa, ya yi waje da shi, ya zazzaga gari da shi, har zuwa wurin da ya yi wa Oniyas ƙeta, can ne ya aika da shi lahira. Ta haka ne Ubangiji ya yi wa Andaraniku ramuwar gayya wadda ta fi gayya zati.

39 A lokacin nan Lisimakus ya sace kaya da dama na Haikalin Allah na Urushalima da taimakon Manalawus. Da fa aka baza labari an sassace kayayyaƙin zinariya na Haikalin Allah, sai yawancin mutane suka matsa wa Lisimakus. 40 Tun da ya ke duk hankalin jamaa ya tashi, sun kuma fara zanga zanga, sai Lisimakus ya shirya wani hari na rashin adalci da dakarai dubu uku, ƙarkashin jagorancin wani jarumi mai suna Auranus, jarumin ɗin ya tsufa, amma da tsufansa da wawancinsa ba a san wanda ya fi wani ba. 41 Amma da Yahudawa suka gane girin Lisimakus, sai waɗansu suka tsinci duwatsu, waɗansu faskare, waɗansu kuma suka dundutsi toka. Da su suka yiwo kukan kura, suka yi wa Lisimakus da jamaarsa ature. 42 Da aka gama karon battar ƙarfen, sai aka ga sun raunata jamaa da dama, har sun kashe waɗansu, sauran kuwa suka ranta ciki na kare. Ɓarawon nan kuwa Lisimakus, wanda ya saci kayan Haikalin Allah, suka yar da shi matacce a kusa da baitulmalin Haikalin Allah.

43 Daganan sai aka tuhumci Manalawus a kan abin da ya aikata. 44 Da sarki ya iso Taya, ko ruwa bai sha ba tukuna, sai ga manzo uku daga majalisar Urushalima, suka je gunsa domin su sanar da shi abin da ya faru. 44 Amma da Manalawus ya ga za a rinjaye shi, sai ya yi wa Talomi, ɗan Darimanesa, toshin baki mai tsoka, don ya yi rinjaye, sarki ya goyi bayansa. 46 Saboda haka fa Talomi ya kira sarkin, suka raɓe a wata yar maciya don su shakata. Ai, nan da nan sai ya sa sarkin ya sauya nufi. 47 Manalawus, wanda ya jawo wannan wahala duka, sai sarki ya sake shi, ya kuma yanke wa adalai hukuncin kisa, waɗanda ko da sun ɗaga ƙararsu zuwa gun azzaluman nan Sikitiyawa, da sun kwana lafiya. 48 Ta haka waɗanda suka motsa don su kāre birnin da alummarsu da kayayyaƙin nan na Wuri Mai Tsarki, sai suka ɗanɗana kuɗarsu ba gaira ba dalili. 49 Saboda haka ne har waɗansu mutanen Taya suka nuna matuƙar rashin amincewarsu da gillar, sai kuma suka yi wa mutanen kyakkyawar janaiza. 49 Amma Manalawus saboda son kuɗi na waɗanda ke manyan sarauta a lokacin, sai ya ci gaba da yin sarauta, yana sarawa, ya yi ta saran jamaa gun manyan sarakuna.

5. Tashin Hankali da Mutuwar Yason

1 kusan wannan lokaci ne Antiyaku ya kai wa Masar hari na biyu. 2 Ana nan sai waɗansu malaiku kamar dakarun doki suka bayyana, suna shawagi koina bisa Urushalima. Har kusan kwana arbain ana ganinsu, kowannensu da sulken zinariya, suna riƙe da isassun kayan yaƙi, ga māsū da zararrun takuba. 3 Ga su nan ƙungiyoyin sojojin doki a shirye don yaƙi, sai wasa kawai suke yi, suna motsa jiki don shirin yaƙi, suna daɓa wa junansu māsū, suna kārewa da garkuwa, suna harɓa kibau. Sai hasken zinariya kake gani, da dai kayayyakin yaƙi iri iri. 4 Ganin haka, sai mutane suka yi ta yin addua, Allah ya sa wannan alamari ya zamar musu alamar alheri.

5 Da dai aka ji jita jita, wai Antiyaku ya baƙunci lahira, sai Yason ya kwashi mutum dubu, suka auka wa birnin Urushalima, ba zato ba tsammani. A loton da masu tsare garu suka ja da baya, abokan gāba suka shiga, suka cinye shi. Sai Manalawus ya tafi ya ɓoye a kagarar birnin. 6 Amma Yason, sai da ya ci gaba da yanyanka yan ƙasarsa, ba tare da nuna wani tausayi ba. Bai gane babbar hasarar da yake haddasawa ba. A nasa zato ca yake, abokan gāba ne yake ta ba kāshi, ashe, bai sani ba, dara ta ci gida. 7 Bayan haka sai ya kasa jan ragamar mulkin daidai. Daga ƙarshe ma dai, da ya ga abin ya gagara, sai ya yi gudun hijira zuwa birnin Ammonawa. 8 Bayan kome ya natsa kuma, sai ya yi mutuwar kare a can. Gama Aratas, Sarkin Larabawa, bai yi naam da shi ba, duk garin da ya je ana yi masa korar kare, duk mutane suka ƙi shi, saboda ya cika keta dokoki, suna cewa, Ka yi nesa da mu, da ya ke ka lalata ƙasarka, ka yi fawa da yanuwanka. Da suka yi ta binsa daga gari zuwa gari, sai ya nufi Masar. 9 Daga can ne ya haye teku zuwa Sufarta da begen zai yi zaman lafiya a can don wata yar dangantaka da ke tsakaninsa da yan ƙasar. Yason, wanda ya taɓa tilasta wa Yahudawa da dama yin gudun hijira, ga shi, shi ma ya yi, a can ne ma ya mutu. 10 Shi da ke sawa a kashe mutane da dama, a har ungulai su ci, sai alhaki ya kama shi har ya rasa makoma. Ba wanda ya yi masa makoki ko janaiza, balle a yi masa kabari gun kakanninsa.

Antiyaku ya Ɓata Garin Urushalima

11 Da sarki ya ji labarin abin da ya faru a Urushalima, sai ya sheƙi ƙanshin, cewa ana yin tawaye ke nan a ƙasar Yahudiya. Don haka, da ya husata, sai ya fito daga Masar, ya wanke hannu, ya auka wa Urushalima. 12 Ya ce wa dakarunsa kada su ji tausayi, su yi wa garin ƙofar rago, koina mutum ya shiga kuma su zaro shi, su kashe. 13 Da ma yaya lafiyar giwa, balle ta haukace, suka shiga gonarsu ta mugunta, suka yi ta kisan manya da yara, samari da mata, da na goye, suka kuma yanyanka yan mata da jarirai. 14 A kwana uku aka yanyanka dubu arbain, aka sayar da waɗansu dubu arbain a bayin yaƙi. 15 Amma duk da haka Antiyaku bai dangana ba, sai ya shiga Wuri Mai Tsarki na duk duniya. Manalawus kuma wanda ya ci amanar ƙasarsa, ya keta haddin shariar Allah, shi ne ya raka Antiyaku. 16 Sai Antiyaku ya kwashe kayan ibada na Wuri Mai Tsarki da ƙazaman hannuwansa, ya kuma kyakketa haddin kyautan da sauran sarakuna suka yi don girmama ɗaukakar wurin. 17 Da ya ke Antiyaku na cike da farin rai, ashe, bai gane ba, zunuban waɗanda ke zaune a birni su ne suka sa Ubangiji ya husata da su a ɗan lokaci, ya bari a cinye birninsu duk da Wuri Mai Tsarki. 18 Amma da mutanen garin ba su aikata laifofi ba, da sun iya yi wa Antiyaku fata fata da bulala, su kore shi saboda aikin rashin juyayi da ya yi, kamar dai yadda aka yi wa Haliyadoru, wanda sarki Saluku ya aika domin ya binciko shaanin baitulmalin ɗin nan. 19 Amma Ubangiji bai zaɓi alumma saboda Wuri Mai Tsarki ba, sai da Wuri Mai Tsarki saboda alummar. 20 Don haka wuyar da mutane ke sha ta shafi Wuri Mai Tsarki ta kowace hanya. Da Ubangiji ya sulhuntu da su kuma, sai aka sake darajanta wurin.

21 Nan take sai Antiyaku ya zare talanti dubu goma sha takwas daga Haikalin Allah, ya tafi da gaggawa zuwa Antakiya. Da girman kansa ya yi zaton zai iya yin abin da ba zai yiwu ba, bai sani ba kana taka, Allah na tashi. 22 Ya bar hakimai a ƙasar da izni su ƙuntata wa jamaa. A Urushalima ya sa Filibus, Bafirijiyen nan wanda ya fi mai naɗa shi ƙeta. 23 A tsaunin Gerazima kuma ya sa Andaraniku. Banda waɗannan hakimai biyu, sai hakimi Manalawus kuma ya tsananta wa jamaa yadda har kusan a ce waɗancan ba su iya ba. Saboda ƙiyayyar da Antiyaku yake yi wa Yahudawa, 24 sai ya aika da Afaloni, jarumin ɗin nan na sojan Misiyawa, da dakaru dubu ashirin da biyu, ya ce masa, Ka yanke mini dukan mazansu, ka kuma sai da matansu da samarinsu su zama bayi. 25 Da gogan naka ya iso Urushalima, ya yi ta nuna halin salamar munafunci, sai ranar Asabar mai tsarki, domin ya san Yahudawa ba za su yi wani aiki ba a ranar. Da ranar ta zo, sai ya sa sojansa su yi rawar daji, kowa na ɗauke da kayan faɗansa. 26 Duk ya kakkashe waɗanda suka fito kallonsu. Saan nan ya fāda wa birnin da sojojinsa, ya yi ta kisan jamaa.

27 Amma Yahuza Makabi, shi da waɗansu mutum tara, sai suka faɗa kurmi, suka yi ta ɓoyon ransu a ƙungurmin jeji kamar dabbobi, suka yi ta cin yayan itatuwan jeji domin su wanzu, domin kuma ba su so su ƙazantu da abin aladun sauran alumma.

6. An yi wa Haikalin Allah Saɓo

1 Ba a dade ba bayan haka, sai sarki ya aiki wani shugaban Atinawa domin ya matsa wa Yahudawa su yi watsi da aladun kakanninsu, su kuma daina bin dokokin Allah. 2 Sarki kuma ya ce a wulakanta Haikalin nan na Allah da ke Urushalima, a sauya masa suna, a ce da shi Gidan Zafsa, ɗan allahn nan na Tsaunin Olimfas. Wancan gidan ibadar da ke Gerazim ma, ya ce da shi Gidan Zafsa Abokin Baƙi, kamar yadda mutanen wurin suka roƙa. 3 Kai, amma dai an aikata mugun abu zahiri! 4 Gama an cika Haikalin Allah da arna, suna ta ci, suna sha, suna holewa. Har suna ta jin daɗin karuwai, sukan kuma yi amfani da su a Wuri Mai Tsarki. Banda haka ma suka shiga Haikalin Allah da kayan da bai kamata ba. 5 Sun rufe bagade rijib da ƙazamun hadayu waɗanda sharia ta hana a miƙa.

An Kashe Sharia

6 Aka hana bin ranar sujada, da kiyaye ranakun idi, waɗanda aka bi tun kakannin kakanni. Har kuma aka hana Yahudawa kiran kansu Yahudawa. 7 Kowane wata ana yin wani biki don girmama sarki. Da ranar ta kewayo, sai aka yayi Yahudawan, aka matsa musu su ci hadayar. Da kuma ranar sadakar Diyonisiyas, gunkin nan, ta kewayo, sai aka rnatsa wa Yahudawa duk su rataya waɗansu kayan ado masu kama da buzayen biri, su shiga tafiyar jeren gwano don girmama gunkin.

8 Sai sarki ya bi shawarar mutanen birnin Talamayas, ya ba da wani umarni, cewa duk biranen Helenawa da ke kewaye da su, su riƙa matsa wa Yahudawa su ci hadayar ama da ake yi. 9 Ya ce a yanka duk wanda ya ce shi ba zai bi aladun Helenawa ba. Don haka ana iya ganin yadda Yahudawa suke bakin halaka ƙwarai. 10 Alal misali, akwai waɗansu mata biyu da aka ɗaure, wai don sun yi wa yayansu kaciya. Waɗannan mata, sai da aka zaga birni da su tukuna, suna saɓe da yayansu. Kana aka ɗaure yayan da iyayen, aka jefa su ƙasa daga bisa garu. 11 Waɗansu Yahudawa kuma suka shiga kogon dutse, don su kiyaye ranar Asabar mai tsarki. Amma da aka gano su, aka tona musu asiri, aka gaya wa Filibus. Sai ya sa aka ƙone su duk gaba daya, saboda Yahudawa sun ƙi yarda su yi faɗan kare kai, don cika kaidar babbar ranarsu mai tsarki ta Asabar.

Nufin Allah game da Waɗannan Masifu

12 Yanzu ina yi wa dukan masu karanta wannan littafi gargaɗi, don kada su yi baƙin ciki a kan waɗannan masifu, amma su gane, wahalolin nan sun auku ba don hallaka jamaarmu ba, amma don a ƙara gyara halinsu. 13 Hakika ba wai za a ƙyale marasa adalci su ci gaba da taadda ba, amma za a hore su ba da daɗewa ba, haka kuwa ramuwar gayya ce. 14 Gama a kan waɗansu alummai Ubangiji ya bari, sai da suka kai kan ganiyar laifinsu, kāna ya hore su. Amma ba haka ya yi mana ba, 15 don haka ya yi mana ramuwar gayya bayan zunubanmu sun cika. 16 Ko alama ba ya janye jinƙansa daga wurinmu. Ko da ya ke yakan yi mana babban horo na wahala iri iri, amma ba zai taɓa yar da jamaarsa ba. 17 Bari abin da muka faɗa ya zama abin tuni ga jamaa. Za mu ci gaba yanzu da ba da labarin.

Eleazara ya Mutu don Nuna Shaida

18 Eleazara, ɗaya daga cikin manyan malaman Attaura, dattijo ne mai daraja, wanda ya kwana biyu, sai aka tilasta masa ya ci naman gursunai, har ma aka maƙare shi, aka sa masa naman a baka. 19 Amma ya gwammace ya mutu da ya yi ƙazamar rayuwa, sai ya tofar da naman. Ya yarda ya karɓi azabar da za a gasa masa, 20 kamar yadda ya kamata kowane mutum ya yi wanda bai yarda ya ci abin da zai kazanta shi ba. Ai, sa kai, ko za a kashe mutum, ya fi bauta ciwo. 21 Don haka sai shugabannin liyafan nan ta haram suka kira shi waje daya, da ya ke sun saba da shi, suka ce ya yi maza maza ya kawo nasa irin naman da sharia ta yarda ya ci, wanda ya shirya don nasa abinci. Suka ce ya nuna kamar yana cin naman liyafar da sarki ya umarta a ci, 22 don ta yin haka ya kuɓuta daga kisan da za a yi masa, a kuma yi masa kome da Ialama saboda tsohuwar abutarsu. 23 Amma ya yi wani nufi da ya dace da dattakonsa, da hurhurarsa, da kirkin rayuwarsa tun ƙuruciyarsa, sai ya ce musu, Ni zan kiyaye dokoki masu tsarki na Allah. Ban damu ba ko da za a ci namana ɗanye.

24 Sai ku aika da ni ko gaban lahira ne, gama irin wannan kawar da kai da kuka ce in yi, bai dace da zamanmu ba, in ji shi, Kada samari matasa da dama su ce, Kai jamaa, ku dubi tsohon nan Eleazara ya ba shekara tasain baya, amma don tsoro, ya shiga wani sabon addini dabam. 25 Ba na so in yi munafunci game da abinci, don in ja zamanina gaba kaɗan, in sa samari su bauɗe, in kunyata tsufana, ina mai da shi abin faɗi ga yan baya. 26 Gama in na zuƙe wa horon mutane yanzu, ta ina zan zuƙe wa horon Mai Iko Dukka? Ko a raye ko a mace, ba zan iya guje masa ba. 27 Saboda haka in na sadaukar da raina yanzu da nufin kaina, saan nan zan tabbata hurhurata ta yi mini rana, 28 zan ma bar wa na baya gurbi mai kyau wanda za su bi, su ma da yardarsu su yi kyakkyawar mutuwa ta kiyaye dokokin nan masu tsarki.

Da dai ya faɗi haka, sai ya tafi gun da ake azabatarwa. 29 Wadanda suke ɗan nuna masa halin kirki dā, yanzu sai suka sauya masa fuska, saboda yanzu sun mai da shi mahaukaci saboda abubuwan da ya faɗa. 30 Da suka bubbuge shi, ya kai gab da mutuwarsa, sai ya ce, Wannan abu sananne ne ga Ubangiji a basiran nan tasa mai tsarki, cewa mai yiwuwa ne dā na kuɓuta daga kisa, amma na yarda na sha wannan mugun bugu, ina kuwa farin cikin shan wannan azaba, domin ina da tsoron Mai Iko Dukka. 31 Ta haka ne ya mutu, inda ya bar wa samari yan baya abin taƙama da misalin halin kirki, ba samari kadai ba ma, amma dukan alummar ƙasa baki ɗaya.

7. Mace da Yayanta guda Bakwai sun Mutu don Nuna Shaida

1 Haka ma aka tsananta wa waɗansu yanuwa guda bakwai, su da uwarsu. In ji sarkin, a yi ta bugunsu da bulala da awargaji, ana matsa musu don su ci naman nan na gursunai. 2 Ɗaya daga cikinsu sai ya yi zakara ya ce, Me kake so ka sani game da mu, da kake yi mana tambayoyi? Gama mu dai, nan da kake ganinmu, sai dai a kashe mu. Ba za mu karya dokokin Allah da muka gāda gun iyayenmu ba. 3 Sai sarkin ya husata, ya yi umarnin a haɗa wuta ganga ganga. 4 Da aka haɗa wutar, nan da nan sai sarkin ya ce a yanke harshen wanda ya yi musu zakaran nan, a kware masa ƙyeya, a kuma yanke hannuwansa da ƙafafu, tun sauran yanuwansa da uwa tasa suna kallo. 5 Da suka yi masa haka, sai sarki ya umarta su ɗauke shi, tun yana da rai, su jefa shi a garuwa, su soya, sai fa aka yi ta jin ƙaurin nan na suyar koina.

Daganan sai yanuwan nan da uwarsu suka ƙarfafa juna, duk su yi mutuwar sa kai, suna cewa, 6 Ai, Ubangiji Allah yana lura da mu a bisa ga gaskiya, yana kuma jin tausayinmu, kamar dai yadda Musa ya ce a wata waƙa tasa wadda ta ce, Ai, zai ji tausayin bayinsa.

7 Bayan sun kashe ɗanuwa na farko da wannan irin kisan gilla, sai suka tattago na biyu. Sai suka kware masa ƙyeya, saan nan suka ce masa, Zaɓi ɗaya, mu kashe ka ta gasa wa duk jikinka azaba, ko kuwa ka ci naman gursunan.

8 Sai na biyun nan ya ce musu da Yahudanci, Ai, ba na yin magana in sāke. Saboda haka shi ma sai suka gasa masa azaba yadda suka gasa wa danuwan nan nasa. 9 A lokacin da ya kusa cikawa, sai ya ce, Kai lalataccen nan, kana kashe mu, amma Sarkin sama da ƙasa zai ta da mu da madawwamin sabon rai, domin mun mutu saboda bin dokokinsa.

10 Bayan shi sai suka kama na uku. Shi ma suka wulakanta shi ƙwarai. Da dai suka matsa masa, sai ya fitar da harshe, ya miƙe hannuwansa, 11 ya ce, Waɗannan abubuwa daga Sama ne na same su. Saboda bin dokokin Allah kuma ni ban mai da su a bakin kome ba. Shi kuma zai sake mayar mini da su, ko sun kuɓuce mini a yanzu. 12 Da fa suka ga haka, har sarkin ma, ba talakawansa kaɗai ba, sai da suka yi mamakin ƙarfin zuciyar saurayin, gama sun ga bai mai da wahalar da yake sha a bakin kome ba.

13 Da shi kuma ya mutu, sai suka kama na huɗu, shi kuma suka yi masa yadda suka yi wa na ukun. 14 Shi kuma, da ya kusan mutuwa, sai ya ce, Ba za mu ƙi mutane su gasa mana azaba, har ma su kashe mu ba, da ya ke Allah ya alkawarta ta da mu daga mutuwa. Amma ku da kuka kashe mu, ba za ku sami damar tashi ga sabon rai ba.

15 Sai kuma suka jawo na biyar shi ma, suka azabta masa. 16 Amma shi, sai ya dubi sarkin, ya ce masa, Saboda kana da iko a kan jamaa kana yi musu abin da ka ga dama. Wata rana kai ma za ka mutu, kada ka zaci Allah ya yi watsi da jamaarmu. 17 Ka ci gaba da yin mugun abin da kake yi, ai, wata rana tsamiya za ta juye da mujiya a kanka da yan baya.

18 Da suka kashe shi, sai suka rarumo na shida. Shi ma, da ya kusan macewa, sai ya ce musu, Kada ku ruɗi kanku a banza. Gama saboda zunuban da muka yi wa Allahnmu ne muke shan wannan azaba haka, da kuma waɗansu abubuwan bantsoro da suka same mu. 19 Saboda haka kada ku yi zaton za ku tafi lami lafiya a kan tawayen da kuka yi wa Allah.

20 Uwar yaran ta yi wani abin mamaki da zai hana a mance da ita. Ko da ya ke a kan idonta ne aka yi ta ƙone yayanta, har guda bakwai rana ɗaya, ba ta nuna ƙaya ta soka ba, domin ta dogara ga Ubangiji. 21 Mace da kamar maza kwari ne babu, ba ta daina ƙarfafa wa yayanta gwiwa ba, har aka kakkashe su. Sai ta yi ta ce musu da Yahudanci, 22 Kada ku damu, ban san yadda kuka wanzu a cikin cikina ba. Ba ni ba ce na ba ku rai da numfashi, ba ma ni ce na ba kowannenku halin da yake da shi ba. 23 Saboda haka wanda ya halicci duniya, ya siffata farkon kowane ɗan adam, ya ƙaddara farkon kome, shi ne da jinƙansa zai sāke mayar muku da rai da numfashinku, tun da ya ke yanzu kun sadaukar da ranku saboda dokokinsa.

24 Sai Antiyaku ya yi tsammani tana yi da shi, tana ci masa mutunci. Saan nan, ba a riga an kashe ɗan autansu ba tukuna, sai Antiyaku ya yi ta roƙonsa, har da rantsuwa cewa, Na rantse da Allah, in ka daina bin aladun nan na kakanninka, zan ba ka arziki da walawa, in mai da kai ɗan majalisata, in ma ba ka wata sarauta a mulkina. 25 Amma saurayin ya yi kunnen shege da shi, sai sarkin ya kira uwar yaron, ya ce mata, Ki rarrashi ɗanki ya bi, don kada a kashe shi. 26 Bayan ya cika ta da tankiya, sai ta yi kamar tana rarrashin danta.

27 Da ta ranƙwafo kusa da danta, sai ta yi magana da shi, ta ce da yarensu, Dana, rabu da mutumin banza. Ka ji ƙaina. Watanka tara fa a cikin cikina, kana na haife ka, na kuma goye ka har shekara uku, na dai yi ta shan ɗawainiya a kanka, ina ta lura da kai, har ka yi girma haka. 28 Don haka ina roƙonka, ɗana, ka ɗaga kanka sama, ka dubi sama da ƙasa, ka ga duk abubuwan da ke cikinsu, ina so ka gane, Allah fa, bai yi su da waɗansu kayan aiki ba, sai da ikonsa. Ta haka ne kuma ya halicci yan adam. 29 Kada ka yi fargaba saboda wannan hauni, amma ka nuna ƙarfin halin nan irin na yanuwanka. Ka yarda a kashe ka, domin a cikin jinƙan Allah in sake karɓarku rayayyu, kai dayanuwanka.

30 Tana magana ke nan, sai ɗan autan ya ce, To, me kuke jira, jairai? Ni, namana ja, ba zan bi umarnin sarki ba, amma zan bi dokar Allah wadda aka danƙa wa kakanninmu ta hannun Musa. Amma kai, da ka tsananta wa Yahudawa da kowane irin mugun abu, ka tabbata za ka mutu, za ka kuwa tarar da Allah. 32 Mu muna shan wannan irin wuya saboda zunuban da muka yi. 33 Idan Ubangijinmu rayayyen nan, ya husata da mu, ya hore mu, in an ɗan jima za mu sulhuntu da shi. 34 Amma kai, jairin nan, mafi kowa baranci, ko kusa kada ka sa zuciyar samun wata gafara gun Allah, tun da ya ke kana tsanantar adalai. 35 Alhakinka na wuyanka, za ku gamu kuwa, kai da Allah Mai Iko Dukka, mai ganin kome da kome. 36 Gama yanuwanmu, bayan yar wuyan nan da ka sa aka gasa musu, sai sarawa suke yi, suna zakawa yanzu a cikin falalar Allah, bisa ga alkawarin da ya yi musu. Allah ya ƙaddara za ka sha azaba tsantsarta a kan almubazarancin da ka yi wa jamaa. 37 Ni da yanuwana, duk mun ba da jikinmu da ranmu domin mu sha wuya, don mu kiyaye dokokin Allah da muka gāda daga gun kakanninmu. Mun roƙi Allah ya nuna jinƙansa da sauri ga alummarmu, ya kuma ba ku wuya da azaba iri iri, don ku yarda da cewa shi kaɗai ne Allah. 38 Ta wurina da yanuwana muna roƙon Allah ya huce da fushin nan da ya yi da dukan alummarmu saboda saɓon da muka yi masa.

39 Da jin wannan, sai sarki ya husata, ya yi wa yaron nan ƙankanci fiye da na sauran, wai ya ba sarki haushi da ya yi masa baa haka. 40 Saboda haka sai ya mutu, bai saɓi Allah ba, domin ya amince da Ubangiji da dukan ransa. 41 Daga ƙarshen duka, sai aka kashe uwar ita ma, bayan an kakkashe yayanta.

42 Mun yi magana sosai a kan ƙin cin liyafar haram da Yahudawa suka yi, da yadda aka tsananta musu. Labarin ya isa haka.

8. Fitowar Yahuza Makabi

1 Amma Yahuza, wanda ake kira Makabi wani lokaci, shi da abokansa suka shiga ƙauyuka a asirce, suka tattara danginsu waɗanda har yanzu ke bin aladun Yahudawa, suka sami mutum dubu shida cif. 2 Suka roƙi Ubangiji ya dubi waɗanda ake zalunta da idon rahama, ya kuma kāre Haikalinsa wanda mutanen banzan nan suke Ialatarwa, 3 ya kuma ji ƙan birni wanda aka ragargaje, ga shi nan, an kusa mai da shi kufai, ya ji tausayin jinin da aka zubar na waɗansu, 4 ya tuna kisan gillar da aka yi wa jarirai da kuma saɓon sunansa da ake ta yi, ya kuma nuna wa masu yin saɓon yadda ake ƙin mugunta. 5 Da dai Makabi ya shirya sojansa, sauran alumma ba su iya karawa da shi ba, gama fushin Ubangiji ya koma jinƙai. 6 Ya yi ta kai harin ba zata, yana ƙone garuruwa da ƙauyuka. Ya yi ta kama wuraren bago na abokan gāba, su kuwa suna ranta ciki na kare. 7 Ya ga irin kai harin nan na dare ya fi rana. Aka kuma yi ta yin zance a kan kwazonsa a koina.

An Ci Nikanar

8 Da Filibus ya ga dai ɗan talikin nan Yahuza, sai fasa ƙasa yake yi a hankali a hankali, ya ga kuma a kullum ba abin da Yahuza ke karo da shi sai nasara, sai Filibus ya rubuta wa Talomi wasiƙa, hakimin nan na Kilisuriya da Finikiya, yana cewa, Don Allah, ku taimaki mulkin sarki mana!

9 Sai Talomi ya zaɓi Nikanar, ɗan Fatarokulus, ɗaya daga cikin yan gaban goshin sarki, ya aike shi da sojojin da suka kai dubu ashirin na dukan kabilan arna, ya ce, Ku je, ku lashe kabilar Yahudawa tas. Har ya haɗa sojan da sanannen mayaƙin nan, mai suna Gorgiyus, wani gwarzon yaƙi. 10 A lokacin nan Romawa suna bin sarki Antiyaku kuɗin gandu na talanti dubu biyu.

Nikanar kuwa ya yi burin samo wa sarki waɗannan kuɗi ta sassayar da kamammun sojojin Yahudawa. 11 Nan da nan sai ya aika a birane, har zuwa gaɓar bakin teku, yana cewa, Ku zo, ku sayi bayi na Yahudawa. Na kuma tabbata za ku sha ɓuɓa, domin zan sayar muku da ƙatti tasain a talanti daya. A loton nan ko kaɗan bai yi zaton Allah zai rama wa kura aniyarta ba.

12 Sai aka ba Yahuza labarin harin da Nikanar ke kawowa, Yahuza kuma ya sanar da dakarunsa wannan labari. 13 Amma waɗansu daga cikin sojansa da ba su dogara ga Allah sosai ba, da suka tsorata, sai suka yi ta ranta ciki na kare. 14 Waɗansu Yahudawa kuwa suka sai da sauran mallakarsu, suka kuma dukufa roƙon Allah ya ceci Yahudawan da jairin nan Nikanar ya sayar kafin ya kawo musu hari ya kama su. 15 Suka roki Allah ya yi haka, ba don halinsu ba, amma saboda alkawaran da ya yi da kakanninsu, da kuma sunan nan nasa mai girma da ɗaukakar da yake da su. 16 Amma Makabi ya tara jamaarsa, ya haɗa mutum dubu shida cif, kana ya ja musu kunne, ya ce kada su ji tsoron jairan sojan abokan gāba, kome yawansu, ya ce, Ku far musu kai tsaye! 17 Ya kuma ce, Ku fa tuna irin haukan da arnan nan suka yi, har suka Ialata Wuri Mai Tsarki, suka tsananta wa na birnin. Banda haka ma, duk sun sa an yi watsi da aladar kakanninmu. 18 Gama su sun amince da kayan faɗansu kawai, in ji shi. Amma mu, ba wanda muka amince da shi, sai Allah Mai Iko Dukka, wanda ta ikonsa ko da yar tsakuwa yana iya falfasa musu kai, yana ma iya fatattaka dukan duniya, in ta ce za ta tare mu. 19 Ya ci gaba da cewa, Ku tuna fa da lokatan da kakanninmu suka sami taimako. Misali, a zamanin sarki Sennakerib, da mutum dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar, suka sheƙa lahira nan take. 20 A lokacin yaƙin nan da Galatiyawa kuma, wanda aka yi a Babila, Yahudawa dubu takwas da waɗansu mutanen Makidomya su dubu huɗu suka wanke hannu, suka auka cikin alamarin. Amma da Makidomyawan suka ji an matse su, suka ja da baya, sai Yahudawa dubu takwas ɗin nan, da taimakon Allah, suka yi wa dubu ɗari da dubu ashirin fata fata, kāna suka naɗi ganima. 21 Da Yahuza ya yi wannan jawabi, sai jawabin ya ƙarfafa wa jamaarsa gwiwa, suka yarda su sai da ransu saboda aladunsu da kuma ƙasarsu.

Saan nan Yahuza ya rarraba mutanensa kashi huɗu. 22 Ya tura yanuwansa guda uku, Saminu, da Yusufu, da Jonatan, ya sa su ciki domin kowannensu ya yi zakaran kungiya guda, wadda ke ƙunshe da mutum dubu goma sha biyar. 23 Ga kuma Eleazara, ƙanen Yahuza, yana taimakonsu. Bayan Yahuza ya yi wa sojansa karatu daga cikin Littafi Mai Tsarki, ya sa duk taron ya haddace kalmomin nan da suka fada, wato Da taimakon Allah. Saan nan ya shugabanci ƙungiya ta farko, ya auka wa Nikanar da yaƙi. 24 Da suka sa Allah gaba, nan da nan sai suka aika da mutum fiye da dubu tara na sojan Nikanar lahira, suka kuma raunata yawancin sauransu, sai yan sauran suka ranta ciki na kare, ba shiri. 25 Suka ƙwace kuɗi kuma daga gun waɗanda suka zo sayensu domin su bautar. Da suka yi musu muguwar kora, 26 sai suka dawo domin kuwa almuru ya fara yi. Gama gab ake da ranar Asabar, shi ya sa suka ƙi kai kora har bango. 27 Da suka ƙwace makaman abokan gāba, suka kwashe ganima sarai, sai suka cika aikin wajibinsu na Asabar, suka yabi Ubangiji da godiya mai yawan gaske, wanda ya kāre su a wannan rana, suka kuma kiyaye ta domin ta zama tushen jinƙan Ubangiji zuwa gare su. 28 Da Asabar ta wuce, sai suka ɗibi ganimar, suka raba wa waɗranda aka gasa wa azaba, da kuma marayu, da mata gwauraye. Su kuma suka raba sauran, su da matansu da yayansu. 29 Da suka gama raba kayan, sai suka roƙi Ubangiji mai jinƙai tare, domin ya yi cikakken sulhu da bayinsa.

An Ci Timoti da Bakadi

30 Da kuma suka yi karon battar ƙarfe da sojojin Timoti da na Bakadi, sai suka aika fiye da dubu ashirin lahira, suka kakkame wuraren tsaro na abokan gāba masu yawa, suka raba ganimar da suka kwasa kashi biyu. Suka riƙe kashi ɗaya, ɗayan kuma suka babbayar ga waɗanda aka gasa wa azaba, da marayu, da mata gwauraye, har ma da tsofaffi kutuf. 31 Da suka kwashe makaman abokan gāba, sai suka ɓoye su a wuraren tsaro, suka naɗi sauran ganima, suka kai Urushalima. 32 Suka kuma kashe shugaban sojojin Timoti, azzalumin nan, wanda ya rnatsa wa Yahudawa lamba kwarai da gaske. 33 A ranar da suka yi bikin samun yancin kai, sai waɗanda suka ƙone ƙofofi masu tsarki suka gudu zuwa wani ƙaramin gida tare da Kalistana. Sai aka bi su, aka ƙone gidan da suke ciki ƙurmus. Ta ha, alhakinsu ya koma kansu.

Ƙasƙancin da aka Yi wa Nikanar

34 Laantaccen nan Nikanar, wanda ya kira dubban fatake su sayi Yahudawa, 35 da taimakon Ubangiji, aka yi masa ƙaskanci, inda ya ga abokan gāba da bai zaci za su iya karawa da shi ba, sun yi masa fata fata. Sai ya tashi, ya tuɓe riga da kayan yaƙi, ya zage buje, ya sheƙa da gudu, ya keta kurmi, sai ka ce bawan da ke so ya tsere, sai da ya kai Antakiya. Haka ya faru domin shi ne ya jawo abin da ya sa aka yi ɗaya ɗaya da sojansa. 35 Ta haka shi da ya yi alkawarin kai wa Romawa kuɗin gandu, sai ya ɓuge da cewa, Ai, Yahudawa suna da Allah mai yaƙi dominsu, ba su taɓo ko kadan. Ya ƙara da cewa, Yahudawa kam, ba mai iya i musu, domin kuwa suna biye sau da ƙafa da dokokin Maɗaukaki.

9. Horon da aka Yi wa Antiyaku da Mutuwarsa

1 A wannan lokaci ne aka ƙasƙanta Antiyaku a ƙasar Farisa, har ya fita ya har garin a kunyace. 2 Gama ya taɓa shiga wani gari da ake cewa da shi Fasafolis, ya nufi yi wa gidan gunkin wurin fashi, ya kuma mallaki birnin. Saboda haka duk, sai mutanen garin suka yi wa sojansu ɗauki, suka kori Antiyaku, inda suka sa ya ranta ciki na kare, shi da jamaarsa. Wan garin kuwa suka dāfe su, sai da suka dāfe kunne, suka yi kamar suna yi. 3 A loton da yake a Ekbatana, sai aka kawo masa labari cewa, Ga abin da ya sami Nikanar da kuma tasasan sojan nan na Timoti. 4 Da ya husata, sai ya yi niyyar yin ramuwar gayyar gaske a kan Yahudawa saboda mutanen Fasafolis, waɗanda suka sa ya ranta ciki na kare ba da daɗewa ba. Sai ya ce wa mai koran karusarsa, Kada ka tsaya koina, sai mun sauka a birnin.

Amma Allah na maganin munafuki, in bai mutu ba ya Ialace. Gama sai ya ce wa ransa, Da saukata Urushalima zan mai da ita hurumin Yahudawa kai tsaye. 5 Amma da ya faɗi kalmomin nan, sai Ubangiji, mai ganin kome, Allah na Israilawa, ya mangare shi da ciwon ciki wanda ba ya warkewa. Sai kuma duk jikinsa ya ɗume da ciwo. 6 Haka ne kuwa ya kamace shi, domin ga shi, azaba mai tsanani ta same shi irin wadda ya gasa wa sauran jamaa. 7 Amma duk da haka, ɗan talikin nan bai saduda ba, sai ma rashin hankalin nan nasa ke ƙaruwa, sai ƙwaffa yake yi a kan Yahudawa, yana cewa a ƙara yin sauri a isa birnin Urushalima. Ba zato ba tsammani, sai ya ɓingiro daga kan karusa din, ya kuwa yi mugun faɗuwa, har dukan gaɓoɓin jikinsa suka mammotsa. 8 Ta haka shi da ke cika baki yana hurji, yana faɗar abin da ya ga dama, sai ga shi ya ɓingire, ana tā da shi a kan gado. Ta nan sai ikon Maɗaukaki ya fito fili zahiri, kowa da kowa ya gani. 9 Tun kafin wannan jairi ya i da mutuwa kuwa, sai da tsutsotsi suka fara fitowa daga jikinsa tukuna, jikinsa ya ruɓe. Saboda tsananin ɗoyin jikin, sai da dukan sojoji suka doɗe hanci. 10 Wanda ba da daɗewa ba yake da taƙama, wai yana mulkin sama da ƙasa, ga shi, yanzu ba wanda ke so ya taɓa shi, don ɗoyin jikinsa ya hana kowa kusatarsa.

11 Ana cikin haka, sai ya farfado, ya komo cikin hankalinsa, ya gane ba mai yi sai Allah, don wuyar da ya sha. 12 Da dai ya kasa ɗaurewa da ɗoyin jikinsa, sai ya ce, Kai, amma ba wani abu da ya fi ga mutum kamar ya zama bawan Allah. Duk mutum mai mutuwa bai kamata ya tsammaci yana daidai da Allah ba. 13 Tilas, ba haƙuri ba, sai jairin nan ya tuba ga Ubangiji, wanda bai ma kamata Ubangiji ya ji ƙansa ba, inda ya rantse, ya ce 14 birnin nan mai tsarki, da ya yi niyyar mayarwa a kufai da kuma hurumi, yanzu zai yanta shi. 15 Da Yahudawan da ke cikinsa, waɗanda dā ya ce ba su cancanci a rufe su a kabari ba, sai a bar su waje kawai, su da yayansu, domin kamuka da ungulai su sami abinci, yanzu kuma ya ce zai sa dukansu su sami yanci irin na Helenawan birnin Atina. 16 Wuri Mai Tsarki kuma, da ya nuna wa matuƙar wulakanci, zai girmama shi yanzu, ya riƙa yi wa wurin sadaka mai tsoka. Zai kuma mayar da kayayyaƙin Wuri Mai Tsarki da ya satar, zai mayar da dukansu, har ma ya ninƙa. Kayan hadayar da ake bukata kuma zai bayar, da kuɗin harajin da zai riƙa samu. 17 Daga ƙarshe dai, shi ma kansa ya ce zai zama Bayahude. Ya kuma alkawarta cewa zai ziyarci unguwanin Yahudawa domin ya bayyana ikon Allah da ya gani zahiri. 18 Amma da ya ji dai kamar ba za a yi da shi ba, gama Allah yana horonsa daidai, sai ya karaya a zuci, ya ɗauki alkalami, ya rubuta wa Yahudawa wasiƙa, wadda ke ƙunshi da roƙe‑roƙensa gare su. Ga abubuwan da ya rubuta:

19 Zuwa ga amintattuna Yalmdawa, daga Antiyaku, sarkinku da kuma babban shugabanku. Gaisuwa mai yawan gaske da fatan alheri duk a gare ku. 20 In kuna nan lafiya, ku da iyalinku, da kuma alamuran yau da kullum da kuka sa gaba, kai, na fi kowa godiya ga Allah. Ni dai yanzu ina nan a ikon Allah. 21 Duk ina tuna da girma da ladabin da kuka nuna mini. Lokacin da na dawo daga yaƙin Farisa, ciwo ya matsa mini. Saboda haka na ga dole in yi shirin yadda za a kiyaye lafiyar jamaa duka, 22 Har yanzu ban ba mutuwa kai ba, domin ina fata zan warke daga ciwona. 23 Amma na sani a lokacin da mahaifina ya tafi nesa don ya ƙara faɗin mulkinsa, sai ya naɗa wanda zai gaje shi, 24 domin in wani abu ya faru, ko in aka ji wani labari mai karya gwiwa, jamaar gari sun san magajin garinsu da shugaban mulkinsu, ba za su damu ba. 25 Bayan haka kuma, duk ina sane da abin da maƙwabtan yayan sarakuna suke yi, musamman waɗanda ke kan iyakar mulkina, yadda suke jira, su ga abin da zai faru. Don haka na zaɓi ɗana Antiyaku ya ci sarauta bayana, wanda sau tari na amince wa, na kuma gabatar da shi a gabanku lokacin da na yi tafiya mai nisa zuwa can arewa. Shi ma na rubuta masa wasiƙa game da wannan alamari. 26 Saboda haka ina yi muku gargaɗi, ina kuma roƙonku, cewa ku riƙa tunawa da alheran da jamaarku da kowannenku kuka samu wurina, kowannenku kuwa ya ci gaba da sona da son ɗana gaba daya. 27 Domin na tabbata shi zai ɗauki halina, zai ma yi maamalar adalci da gaskiya da ku.

28 Ta haka mai kisankan nan, sarkin cika baki, bayan ya sha irin wuyar da ya riƙa gasa wa mutane, sai ya yi wata irin mutuwa mai bantausayin gaske, inda ya yi mutuwar kare a tsaunukan baƙon gari. 29 Sai Filibus, wani ɗan gidansa, ya ɗau gawar ya kai gida, amma da ya shiga yin fargaban ɗan Antiyaku, sai ya kawar da jiki zuwa gun Talomi Filamitu, Sarkin Masar.

10. Tsabtace Birnin Urushalima da Haikalin Allah

1 Yanzu Makabi da jamaarsa da ya ke Ubangiji ne ke musu jagora, sai suka mallaki Haikalin Allah da birnin Urushalima. 2 Suka kuma rushe bagaden da baƙi suka gina a tsakar gari, suka kuma tuge darnuka waɗanda ke kewaye da filin bauta wa gumaka. 3 Suka tsabtace Wuri Mai Tsarki, suka sāke gina wani bagade. Saan nan suka burga wuta wadda suka yi hadayar ƙonawa da ita, abin da suka rabu da yi yau kamar shekara biyu, suka ƙona turare, suka kunkunna fitilu, suka kuma shirya gurasar ajiyewa. 4 Da suka gama yin haka, duk sai suka rusuna, suka roƙi Ubangiji ya fisshe su daga irin wannan tsaka mai wuya haka, suka ce, Ya Ubangiji, ko mun saɓa maka nan gaba, ka hore mu kaɗan da kanka. Amma kada ka danka mu a hannun wata alumma wadda ba ta san kome ba. 5 A ranar da baƙi suka lalata Wuri Mai Tsarki, ran nan ne aka share shi, wato rana ashirin da biyar ga watan Kisle.

6 Suka kwana takwas suna ci, suna sha, suna holewa, kamar yadda suke yi a ranakun Idin Bukkoki. Suna yi, suna tuna yadda ba da daɗewa ba ne suka riƙa yin Idin Bukkoki a duwatsu da kogwanni kamar namomin jeji. 7 Saboda haka sai suka riƙe sanduna waɗanda suka ɗaɗɗaura wa ganyen itatuwa, kamar su ɓaure, da gwandar dawa, da kuma na giginya. Suka kuma yi waƙar yabo da godiya ga wanda ya ba da nasarar sāke tsarkake Wuri Mai Tsarki nan nasa. 8 Suka kafa wata doka a idon kowa, cewa dole ne Yahudawa su riƙa yin wannan idi kowace shekara in ranakun nan sun kewayo.

Mutuwar Talomi

9 Ta haka zamanin Antiyaku, wanda wani lokaci ake ce da shi Afifanesa, ya shuɗe. 10 Yanzu za mu gaya muku abin da ya faru a zamanin mulkin Antiyaku, wanda wani lokaci ake ce da shi Yufatari, ɗan jairin mutumin nan da muka yi magana dazu. Za mu kuma ɗan bayyana manyan wahalolin da suka faru a lokacin yaƙe‑yaƙe. 11 Da wannan yaro ya hau kujerar mulkin, sai ya zaɓi wani mutum mai suna Lisiyas, ya naɗa shi mai jagorancin mulki da shugaban Kilisuriya, da na Finikiya. 12 Talomi, wanda aka ce da shi Makarom, sai ya shiga nuna wa Yahudawa jinƙai saboda mugun abin da aka yi musu dā, ya nufa a riƙa yin kyakkyawar maamala da su. 13 Da ya fara yin haka, sai yan majalisar sarki suka kai ƙararsa gun sarki. Talomi sai kawai ya ji kowa na kiransa maci amana, domin sun ce ya yi watsi da Kubrus, wurin da Filamita ya danƙa masa, ya ma goyi bayan sarki Antiyaku, wanda ke da suna Afifanesa, wato ya zama inuwar giginya na nesa ka sha ta. Da ya ga duk kowa ya juya masa baya, ba su kuma bin umarnansa, sai ya ɗirki dafi, ya mutu.

Yahudawa sun Ci Edomawa

14 Da Gorgiyus ya zama hakimin wurin, sai ya shiga ɗibar sojan ijara, ya shiga gwabza yaƙi da Yahudawa, ba kama hannun yaro. 15 A lokacin nan Edomawa, waɗanda ke riƙe da manyan mafakai, su ma sai ya zama ba sa ga maciji da Yahudawa, suka riƙa marabtar waɗanda shugabannin Urushalima suka koro, suka kuma nuna halin son hura wuta, ba kashe ta ba. 16 Amma Makabin nan da jamaarsa, bayan sun yi addua sun roƙi Allah ya taya su, sai suka yi ƙundumbala, suka auka wa Edomawa a mafakansu. 17 Suka kore su fata fata, suka ci wuraren tsaro, sai su kori masu tsaron garu, su yi ta yin korar fage da su. Duk wanda suka ci ma, sai su take su yanke. Nan da nan suka aika da kimmanin dubu ashirin garinsu na kaito. 18 A loton ne mutum dubu tara suka rurruga suka shiga manyan hasumiyoyi biyu masu ƙarfi duk da abincinsu da makamansu. 19 Sai Makabin nan ya cuna musu Saminu, da Yusufu, da Zakiyas, da dai isassun mutane don a tsare abokan gāba cikin maɓoyansu. Shi kuwa ya tafi wuraren da ya tsammaci an fi bukatarsa. 20 Amma waɗansu daga jamaar Saminu, waɗanda ba abin da ya rufe musu ido kamar kuɗi, suka amshi cin hanci daga wurin waɗansu da ke cikin hasumiyoyin nan. Da aka cika musu aljihunsu, sai suka ƙyale su, suka tsira. 21 Da Makabi ya ji abin da ya faru, sai ya tara jarumawan soja, ya ja musu kunnuwa yana cewa, Don me kuka ba da yanuwanku a kan shaanin kuɗi, kuka yanta abokan gāba don su yake ku? 22 Sai ya sa a yanyanke masu cin amanan nan, ba tare da ɓata lokaci ba, ya kuma ci hasumiyoyin nan guda biyu. 23 Da ya ke duk inda ya buga, ba abin da yake yi sai karo da saa, sai ya kakkashe jamaar da ke cikin hasumiyoyin nan guda biyu, yawansu kuwa ya zarce dubu ashirin.

Yahudawa sun Ci Timoti

24 Yanzu kuwa Timoti, wanda Yahudawa suka taɓa yi wa fata fata dā, sai ya kwashe sojan ijara na ƙafa masu ɗumbun yawa daga wurare dabam dabam, da kuma sojan doki masu yawa daga Asiya. Ya kuwa yiwo wa Yahudiya tsinke, da nufin ya cinye ta ƙarfi da yaji. 25 Da ya gabato garin, sai Makabi da askarawansa suka yi hurwa da toka, suka sassa tsummoki, suna ta roƙon Allah. 26 Suka yi ta yin rubda ciki a gaban bagade, suka roƙi Allah, suka ce, Ka kori abokan gābanmu, ka kuma ƙasƙanta maƙiyanmu, kamar dai yadda sharia ta alkawarta.

27 Da suka gama adduarsu, sai kowa ya saɓi kayan yaƙi, suka ja dāgā can bayan gari. Da suka ɗan matsi abokan gāba kadan, sai suka tsaitsaya cirko cirko. 28 Can da asuba ta keto, sai suka auka wa juna da yaƙi. Sai ƙungiyar Yahudawa ta ga alamar nasara saboda gwanintarsu da kuma taimakon Ubangiji, ƙungiyar Timoti sai duk suka haɗiyi kwabo.

29 Da yaƙin ya rincaɓe, sai abokan gāba suka ga kamar waɗansu dakarai guda biyar sun ɗiro daga sama bisa waɗansu ƙosassun dawakai masu linzaman zinariya, suna yi wa Yahudawa jagora. 30 Dakaran sun kekkewaye Makabi da kayan yaƙinsu yadda, sai kuɗa kawai ne ke iya taɓa shi ya kwana Iafiya. Suna ta hahharba kibau, suna kuma jifar abokan gāba da yan komaɗai masu hasken wuta. Saboda haka, sai abokan gaba suka ruɗe, suka yi dundumi, suka daburce, kowa ya ruga nasa wuri. 31 Dubu biyu da ɗari biyar suka sheƙa lahira, banda sojan doki ɗari shida. 32 Timoti kuwa, shi da ya ke yi musu jagora, sai ya ranta ciki na kare zuwa wata maɓoya, mai suna Gazara. Wani birni ne mai ƙaƙƙarfar garu, inda wani shugaba yake, mai suna Kairau.

33 Sai Makabi da mazajensa suka matsi birnin, suka kewaye shi da yaƙi har kwana huɗu, don na ciki su galabaita. 34 Na cikin kuwa, da suke dogara da ƙarfin garun, sai suka cika baki suna hurzarwa da zage‑zage, wai ko da wa suka haɗu, kwanansa ya ƙare. 35 Amma da asubar fari ran kwana na biyar, sai waɗansu samari su ashirin, daga ƙungiyar Makabi suka ƙosa da wannan irin cika baki, suka yi kukan kura, suka ragargaza garun, suka shiga, suka yi ta banke duk wanda suka tarar. 36 Waɗansu mazajen Yahuza suka riƙa ɓullo wa na cikin mafakar ta baya. Sai suka ƙone hasumiyoyi, suna ƙone na ciki da ransu. Wadansu soja kuma suka rushe ƙyamaren kofar gari, suka shigar da sauran sojan da ke waje, duk suka mamaye birnin. 37 Timoti ya ɓoye cikin rijiya, amma aka same shi, aka kashe shi da ɗanuwansa, Kairau, da wani mai suna Afalafana. 38 Da suka ga duk sun kintsa su, sai suka yi waƙar yabon Allah ga Ubangiji wanda ya ba Israilawa saa.

11. Yahudawa sun Ci Lisiyas

1 Ba a daɗe da yin haka ba, sai Lisiyas, bafaden nan wanda yake dangantaka da sarki, ya kuma yi jagorar mulkin, ya husata a kan abin da ya faru. 2 Sai ya tara sojan ƙafa wajen dubu tamanin, da dai duk sojansa na doki, ya fita don ya auka wa Yahudawa da yaƙi. Nufinsa ya ƙwato wa Helenawa birnin Urushalima, 3 ya kuma yi burinsa na sa wa Haikalin Allah kuɗin haraji, kamar yadda ya yi wa gidajen gumakan sauran alumma, a kuma riƙa zaɓen babban firist kowace shekara ga wanda zai ba da cin hanci. 4 Bai ma kula da ikon Allah ba, sai kawai ya dukufa a kan sojan nan nasa masu ɗumbun yawa na ƙafa, da dubban nan na doki, da kuma giwayen nan nasa guda tamanin.

5 Sai ya auka wa Yahudiya kai tsaye, ya doshi Bet‑zur haigan, wadda ke da nisa kimmanin mil ashirin daga Urushalima, ya matsa wa gun lamba. 6 Da Makabi da askarawansa suka ji, wai Lisiyas ya auka wa wuraren tsaron nan, su da dukan jamaarsu, sai suka ɗaɗɗora hannuwa a ka, suka fashe da kuka, suka kuma roƙi Ubangiji, ya aiko da malaika wanda zai ceci Israilawa. 7 Makabi ne ya fara saɓa makamai, ya fita, ya ce wa sauran, Dukanmu mu sai da rawnu domin yanuwanmu su tsira. Duk suka yiwo kukan kura gaba ɗaya, suka fito. 8 A can ne, tun suna kusa da Urushalima, suka hangi wani mahayin ingarma a gabansu, yafe da fararen tufafi, yana jefa takobinsa na zinariya sama, yana bi, yana caɓewa. 9 Da ganinsa haka, sai suka yabi jinƙan Allah gaba ɗaya, suka yi ƙarfi a zuci kuma, har ya zamana a shirye suke su auka wa duk abin da ya tare musu gaba, mutane, ko mugayen namonin jeji, ko ma da katangan ƙarfe ne. 10 Tun da ya ke Ubangiji ya ji tausayinsu haka, sai suka kai hari gaba ɗaya, tare da mataimakin nan nasu daga Sama. 11 Da suka yi wani ƙundumbala, sai da suka hallaka sojan ƙafa dubu goma sha ɗaya, da na doki dubu da ɗari shida nan take, suka sa sauran ranta ciki na kare. 12 Yawancin waɗanda suka tsira, sai suka yi ƙazamin rauni, suka kuma yi hasarar duk kayansu na yaƙi.

Lisiyas shi ma, da dai ya ga abin ba na arziki ba ne, sai ya ce, Kafa, me na ci ban ba ki ba?

Yahudawa sun yi Sulhu da Suriyawa

13 Amma da ya ke Lisiyas mai azanci ne, sai ya yi mamakin nasarar da Yahudawa ke samu a kansa, nan da nan kuma ya gane ba mai iya karawa da Yahudawa, gama Allah mai iko yana taya su. Sai ya aika da saƙon a yi sulhun gaskiya a cikin ruwan sanyi. Ya ƙara da cewa, Zan shawarci sarki, ina kuwa tsammani ba zai juya mini baya ba, zai nuna, shi yanzu ya zama abokinku. 14 Da ya ke Makabin nan mai kula da lafiyar jamaa ne da jin daɗdinsu, sai ya amince da dukan abubuwan da Lisiyas ya roƙa. Sarki kuma ya sa hannu a dukan kaidodin da Makabi ya rubuta game da Yahudawa, ya ba Lisiyas su ya kai wa Makabi.

Wasiƙar Lisiyas zuwa ga Yahudawa

16 Ga wasiƙar da Lisiyas ya rubuta wa Yahudawa, inda ya ce, Daga hannun Lisiyas zuwa ga Yahudawa. Gaisuwa mai yawa da fatan alheri.

17 Yahaya da Absalom waɗanda kuka aiko gunmu, sun kawo mini wasiƙarku da kuka sa hannunku a kai, sun kuma roƙe ni in ba da amsa a kan abubuwan da ta ƙunsa. 18 Na kuma sanar da sarki dukan abin da ya kamata ya sani. Ya kuma yarda da yawancin abubuwan da kuka faɗa. 19 Idan za ku ci gaba da nuna halayen nan naku na kirki ga mulkinmu, zan duba hanyoyin da za mu bi don ƙara inganta zaman jin daɗinku nan gaba. 20 A game da waɗannan alamura kuma, na umarci wakilaina da wakilanku su yi shawara da ku dalla dalla a kansu. 21 Allah ya taya mana. Amin. Mun hatimci wannan wasiƙa ran ashirin da huɗu ga watan nan na Diyaskorinti, a shekara ta ɗari da arbain da takwas.

Wasiƙar Sarki Antiyaku zuwa ga Lisiyas

22 Ga abin da wasiƙar sarkin ta ce, Daga hannun sarki Antiyaku zuwa ga Lisiyas ɗanuwansa. Gaisuwa kwando kwando. 23 Tun da ya ke ubanmu ya ƙaura, ya tafi yin wata sarauta a can sama, muna burin kada yawan tashin-tashin ya dami mutanen nan samun daula cikin harkokinsu. 24 Mun sami labari, cewa Yahudawa ba su yi naam da aladarmu ta Helenawa ba, suna so a ƙyale su, su ci gaba da bin aladarsu irin ta Yahudawa. 25 A ganina, tun da ya ke mun shawarta a ƙyale wannan alumma, ta wala, to, sai mu mayar musu da ɗakin ibadarsu, mu kuma bar su su bi aladun kakanninsu. 26 Zai yi kyau ƙwarai da gaske yanzu, in ka aika musu da saƙon yanci da na abokantaka, domin su san abin da muke ciki, su ma su saki jiki, su yi ta farin ciki da harkokinsu na yau da kullum.

Wasiƙar Sarki zuwa ga Yahudawa

27 Ga kuma abin da wasiƙar sarki zuwa ga alummar Yahudawa ta ce, Daga gare ni sarki Antiyaku, zuwa ga yan majalisar Yahudawa da sauran Yahudawa ga baki daya. Gaisuwa mai yawan gaske. 28 Idan kuna nan lafiya kalau, na ji dadin haka. Mu ma a nan lafiya sumul muke. 29 Manalawus ya gaya mana, cewa kuna so ku daddawo gida, ku ci gaba da yin alamuranku. 30 Saboda haka, duk Yahudawan da suka iso gida kafin ran talatin ga watan nan na Santiku, mun ba su cikakken izni 31 su bi nasu dokoki a kan abinci da sauran abubuwa, kamar dai yadda suka yi dā, ba wanda za a sāke wulakantawa, wai don ya yi wani ɗan kuskuren da bai sani ba. 32 Ga Manalawus nan kuma na aiko muku domin ya ƙarfafa muku gwiwa. 33 Gamon alheri. Mun hatimci wasiƙar ran goma sha biyar ga watan Samiku, shekara ta ɗari da arbain da takwas (164 B.C.).

Wasiƙar Romawa zuwa ga Yahudawa

34 Mutanen Roma ma sai da suka rubuta wasiƙar da ta ce, Daga Kintasu Mamiyus da Titus Manau, jakadun Roma, zuwa ga Yahudawa. Gaisuwa mai yawan gaske da fatan atheri. 35 Bisa ga abubuwan da Lisiyas ɗanuwan sarki ya ce muku, mu ma mun yarda. 36 Amma bisa ga alamarin da ya ce, Sai kun ga sarki, kun yi shawara a kai, sai ku aiko mana, domin mu gaya wa sarki abin da zai dace da ku. Gama yanzu hakanan muna kan hanyarmu ta zuwa Antakiya. 37 Saboda haka ku hanzarta, ku aiko da dattawa, domin su sanar da mu abin da kuka ga ya kamata. 38 Gamon alheri. Mun sa hatiminmu a ran goma sha biyar ga watan Santiku, a shekara ta ɗari da arbain da takwas.

12. An Sake Matsa wa Yahudawa Lamba

1 Da aka kai ga wannan yarjejeniya, sai Lisiyas ya koma wurin sarki, Yalludawa kuma suka ci gaba da nome‑nomensu. 2 Amma waɗansu hakimai na wurare dabam dabam, misali su Timoti da Afaloni, yayan Ganayus, da su Hayaromi da Damafani, tun ba Nikanar shugaban Kubrusawa ba, ba su bar Yahudawa su yi zaman lafiya da salama ba.

3 Wadansu jairai kuma daga Yafa, ai, abin da suka yi ya wuce kima. Suka gayyaci Yahudawan da ke zaune a cikinsu, su da matansu da yayansu wai su tafi yawo a cikin waɗansu jiragen ruwa da aka shirya. Ba su nuna wa Yahudawa wata alama ta rashin amana ba. 4 Da ya ke duk manyan gari ne suka ce a gayyaci Yahudawa, da ya ke kuma Yahudawa suna neman salama, ba su tsammaci wani hainci ba ko kaɗan, suka yarda su shiga jiragen. Sai mutanen nan na Yafa suka tafi da su wani wuri mai zurfi na teku, suka dulmuyar da su. Wajen mutum metan ne, suka mutu ta haka.

Kokarin da Yahuza Makabi ya Yi

5 Da fa Yahuza ya ji irin mugun abin da aka yi wa mutanen ƙasarsa, sai ya tattara dakarunsa, 6 ya kuma roƙi taimakon Allah mai shariar adalci, sai ya tafi da mutanensa, ya auka wa waɗanda suka yi wa yanuwan nan nasu kisan gilla. Ya ƙone tashar jiragen ruwansu da dad dare, ya kuma ƙone dukan jiragensu, ya karkashe duk waɗanda suka yiwo gudun hijira zuwa wurin. 7 Saan nan da ya ke an kukkulle ƙofolin birnin, sai ya ɗan kawar da jiki, yana nufin wata rana ya koma ya karkashe dukan mutanen Yafa.

8 Yahuza kuma ya ji wani labari, cewa mutanen Yamaniya su ma suna shirin kashe duk Yahudawan da ke cikinsu. 9 Sai ya auka wa mutanen Yamaniya da duhu, ya ƙone tashar jiragen ruwansu da kuma jiragen, har aka rika ganin harshen wutar a birnin Urushalima, nisan kimmanin mil talatin.

10 Da suka gama da waɗannan, suka sauya zuwa gun Timoti kuma. Sai Larabawa fiye da dubu biyar na sojan kafa, da ɗari biyar na doki suka auka musu. 11 Da aka gwabza, sai sojan Yahuza suka yi nasara da taimakon Allah. Nan take sai Larabawa suka roƙi Yahuza, cewa sun tuba, sun bi shi, idan ya alkawarta yin abuta da su. Suka ce, Za mu ba ka shanu ku ci, kai da sojanka. Za mu kuma taimake ku ta kowace hanya. 12 Da Yahuza ya ga mai yiwuwa ne su taimaka ƙwarai, sai ya yarda, aka yi sulhu. Bayan an yi yarjejeniyar yin abuta, sai Larabawan suka koma, suka shiga alfarwansu.

13 Sai Yahuza ya lashe wani ɗan birni mai suna Kasafina, wanda aka ƙayatar ƙwarai, mai kakkaurar garu, wanda ke cike da arna iri iri, ga su nan barkatai. 14 Waɗanda ke cikin birni, ganin yadda suke da garu mai kauri da abinci mai yawa, sai suka yi ta yi wa Yahuza da askarawansa barancin gaske, suna yi musu gwalo, har suna cewa, Duk ran da muka yi karon battar ƙarfe da ku, kāshinku ya bushe. 15 Amma Yahuza da askarawansa suka yi ta roƙon wanda ya halicci duniya, wanda ya rushe birnin Yariko ba tare da makamin hauran ƙyamaren ƙofa ba ko tsanin hawan garu, a zamanin Joshuwa. Saan nan Yahudawa suka yi kukan kura, suka hau garun. 16 Da ikon Allah suka ci birnin, suka yanyanka mutanen da suka fi bakin bunu yawa, yadda wani ɗan tafki da ke bayan garin, mai tsawon rabin mil ya cika makil da jini.

17 Da suka gama, suka bar garin da nisan mil tasain, sai ga su a Gazara, wani gari na Yahudawa da ake kira Tobiyawa. 18 Ba su sami Timoti a can ba, gama saan nan ya riga ya zare jiki daga garin, bai yi kome ba tukuna, sai ya bar wata babbar rundunar soja a damfararriyar kagara. 19 Sai Dasitaya da Susibataris waɗanda suke jarumawa ɗin na Makabi, suka yi tafiya, suka hallaka waɗanda Timoti ya ɓoye a kagaran nan, yawansu kuwa ya kai mutum fiye da dubu goma. 20 Amma Makabin, shi sai ya raba sojansa runduna runduna a kowace runduna ya sa shugaba ɗaya, suka kuwa runtumi Timoti wanda ke da sojan ƙafa fiye da dubu ɗari da dubu ashirin, da na doki dubu biyu da ɗari biyar. 21 Da fa Timoti ya ji su Yahuza sun doso, sai ya aika da mata da yara, har ma da akwatunan kaya zuwa wani wuri mai suna Kamayim, gama bahagon wuri ne, yana da wuya soja su kutsa kai ciki. 22 Amma da askarawan runduna ta farko ta sojan Yahuza ta ɓullo, sai duk abokan gāba suka fāɗi sumammu saboda ganin wani haske mai bantsoro na wanda ke ganin dukan abu. Da suka farfado, suka tashi suka ranta ciki na kare. Banda haka ma, da ya ke sun rurruɗe, sai suka yi ta caɓa wa juna takuba. 23 Yahuza kuwa ya ƙara matsa wa masu saɓon nan lamba, yana ta fille musu kawuna da takobi. Kafin a ce haka, ya aika da mutum dubu talatin garinsu na kaito.

24 Timoti kuwa sai su Dasitaya da Susibataris suka yi masa kamun zakara, su da askarawansu. Amma da ya ke Timoti mutum ne mai wayo, sai ya durƙusa nan a gabansu, yana ta yi musu hurwa, kada su kashe shi, yana cewa, Ku yi mini rai, saboda ina da danginku da dama kamammu. In kuwa na mutu yanzu, sun banu sun Ialace. 25 Da Yahudawa suka ga dai alkawarai nasa sun yi yawa, har kuma yana yan rantse‑rantse, sai suka sake shi domin su ceci yanuwansu.

Wadansu Nasarorin da Yahuza Makabi ya Yi

26 Saan nan Yahuza ya karya linzami, ya nufi Kamayim da gidan gunkin nan Ataragata, ya auka musu, ya kashe mutane dubu ashirin da biyar can ma. 27 Da ya ga ya cinye su, sai ya doshi Efron, wani wurin tsaro inda jamaa iri iri suke zaune. Sai ƙarfafan samarin birnin suka tsaya koina bisa garun, suna ta harbi ba ji ba gani, domin sun ga suna da kayan yaƙi, ga su nan barkatai. 27 Amma bayan Yahudawa sun roƙi Mai Iko Dukka wanda yakan yi ɗaya ɗaya da abokan gāba da ƙyiftawar ido, sai suka maye birnin, suka kashe mutum dubu ashirin da biyar daga cikin waɗanda ke a birnin.

29 Fitowa daga nan ke da wuya, sai Yahudawa suka nufi Saitafolis, wani gari mai nisa mil sabain da biyar daga Urushalima. 30 Amma Yahudawan da ke can suka faɗi irin halin kirki da ake yi musu a wurin, da kuma irin taimakon da ake yi musu in suna shan wata wahala. 31 Sai sojan suka yi wa mutanen garin godiya, suna cewa, To, muna so ku ci gaba da nuna wa jamaarmu alheri. Sai suka zarce zuwa Urushalima, gama idin yankan alkama ya gabato, wato Idin Fentikos.

32 Bayan Idin Fentikos, sai kuma suka wanke hannu, suka fāɗa wa Gorgiyus, hakimin Edom. 33 Gorgiyus kuma ya fito da nasa sojan ƙafa dubu uku, da na doki ɗari hudu. 34 Da suka gwabza, har yaƙi ya ci, Yahudawa kaɗan suka mutu a gun yaƙin. 35 Amma wani mai suna Dasitaya, ɗaya daga cikin jamaar Bakanori, wani shahararren mahayin doki, ya yi wuf, ya cafke Gorgiyus, ya murɗe shi cikin cunar riga, ya yi ta ja, da niyya ya kai shi gun Makabi da rai. Amma wani mahayi na ƙungiyar Tarakiyawa ya laɓaɓo, ya sare wa Dasitaya hannun a kafada. Daganan sai Gorgiyus ya ranta, sai Marisa. 36 Saan nan Idirisu da jamaarsa sun yi sara da takuba har sun gaji. Sai Yahuza ya kira sunan Ubangiji, domin Ubangiji ya nuna shi mataimakinsu ne, ya kuma shugabanci yaƙin. 11 Sai Yahuza ya kira askarawansa da yarensu, ya ce, Kai, ku tashi, mu auka musu, yana tafe, yana waƙa. Mutanen Gorgiyus ba sani ba sabo, sai ga maza bisa kansu, duk suka daburce, suka gudu.

Yahudawa sun Yi wa Matattu Sadaka

38 Yahuza ya haɗa sojansa kaf, saan nan ya tafi birnin Adullam. Da ya ke rana ta bakwai ta kusa kewayowa, sai suka tsabtace kansu bisa ga aladarsu, suka yi sujadarsu ta ran Asabar. 39 Kashegari, da ya ke abin ya zama ranar, dole sai Yahuza da jamaarsa suka tafi, suka kwakkwaso gawawwakin waɗanda suka mutu, suka rurrufe a hurumin kakanninsu. 40 Amma a jikin kowane mamaci suka sami layun da ke shaida masu bauta wa ɗan gunkin nan na Yamaniya ne, wato irin layun da sharia ta hana Yahudawa su rataya. Nan take sai suka gane, wannan ne dalilin da ya sa mutanen ba su kai labari ba. 41 Ga baki ɗaya sai suka yi wa Ubangiji, mai shariar adalci, wanda ke bayyana abubuwan da ke ɓoye su fito fili, yabo. 42 Sai suka ci gaba da roƙon Allah, suka ce, Ya Ubangiji, ka ɗauraye matattun nan daga duk laifofin da suka yi maka.

Jarumin nan Yahuza yana zagawa, yana ja wa jamaa kunne cewa, Ku yi nesa da yin saɓo dai, gama kun ga yadda waɗanda suka yi saɓo suka yi ta ɓingiri. Gani ga wane kuwa ya ishi wane tsoron Allah. 43 Nan take sai ya fara karɓar wata sadaka a gun sojansa, har ya tara kuɗi, azurfa dubu biyu, ya aika da su Urushalima, ya ce firistoci su miƙa hadaya domin Allah ya wanke wa matattun laifofi. Ta yin haka sai ya kyauta ƙwarai da gaske, domin ya tabbata da tashin kiyama. 44 Gama da bai gaskata waɗanda suka mutu za su tashi ba, lalle da an yi babban wawanci a kan roƙon Allah saboda waɗanda suka mutu. 45 Amma da ya ke yana neman sakamakon nan mai ɗaukaka wanda duk waɗanda suka mutu suna bin Allah za su samu, to, wannan dabara ta yi kyau, ya kamata kuma a yi ta. Ta haka ne ya yi wa matattu addua, domin su sami gafarar laifofin da suka taɓa yi wa Allah.

13. Suriyawa sun Kai wa Yahudiya Hari

1 A shekara ta ɗari da arbain da tara (163 ko 1ɓ2 B.C.) sai Yahuza da askarawansa suka sami labari, cewa Antiyaku Yufatari zai wayi gari, ya auka wa Yahudiya da dakaru masu ɗumbun yawa. 2 Ashe, Antiyaku tare da Lisiyas yake tafe, Lisiyas ɗin nan, wanda ya riƙe shi, yake kuma da ragamar mulkinsa. Suna da sojan ƙafa, Helenawa, dubu ɗari da dubu goma, da na doki dubu biyar da ɗari uku, da giwaye ashirin da biyu, da kuma karusai ɗari uku da ke ɗauke da waɗansu irin adduna.

Mutuwar Manalawus

3 Manalawus ma sai ya goyi bayansu, amma da baki biyu, har ya ce wa Antiyaku, Ku ƙara matsa musu lamba. Bai yi haka don kāre ƙasarsa ba, amma burinsa, wai don kawai a ba shi wani babban matsayi a aikin mulki. 4 Amma Sarkin sarakuna ya tura Antiyaku don ya husata da Manalawus mai saɓon nan.

Da dai Lisiyas ya gaya wa Antiyaku abin da Manalawus ya yi, ya ce, Shi ne duk ya jawo hargitsin.

Sai Antiyaku ya ce, Ku kama shi ku tafi da shi garin Baroya, ku kashe shi ta yadda mutanen wurin ke yanke hukuncin kisa. 5 Gama akwai wata hasumiya a garin, mai bisa kamu hamsin cike yake da toka. Hasumiyar tana da wani ƙaton kududdufi a tsaka, daga saman hasumiyar wani bango mai shan zobe ya gangara zuwa ga tokar da ke can ƙasa. 6 A babban kududdufin nan ne suka tunkuda duk wanda ya saɓa wa gidan gunkinsu, ko ya yi wani babban laifi dabam. 7 Ta haka ne aka kashe Manalawus mai saɓon nan. Ƙone shi aka yi ƙurmus, yadda ba sai an yi wahalar rufewa ba. 8 Ya kamata a ƙone Manalawus haka, gama sau tari Manalawus na wulakanta wurin da ake ƙona hadaya mai tsarki ga Allah.

Yahudawa sun Yaƙi Mutanen Sarki a Modayin

9 Sai hatsabibin sabon sarkin ya tashi, wai zai nuna wa Yahudawa mugun halin da ubansa ya yi a nasa zamani. 10 Amma da dai Yahum ya ji haka, sai ya umarci Yahudawa su riƙa yin addua ga Ubangiji, ba dare ba rana, domin Ubangiji ya yi musu taimakon gaggawa 11 lokacin da abokan gāba ke nema su hana su bin sharia, su kuma kwace musu ƙasarsu da Wuri Mai Tsarki, kada kuma Ubangiji ya bar arnan nan masu saɓo su koma cin nasara a kan alummar Yahudawa, wadda ta ɗan fara sake rayuwa. 12 Da duk suka dukufa gaba ɗaya, dukansu suka kwana uku suna roƙon jinƙan Ubangiji tare da kuka, da azumi, da yin sujada ba fasawa. Sai Yahuza ya ƙarfafa musu gwiwa, saan nan ya ce musu, Ku tashi tsaye, kowa ya ja ɗamara.

13 Da ya tattauna, shi da dattawa, sai ya yi nufin kai harin da taimakon Ubangiji, tun kafin askarawan wancan gogan Antiyaku su auka wa Yahudiya su ci birnin. 14 Da ya danƙa kome a ikon Mahalicci, sai ya ce wa askarawansa, Ko da za a ƙare mu da ɗaya ɗaya, mu dai mu kāre dokokinmu, da Haikalin Allah, da birnin, da ƙasar, da kuma tsarin mulkinmu. Sai ya kafa sansaninsa kusa da Modayin.

15 Ya ce wa askarawansa, Saad da kuka ga abokan gāba tafe, ku ce, Da taimakon Allah. Ya kuma zaɓi dakarun da ko wuta aka ce su fāɗa, sai su fāɗa. Ya auka wa tantin sarki, suka ma kashe jamaar sansanin abokan gāba masu yawa wajen dubu biyu. Wani soja kama ya sa mashi, ya soke giwar da ke gaba, duk da mahayinta. 16 Daga ƙarshe dai, bayan sun ci nasara sun yi wa sansanin abokan gāba kaca kaca, sai suka koma gida. 17 Gabanin asuba ne wannan ya faru, gama taimakon Ubangiji ne ke yi musu yaƙin.

Yahudawa sun yi Sulhu da Antiyaku

18 Da sarkin ya ɗanɗana kuɗarsa ta hannun Yahudawa, sai ya ce zai sāke dabara don ya ci ƙasarsu. 19 Sai ya auka wa Bet‑zur, wani wurin tsaro na Yahudawa, amma suka taso ƙyeyarsa gaba, suka kore shi fata fata. 20 Saan nan Yahum ya ba askarawansa da ke a Bet‑zur duk abin da suke bukata. 21 Amma Radaku, wani jarumin Yahudawa, sai ya je ya gaya wa abokan gāba duk abin da Yahudawa ke ciki. Yahudawa kuwa suka neme shi, suka kama shi, suka jefa shi kurkuku. 22 Sai sarki Antiyaku ya sake neman ci Bet‑zur ta yin sulhun munafunci da mutanen da ke ciki. Suka yi alkawari da juna, ya ja da baya. 23 Kana ya dawo, ya tada wa Yahuza da jamaarsa, su kuwa suka yarɓar da shi can. Da fa sarki ya ji an ce Filibus, wanda ya bar ragamar mulki a hannunsa, ya yi tawaye yanzu a birnin Antakiya, sai ya daburce, ya kira Yahudawa su yi sulhu da juna, ya yarda da kaidodin da suka ce, ya ma rantse, cewa zai kāre mutuncinsu. Bayan sun ƙulla yarjejeniya, shi da Yahudawa, sai ya yi wa Allah hadaya, ya kuma girmama Wuri Mai Tsarki ta wurin ba da sadakar kuɗi masu tsoka. 24 Ya amince wa Makabi, ya ma mai da shi hakimi tun daga Talamayas har zuwa Gaza. Amma da sarki ya tafi Talamayas, mutanen Talamayas ba su yarda da yarjejeniyar da aka ƙulla ba. Haushi ya kama su matuƙa, har suke so a hamɓarar da kaidodinta. 26 Amma Lisiyas ya tsaya gaban taron, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, yana so su goyi bayansa a kan yarjejeniyar. Ya kuwa yi saa, hankalinsu ya kwanta, suka yarda. Saan nan ya koma Antakiya.

Labarin yadda sarki ya yi ta kai hare-hare ke nan, ana koro shi.

14. Rikicin da Alkima ya Yi

1 Bayan shekara uku, sai Yahuza ya ji labarin Dimitiriyas, ɗan nan na Saluku, ya kutsa kai a tashar jirgin ruwan nan na Turabulus da ƙwararrun soja da jiragen ruwa. 2 Ya ji, wai har ma Dimitiriyas ya ci ƙasar, ya kuma kashe Antiyaku da Lisiyas.

3 Amma wani mutum mai suna Alkimu, wanda dā shi babban firist ne, ya kuma keta haddi da gangan a loton da aka yi tawaye, ya ga ba yadda zai yi ya sāke samun matsayinsa na firistanci gun bagade mai tsarki, 4 sai ya tafi gun Dimitiriyas shekara ta ɗari da hamsin da ɗaya, ya ba shi rawanin zinariya da reshen dabino da kuma rassan zaitun, irin waɗanda a kan sa a Haikalin Allah. A ranar Alkimu bai ce kala ba. 5 Amma sai za ni ta tarar da mu je lokacin da Dimitiriyas ya kira shi wata taruwar majalisarsa, ya kuma ce ya yi tuhumarsa a kan alamarin da Yahudawa suke ciki. Sai Alkima ya ce, 6 Yahudawan nan da ake ce da su Hasidiyawa, waɗanda jaruminsu ke da suna Makabi, sun hana gari sakat da yaƙe‑yaƙe, sun ma hana kwanciyar hankali a ƙasar. 7 Saboda haka an ƙwace mini darajar da na gāda daga kakannina, ina nufin sarautar babban firist. Ga shi kuwa, na taho nan yanzu, 8 da farko dai don na damu da gaske a kan halin da harkokin sarki suke ciki. Abu na biyu kuma shi ne don ina kulawa da mutanen garinmu, gama ta barancin jamaar Makabi waɗanda na faɗan nan, ga shi yanzu alummarmu ta shiga halin ƙaƙa naka yi. 9 Da ka gama binciken koke‑kokemnu sarai, yallaɓai, ina so ka yi juyayin ƙasarmu da lambar da ake matsa wa kabilarmu, da irin alherin nan naka da kake nuna wa kowa da kowa. 10 Gama in dai ɗan sababin nan, Yahuza Makabi, na numfashi, to, mulkin kuwa ba za ta yi zaman lafiya ba. 11 Da dai ya ce haka, nan da nan sai fādawan sarki suka yi farat, suka shiga zuga Dimitiriyas a kan Makabi.

Yahudawa sun Yaƙi Nikanar, sun kuma Sulhunta

12 Nan da nan sai sarki ya ce wa Nikanar, jarumin sojojin giwaye, Na naɗa ka hakimin ƙasar Yahudiya. 13 Ya kuma ce masa, Tashi maza, ka kashe Yahuza, ka kuma yi ɗaya ɗaya da askarawansa, saan nan ka naɗa Alkimu sarautar babban firist na ɗakin sujada mafi girma duka. 14 Da fa arnan nan na Yahudiya da suka so su kori Yahuza suka ji haka, duk sai suka goyi bayan Nikanar, suna tsammani wahalar Yahudawa, da kuma balainsu zai amfana musu wani abu.

15 Da Yahudawa suka ji Nikanar ya doso, su da irin arnan nan, sai suka yi ta hurwa da toka, suna addua ga wanda ke kāre mutanen nan nasa koyaushe, kada ya bari abin mallakarsa ya halaka. 16 Da shugabansu, Yahuza, ya yi wata irin gunza, su kuwa suka yiwo waje, suka nufi wani gari mai suna Adasa, suka ja dāgā. 17 Saminu, wani ɗanuwan Yahuza, ya fara karawa da Nikanar, amma da ya ke mabiyan Nikanar sun kawo harin ba zata, sai suka ɗan kori Saminu. 18 Amma da Nikanar ya shaƙi labarin Yahuza da bijintarsa a yaƙi don kāre mutuncin ƙasarsu, sai jikinsa ya yi sanyi ƙalau. 19 Saboda haka ya aika da Fasidoniyus, da Tiyodata, da Mattatiyas don su ƙulla yarjejeniyar yin abuta da Yahudawa.

20 Da aka tattauna a kai, shugabannin kowace jamaa suka sanar da ita abin da ke nan, jamaa kuma suka ce sun yarda, sai aka ƙulla yarjejeniyar. 21 Shugabanni suka sa ranar da za su ƙara yin nasu taro don su yi shawararsu ta manya. Aka kawo karusa guda daga kowace kungiya ta soja, aka kawo karusa biyu, aka girke. 22 Yahuza ya sa soja ƙungiya ƙungiya don su kāre harin ba zata, kada abokan gāba su kawo wani tashin‑tashin. Amma taron ya tashi lafiya, kowa ya ce Alhamdu lillahi. 23 Nikanar ya share gindi, ya zauna a Urushalima, bai taka was kowa ya zubar ba, ya ma kori yan iskan da suka kewaye shi, don ƙara kiyaye lafiyar garin. 24 Ya kuma riƙa yin dama dama da Yahuza, gama ya shaku kwarai da shi. 25 Har ya gargaɗe shi ya yi aure, ya bar baya. Yahuza kuwa ya yi auren, ya zauna wuri ɗaya, ya shiga shaanin kula da iyali.

Alkima ya Ta da Hankalin Nikanar

26 Amma da Alkima ya ga ran Nikanar da na Yahuza sun gami juna, har sun shaƙu haka, sai ya tafi da takardar yarjejeniya, ya warware wa Dimitiriyas duk abin da aka shirya. Ya ce masa, Nikanar ba ya bin kaidodin mulki, gama har ya ƙulla abuta da Yahuza, ɗan tawayen nan, wai shi ne zai gaji sarautar Nikanar nan gaba.

27 Sarki kuwa ya damu saboda wannan ƙarya da aka sheƙa masa, har ya husata ƙwarai. Sai ya rubuta wa Nikanar, yana cewa, Ban ji daɗin yarjejeniyar da ka yi ba, maza ka aika da Makabin nan Antakiya, a sa shi kurkuku, ba da ɓata lokaci ba. 28 Da saƙon ya kai gun Nikanar, sai ya damu ƙwarai, domin ba ya so ya ta da alkawarinsa da mutumin da bai yi wani laifi ba. 29 Amma da ya ga ba dama a yi ja‑in‑ja da sarki, sai ya yi ta neman hanyar da zai yi wa Makabi zamba da aminci.

30 Makabi kuwa, da ya ga irin take-taken da Nikanar ke yi masa, ga shi kuma, halin Nikanar na sauyawa, sai ya ce, Gara in yi nesa da ɗan sababin nan. Sai ya ɗibi dakaru masu yawan gaske, ya kawar da jiki daga wurin Nikanar.

31 Lokacin da Nikanar ya ga kamar an ruɗe shi, sai ya tafi Haikalin Allah mafi girma duka a loton da firist ke yin hadaya yadda sharia ta faɗa, sai ya ce, Ku fito mini da Makabi, ko da girma da arziki, ko da tsiya.

32 Da dai suka ba shi amsa suka ce, Ba mu ga wanda kake nema ba, har suna rantsuwa.

33 Sai ya ɗaga hannu sama wajen Wuri Mai Tsarki, ya yi rantsuwa kamar haka, ya ce, Har idan ba ku fito mini da Yahuza ɗaurarre ba, yanzu zan rushe Haikalin Allahn nan, da bagaden da ke ciki, in gina wa babban gunkin nan namu Diyonisu wurin shakatawa. 34 Da dai ya ce haka, sai ya sa kai ya fita. Saan nan fa sai firistoci suka ɗora hannuwa a kā, suka yi ta roƙon Allah wanda ya saba kāre alummarsu, suka ce, 35 Ya Ubangijin sama da kasa, ko da ba ka bukatar kome, mun sani kana jin daɗin mazaunin nan naka a tsakaninmu. 36 Saboda haka yanzu, ya mai tsarkin nan, Sarkin dukan tsarkakewa, ka keɓe wannan gida naka har abada, wanda aka tsarkake ba da daɗewa ba. Kada ka bari a Ialata shi.

Labarin Razi

37 Akwai wani mutum mai suna Razi, ɗaya daga cikin dattawan Urushalima, wanda yake ƙaunar jamaa da gaske. Saboda halin kirkin nan nasa, har ana kiransa uban Yahudawa. Sai aka kawo ƙararsa gun Nikanar, wai shi ɗan tawaye ne. 28 A zamanin da aka fara yaƙin yantar ƙasar Yahudiya an taɓa yi wa Razin ɗin nan hukunci domin ya cika bin aladun Yahudawa. Ya kuma kutsa kansa cikin hatsari saboda cika maƙe wa aladun Yahudawa. 29 Don Nikanar ya nuna irin ƙiyayyar da yake yi wa Yahudawa, sai ya tura soja fiye da ɗari biyar, ya ce su komo da Razi. 30 Gama ya ce, In na kama shi, Yahudawa za su yi babban rashi.

41 Da sojan suka kai hasumiyar da Razi yake, sai suka yi ta haurin ƙofa, suna so ta bude, su kuwa su kutsa kai ciki. Sai suka ce, A kawo wuta, mu ƙcone ƙyamaren ƙurmus.

Da ya ke an yi wa Razi zobe, ba shiga ba fita ke nan, sai ya kirma wa kansa wuƙa a ruwan ciki, 42 don ya ce a ransa, Gara in mutu asiri rufe, da a yi mini kisan wulakanci, duk da martaban nan tawa. 43 Da ya yi niyyar kashe kai nasa ɗin, ashe, wukar ta goce kaɗan. Sai ya ji har sojojin sun shigo hasumiyar. Ya tashi, ya garzaya da gudu, ya hau kan bangon hasumiyar, ya yi ƙundumbala cikin taron. 44 Arnma da ya ke sun ga yana fadowa, suka goce, ya fāɗa a tsakiyarsu.

45 Sai ya ajiye zuciya ya miƙe a husace, jini yana ta zuba daga gun raunukansa. Duk da haka dai ya kutsa kai cikin jamaa, 46 sai da ya hau kan wani dutse, kāna ya tsaya. Jini na ɗaukarsa, sai ya ɗaga yagaggen cikinsa ya ciro yan ciki da suka tsinke, ya watsa su cikin taron da hannunsa biyu, yana cewa, Ya Ubangiji, Sarkin ba da rai da numfashi, ka sa in sāke samun rai da numfashi a can wurin Ubangiji. Ta haka ya mutu.

15. Nikanar ya Saɓi Allah

1 Da dai Nikanar ya ji, wai Yahuza da jamaarsa suna can garin Samariya, sai ya yi nufin kai musu harin ba zata a ranar hutun Asabar. 2 Da Yahudawan da ya matsa wa su bi shi suka ce masa, Kada ka yi kisan gilla irin wannan, amma kai ma ka girmama wannan rana wadda Mahalicci mai ganin dukan abu, ya tsarkake fiye da sauran ranaku.

3 Sai matsiyacin ya ce musu, Wa ya gaya muku akwai wani Sarki a Sama da ya ce ku keɓe kowace ranar Asabar don hutu?

4 Suka ce masa, Akwai wani Sarki a Sama, Ubangiji Allah, rayayye ne, wanda ya umarce mu mu keɓe rana ta bakwai.

5 Sai ya ce, Ai, ni ne sarkin mallakar duniya, na kuwa umarce ku yanzu, ku saɓi makamanku, ku yi abin da na ce muku. Amma wane mutum, ai, bai iya tumɓuke kome na nufinsa na ƙeta ba.

Yahuza Makabi ya Ƙarfafa wa Mutanensa Zuciya

6 Nikanar, ta wurin cika bakinsa da almubazaranci, ya so ya gina wata lambar da za ta nuna nasarar da yake nufin yi a kan Yahuza da jamaarsa. 7 Amma Makabi dai bai daina sa zuciya zai sami taimako daga wurin Ubangiji ba. 8 Shi ma ya ce wa sojansa, Ko kaɗan kada ku firgita, don kun ga arnan can na kawo mana hari, amma abin da za ku riƙa tunawa kawai, shi ne taimakon da Allah ya yi ta yi mana. Yanzu ma sai mun ga bayansu da ikon Allah kuwa.

9 Ya yi ta ƙarfafa musu gwiwa da kalmomi daga cikin littattafan sharia da na annabawa, ya ce, Ku kuma tuna da irin faɗan da muka yi, muna kuma samun nasara.

Nan da nan ya ji sun ce, Yau kuwa da wa aka haɗa mu, mu kara? 10 Da ya ga duk ya sa su kuzari, sai ya ba su umarnai iri iri, ya kuma ce, Ku yi hankali da maganar arna, yadda suke cin amana, ga kuma yin alkawari su fasa. 11 Bayan ya ƙarfafa su da makamai, ba na garkuwoyi da mūsu ba, amma na ikon da jawabinsa ke ba su, sai ya gaya musu wani mafarki mai makama da ya yi, wanda ya sa sojansa suka yi murna.

12 Ya ce musu, Ga abubuwan da na gani a mafarkin. Na ga Oniyas, wanda dā ke babban firist, mutumin kirkin nan, mai faranta wa kowa rai ta sakin fuskarsa, da ladabinsa, da maganarsa, domin ya koya, ya iya tun yana yaro, ga shi nan, ya ɗaga hannuwa, yana yi wa Yahudawa addua gaba ɗayansu. 13 Saan nan kuma na ga wani mutum dabam, mai hurhura da kwarjini, mai faɗi a ji, ga alama kuma yana jin kansa. 14 Sai Oniyas ya ce, Wannan shi ne Irmiya, annabin nan na Allah, wanda yake ƙaunar yanuwa, yana kuma yi musu addua ƙwarai da gaske, da kuma birnin nan mai tsarki. 15 Na ga Irmiya ya miƙo mini wani takobi na zinariya. Yana cikin miƙo mini, sai ya ce, 16 Amshi wannan takobi mai tsarki, kyauta ce daga gun Allah. Da takobin ne za ka yi ta ɗauke wa abokan gāba kai.

Ƙarshen Nikanar

17 Da fa Yahuza ya ƙarfafa su haka da jawabinsa mai daɗin ji, mai sa su kuzari, sai samarin suka ce, Mu yanzu ma, ba za mu yi wa abokan gāba wani kwanto ba, amma mu kara da su da ƙarfin tuwonmu, mu ci su nan da nan, domin mun ga birnin, da Wuri Mai Tsarki, da kayansa na ibada, duk ba namu ba ne sosai. 18 Suka ma kusan mancewa da shaanin matansu, da na yayansu, da na yanuwa da dangi, suka dukufa sosai don su kāre Wuri Mai Tsarki tukuna. 19 Waɗanda ke zaune a birnin kuwa hankalinsu bai kwanta ba, domin suna damuwa game da dāgār da za a ja a filin da ke bayan garin.

20 Sai dukan jamaa suka yi ta sauraron abin da zai faru. Abokan gāba kuma duk suka matso, suna so a gwabza yaƙi, suka sa giwayensu wurin da za su fi yin ɓarna, sojansu na doki kuwa a gefe gefe. 21 Ganin yadda abokan gāba suka matso musu haka da makamai iri iri da mahaukatan giwaye, sai Makabi ya roƙi Ubangiji mai aikata muujizai. Gama Yahuza ya san ba makamai ke yin yaƙi ba, sai taimakon Ubangiji, gama yana ba waɗanda ya ga sun cancanta cin nasara a kan kari.

22 Yahuza ya yi roƙo da waɗannan maganganu, ya ce: Ya Ubangiji, kai ne ka aiko mana da malaika a zamanin sarki Hezekiya na Yahudiya, har sarki Hezekiya ya kashe jamaar Sennakerib dubu ɗari da dubu tamanin da dubu takwas nan take. 23 Don haka yanzu ma, ya Sarkin Sama, ka aiko da wani malaika ya gigita mana duk wanda ke gabanmu. 24 Ta ikonka ka watsa waɗanda suka zo da niyyar cin mutuncin jamaarka mai tsarki. Da waɗannan maganganu ya gama roƙonsa.

25 Nikanar da jamaarsa sai ƙara matsowa suke yi, suna busa sarewa, suna yin waƙoƙin yaƙi. 21 Amma Yahuza da tashi, jamaar suka auka wa abokan gaba da roƙe‑roƙe ga Ubangiji, 21 Suna ta kai wa abokan gaba naushi, suna yin addua a zuci. Nan take suka zubar da mutum fiye da dubu talatin da biyar ƙas, suna cike da farin rai domin Allah ya nuna musu ikonsa. 22 Da suka gama kisan abokan gāba, suna komawa gida ke nan, sai suka ga Nikanar a kwance, matacce. Ga shi, cuku cuku da kayan yaƙinsa. Suka kuwa ce, Me za mu yi, ba ihu ba? Suka kuma yabi Ubangiji da yaren kakanninsu, suna ɗaga muryarsu.

30 Sai Yahuza, wanda ya fi kowa aniya a aikin kare jamaarsa, mai ƙaunar alummarsa tun ƙuruciyarsa, ya umarce su, ya ce su yanke kan Nikanar da hannunsa na dama, a tafi da su birnin Urushalima. 31 Da ya isa Urushalima, sai ya tara dukan jamaarsa, ya sa firistoci su kewaye bagade, saan nan ya aika wa na kagara, su ma su zo su gani. 32 Da suka taru, sai ya nuna musu kan ɗan sababin nan, Nikanar, da hannunsa wanda ya cira wa Haikalin Mai Iko Dukka, yana cika bakin nan, yana hurzarwa, cewa sai ya ƙaskanta Haikalin. 33 Saan nan ya sa aka datse harshen Nikanar, ya ce zai yanyanka shi, ya ba ungulai shi guntu guntu su sha gara, gangar jikin kuwa zai rataye can gaban Haikalin Allah don kowa ya gani. 34 Sai dukansu, gaba ɗaya suka yi wa Allah godiya da ya raba su da wannan ɗan sababi lafiya, suna cewa, Mai albarka kake, ya Ubangiji, domin ka keɓe Wurinka Mai Tsarki don kada a lalata shi.

35 Sai Yahuza ya rataye kan Nikanar a kan garun kagara don kowa da kowa ya ga irin nasarar da Ubangiji ya ba jamaarsa. 36 Sai suka ce, Dole ne mu dinga tunawa da wannan rana, mu riƙa yin bikinta ran sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, da harshen Suriyawa, ranar jajibirin ranar Mordekai ke nan.

Ƙarshen Magana

37 Tun da ya ke ta haka aka ƙare da Nikanar, daga wannan lokaci kuma birnin ya koma karƙashin ikon Yahudawa, sai in ce, Da wannan na zo ƙarshen labarina. 38 In abin da na rubuta yana da daɗin karantawa, to, da ma burina ke nan. In kuma labarin bai fito sosai ba, ni dai na yi iyakar kokarina. 39 Kamar yadda bai dace ba in an sha gishiri shi kaɗai, ko kuwa a sha miya ba gishiri, amma in an haɗa su daidai wa daida, a ji daɗin abinci, haka aikin gwaninta yake in an rubuta labari daidai don masu karatu su ji daɗinsa. A nan za mu kwana.

*      *      *      *      *
*      *      *
*