Philippians
1Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da kuma masu hidimarta.
2Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.
3Ina gode Allahna duk sa'ad da nake tunawa da ku, 4a kullum kuwa a kowace addu'a da nake muku duka, da farin ciki nake yi. 5Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu. 6Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu. 7Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita. 8Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi. 9Addu'ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa, 10domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu, 11kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.
12'Yan'uwa, ina so ku sani, al'amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara, 13har dai ya zama sananne ga dukan sojan fāda da sauran jama'a, cewa ɗaurina saboda Almasihu ne. 14Har ma galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.
15Lalle waɗansu suna wa'azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne. 16Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara. 17Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.
18Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Almasihu, na kuma yi farin ciki da haka. I, zan yi farin ciki kuwa. 19Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu. 20Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata. 21Domin ni, a gare ni, rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce. 22In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa. 23Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa. 24Amma in wanzu a cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku. 25Na tabbata haka ne, na kuwa sani zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku yin farin ciki, 26ku kuma sami ƙwaƙƙwaran dalilin yin taƙama da Almasihu ta wurina, saboda sāke komowata gare ku.
27Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa, 28ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam. Wannan kuwa ishara ce a gare su ta hallakarsu, ku kuwa ta cetonku, isharar kuwa daga Allah take. 29Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa, 30kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.
1In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku, 2to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya. 3Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi. 4Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan'uwansa ma.
5Ku ɗauki halin Almasihu Yesu, 6wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba, 7sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam. 8Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye. 9Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da yake birbishin kowane suna, 10domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa, 11kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba.
12Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan. 13Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.
14Kome za ka yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama, 15don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya, 16kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba. 17Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka. 18Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.
19Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku. 20Ba ni da wani kamarsa, wanda da sahihanci zai tsananta kula da zamanku lafiya. 21Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba. 22Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. 23Shi ne nake fata in aiko, da zarar na ga yadda al'amarina yake gudana. 24Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.
25Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan'uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya. 26Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya. 27Lalle ya yi rashin lafiya, har ya yi kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba kuwa shi kaɗai ba, har ni ma, don kada in yi baƙin ciki a kan baƙin ciki. 28Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi domin ku yi farin cikin sāke ganinsa, ni kuma in rage baƙin cikina. 29Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane, 30domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.
1A ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi farin ciki da Ubangiji. Sāke rubuto muku waɗannan abubuwa bai gundure ni ba, ga shi kuwa, domin lafiyarku ne.
2Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma'aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan! 3Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al'amuran ganin ido, 4ko da yake ni ina iya dogara da al'amuran ganin ido, in dai nake so. In kuma akwai wanda yake tsammani yana iya dogara ga al'amuran ganin ido, to, ni na fi shi. 5An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra'ila ne, na kabilar Biliyaminu, Ba'ibrane ɗan Ibraniyawa, bisa ga Shari'a kuwa ni Bafarisiye ne, 6a wajen himma kuwa mai tsananta wa Ikilisiya ne ni, wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari'a, marar abin zargi nake.
7Amma dai kowace irin riba na taɓa ci, na ɗauka hasara ce saboda Almasihu. 8Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yă zama nawa, 9a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya. 10Muradina ke nan, in san Almasihu, in san ikon tashinsa daga matattu, in yi tarayya da shi a shan wuyarsa, in kuma zama kamarsa a wajen mutuwarsa, 11domin ta ko ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.
12Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a'a, sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi. 13Ya 'yan'uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da yake baya, ina kutsawa zuwa ga abin da yake gaba. 14Ina nacewa gaba gaba zuwa manufar nan, domin in sami ladar kiran nan zuwa sama, da Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu. 15Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra'ayi. In kuwa a game da wani abu ra'ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma. 16Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.
17Ya ku 'yan'uwa, ku yi koyi da ni dukanku baki ɗaya, ku kuma dubi waɗanda zamansu yake daidai da gurbin da muka bar muku. 18Domin da yawa waɗanda na sha gaya muku, yanzu kuma nake gaya muku, har da kawaye, suna bin Yesu, in ji su, amma su magabtan gicciyen Almasihu ne. 19Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya. 20Mu kuwa 'yan Mulkin Sama ne, daga can ne kuma muke ɗokin zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu, 21wanda zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, ya mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka, da ikon nan nasa na sarayar da dukkan abubuwa a gare shi.
1Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
2Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne. 3Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.
4A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki. 5Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah. 7Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.
8Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani. 9Abin da kuka koya, kuka yi na'am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.
10Na yi farin ciki da Ubangiji ƙwarai da yake a yanzu kam, kularku gare ni ta farfaɗo, ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba. 11Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake. 12Na san yadda zan yi in yi zaman ƙunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A kowane irin hali duka na horu da ƙoshi da yunwa, yalwa da rashi. 13Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.
14Amma kuwa kun kyauta da kuka taya ni cikin ƙuntatata. 15Ku kuma Filibiyawa, ku kanku kun sani tun da aka fara yin bishara, sa'ad da na bar ƙasar Makidoniya, ba wata ikilisiyar da ta yi tarayya da ni wajen hidimar bayarwa da karɓa, sai dai ku kaɗai. 16Ko sa'ad da nake Tasalonika ma, kun aiko mini da taimako ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. 17Ba cewa, don ina neman kyautarku ba ne, a'a, nemar muku amfani nake yi, a ƙara a kan ribarku. 18An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu. 20Ɗaukaka tă tabbata ga Allahnmu, Ubanmu, har abada abadin. Amin! Amin!
21Ku gai da kowane tsattsarka cikin Almasihu Yesu. 'Yan'uwan da suke tare da ni suna gai da ku. 22Dukan tsarkaka suna gai da ku, tun ba ma na fadar Kaisar ba.
23Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.