Nahum

Nahum

1

Fushin Ubangiji a kan Nineba

1Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.

2Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya, Ubangiji mai sakayya ne, mai hasala. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa. Yana tanada wa maƙiyansa fushi.

3Ubangiji mai jinkirin fushi ne, Mai Iko Dukka. Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifi ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da cikin hadiri, Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.

4Yakan tsauta wa teku, sai teku ta ƙafe. Yakan busar da koguna duka. Bashan da Karmel sukan bushe, Tohon Lebanon yakan yanƙwane.

5Duwatsu sukan girgiza a gabansa, Tuddai kuma su narke. Duniya ta murtsuke a gabansa, Da dukan mazauna a cikinta.

6Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.

7Ubangiji mai alheri ne, Shi mafaka ne a ranar wahala. Ya san waɗanda suke fakewa a gare shi.

8Zai shafe maƙiyansa da ambaliyar ruwa, Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwa cikin duhu.

9Me kuke ƙullawa game da Ubangiji? Ubangiji zai wofintar da abin nan da kuke ƙullawa, Sau ɗaya kawai zai hallaka ku.

10Suna maye da abin shansu, Za su ƙone kamar sarƙaƙƙiyar ƙaya, Da busasshiyar ciyawa.

11Daga cikinki wani ya fito, Wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci, Ya ƙulla shawara marar amfani.

12Ni Ubangiji na ce, “Ko da yake suna da ƙarfi, suna kuma da yawa, Za a datse su, su ƙare. Ko da yake na wahalar da kai, Ba zan ƙara wahalar da kai ba.

13Yanzu zan karya karkiyarsa daga wuyanka, Zan kuma tsinke sarƙarta.”

14Ubangiji ya riga ya yi umarni a kanka cewa, “Sunanka ba zai ci gaba ba, Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi Da siffofi na zubi daga gidan gumakanka. Zan shirya maka kabari, gama kai rainanne ne.”

Labarin Fāɗuwar Nineba

15Duba a kan duwatsu, ƙafafun wanda yake kawo albishir, Wanda yake shelar salama! Ya Yahuza, ka yi bikin idodinka, Ka kuma cika wa'adodinka. Gama mugun ba zai sāke zuwa ya yi gāba da kai ba, An datse shi ƙaƙaf.

2

1Wanda yake farfashewa ya auko maka, Sai ka sa mutane a kagara, a yi tsaron hanya, Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinka duka.

2Gama Ubangiji zai mayar wa Yakubu da darajarsa kamar ta Isra'ila. Ko da masu washewa sun washe su, Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.

3Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne, Sojojinsa kuma suna saye da mulufi. Da ya shirya tafiya, Karusai suna walƙiya kamar harshen wuta, Ana kaɗa mashi da bantsoro.

4Karusai sun zabura a tituna a haukace. Suna kai da kawowa a dandali, Suna walwal kamar jiniya, Suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.

5Sai aka kira shugabanni, Suka zo a guje suna tuntuɓe, Suka gaggauta zuwa garu, Suka kafa kagara.

6An buɗe ƙofofin kogi, Fāda ta rikice.

7An tsiraita sarauniya, an tafi da ita, 'Yan matanta suna makoki, suna kuka kamar kurciyoyi, Suna bugun ƙirjinsu.

8Nineba tana kama da tafki wanda ruwansa yake zurarewa, Suna cewa, “Tsaya, tsaya,” Amma ba wanda ya waiga.

9A washe azurfa! A washe zinariya! Dukiyar ba ta da adadi, Akwai dukiya ta kowane iri.

10Nineba ta hallaka! Ta lalace, ta zama kufai! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa! Kwankwaso yana ciwo, Fuskoki duka sun kwantsare!

11Ina kogon nan na zakoki, Inda aka ciyar da 'ya'yan zaki, Inda zaki da zakanya da kwiyakwiyansu sukan tafi, Su tsere daga fitina>

12Zaki ya kashe abin da ya ishi kwiyakwiyansa. Ya kaso wa zakanyarsa abin da ya ishe ta. Ya cika kogonsa da ganima.

Ragargajewar Nineba

13“Ga shi, ina gāba da ke. Ni Ubangiji Allah Mai Runduna na faɗa. Zan ƙone karusanki, Takobi kuwa zai karkashe sagarun zakokinki, Zan hana miki ganima a duniya. Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunki ba.”

3

1Kaiton birnin jini, Wanda yake cike da ƙarairayi da ganima, Da waso kuma ba iyaka!

2Ku ji amon bulala da kwaramniyar ƙafafu, Da sukuwar doki da girgizar karusai!

3Sojojin dawakai suna kai sura, Takuba suna walƙiya, māsu suna ƙyalƙyali. Ga ɗumbun kisassu, da tsibin gawawwaki, Matattu ba su ƙidayuwa, Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!

4Ya faru saboda yawan karuwancin Nineba kyakkyawa mai daɗin baki, Wadda ta ɓad da al'umman duniya da karuwancinta, Ta kuma ɓad da mutane da daɗin bakinta.

5Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ina gāba da ke, Zan kware fatarinki a idonki, Zan sa al'ummai da mulkoki su dubi tsiraicinki.

6Zan watsa miki ƙazanta, In yi miki wulakanci, In maishe ki abin raini.

7Dukan waɗanda za su dube ki Za su ja da baya su ce, “‘Nineba ta lalace, wa zai yi kuka dominta?” A ina zan samo miki waɗanda za su ta'azantar da ke?”

8Kin fi No ne? Wadda take a bakin Nilu, Wadda ruwa ya kewaye ta? Teku ce kagararta. Ruwa ne kuma garunta.

9Habasha da Masar su ne ƙarfinta marar iyaka, Fut da Libiya su ne kuma mataimakanta.

10Duk da haka an tafi da ita, an kai ta cikin bauta. An fyaɗa ƙanananta a ƙasa, An yi kacakaca da su a kowace mararraba. An jefa kuri'a a kan manyan mutanenta, Aka ɗaure dukan manyan mutanenta da sarƙoƙi.

11Ke Nineba kuma za ki bugu, Za a ɓoye ki. Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.

12Dukan kagaranki suna kama da itatuwan ɓaure, Waɗanda 'ya'yansu suka harba. Da an girgiza sai su faɗo a bakin mai sha.

13Sojojinki kamar mata suke a tsakiyarki! An buɗe wa maƙiyanki ƙofofin ƙasarki. Wuta za ta cinye madogaran ƙofofinki.

14Ki tanada ruwa domin za a kewaye ki da yaƙi! Ki ƙara ƙarfin kagaranki! Ki tafi kududdufi, ki kwaɓa laka! Ki ɗauki abin yin tubali!

15A can wuta za ta cinye ki, Takobi zai sare ki, Zai cinye ki kamar fara. Ki riɓaɓɓanya kamar fara. Ki kuma riɓaɓɓanya kamar ɗango.

16Kin yawaita 'yan kasuwanki suna da yawa fiye da taurari, Amma sun tafi kamar fara waɗanda sukan buɗe fikafikansu su tashi, su tafi.

17Shugabanninki kamar ɗango suke, Manyan mutanenki kamar cincirindon fāra ne, Suna zaune a kan shinge a kwanakin sanyi, Sa'ad da rana ta fito, sukan tashi su tafi, Ba wanda ya san inda suke.

18Ya Sarkin Assuriya, masu tsaronka suna barci, Manyan mutanenka suna kwankwance, Mutanenka sun watse cikin duwatsu, Ba wanda zai tattaro su.

19Ba abin da zai rage zafin rauninka, Rauninka ba ya warkuwa. Duk wanda ya ji labarinka, zai tafa hannuwansa Gama wane ne ba ka musguna wa ba>