Proverbs
1Karin maganar Sulemanu, ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila. 2Ga Karin magana da za su taimake ka ka rarrabe da hikima, da kyakkyawar shawara, da fahimtar ma'anar zurfafan karin magana, 3da yadda za ka karɓi koyarwa ta hanyar hikima, da adalci, da gaskiya, da sanin abin da yake daidai. 4Sukan sa marar sani ya zama masani, sukan koya wa samari yadda za su zama masu amfani. 5Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana, 6don su fahimci ɓoyayyiyar ma'anar da take cikin karin magana, da mawuyatan al'amura waɗanda masu hikima suka ƙago.
7In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.
8Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, ka mai da hankali ga abin da mahaifiyarka take faɗa. 9Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau.
10Ɗana sa'ad da masu zunubi suka jarabce ka, kada ka yarda 11in suka ce maka, “Zo mu tafi mu nemi wani mutum mu kashe, mu je, mu fāɗa wa marasa laifi mu ji daɗi! 12Ba mu damu da ransu da lafiyarsu ba, mu dai mu tafi mu kashe su, mu hallaka su ɗungum. 13Za mu sami dukiya iri iri, mu cika gidajenmu da ganima! 14Ka zo ka haɗa kai da mu, dukanmu kuwa za mu raba abin da muka sato.”
15Ɗana, kada ka gama kanka da irin waɗannan mutane, ka yi nesa da su. 16Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai. 17Ba shi da amfani a kafa tarko a idon tsuntsun da ake so a kama. 18Amma waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu. 19Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.
20Ku kasa kunne! Hikima tana kira a tituna da a kasuwoyi. 21Tana kira da ƙarfi a ƙofofin birni, a duk inda mutane suke tattaruwa.
22Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba? 23Ku kasa kunne lokacin da nake tsauta muku, zan ba ku shawara mai kyau, mu yi tarayya cikin ilimina. 24Ina ta kiranku ina gayyatarku ku zo, amma ba ku kula ba, ba ku mai da hankali gare ni ba. 25Kun ƙi bin shawarwarina duka, ba ku yarda in gyara kuskurenku ba. 26Saboda haka, lokacin da kuke shan wahala, zan yi muku dariya. Zan yi muku ba'a lokacin da razana ta auka muku, 27sa'ad da ta zo muku kamar hadiri mai ƙaƙƙarfar iska mai wahalarwa, sa'ad da kuke shan azaba da damuwa. 28Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba. 29Domin ba ku taɓa sanin amfanin ilimi ba, kun ƙi tsoron Ubangiji a kullum. 30Ba ku taɓa yarda da shawarata ba, ko ku yarda in gyara kuskurenku. 31Saboda haka za ku karɓi sakayyarku, ayyukanku za su cuce ku. 32Marasa sani sukan mutu saboda ba su yarda da hikima ba. Wawaye kuwa sukan hallaka saboda rashin kulawarsu. 33Amma duk wanda ya kasa kunne gare ni, zai zauna lafiya. Ba abin da zai same shi, ba abin da zai tsorata shi.”
1Ɗana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na faɗa maka ka yi. 2Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi. 3I, ka roƙi ilimi da tsinkaya. 4Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya. 5Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah. 6Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa. 7Shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci. 8Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.
9Idan ka kasa kunne gare ni za ka san abin da yake daidai, da abin da yake gaskiya, da abin da yake na kirki. Za ka san abin da za ka yi. 10Za ka zama mai hikima, iliminka zai faranta maka rai. 11Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka. 12Za su hana ka aikata mugayen ayyuka, za su nisantar da kai daga mutane masu ta da hargitsi da irin maganganunsu, 13mutane waɗanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi, 14waɗanda suke jin daɗin yin laifi, suna nishaɗi cikin mugunta. 15Ba za a dogara da su ba, ba kuwa za a iya amincewa da su ba.
16Za a nisantar da kai daga mazinaciya, wadda take ƙoƙari ta lalatar da kai da daɗin bakinta, 17marar aminci ga mijinta, wadda ta manta da tsarkakan alkawaran da ta ɗauka. 18Idan ka tafi gidanta ka kama hanyar mutuwa. Tafiya can kama hanyar zuwa lahira ne. 19Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa. Ba zai ƙara komowa ga hanyar rai ba. 20Saboda haka dole ka bi hanyar da mutanen kirki suka bi, ka bi gurbin adalai. 21Mutane adalai, masu kamewa, su ne za su zauna ƙasarmu. 22Amma Allah zai fizge mugaye daga ƙasar, ya kuma tumɓuke masu zunubi kamar yadda ake tumɓuke shuke-shuke daga ƙasa.
1Ɗana kada ka manta da abin da na koya maka. Kullum ka tuna da abin da na faɗa maka ka yi. 2Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata. 3Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka. 4Idan ka yi wannan kuwa, Allah zai yi murna da kai. Za ka yi nasara cikin hulɗar da kake yi da mutane.
5Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. 6A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da yake daidai. 7Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta. 8Idan ka kiyaye wannan, zai zama maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake sha. 9Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka. 10Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka.
11Ɗana, sa'ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa. 12Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi. 13Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi. 14Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya. 15Tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani. 16Hikima takan tsawanta ranka, ta kuma ba ka dukiya da daraja. 17Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka. 18Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da 'ya'ya.
19Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa, Ya shimfiɗa sararin sama a inda yake ta wurin saninsa.
20Hikimarsa ta sa ruwan koguna ya yi gudu, Gizagizai kuwa su zubo da ruwa bisa duniya.
21Ɗana ka riƙe hikimarka da basirarka. Ko kusa kada ka bari su rabu da kai. 22Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki. 23Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe. 24Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare. 25Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri. 26Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba.
27Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa. 28Sam, kada ka ce wa maƙwabcinka ya dakata sai gobe, idan dai kana iya taimakonsa yanzu. 29Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, gama yana zaune kusa da kai, yana kuwa amincewa da kai. 30Kada ka yi jayayya ba dalili da wanda bai taɓa cutarka ba. 31Kada ka ji kishin masu ta da zaune tsaye, ko ka yi sha'awar aikata ayyukansu, 32gama Ubangiji yana ƙin mutanen da suke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su. 33Ubangiji yakan la'antar da gidajen masu mugunta, amma yakan sa wa gidajen adalai albarka. 34Ba ruwansa da masu girmankai, amma masu tawali'u sukan sami tagomashi a wurinsa. 35Mutane masu hikima za su sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.
1'Ya'yana ku kasa kunne ga koyarwar mahaifinku. Ku mai da hankali, za ku zama haziƙai. 2Abin da nake koya muku, abu mai kyau ne, saboda haka ku tuna da shi duka. 3Sa'ad da nake ɗan yaro tilo a wurin iyayena, 4mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu. 5Ka nemi hikima da basira! Kada ka manta ko ka ƙyale abin da na faɗa. 6Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka. 7Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira. 8Ka ƙaunaci hikima, za ta girmama ka. Ka rungume ta, za ta kawo maka daraja. 9Za ta zamar maka rawanin daraja.”
10Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai. 11Gama na koya maka hikima da hanyar zama mai kyau. 12Idan ka yi tafiya da hikima ba abin da zai tsare maka hanya, sa'ad da kake gudu ba za ka yi tuntuɓe ba. 13Kullum ka tuna da abin da ka koya, iliminka shi ne ranka, ka lura da shi da kyau. 14Kada ka tafi inda mugaye suke tafiya, kada ka bi gurbin mugaye. 15Kada ka yi mugunta! Ka nisance ta! Ka ƙi ta, yi tafiyarka. 16Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani. 17Mugunta da ta'adi kamar ci da sha suke a gare su.
18Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka. 19Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.
20Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa. Ka kasa kunne ga kalmomina. 21Kada ka kuskura su rabu da kai, ka tuna da su, ka ƙaunace su. 22Za su ba da rai da lafiya ga dukan wanda ya fahimce su. 23Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja. 24Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗawa. 25Ka duba gaba sosai gabanka gaɗi, ba tsoro. 26Ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai. 27Ka rabu da mugunta ka yi tafiyarka sosai, kada ka kauce ko da taki ɗaya daga hanyar da take daidai.
1Ɗana, ka mai da hankali, ka kasa kunne ga hikimata da basirata. 2Sa'an nan ne za ka san yadda za ka yi kome daidai, kalmominka za su nuna kana da ilimi. 3Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi. 4Amma bayan an gama duka, ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba. 5Za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce. 6Ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba.
7'Ya'yana, ku kasa kunne gare ni yanzu, kada ko kusa ku manta da abin da nake faɗa. 8Ku yi nesa da irin wannan mace! Kada ku yarda ku yi ko kusa da ƙofarta! 9Idan kuwa kun yi, girmamawar da ake yi muku za ta zama ta waɗansu. Za ku yi mutuwar ƙuruciya ta hannun mutane marasa imani. 10Hakika, baƙi za su kwashe dukan dukiyarku, abin da kuka sha wahalar samu kuma zai zama rabon wani dabam. 11Za ku kwanta kuna nishi a kan gadon mutuwa, namanku da tsokokinku za su zagwanye. 12Sa'an nan za ku ce, “Me ya sa ban taɓa koyo ba? Me ya sa ban yarda wani ya kwaɓe ni ba? 13Ban kasa kunne ga malamaina ba. Ban mai da hankalina gare su ba. 14Farat ɗaya sai aka kunyatar da ni a bainar jama'a.”
15Ka yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta ita kaɗai. 16Idan kuma waɗansu mata sun haifa maka 'ya'ya, 'ya'yan nan ba za su yi maka wani amfani ba. 17'Ya'yanka za su yi girma su taimake ka, ba na baƙi ba. 18Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro, 19kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa. Bari kyanta ya ɗau hankalinka. Bari ƙaunarta ta kewaye ka. 20Ɗana, don me za ka fi son matar wani? Don me za ka bar matar wani ta lallame ka da daɗin bakinta? 21Ubangiji yana ganin dukan abin da kake yi. Inda ka shiga duk yana kallonka. 22Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi. 23Yakan mutu saboda rashin kamewarsa, cikakkiyar wautarsa za ta kai shi kabarinsa.
1Ɗana, ka taɓa yin alkawari ka ɗaukar wa wani lamuni? 2Maganganunka sun taɓa kama ka, ko alkawaranka sun taɓa zamar maka tarko? 3To, ɗana, kana cikin ikon wannan mutum, amma ga yadda za ka yi ka fita, sheƙa zuwa wurinsa, ka roƙe shi ya sake ka. 4Kada ka yarda ka yi barci ko ka huta. 5Ka fita daga cikin tarkon kamar tsuntsu ko barewar da ta tsere wa maharbi.
6Bari ragwaye su yi koyi da tururuwa. 7Ba su da shugaba, ba su da sarki, ko mai mulki, 8amma da kaka sukan tanada wa kansu abinci, domin kwanakin bazara. 9Har yaushe rago zai yi ta ɓalɓalcewa? Yaushe zai farka? 10Yakan ce, “Bari in ɗan ruruma, in naɗa hannuwana in shaƙata.” 11Amma lokacin da yake sharar barci, tsiya za ta auka masa kamar ɗan fashi da makamai.
12Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita. 13Sukan yi ƙyifce, ko su yi nuni don su yaudare ka. 14A kowane lokaci suna shirya mugunta a kangararren hankalinsu, suna kuta tashin hankali ko'ina. 15Saboda wannan masifa za ta fāɗa musu farat ɗaya ba makawa, za a yi musu mummunan raini. 16-19Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba, duban raini, harshe mai faɗar ƙarya, hannuwan da suke kashe marasa laifi, kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru, mutum mai gaggawar aikata mugunta, mai yawan shaidar zur, mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.
20Ɗana, ka yi abin da mahaifinka ya faɗa maka, kada ka manta da koyarwar mahaifiyarka. 21Kullum ka kiyaye abin da suke faɗa maka, ka kulle su kuma a zuciyarka. 22Koyarwarsu za ta bi da kai sa'ad da kake tafiya, ta kiyaye ka da dare, ta kuma ba ka shawara da rana. 23Doka da abubuwan da take koyarwa haske ne mai haskakawa. Tsautawa tana iya koya maka zaman duniya. 24Za ta tsare ka daga mugayen mata, daga kalmomin alfasha da suke fitowa daga bakin matan waɗansu. 25Kada kyansu ya jarabce ka, kada ka faɗa cikin tarkon feleƙensu. 26Mutum ta dalilin karuwa zai sha hasarar abin da ya mallaka duka ta wurin zina.
27Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa'an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba? 28Ka iya tafiya a kan garwashi sa'an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba? 29Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani. Duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala. 30Mutane ba sukan raina wanda ya saci abinci don yana jin yunwa ba, 31duk da haka in an kama shi, sai ya biya diyya sau bakwai, tilas kuwa ya ba da dukan abin da yake da shi. 32Amma mazinaci marar hankali ne, gama hallaka kansa yake yi. 33Zai sha dūka, a wulakanta shi, zai dawwama cikin kunya. 34Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama. 35Ba zai karɓi biya ba, ba kyautar da za a yi masa wadda za ta kwantar da fushinsa.
1Ɗana, ka tuna da abin da na faɗa, kada ka manta da abin da na ce maka ka yi. 2Ka yi abin da na faɗa maka, za ka rayu. Ka natsu, ka bi koyarwata, ka tsare ta kamar ƙwayar idonka. 3Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka. 4Ka mai da hikima 'yar'uwarka, basira kuwa ta zama ƙawarka ta jikinka. 5Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.
6Wata rana ina leƙawa ta tagar ɗakina, 7sai na ga waɗansu samari masu yawa waɗanda ba su gogu da duniya ba, musamman sai na lura da wani dolo a cikinsu. 8Yana tafe a kan titi kusa da kusurwar da take a zaune, yana wucewa kusa da gidanta, 9da magariba cikin duhu. 10Sai ta tarye shi, ta ci ado kamar karuwa, tana shirya yadda za ta yaudare shi. 11(Ba ta jin tsoro, ba ta kuma jin kunya, koyaushe tana ta gantali a tituna. 12Takan tsaya tana jira a kowace kusurwa, wani lokaci a tituna, wani lokaci kuma a kasuwa.) 13Ta rungumi saurayin, ta sumbace shi, ta dubi tsabar idonsa ta ce, 14“Na miƙa hadayu yau, ina da nama na hadayu. 15Shi ya sa na fito ina nemanka, ina so in gan ka, ga shi kuwa, na gan ka! 16Na lulluɓe gadona da zannuwan lilin masu launi iri iri daga Masar. 17Na yayyafa musu turaren mur da na aloyes da na kirfa. 18Ka zo mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna. 19Mijina ba ya gida, ya yi tafiya mai nisa. 20Ya tafi da kuɗi masu yawa, ba zai komo ba sai bayan mako biyu.” 21Ta jarabce shi da kwarkwasarta, sai ya ba da kai ga daɗin bakinta. 22Nan da nan ya bi ta kamar sā zuwa mayanka, kamar barewa tana tsalle zuwa cikin tarko, 23inda kibiya za ta soke zuciyarta. Yana kama da tsuntsun da yake zuwa cikin tarko, bai kuwa sani ransa yana cikin hatsari ba.
24Yanzu fa 'ya'yana, ku kasa kunne gare ni, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa. 25Kada ku yarda irin wannan mace ta rinjayi zuciyarku, kada ku yi ta yawon nemanta. 26Ita ce sanadin hallakar mutane da yawa, ta sa mutane da yawa mutuwa, har ba su ƙidayuwa. 27Tafiya gidanta kuna kan hanya zuwa mutuwa ke nan, gajeruwar hanya ce zuwa lahira.
1Ku kasa kunne! Hikima tana kira. Tana so a ji ta.
2Tana tsaye bisa kan tuddai a bakin hanya Da a mararraban hanyoyi.
3A ƙofofin shiga birni, tana kira,
4“Ina roƙonku, ya ku, 'yan adam, Ina kiran kowane mutum da yake a duniya.
5Ba ku balaga ba? To, ku balaga. Ku wawaye ne? Ku koyi hankali.
6Ku kasa kunne ga jawabina mafi kyau, Dukan abin da na faɗa muku daidai ne.
7Abin da na faɗa gaskiya ne, Ƙarairayi abin ƙi ne a gare ni.
8Kowane abu da na faɗa gaskiya ne, Ba wani abu da yake na laifi ko na ruɗawa.
9Ga mutum mai basira, dukan abu ne a sarari, Ga wanda aka sanar da shi sosai, abu ne a sawwaƙe.
10Ka zaɓi koyarwata fiye da azurfa, Ka zaɓi ilimi fiye da zinariya tsantsa.
11“Ni ce hikima, na fi lu'ulu'ai, Cikin dukan abin da kake so, ba kamata.
12Ni ce hikima, ina da basira, Ina da ilimi da faɗar daidai.
13Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji, Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi, Da maganganu na ƙarya.
14Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi. Ina da fahimi, ina da ƙarfi.
15Nakan taimaki sarakuna su yi mulki, Mahukunta kuma su tsara dokoki masu kyau.
16Kowane mai mulki a duniya, da taimakona yake mulki, Ƙusoshin hukumomi da dattawan gari duka ɗaya.
17Ina ƙaunar waɗanda ke ƙaunata, Dukan wanda ke nemana kuma zai same ni.
18Ina da dukiya da daraja da zan bayar, Da wadata da nasara kuma.
19Abin da za ka samu daga gare ni Ya fi zinariya kyau, da azurfa tsantsa.
20A kan hanyar adalci nake tafiya, Rankai a kan hanyoyin gaskiya.
21Ina ba da dukiya ga waɗanda suke ƙaunata, Ina kuma cika gidajensu da wadata.
22“Ni ce halittar farko da Ubangiji Ya fara halittawa daga cikin ayyukansa tuntuni.
23Da farkon farawa ni aka fara halittawa Kafin a yi duniya.
24Ni aka fara yi kafin tekuna, A sa'ad da ba maɓuɓɓugan ruwa.
25Ni aka fara yi kafin a yi duwatsu, Kafin a kafa tuddai a wurarensu,
26Kafin Allah ya halicci duniya da filayenta, Ko ɗan ɓarɓashin ƙasa.
27A can nake sa'ad da ya shata sararin sama, Da sa'ad da ya shimfiɗa al'arshi a hayin tekuna,
28Da sa'ad da ya sa gizagizai a sararin sama, Ya buɗe maɓuɓɓugan teku,
29Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa. Ina can sa'ad da ya kafa harsashin ginin duniya.
30Ina kusa da shi kamar mai tsara fasalin gini, Ni ce abar murnarsa kowace rana, A koyaushe ina farin ciki a gabansa.
31Ina farin ciki da duniya, Ina murna da 'yan adam.
32“Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni, Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki.
33Ku saurari abin da aka koya muku, Ku zama masu hikima, kada ku yi sakaci da ita.
34Mutumin da ya kasa kunne gare ni, zai yi farin ciki hakanan, Wato yakan tsaya a ƙofata koyaushe, Yana kuma jira a ƙofar shiga gidana.
35Mutumin da ya same ni ya sami rai, Ubangiji zai ji daɗinsa.
36Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa, Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”
1Hikima ta gina gidanta, ta yi masa ginshiƙai bakwai. 2Ta sa an yanka dabba don biki, ta gauraya ruwan inabi da kayan yaji, ta shirya tebur. 3Ta aiki barorinta 'yan mata su je su hau wuri mafi tsayi a birni su yi kira. 4“Ku shigo, ku jahilai!” Ga dolo kuwa ta ce, 5“Zo ka ci abincina ka sha ruwan inabin da na gauraya. 6Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi.”
7Idan ka kwaɓi mai fāriya, za ka gamu da cin mutunci, idan ka tsauta wa mugu, kai ne za ka cutu. 8Faufau kada ka kuskura ka kwaɓi mai fāriya, zai ƙi ka saboda wannan, amma idan ka kwaɓi mai hikima zai girmama ka. 9Dukan abin da ka faɗa wa mutum mai hikima, zai ƙara masa hikima. Dukan abin da ka faɗa wa adali zai ƙara masa ilimi.
10Domin ka zama mai hikima dole ka fara da tsoron Ubangiji. Idan ka san Mai Tsarki, ka sami ganewa. 11Hikima za ta ƙara shekarunka. 12Kai ne da riba in ka sami hikima. Kai za ka sha hasara in ka ƙi ta.
13Wawanci kamar mace ce mai kwakwazo, jahila, marar kunya. 14Takan zauna a ƙofar gidanta, ko a wurin da ya fi duka bisa a cikin gari. 15Takan yi ta kiran masu wucewa waɗanda hankalinsu ke a kan ayyukansu, ta ce, 16“Ku shigo, ku jahilai!” Takan ce wa dolo, 17“Ruwan da aka sata ya fi daɗi, hakanan kuma abincin da ake satar ya fi daɗi.” 18Waɗanda suka fāɗa a hannunta ba su sani mutuwa za su yi ba, waɗanda suka riga sun shiga kuwa suna can sun nutse cikin lahira.
1Karin maganar Sulemanu ke nan. Ɗa mai hikima abin fāriya ne ga mahaifinsa, amma wawa yakan jawo wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
2Abin da ka samu ta hanyar zamba ba zai yi albarka ba, amma gaskiya za ta cece ka.
3Ubangiji ba zai bar mutumin kirki da yunwa ba, amma zai hana mugu ya kai ga biyan bukatarsa.
4Ragwanci zai sa talauci, amma yin aiki sosai zai arzuta ka.
5Mutum mai hankali yakan tattara amfanin gona da kaka, amma abin kunya ne a yi barci a lokacin girbi.
6Mutumin kirki yakan karɓi albarka, maganganun mugun kuwa sukan ɓoye mugun halinsa.
7Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye.
8Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace.
9Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su.
10Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, amma wanda ya bayyana gaskiya zai kawo salama.
11Kalmomin mutumin kirki maɓuɓɓugan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
12Ƙiyayya takan haddasa wahala, amma ƙauna takan ƙyale dukan laifofi.
13Mutane masu fasaha sukan yi magana mai ma'ana, amma wawaye suna bukatar horo.
14Mutane masu hikima sukan nemi ilimi iyakar iyawarsu, amma sa'ad da wawa ya yi magana, wahala tana kusa.
15Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci.
16Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a ƙara yin wani zunubi.
17Mutumin da ke kasa kunne sa'ad da ake kwaɓarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hatsari.
18Mutumin da ke faɗar ƙarairayi maƙiyi ne, dukan wanda ke baza jitajita wawa ne.
19Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.
20Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani.
21Kalmomin mutumin kirki za su amfani mutane da yawa, amma kana iya hallaka kanka da wauta.
22Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.
23Wawa ne ke jin daɗin aikata mugunta, amma mai fasaha yana jin daɗin hikima.
24Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.
25Hadiri yakan taso ya wargaza mugaye, amma amintattu lafiya lau suke a koyaushe.
26Sam, kada ka sa malalaci ya yi maka wani abu, zai sa ka ka yi fushi, idanunka su cika da hawaye mai zafi.
27Ka yi tsoron Ubangiji za ka rayu, ka yi tsawon rai, amma mugaye sukan mutu tun kwanansu bai ƙare ba.
28Abin da mutanen kirki ke sa zuciya yakan kai su ga murna, amma mugaye ba su da wani abu da za su sa zuciya a kai.
29Ubangiji yana kiyaye marasa laifi, amma yakan hallaka masu mugunta.
30Kullayaumi adalai sukan yi zamansu lafiya, amma mugaye ba za su zauna a ƙasar ba.
31Maganar adalai ta hikima ce, amma harshen da ke hurta mugunta, za a dakatar da shi.
32Adalai sun san irin maganar da ta cancanta su faɗa, amma mugaye, kullum sukan faɗi maganar da za ta cutar.
1Ubangiji yana ƙin masu yin awo da ma'aunin zamba, amma yana farin ciki da masu yin awo da ma'auni na gaskiya.
2Masu girmankai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa.
3Mutanen kirki su ne gaskiya takan bi da su. Rashin aminci kuwa yana hallaka maciya amana.
4Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.
5Gaskiya takan sa zaman mutanen kirki ya zama a sawwaƙe, amma mugun mutum shi yake kā da kansa da kansa.
6Adalci yakan ceci amintaccen mutum, amma marar aminci, haɗamarsa ce take zamar masa tarko.
7Mugun mutum yakan mutu da burinsa. Dogara ga dukiya bai amfana kome ba.
8Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.
9Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto.
10Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa'ad da mugaye suka mutu.
11Biranen da adalai ke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.
12Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la'akari yakan kame bakinsa.
13Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.
14Al'ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.
15Wanda ya ɗaukar wa baƙo lamuni zai yi da na sani, zai fi maka sauƙi idan ba ruwanka.
16Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su sami dukiya.
17In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar.
18A ainihi mugaye ba su cin ribar kome, amma idan ka yi abin da ke daidai, ka tabbata za a sāka maka da alheri.
19Mutumin da ya yi niyyar aikata abin da ke daidai zai rayu, amma mutumin da ya dukufa ga aikata mugunta zai mutu.
20Ubangiji yana ƙin masu muguwar niyya, amma yana murna da waɗanda ke aikata abin da ke daidai!
21Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba.
22Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.
23Abin da mutanen kirki suke so kullum yakan jawo alheri, idan mugaye sun sami biyan bukatarsu kowa zai yi ɓacin rai.
24Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.
25Ka yi alheri za ka arzuta. Ka taimaki waɗansu, su kuma za su taimake ka.
26Mutane sukan la'anci mai ɓoye hatsi, yana jira ya yi tsada, amma sukan yabi wanda yake sayar da nasa.
27Idan nufe-nufenka na kirki ne za a girmama ka, amma idan kai mai neman tashin hankali ne, to, abin da zai same ka ke nan.
28Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda ke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.
29Mutumin da ke jawo wa iyalinsa wahala, ƙarshensa talaucewa. Wawaye za su zama barorin masu hikima a koyaushe.
30Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.
31Idan an sāka wa mutumin kirki da alheri a duniya, hakika za a hukunta wa mugaye da masu zunubi.
1Mutumin da yake ƙaunar ilimi yakan so a faɗa masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ƙi yarda a faɗa masa laifinsa.
2Ubangiji yana murna da mutanen kirki, amma yakan hukunta masu shirya mugunta.
3Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram.
4Matar kirki abar fāriya ce, abar murna ga mijinta, amma idan ta sa shi kunya, ta zama masa kamar ciwo a ƙashinsa.
5Amintattun mutane za su yi maka abin da ke daidai, amma mugaye za su ruɗe ka.
6Maganganun mugaye na kisankai ne, amma kalmomin adalai sukan ceci waɗanda ake neman ransu.
7Mugaye sukan gamu da faɗuwarsu, ba magāda, amma iyalan adalai sukan dawwama.
8Idan kai haziƙi ne, za a yabe ka, amma idan kai dakiki ne, mutane za su raina ka.
9Gara kana talakanka, kana neman abinci, da ka mai da kanka kai wani abu ne, alhali kuwa abin da za ka ci ya fi ƙarfinka.
10Mutumin kirki yakan lura da dabbobinsa, amma mugaye sukan yi wa nasu ƙeta.
11Manomin da ke aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan aikin banza.
12Iyakar abin da mugaye suke so, shi ne su sami muguntar da za su yi, amma adalai suna tsaye daram.
13Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala.
14Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai sami abin da ya cancance shi.
15Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.
16Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.
17Sa'ad da ka faɗi gaskiya, ka yi adalci, amma ƙarairayi su ne jagorar aikata rashin adalci.
18Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.
19Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.
20Waɗanda ke shawarta mugunta za a auka musu farat ɗaya, amma waɗanda ke aikata alheri za su yi farin ciki.
21Ba wani mugun abu da zai sami adali, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala.
22Ubangiji yana ƙin maƙaryata, amma yana murna da masu faɗa da cikawa.
23Mai la'akari zai bar wa cikinsa abin da ya sani, amma wawaye sukan yi ta tallar wautarsu.
24Mutum mai mai da hankali ga aikinsa zai sami iko, amma ragwanci zai sa mutum ya zama bawa.
25Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.
26A koyaushe adalin mutum yakan gwada halinsa, amma mugaye sukan ɓata a hanya.
27Rago ba zai kai ga biyan bukatarsa ba, amma mai ƙwazo zai sami dukiya.
28Adalci hanyar rai ne, amma wauta hanyar mutuwa ce.
1Ɗa mai hikima yakan mai da hankali sa'ad da mahaifinsa yake kwaɓarsa, amma mutum mai girmankai ba ya yarda da kuskurensa.
2Mutanen kirki za a sāka musu da alheri a kan abin da suke faɗa, amma mayaudara sukan ƙosa su ta da zaune tsaye.
3Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.
4Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.
5Masu aminci suna ƙin ƙarairayi, amma maganganun mugun abin kunya ne da ƙasƙanci.
6Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.
7Waɗansu mutane sukan nuna su attajirai ne, alhali kuwa ba su da kome. Waɗansu kuma sukan nuna su matalauta ne, alhali kuwa suna da dukiya.
8Kuɗin attajiri suna iya ceton ransa, bai kyautu ba a razana matalauci.
9Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da ke mutuwa.
10Fāriya ba ta kawo kome sai wahala. Hikima ce a nemi shawara.
11Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta ƙaruwa.
12Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.
13Idan ka ƙi shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya.
14Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.
15Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke.
16Mutum mai hankali a koyaushe yakan yi tunani kafin ya aikata, amma wawa yakan tallata jahilcinsa.
17Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma waɗanda suke amintattu sukan kawo salama.
18Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsautawa za a girmama shi.
19Abu mai kyau ne mutum ya sami biyan bukatarsa! Wawaye sukan ƙi barin mugunta.
20Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.
21Wahala tana bin masu zunubi ko'ina, amma za a sāka wa adalai da kyawawan abubuwa.
22Mutumin kirki zai sami dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai.
23Saurukan da ba a aikatawa, za su ba da isasshen abinci ga matalauci, amma mutane marasa gaskiya sukan hana albarka.
24Idan ba ka horon ɗanka, ba ka ƙaunarsa ke nan, amma idan kana ƙaunarsa za ka riƙa kwaɓarsa.
25Adalai suna da isasshen abinci, amma mugaye fama suke da yunwa koyaushe.
1Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.
2Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji.
3Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci.
4Idan ba ka da shanun noma ba za ka sami hatsi mai yawa ba, amma idan kana da su za ka sami hatsi mai yawan gaske.
5Amintaccen mashaidi a koyaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.
6Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.
7Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka.
8Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.
9Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.
10Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.
11Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.
12Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.
13Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa'ad da murna ta tafi, koyaushe baƙin ciki yana nan.
14Mugu zai sami abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai sami sakayyar ayyukansa.
15Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la'akari yana lura da takawarsa.
16Mutum mai hankali yana lura don ya kauce wa wahala, amma wawa rashin kula gare shi, yakan aikata kome da gaggawa.
17Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.
18Jahilai sukan sami abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci.
19Tilas mugaye su rusuna wa adalai, su roƙe su tagomashi da tawali'u.
20Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa.
21Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum.
22Waɗansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure.
23Idan ka yi aiki za ka sami abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci.
24Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.
25Sa'ad da mashaidi ya faɗi gaskiya zai ceci rayuka, amma maƙaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa'ad da ya faɗi ƙarairayi.
26Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.
27Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne maɓuɓɓugar rai.
28Darajar sarki ta dogara ga irin yawan mutane da ya mallaka, idan ba su, shi ba kome ba ne.
29Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.
30Kwanciyar rai lafiya ce ga jiki, amma kishi yana kama da ciwon da yake cin ƙashi.
31Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.
32Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakonsa.
33Hikima tana cikin kowane tunani na haziƙi, wawa bai san kome game da hikima ba.
34Adalci yakan ɗaukaka al'umma, amma zunubi yakan kunyatar da al'umma.
35Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun 'yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.
1Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.
2Sa'ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha'awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.
3Ubangiji yana ganin abin da ke faruwa a ko'ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.
4Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.
5Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.
6Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa'ad da wahala ta zo.
7Mutane masu hikima suke yaɗa ilimi, amma banda wawaye.
8Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.
9Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da ke yin abin da ke daidai.
10Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.
11Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da ke can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa>
12Mai girmankai ba ya so a tsauta masa. Faufau ba zai nemi shawara a wurin masu hikima ba.
13Sa'ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa'ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.
14Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su.
15Wahaltaccen mutum a koyaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.
16Gara a zauna da talauci da tsoron Ubangiji, da a sami dukiya game da wahala.
17Gara cin mabunƙusa tare da waɗanda kake ƙauna, da ka ci abinci mai romo a inda ƙiyayya take.
18Zafin rai yakan kawo jayayya, amma haƙuri yana kawo salama.
19Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko'ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.
20Ɗa mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa.
21Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da ke daidai.
22Ka nemi dukan shawarwarin da ka iya ka samu, za ka yi nasara, idan ba tare da shawara ba, za ka fāɗi.
23Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da ke daidai a lokacin da ya dace!
24Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haura zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.
25Ubangiji zai rushe gidajen masu girmankai, amma zai kiyaye dukiyar gwauruwa, wato mata wadda mijinta ya mutu.
26Ubangiji yana ƙin tunanin mugaye, amma yana murna da kalmomi masu daɗi.
27Mai ƙoƙarin cin ƙazamar riba yana jefa iyalinsa a wahala ke nan. Kada ka karɓi hanci, za ka yi tsawon rai.
28Mutanen kirki sukan yi tunani kafin su ba da amsa. Mugaye suna da saurin ba da amsa, amma takan jawo wahala.
29Sa'ad da mutanen kirki sukan yi addu'a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.
30Fuska mai fara'a takan sa ka yi murna, labari mai daɗi kuma yakan sa ka ji daɗi.
31Idan ka mai da hakali sa'ad da ake tsauta maka kai mai hikima ne.
32Idan ka ƙi koyo kana cutar kanka, idan ka karɓi tsautawa za ka zama mai hikima.
33Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali'u kafin ka sami girmamawa.
1Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce.
2Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji yana auna manufarka.
3Ka roƙi Ubangiji, ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.
4Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce.
5Ubangiji yana ƙin kowane mutum da ke fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.
6Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.
7Lokacin da ka yi abin da Ubangiji ke so, ka iya mai da maƙiyanka su zama abokai.
8Gara ka sami kaɗan ta hanyar gaskiya, da ka tara abu mai yawa ta hanyar zamba.
9Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne ke bi da kai cikin ayyukanka.
10Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a koyaushe yakan yanke shawarar da ke daidai.
11Ubangiji yana son ma'aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai.
12Sarakuna ba za su iya jurewa da mugunta ba, gama adalci ke sa hukuma ta yi ƙarfi.
13Sarki yana so ya ji gaskiya, zai kuwa ƙaunaci mutanen da ke faɗar gaskiya.
14Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.
15Alherin sarki kamar gizagizai ne masu kawo ruwan sama a lokacin bazara, akwai rai a ciki.
16Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.
17Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.
18Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.
19Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali'u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.
20Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki.
21Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.
22Hikima maɓuɓɓugar rai ce ga mai hikima, amma ɓata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.
23Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya faɗa yakan yi rinjaye ƙwarai.
24Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.
25Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.
26Marmarin cin abinci yakan sa ɗan ƙodago ya yi aiki da ƙwazo, domin yana so ya ci ya ƙoshi.
27Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.
28Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.
29Mutum mai ta da zaune tsaye yakan ruɗi abokansa, ya kai su ga bala'i.
30Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.
31Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.
32Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
33Mutane sukan jefa kuri'a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.
1Gara a ci ƙanzo da rai a kwance, da gida cike da liyafa, amma cike da tashin hankali.
2Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon.
3Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.
4Mugaye sukan kasa kunne ga mugayen dabaru, maƙaryata kuma sukan kasa kunne ga ƙarairayi.
5Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.
6Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.
7Mutumin da yake kamili ba ya faɗar ƙarya, haka ma wawa ba zai faɗi wani abin kirki ba.
8Waɗansu mutane suna tsammani cin rashawa yakan yi aiki kamar sihiri, sun gaskata zai iya yin kome.
9Idan kana so mutane su so ka, ka riƙa yafe musu sa'ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta.
10Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa ɗaya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
11Mutuwa za ta zo wa mugaye kamar mugun manzo wanda a koyaushe yana so ya kuta tashin hankali.
12Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da waɗansu wawaye suna aikin dakikancinsu.
13Idan ka sāka alheri da mugunta, ba za ka iya raba gidanka da mugunta ba, faufau.
14Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.
15Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.
16Kashe kuɗi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani.
17A koyaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, 'yan'uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.
18Sai mutum marar tunani ne kaɗai zai ɗauki lamunin basusuwan maƙwabcinsa.
19Shi wanda yake son zunubi, yana son wahala ke nan, wanda kuma yake yin fāriya a dukan lokaci yana neman tashin hankali ke nan.
20Mutumin da yakan yi tunanin mugunta, ya kuma hurta ta, kada ya sa zuciya ga samun abin kirki, sai dai bala'i kaɗai.
21Mahaifi wanda ɗansa yake yin abubuwan wauta, ba shi da kome sai ɓacin rai da baƙin ciki.
22Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da baƙin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.
23Alƙalai marasa gaskiya suna cin hanci a ɓoye, sa'an nan ba za su aikata adalci ba.
24Baligi da hikima yake aikinsa, amma wanda bai balaga ba, bai san abin da zai yi ba.
25Wawan da yakan jawo wa mahaifinsa ɓacin rai, abin baƙin ciki yake ga mahaifiyarsa.
26Ba daidai ba ne a ci marar laifi tara, yi wa mutumin kirki bulala kuwa rashin adalci ne.
27Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai. 28Banda haka ma, ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, mai basira.
1Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da take daidai ba zai yarda ba.
2Wawa bai kula ba, ko ya fahimci abu, ko bai fahimta ba. Abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya nuna kuzarinsa.
3Zunubi da kunya a tattare suke. Idan ka yar da mutuncinka za ka sha ba'a a maimakonsa.
4Harshen ɗan adam yana iya zama shi ne asalin hikima mai zurfi kamar teku, sabo kamar ruwan rafi mai gudu.
5Ba daidai ba ne a yi wa mugun mutum alheri, sa'an nan a ƙi yi wa marar laifi adalci.
6Sa'ad da wawa ya fara jayayya, yana neman dūka ne.
7Sa'ad da wawa ya yi magana yana lalatar da kansa ne, maganarsa tarko ce, da ita ake kama shi.
8Ɗanɗanar jita-jita daɗi gare ta, mukan ƙosa mu haɗiye ta.
9Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa.
10Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.
11Attajirai suna zato dukiyarsu ita ce za ta kiyaye su kamar garuka masu tsayi da suke kewaye da birni.
12Ba wanda za a girmama sai mai tawali'u, mutum mai girmankai kuwa yana kan hanyar hallaka.
13Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai bankunya.
14Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa'ad da yake ciwo, amma idan ya karai, to, tasa ta ƙare.
15Mutane masu basira, a koyaushe suna da himma, a shirye kuma suke domin su koya.
16Kana so ka sadu da babban mutum? Ka kai masa kyauta, za ka gan shi a sawwaƙe.
17Wanda ya fara mai da magana a majalisa yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai abokin shari'arsa ya mai da tasa maganar tukuna.
18Idan mutum biyu ƙarfafa suna jayayya da juna a gaban shari'a, kuri'a a asirce kaɗai take iya daidaita tsakaninsu.
19Ɗan'uwan da ya ji haushinka zai gagare ka, idan ka yi faɗa da shi zai rufe maka ƙofarsa.
20Bisa ga sakamakon hurcinka haka za ka rayu.
21Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.
22Idan ka sami mace ka sami abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji ya yi maka.
23Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.
24Waɗansu abokai ba su sukan ɗore ba, amma waɗansu abokai sun fi 'yan'uwa aminci.
1Gara mutum ya zama matalauci amma mai aminci, da a ce ya zama maƙaryaci, wawa.
2Yin ɗokin da ba ilimi ba shi da amfani, rashin haƙuri kuma zai jawo maka wahala.
3Waɗansu mutane sukan lalatar da kansu ta wurin ayyukansu na jahilci, sa'an nan su sa wa Ubangiji laifi.
4Attajirai sukan sami sababbin abokai a koyaushe, amma matalauta ba zu su iya riƙon 'yan kaɗan da suke da su ba.
5Idan ka faɗi ƙarya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kuɓuta ba.
6Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin manyan mutane, kowa na so a ce shi abokin mutumin nan ne, mai yawan alheri.
7'Yan'uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Kome ƙoƙarin da zai yi ba zai sami ko ɗaya ba.
8Ka yi wa kanka gatanci, ka koyi dukan abin da kake iyawa, sa'an nan ka tuna da abin da ka koya, za ka arzuta.
9Ba wanda zai faɗi ƙarya a majalisa ya rasa shan hukunci, maƙaryaci, tasa ta ƙare.
10Ko kusa wawaye ba za su yi zaman jin daɗi ba, hakanan kuma bayi ba za su yi mulki a kan iyayengijinsu ba.
11Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba.
12Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.
13Dakikin ɗa yana jawo wa mahaifinsa lalacewa, mace mai mita tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.
14Mutum na iya cin gādon gida da kuɗi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kaɗai yake ba shi mace mai hankali.
15Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.
16Ka kiyaye umarnai za ka rayu, in ka ƙi binsu kuwa za ka mutu.
17Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.
18Ka yi wa 'ya'yanka tarbiyya tun suna ƙanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan.
19Idan mutum mai zafin rai ne, ƙyale shi ya sha sakamakonsa. Idan ka fisshe shi daga cikin wahala sau ɗaya, sai ka sāke yi.
20Ka saurari shawara, ka yarda ka koya, wata rana za ka zama mai hikima.
21Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata.
22Abin kunya ne mutum ya zama mai haɗama, matalauci kuma ya fi maƙaryaci.
23Ka yi tsoron Ubangiji za ka yi tsawon rai, ka kuma sami biyan bukata, ba abin da zai cuce ka.
24Waɗansu mutane sun cika lalaci, ko abincinsu ba su iya taunawa.
25Za a hukunta mai fāriya saboda ya zama ishara ga mutanen da ba su san kome ba, mutum mai hikima yakan koya sa'ad da aka tsauta masa.
26Sai marar kunya, marar mutunci yake wulakanta mahaifinsa, ko ya kori mahaifiyarsa daga gidansa.
27Ɗana idan ka bar yin nazari za ka manta da abin da ka riga ka koya.
28Ba gaskiya ga mashaidin da ya yi niyyar cutar wani. Mugaye suna ƙaunar yin mugunta.
29Wawa mai fāriya hakika zai sha dūka.
1Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.
2Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.
3Kowane wawa yakan fara yin jayayya, abin da ya fi daraja shi ne ka fita ka ware kanka.
4Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.
5Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.
6Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.
7'Ya'yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa'a.
8Sarkin da yake yin shari'a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.
9Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa>
10Allah yana ƙin masu ma'aunin algus.
11Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.
12Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.
13Idan barci ne sana'arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.
14Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.
15In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu'ulu'ai tamani.
16Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.
17Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.
18Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.
19Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.
20Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.
21Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.
22Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.
23Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma'aunin algus.
24Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai>
25Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa'adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.
26Sarki mai hikima zai bincika ya gane waɗanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi.
27Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya ɓoye masa ba.
28Sarki zai zauna dafa'an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.
29Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.
30Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.
1Ubangiji ne yake mallakar tunanin sarki a sawwaƙe kamar yadda yake yi da ruwan rafi.
2Ko da a ce dukan abin da kake yi daidai ne, ka tuna fa Ubangiji ya san manufarka.
3Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.
4Girmankai da fāriya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.
5Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba.
6Dukiyar da aka tara ta hanyar rashin gaskiya takan ƙare nan da nan, takan kuma kai ga mutuwa.
7Mugaye, tasu ta ƙare saboda muguntarsu, gama sun ƙi yin abin da yake daidai.
8Mutane masu laifi sukan bi ta karkatacciyar hanya, marasa laifi kuwa suna aikata abin da yake daidai.
9Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mace mai mita.
10Mugaye sun zaƙu su aikata mugunta, ba su yi wa kowa jinƙai.
11Sa'ad da aka hukunta mai girmankai, ko marar tunani yakan koyi wani abu, mutum mai hikima yakan koyi abin da ake koya masa.
12Adali ya san tunanin mugaye, yakan kuwa zama sanadin lalacewarsu.
13Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.
14Kyauta a asirce takan kwantar da zuciyar wanda yake fushi da kai.
15Sa'ad da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi baƙin ciki.
16Mutuwa tana jiran wanda ya ƙi bin hanyar hankali.
17Sa kai cikin nishaɗi, wato shan ruwan inabi, da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba.
18Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu.
19Gara ka zauna a hamada, da ka zauna tare da mace mai mita, mai yawan kai ƙara.
20Mutane masu hikima suna zaune da wadata da nishaɗi, amma wawaye da zarar sun sami kuɗi sukan kashe su nan da nan.
21Ka yi alheri ka yi aminci, za ka yi tsawon rai waɗansu kuma za su girmama ka, su yi maka abin da yake daidai.
22Sarkin yaƙi mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke taƙama da shi.
23Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.
24Ba kalmar da ta fi “Fāɗin rai” dacewa ga mutum mai girmankai, mai fāriya marar tunani.
25Malalacin mutumin da ya ƙi yin aiki, kansa yake kashewa.
26Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.
27Ubangiji yana ƙin hadayar da mugaye suka miƙa masa, tun ba wadda suka miƙa ta da mugun nufi ba.
28Ba a gaskata shaidar maƙaryaci, amma mutumin da yakan yi tunani a kan al'amura, akan karɓi tasa.
29Adali ya tabbatar da kansa, haka ma mugun mutum yakan yi da'awa, cewa shi ma ya tabbatar da kansa.
30Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.
31Kana iya shirya dawakai don zuwa yaƙi, amma nasara ta Ubangiji ce.
1Idan ya zama dole ne ka zaɓa tsakanin kyakkyawan suna ko dukiya, to, ka zaɓi kyakkyawan suna, tagomashi kuma ya fi azurfa da zinariya.
2Ba bambanci tsakanin mawadaci da matalauci, gama Ubangiji ne ya halicce su duka.
3Mutum mai hankali, in ya ga wahala tana zuwa yakan kauce mata, amma shashasha yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
4Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali'u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.
5Idan kana ƙaunar ranka ka nisanci tarkunan da aka kafa a hanya don su kama mugaye.
6Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.
7Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.
8In ka shuka rashin gaskiya masifa ce za ta tsiro, wato hukunci mai tsanani wanda zai hallakar da kai.
9Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.
10Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.
11In ka yi ladabi za ka zama aminin sarki, gama yana ƙaunar amintaccen mutum.
12Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.
13Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”
14Zina tarko ce, takan kama waɗannan waɗanda Ubangiji yake fushi da su.
15Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.
16Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.
17Ka kasa kunne zan koya maka abin da masu hikima suka faɗa, yi nazari a kan koyarwarsu. 18Za ka yi murna in ka tuna da su, ka iya faɗarsu. 19Ina so ka dogara ga Ubangiji, don haka zan faɗa maka su yanzu. 20Na rubuta maka karin magana, suna ƙunshe da ilimi da kyakkyawar shawara. 21Zan koya maka ainihin gaskiya, domin sa'ad da aka aike ka ka nemo ta, za ka iya kawo amsa daidai.
22Kada ka ƙwari matalauci don ka fi shi, kada ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari'a. 23Ubangiji zai yi magana dominsu a kan shari'ar da suke yi, ya nemi ran duk wanda yake neman rayukansu.
24Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai. 25Mai yiwuwa ne ka koyi irin ɗabi'unsu, har ka kasa sākewa.
26Kada ka yi alkawarin ɗaukar wa wani lamuni, 27gama idan ka kāsa biya har gadonka ma za su ɗauke.
28Kada ka kawar da shidar kan iyaka wadda kakanninka suka kafa.
29Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.
1Sa'ad da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake. 2Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne. 3Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.
4Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya. 5Kuɗinka sun iya ƙarewa kamar ƙyiftawar ido, kamar suna da fikafikai su tashi kamar gaggafa.
6Kada ka ci abincin marowaci, ko ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da ya sa a gabanka. 7Zai ce, “Bari a ƙara maka,” amma ba haka yake nufi ba. Kamar gashi yake a cikin maƙogwaronka. 8Za ka harar da abin da ka ci, dukan daɗin bakinka zai tafi a banza.
9Kada ka yi wa wawa magana irin ta haziƙai, gama ba zai yaba da maganarka ba.
10Kada ka kuskura ka kawar da shaidar iyaka, ko ka ƙwace gonar marayu. 11Ubangiji Mai Iko shi ne kāriyarsu, shi zai yi magana dominsu.
12Ka mai da hankali ga malaminka, ka koyi dukan abin da kake iyawa.
13Kada ka bar yaro ba horo, gama ko ka duke shi ba za a kashe shi ba. 14Lalle ne za ka ceci ransa.
15Ɗana, idan ka zama mai hikima zan yi murna ƙwarai. 16Zan yi murna idan na ji kana faɗar magana da hikima.
17Kada ka yi ƙyashin masu aikata zunubi tsoron Ubangiji kaɗai za ka sa a gaba. 18Idan haka ta samu za ka yi farin ciki nan gaba.
19Ka saurara, ya ɗana, ka zama mai hikima. Ka yi tunani mai zurfi a kan hanyarka. 20Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu haɗama. 21Gama bugaggu da ruwan inabi da masu zarin ci za su zama matalauta. Idan iyakar abin da kake yi daga ci sai barci ne, nan da nan za ka ga kana saye da tsummoki.
22Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa'ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.
23Gaskiya, da hikima, da ilimi, da hankali, sun cancanta a saye su, kome tamaninsu.
24Mahaifin adali yana da dalilin yin murna. Zai yi fāriya a kan ɗa mai hikima.
25Ka sa mahaifinka da mahaifiyarka su yi fāriya da kai, ka sa mahaifiyarka farin ciki.
26Ɗana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali. 27Karuwa, da mata mazinata, tarkon mutuwa ne su. 28Sukan laɓe su jira ka kamar mafasa, suna sa mutane da yawa su zama marasa aminci.
29Wa ake yi wa kaito? Wa yake da baƙin ciki? Wane ne mafaɗaci? Wa yake yin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido? 30Sai riƙaƙƙen mashayi wanda yake gaurayar ruwan inabi. 31Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da yake ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa'ad da kake motsa shi. 32Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka. 33Idanunka za su riƙa gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka faɗi magana sosai ba. 34Za ka ji kamar kana can cikin teku, jirin teku na ɗibarka kana lilo a kan rufin jirgin ruwa da yake tangaɗi. 35Za ka ce, “Lalle an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in ƙara sha.”
1Kada ka ji ƙyashin mugaye, kada ka yi ƙoƙarin yin abuta da su. 2Duk tunaninsu na yin mugunta ne, a duk lokacin da suka buɗe bakinsu sai sun cuci wani.
3An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi. 4Ta wurin ilimi a kan ƙawata ɗakuna da kyawawan kayayyaki masu tamani.
5Mai hikima ƙaƙƙarfa ne, i, mai ilimi yana daɗa ƙarfi. 6Banda wannan ma, dole ne ka shisshirya a natse kafin ka kama yaƙi. Bisa ga shawarwarin da za ka samu ne za ka yi nasara.
7Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa'ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.
8Idan a koyaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali. 9Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama'a suna ƙin mutum mai rainako.
10Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.
11Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi. 12Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.
13Ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaƙi a harshenka, 14haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.
15Kada ka shirya dabarun yi wa amintacce ƙwace, ko ka ƙwace masa gidansa, wannan mugunta ce. 16Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a koyaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.
17Kada ka yi murna sa'ad da bala'i ya aukar wa maƙiyinka. 18Ubangiji zai sani in kana murna, ba kuwa zai so haka ba, mai yiwuwa ne ba zai hukunta shi ba.
19Kada ka damu saboda mugaye, kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba. 20Gama mugun mutum ba shi da sa zuciya, ba abin da zai sa zuciya a kansa nan gaba.
21Ɗana, ka yi tsoron Ubangiji, ka kuma ji tsoron sarki, kada ka yi harkar kome da mutanen da suka tayar musu. 22Irin waɗannan mutane sukan hallaka farat ɗaya. Ka taɓa yin tunani a kan bala'in da Allah ko sarki sukan aukar>
23Masu hikima kuma sun faɗi waɗannan abu. Kuskure ne alƙali ya yi son zuciya. 24Idan ya kuɓutar da mugu, kowane mutum da yake a duniya zai la'anta shi ya ƙi shi. 25Alƙalan da suke hukunta wa mai laifi kuwa, za su arzuta, su ji daɗin kyakkyawan suna.
26Amsar gaskiya ita ce alamar abuta ta ainihi.
27Kada ka gina gidanka ka kafa shi, sai ka gyara gonakinka, ka tabbata za ka sami abin zaman gari.
28Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isasshen dalili ba, ko ka faɗi ƙarya a kansa. 29Kada ka ce, “Zan yi masa daidai da yadda ya yi mini, zan rama masa!”
30Na ratsa ta gonakin inabin wani malalaci, dakiki, 31suna cike da ƙayayuwa, ciyayi sun sha kansu, katangar dutse da take kewaye da su ta faɗi. 32Da na dubi wannan, na yi tunani a kansa, ya zamar mini ishara. 33“Yi ta ruruminka, ci gaba da barcinka, rungume hannuwanka don ka shaƙata.” 34Amma sa'ad da kake ta sharar barci fatara za ta auka maka kamar ƙungiyar 'yan fashi.
1Ga waɗansu sauran karin maganar Sulemanu waɗanda magatakardan Hezekiya Sarkin Yahuza suka juya.
2Muna girmama Allah saboda abin da ya rufe, muna girmama sarakuna saboda abin da suka ba da bayaninsa.
3Ba ku taɓa sanin abin da sarki yake tunani ba, gama tunaninsa sun fi ƙarfinmu. Kamar nisan sararin sama suke ko zurfafan teku.
4Ka tace azurfa, gwani kuwa zai yi wani kyakkyawan abu da ita. 5A kawar da mugayen mashawarta daga gaban sarki, hukumarsa za ta shahara a kan adalci.
6Sa'ad da kake tsaye a gaban sarki, kada ka nuna kai wani abu ne, kana kai kanka inda Allah bai kai ka ba. 7Gara a roƙe ka ka hau zuwa babban matsayi, da a faɗa maka ka ba da wurin da kake ga wanda ya fi ka maƙami.
8Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi>
9Idan kai da maƙwabcinka kun saɓa, ku daidaita a tsakaninku, kada a tona asiri. 10Mai yiwuwa ne wani ya ji ya zarge ku, ba za ku taɓa rabuwa da wannan kunya ba.
11Manufar da aka bayyana sosai kamar zubin zinariya take wanda aka yi a kan azurfa.
12Faɗakarwar da mutumin da ya gogu da al'amuran duniya ya yi ga wanda yake da niyya ya kasa kunne, tamaninta ya fi na zoben zinariya, ko kayan ado da aka yi da zinariya tsantsa.
13Amintaccen manzo yakan wartsakar da wanda ya aike shi, kamar ruwan sanyi yake a lokacin zafi.
14Mutanen da suke yin alkawari, ba su cikawa, kamar holoƙo suke, hadirin kaka.
15Rinjayen da aka yi cikin haƙuri yakan rushe ƙaƙƙarfar tsayayya, har ma yakan i wa masu ƙarfin gaske.
16Kada ka kuskura ka sha zuma gaba da kima, in ya yi maka yawa za ka yi hararwa. 17Kada ka cika ziyartar maƙwabcinka, ko zai gaji da kai har ya ƙi ka.
18Mutumin da yakan faɗi ƙarairayi a kan maƙwabcinsa, shi kamar kakkaifan takobi ne, ko kulki, ko kibiya mai tsini.
19Dogara ga marar aminci a lokacin hargitsi, kamar ƙoƙarin yin tauna da ruɓaɓɓun haƙora ne, ko yin tafiya da mai gurguwar ƙafa, 20ko kuma ka yi ƙoƙarin jin ɗumi ta wurin tuɓe tufafinka a ranar da ake sanyi. Raira waƙa ga mai baƙin ciki kamar marmasa gishiri a kan rauni ne.
21Idan maƙiyinka yana jin yunwa ka cishe shi, idan yana jin ƙishi ka ba shi abin sha. 22Za ka sa ya sha kunya, Ubangiji kuma zai sāka maka.
23Iskar arewa takan kawo ruwan sama, haka kuma jita-jita takan kawo fushi.
24Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mata mai mita.
25Jin labari mai daɗi wanda ba ka zato, yana kamar shan ruwan sanyi ne a sa'ad da ka sha rana kana jin ƙishi.
26Mutumin kirki wanda yakan yarda da mugun yana tunasshe ka da ƙazantattun maɓuɓɓuga ko rijiya mai dafi.
27Kamar yadda shan zuma da yawa ba shi da kyau a gare ka, haka kuma ƙoƙarin neman yabo mai yawa yake.
28Idan ba ka iya danne fushinka ba, ka zama mai kasala kamar birnin da ba shi da garuka, yana buɗe don a faɗa masa.
1Yabo bai dace da wawa ba, kamar yadda dusar ƙanƙara ba ta dace da lokacin zafi ba, ko ruwan sama a lokacin girbi.
2La'ana ba za ta kama ka ba, sai dai in ka cancance ta. Tana kamar tsuntsayen da suke firiya da dare ba za su sauka ba.
3Sai ka fyaɗi doki, ka sa wa jaki linzami, wawa kuma sai ka doke shi.
4Idan ka amsa tambayar wauta, ka zama wawa daidai da mutumin da ya yi tambayar.
5Ka amsa wauta ga tambayar wauta, wanda ya yi tambayar zai gane wawancinsa.
6Mutumin da ya sa wawa ya isar masa da saƙo ya datse ƙafafunsa, yana nemar wa kansa wahala.
7Wawa yakan yi amfani da karin magana kamar yadda tauyayyen mutum yake amfani da ƙafafunsa.
8Wanda ya yabi wawa yana kama da wanda ya ɗaura dutse a majajjawa.
9Karin magana a bakin wawa kamar sukar ƙaya ce a hannun mai maye.
10Wanda ya ɗauki wawa aiki yana cutar duk wanda aikin ya shafa.
11Wawan da yake maimaita aikin wautarsa yana kama da kare mai yin amai ya koma ya tanɗe.
12Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
13Don me malalaci yakan kasa fita daga gida? Zaki yake tsoro>
14Malalaci yana ta jujjuyawa a gadonsa kamar yadda ƙyauren ƙofa yake juyawa.
15Malalaci yana sa hannu cikin ƙwaryar abinci, amma ya kāsa kaiwa bakinsa.
16Malalaci yana ganin kansa mai hikima ne fiye da mutum bakwai waɗanda suke da dalilai a kan ra'ayinsu.
17Mutumin da ya tsoma baki cikin jayayyar da ba ta shafe shi ba sa'ad da yake wucewa, yana kama da mutum wanda yake kama kare a kunne. 18-19Mutum wanda yakan ruɗi maƙwabcinsa sa'an nan ya ce, wasa yake yi kawai, yana kama da mahaukaci wanda yake wasa da wuta, da kibau, da mutuwa.
20Idan ba itace wuta takan mutu, haka kuma idan ba mai gulma ba za a yi jayayya ba.
21Kamar yadda gawayi yake ga garwashin wuta, itace kuma ga wuta, haka mai gardama yake ga jayayya.
22Kamar yadda lomar abinci mai daɗi takan gangara can cikin ciki haka maganar mai gulma take.
23Bakin da ba ya faɗar gaskiya, da zuciya mai ƙiyayya suna kama da kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba.
24Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye ta da maganar bakinsa, yana kuma ƙunshe da munafunci. 25Sa'ad da yake magana mai kyau kada ka gaskata shi, domin zuciyarsa tana cike da mugunta. 26Ko da yake kila zai ɓoye ƙiyayyarsa, duk da haka muguntarsa za ta bayyana ga mutane.
27Wanda ya haƙa ramin mugunta shi zai faɗa ciki, wanda kuma ya mirgino dutse, zai fāɗo a kansa.
28Maƙaryaci yana ƙin wanda ya yi wa ƙarya, mai daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.
1Kada ka yi fāriya a kan abin da za ka yi gobe domin ba ka san abin da zai faru daga yanzu zuwa gobe ba.
2Bari waɗansu su yabe ka ko da baƙi ne, faufau kada ka yabi kanka.
3Dutse da yashi suna da nauyi ƙwarai, amma nauyin wahalar da wawa zai haddasa ya fi nasu duka.
4Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma duk da haka bai kai ga kishi ba.
5Gara ka tsauta wa mutum a fili da ka bar shi ya zaci ba ka kula da shi ba sam.
6Aboki aboki ne ko da ya cuce ka, amma maƙiyi ko ya rungume ka kada ka sake!
7Wanda ya ƙoshi ba zai ko kula da zuma ba, amma wanda yake jin yunwa abinci mai ɗaci zaƙinsa yake ji.
8Mutumin da ya bar gida yana kama da tsuntsun da ya bar sheƙarsa.
9Turare da man ƙanshi sukan sa ka ji daɗi, haka abuta ta ainihi takan ƙara maka ƙarfi.
10Kada ka manta da abokanka, ko abokan mahaifinka. Idan kana shan wahala kada ka nemi taimako wurin ɗan'uwanka. Maƙwabci na kusa yana iya taimakonka fiye da ɗan'uwan da yake nesa.
11Ɗana, ka zama mai hikima, ni kuwa zan yi farin ciki, zan iya amsa kowace irin sūkar da wani zai yi mini.
12Mutum mai hankali yakan hango hatsari ya kauce masa, amma mutumin da ba shi da kula, yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
13Ka karɓe tufar wanda ya zamar wa baƙo lamuni, da kuma wanda ya zama lamunin karuwa.
14In ka farkar da abokinka da babbar murya tun da sassafe, daidai ne da zaginsa.
15Mace mai mita kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa. 16Kaƙa za ka iya sa ta ta kame bakinta? Ka taɓa ƙoƙarin tsai da iska? Ko kuwa ka taɓa ƙoƙarin dintsi mai a tafin hannunka>
17Daga wurin mutane mutane suke koyo, kamar yadda a kan wasa ƙarfe da ƙarfe.
18Ka lura da itacen ɓaure, zai yi 'ya'ya ka ci. Baran da ya lura da maigidansa za a girmama shi.
19Yadda kake ganin fuskarka a ruwa, haka kake ganin kanka a zuciyarka.
20Muradin mutum kamar lahira yake, a kullum ba ya ƙoshi.
21Da wuta ake gwada azurfa da zinariya, amma yabon da ake yi wa mutum shi ne magwajinsa.
22Ko da za ka doki wawa ka bar shi tsakanin rai da mutuwa, duk da haka yana nan da wautarsa kamar yadda yake.
23Ka lura da garkunan tumakinka da na shanunka da kyau iyakar iyawarka, 24domin dukiya ba ta tabbata har abada, al'ummai ma haka ne. 25Ka yanki ingirici, lokacin da yake toho kana iya yankar ciyawa a gefen tuddai. 26Kana iya yin tufafi da ulun tumakinka, kana iya sayen gona da kuɗin awakinka. 27Madarar awakinka za ta zama abincinka kai da iyalinka, da kuma barorinka 'yan mata.
1Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba shi da tsoro.
2Al'umma za ta ƙarfafa ta jure idan shugabanninta masu basira ne, masu hankali. Amma idan ƙasar mai aikata zunubi ce za ta sami shugabanni da yawa.
3Mai mulki wanda yake zaluntar talakawa, ya zama kamar ruwa mai lalatar da amfanin gona.
4Wanda ba ya bin doka tare da mugaye yake, amma idan kana bin doka kai abokin gāban mugaye ne.
5Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai.
6Gara ka zama matalauci mai aminci da ka zama mawadaci, marar aminci.
7Saurayi wanda ya kiyaye doka mai basira ne shi, amma wanda yake abuta da 'yan iska zai zama mai jawo wa mahaifinsa kunya.
8Idan kana tara dukiya ta wurin ba da bashi da ruwa kana kuma ƙwarar jama'a, dukiyarka za ta koma ga wanda yake yi wa talakawa alheri.
9Idan ka ƙi biyayya ga doka, Allah zai ƙi jin addu'o'inka.
10Idan ka yaudari mutumin kirki don ya faɗa cikin mugunta, kai kanka ne za ka fāɗa cikin tarkon da ka haƙa. Marar laifi kuwa zai sami babban sakamako.
11Attajirai, a koyaushe, zato suke su masu hikima ne, amma matalauci mai tunani ya fi sanin abin da yake daidai.
12Sa'ad da mutanen kirki suke sarauta, kowa da kowa yakan yi biki, amma sa'ad da mugaye suka kama mulki mutane sukan riƙa ɓuya.
13Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa'an nan Allah zai yi maka jinƙai.
14Mutumin da yake tsoron Ubangiji koyaushe, zai yi farin ciki, amma idan ya taurare zai lalace.
15Talakawa ba su da wani taimako sa'ad da suke ƙarƙashin mulkin mugun. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanɗa.
16Mai mulki wanda ba shi da basira yakan zama mai mugun tsanani. Amma wanda yake ƙin rashin aminci, ko ta ƙaƙa zai daɗe yana mulki.
17Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.
18Ka yi aminci za ka zauna lafiya, idan kuwa ka yi rashin aminci za ka fāɗi.
19Manomin da yake aiki sosai, zai sami wadataccen abinci, amma mutanen da suke zaman banza koyaushe, za su zama matalauta.
20Amintaccen mutum zai cika kwanakinsa lafiya, amma idan kana so ka sami dukiya dare ɗaya, za a hukunta ka.
21Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda 'yar ƙaramar rashawa.
22Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.
23Wanda ya tsauta wa mutum zai sami yabo daga baya, fiye da wanda ya yi masa daɗin baki.
24Wanda yake yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa sata, yana kuwa tsammani ba laifi ba ne, daidai da ɓarawo yake.
25Mutum mai haɗama yana haddasa tashin hankali, amma wanda ya dogara ga Ubangiji zai sami wadar zuci.
26Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.
27Wanda yake bayarwa ga matalauta, ba zai talauce ba, amma wanda bai kula da su ba, mutane da yawa za su la'ance shi.
28Mutane sukan ɓuya sa'ad da mugaye suka sami iko, amma sa'ad da iko ya fita daga hannunsu adalai sukan ƙaru.
1Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.
2Sa'ad da masu adalci suke mulki, jama'a sukan yi murna, amma sa'ad da mugaye suke mulki, jama'a sukan yi nishi.
3Wanda yake ƙaunar hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa. Amma wanda yake abuta da karuwai zai lalatar da dukiyarsa.
4Sarkin da yake aikata adalci ƙasarsa za ta yi ƙarƙo, amma wanda yake karɓar rashawa zai lalatar da ƙasar.
5Mutum wanda yake yi wa maƙwabcinsa daɗin baƙi yana kafa wa kansa tarko.
6Laifin mugun zai zama tarko a gare shi, amma adali zai raira waƙa, ya yi farin ciki.
7Adali yana sane da hakkin matalauta, amma mugun bai san wannan ba.
8Ashararai sukan sa wa birni wuta, amma masu hikima sukan kwantar da hasala.
9Idan gardama ta shiga tsakanin mai hikima da wawa, sai wawa ya yi ta fushi, ko kuwa ya yi ta dariya, gardamar dai ba za ta ƙare ba.
10Mutane masu kisankai suna ƙin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa.
11Wawa yakan nuna fushinsa koyaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa.
12Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.
13Matalauci da azzalumi suna tarayya a abu ɗaya, wato dukansu Ubangiji ne yake ba su ganin gari.
14Idan sarki yana yi wa talakawa shari'ar gaskiya, zai daɗe yana mulki.
15Horo da tsautawa suna ba da hikima, amma yaron da aka sangarta zai jawo wa mahaifiyarsa kunya.
16Sa'ad da mugaye suke mulki, laifofi suka ƙaru, amma adalai za su ga faɗuwar waɗannan mutane.
17Ka hori ɗanka zai daɗaɗa maka rai, ya kuma faranta maka zuciya.
18Inda ba a bin faɗar Allah, jama'a za su kangare, amma mai farin ciki ne wanda yake kiyaye dokar Allah.
19Bara ba ya horuwa ta wurin magana kawai, gama ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
20Ka ga mutum mai garajen yin magana? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
21Baran da aka shagwaɓa tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa tankar magājin gida.
22Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.
23Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.
24Abokin ɓarawo mugun maƙiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce kome ba.
25Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.
26Mutane da yawa sukan nemi farin jini daga wurin mai mulki, amma Ubangiji ne yake yi wa mutum adalci.
27Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga adali, adali kuma abin ƙyama ne ga mugun.
1Waɗannan su ne maganar Agur ɗan Yake, da ya yi wa Etiyel da Yukal,
2“Hakika wautata ta sa na zama kamar dabba ba mutum ba, Ba ni kuwa da fahimi irin na mutum.
3Ban koyi hikima ba, Ban kuwa san kome game da Allah ba.
4Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko? Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa? Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa? Wa kuma ya kafa iyakar duniya? Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa? Hakika ka sani!
5“Kowace maganar Allah takan tabbata. Shi garkuwa ne ga waɗanda suke fakewa a wurinsa. 6Kada ka yi ƙari a kan maganarsa, don kada ya tsauta maka, a kuma bayyana kai maƙaryaci ne.”
7Abu biyu na roƙe ka, kada ka hana mini su kafin in mutu. 8Ka kawar da ƙarya nesa da ni. Kada ka ba ni talauci ko dukiya, sai dai ka ba ni abinci daidai da bukatata, 9don kada in wadata, har in yi musunka, in ce, “Wane ne Ubangiji?” Kada kuwa in yi talauci har in yi sata in saɓi sunan Allahna.
10Kada ka kushe bara a wurin maigidansa domin kada ka yi laifin da zai sa a la'ance ka.
11Akwai waɗansu mutane da sukan zagi iyayensu maza, ba sukan kuma nuna godiya ga iyayensu mata ba.
12Akwai waɗansu mutane da suke ganin kansu tsarkaka ne, alhali kuwa ƙazamai ne su.
13Akwai waɗansu mutane da suke yi wa jama'a ƙallon raini suna ɗaurin gira.
14Akwai waɗansu mutane waɗanda haƙoransu takuba ne, mataunansu kuma wuƙaƙe ne, don su cinye matalauta da masu fatara daga duniya. 15-16Matsattsaku tana da 'ya'ya mata biyu, ana kiransu, “Ba ni, Ba ni.” Akwai abu uku da ba su ƙoshi, i, har huɗu ma da ba su cewa, “Ya isa,” wato lahira, macen da ba ta haihuwa, ƙasa wadda ba ta ƙoshi da ruwa, wuta wadda ba ta cewa, “Ya isa.”
17Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye. 18-19Akwai abu uku, i, har huɗu ma, waɗanda ban iya fahimtar su ba, wato yadda gaggafa take tashi a sararin sama, yadda maciji yake jan ciki a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, Sha'anin namiji da 'ya mace.
20Ga yadda al'amarin mazinaciya yake, takan yi sha'aninta sa'an nan ta yi wanka ta ce, “Ban yi laifin kome ba!” 21-23Akwai abu uku, i, har huɗu ma waɗanda duniya ba ta jurewa da su, wato bara da ya zama sarki, wawa da ya ƙoshi da abinci, mummunar mace da ta sami miji, baiwar da ta gāji uwargijiyarta. 24-28Akwai ƙananan abubuwa huɗu a duniya, amma suna da hikima ƙwarai, wato tururuwa talikai ne marasa ƙarfi, amma duk da haka sukan tanadi abincinsu da rani, remaye ba ƙarfafa ba ne, duk da haka suna yi wa kansu gidaje a cikin duwatsu, fara ba su da sarki, amma duk da haka suna tafiya sahu-sahu. ƙadangare ma wanda ka iya kama shi a hannu, amma yana zama a cikin fādodin sarakuna. 29-31Akwai abu uku, i, har huɗu ma da suke da kwarjini da taƙama a tafiyarsu, wato Zaki wanda ya fi dukan dabbobi ƙarfi, ba ya ratse wa kowa daga cikinsu, bunsuru da zakara mai taƙama, sarkin da yake tafiya gaban jama'arsa.
32Idan ka yi wauta kana ta ɗaukaka kanka, ko kuwa kana shirya mugunta, ka tsaya ka yi tunani! 33Gama kaɗa madara takan kawo mai, murɗa hanci takan sa a yi haɓo, tsokanar fushi takan kawo jayayya.
1Wannan ita ce maganar sarki Lamuwel wadda uwarsa ta koya masa.
2“Mene ne, ɗana? Mene ne, ya ɗana ne cikina? Mene ne, ɗana na wa'adi? 3Kada ka ba da ƙarfinka ga mata, kada kuwa ka mai da hankali gare su, waɗanda suke hallaka sarakuna. 4Bai dace ba, ya Lamuwel, bai dace ba ko kaɗan, sarakuna su sha ruwan inabi, ko masu mulki su yi marmarin barasa, 5don kada su sha su manta da doka, su kuma kauce wa gaskiya a shari'ar waɗanda aka zalunta. 6A ba da barasa ga wanda yake cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi kuma ga waɗanda suke cikin ɓacin rai. 7Bari ya sha don ya manta da talaucinsa, don kada kuma ya ƙara tunawa da ɓacin ransa.
8“Ka yi magana domin bebaye, domin kuma hakkin dukan waɗanda ba su da wani mataimaki. 9Ka yi magana dominsu, ka yi shari'ar adalci, ka kiyaye hakkin matalauta da masu bukata.”
10Wa yake iya samun cikakkiyar mace? Darajarta ta fi ta lu'ulu'ai.
11Mijinta yakan amince da ita, ba kuwa zai yi hasara ba.
12Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakinta.
13Takan samo ulu da lilin, ta yi saƙa da hannuwanta da farin ciki.
14Takan kawo abincinta daga nesa, kamar fatake.
15Takan yi asubanci ta shirya wa iyalinta abinci, ta kuma shirya wa 'yan matan gidanta aike-aiken da za su yi.
16Takan lura da gona sosai kafin ta saya, da ribar da ta ci take dasa gonar inabi.
17Takan himmantu ta yi aiki tuƙuru.
18Ta sani akwai riba a cikin kasuwancinta. Fitilarta na ci dare farai.
19Da hannunta take kaɗi, tana kuma saƙa da hannuwanta.
20Takan yi wa matalauta da masu fatara karamci.
21Ba ta jin tsoron lokacin sanyi gama 'ya'yanta duka suna da tufafi masu ƙauri.
22Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa, tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.
23Mijinta sananne ne a dandali, sa'ad da yake zaune tare da dattawan gari.
24Takan yi riguna na lilin ta sayar, takan kuma sayar wa fatake da abin ɗamara.
25Wadata da mutunci su ne suturarta. Ba ta jin tsoron tsufa.
26Tana magana da hikima. Koyarwarta ta alheri ce.
27Tana lura da al'amuran 'ya'yanta da kyau. Ba ruwanta da ƙyuya.
28'Ya'yanta sukan tashi su gode mata, mijinta kuma yana yabonta.
29Ya ce, “Mata da yawa sun yi abin yabo, amma ke kin fi su duka.”
30Kayan tsari da jamali duk banza ne, amma mace mai tsoron Ubangiji, ita ce abar yabo.
31A yi mata cikakken yabo saboda ayyukanta, za a yabi ayyukanta a dandali.