Psalms
LITTAFI NA FARI: Farin Ciki na Gaskiya: (Zabura na 1-41)
1Albarka ta tabbata ga mutumim da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.
2Maimakon haka, yana in daɗin karanta shari'ar Allah, Yana ta nazarinta dare da rana.
3Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.
4Amma mugaye ba haka suke ba, Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.
5Allah kuwa zai hukunta mugaye, Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.
6Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.
1Don me al'ummai suke shirin tayarwa? Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza>
2Sarakunan duniya sun yi tayarwa, Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare, Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.
3Suna cewa, “Bari mu 'yantar da kanmu daga mulkinsu, Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”
4Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama, Ya mai da su abin dariya.
5Ya yi musu magana da fushi, Ya razanar da su da hasalarsa,
6Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka, Na naɗa sarkina.”
7Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta. Ubangiji ya ce mini, “‘Kai ɗana ne, Yau ne na zama mahaifinka.
8Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al'ummai, Dukan duniya kuma za ta zama taka.
9Za ka mallake su da sandan ƙarfe, Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.”
10Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna, Ku mai da hankali, ku mahukunta!
11Ku bauta wa Ubangiji da tsoro, Ku yi rawar jiki, ku rusuna masa,
12Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!
1Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji, Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!
2Suna magana a kaina, suna cewa, “Allah ba zai taimake shi ba!”
3Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari, Kana ba ni nasara, Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.
4Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako, Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.
5Na kwanta na yi barci, Na kuwa tashi lafiya lau, Gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6Ba na jin tsoron dubban abokan gāba Waɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.
7Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana, Ka hallakar da dukan mugaye.
8Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, Bari ya sa wa jama'arsa albarka!
1Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!
2Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina? Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza, Da bin abin da yake na ƙarya>
3Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa, Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi.
4Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku, Ku yi tunani da gaske a kan wannan A kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.
5Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace, Ku kuma dogara gare shi.
6Akwai mutane da yawa da suke cewa, “Da ma a sa mana albarka!” Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!
7Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne, Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.
8Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni, Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.
1Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji, Ka kuma ji ajiyar zuciyata.
2Ya Sarkina, Allahna, Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.
3A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji, Da safe za ka ji muryata, Da hantsi zan yi addu'ata, In kuma jira amsa.
4Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne, Ba ka yarda da mugunta a gabanka.
5Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya, Kana ƙin mugaye.
6Kakan hallakar da duk maƙaryata, Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.
7Amma ni, ina iya zuwa wurinka, Saboda ƙaunarka mai girma, In yi sujada a tsattsarkan Haikalinka, In kuma rusuna maka da bangirma.
8Ina da abokan gāba da yawa, ya Ubangiji, Ka bi da ni in aikata nufinka, Ka kuma fayyace mini hanyarka domin in bi ta!
9Abin da maƙiyana suke faɗa, Ba abin da za a yarda da shi ba ne, Su dai, so suke su hallakar kawai, Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake, Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.
10Ka kāshe su, ka hukunta su, ya Allah Ka watsar da mugayen shirye-shiryensu, Ka kore su daga gabanka sabili da yawan zunubansu, Da kuma tayarwar da suke yi maka.
11Duk waɗanda suka fake gare ka za su yi farin ciki, Kullum za su yi ta raira waƙa domin murna. Kana kiyaye waɗanda suke ƙaunarka, Suna kuwa matuƙar murna saboda kai.
12Ka sa wa masu yi maka biyayya albarka, ya Ubangiji, Alherinka yana kāre su kamar gārkuwa.
1Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini! Kada ka hukunta ni da fushinka!
2Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis, Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.
3Duk na damu ƙwarai da gaske. Sai yaushe wannan zai ƙare, ya Ubangiji>
4Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni, Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa.
5Ba za a tuna da kai a lahira ba, Ba wanda zai yabe ka a can!
6Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki, Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana. Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.
7Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka, Har da ƙyar nake iya gani, Duk kuwa saboda abokan gābana!
8Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta! Ubangiji yana jin kukana.
9Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako, Yana kuwa amsa addu'o'ina.
10Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu, Suna cikin matsanancin ruɗami, Za a kwashe su farat ɗaya.
1Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka, Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata,
2Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni, Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni, A can za su yayyage ni kamar zaki.
3Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan, Wato idan na yi wa wani laifi,
4Idan na ci amanar abokina, Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,
5To, bari abokan gābana su fafare ni, su kama ni, Bari su datse ni har ƙasa, su kuma kashe ni, Su bar ni ƙasa, matacce!
6Ka tashi da fushinka, ya Ubangiji, Ka kuma tashi ka yi gāba da hasalar abokan gābana! Ka tashi, ka taimake ni, gama adalci kake so a yi.
7Ka tattaro dukan kabilun da suke kewaye da kai, Ka yi mulki a kansu daga Sama.
8Ya Ubangiji, kai ne alƙalin dukan mutane. Ka shara'anta mini bisa ga adalcina, Gama ba ni da laifi, ina kuma da kirki.
9Ka tsai da muguntar mugaye, Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki. Kai Allah mai adalci ne, Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.
10Allah ne mai kiyaye ni, Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.
11Allah alƙali ne mai adalci, Kullum kuwa yana kā da mugaye.
12Idan mutane ba su tuba ba, Allah zai wasa takobinsa,
13Zai ɗana bakansa ya shirya shi, Zai ɗauki makamansa masu dafi, Ya kuma auna kibansa masu wuta.
14Ka duba, yadda mugu yake tunanin mugunta a ransa, Yana shisshirya wahala, yana kuma aikata ruɗi.
15Yana haƙa rami mai zurfi a ƙasa, Sa'an nan ya fāɗa ramin da ya haƙa!
16Saboda haka muguntarsa ta hukunta shi ke nan, Rikicin kansa ya yi masa lahani.
17Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa, Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.
1Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya. Yabonka ya kai har sammai,
2Yara da jarirai suna raira shi, Ka gina kagara saboda magabtanka, Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.
3Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi, Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
4Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi, Mutum kurum, har da kake lura da shi>
5Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi, Ka naɗa shi da daraja da girma!
6Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta, Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa,
7Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji,
8Da tsuntsaye da kifaye, Da dukan halittar da take cikin tekuna.
9Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya!
1Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji, Zan hurta dukan abubuwa masu banmamaki da ka yi.
2Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai, Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!
3Magabtana sun jā da baya da suka gan ka, Suka faɗi, suka mutu.
4Kai da kake alƙali mai adalci Ka zauna a kursiyinka, Ka kuwa yi shari'ar da ta yi mini daidai.
5Ka kā da arna, Ka kumar hallakar da mugaye, Ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba.
6An hallaka abokan gābanmu har abada, Ka lalatar da biranensu, An kuma manta da su sarai.
7Amma Ubangiji sarki ne har abada, Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.
8Yana mulkin duniya da adalci, Yana yi wa mutane shari'a da gaskiya.
9Ubangiji mafaka ne ga waɗanda ake zalunta, Wurin ɓuya a lokatan wahala.
10Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.
11Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona! Ku faɗa wa kowace al'umma abin da ya yi!
12Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya, Ba ya mantawa da kukansu, Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.
13Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai! Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini! Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,
14Domin in iya tsayawa a gaban jama'ar Urushalima, In faɗa musu dukan abin da ya sa nake yabonka. Zan yi farin ciki saboda ka cece ni.
15Arna sun haƙa rami sun kuwa fāɗa ciki, Sun ɗana tarko, ya kuwa kama su.
16Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci, Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.
17Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye, Da dukan waɗanda suke ƙin Allah.
18Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba, Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada.
19Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka! Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su.
20Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji, Ka sa su sani su mutane ne kawai.
1Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa? Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala>
2Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta, Ɗana tarkon da suka yi ya kama su.
3Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa, Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.
4Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!” Wannan ne abin da mugu yake tunani.
5Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi. Ba zai fahimci hukuncin Allah ba, Yana yi wa abokan gābansa duban raini.
6Yana ce wa “Ba zan taɓa fāɗuwa ba, Ba zan taɓa shan wahala ba.”
7Maganganunsa suna cike da zage-zage, da ƙarairayi, da barazana, Yana da saurin faɗar maganganun ƙiyayya da na mugunta.
8Yakan ɓuya cikin ƙauyuka, Ya jira a can har ya kashe marasa laifi. Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,
9Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki. Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama, Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!
10Yakan ragargaza kāsasshe, Ya gwada masa ƙarfi, ya ci nasara a kansa.
11Mugun mutum yakan ce wa kansa, “Allah bai kula ba! Ya rufe idonsa, ba zai taɓa ganina ba.”
12Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni! Kada ka manta da waɗanda ake zaluntarsu, ya Allah!
13Yaya mugun zai riƙa raina Allah, Har ya riƙa ce wa kansa, “Ba zai hukunta ni ba?”
14Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.
15Ka karya ikon mugaye, masu mugunta, Ka hukunta su saboda muguntarsu, Har hukuncinsu ya cika sarai.
16Ubangiji sarki ne har abada abadin, Arna kuma za su ɓace daga ƙasarsa.
17Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji, Za ka ba su ƙarfin hali.
18Za ka ji koke-koken waɗanda ake zalunta da na marayu, Ka yi shari'ar da za su ji daɗi, Domin kada 'yan adam su ƙara haddasa wata razana.
1Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya, Wauta ce idan kun ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,
2Domin mugaye sun ja bakkunansu, Sun kuma ɗana kibansu Domin su harbi mutanen kirki a duhu.
3Ba abin da mutumin kirki zai iya yi Sa'ad da kome ya lalace.”
4Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Yana da kursiyinsa a Sama. Yana kallon dukan mutane Yana sane da abin da suke yi.
5Yana auna masu kirki da mugaye dukka, Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.
6Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
7Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka, Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa.
1Ka cece ni, ya Ubangiji, Ba sauran mutanen kirki, Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.
2Dukan mutane suna yi wa juna ƙarya, Suna ruɗin junansu da yaudara.
3Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru, Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya!
4Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama, Ba kuwa wanda zai hana mu. Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?”
5Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu, Domin ana zaluntar masu bukata, Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi. Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”
6Alkawaran Ubangiji abin dogara ne, Alkawarai ne na ainihi kamar azurfa Da aka tace har sau bakwai cikin matoya.
7Ka kiyaye lafiyarmu, ya Ubangiji, Ka kiyaye mu daga irin waɗannan mutane.
8Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga, Suna ta yabon abin da yake mugunta.
1Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji? Har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka>
2Har yaushe raina zai jure da shan wahala? Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana? Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina>
3Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini, Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.
4Sa'an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba! Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.
5Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka, Zan yi murna gama za ka cece ni.
6Zan raira waƙa ga Ubangiji, Gama ya kyautata mini.
(Zab 53.1-6)
1Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!” Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.
2Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane, Ya ga ko da akwai masu hikima Waɗanda suke yi masa sujada.
3Amma dukansu sun koma baya, Su duka mugaye ne, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai, Babu ko ɗaya.
4Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba? Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne? Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke zaman gari, Ba su yin addu'a gare ni.”
5Amma za su razana, Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.
6Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya, Saboda yana dogara ga Ubangiji.
7Ina addu'a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona! Sa'ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama'arsa, Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki, Jama'ar Isra'ila za su yi murna.
1Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka? Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka>
2Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, Yana kuwa aikata abin da yake daidai, Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,
3Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu. Ba ya zargin abokansa, Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.
4Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su, Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya, KUllum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,
5Yana ba da rance ba ruwa, Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.
1Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.
2Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina, Dukan kyawawan abubuwan da nake da su Daga gare ka suke.”
3Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita! Ba abin da raina ya fi so, Sai in zauna tare da su.
4Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka, Za su jawo wa kansu wahala. Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba. Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.
5Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji, Kai ne kake biyan dukan bukatata, Raina yana hannunka.
6Kyautanka zuwa gare ni da bansha'awa suke, Kyawawa ne kuwa ƙwarai!
7Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni, Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.
8A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni, Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni.
9Don haka cike nake na murna da farin ciki, Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,
10Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba, Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.
11Za ka nuna mini hanyar rai, Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki, Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.
1Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum, Ka lura da kukana na neman taimako! Ka kasa kunne ga addu'ata, Gama ni ba mayaudari ba ne.
2Za ka shara'anta shari'ar da za ta gamshe ni, Saboda ka san abin da yake daidai.
3Ka san zuciyata, Kakan zo gare ni da dare, Ka riga ka jarraba ni sarai, Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba. Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.
4Zancen aikin sauran mutane, Na yi biyayya ga umarninka Ban bi hanyar rashin hankali ba.
5Ina tafiya a kan tafarkinka kullum, Ban kuwa kauce ba.
6Ina addu'a gare ka, ya Allah, Domin kakan amsa mini, Don haka ka juyo wurina ka kasa kunne ga maganata.
7Ka bayyana ƙaunarka mai banmamaki, Ya Mai Ceto, Muddin muna kusa da kai mun tsira daga maƙiyanmu.
8Ka kiyaye ni kamar yadda ake kiyaye idanu, Ka ɓoye ni a inuwar fikafikanka,
9Daga hare-hare na mugaye. Maƙiyana cike da ƙiyayya sun kewaye ni.
10Ba su jin tausayi, suna magana da girmankai,
11Yanzu suna kewaye da ni duk inda na juya, Suna jira su sami dama su fyaɗa ni ƙasa.
12Kamar zakoki suke nema su yayyage ni kaca-kaca, Kamar sagarun zakoki suna fakona a wurin ɓuyarsu.
13Ka zo, ya Ubangiji, Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su! Ka cece ni da takobinka daga mugaye,
14Ka cece ni daga gare su da ikonka, Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyar nan, Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu, Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su, Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!
15Zan gan ka domin ni adali ne, Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.
(2 Sam 22.1-51)
1Ina ƙaunarka ƙwarai, ya Ubangiji! Kai ne mai kāre ni.
2Ubangiji ne Mai Cetona, Shi ne garkuwata mai ƙarfi. Allahna, shi ne yake kiyaye ni, Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi, Yana kiyaye ni kamar garkuwa, Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.
3Na yi kira ga Ubangiji, Yakan cece ni daga magabtana, Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
4Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta, Hallaka ta auko mini a kai a kai.
5Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta, Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
6A shan wahalata na kira ga Ubangiji, Na yi kira ga Allahna domin neman taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
7Sai duniya ta raurawa ta girgiza, Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgiza Saboda Allah ya husata!
8Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa, Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.
9Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
10Ya sauko ta bisa bayan kerubobi, Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.
11Ya rufe kansa da duhu, Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.
12Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko Daga cikin walƙiya da take gabansa, Suka keto ta cikin gizagizai masu duhu.
13Sa'an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama, Aka ji muryar Maɗaukaki. Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.
14Ya harba kibansa, ya watsa magabtana, Da walƙiya ya kore su.
15Kashiyar teku ta bayyana, Tussan duniya sun bayyana, Sa'ad da ka tsauta wa magabtana ya Ubangiji, Sa'ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.
16Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni, Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.
17Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi, Daga kuma dukan masu ƙina, Gama sun fi ƙarfina!
18Sa'ad da nake shan wahala suka auka mini, Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
19Ya fisshe ni daga cikin hatsari, Ya cece ni, don yana jin daɗina.
20Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne, Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.
21Na yi biyayya da umarnan Ubangiji, Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.
22Na kiyaye dukan dokokinsa, Ban yi rashin biyayya da umarnansa ba.
23Ya sani ba ni da laifi, Domin na kiyaye kaina daga mugunta.
24Don haka ya sāka mini, domin ni adali ne, Gama ya sani ni marar laifi ne.
25Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci, Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.
26Kai Mai Tsarki ne ga waɗanda suke tsarkaka, Amma kana gāba da mugaye.
27Kakan ceci masu tawali'u, Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.
28Ubangiji yakan ba ni haske, Allah yakan kawar da duhuna.
29Yakan ba ni ƙarfin da zan fāɗa wa magabtana, Da ikon rinjayar kagararsu.
30Wannan Allah dai! Ayyukansa kamiltattu ne ƙwarai, Maganarsa abar dogara ce! Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinsa.
31Ubangiji shi kaɗai ne Allah, Allah ne kaɗai kāriyamu.
32Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni, Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.
33Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa. Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.
34Yakan horar da ni don yaƙi, Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.
35Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni, Na zama babban mutum saboda kana lura da ni, Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.
36Ka tsare ni, ba a kama ni ba, Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.
37Na kori magabtana, har na kama su, Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.
38Zan buge su har ƙasa, ba kuwa za su tashi ba, Za su fāɗi ƙarƙashin ƙafafuna.
39Kakan ba ni ƙarfin yin yaƙi, Kakan ba ni nasara a kan magabtana.
40Ka kori magabtana daga gare ni, Zan hallaka waɗanda suke ƙina.
41Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu, Za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba.
42Zan murƙushe su har su zama ƙura Wadda iska take kwashewa, Zan tattake su kamar caɓi a titi.
43Ka cece ni daga mutane masu tawaye, Ka naɗa ni in yi mulkin sauran al'umma, Jama'ar da ban san ta ba, ta zama abin mulkina.
44Za su yi biyayya sa'ad da suka ji ni, Baƙi za su rusuna mini,
45Za su karai, Su fita, suna rawar jiki daga kagaransu.
46Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai kāre ni! Allah ne, Mai Cetona! A yi shelar girmansa!
47Yakan ba ni nasara a kan magabtana, Yakan sa jama'a a ƙarƙashina,
48Yakan cece ni daga maƙiyana. Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,
49Don haka zan yabe ka a cikin al'ummai, Zan raira maka yabo.
50Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara. Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa, Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.
1Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah! Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!
2Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye, Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da yake biye.
3Ba magana ko kalma da aka hurta, Ba wani amon da aka ji,
4Duk da haka muryarsu ta game duniya duka, Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya. Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,
5Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa, Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.
6Takan fara daga wannan ƙarshen sararin sama, ta kewaye zuwa wancan. Ba abin da zai iya ɓuya daga zafinta.
7Dokar Ubangiji cikakkiya ce, Tana wartsakar da rai. Umarnan Ubangiji abin dogara ne, Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.
8Ka'idodin Ubangiji daidai suke, Waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi. Umarnan Ubangiji daidai suke, Sukan ba da fahimi ga zuciya.
9Daidai ne a bauta wa Ubangiji, A ci gaba da yi har abada. Duk abin da Ubangiji ya hukunta daidai ne, A kullum hukuntan Ubangiji daidai suke.
10Abin da ake so ne fiye da zinariya, I, fiye da tatacciyar zinariya ma, Sun fi zuma zaƙi, I, fiye da tatacciyar zuma ma.
11Suna ba ni ilimi, ni baranka, Ina samun ladan yin biyayya da su.
12Ba mai iya ganin kuskuren kansa, Ka cece ni daga ɓoyayyun laifofi!
13Ka tsare ni kuma daga laifofi na fili, Kada ka bari su mallake ni. Sa'an nan zan zama kamili, In kuɓuta daga mugun zunubi.
14Ka sa maganata da tunanina su zama abin karɓa a gare ka, Ya Ubangiji, Mafakata da Mai Fansata!
1Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala! Allah na Yakubu ya kiyaye ka!
2Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa, Ya kawo maka gudunmawa daga Sihiyona.
3Ya karɓi hadayunka, Ya kuma ji daɗin dukan sadakokinka.
4Ya ba ka abin da kake bukata, Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
5Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara, Mu yi bikin cin nasara da ka yi, Da yabon Ubangiji Allahnmu. Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka!
6Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa, Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki, Da ikonsa mai girma yakan sa shi ya yi nasara.
7Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara, Waɗansu kuwa ga dawakansu, Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!
8Za su yi tuntuɓe su fāɗi, Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!
9Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji, Ubangiji zai amsa mana sa'ad da muka yi kira.
1Sarki yana murna, ya Ubangiji, Domin ka ba shi ƙarfi, Yana cike da farin ciki, Don ka sa ya ci nasara.
2Ka biya masa bukatarsa, Ka amsa roƙonsa.
3Ka zo gare shi da albarka mai yawa, Ka sa kambin zinariya a kansa.
4Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo, Da yawan kwanaki.
5Darajarsa tana da girma saboda taimakonka, Ka sa ya yi suna da martaba.
6Albarkarka tana a kansa har abada, Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.
7Sarki yana dogara ga Maɗaukaki, Saboda madawwamiyar ƙaunar Ubangiji Zai zama sarki har abada.
8Sarki zai kakkama dukan magabtansa, Zai kakkama duk waɗanda suke ƙinsa.
9Ubangiji zai hallaka su kamar harshen wuta, sa'ad da ya bayyana. Ubangiji zai cinye su a cikin fushinsa, Wuta kuma za ta cinye su ƙurmus.
10Sarki zai karkashe 'ya'yansu duka, Zai yanyanke dukan zuriyarsu.
11Sun ƙulla mugayen dabaru, suna fakonsa, Amma ba za su yi nasara ba.
12Zai harba kibansa a kansu, Ya sa su juya su gudu.
13Ya Ubangiji, ka zo da ƙarfinka! Za mu raira waƙa mu yabi ikonka.
1Ya Allahna, ya Allahna, Don me ka yashe ni? Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako, Amma har yanzu ba ka zo ba!
2Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna, Amma ba ka amsa ba. Da dare kuma na yi kira, Duk da haka ban sami hutawa ba.
3Amma an naɗa ka Mai Tsarki, Wanda Isra'ila take yabonsa.
4Kakanninmu suka dogara gare ka, Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.
5Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari, Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.
6A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai, Rainanne, abin ba'a ga kowa da kowa!
7Duk wanda ya gan ni Sai ya maishe ni abin dariya, Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.
8Suke ce, “Ka dogara ga Ubangiji, Me ya sa bai cece ka ba? Idan Ubangiji na sonka, Don me bai taimake ka ba?”
9Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni, A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.
10Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka, Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.
11Kada ka yi nisa da ni! Wahala ta gabato, Ba kuwa mai taimako.
12Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai, Dukansu suna kewaye da ni, Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.
13Sun buɗe bakinsu kamar zakoki, Suna ruri, suna ta bina a guje.
14Ƙarfina ya ƙare, Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa. Dukan gaɓoɓina sun guggulle, Zuciyata ta narke kamar narkakken kākin zuma.
15Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura, Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama. Ka bar ni matacce cikin ƙura.
16Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni, Suka taso mini kamar garken karnuka, Suka soke hannuwana da ƙafafuna.
17Ana iya ganin ƙasusuwana duka. Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.
18Suka rarraba tufafina a tsakaninsu, Suka jefa kuri'a a kan babbar rigata.
19Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji! Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!
20Ka cece ni daga takobi, Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.
21Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki, Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.
22Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi, Zan yabe ka cikin taronsu.
23“Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji! Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu! Ku yi masa sujada, ku jama'ar Isra'ila!
24Ba ya ƙyale matalauta, Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu, Ba ya rabuwa da su, Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”
25Zan yabe ka a gaban babban taron jama'a Saboda abin da ka yi, A gaban sukan masu yi maka biyayya, Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.
26Matalauta za su ci yadda suke so, Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi, Su arzuta har abada!
27Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.
28Ubangiji Sarki ne, Yana mulki a kan al'ummai.
29Masu girmankai duka za su rusuna masa, 'Yan adam duka za su rusuna masa, Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.
30Zuriya masu zuwa za su bauta masa, Mutane za su ambaci Ubangiji ga zuriya mai zuwa.
31Mutanen da ba a haifa ba tukuna, za a faɗa musu, “Ubangiji ya ceci jama'arsa!”
1Ubangiji makiyayina ne, Ba zan rasa kome ba.
2Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa, Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.
3Yana ba ni sabon ƙarfi. Yana bi da ni a hanyar da yake daidai kamar yadda ya alkawarta.
4Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji, Gama kana tare da ni! Sandanka na makiyayi da kerenka Suna kiyaye lafiyata.
5Ka shirya mini liyafa Inda maƙiyana duk za su iya ganina, Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai, Ka cika tanduna fal da mai.
6Hakika, alherinka da ƙaunarka Za su kasance tare da ni muddin raina. Haikalinka zai zama gidana har abada.
1Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne, Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.
2Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa, Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.
3Wa yake da iko ya hau tudun Ubangiji? Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka>
4Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani, Wanda ba ya yi wa gumaka sujada, Ko kuma ya yi alkawarin ƙarya.
5Ubangiji zai sa masa albarka, Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.
6Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah, Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.
7A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo!
8Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!
9A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo!
10Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!
1A gare ka nake yin addu'a, ya Ubangiji,
2A gare ka nake dogara, ya Allah. Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa, Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!
3Waɗanda suke dogara gare ka, Ba za su kāsa yin nasara ba, Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.
4Ka koya mini al'amuranka, ya Ubangiji, Ka sa su zama sanannu a gare ni.
5Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka, Gama kai Mai Cetona ne. Dukan yini ina dogara a gare ka.
6Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka, Waɗanda ka nuna tun a dā.
7Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata. Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka, Ka tuna da ni, ya Ubangiji!
8Ubangiji mai adalci ne, mai alheri, Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi.
9Yana bi da masu tawali'u a tafarkin da yake daidai, Yana koya musu nufinsa.
10Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.
11Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.
12Waɗanda suke biyayya da Ubangiji Za su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.
13Kullayaumi za su arzuta, 'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.
14Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.
15A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako, Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.
16Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.
17Damuwar zuciyata ta yi yawa, Ka raba ni da dukan damuwa, Ka cece ni daga dukan wahalata.
18Ka kula da wahalata da azabata, Ka gafarta dukan zunubaina.
19Ka duba yawan magabtan da nake da su, Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini!
20Ka yi mini kāriya, ka cece ni, Gama na zo wurinka neman kāriya.
21Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni, Gama na dogara gare ka.
22Ka fanshi jama'arka daga dukan wahalarsu, ya Allah!
1Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, Gama na yi abin da yake daidai, Na dogara gare ka gaba ɗaya.
2Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, Ka gwada muradina da tunanina.
3Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni, Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.
4Ba na tarayya da mutanen banza, Ba abin da ya gama ni da masu riya.
5Ina ƙin tarayya da masu mugunta, Nakan kauce wa mugaye.
6Ya Ubangiji, na wanke hannuwana Don in nuna ba ni da laifi, Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.
7Na raira waƙar godiya, Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
8Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, Inda ɗaukakarka take zaune.
9Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi, Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,
10Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci, A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.
11Amma ni, ina yin abin da yake daidai, Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!
12Na kuɓuta daga dukan hatsarori, A taron sujada na yabi Ubangiji!
1Ubangiji ne haskena da cetona, Ba zan ji tsoron kowa ba. Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari, Ba zan ji tsoro ba.
2Sa'ad da mugaye suka tasar mini, Suna ƙoƙari su kashe ni, Za su yi tuntuɓe su fāɗi.
3Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni, Ba zan ji tsoro ba. Ko da magabtana sun tasar mini, Zan dogara ga Allah.
4Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji, Abu ɗaya kaɗai nake bukata, Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji, In yi ta al'ajabin alherinsa Dukan kwanakin raina, In roƙi biyarwarsa a can.
5A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa, Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa, Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.
6Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni. Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa! Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!
7Ka ji ni, ya Ubangiji, sa'ad da na ya yi kira gare ka! Ka yi mini jinƙai ka amsa mini!
8Ka ce, “Zo wurina,” Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,
9Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji! Kada ka yi fushi da ni, Kada kuwa ka kori bawanka. Kai ne kake taimakona, tun dā ma, Kada ka bar ni, kada ka yashe ni, Ya Allahna, Mai Cetona!
10Mai yiwuwa ne ubana da uwata su yashe ni, Amma Ubangiji zai lura da ni.
11Ka koya mini abin da ya kamata in yi, ya Ubangiji, Ka bi da ni kan lafiyyiyar hanya, Domin ina da magabta da yawa.
12Kada ka bar ni a hannun magabtana, Waɗanda suke fāɗa mini da ƙarairayi da kurari.
13Hakika zan rayu domin in ga alherin Ubangiji Da zai yi wa jama'arsa.
14Ka dogara ga Ubangiji! Ka yi imani, kada ka karai. Ka dogara ga Ubangiji!
1Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni, Ka ji kukana! In kuwa ba ka amsa mini ba, Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.
2Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako, Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.
3Kada ka kāshe ni tare da mugaye, Tare da masu aikata mugunta, Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce, Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.
4Ka hukunta su saboda abin da suka aikata. Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu, Ka ba su abin da ya cancance su!
5Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba, Ko kuma abin da ya halitta, Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.
6A yabi Ubangiji, Gama ya ji kukana na neman taimako!
7Ubangiji yakan kiyaye ni, ya tsare ni. Na dogara gare shi. Ya taimake ni, don haka ina murna, Ina raira masa waƙoƙin yabo.
8Ubangiji yana kiyaye jama'arsa, Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.
9Ka ceci jama'arka, ya Ubangiji, Ka sa wa waɗanda suke naka albarka! Ka zama makiyayinsu, Ka lura da su har abada.
1Ku yabi Ubangiji, ku alloli, Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.
2Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja, Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.
3An ji muryar Ubangiji a kan tekuna, Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.
4An ji muryar Ubangiji A dukan ikonsa da zatinsa!
5Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul, Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.
6Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa, Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.
7Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.
8Muryarsa ta sa hamada ta girgiza, Ta girgiza hamadar Kadesh.
9Muryar Ubangiji ta sa barewa ta haihu, Ta sa itatuwa su kakkaɓe, Sa'ad da aka yi sowa a cikin Haikalinsa, Aka ce, “'Daukaka ga Allah!”
10Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi, Yana sarauta kamar sarki har abada.
11Ubangiji yana ba jama'arsa ƙarfi, Ya sa musu albarka da salama.
1Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni, Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.
2Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna, Ka kuwa warƙar da ni.
3Ka dawo da ni daga lahira. Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa, Amma ka ceci raina.
4Ku raira yabo ga Ubangiji, Ku amintattun jama'arsa! Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata, Ku yi masa godiya!
5Fushinsa ba ya daɗewa, Alherinsa kuwa har matuƙa ne. Mai yiwuwa ne ya zama ana kuka da dare, Amma a yi murna da safe.
6Ina zaune jalisan, na ce wa kaina, “Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.”
7Kana yi mini alheri, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse. Amma sa'ad da ka ɓoye mini fuskarka, Sai in cika da tsoro.
8Ina kira gare ka, ya Ubangiji, Ina roƙon taimakonka.
9Wane amfani za a samu daga mutuwata? Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari? Ko matattu suna iya yabonka? Za su iya shelar madawwamin alherinka>
10Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai! Ka taimake ni, ya Ubangiji!
11Ka mai da baƙin cikina Ya zama rawar farin ciki, Ka tuɓe mini tufafin makoki, Ka sa mini na farin ciki.
12Don haka ba zan yi shiru ba, Zan raira maka yabo, Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan gode maka har abada.
1Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni. Kada ka bari a yi nasara da ni. Kai Allah mai adalci ne, Ka cece ni, ina roƙonka!
2Ka ji ni! Ka cece ni yanzu! Ka zama mafakata, don ka kiyaye ni, Ka zama mai kāre ni, don ka cece ni.
3Kai ne mafakata da kariyata, Ka bi da ni yadda ka alkawarta.
4Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina, Kai ne inuwata.
5Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni. Za ka fanshe ni, ya Ubangiji, Kai Allah mai aminci ne.
6Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada, Amma ni na dogara gare ka.
7Zan yi murna da farin ciki, Saboda madawwamiyar ƙaunarka. Ka ga wahalata, Ka kuwa san damuwata.
8Ba ka bar magabtana su kama ni ba, Ba kiyaye ni.
9Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Gama ina shan wahala, Idanuna sun gaji saboda yawan kuka, Na kuwa tafke ƙwarai!
10Baƙin ciki ya gajerta kwanakina, Kuka kuma ya rage shekaruna. Na raunana saboda yawan wahalata, Har ƙasusuwana suna zozayewa!
11Magabtana duka suna mini ba'a, Maƙwabtana sun raina ni, Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona, Sa'ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.
12Duk an manta da ni kamar matacce, Na zama kamar abin da aka jefar.
13Na ji magabtana da yawa suna raɗa, Razana ta kewaye ni! Suna ƙulla maƙarƙashiya don su kashe ni.
14Amma a gare ka na dogara, ya Ubangiji, Kai ne Allahna.
15Kana lura da ni kullum, Ka cece ni daga magabtana, Daga waɗanda suke tsananta mini.
16Ni, bawanka ne, Ka dube ni da alherinka, Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
17Ina kira gare ka, ya Ubangiji, Kada ka bari a ci nasara a kaina! Ka sa a ci nasara a kan mugaye, Ka sa su yi shiru a lahira.
18Ka rufe bakin maƙaryatan can Dukan masu girmankai da masu fāriya, Waɗanda suke wa adalai maganar raini!
19Abin al'ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka! Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma, Yana da banmamaki. Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.
20Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane, A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.
21Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Gama ya nuna mini ƙaunarsa mai ban al'ajabi, Sa'ad da aka kewaye ni, aka fāɗa mini!
22Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka. Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.
23Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama'arsa duka! Ubangiji yana kiyaye masu aminci, Amma yakan hukunta masu girmankai da tsanani.
24Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, Dukanku da kuke sa zuciya ga Ubangiji!
1Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa, Mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.
2Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba, Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.
3Sa'ad da ban hurta zunubaina ba, Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.
4Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji, Ƙarfina duka ya ƙare sarai, Kamar yadda laima take bushewa, Saboda zafin bazara.
5Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka, Ban ɓoye laifofina ba. Na ƙudurta in hurta su gare ka, Ka kuwa gafarta dukan laifofina.
6Saboda haka dukan jama'arka masu biyayya, Za su yi addu'a gare ka, lokacin bukata. Sa'ad da babbar rigyawa ta malalo, Ba za ta kai wurinsu ba.
7Kai ne maɓoyata, Za ka cece ni daga wahala. Ina raira waƙa da ƙarfi saboda cetonka, Domin ka kiyaye ni.
8Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi, Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.
9Kada ka zama wawa kamar doki ko alfadari, Wanda dole sai da linzami, da ragama za a sarrafa shi, Sa'an nan ya yi maka biyayya.”
10Tilas ne mugu ya sha wahala, Amma masu dogara ga Ubangiji, Madawwamiyar ƙaunarsa tana kiyaye su.
11Dukanku adalai, ku yi murna, Ku yi farin ciki, Saboda abin da Ubangiji ya yi! Dukanku da kuke yi masa biyayya, Ku yi sowa ta farin ciki!
1Dukanku adalai ku yi murna, A kan abin da Ubangiji ya yi, Ku yabe shi, ku da kuke masa biyayya!
2Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya. Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.
3Ku raira masa sabuwar waƙa, Ku kaɗa garaya da gwaninta, Ku kuma raira waƙa da ƙarfi!
4Kalmomin Ubangiji gaskiya ne, Ayyukansa duka kuwa abin dogara ne.
5Ubangiji yana ƙaunar abin da yake na adalci da gaskiya, Madawwamiyar ƙaunarsa ta cika duniya.
6Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa, Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa.
7Ya tattara tekuna wuri ɗaya. Ya rurrufe zurfafan teku a ɗakunan ajiya.
8Bari duk duniya ta ji tsoron Ubangiji! Ku ji tsoronsa ku mutanen duniya!
9Da magana ya halicci duniya, Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.
10Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma, Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.
11Amma shirye-shiryensa sukan tabbata har abada. Nufe-nufensa kuma dawwamammu ne har abada.
12Mai farin ciki ce al'ummar da Ubangiji yake Allahnta, Masu farin ciki ne jama'ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa!
13Daga Sama Ubangiji ya dubo dukan 'yan adam.
14Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.
15Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.
16Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba, Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.
17Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara, Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba.
18Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa, Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.
19Yakan cece su daga mutuwa, Yakan rayar da su a lokacin yunwa.
20Ga Ubangiji muke sa zuciya, Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.
21Saboda da shi muke murna, Muna dogara ga sunansa mai tsarki.
22Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji, Da yake a gare ka muke sa zuciya.
1Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin, Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.
2Zan yabe shi saboda abin da ya yi, Da ma dukan waɗanda suke da tawali'u su kasa kunne, su yi murna!
3Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni, Mu yabi sunansa tare!
4Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini, Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.
5Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna, Ba za su ƙara ɓacin rai ba.
6Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa. Ya cece su daga dukan wahalarsu.
7Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji, Ya cece su daga hatsari.
8Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri! Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!
9Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka, Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.
10Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa, Amma masu biyayya ga Ubangiji, Ba abu mai kyau da sukan rasa.
11Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni, Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.
12Kuna so ku ji daɗin rai? Kuna son tsawon rai da farin ciki>
13To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.
14Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri, Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.
15Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,
16Amma yana ƙin masu aikata mugunta, Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.
17Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.
19Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.
20Ubangiji yakan kiyaye shi sosai, Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba.
21Mugunta za ta kashe mugu, Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su.
22Ubangiji zai fanshi bayinsa, Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafaka Za a bar su da rai.
1Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji, Ka yi faɗa da masu faɗa da ni!
2Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.
3Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka, Ka yi gaba da masu fafarata. Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!
4Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su! Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!
5Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa, Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu!
6Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi, A sa'ad da mala'ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!
7Suka kafa mini tarko ba dalili, Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki.
8Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su. Tarkunan da suka kafa za su kama su, Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!
9Sa'an nan zan yi murna saboda Ubangiji, Zan yi murna, gama ya cece ni.
10Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji, “Ba wani kamarka! Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi, Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!”
11Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina, Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.
12Sun sāka mini alheri da mugunta, Cike nake da nadama.
13Amma sa'ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki, Na ƙi cin abinci, Na yi addu'a da kaina a sunkuye,
14Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan'uwa addu'a. Ina tafe a takure saboda makoki, Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.
15Sa'ad da nake shan wahala, Murna suke yi duka, Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya, Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.
16Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya, Suna hararata da ƙiyayya.
17Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu, Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!
18Sa'an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama'a. Zan yabe ka a gaban babban taro.
19Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata! Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina!
20Ba su yin maganar zumunci, A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana.
21Sukan zarge ni da kakkausan harshe, Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”
22Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan. Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji, Kada ka yi nisa!
23Ka tashi, ya Ubangiji, ka kāre ni. Ya Allah ka tashi, ka bi mini hakkina.
24Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina, Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna!
25Kada ka bar su su ce ce wa kansu, “Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!” Kada ka bar su su ce, “Mun rinjaye shi!”
26Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata, A rinjaye su, su ruɗe. Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni, Su sha kunya da wulakanci!
27Ka sa waɗanda suke murna da kuɓutata Su yi ta sowa ta murna, suna cewa, “Ubangiji mai girma ne! Yana murna da cin nasarar bawansa!”
28Sa'an nan zan yi shelar adalcinka, Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka.
1Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa, Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa.
2Domin yana ganin kansa shi wani abu ne, A tsammaninsa Allah ba zai tona asirinsa ba, Ya hukunta zunubinsa.
3Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi, Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.
4Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa, Halinsa ba shi da kyau, Ba ya ƙin abin da yake mugu.
5Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji, Ta kai har sammai, Amincinka ya kai sararin sammai.
6Adalcinka kafaffe ne, Kamar namyan duwatsu. Hukuntanka kamar teku mai zurfi suke. Ya Ubangiji, kai kake lura da mutane da dabbobi.
7Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji! Mutane sukan sami mafarka a ƙarƙashin fikafikanka.
8Sukan yi biki da yalwataccen abincin da yake Haikalinka, Kakan shayar da su daga koginka na alheri.
9Kai ne mafarin dukan rai, Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske,
10Ka yi ta ƙaunar waɗanda suka san ka, Ka yi wa adalai alheri.
11Kada ka bar masu girmankai su fāɗa mini, Kada ka bar mugaye su kore ni.
12Dubi inda mugaye suka fāɗi! Can suka kwanta, ba su iya tashi.
1Kada ka damu saboda mugaye, Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.
2Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa, Za su mutu kamar yadda tsire-tsire yake bushewa.
3Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta, Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.
4Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji, Zai kuwa biya maka bukatarka.
5Ka miƙa kanka ga Ubangiji, Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.
6Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske, Adalcinka kuma ya haskaka kamar tsakar rana.
7Ka natsu a gaban Ubangiji, Ka yi haƙuri, ka jira shi, Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya, Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.
8Kada ka yi fushi, kada ka hasala! Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.
9Waɗanda suka dogara ga Ubangiji, Za su yi zamansu lafiya a ƙasar, Amma za a kori mugaye.
10A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe, Za ka neme su, amma ba za a same su ba,
11Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, Su ji daɗin cikakkiyar salama.
12Mugu yakan yi wa mutumin kirki makarƙashiya, Yana harararsa da ƙiyayya.
13Ubangiji yana yi wa mugu dariya, Domin Ubangiji ya sani ba da daɗewa ba mugun zai hallaka.
14Mugaye sun zare takuba, Sun tanƙware bakkunansu Don su kashe matalauta da masu bukata, Su karkashe mutanen kirki.
15Amma takubansu za su sassoke su, Za a kakkarya bakkunansu.
16Ƙanƙanen abin da mutumin kirki yake da shi, Ya fi dukan dukiyar mugaye amfani,
17Gama Ubangiji zai raba mugaye da ƙarfinsu, Amma zai kiyaye mutanen kirki.
18Ubangiji yana kula da masu yi masa biyayya, Ƙasar kuwa za tama tasu har abada.
19Ba za su sha wahala a lokacin tsanani ba, Za su sami yalwa a lokacin yunwa.
20Amma mugaye za su mutu, Magabtan Ubangiji kuwa za su shuɗe kamar furen jeji, Za su ɓace kamar hayaƙi.
21Mugu yakan ci bashi, ya ƙi biya, Amma mutumin kirki mai alheri ne, Mai bayarwa hannu sake.
22Waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka, Za su zauna lafiya lau a ƙasar, Amma waɗanda ya la'anta Za a kore su su fita.
23Ubangiji yakan bi da mutum lafiya A hanyar da ya kamata ya bi, Yakan ji daɗin halinsa,
24In ya fāɗi, ba zai yi warwar ba, Gama Ubangiji zai taimake shi Ya tashi tsaye.
25Yanzu dai na tsufa, ni ba yaro ba ne, Amma ban taɓa ganin Ubangiji ya yar da mutumin kirki ba, Ko kuma a ga 'ya'yansa suna barar abinci.
26A koyaushe yakan bayar a sake, Yana ba da rance ga waɗansu, 'Ya'yansa kuwa dalilin albarka ne.
27Ka rabu da mugunta ka aikata nagarta, Za ka kuwa zauna a ƙasar har abada,
28Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai, Ba ya rabuwa da amintattun jama'arsa, Yana kiyaye su koyaushe, Amma za a kori zuriyar mugaye.
29Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar, Su gāje ta har abada.
30Kalmomin mutumin kirki suna da hikima, Yana faɗar abin da yake daidai.
31Yakan riƙe dokar Allahnsa a zuciyarsa, Ba ya kauce mata, faufau.
32Mugu yakan yi fakon mutumin kirki, Ya yi ƙoƙari ya kashe shi,
33Amma Ubangiji ba zai bar shi a hannun magabtansa ba, Ko kuwa ya bari a kāshe shi Sa'ad da ake masa shari'a.
34Ka sa zuciyarka ga Ubangiji Ka kiyaye dokokinsa, Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar, Za ka kuwa ga an kori mugaye.
35Na ga wani mugu, azzalumi, Ya fi kowa tsayi, Kamar itacen al'ul na Lebanon,
36Amma bayan ƙanƙanen lokaci, Da na zaga, ban gan shi ba, Na neme shi, amma ban same shi ba.
37Dubi mutumin kirki, ka lura da adali, Mutumin salama yakan sami zuriya,
38Amma za a hallaka masu zunubi ƙaƙaf, Za a kuma shafe zuriyarsu.
39Ubangiji yakan ceci adalai, Ya kiyaye su a lokatan wahala.
40Yakan taimake su, ya kuɓutar da su, Yakan cece su daga mugaye, Gama sukan zo wurinsa don ya kāre su.
1Kada ka yi fushi har ka tsauta mini, ya Ubangiji! Kada ka hukunta ni da fushinka!
2Ka hukunta ni, ka kuwa yi mini rauni, Ka kuma buge ni har ƙasa.
3Saboda fushinka ina ciwo mai tsanani, Duk jikina ya kamu da ciwo saboda zunubina.
4Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina, Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.
5Saboda wawancina, miyakuna sun ruɓe, suna wari,
6An tanƙware ni, an ragargaza ni, Ina ta kuka dukan yini.
7Ina fama da zazzaɓi, Ina rashin lafiya ƙwarai.
8An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina, Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.
9Ka san bukatata, ya Ubangiji, Kana jin dukan nishe-nishena.
10Zuciyata tana ɗar, ƙarfina ya ƙāre, Idanuna sun dushe.
11Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna, Har iyalina ma sun guje mini.
12Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna, Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni, Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
13Kamar kurma nake, ba na iya ji, Kamar kuma bebe, ba na iya magana.
14Ni kamar mutumin da ba ya iya amsawa nake, don ba na ji.
15Na dogara gare ka, ya Ubangiji, Kai za ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.
16Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata. Kada ka bar su su yi kirari a kan fāɗuwata!
17Ina gab da fāɗuwa, Ina cikin azaba kullum.
18Na hurta zunubaina, Sun cika ni da taraddadi.
19Magabtana lafiyayyu ne masu ƙarfi. Waɗanda suke ƙina ba dalili, suna da yawa.
20Masu rama nagarta da mugunta, Suna gāba da ni, Domin ina ƙoƙarin aikata abin da yake daidai.
21Kada ka yashe ni, ya Ubangiji, Kada ka rabu da ni, ya Allahna!
22Sai ka taimake ni yanzu, ya Ubangiji, Mai Cetona!
1Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi, Don kada harshena ya sa ni zunubi, Ba zan ce kome ba sa'ad da mugaye suke kusa.”
2Na yi shiru, ban ce kome ba, Ko a kan abin da yake da kyau! Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi,
3Zuciyata kuwa ta cika da taraddadi, Bisa ga yawan tunanina, haka yawan wahalata zai zama, Dole ne in yi ta tambaya,
4“Ya Ubangiji, kwana nawa zan yi a duniya? Yaushe zan mutu? Ka koya mini ranar da ajalina zai auko.
5“Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina! Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne. Hakika duk mutum mai rai, Bai fi shaƙar iska ba.
6Bai kuma fi inuwa ba! Duk abin da yake yi banza ne, Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!
7“A kan me zan sa zuciya, ya Ubangiji? A gare ka nake dogara.
8Ka cece ni daga dukan zunubaina, Kada ka bar wawaye su yi mini ba'a.
9Zan yi shiru, ba zan ce kome ba, Saboda ka sa na sha wahala haka.
10Kada ka ƙara hukunta ni! Na kusa mutuwa saboda bugun da kake yi mini!
11Kakan hukunta zunuban mutum ta wurin tsautawarka, Kamar yadda asu yake lalata abu. Hakika mutum bai fi shaƙar iska ba!
12“Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka kuma kasa kunne ga roƙona, Kada ka yi shiru sa'ad da na yi kuka gare ka! Yadda dukan kakannina suka yi, Ni baƙonka ne na ɗan lokaci.
13Ka ƙyale ni ko zan sami kwanciyar rai, Kafin in tafi, ai, tawa ta ƙāre.”
1Na yi ta jiran taimakon Ubangiji, Sa'an nan ya kasa kunne gare ni, ya ji kukana.
2Ya fisshe ni daga rami mai hatsari! Ya aza ni a kan dutse lafiya lau. Ya kawar mini da tsoro.
3Ya koya mini raira sabuwar waƙa, Waƙar yabon Allahnmu. Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata, Za su kuwa dogara ga Ubangiji.
4Mai farin ciki ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, Wanda bai juya ga gumaka ba, Ko ya haɗa kai da masu sujada ga allolin karya.
5Ka yi mana abubuwa masu yawa, ya Ubangiji Allahna. Ba wani kamarka! Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka, Sun fi ƙarfin in faɗa.
6Ba ka bukatar bayebaye da hadayu, Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawa Na dabbobi a bisa bagade ba, Ko bayabaye don a kawar da zunubai. A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.
7Sai na amsa, “Ga ni, umarnanka zuwa gare ni Suna a Littafin Shari'a.
8Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah! Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.”
9A taron dukan jama'arka, ya Ubangiji, Na ba da albishir na cetonka. Ka sani ba zan fasa hurta shi ba.
10Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba, Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe. Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka, Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
11Ya Ubangiji, na sani ba za ka fasa yi mini jinƙai ba! Ƙaunarka da amincinka za su kiyaye lafiyata kullum.
12Wahalai iri iri sun kewaye ni, har ba su ƙidayuwa! Alhakin zunubaina ya tarar da ni, Har ba na iya gani, Sun fi gashin kaina yawa, na karaya.
13Ka cece ni, ya Allah, Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
14Ka sa masu so su kashe ni, A ci nasara a kansu, su ruɗe! Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina Su koma baya, su sha kunya!
15Ka sa waɗanda suke mini ba'a Su razana sabili da fāɗuwarsu!
16Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka Su yi murna, su yi farin ciki! Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”
17Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki, Ya Allah, ka zo wurina da hanzari. Kai ne mataimakina da Mai Cetona, Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!
1Mai farin ciki ne wanda yake kula da matalauta, Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake shan wahala.
2Ubangiji zai kiyaye shi, ya keɓe ransa. Ubangiji zai sa ya ji daɗi a ƙasar, Ba zai bar shi a hannun magabtansa ba.
3Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake ciwo Ya mayar masa da lafiyarsa.
4Na ce, “Na yi maka zunubi, ya Ubangiji, Ka yi mini jinƙai ka warkar da ni!”
5Magabtana suna mugayen maganganu a kaina, Suna cewa, “Yaushe ne zai mutu a manta da shi?”
6Masu zuwa su gaishe ni ba da zuciya ɗaya suke zuwa ba, Sukan tattara duk mugun labari a kaina Sa'an nan su je su yi ta bazawa ko'ina.
7Maƙiyana duk suna raɗa da junansu a kaina, Sukan ɗauka na fi kowa mugunta.
8Suna cewa, “Yana ciwon ajali, Ba zai taɓa tashi daga gadonsa ba.”
9Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.
10Ka ji ƙaina ya Ubangiji, ka maido mini da lafiyata, Zan kuwa sāka wa magabtana!
11Zan sani kana jin daɗina, Domin ba za su rinjaye ni ba,
12Za ka taimake ni domin ina yin abin da yake daidai, Za ka sa ni a gabanka har abada.
13Bari mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila. Ku yabe shi yanzu da har abada! Amin! Amin!
LITTAFI NA BIYU: Kewar Allah a Baƙuwar Ƙasa (Zabura ta 42-72)
1Kamar yadda kishimi yake marmarin ruwan sanyi daga rafi, Haka nake marmarinka, ya Allah.
2Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai, Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka>
3Dare da rana ina kuka, Hawayena kaɗai su ne abincina, A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata, “Ina Allahnka?”
4Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.
5Me ya sa nake baƙin ciki haka? Me ya sa nake damuwa ƙwarai? Zan dogara ga Allah, Zan sāke yin yabonsa, Mai Cetona, Allahna.
6Zuciyata ta karai Saboda haka zan tuna da kai A wajen Urdun, da kusa da Dutsen Harmon, da na Mizar, Zan tuna da kai.
7Zurfafan tekuna suna kiran junansu, Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri! Igiyoyin ruwa na baƙin ciki Suka yi wa raina ambaliya.
8Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana! Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare, In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.
9Ga Allah wanda yake tsarona yana ce, “Me ya sa ka manta da ni? Me ya sa nake ta shan wahala Saboda muguntar maƙiyana?”
10An ragargaza ni da zargin maƙiyana Waɗanda suke tambayata kullum, “Ina Allahnka?”
11Me ya sa ni ɓacin rai haka? Me ya sa ni damuwa? Zan dogara ga Allah. Har yanzu ma zan yabe shi, Mai Cetona, Allahna.
1Ya Allah, ka kuɓutar da ni, Ka kiyaye al'amarina daga marasa tsoronka, Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!
2Ya Allah, kai ne kake kāre ni, Me ya sa ka yashe ni? Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana>
3Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka, Bari su bishe ni, Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka, Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!
4Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah, Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki, In raira waƙar yabo a gare ka da garayata, Ya Allah, Allahna!
5Me ya sa nake baƙin ciki? Me ya sa nake damuwa? Zan dogara ga Allah, Zan ƙara yabonsa, Mai Cetona, Allahna.
1Da kunnuwanmu muka ji, ya Allah, Kakanninmu suka faɗa mana, Manya manyan abubuwa da ka aikata a lokacinsu, A zamanin dā,
2Yadda kai da kanka ka kori arna, Ka dasa jama'arka a ƙasaru, Yadda ka hori sauran al'umma, Amma ka sa jama'arka su wadata.
3Ba da takubansu suka ci ƙasar ba, Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba, Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka, Ta wurin tabbatar musu kana tare da su, Kana nuna musu kana ƙaunarsu. 4“Ya Allah, kai ne Sarkina, Ka ba jama'arka nasara.
5Da ikonka muka kori abokan gābanmu, Saboda kasancewarka tare da mu Muka rinjayi magabtanmu.
6Ban dogara ga bakana ba, Takobina kuwa ba zai cece ni ba.
7Amma ka cece mu daga abokan gābanmu, Ka kori waɗanda suke ƙinmu.
8Za mu yabe ka kullum, Mu yi maka godiya har abada.”
9Amma yanzu, ya Allah, ka yashe mu, Ka bari aka kore mu, Ba ka ƙara fita ka yi tafiya tare da sojojinmu ba.
10Ka sa muka gudu daga gaban abokan gābanmu, Suka ƙwace abin da muke da shi.
11Ka bari aka yanyanka mu kamar tumaki, Ka warwatsar da mu a baƙuwar ƙasa.
12Ka sayar da jama'arka A bakin 'yan kuɗi ƙalilan, Ba ka ci ribar cinikin ba.
13Maƙwabtanmu suna yi mana dariya saboda kai, Suna yi mana ba'a, sun maishe mu abin wasa.
14Ka maishe mu abin raini a wurin arna, Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.
15Kullum a cikin kunya nake, Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,
16Saboda dukan wulakanci, Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.
17Dukan wannan ya same mu, Ko da yake ba mu manta da kai ba, Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.
18Ba mu ci amanarka ba, Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.
19Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan, Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.
20Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu, Muka yi addu'a ga gumaka,
21Hakika ka gane, Domin ka san asirin tunanin mutane.
22Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci, Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.
23Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci? Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!
24Me ya sa ka ɓuya mana? Kada ka manta da ƙuncinmu da wahalarmu!
25Mun fāɗi, an turmushe mu a ƙasa, An bar mu kwance cikin ƙura.
26Ka tashi ka taimake mu! Ka fanshe mu saboda madawwamiyar ƙaunarka!
1Kwanyata ta cika da kyawawan kalmomi, Lokacin da nake tsara waƙar sarki, Harshena kuwa kamar alkalami ne na ƙwararren marubuci.
2Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane, Kai mai kyakkyawan lafazi ne, Kullum Allah yakan sa maka albarka!
3Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki, Kai mai iko ne, Maɗaukaki!
4Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara, Domin ka tsare gaskiya da adalci. Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.
5Kibanka suna da tsini, Suna huda zuciyar abokan gābanka, Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.
6Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin! Kana mulkin mallakarka da adalci.
7Kana ƙaunar abin da yake daidai, Kana ƙin abin da yake mugu. Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka, Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.
8Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na al'ul, da na kashiya, A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.
9Daga cikin matan da suke fādarka, har da 'ya'yan sarakuna. A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye. Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.
10Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki, Ki manta da mutanenki da danginki.
11Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki, Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.
12Mutanen Taya za su kawo miki kyautai, Attajirai za su zo su sami farin jini a gare ki.
13Gimbiya tana fāda, kyakkyawa ce ainun, Da zaren zinariya aka saƙa rigarta,
14Aka kai ta wurin sarki tana saye da riga mai ado. Ga 'yan matanta a biye, Aka kawo su wurin sarki.
15Da farin ciki da murna suka zo, Suka shiga fādar sarki.
16Za ka haifi 'ya'ya maza da yawa, Waɗanda za su maye matsayin kakanninka, Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.
17Waƙata za ta sa a yi ta tunawa da sunanka har abada, Dukan jama'a za su yabe ka a dukan zamanai masu zuwa.
1Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake ya yi taimako a lokacin wahala.
2Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, Ko da duniya za ta girgiza, Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,
3Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa, Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.
4Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah, Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.
5Allah yana zaune cikin birnin, Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau. Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.
6An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza, Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.
7Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!
8Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi! Dubi irin ayyukan al'ajabi da ya yi a duniya!
9Ya hana yaƙoƙi ko'ina a duniya, Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu, Yana ƙone karusai da wuta.
10Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!”
11Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!
1Ku yi tāfi saboda farin ciki, Ya ku jama'a duka! Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!
2A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka, Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.
3Ya ba mu nasara a bisa jama'o'i, Ya sa muka yi mulkin al'ummai,
4Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune, Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama'arsa Wadda yake ƙauna.
5Allah ya hau kan kursiyinsa! Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni, Lokacin da Ubangiji yake hawa!
6Ku raira yabbai ga Allah, Ku raira yabbai ga sarkinmu!
7Allah sarki ne na duniya duka, Ku yabe shi da waƙoƙi!
8Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki, Yana mulkin al'ummai,
9Masu mulkin al'ummai suka tattaru Tare da jama'ar Allah na Ibrahim. Allah shi ne garkuwar jarumawa, Yana mulkin duka!
1Ubangiji mai girma ne, Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu, A kan tsattsarkan dutsensa.
2Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo, Mai kyan gani ne na Allah, Birnin babban Sarki. Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!
3Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa, A kagarar birnin.
4Sarakuna suka tattaru, Suka zo Dutsen Sihiyona,
5Da suka gan shi sai suka yi mamaki, Suka tsorata suka gudu.
6Tsoro ya kama su suka razana, Kamar mace wadda take gab da haihuwa.
7Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.
8Mun ji labarin waɗannan al'amura, Yanzu kuwa mun gan su A birnin Allahnmu, Mai Runduna, Zai kiyaye birnin lafiya har abada.
9A cikin Haikalinka, ya Allah, Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.
10A ko'ina jama'a suna yabonka, Sunanka ya game duniya duka. Kana mulki da adalci.
11Bari jama'ar Sihiyona su yi murna! Gama kana shari'a ta gaskiya, Bari biranen Yahuza su yi farin ciki.
12Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona, Ku ƙirga yawan hasumiyarsa.
13Ku lura da garukanta, ku bincike kagaranta, Saboda ku iya faɗa wa tsara mai zuwa,
14Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin, Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa.
1Ku ji wannan, ko wannenku, Ku saurara jama'a duka na ko'ina,
2Da manya da ƙanana duka ɗaya, Da attajirai da matalauta baki ɗaya.
3Zan yi magana da hikima, Zan yi tunani mai ma'ana.
4Zan mai da hankalina ga ka-cici-ka-cici, In bayyana ma'anarsa sa'ad da nake kaɗa molo.
5Don me zan ji tsoro a lokacin hatsari, Sa'ad da mugaye suka kewaye ni,
6Mutanen da suke dogara ga dukiyarsu, Waɗanda suke fāriya saboda yawan wadatarsu>
7Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba, Ba kuwa zai iya biyan kuɗin ransa ga Allah ba.
8Gama kuɗin biyan ran mutum ba shi da iyaka. Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba,
9Ba kuwa zai rayar da shi, Ko ya hana shi mutuwa har abada ba.
10Yakan sa masu hikima su ma su mutu, Hakanan ma wawaye da mutanen banza, Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu.
11Kaburburansu za su zama gidajensu har abada, Can za su kasance kullum, Ko da yake a dā suna da ƙasa ta kansu.
12Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba, Zai mutu kamar dabba.
13Dubi abin da zai faru ga waɗanda suke dogara ga kansu, Da irin ƙaddarar waɗanda dukiya ta ishe su.
14Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki, Mutuwa ce za ta yi kiwonsu. Da safe adalai za su ci nasara a kansu, Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu, Nesa da gidajensu.
15Amma Allah zai fanshe ni, Zai ɗauke ni daga ikon mutuwa.
16Kada ka damu sa'ad da mutum ya zama attajiri, Ko kuwa dukiyarsa ta ƙasaita,
17Domin ba zai ɗauke ta a lokacin mutuwarsa ba, Dukiyarsa ba za ta shiga kabari tare da shi ba.
18Ko da a ce mutum ya sami falalar wannan rai, Ana kuwa ta yabonsa saboda nasarar da ya ci,
19Duk da haka zai tarar da kakanninsa waɗanda suka mutu, Inda duhu ya dawwama har abada.
20Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba, Zai mutu kamar dabba.
1Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana, Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.
2Allah yana haskakawa daga Sihiyona, Da cikar jamalin Sihiyona.
3Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba, Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.
4Ya kira sammai da duniya su zama shaidu, Su ga yadda yake shara'anta jama'arsa.
5Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna, Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su, Ta wurin miƙa hadaya.”
6Sammai suna shelar adalcin Allah, Domin shi yake yin shari'a!
7“Ku ji, ya ku jama'ata, zan kuwa yi magana, Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra'ila. Ni ne Allah, Allahnku.
8Ban tsauta muku saboda hadayunku ba, Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.
9Ba na bukatar bijimai daga gonakinku, Ko awaki daga garkunanku.
10Gama namomin jeji nawa ne, Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.
11Dukan tsuntsayen da suke tashi a sararin sama nawa ne, Da dukan masu rai da suke ƙasa.
12“Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba, Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.
13Nakan ci naman bijimai ne? Ko nakan sha jinin awaki>
14Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya, Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.
15Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”
16Amma Allah ya ce wa mugaye, “Don me za ku haddace umarnaina? Don me za ku yi magana a kan alkawaraina>
17Kun ƙi in tsauta muku, Kun yi watsi da umarnaina.
18Sa'ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi. Kuna haɗa kai da mazinata.
19“Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta, Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.
20A shirye kuke ku sari 'yan'uwanku, Ku sa musu laifi.
21Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba, Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake. Amma yanzu zan tsauta muku, In bayyana muku al'amarin a fili.
22“Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni, In ba haka ba zan hallaka ku, Ba wanda zai cece ku.
23Wanda yake yin godiya a sa'ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni, Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”
1Ka yi mini jinƙai, ya Allah, Sabili da madawwamiyar ƙaunarka. Ka shafe zunubaina, Saboda jinƙanka mai girma!
2Ka wanke muguntata sarai, Ka tsarkake ni daga zunubina!
3Na gane laifina, Kullum ina sane da zunubina.
4Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa, Na kuwa aikata mugunta a gare ka. Daidai ne shari'ar da ka yi mini, Daidai ne ka hukunta ni.
5Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni, Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.
6Amintacciyar zuciya ita kake so, Ka cika tunanina da hikimarka.
7Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka, Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.
8Bari in ji sowa ta farin ciki da murna. Ko da yake ka ragargaza ni, Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.
9Ka kawar da fuskarka daga zunubaina, Ka shafe duk muguntata.
10Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah, Ka sa sabon halin biyayya a cikina.
11Kada ka kore ni daga gabanka, Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.
12Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka, Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.
13Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka, Za su kuwa komo wurinka.
14Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona, Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.
15Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji, Zan kuwa yabe ka.
16Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka, Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah, Zuciya mai ladabi da biyayya, Ba za ka ƙi ba, ya Allah.
18Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta, Ka sāke gina garun Urushalima.
19Sa'an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi, Da dukan hadayun ƙonawa. Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.
1Me ya sa kake fāriya da muguntarka, Ya kai, babban mutum? Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.
2Kana shirya maƙarƙashiya don ka lalatar da waɗansu, Harshenka kamar aska mai kaifi yake. Kana ƙirƙiro ƙarairayi kullum.
3Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta, Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya.
4Kana jin daɗin cutar mutane da maganganunka, Ya kai, maƙaryaci!
5Don haka Allah zai ɓata ka har abada, Zai kama ka, ya jawo ka daga alfarwarka, Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai.
6Adalai za su ga wannan, su ji tsoro, Za su yi maka dariya, su ce,
7“Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah Don ya sami zaman lafiyarsa ba. A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa. Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”
8Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah, Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.
9Zan gode maka, ya Ubangiji, Saboda abin da ka aikata. Zan dogara gare ka, Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka, Domin kai mai alheri ne.
(Zab 14.1-7)
1Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah.” Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.
2Daga Sama Allah ya dubi mutane, Ya ga ko akwai masu hikima Waɗanda suke yi masa sujada.
3Amma dukansu sun koma baya, Su duka mugaye ne, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai, Babu ko ɗaya.
4Allah ya ce, “Ashe, ba su sani ba? Ashe, mugayen nan jahilai ne? Ta wurin yi wa jama'arta fashi suke rayuwa, Ba sa yin addu'a gare ni.”
5Amma sa'an nan za su firgita ƙwarai, Irin yadda ba su taɓa yi ba, Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka. Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su.
6Dā ma ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona! Sa'ad da Allah ya sāke arzuta jama'arsa, Zuriyar Yakubu za ta yi farin ciki, Jama'ar Isra'ila kuwa za ta yi murna.
1Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah, Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!
2Ka ji addu'ata, ya Allah, Ka saurari kalmomina!
3Masu girmankai sun tasar mini, Mugaye suna nema su kashe ni, Mutanen da ba su kula da Allah ba.
4Na sani Allah ne mai taimakona, Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!
5Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu! Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.
6Da murna zan miƙa maka hadaya, Zan yi maka godiya, ya Ubangiji, Domin kai mai alheri ne.
7Ka cece ni daga dukan wahalaina, Na kuwa ga an kori maƙiyana.
1Ka ji addu'ata, ya Allah, Kada ka ƙi jin roƙona!
2Ka saurare ni, ka amsa mini, Gama damuwata ta gajiyar da ni tiƙis.
3Hankalina ya tashi saboda yawan kurarin maƙiyana, Saboda danniyar mugaye. Sukan jawo mini wahala, Suna jin haushina suna ƙina.
4Azaba ta cika zuciyata, Tsorace-tsoracen mutuwa sun yi mini nauyi.
5Tsoro da rawar jiki sun kama ni, Na cika da razana.
6Na ce, “Da a ce ina da fikafikai kamar kurciya, Da sai in tashi, in tafi, in nemi wurin hutawa!
7In tafi can nesa, In yi wurin zamana a hamada.
8Zan hanzarta in nemi mafaka Daga iska mai ƙarfi da hadiri.”
9Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.
10Dare da rana suna ta yawo a kan garu suna ta kewaye birnin, Birnin kuwa cike yake da laifi da wahala.
11Akwai hallaka a ko'ina, Tituna suna cike da azzalumai da 'yan danfara.
12Da a ce maƙiyina ne yake mini ba'a, Da sai in jure. Da a ce abokin gābana ne yake shugabancina, Da sai in ɓuya masa.
13Amma kai ne, aminina, Abokin aikina ne, abokina ne kuma!
14Dā mukan yi taɗi da juna ƙwarai, Mukan tafi Haikali tare da sauran jama'a.
15Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari, Allah ya sa su gangara ƙasar matattu da ransu! Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.
16Amma ina kira ga Allah, ya taimake ni, Ubangiji kuwa zai cece ni.
17Koke-kokena da nishe-nishena Suna hawa zuwa gare shi da safe, da tsakar rana, da dad dare, Zai kuwa ji muryata.
18Zai fisshe ni lafiya Daga yaƙe-yaken da nakan yi da magabtana masu yawa.
19Allah, shi wanda yake mulki tun fil azal, Zai ji ni, zai kore su. Ba abin da suka iya yi a kai, Domin ba su tsoron Allah.
20Abokina na dā, Ya yi wa abokansa faɗa, Ya ta da alkawarinsa.
21Kalmominsa sun fi mai taushi, Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa, Kalmominsa sun fi mai sulɓi, Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.
22Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, Zai kuwa taimake ka, Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.
23Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.
1Ka yi mini jinƙai, ya Allah, Gama mutane sun tasar mini, Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe!
2Dukan yini maƙiyana suna tasar mini, Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.
3Sa'ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki, A gare ka nake dogara.
4Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa, Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba. Me mutum kawai zai yi mini>
5Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini, A kan kowane abu da nake yi, Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!
6Sukan taru a ɓoye, Suna kallon duk abin da nake yi. Suna sa zuciya za su iya kashe ni.
7Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu, Da fushinka ka kori waɗannan mutane!
8Ka san irin wahalar da nake sha, Kana riƙe da lissafin yawan hawayena. Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba>
9A ranar da na yi kira gare ka, Za a komar da abokan gābana baya, Gama na sani Allah yana tare da ni!
10Ina dogara ga Allah, ina yabon alkawarinsa, Ina dogara ga Ubangiji, ina yabon alkawarinsa.
11A gare shi nake dogara, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum kawai zai yi mini>
12Zan miƙa maka abin da na yi alkawari, ya Allah, Zan miƙa maka hadaya ta godiya.
13Domin ka cece ni daga mutuwa, Ka hana a ci nasara a kaina. Saboda haka a gaban Allah nake tafiya A hasken da yake haskaka wa masu rai.
(Zab 108.1-5)
1Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai, Gama na zo gare ka neman tsira. Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka, Sai dukan hatsari ya wuce.
2Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki, Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
3Daga sammai Allah zai amsa mini, Zai kori waɗanda suka tasar mini, Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.
4Raina yana tsakiyar zakoki, Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane. Haƙoransu kamar māsu da kibau suke, Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.
5Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni, Damuwa ta fi ƙarfina. Sun yi wushefe a kan hanyata, Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.
7A shirye nake, ya Allah, Na shirya sosai! Zan raira waƙoƙi in yabe ka!
8Ka farka, ya raina! Ku farka, molona da garayata! Zan sa rana ta farka!
9Zan gode maka a cikin sauran al'umma, ya Ubangiji! Zan yabe ka a cikin jama'a!
10Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai, Amincinka kuma har sararin sammai.
11Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
1Hakika za ku yanka daidai, ku manya? Za ku shara'anta wa mutane daidai>
2A'a, tunanin muguntar da za ku aikata kaɗai kuke yi, Kuna aikata laifofin ta da hargitsi a ƙasar.
3Mugaye, laifi suke yi dukan kwanakinsu, Tun daga ranar da aka haife su suke ta faɗar ƙarya.
4Cike suke da dafi kamar macizai, Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa,
5Wanda ba ya jin muryar gardi, Ko kuma waƙar gwanin sihiri.
6Ka kakkarya haƙoransu, ya Allah, Ka ciccire fiƙoƙin waɗannan zakoki masu zafin rai, ya Ubangiji!
7Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye, Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya.
8Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi, Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce. Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.
9Kafin tukunya ta ji zafin wuta, Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai.
10Adalai za su yi murna sa'ad da suka ga an hukunta masu zunubi, Za su wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
11Mutane za su ce, “Hakika an sāka wa adalai, Hakika akwai Allah wanda yake shara'anta duniya!”
1Ka cece ni daga maƙiyana, ya Allahna, Ka kiyaye ni daga waɗanda suka tasar mini!
2Ka cece ni daga waɗannan mugaye, Ka tsirar da ni daga masu kisankan nan!
3Duba! Suna jira su auka mini, Mugaye suna taruwa gāba da ni, Ba domin wani zunubi ko wani laifin da na yi ba,
4Ba domin na yi wani laifi ba, ya Ubangiji, Har da suka gaggauta gāba da ni. Kai da kanka ka gani, ya Allah na Isra'ila! Ka tashi ka taimake ni.
5Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni, Ka tashi ka hukunta al'ummai, Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!
6Da maraice suka komo, Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.
7Ji abin da suke fada! Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu, Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
8Amma kai dariya kake yi musu, ya Ubangiji, Ka mai da al'ummai duka abin bandariya!
9Mai tsarona, kai ne kake kiyaye ni, Kai ne mafakata, ya Allah.
10Allahna wanda yake ƙaunata, zai zo gare ni, Zai sa in ga an kori magabtana.
11Kada ka kashe su, ya Allah, don kada jama'ata su manta. Ka watsar da su da ikonka, ka hallaka su ya Ubangiji mai kiyaye mu!
12Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne, Da ma a kama su saboda girmankansu, Domin suna la'antarwa, suna ƙarya!
13Da fushinka ka hallaka su, Ka hallaka su ɗungum. Sa'an nan jama'a za su sani Allah yana mulkin Isra'ila, Mulkinsa ya kai ko'ina a duniya!
14Da maraice maƙiyana suka komo, Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.
15Suna kai da kawowa ko'ina neman abinci, In ba su sami abin da ya ishe su ba, Sukan yi gunaguni.
16Amma zan raira waƙa a kan ikonka, Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfi Ga zancen madawwamiyar ƙaunarka. Kai mafaka ne a gare ni, Wurin ɓuya a kwanakin wahala.
17Zan yabe ka, mai tsarona, Allah ne mafakata, Allah wanda ya ƙaunace ni.
(Zab 108.6-13)
1Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu, Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!
2Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta. Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!
3Ka sa jama'arka su sha wahala ƙwarai, Ka ba mu ruwan inabin da ya bugar da mu.
4Ka ta da tuta ga masu tsoronka, Domin su juya su gudu daga abokin gāba.
5Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata, Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.
6A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce, “Da nasara zan raba Shekem, Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.
7Gilyad tawa ce, har da Manassa ma, Ifraimu ne kwalkwalina, Yahuza kuma sandana ne na sarauta.
8Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki, Edom kuwa kamar akwatin takalmina. Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”
9Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara? Wa zai kai ni Edom>
10Da gaske ka yashe mu ke nan? Ba za ka yi tafiya tare da sojojinmu ba>
11Ka taimake mu, mu yaƙi abokan gāba, Domin taimako irin na mutum banza ne!
12Idan Allah yana wajenmu, Za mu yi nasara, Zai kori abokan gābanmu.
1Ya Allah, ka ji kukana, Ka ji addu'ata!
2Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai, Zan yi kira gare ka! Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.
3Kai ne kāriyata mai ƙarfi Da take kiyaye ni daga maƙiyana.
4Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina, Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka.
5Ya Allah, kā ji alkawaraina, Kā kuwa ba ni abin da ya dace, Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka.
6Ka ƙara wa sarki tsawon rai, Ka sa ya rayu dukan lokaci!
7Ka sa ya yi mulki har abada a gabanka, ya Allah, Ka tsare shi da madawwamiyar ƙaunarka, da amincinka.
8Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin, A sa'ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta.
1Ga Allah kaɗai na dogara, Cetona daga gare shi yake fitowa.
2Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
3Har yaushe dukanku za ku fāɗa wa wani don ku yi nasara da shi, Kamar rusasshen garu, Ko kuma dangar da ta fāɗi>
4Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja, Kuna jin daɗin yin ƙarairayi. Kuna sa masa albarka, Amma a zuciyarku la'antarwa kuke yi.
5Ga Allah kaɗai na dogara, A gare shi na sa zuciyata.
6Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
7Cetona da darajata daga Allah ne, Shi ne ƙaƙƙarfan makiyayina, Shi ne mafakata.
8Ya jama'ata, ku dogara ya Allah a kowane lokaci! Ku faɗa masa dukan wahalarku, Gama shi ne mafakarmu.
9Talakawa kamar shaƙar numfashi suke, Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma'auni, sam ba su da nauyin kome, Sun fi numfashi shakaf.
10Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar kome ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta ƙaru, Kada ku dogara gare ta.
11Sau ɗaya Allah ya faɗa, Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.
12Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka wa Kowane mutum bisa ga ayyukansa.
1Ya Allah, kai ne Allahna, Ina sa zuciya gare ka. Duk niyyata ta nemanka ce, Raina yana ƙishinka, Kamar bussasshiyar ƙasa, Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.
2Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka, In dubi ɗaukakarka da darajarka.
3Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa, Saboda wannan zan yabe ka.
4Muddin raina, zan yi maka godiya, Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.
5Raina zai yi liyafa, ya ƙoshi sosai, Ni kuwa zan raira waƙoƙin murna na yabo a gare ka.
6Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai, Dare farai ina ta tunawa da kai,
7Domin kai kake taimakonka kullayaumin. Da murna, nake raira waƙa, A inuwar fikafikanka,
8Raina yana manne maka, Ikonka yana riƙe da ni.
9Waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, Za su gangara zuwa lahira,
10Za a kashe su cikin yaƙi, Kyarketai kuwa za su cinye gawawwakinsu.
11Sarki zai yi farin ciki ga Allah, Duk waɗanda suka yi alkawarai da sunan Allah Za su yi murna, Amma za a rufe bakunan maƙaryata.
1Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata! Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!
2Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, Da iskancin mugayen mutane.
3Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
4Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau, Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.
5Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu, Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu. “Ba wanda zai ga mu,” in ji su.
6Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce, “Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa!
7Amma Allah zai harbe su da kibansa, Za a yi musu rauni nan da nan.
8Zai hallaka su saboda maganganunsu, Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.
9Dukansu za su ji tsoro, Za su faɗi abin da Allah ya aikata, Su yi tunani a kan ayyukansa.
10Dukan masu adalci za su yi murna, Saboda abin da Ubangiji ya aikata. Za su sami mafaka a gare shi, Dukan mutanen kirki za su yabe shi.
1Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona, Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.
2Saboda kakan amsa addu'o'i, Dukan mutane za su zo wurinka.
3Zunubanmu sun kāshe mu, Amma za ka gafarta zunubanmu.
4Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe su Su zauna a tsattsarkan wurinka! Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka, Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!
5Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu, Ka kuma cece mu ta wurin aikata al'amuran banmamaki. Mutane daga ko'ina a duniya, Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna, Sun dogara gare ka.
6Ka kakkafa duwatsu ta wurin ikonka, Ka bayyana ƙarfin ikonka.
7Kakan kwantar da rurin tekuna, Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa, Kakan kwantar da tarzomar jama'a.
8Dukan duniya ta tsorata, Saboda manyan ayyuka da ka aikata. Ayyukanka sukan kawo sowa ta farin ciki Daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.
9Kakan nuna kana kulawa da ƙasar, Ta wurin aiko mata da ruwa. Ka arzuta ta, ta zama dausayi. Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba, Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki, Abubuwan da ka aikata ke nan.
10Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome, Ka jiƙe su da ruwa, Ka tausasa ƙasar da yayyafi, Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.
11Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka! Inda ka tafi duka akwai wadata!
12Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba, Tuddai kuma suna cike da farin ciki.
13Sauruka suna cike da tumaki, Kwaruruka suna cike da alkama, Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!
1Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki, Ya jama'a duka!
2Ku raira waƙar darajar sunansa, Ku yabe shi da ɗaukaka!
3Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawa Suna da banmamaki ƙwarai! Ikonka yana da girma ƙwarai, Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.
4Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada, Yana raira maka waƙar yabbai, Yana raira yabbai ga sunanka.”
5Zo, ka ga abin da Allah ya yi, Ayyukansa masu ban al'ajabi Waɗanda ya aikata ga mutane.
6Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa, Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa. A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.
7Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa, Yana duban al'ummai, Don kada 'yan tawaye su tayar masa!
8Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al'ummai, Bari a ji yabon da kuke yi masa.
9Shi ne yake rayar da mu, Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.
10Ka jarraba mu, ya Allah, Kamar yadda ake tace azurfa da wuta, Hakanan ka jarraba mu.
11Ka bar mu muka fāɗa a tarko, Ka ɗora mana kaya masu nauyi.
12Ka bar maƙiyanmu suka tattaka mu, Mun ratsa ta cikin wuta da rigyawa, Amma yanzu ka kawo mu a lafiyayyen wuri.
13Zan kawo hadayun ƙonawa a ɗakinka, Zan miƙa maka abin da na alkawarta.
14Zan ba ka abin da na ce zan bayar, A lokacin da nake shan wahala.
15Zan miƙa tumaki don a ƙona a kan bagade, Nan za a ji ƙanshi mai daɗi na ƙonannun awaki, Zan miƙa hadayu na bijimai da na awaki.
16Ku zo ku ji, dukanku, ku da kuke girmama Allah, Ni kuwa zan faɗa muku abin da ya yi mini.
17Na yi kira gare shi neman taimako, A shirye nake in yabe shi da waƙoƙi.
18Da ban watsar da zunubaina ba, Da Ubangiji bai ji ni ba.
19Amma hakika Allah ya ji ni, Ya saurari addu'ata.
20Ina yabon Allah, Domin bai ƙi addu'ata ba, Bai kuwa hana mini madawwamiyar ƙaunarsa ba.
1Ka yi mana jinƙai, ya Allah, ka sa mana albarka, Ka dube mu da idon rahama,
2Domin dukan duniya ta san nufinka, Dukan sauran al'umma kuma su san cetonka.
3Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah, Da ma dukan mutane su yabe ka!
4Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki, Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci, Kana kuma bi da dukan sauran al'umma.
5Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah, Da ma dukan mutane su yabe ka!
6Ƙasa ta ba da amfaninta, Allah, wanda yake Allahnmu ne, ya sa mana albarka.
7Allah ya sa mana albarka, Da ma dukan jama'a ko'ina su girmama shi.
1Da ma Allah ya tashi ya warwatsa maƙiyansa! Da ma su waɗanda suke ƙinsa su gudu!
2Kamar yadda iska take korar hayaƙi, Hakanan zai kore su, Kamar yadda kākin zuma yakan narke a gaban wuta, Hakanan mugaye za su hallaka a gaban Allah.
3Amma adalai za su yi murna, Su kuma yi farin ciki a gaban Allah, Za su yi murna ƙwarai da gaske.
4Ku raira waƙa ga Allah, Ku raira waƙar yabo ga sunansa, Ku yi hanya ga wanda yake ratsa gizagizai. Sunansa kuwa Ubangiji ne, ku yi murna a gabansa!
5Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa, Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye, Wato matan da mazansu suka mutu.
6Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki, Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi, Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.
7Sa'ad da ka bi da jama'arka, ya Allah, Sa'ad da ka yi tafiya a hamada,
8Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa, Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza, Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.
9Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah, Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.
10Jama'arka suka gina gidajensu a can, Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.
11Ubangiji ya ba da umarni, Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,
12“Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu! Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”
13Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa, Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya.
(Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)
14Sa'ad da Allah Mai Iko Dukka Ya warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon, Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.
15Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan? Tulluwarka nawa, dutsen Bashan>
16Me ya sa, daga manyan kawunanka Kake yi wa dutsen da Allah ya zaɓa Ya zauna a kai, duban raini? A nan Ubangiji zai zauna har abada!
17Daga Sinai da dubban manyan karusansa, Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.
18Ya hau kan tsaunuka Tare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi, Yana karɓar kyautai daga wurin mutane, Daga wurin 'yan tawaye kuma. Ubangiji Allah zai zauna a can.
19Ku yabi Ubangiji, Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum, Shi ne Allah wanda ya cece mu.
20Allahnmu, Allah Mai Ceto ne, Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu, Wanda yake cetonmu daga mutuwa.
21Hakika Allah zai farfashe kawunan abokan gābansa, Da na waɗanda suka nace bin hanyoyinsu na zunubi.
22Ubangiji ya ce, “Zan komo da su daga Bashan, Zan komo da su daga zurfin teku,
23Don ku wanke sawayenku a cikin jinin maƙiyanku, Karnukanku kuwa za su lashe iyakar abin da suke so.”
24Ya Allah, jama'a duka sun ga irin tafiyarka ta nasara, Irin tafiyar Allah, Sarkina, zuwa tsattsarkan wurinsa.
25Mawaƙa suna kan gaba, mabusa suna biye, A tsakiya kuwa 'yan mata suna kaɗa bandiri.
26“Ku jama'ar Allah, ku yabe shi cikin taronku, Ku yabi Ubangiji, dukanku, ku zuriyar Isra'ila!”
27Ga Biliyaminu mafi ƙanƙanta Cikin kabilai, a kan gaba, Sa'an nan shugabannin Yahuza da ƙungiyarsu, Daganan sai shugabannin Zabaluna da na Naftali suna biye da su.
28Ka nuna ikonka, ya Allah, Ikon nan da ka nuna saboda mu.
29Daga Haikalinka a Urushalima, Sarakuna sukan kawo maka kyautai.
30Ka tsauta wa Masar, naman jejin nan Mai zafin hali da yake cikin iwa, Ka tsauta wa sauran al'umma, taron bijiman nan da 'yan maruƙansu, Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu. Ka warwatsar da jama'ar nan Masu son yin yaƙi!
31Wakilai za su zo daga Masar, Habashawa za su miƙa hannuwansu sama, Su yi addu'a ga Allah.
32Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya, Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,
33Shi wanda ya hau cikin sararin sama, Daɗaɗɗen sararin sama! Ku kasa kunne ga muryarsa mai ƙarfi!
34Ku yi shelar ikon Allah, Ɗaukakarsa tana bisa kan Isra'ila, Ikonsa yana cikin sararin sama.
35Allah al'ajabi ne a tsattsarkan wurinsa, Allah na Isra'ila! Yana ba da ƙarfi da iko ga jama'arsa. Ku yabi Allah!
1Ka cece ni, ya Allah! Ruwa ya sha kaina.
2Ina nutsewa cikin laka mai zurfi, Ba kuwa ƙasa mai ƙarfi, Na tsunduma cikin ruwa mai zurfi, Raƙuman ruwa kuwa sun kusa kashe ni.
3Na gaji da kira, ina neman taimako, Maƙogwarona yana yi mini ciwo, Idanuna duka sun gaji, Saboda ina zuba ido ga taimakonka.
4Waɗanda suke ƙina ba dalili Sun fi gashin kaina yawa, Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina, Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni. Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.
5Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah, Ka san irin wawancin da na yi!
6Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka, Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka! Kada ka bar ni in jawo abin kunya Ga waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!
7Sabili da kai ne aka ci mutuncina, Kunya ta rufe ni.
8Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana, Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.
9Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a Haikalinka Tana iza ni a ciki kamar wuta, Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
10Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi, Jama'a kuwa suka ci mutuncina.
11Na sa tufafin makoki, Sai suka maishe ni abin dariya.
12A tituna suna ta magana a kaina, Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.
13Amma ni, za yi addu'a gare ka, ya Ubangiji, Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa, Sabili da muhimmiyar ƙaunarka, Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.
14Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka, Ka kiyaye ni daga maƙiyana, Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.
15Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni. Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa, Ko in nutse a cikin kabari.
16Sabili da madawwamiyar ƙaunarka, ka amsa mini, ya Ubangiji, Ka juyo wurina, saboda juyayinka mai girma!
17Kada ka ɓoye kanka daga bawanka, Ina shan babbar wahala, ka yi hanzari ka amsa mini!
18Ka zo ka fanshe ni, Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.
19Ka san yadda ake cin mutuncina, Da yadda ake kunyata ni, ake ƙasƙantar da ni, Kana ganin dukan abokan gābana.
20Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini, Ni kuwa ba ni da mataimaki, Na sa zuciya za a kula da ni, Amma babu. Na sa zuciya zan sami ta'aziyya, Amma ban samu ba.
21Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi, Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.
22Allah ya sa bukukuwansu su zama lalacewarsu, Shagulgulansu kuma su zama sanadin fāɗuwarsu!
23Ka makantar da su, har da ba za su iya gani ba, Kullum ka sa bayansu ya ƙage!
24Ka kwarara musu fushinka, Bari zafin fushinka ya ci musu!
25Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu, Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!
26Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta, Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.
27Ka riɓaɓɓanya zunubansu, Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.
28Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai, Kada a sa su a lissafin jama'arka.
29Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala, Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!
30Zan raira waƙar yabo ga Allah, Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,
31Wannan zai daɗaɗa wa Ubangiji rai Fiye da hadayar bijimi, Fiye da a ba shi bijimi bana bakwai.
32Sa'ad da masu bukata suka ga wannan za su yi murna, Waɗanda suke yi wa Allah sujada kuwa za a ƙarfafa su.
33Ubangiji yana kasa kunne ga masu bukata, Bai manta da jama'arsa da suke a kurkuku ba.
34Ku yabi Allah, ku al'arshi da duniya, ku yabi Allah, Tekuna da dukan talikan da suke cikinsu!
35Gama zai ceci Sihiyona, Ya sāke gina garuruwan Yahuza, Jama'arsa za su zauna a wurin, su mallaki ƙasar.
36Zuriyar bayinsa za su gāje ta, Masu ƙaunarsa za su zauna a wurin.
1Ka cece ni, ya Allah! Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
2Ka sa masu so su kashe ni, A ci nasara a kansu, su ruɗe! Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya!
3Ka sa waɗanda suke mini ba'a Su razana sabili da fāɗuwarsu!
4Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka Su yi murna, su yi farin ciki! Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”
5Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki, Ya Allah, ka zo wurina da hanzari. Kai ne mataimakina da Mai Cetona, Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!
1A gare ka, ya Ubangiji, lafiya lau nake, Faufau kada ka bari a yi nasara da ni!
2Sabili da kai adali ne ka taimake ni, ka cece ni. Ka kasa kunne gare ni, ka cece ni!
3Ka zama mini lafiyayyiyar mafaka, Da kagara mai ƙarfi, domin ka tsare ni, Kai ne mafakata da kāriyata.
4Ya Allahna, ka cece ni daga mugaye, Daga ikon mugga, wato mugayen mutane.
5Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya, Tun ina yaro, nake dogara gare ka.
6A duk kwanakina a gare ka nake dogara, Kana kiyaye ni tun da aka haife ni, Kullayaumi zan yabe ka!
7Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa, Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.
8Ina yabonka dukan yini, Ina shelar darajarka.
9Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni, Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!
10Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni, Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.
11Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi, Gama ba wanda zai cece shi!”
12Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah, Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!
13Ka sa a kori waɗanda suka tasar mini, A hallaka su! Ka sa a kunyata waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, A wulakanta su sarai!
14A koyaushe zan sa zuciya gare ka, Zan yi ta yabonka.
15Zan ba da labarin adalcinka, Zan yi magana a kan cetonka duk yini, Ko da yake ya fi ƙarfin in san shi duka.
16Zan tafi in yi yabon ikonka, ya Ubangiji Allah, Zan yi shelar adalcinka, Naka, kai kaɗai.
17Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro, Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.
18Yanzu da na tsufa, na kuma yi furfura, Kada ka rabu da ni, ya Allah! Ka kasance tare da ni sa'ad da nake shelar ikonka da ƙarfinka ga mutanen dukan zamanai masu zuwa.
19Adalcinka, ya Allah, ya kai har sammai. Ka aikata manyan ayyuka, Ba waninka!
20Ka aiko mini da wahala da azaba, Amma za ka mayar mini da ƙarfina, Za ka tashe ni daga kabari.
21Za ka girmama ni har abada, Za ka sāke ta'azantar da ni.
22Hakika zan yabe ka da garaya, Zan yabi amincinka, ya Allahna. Da garayata zan yi maka waƙoƙi, Ya Mai Tsarki na Isra'ila.
23Zan ta da muryar farin ciki Sa'ad da nake raira maka waƙar yabbai, Zan raira waƙa da zuciya ɗaya, Gama dā ka fanshe ni.
24Zan yi magana a kan adalcinka dukan yini, Saboda an yi nasara da waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, sun ruɗe.
1Ka koya wa sarki ya yi shari'a Da adalcinka, ya Allah, Ka kuma ba shi shari'arka,
2Don ya yi mulkin jama'arka bisa kan shari'a, Ya kuma bi da mulki da adalci.
3Ka sa ƙasar ta mori wadatarta, Ka sa al'ummar ta san adalci.
4Ka sa sarki ya yi wa talakawa shari'ar gaskiya, Ya taimaki waɗanda suke da bukata, Ya kuma hukunta azzalumai!
5Ka sa su girmama ka Muddin rana tana haskakawa, Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.
6Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki, Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.
7Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa, Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.
8Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.
9Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa, Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.
10Sarakunan Esbanya da na tsibirai, Za su ba shi kyautai, Sarakunan Arabiya da na Habasha Za su kawo masa kyautai.
11Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa, Dukan sauran al'umma za su bauta masa!
12Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi, Da waɗanda suke da bukata, Da waɗanda ba a kula da su.
13Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta, Yakan ceci rayukan waɗanda suke da bukata.
14Yakan cece su daga zalunci da kama-karya, Rayukansu suna da daraja a gare shi.
15Ran sarki ya daɗe! Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya, Da ma a yi masa addu'a dukan lokaci, Allah ya sa masa albarka kullum!
16Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar, Da ma amfanin gona ya cika tuddan, Ya yi yawa kamar itatuwan al'ul na Lebanon, Da ma birane su cika da mutane, Kamar ciyayin da suke girma a sauruka.
17Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada, Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa. Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin, Dukan jama'a su roƙi Allah ya sa musu albarka, Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.
18Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila, Wanda shi kaɗai ne yake aikata al'amuran nan masu banmamaki!
19Ku yabi sunansa mai daraja har abada, Allah ya sa ɗaukakarsa ta cika dukan duniya! Amin! Amin!
20Ƙarshen addu'o'in Dawuda, ɗan Yesse ke nan.
LITTAFI NA UKU: Ƙarshen Mugaye (Zabura ta 73-89)
1Hakika, Allah yana yi wa Isra'ila alheri, Da waɗanda suke da tsarkin zuciya!
2Amma ina gab da fāɗuwa, Ƙafafuna sun kusa zamewa,
3Saboda na ji kishin masu girmankai, Sa'ad da na ga mugaye suna arziki.
4Ba su jin zafin ciwo, Su ƙarfafa ne, lafiyayyu.
5Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha, Ba su da wahala kamar sauran mutane,
6Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya, Suka sa hargitsi kuma kamar riga.
7Zuciyarsu, cike take da mugunta, Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.
8Sukan yi wa waɗansu ba'a, Suna faɗar mugayen abubuwa, Masu girmankai ne su, suna shawara A kan yadda za su zalunci waɗansu.
9Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama, Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya,
10Har jama'ar Allah ma sukan koma wurinsu, Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu.
11Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba, Maɗaukaki ba zai bincika ba!”
12Haka mugaye suke. Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi.
13Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki, Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi>
14Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini, Kana horona kowace safiya!
15Da na faɗi waɗannan abubuwa, Da na zama marar gaskiya ga jama'arka.
16Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan, Ko da yake ya cika wuya,
17Sai sa'ad da na shiga Haikalinka, Sa'an nan na fahimci abin da zai sami mugaye.
18Hakika ka sa su a wurare masu santsi, Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!
19Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su, Suka yi mummunan ƙarshe!
20Ya Ubangiji, kamar mafarki suke Wanda akan manta da shi da safe, Sa'ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.
21Sa'ad da zuciyata ta ɓaci, Hankalina ya tashi,
22Sai na zama wawa, ban fahimta ba, Na nuna halin dabba a gabanka.
23Duk da haka ina tare da kai kullayaumin, Kana riƙe da hannuna.
24Shawararka, tana bi da ni, Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.
25In banda kai, wa nake da shi a Sama? Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya>
26Kwanyata da jikina za su raunana, Amma Allah ne ƙarfina, Shi nake so har abada!
27Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu, Za ka hallakar da marasa aminci gare ka.
28Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah! Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah, Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.
1Don me ka yashe mu haka, ya Allah? Za ka yi ta fushi da jama'arka har abada ne>
2Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni, Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa, Don su zama kabilarka. Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!
3Ka zo, ka yi yawo a wannan kufai, Abokan gābanmu sun lalatar da kome na cikin Haikali!
4Abokan gābanka suka yi sowa ta nasara A inda akan sadu da kai, Sun ƙwace Haikalin.
5Suna kama da masu saran itace, Suna saran itatuwa da gaturansu.
6Da gaturansu da gudumarsu, Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.
7Sun sa wa Haikalinka wuta, Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada, Sun farfashe shi duk.
8Sun yi niyya su murƙushe mu sarai, Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.
9Ba sauran tsarkakan alamu, Ba sauran annabawan da suka ragu, Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.
10Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a? Za su yi ta zargin sunanka har abada ne>
11Me ya sa ka ƙi taimakonmu? Ka tasar musu ka hallaka su!
12Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko, Ka yi nasara da duniya.
13Da ƙarfin ikonka ka raba teku, Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,
14Ka ragargaje kawunan kadduna, Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.
15Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu, Ka sa manyan koguna sa ƙafe.
16Ka halicci yini da dare, Ka sa rana da wata a wurarensu.
17Ka yi wa duniya kan iyaka, Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.
18Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a, Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.
19Kada ka ba da jama'arka marasa taimako A hannun mugayen maƙiyansu, Kada ka manta da jama'arka waɗanda ake tsananta musu!
20Ka tuna da alkawarin da ka yi mana, Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!
21Kada ka bari a kori waɗanda ake zalunta, Amma bari matalauta da masu mayata su yabe ka.
22Ka tashi, ya Allah, ka kāre kanka! Ka tuna fa, marasa tsoronka suna ta yi maka ba'a dukan yini!
23Kada ka manta da hargowar maƙiyanka, Kada ka manta da hayaniyar da magabtanka suke ta yi.
1Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka! Muna shelar sunanka mai girma, Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!
2“Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah, “Zan kuwa yi shari'ar gaskiya.
3Ko da duniya da dukan waɗanda suke zaune cikinta za su ɓace, Zan ƙarfafa harsashin gininta.
4Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama, Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya,
5Na dai faɗa musu su daina yanga, Su daina yin taƙama.”
6Hukunci ba daga gabas, ko yamma, Ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba.
7Allah yake yin shari'a, Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu.
8Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo, Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi, Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha, Suka shanye shi ƙaƙaf.
9Amma har abada ba zan daina yin magana a kan Allah na Yakubu ba, Ko in daina raira yabbai gare shi.
10Shi zai karya ikon mugaye, Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi.
1Allah sananne ne a Yahuza, Mashahuri ne kuma a Isra'ila.
2Wurin zamansa yana Urushalima, A dutsen Sihiyona zatinsa yake.
3A can yake kakkarya kiban abokan gāba, Da garkuwoyinsu, da takubansu, i, har da dukan makamansu.
4Ina misalin darajarka, ya Allah! Ina misalin ɗaukakarka a sa'ad da ka komo daga kan duwatsu, Daga korar abokan gābanka!
5An kwashe ganimar sojojinsu masu ƙarfin hali, Yanzu suna barci, barcin matattu, Ba waninsu da ya ragu, Da zai yi amfani da makamansa.
6Sa'ad da ka fafare su, ya Allah na Yakubu, Dawakansu da mahayansu suka fāɗi matattu.
7Amma mutane suna jin tsoronka! Wa zai iya tsayawa a gabanka Sa'ad da ka yi fushi>
8Daga Sama ka sanar da shari'arka, Duniya ta tsorata, ta yi tsit,
9Sa'ad da ka tashi domin ka yanke hukunci, Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya.
10Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.
11Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa, Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai. Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,
12Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai, Ya tsoratar da manyan sarakuna.
1Na ta da murya, na yi kuka ga Allah, Na ta da murya, na yi kuka, ya kuwa ji ni.
2A lokacin wahala, nakan yi addu'a ga Ubangiji, Dukan dare nakan ɗaga hannuwana sama in yi addu'a, Amma ban sami ta'aziyya ba.
3Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya. Sa'ad da nake tunani, Nakan ji kamar in fid da zuciya.
4Ba ya barina in yi barci, Na damu har na kāsa magana.
5Na yi tunanin kwanakin da suka wuce, Nakan kuma tuna da shekarun da suka wuce da daɗewa.
6Dare farai ina ta tunani mai zurfi, A cikin tunani nakan yi wa kaina tambaya.
7A kullum ne Ubangiji zai yashe ni? Ba kuma zai ƙara yin murna da ni ba>
8Ya daina ƙaunata ke nan? Alkawarinsa ba shi da wani amfani>
9Allah ya manta da yin jinƙai ne? Fushinsa ya maye matsayin juyayinsa ne>
10Sa'an nan sai na ce, “Abin da ya fi mini zafi duka, Shi ne ikon Maɗaukaki ya ragu.”
11Zan tuna da manyan ayyukanka, ya Ubangiji, Zan tuna da al'amura masu banmamaki da ka aikata a dā.
12Zan tuna da dukan abubuwan da ka yi, Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka.
13Dukan abin da kake yi mai tsarki ne, ya Allah! Ba wani allah mai girma kamarka!
14Kai ne Allah wanda kake aikata al'ajabai, Ka nuna ikonka cikin sauran al'umma.
15Ta wurin ikonka ka fanshi jama'arka, Zuriyar Yakubu da ta Yusufu.
16Ya Allah, sa'ad da ruwaye suka gan ka, sai su tsorata, Zurfafan teku kuma suka yi rawar jiki.
17Gizagizai suka zubo da ruwa, Aka buga tsawa daga sama, Aka kuwa yi walƙiya ko'ina.
18Bugawar tsawarka ta gama ko'ina, Hasken walƙiya ya haskaka dukan duniya, Duniya ta yi rawa, ta girgiza, ta kaɗu.
19Ka yi tafiya a teku, Ka haye teku mai zurfi, Amma ba a ga shaida inda ka taka ba.
20Ka bi da jama'arka yadda makiyayi yake yi, Musa da Haruna suke lura da su.
1Ku kasa kunne ga koyarwata, ya ku jama'ata, Ku kula da abin da nake faɗa.
2Zan yi magana da ku, In faɗa muku asirai na dā,
3Abubuwan da muka ji muka kuwa sani, Waɗanda kakanninmu suka faɗa mana.
4Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga 'ya'yanmu ba, Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwa Labarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa, Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.
5Ya ba da dokoki ga jama'ar Isra'ila, Da umarnai ga zuriyar Yakubu. Ya ba kakanninmu ka'idodi, Don su koya wa 'ya'yansu dokokinsa,
6Saboda tsara mai zuwa ta koye su, Su kuma su koya wa 'ya'yansu.
7Ta haka su ma za su dogara ga Allah, Ba za su manta da abin da ya yi ba, Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.
8Kada su zama kamar kakanninsu, Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya. Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba, Ba su kuwa yi masa aminci ba.
9Ifraimawa waɗanda suka yi yaƙi da bakkuna da kibau Suka gudu a ranar yaƙi.
10Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba, Sun ƙi biyayya da dokokinsa.
11Sun manta da abin da ya aikata, Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.
12Kakanninsu na kallo sa'ad da Allah ya aikata wata mu'ujiza A filin Zowan a ƙasar Masar.
13Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta, Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.
14Da rana sai ya bi da su da girgije, Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.
15Ya tsaga duwatsu, suke buɗe a hamada, Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.
16Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse, Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.
17Amma sun ci gaba da yi wa Allah zunubi, A hamada suka yi wa Maɗaukaki tawaye.
18Da gangan suka jarraba Allah, Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.
19Suka yi magana gāba da Allah, suka ce, “Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada>
20Gaskiya ce, ya bugi dutse, Ruwa kuwa ya fito a yalwace, Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”
21Saboda haka Allah ya yi fushi sa'ad da ya ji su, Ya aukar wa jama'arsa da wuta, Fushinsa ya haɓaka a kansu,
22Saboda ba su amince da shi ba, Ba su kuma gaskata yana da ikon cetonsu ba.
23Amma ya yi magana da sararin sama, Ya umarci ƙofofinsa su buɗe,
24Ya ba su tsaba daga sama, Da ya sauko musu da manna, su ci.
25Ta haka suka ci abincin mala'iku. Allah ya ba su iyakar abin da za su iya ci.
26Sa'an nan sai ya sa iskar gabas ta hura, Da ikonsa kuma ya sa iskar kudu ta tashi.
27Ya aika da tsuntsaye bisansu kamar ƙura, Yawansu kamar yashi a gaɓa,
28Sai suka fāɗo a zango, Kewaye da alfarwai ko'ina.
29Sai mutane suka ci suka ƙoshi, Allah ya ba su iyakar abin da suke bukata.
30Amma sa'ad da suke cikin ci, Tun ba su ƙoshi ba,
31Sai Allah ya yi fushi da su. Ya karkashe ƙarfafan mutane, Da samarin Isra'ila na gaske!
32Ko da yake ya aikata mu'ujizai da yawa, Duk da haka jama'a suka ci gaba da yin zunubi, Ba su kuwa gaskata shi ba.
33Ta haka ya ƙare kwanakinsu kamar fitar numfashi, Bala'i ya aukar wa rayukansu farat ɗaya.
34Amma sa'ad da ya kashe waɗansunsu, Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba, Suka yi addu'a sosai a gare shi.
35Sun tuna, ashe, Allah ne mai kiyaye su, Sun tuna Maɗaukaki shi ne Mai Fansarsu.
36Amma maganganunsu duka ƙarya ne, Dukan abin da suka faɗa kuwa daɗin baki ne kawai.
37Ba su yi masa biyayya ba, Ba su yi aminci game da alkawarin da suka yi da shi ba.
38Amma Allah ya yi wa jama'arsa jinƙai, Ya gafarta zunubansu, Bai hallaka su ba. Sau da yawa yakan kanne fushinsa, Ya dakatar da hasalarsa.
39Yakan tuna su mutane ne kawai, Kamar iskar da take hurawa ta wuce.
40Sau da yawa suka tayar masa a hamada. Sau da yawa suka sa shi yin ɓacin rai!
41Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai, Suka kuwa sa Mai Tsarki na Isra'ila yin fushi.
42Suka manta da ikonsa mai girma. Suka manta da lokacin da ya cece su daga abokan gābansu,
43Lokacin da ya aikata manyan ayyuka da mu'ujizai A filin Zowan, ta ƙasar Masar.
44Ya mai da koguna su zama jini, Masarawa kuwa suka kasa sha daga rafuffukansu.
45Ya aiko da ƙudaje gare su, suka wahalshe su, Kwaɗi suka lalata filayensu.
46Ya aiko da gamzari don su ci amfanin gonakinsu, Ya aiko da ɗango su lalata gonakinsu.
47Ya kashe kurangar inabinsu da ƙanƙara, Ya kuma kashe itatuwan ɓaurensu da jaura.
48Ya karkashe shanunsu da ƙanƙara, Ya kuma karkashe garkunan tumakinsu da na awakinsu da tsawa.
49Ya buge su da fushinsa mai zafi, da hasalarsa, Ya sa su damuwa ƙwarai, Da ya aiko da mala'iku masu hallakarwa.
50Bai kanne fushinsa ba, Bai bar su da rai ba, Amma ya karkashe su da annoba.
51Ya karkashe 'yan fari maza Na dukan iyalan da suke Masar.
52Sa'an nan ya bi da jama'arsa Kamar makiyayi, ya fito da su, Ya yi musu jagora cikin hamada.
53Ya bi da su lafiya, ba su kuwa ji tsoro ba, Amma teku ta cinye abokan gābansu.
54Ya kawo su tsattsarkar ƙasarsa, Ya kawo su a duwatsun da shi kansa ya ci da yaƙi.
55Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.
56Amma sai suka yi wa Allah Mai Iko Dukka tawaye, Suka jarraba shi. Ba su kiyaye dokokinsa ba,
57Amma suka yi tawaye da rashin aminci Kamar kakanninsu, Kamar kiban da aka harba da tanƙwararren baka, Waɗanda ba su da tabbas.
58Suka sa shi ya yi fushi saboda Masujadansu na arnanci. Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.
59Allah ya yi fushi sa'ad da ya ga haka, Don haka ya rabu da jama'arsa ɗungum.
60Ya bar alfarwarsa da take a Shilo, Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.
61Ya yardar wa abokan gāba su ƙwace akwatin alkawari, Inda aka ga ikonsa da darajarsa,
62Ya ji fushi da jama'arsa, Ya bar abokan gābansu su karkashe su.
63Aka karkashe samari a cikin yaƙi, 'Yan mata kuma suka rasa ma'aura.
64Aka karkashe firistoci da takuba, Matansu ba su yi makoki dominsu ba.
65Daga bisani sai Ubangiji ya tashi Kamar wanda ya farka daga barci, Kamar jarumi wanda ya bugu da ruwan inabi.
66Ya tura abokan gābansa baya, Da mummunar kora mai bankunya Da ba za su sāke tashi ba.
67Ubangiji ya rabu da zuriyar Yusufu, Bai kuma zaɓi kabilar Ifraimu ba.
68A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza, Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.
69A can ya gina Haikalinsa, Kamar wurin zamansa a Sama. Ya kafa shi da ƙarfi kamar duniya, Tabbatacce a kowane lokaci.
70Ya zaɓi bawansa Dawuda, Ya ɗauko shi daga wurin kiwon tumaki,
71Ya ɗauko shi daga inda yake lura da 'yan raguna. Ya naɗa shi Sarkin Isra'ila, Ya naɗa shi makiyayin jama'ar Allah.
72Dawuda kuwa ya lura da su da zuciya ɗaya, Da gwaninta kuma ya bi da su.
1Ya Allah, arna sun fāɗa wa ƙasar jama'arka! Sun ƙazantar da Haikalinka tsattsarka, Sun bar Urushalima kufai.
2Suka bar wa ta tsuntsaye gawawwakin jama'arka su ci, Suka bar wa namomin jeji gawawwakin bayinka.
3Suka zubar da jinin jama'arka kamar ruwa. Jini ya yi ta gudu kamar ruwa Ko'ina a Urushalima, Ba ma wanda ya ragu don ya binne gawawwaki.
4Sauran al'umma da suke kewaye da mu, Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya, Suka yi mana ba'a.
5Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji? Har abada ne? Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta>
6Ka yi fushi da al'umman da ba su yi maka sujada, Ka yi fushi da jama'ar da suka ƙi ka!
7Sun karkashe mutanenmu, Sun kuwa lalatar da ƙasarmu.
8Kada ka hukunta mu saboda zunuban kakanninmu, Amma ka yi mana jinƙai yanzu, Gama mun fid da zuciya sarai.
9Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, Saboda girmanka. Ka cece mu, ka gafarta mana zunubanmu, Don mutane su yabe ka.
10Don me al'ummai za su tambaye mu cewa, “Ina Allahnku?” Bari mu ga ka hukunta al'ummai Saboda sun zubar da jinin bayinka!
11Ka kasa kunne ga nishin 'yan sarƙa, Ka kuɓutar da waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa, Ta wurin ikonka mai girma.
12Ya Ubangiji, ka rama wa al'umman nan har sau bakwai, Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.
13Mu waɗanda muke jama'arka, tumakin garkenka, Za mu gode maka, mu yabe ka har abada.
1Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila, Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka, Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.
2Ka bayyana ƙaunarka ga kabilar Ifraimu, Da ta Biliyaminu, da ta Manassa! Ka nuna mana ikonka, Ka zo ka cece mu!
3Ka komo da mu, ya Allah! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
4Har yaushe ke nan ya Ubangiji Allah Mai Runduna, Za ka yi ta fushi da addu'o'in jama'arka>
5Ka ciyar da mu da hawaye, Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.
6Ka bar al'umman da suke maƙwabtaka da mu Su yi ta faɗa a kan ƙasarmu, Abokan gābanmu kuma suna yi mana ba'a.
7Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
8Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar, Ka kori sauran al'umma, Ka dasa kurangar a ƙasarsu.
9Ka gyara mata wuri don ta yi girma, Saiwoyinta suka shiga ƙasa sosai, Ta yaɗu, ta rufe dukan ƙasar.
10Ta rufe tuddai da inuwarta, Ta rufe manya manyan itatuwan al'ul da rassanta.
11Rassanta sun miƙe har Bahar Rum, Har zuwa Kogin Yufiretis.
12Me ya sa ka rushe shingen da yake kewaye da ita? Ga shi yanzu, duk mai wucewa yana iya satar 'ya'yanta.
13Aladen jeji kuma za su tattake ta, Namomin jeji duka za su cinye ta.
14Ka juyo wurinmu, ya Allah Mai Runduna! Daga Sama, ka dube mu, Ka zo ka ceci kurangar inabinka!
15Ka zo ka ceci kurangar inabin nan Wadda kai da kanka ka dasa, Wannan ƙaramar kuranga, Ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!
16Abokan gābanmu sun sa mata wuta, sun sare ta, Ka yi fushi da su, ka hallaka su!
17Ka kiyaye jama'arka wadda ka zaɓa, Ka keɓe ta. Al'umman nan wadda ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!
18Ba za mu ƙara rabuwa da kai ba, Ka rayar da mu, mu kuwa za mu yabe ka.
19Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
1Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu, Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!
2A fara waƙa, ku buga bandiri, Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.
3Ku busa ƙaho domin idin, A amaryar wata, Da a tsakiyar farin wata.
4Wannan doka ce a Isra'ila, Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.
5Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila, A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar. Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,
6“Na ɗauke muku kayayyaki masu nauyi da kuke ɗauke da su a kā, Na sa kuka ajiye kwandunan aikinku.
7Sa'ad da kuke shan wahala Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku. Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku, Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.
8“Ya kuma jama'ata Isra'ila ku kasa kunne, Ina kuwa so ku saurara gare ni.
9Faufau kada ku bauta wa gumaka, Ko ku yi sujada ga wanina.
10Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku.
11“Amma jama'ata ba sa kasa kunne gare ni ba. Isra'ila ta ƙi yi mini biyayya.
12Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu, Su aikata duk irin abin da suka ga dama.
13Ina kuwa so jama'ata su kasa kunne gare ni, Su kuwa yi mini biyayya!
14Da sai in kori abokan gābansu nan da nan, In yi nasara da dukan maƙiyansu.
15Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro, Hukuncinsu na har abada ne.
16Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama, In ƙosar da ku da zuma.”
1Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa, Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.
2Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a, Ku daina goyon bayan mugaye!
3Ku kāre hakkin talakawa da na marayu, Ku yi adalci ga matalauta, Da waɗanda ba su da mataimaki.
4Ku kuɓutar da talakawa da matalauta, Ku cece su daga ikon mugaye!
5“Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye! Kuna zaune cikin duhu, Ga shi, ba adalci a duniya sam!
6Na faɗa muku, ku alloli ne, Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.
7Amma za ku mutu kamar kowane mutum, Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”
8Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya, Dukan al'ummai naka ne.
1Ya Allah, kada ka yi shiru, Kada ka tsaya cik, Ya Allah, kada kuma ka yi tsit!
2Duba, abokan gābanka suna tawaye, Maƙiyanka sun tayar.
3Suna ta ƙulle-ƙulle a asirce gaba da jama'arka, Suna shirya maƙarƙashiya gāba da waɗanda kake tsaronsu.
4Suna cewa, “Ku zo, mu hallakar da al'ummarsu, Don a manta da Isra'ila har abada!”
5Suka yarda a kan abin da suka shirya, Suka haɗa kai gāba da kai.
6Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa, Da mutanen Mowab, da Hagarawa,
7Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek, Da na Filistiya, da na Taya.
8Assuriya ma ta haɗa kai da su, Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.
9Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa, Ka yi musu yadda ka yi wa Sisera Da Yabin a Kogin Kishon,
10Waɗanda aka kora a Endor, Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa.
11Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib, Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna,
12Waɗanda suka ce, “Za mu ƙwace ƙasar da take ta Allah, ta zama tamu.”
13Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura, Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.
14Kamar yadda wuta take cin jeji, Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,
15Ka runtume su da hadirinka, Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi.
16Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su, Don su so su bauta maka.
17Ka sa a kore su, a razanar da su har abada, Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!
18Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji, Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!
1Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai, Ya Allah Mai Iko Dukka!
2A can nake so in kasance! Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji. Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.
3Har ba'u ma sukan yi sheƙa, Tsattsewa suna da sheƙunansu, A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu. Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.
4Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka, Kullum suna raira yabonka!
5Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka, Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.
6Sa'ad da suke ratsa busasshen kwari, Sai ya zama maɓuɓɓugar ruwa, Ruwan sama na farko yakan rufe wurin da tafkuna.
7Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu, Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona!
8Ka ji addu'ata, ya Ubangiji Allah Mai Runduna, Ka ji ni, ya Allah na Yakubu!
9Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu, Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka.
10Kwana guda da za a yi a Haikalinka, Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam. Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna, Da in zauna a gidajen mugaye.
11Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
12Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka, Ya Allah Mai Runduna!
1Ya Ubangiji, ka yi wa ƙasarka alheri, Ka sāke arzuta Isra'ila kuma.
2Ka gafarta wa jama'arka zunubansu, Ka kuwa gafarta musu dukan kuskurensu,
3Ka daina yin fushi da su, Ka kuwa kawar da zafin fushinka.
4Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu, Ka daina jin haushinmu!
5Za ka yi fushi da mu har abada? Ba za ka taɓa hucewa ba>
6Ka daɗa mana ƙarfi, ka yarda ka sabunta ƙarfinmu, Mu kuwa, jama'arka, za mu yabe ka.
7Ka ƙaunace mu da madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji, Ka taimake mu da cetonka.
8Ina kasa kunne ga abin da Ubangiji Allah yake cewa, Mu da muke mutanensa, ya alkawarta mana salama, Idan ba mu koma kan al'amuranmu na wauta ba.
9Hakika a shirye yake ya ceci waɗanda suke girmama shi, Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.
10Ƙauna da aminci za su sadu wuri ɗaya, Adalci da salama za su gamu.
11Amincin mutum zai yunƙura daga duniya, ya nufi sama. Adalcin Allah kuwa zai dubo daga Sama.
12Ubangiji zai arzuta mu, Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.
13Adalci zai yi tafiya a gaban Ubangiji, Ya shirya masa tafarki.
1Ka kasa kunne gare ni, ya Ubangiji, ka amsa mini, Gama ba ni da ƙarfi, ba ni kuwa da mataimaki.
2Ka cece ni daga mutuwa, saboda ni mai aminci ne a gare ka, Ka cece ni saboda ni bawanka ne, ina kuwa dogara gare ka.
3Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.
4Ka sa bawanka ya yi murna, ya Ubangiji, Saboda addu'o'ina sun hau zuwa gare ka.
5Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara, Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.
6Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka ji kukana na neman taimako!
7Nakan kira gare ka a lokacin wahala, Saboda kakan amsa addu'ata.
8Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji, Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.
9Dukan sauran al'umma da ka halitta Za su zo su rusuna har ƙasa a gabanka. Za su yabi girmanka,
10Gama kai kaɗai ne maɗaukaki, ya Allah, Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.
11Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi, Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci. Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.
12Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji Allahna, Zan riƙa shelar girmanka har abada.
13Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni! Gama ka cece ni daga zurfin kabari.
14Masu girmankai sun tasar mini, ya Allah, Ƙungiyar mugaye tana ƙoƙari ta kashe ni, Mutanen da ba su kula da kai ba.
15Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna, Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.
16Ka juyo gare ni, ka yi mini jinƙai, Ka ƙarfafa ni, ka cece ni, Gama ina bauta maka, kamar yadda mahaifiyata ta yi.
17Ka nuna mini alherinka, ya Ubangiji, Sa'an nan su waɗanda suke ƙina za su sha kunya, Sa'ad da suka ga ka ta'azantar da ni, Ka kuma taimake ni.
1Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,
2Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila.
3Ya birnin Allah, ka kasa kunne, Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.
4“Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya, Zan sa Masar da Babila a cikinsu, Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha, Su ma na Urushalima ne.”
5A kan Sihiyona kuwa za a ce, “Dukan sauran al'umma nata ne.” Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta.
6Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i, Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.
7Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa, Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.”
1Ya Ubangiji Allah, Mai Cetona, Duk yini ina ta kuka, Da dare kuma na zo gare ka.
2Ka ji addu'ata, Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako!
3Wahala mai yawa ta auko mini, Har ina gab da mutuwa.
4Ina daidai da sauran mutanen da suke gab da mutuwa, Dukan ƙarfina ya ƙare.
5An yashe ni a cikin matattu, Kamar waɗanda aka karkashe, Suna kuma kwance cikin kaburburansu, Waɗanda ka manta da su ɗungum, Waɗanda taimakonka ya yi musu nisa.
6Ka jefar da ni cikin zurfin kabari, Da cikin rami mafi zurfi, mafi duhu.
7Fushinka yana da nauyi a kaina, An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.
8Ka sa abokaina su yashe ni, Ka sa sun ware ni. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta.
9Idanuna sun raunana saboda wahala. Ya Ubangiji, kowace rana ina kira gare ka, Ina ta da hannuwana zuwa gare ka da addu'a!
10Kakan yi wa matattu mu'ujizai ne? Sukan tashi su yabe ka>
11Akan yi maganar madawwamiyar ƙaunarka a kabari? Ko amincinka a inda ake hallaka>
12Za a iya ganin mu'ujizanka a cikin duhu? Ko kuwa alherinka a lahira>
13Ya Ubangiji, ina kira gare ka, neman taimako, Kowace safiya nakan yi addu'a gare ka.
14Me ya sa ka yashe ni, ya Ubangiji? Me ya sa ka ɓoye kanka daga gare ni>
15Tun ina ƙarami nake shan wahala, Har ma na kusa mutuwa, Na tafke saboda nauyin hukuncinka.
16Hasalarka ta bi ta kaina, Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.
17Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa, Ta kowace fuska, sun rufe ni.
18Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni, Duhu ne kaɗai abokin zamana.
1Ya Ubangiji zan raira waƙar Madawwamiyar ƙaunarka koyaushe, Zan yi shelar amincinka a dukan lokaci.
2Na sani ƙaunarka za ta dawwama har abada, Amincinka kuma tabbatacce ne kamar sararin sama.
3Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa, Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,
4“‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki, Zan kiyaye mulkinka har abada.”
5Talikan da suke Sama suna raira waƙa a kan Abubuwan banmamaki da kake yi, Suna raira waƙa kan amincinka, ya Ubangiji.
6Ba wani kamarka a Sama, ya Ubangiji, Ba wani daga su cikin talikai da yake daidai da kai.
7Ana girmama ka a cikin majalisar talikai, Duk waɗanda suke kewaye da kai suna jin tsoronka ƙwarai.
8Ya Ubangiji Allah, Mai Runduna, Ba wani mai iko kamarka, Kai mai aminci ne a kowane abu.
9Kai kake mulkin haukan teku, Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.
10Ka ragargaza dodon nan Rahab, ka kashe shi, Da ƙarfin ikonka ka cinye maƙiyanka.
11Duniya taka ce, haka ma samaniya taka ce, Kai ne ka halicci duniya da dukan abin da yake cikinta.
12Kai ne ka yi kudu da arewa, Dutsen Tabor da Dutsen Harmon Suna raira waƙa gare ka don farin ciki.
13Kai kake da iko! Kai kake da ƙarfi!
14A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka, Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.
15Masu farin ciki ne jama'ar da suke yi maka sujada, suna raira waƙoƙi, Waɗanda suke zaune a hasken alherinka.
16Suna murna dukan yini saboda da kai, Suna kuwa yabonka saboda alherinka.
17Kana sa mu ci babbar nasara, Da alherinka kakan sa mu yi rinjaye,
18Sabili da ka zaɓar mana mai kāre mu, Kai, Mai Tsarki na Isra'ila, Kai ne ka ba mu sarkinmu.
19Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce, “Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja, Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama'a.
20Na zaɓi bawana Dawuda, Na naɗa shi sarkinku.
21Ƙarfina zai kasance tare da shi, Ikona kuma zai ƙarfafa shi.
22Abokan gābansa ba za su taɓa cin nasara a kansa ba, Mugaye ba za su kore shi ba.
23Zan ragargaza magabtansa, In karkashe duk waɗanda suke ƙinsa.
24Zan ƙaunace shi kullum, in amince da shi, Zan sa ya yi nasara kullayaumin.
25Zan faɗaɗa mulkinsa tun daga Bahar Rum, Har zuwa Kogin Yufiretis.
26Zai ce mini, “‘Kai ubana ne da Allahna, Kai ne kake kiyaye ni, kai ne Mai Cetona.”
27Zan maishe shi ɗan farina, Mafi girma daga cikin dukan sarakuna.
28Zan riƙa ƙaunarsa har abada, Alkawarin da na yi da shi kuma zai tabbata har abada.
29A kullayaumin daga cikin zuriyarsa ne za a naɗa sarki, Mulkinsa zai dawwama kamar sararin sama.
30“Amma idan zuriyarsa sun ƙi yin biyayya da shari'ata, Ba sa kuwa zauna cikin ka'idodina ba,
31In sun ƙyale koyarwata, Ba su kiyaye umarnaina ba,
32To, sai in hukunta su saboda zunubansu, Zan bulale su saboda laifofinsu.
33Amma fa, ba zan daina ƙaunar Dawuda ba, Ba kuwa zan rasa cika alkawarin da na yi masa ba.
34Ba zan keta alkawarin da na yi masa ba, Ba zan soke ko ɗaya daga cikin alkawaran da na yi masa ba.
35“Da sunana mai tsarki na yi alkawari sau ɗaya tak, Ba zan yi wa Dawuda ƙarya ba!
36Zuriyarsa za ta kasance kullum, Zan lura da mulkinsa muddin rana tana haskakawa.
37Zai dawwama kamar wata, Kamar amintaccen mashaidin nan da yake a sararin sama.”
38Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka, Ka rabu da shi, ka yashe shi.
39Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka, Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.
40Ka rurrushe garun birninsa, Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.
41Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa, Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.
42Ka ba maƙiyansa nasara, Ka sa dukansu su yi murna.
43Ka sa makamansa su zama marasa amfani, Ka bari a ci shi da yaƙi.
44Ka ƙwace masa sandan sarautarsa, Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.
45Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa, Ka rufe shi da kunya.
46Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji? Har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta>
47Ka tuna kwanakin mutum kaɗan ne, ya Ubangiji, Ka tuna yadda ka halicci mutane duka masu mutuwa ne!
48Wa zai rayu har abada, ba zai mutu ba? Ƙaƙa mutum zai hana kansa shiga kabari>
49Ya Ubangiji, ina ƙaunarka ta dā? Ina alkawaran nan waɗanda ka yi wa Dawuda>
50Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka, Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.
51Ya Ubangiji, kada ka manta da yadda maƙiyanka suka ci mutuncin zaɓaɓɓen sarki da ka naɗa! Suka yi ta cin mutuncinsa duk inda ya tafi.
52Mu yabi Ubangiji har abada! Amin! Amin!
LITTAFI NA HUƊU: Allah Madawwami, Mutum mai Shuɗewa (Zabura ta 90-106)
1Ya Ubangiji, a koyaushe kai ne wurin zamanmu.
2Kafin a kafa tuddai, Kafin kuma ka sa duniya ta kasance, Kai Allah ne, Madawwami. Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.
3Kakan sa mutane su koma yadda suke, Su zama ƙura.
4A gare ka shekara dubu kamar kwana ɗaya ne, Kamar jiya ce wadda ta shige, Gajeruwa ce kamar sa'a guda ta dare.
5Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi, Kamar mafarki suke, ba su daɗewa. Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,
6Su yi girma har su yi huda, Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.
7Mun hallaka ta wurin fushinka, Mun razana saboda hasalarka.
8Ka jera zunubanmu a gabanka, Zunubanmu na ɓoye kuwa, Ka sa su a inda za ka gan su.
9Fushinka ya gajerta tsawon ranmu, Ranmu ya ƙare kamar ajiyar zuciya.
10Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in, In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru Suke kawo mana, damuwa ce da wahala, Nan da nan sukan wuce, Tamu da ƙare.
11Wa ya san iyakar ikon fushinka? Wa ya san irin tsoron da hasalarka za ta kawo>
12Ka koya mana mu sani ranmu na ɗan lokaci ne, Domin mu zama masu hikima.
13Ya Ubangiji, sai yaushe za ka ji tausayinmu? Ka ji tausayin bayinka!
14Ka cika mu da madawwamiyar ƙaunarka a kowace safiya, Don mu raira waƙoƙin murna dukan kwanakin ranmu.
15Yanzu sai ka sa mu yi farin ciki mai yawa, Kamar yadda ka sa muka yi baƙin ciki A dukan shekarun nan da muka sha wahala.
16Ka yarda mana, mu bayinka, mu ga ayyukanka masu girma, Ka yardar wa zuriyarmu su ga ikonka mai girma.
17Ka yarda, albarkarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu. Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi! I, ka ba mu nasara a dukan abin da muke yi!
1Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki Zai zauna lafiya, Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,
2Ya iya ce wa Ubangiji, “Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare ka nake dogara!”
3Hakika zai kiyaye ka Daga dukan hatsarorin da ka ɓoye, Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.
4Zai rufe ka da fikafikansa, Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu. Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.
5Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba, Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,
6Ko annobar da take aukowa da dare, Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.
7Mutum dubu za su fāɗi daura da kai, Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai, Amma kai, ba za a cuce ka ba.
8Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.
9Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka, Maɗaukaki ne yake tsaronka,
10To, ba bala'in da zai same ka, Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.
11Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai, Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.
12Za su ɗauke ka a hannuwansu, Don kada ka buga ƙafarka a dutse.
13Za ka tattake zakoki da macizai, Za ka tattake zakoki masu zafin rai Da macizai masu dafi.
14Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata, Zan kiyaye waɗanda suka san ni.
15Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.
16Zan ba su tsawon rai lada, Hakika kuwa zan cece su.”
1Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya, A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,
2A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya, Amincinka kuma kowane maraice,
3Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya, Da amon garaya mai daɗi.
4Ya Ubangiji, Ayyukanka masu iko suna sa ni murna, Saboda abin da ka aikata Ina raira waƙa domin farin ciki.
5Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji! Tunaninka da zurfi suke!
6Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba, Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,
7Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire, Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta, Duk da haka za a hallaka su ɗungum.
8Gama kai, ya Ubangiji, Maɗaukaki ne har abada.
9Mun sani maƙiyanka za su mutu, Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.
10Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa, Ka sa mini albarka da farin ciki.
11Na ga fāɗuwar maƙiyana, Na ji kukan mugaye.
12Adalai za su yi yabanya Kamar itatuwan giginya, Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.
13Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji, Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.
14Waɗanda suke yin 'ya'ya da tsufansu, A kullum kuwa kore shar suke, Suna da ƙarfinsu kuma.
15Wannan ya nuna Ubangiji adali ne, Shi wanda yake kāre ni, Ba kuskure a gare shi.
1Ubangiji sarki ne! Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne. Hakika duniya ta kahu sosai a inda take, Ba kuwa za ta jijjigu ba.
2Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko, Kana nan tun fil azal.
3Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu, Suna ta da muryarsu da ruri.
4Ubangiji yana mulki cikin Sama, Mulkinsa mafifici ne, Fiye da rurin teku, Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.
5Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji, Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai, Har abada abadin.
1Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci, Ka bayyana fushinka!
2Kai ne mai yi wa dukan mutane shari'a, Ka tashi, ka sāka wa masu girmankai Abin da ya dace da su!
3Har yaushe mugaye za su yi ta murna? Har yaushe ne, ya Ubangiji>
4Har yaushe za su yi shakiyanci, Su yi ta ɗaga kai? Har yaushe, ya Ubangiji>
5Suna ragargaza jama'arka, ya Ubangiji, Suna zaluntar waɗanda suke naka.
6Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu.
7Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu, Allah na Isra'ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”
8Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka? Sai yaushe za ku koya>
9Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba? Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba>
10Shi ne yake shugabancin sauran al'umma, ba zai hukunta su ba? Shi ne yake koya wa dukan mutane, shi ba shi da sani ne>
11Ubangiji ya san tunaninsu, Ya san kuma hujjojinsu na rashin hankali.
12Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa, Mutumin da kake koya masa shari'arka.
13Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala, Kafin a haƙa wa mugaye kabari.
14Ubangiji ba zai rabu da jama'arsa ba, Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba.
15Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai, Dukan adalai kuwa za su yi na'am da shi.
16Wa zai tsaya mini gāba da mugaye? Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta>
17Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba, Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi.
18Na ce, “Ina kan fāɗuwa,” Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
19Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa, Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.
20Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya, Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,
21Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya, Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa.
22Amma Ubangiji yakan kāre ni, Allahna yakan kiyaye ni.
23Shi zai hukunta su saboda muguntarsu, Ya hallaka su saboda zunubansu. Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.
1Ku zo mu yabi Ubangiji! Mu raira waƙa domin farin ciki ga mai kiyaye mu, Da Mai Cetonmu!
2Mu zo gabansa da godiya, Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!
3Gama Ubangiji Allah ne mai iko, Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.
4Yana mulki bisa dukan duniya, Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.
5Yana mulki bisa tekun da ya yi, Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.
6Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada, Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!
7Shi ne Allahnmu, Mu ne jama'ar da yake lura da ita, Mu ne kuma garken da yake ciyarwa. Yau ku ji abin da yake faɗa.
8“Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba, Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.
9A can suka gwada ni suka jarraba ni, Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.
10A shekara arba'in ɗin nan, Jama'ar nan ta zama abar ƙyama gare ni, “‘Su marasa biyayya ne,” in ji ni, “‘Gama sun ƙi bin umarnaina!”
11Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi. Na ce, “‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.”
(1 Tar 16.23-33)
1Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji! Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!
2Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi! Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa, “Ya cece mu!”
3Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma, Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.
4Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi, Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.
5Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai, Amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi, Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.
7Dukan jama'ar da ke bisa duniya su yabi Ubangiji! Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
8Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka, Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.
9Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana, Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!
10A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne! Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta, Ba za a iya kaushe ta ba, Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”
11Duniya da sararin sama, ku yi murna! Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki.
12Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku! Sa'an nan itatuwan da suke cikin kurama Za su ta da murya saboda farin ciki
13A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya. Zai mallaki dukan jama'ar duniya Da adalci da gaskiya.
1Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya! Ku yi murna, dukanku tsibiran da kuke cikin tekuna!
2Gajimare da duhu sun kewaye shi. A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.
3Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansa Waɗanda suke kewaye da shi.
4Walƙiyarsa ta haskaka duniya, Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.
5Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma, A gaban Ubangijin dukan duniya.
6Sammai suna shelar adalcinsa, Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.
7Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya, Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu. Dukan alloli za su rusuna a gabansa.
8Jama'ar Sihiyona suna murna, Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki, Sabili da irin shari'unka, ya Ubangiji!
9Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya, Ka fi sauran alloli duka girma.
10Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta. Yakan kiyaye rayukan jama'arsa, Yakan cece su daga ikon mugaye.
11Haske yakan haskaka adalai, Haka kuma murna ta cika ga masu nagarta.
12Dukanku adalai ku yi murna, Saboda abin da Ubangiji ya yi! Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya yi, Ku yi masa godiya!
1Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji, Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki! Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara.
2Ubangiji ya bayyana cin nasararsa, Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al'umma.
3Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila, Da tabbatacciyar ƙauna da aminci. Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu!
4Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji. Dukanku waɗanda kuke a duniya, Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi, Saboda farin ciki!
5Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu, Ku kaɗa garayu!
6Ku busa kakaki da ƙahoni, Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki!
7Ki yi ruri, ya ke teku, Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki, Ki raira waƙa, ke duniya, Da dukan waɗanda suke zaune cikinki!
8Ku yi tāfi, ya ku tekuna, Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki.
9A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya! Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya.
1Ubangiji Sarki ne, Mutane suna rawar jiki, Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi, Duniya ta girgiza.
2Ubangiji mai iko ne a Sihiyona, Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.
3Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki, Mai Tsarki ne shi!
4Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai, Ka kawo adalci cikin Isra'ila, Ka kawo adalci da gaskiya.
5Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a gaban kursiyinsa! Mai Tsarki ne shi!
6Musa da Haruna firistocinsa ne, Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne. Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.
7Ya yi magana da su daga girgije, Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.
8Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka, Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara, Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.
9Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki! Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!
1Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!
2Ku yi wa Ubangiji sujada da murna, Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!
3Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne, Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.
4Ku shiga Haikalinsa da godiya, Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi! Ku gode masa, ku yabe shi!
5Ubangiji nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce, Amincinsa kuwa har abada abadin ne.
1Waƙata ta aminci ce da gaskiya. Ina raira maka ita, ya Ubangiji.
2Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.
3Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan. Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah, Ba ruwana da su.
4Ba zan yi rashin aminci ba, Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.
5Zan hallakar da mai raɗar abokinsa, Ba zan jure da mutum mai girmankai, Ko mai alfarma ba.
6Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah, Zan yardar musu si yi zamansu a fādata, Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminci Su yi mini hidima.
7Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba, Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.
8A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu, Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.
1Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka ji kukana na neman taimako!
2Kada ka ɓoye mini sa'ad da nake shan wahala! Ka ji ni, ka amsa mini da sauri sa'ad da na yi kira!
3Raina ya ɓace kamar hayaƙi, Jikina yana ƙuna kamar wuta.
4An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa, Ba ni da marmarin cin abinci.
5Ina nishi da ƙarfi, Ba abin da ya ragu gare ni, In banda ƙashi da fata.
6Ni kamar tsuntsu nake cikin hamada, Kamar mujiya a kufai.
7Kwana nake ba barci, Na zama kamar tsuntsun da yake fama da kewa A bisa kan daƙi.
8Maƙiyana suna cin mutuncina dukan yini. Waɗanda suke mini ba'a, Suna la'antarwa da sunana.
9Toka ce abincina, Hawayena kuwa sun gauraya da abin da nike sha,
10Sabili da fushinka da hasalarka. Ka ɗauke ni, ka jefar da ni.
11Raina kamar inuwar maraice yake, Kamar busasshiyar ciyawa nake.
12Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada, Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.
13Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona, Lokaci ya yi da za ka yi mata jinƙai, Wannan shi ne lokacin!
14Bayinka suna ƙaunarta, Ko da yake an hallakar da ita, Suna jin tausayinta, Ko da yake ta zama kufai.
15Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji, Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.
16Sa'ad da Ubangiji ya sāke gina Sihiyona Zai bayyana girmansa.
17Zai saurari jama'arsa wadda ya rabu da ita, Zai kuwa ji addu'arta.
18Ku rubuta abin da Ubangiji ya aikata don zamani mai zuwa, Don waɗanda ba a haife su ba tukuna, Su ma su yabe shi.
19Ubangiji ya duba ƙasa Daga Sama, tsattsarkan wurinsa, Daga Sama ya dubi duniya,
20Don ya ji nishin ɗaurarru, Don ya saki waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa.
21Saboda wannan mutane za su yi shelar sunan Ubangiji a Sihiyona, Za su yi masa godiya a Urushalima,
22Sa'ad da sauran al'umma da mulkoki suka taru Don su yi wa Ubangiji sujada.
23Tun ina ƙaramin yaro Ubangiji ya sa na rasa ƙarfi, Ya gajerta kwanakina.
24Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu, Tun da yake ban tsufa ba tukuna! Ya Ubangiji har abada kake.
25Ka halicci duniya tun tuntuni, Da ikonka ne ka yi sammai.
26Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama, Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa, Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.
27Amma kai, kana yadda kake kullayaumin, Har abada kake.
28'Ya'yanmu za su yi zaman lafiya, Zuriyarsu kuma za su zauna cikin kiyayewarka kullayaumin.
1Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi sunansa mai tsarki!
2Ka yabi Ubangiji, ya raina, Kada ka manta da yawan alherinsa.
3Ya gafarta dukan zunubaina, Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.
4Ya cece ni daga kabari, Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.
5Ya cika raina da kyawawan abubuwa, Don in zauna gagau, Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.
6Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari'a ta gaskiya. Yakan ba su hakkinsu.
7Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa. Ya yardar wa jama'ar Isra'ila su ga manyan ayyukansa.
8Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma, Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.
9Ba zai yi ta tsautawa kullum ba, Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.
10Yakan yi mana rangwame sa'ad da yake hukunta mu, Ko sa'ad da yake sāka mana saboda zunubanmu da laifofinmu.
11Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya, Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.
12Kamar yadda gabas take nesa da yamma, Hakanan ne ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.
13Kamar yadda uba yake yi wa 'ya'yansa alheri, Hakanan kuwa Ubangiji yake yi wa masu tsoronsa alheri.
14Ubangiji ya san abin da aka yi mu da shi, Yakan tuna, da ƙura aka yi mu.
15Mutum fa, ransa kamar ciyawa ne, Yakan yi girma, ya yi yabanya kamar furen jeji.
16Sa'an nan iska ta bi ta kansa, yakan ɓace, Ba mai ƙara ganinsa.
17Amma ƙaunar Ubangiji ga waɗanda suke girmama shi har abada ce. Alherinsa kuwa tabbatacce ne har dukan zamanai,
18Ga waɗanda suke riƙe da alkawarinsa da gaskiya, Waɗanda suke biyayya da umarnansa da aminci.
19Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama, Shi yake sarautar duka.
20Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku, Ku da kuke biyayya da umarnansa, Kuna kasa kunne ga maganarsa!
21Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da kuke a Sama, Ku yabi Ubangiji, ku bayinsa masu aikata abin da yake so!
22Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa, A duk inda yake mulki! Ka yabi Ubangiji, ya raina!
1Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ya Ubangiji Allahna, mai girma ne kai! Kana saye da ɗaukaka da daraja,
2Ka yi lulluɓi da haske. Ka shimfiɗa sammai kamar alfarwa.
3Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama. Gajimare ne karusanka, A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.
4Iska ce jakadanka, Walƙiya kuwa ita ce baiwarka.
5Ka sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta, Ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.
6Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba, Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.
7Amma sa'ad da ka tsauta wa ruwa, Sai ya tsere, Sa'ad da ya ji ka daka tsawa, Sai ya sheƙa a guje.
8Ya haura kan duwatsu, ya gangara cikin kwaruruka, Wurin da ka shirya masa.
9Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba, Don kada ya sāke rufe duniya.
10Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka, Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.
11Su ne suke shayar da namomin jeji, Jakunan jeji kuma, a nan sukan kashe ƙishinsu.
12A itatuwan da suke kusa da wurin, Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.
13Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu, Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.
14Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu, Tsire-tsire kuma don amfanin mutum, Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,
15Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki, Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara'a, Da abincin da zai ba shi ƙarfi.
16Itatuwan al'ul na Lebanon sukan sami isasshen ruwan sama, Itatuwa ne na Ubangiji kansa, waɗanda shi ya dasa.
17A nan tsuntsaye suke yin sheƙunansu, A bisa itatuwan fir shamuwa take yin sheƙa.
18A kan duwatsu masu tsayi awakin jeji suke zama, Remaye sukan ɓuya a kan tsaunukan bakin teku.
19Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai, Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.
20Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.
21Sagarun zakoki sukan yi ruri sa'ad da suke farauta, Suna neman abincin da Allah zai ba su.
22Sa'ad da rana ta fito, Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.
23Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu, Su yi ta aiki har maraice ya yi.
24Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa! Da hikima ƙwarai ka halicce su! Duniya cike take da talikanka.
25Ga babbar teku mai fāɗi, Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune, Manya da ƙanana gaba ɗaya.
26Jiragen ruwa suna tafiya a kansa, Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.
27Dukansu a gare ka suke dogara, Don ka ba su abinci sa'ad da suke bukata.
28Ka ba su, sun ci, Ka tanada musu abinci, sun ƙoshi.
29Sa'ad da ka rabu da su sukan tsorata, In ka zare numfashin da ka ba su, sai su mutu, Su koma turɓaya, da ma da ita aka yi su.
30Amma sa'ad da ka hura musu numfashi, sai su rayu, Kakan sabunta fuskar duniya.
31Da ma darajar Ubangiji ta dawwama har abada! Da ma Ubangiji ya yi farin ciki da abin da ya halitta!
32Ya dubi duniya, sai ta girgiza, Ya taɓa duwatsu, sai suka tuɗaɗo da hayaƙi.
33Zan raira waƙa ga Ubangiji dukan raina, Zan raira yabbai ga Allah muddin raina.
34Da ma ya ji daɗin waƙata, Saboda yakan sa ni in yi murna.
35Da ma a hallakar da masu zunubi daga duniya, Da ma mugaye su ƙare ƙaƙaf! Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi Ubangiji!
(1 Tar 16.8-22)
1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa, Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
2Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi, Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
3Ku yi murna saboda mu nasa ne, Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
4Ku je wurin Ubangiji neman taimako, Ku tsaya a gabansa koyaushe. 5-6Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim, Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu, Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki, Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
7Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu, Umarnansa domin dukan duniya ne.
8Zai cika alkawarinsa har abada, Alkawaransa kuma don dubban zamanai,
9Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim, Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.
10Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila, Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,
11“Zan ba ka ƙasar Kan'ana, Za ta zama mallakarka.”
12Jama'ar Ubangiji kima ne, Baƙi ne kuwa a ƙasar.
13Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa, Daga wannan mulki zuwa wancan,
14Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba, Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.
15Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu, Kada ku cuci annabawana!”
16Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu, Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,
17Sai ya aika da Yusufu ya riga su zuwa, Shi wanda aka sayar da shi kamar bawa.
18Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarƙa, Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe,
19Har kafin faɗar da ya yi, ta cika. Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.
20Sa'an nan Sarkin Masar ya sake shi, Mai mulkin dukan sauran al'umma ya 'yantar da shi.
21Ya sa shi ya lura da mulkinsa, Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.
22Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma'aikatan hukuma. Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.
23Sa'an nan Yakubu ya tafi Masar, Ya zauna a ƙasar.
24Ubangiji ya sa jama'arsa suka hayayyafa da yawa, Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.
25Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa, Suka yi wa bayinsa munafunci.
26Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.
27Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah, Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.
28Ya aika da duhu a bisa ƙasar. Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.
29Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini, Ya karkashe kifayensu duka.
30Ƙasarsu ta cika da kwaɗi, Har a fādar sarki.
31Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwari Suka cika dukan ƙasar.
32Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsu Maimakon ruwan sama.
33Ya lalatar da 'ya'yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu, Ya kakkarya itatuwansu.
34Ya ba da umarni, sai fāri suka zo, Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.
35Suka cinye dukan tsire-tsire na ƙasa. Suka cinye dukan amfanin gonaki.
36Ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza Na dukan iyalan Masarawa.
37Sa'an nan ya bi da Isra'ilawa, suka fita, Suka kwashi azurfa da zinariya, Dukansu kuma ƙarfafa ne lafiyayyu.
38Masarawa suka yi murna da fitarsu, Gama sun tsoratar da su.
39Ya sa girgije ya yi wa jama'arsa inuwa, Da dare kuma wuta ta haskaka musu.
40Suka roƙa, sai aka ba su makware, Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.
41Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo, Yana gudu cikin hamada kamar kogi.
42Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki Wanda ya yi wa bawansa Ibrahim.
43Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa, Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.
44Ya ba su ƙasar baƙi, Ya sa su gāje gonakinsu,
45Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa, Su kuma kiyaye umarninsa. Ku yabi Ubangiji!
1Ku yabi Ubangiji! Ku yi wa Ubangiji godiya, gama nagari ne shi, Ƙaunarsa madawwamiya ce.
2Wa zai iya faɗar dukan manya manyan ayyuka da ya yi? Wa zai iya yi masa isasshen yabo>
3Masu farin ciki ne waɗanda suke biyayya da umarnansa, Waɗanda kullayaumi suke aikata abin da yake daidai!
4Ka tuna da ni sa'ad da za ka taimaki jama'arka, ya Ubangiji! Ka sa ni cikinsu, sa'ad da za ka cece su.
5Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka, In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu, In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.
6Mun yi zunubi yadda kakanninmu suka yi, Mugaye ne, mun aikata mugunta.
7Kakanninmu a Masar Ba su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba, Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu, Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.
8Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta, Domin ya nuna ikonsa mai girma.
9Ya tsauta wa Bahar Maliya, ta ƙafe, Har ya bi da jama'arsa su haye Kamar a bisa busasshiyar ƙasa.
10Ya cece su daga maƙiyansu, Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.
11Ruwa ya cinye maƙiyansu, Ba wanda ya tsira.
12Sa'an nan jama'arsa suka gaskata alkawarinsa, Suka raira yabo gare shi.
13Amma nan da nan, suka manta da abin da ya yi, Suka aikata, ba su jira shawararsa ba.
14Suka cika da sha'awa cikin hamada, Suka jarraba Allah,
15Sai ya ba su abin da suke roƙa, Amma ya aukar musu da muguwar cuta.
16Can cikin hamada suka ji kishin Musa Da Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,
17Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan, Ta binne Abiram da iyalinsa.
18Wuta ta sauko bisa magoya bayansu, Ta ƙone mugayen mutanen nan.
19Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb, Suka yi masa sujada.
20Suka musaya ɗaukakar Allah Da siffar dabba mai cin ciyawa.
21Suka manta da Allah wanda ya cece su, Ta wurin manyan ayyuka da ya yi a Masar.
22Kai, Allah ya aikata abubuwa masu ban al'ajabi a can! Ga kuma abubuwa masu banmamaki da ya aikata a Bahar Maliya!
23Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama'arsa, Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah, Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.
24Sai suka ƙi ƙasar nan mai ni'ima, Saboda ba su gaskata alkawarin Allah ba.
25Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni, Sun ƙi su saurari Ubangiji.
26Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi, Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,
27Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna, Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.
28Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor, Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.
29Suka tsokani Ubangiji, ya yi fushi saboda ayyukansu, Mugawar cuta ta auka musu,
30Amma Finehas ya tashi, ya yanke hukunci a kan laifin, Aka kuwa kawar da annobar.
31Tun daga lokacin nan ake ta tunawa da shi, Saboda abin da ya yi. Za a yi ta tunawa da shi a dukan zamanai masu zuwa.
32Jama'ar Ubangiji suka sa ya yi fushi. A maɓuɓɓugan Meriba, Musa ya shiga uku saboda su.
33Suka sa Musa ya husata ƙwarai, Har ya faɗi abubuwan da bai kamata ya faɗa ba.
34Suka ƙi su kashe arna, Yadda Ubangiji ya umarta,
35Amma suka yi aurayya da su, Suka kwaikwayi halayen arnan.
36Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada. Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.
37Suka miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.
38Suka karkashe mutane marasa laifi, Wato 'ya'yansu mata da maza. Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana, Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.
39Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu, Suka zama marasa aminci ga Allah.
40Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa, Ransa bai ji daɗinsu ba.
41Sai ya bar su ƙarƙashin ikon arna, Abokan gābansu suka mallake su.
42Abokan gābansu suka zalunce su, Suka tilasta su, su yi musu biyayya.
43Sau da yawa Ubangiji yakan ceci jama'arsa, Amma sun fi so su yi masa tawaye, Suna ta nutsawa can cikin zunubi.
44Duka da haka Ubangiji ya ji su sa'ad da suka yi kira gare shi, Ya kula da wahalarsu.
45Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa, Ya sāke ra'ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.
46Ubangiji ya sa waɗanda suka kama su Su ji tausayinsu.
47Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu, Ka komo da ma daga cikin sauran al'umma, Domin mu yabi sunanka mai tsarki, Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.
48Sai mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila, Mu yabe shi yanzu da har abada kuma! Dukan jama'a za su amsa su ce, “Amin! Amin!” Ku yabi Ubangiji!
LITTAFI NA BIYAR: Ubangiji ne Mai Kuɓutarwa daga Wahala (Zabura ta 107-150)
1Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce!
2Ku zo mu yabi Ubangiji tare, Dukanku waɗanda ya fansa, Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.
3Ya komo da ku daga ƙasashen waje, Daga gabas da yamma, kudu da arewa.
4Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya, Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.
5Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa, Suka fid da zuciya ga kome.
6Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
7Ya fisshe su, ya bi da su sosai, Zuwa birnin da za su zauna.
8Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!
9Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa, Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.
10Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa, 'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,
11Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki, Sun kuwa ƙi koyarwarsa.
12Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki, Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.
13A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
14Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa, Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.
15Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
16Ya kakkarya ƙofofin da aka yi da tagulla. Ya kuma ragargaza ƙyamaren da aka yi da baƙin ƙarfe.
17Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu, Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.
18Ba su so su ga abinci, Sun kusa mutuwa.
19A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.
20Da umarninsa ya warkar da su, Ya cece su daga kabari.
21Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
22Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu, Su raira waƙoƙin murna, Su faɗi dukan abin da ya yi!
23Waɗansu suka yi tafiya a teku da jirage, Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.
24Suka ga abin da Ubangiji ya aikata, Ayyukansa masu banmamaki waɗanda ya yi a tekuna.
25Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi, Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.
26Aka ɗaga jiragen ruwa sama, Sa'an nan suka tsinduma cikin zurfafa. Da mutanen suka ga irin hatsarin da suke ciki, Sai zuciyarsu ta karai.
27Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangaɗi kamar bugaggu, Gwanintarsu duka ta zama ta banza.
28Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabarsu.
29Ya sa hadiri ya yi tsit, Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.
30Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru, Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya, Wurin da suke so.
31Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa, Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
32Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama'a, Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.
33Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf, Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.
34Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani, Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.
35Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa, Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.
36Ya bar mayunwata su zauna a can, Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.
37Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi, Waɗanda suka ba da amfani mai yawan gaske.
38Ya sa wa jama'arsa albarka, Suka kuwa haifi 'ya'ya da yawa. Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.
39Sa'ad da aka ci nasara a kan jama'ar Allah, Aka ƙasƙantar da su ta wurin mugun zalunci, Da wahalar da aka yi musu.
40Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama'arsa. Ya sa su suka yi ta kai da kawowa A hamada inda ba hanya.
41Ya tsamo masu bukata daga cikin baƙin cikinsu, Ya sa iyalansu su riɓaɓɓanya kamar garkunan tumaki.
42Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna, Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.
43Da ma a ce masu hikima Za su yi tunani a kan waɗannan abubuwa, Da ma kuma su yarda Da madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.
(Zab 57.7-11; 60.5-12)
1A shirye nake, ya Allah, Na shirya sosai! Zan raira waƙa in yabe ka! Ka farka, ya raina!
2Ku farka, ya molona da garayata! Zan farkar da rana!
3Zan yi maka godiya a tsakiyar sauran al'umma, ya Ubangiji! Zan yabe ka a tsakiyar kabilai!
4Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai, Amincinka kuma ya kai sararin sammai.
5Ya Allah, ka bayyana girmanka a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata, Domin jama'ar da kake ƙauna ta sai cetonka.
7A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce, “Da nasara zan raba Shekem, Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.
8Gileyad tawa ce, har da Manassa ma, Ifraimu ne kwalkwalina, Yahuza kuma sandana ne na sarauta.
9Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki, Edom kuwa kamar akwatin takalmina. Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”
10Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara? Wa zai kai ni Edom>
11Da gaske ka yashe mu ke nan? Ba za ka yi tafiya Tare da sojojinmu ba>
12Ka taimake mu, mu yaƙi abokin gāba, Domin taimako irin na mutum banza ne!
13Idan Allah yana wajenmu, Za mu yi nasara, Zai kori abokan gābanmu.
1Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!
2Mugaye da maƙaryata sun tasar mini, Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.
3Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina. Suna tasar mini ba dalili.
4Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu, Har ina yi musu addu'a.
5Sukan sāka mini alheri da mugunta, Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.
6Ka zaɓi lalataccen mutum ya shara'anta maƙiyina, Ka sa ɗaya daga cikin maƙiyansa Ya gabatar da ƙararsa.
7Ka sa a same shi da laifi a shari'ar da ake yi masa, Ka sa har addu'ar da yake yi Ta zama babban laifi!
8Ka aukar masa da ajalinsa nan da nan, Ka sa wani ya ɗauki matsayinsa!
9Ka sa 'ya'yansa su zama marayu, Matarsa kuwa ta zama gwauruwa!
10Ka sa 'ya'yansa su rasa gidan zama, su riƙa yawon bara. Ka sa a kore su daga kufan da suke zaune!
11Ka sa waɗanda suke binsa bashi su kwashe Dukan abin da yake da shi. Ka sa baƙi su kwashe dukan abin da ya sha wahalar nema.
12Ka sa kada kowa ya yi masa alheri sam, Kada ka bar kowa ya lura da marayunsa.
13Ka sa dukan zuriyarsa su mutu, Har a manta da sunansa a tsara mai zuwa.
14Sai ka tuna, ya Ubangiji, da muguntar kakanninsa, Kada ka manta da zunuban mahaifiyarsa.
15Ka tuna da zunubansu kullayaumin, ya Ubangiji, Amma su kansu a manta da su ɗungum!
16Gama mutumin nan bai taɓa tunanin yin alheri ba, Yakan tsananta wa talakawa, da matalauta, da kasassu, har ya kashe su.
17Yana jin daɗin la'antarwa, ka sa a la'anta shi! Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!
18Yakan la'antar a sawwaƙe kamar yadda yake sa tufafinsa. Ka sa la'antarwa da yake yi Su jiƙa shi kamar ruwa, Su shiga har ƙasusuwansa kamar mai,
19Su lulluɓe shi kamar tufa, Su kuma kewaye shi kamar ɗamara.
20Ya Ubangiji, ka sa haka, Wato ya zama yadda za a hukunta wa maƙiyana ke nan, Waɗanda suke faɗar mugayen abubuwa a kaina!
21Amma ya Ubangiji, Allahna, ka taimake ni, Yadda ka alkawarta, Ka cece ni sabili da alherin ƙaunarka.
22Ni talaka ne, matalauci, Na ji zafi ƙwarai a can zuciyata.
23Na kusa ɓacewa kamar inuwar maraice, An hurar da ni can kumar ƙwaro.
24Gwiwoyina sun yi suwu saboda rashin abinci, Jikina kuma ya rame, ba shi da ƙarfi.
25Sa'ad da mutane suka gan ni sun yi mini ba'a, Suna kaɗa kai saboda raini.
26Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna, Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
27Ka sa maƙiyana su sani, Kai ne Mai Cetona.
28Watakila su la'anta ni, Amma kai za ka sa mini albarka, Ka sa a kori waɗanda suke tsananta mini. Da ma ka sa ni da nake bawanka, in yi murna.
29Ka sa kunya ta rufe maƙiyana, Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.
30Da murya mai ƙarfi zan yi wa Ubangiji godiya. Zan yabe shi a taron jama'a,
31Saboda yakan kāre talaka, Domin ya cece shi daga waɗanda Suka sa masa laifin mutuwa.
1Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”
2Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, “Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”
3A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.
4Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”
5Ubangiji yana damanka, Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.
6Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma, Ya rufe fagen fama da gawawwaki, Zai kori sarakunan duk duniya.
7Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya, Ya wartsake ya sami ƙarfi. Zai yi tsayawar nasara.
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Zan yi wa Ubangiji godiya da zuciya ɗaya, A cikin taron jama'arsa.
2Abubuwan banmamaki ne Ubangiji yake aikatawa! Duk waɗanda suke murna da su Suna so su fahimce su.
3Dukan abin da yake yi, Cike yake da girma da ɗaukaka, Adalcinsa har abada ne.
4Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba, Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.
5Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci, Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.
6Ya nuna ikonsa ga jama'arsa Saboda ya ba su ƙasashen baƙi.
7Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne. Dukan umarnansa, abin dogara ne.
8Sukan tabbata har abada, Da gaskiya da adalci aka ba da su.
9Ya kawo wa jama'arsa ceto, Ya kuma yi musu madawwamin alkawari. Mai Tsarki ne shi, Maɗaukaki!
10Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji, Yakan ba da kyakkyawar ganewa Ga dukan waɗanda suke bin umarnansa, Sai ku yabe shi har abada!
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa.
2'Ya'yansa za su zama manyan ƙasar, Zuriyar mutumin kirki za ta yi albarka.
3Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya, Adalcinsa zai tabbata har abada.
4Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu, Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya.
5Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake, Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.
6Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai, Ba za a taɓa mantawa da shi ba.
7Ba ya tsoron jin mugun labari, Bangaskiyarsa tana da ƙarfi, Ga Ubangiji yake dogara.
8Ba shi da damuwa ko tsoro, Ya tabbata zai ga fāɗuwar maƙiyansa.
9Yakan bayar ga matalauta hannu sake, Alherinsa kuwa dawwamamme ne. Zai zama mai iko wanda ake girmamawa.
10Sa'ad da mugaye suka ga wannan, Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace, Sa zuciyarsu ta ƙare har abada.
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku bayin Ubangiji, Ku yabi sunansa!
2Za a yabi sunansa yanzu da har abada!
3Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji!
4Ubangiji yake mulkin dukan sauran al'umma, Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai.
5Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu. Yana zaune a can ƙwanƙolin sama,
6Amma ya duba ƙasa, Ya dubi sammai da duniya.
7Yakan ɗaga talakawa daga ƙura, Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.
8Yakan sa su zama abokan sarakuna, Sarakunan jama'arsa.
9Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta, Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Sa'ad da jama'ar Isra'ila suka bar Masar, Sa'ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan,
2Yahuza ya zama tsattsarkar jama'ar Ubangiji, Isra'ila ya zama abin mallakarsa.
3Bahar Maliya da ya duba, sai ya gudu, Kogin Urdun ya daina gudu.
4Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki, Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki.
5Me ya faru ne, ya teku, da ya sa ki gudu? Kai fa Urdun, me ya sa ka daina gudu>
6Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki? Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle, Kuna kewayawa kamar tumaki>
7Ki yi rawar jiki, yake duniya, Saboda zuwan Ubangiji, A gaban Allah na Yakubu,
8Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa, Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai, Masu bulbulo da ruwa.
1A gare ka kaɗai, ya Ubangiji, A gare ka kaɗai, ba a gare mu ba, Dole a girmama ka, Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
2Me ya sa sauran al'umma suke tambayarmu, “Ina Allahnku?”
3Allahnmu yana Sama, Yana aikata yadda yake so.
4Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne, Da hannu aka siffata su.
5Suna da baki, amma ba sa magana, Suna da idanu, amma ba sa gani.
6Suna da kunnuwa, amma ba sa ji, Suna da hanci, amma ba sa jin ƙanshi.
7Suna da hannuwa, amma ba sa iya riƙon kome, Suna da ƙafafu, amma ba sa iya tafiya. Ba su da murya sam.
8Ka sa waɗanda suka yi su, Da dukan masu dogara gare su, Su zama kamar gumakan da suka yi!
9Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama'ar Isra'ila! Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
10Ku dogara ga Ubangiji, ya ku firistoci na Allah! Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
11Ku dogara ga Ubangiji, dukanku waɗanda kuke tsoronsa! Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
12Ubangiji yana tuna da mu, zai kuwa sa mana albarka, Zai sa wa jama'ar Isra'ila albarka, Da dukan firistoci na Allah.
13Zai sa wa dukan waɗanda suke tsoronsa albarka. Babba da yaro.
14Ubangiji ya ba ku 'ya'ya, Ku da zuriyarku.
15Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasa Ya sa muku albarka!
16Samaniya ta Ubangiji ce kaɗai, Amma ya ba mutane duniya.
17Matacce ba ya yabon Ubangiji, Ko wanda ya gangara zuwa cikin kabari.
18Amma mu da muke rayayyu, za mu yi masa godiya. A yanzu da har abada. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina, Yana kasa kunne ga addu'o'ina.
2Yakan kasa kunne gare ni, A duk lokacin da na yi kira gare shi.
3Mutuwa ta ɗaure ni da da igiyarta tam, Razanar kabari ta auka mini, Na cika da tsoro da alhini.
4Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”
5Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri, Allahnmu mai rahama ne.
6Ubangiji yakan kiyaye kāsassu, Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.
7Kada ki yi shakka, ya zuciyata, Gama Ubangiji yana yi mini alheri.
8Ubangiji ya cece ni daga mutuwa, Ya share hawayena, Bai bari a kāshe ni ba.
9Don haka nake tafiya a gaban Ubangiji A duniyar masu rai.
10Na dai yi ta gaskatawa, ko da yake Na ce, “An ragargaza ni sarai.”
11Sa'ad da na ji tsoro na ce, “Ba wanda za a iya dogara gare shi.”
12Me zan bayar ga Ubangiji Saboda sukan alheransa gare ni>
13Zan miƙa hadaya ta sha ga Ubangiji, Ina gode masa domin dā ya cece ni.
14Zan ba shi abin da na alkawarta A taron dukan jama'arsa.
15Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa, Abu mai daraja ne!
16Ni bawanka ne, ya Ubangiji, Ina bauta maka yadda mahaifiyata ta yi, Ka 'yantar da ni.
17Zan miƙa maka hadaya ta godiya, Zan yi addu'ata a gare ka. 18-19A taron dukan jama'arka, A shirayun Haikalinka, A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Ku yabi Ubangiji, ku dukan sauran al'ummai! Ku yabe shi, ku dukan kabilai!
2Madawwamiyar ƙaunarsa, da ƙarfi take, Amincinsa kuma tabbatacce ne har abada. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Ku gode wa Ubangiji, Domin shi mai alheri ne, Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.
2Bari jama'ar Isra'ila su ce, “Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
3Bari dukan firistoci na Allah su ce, “Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
4Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce, “Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
5A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji Ya kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.
6Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba. Me mutane za su iya yi mini>
7Ubangiji ne yake taimakona, Zan kuwa ga fāɗuwar maƙiyana da idona.
8Gwamma a dogara ga Ubangiji, Da a dogara ga mutane.
9Gwamma a dogara ga Ubangiji, Da a dogara ga shugabanni na mutane kawai.
10Maƙiya da yawa sun kewaye ni, Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!
11Suka kewaye ni a kowane gefe Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!
12Suka rufe ni kamar ƙudan zuma, Amma suka ƙone nan da nan kamar wutar jeji, Ta wurin ikon Ubangiji na hallaka su!
13Aka auko mini da tsanani, Har aka kore ni, Amma Ubangiji ya taimake ni.
14Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni, Shi ne Mai Cetona!
15Ku kasa kunne ga sowar murna ta nasara A cikin alfarwan jama'ar Allah. “Ikon Ubangiji mai girma ne ya aikata wannan!
16Ikonsa ne ya kawo mana nasara, Babban ikonsa a wurin yaƙi!”
17Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi, Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.
18Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani, Amma bai kashe ni ba.
19A buɗe mini ƙofofin Haikali, Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!
20Wannan ƙofar Ubangiji ce, Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!
21Ina yabonka, ya Ubangiji, domin ka ji ni, Domin ka ba ni nasara!
22Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani, Sai ya zama shi ya fi duka amfani.
23Ubangiji ne ya yi haka, Wannan kuwa abin banmamaki ne!
24Wace irin rana ce haka da Ubangiji ya ba mu! Bari mu yi farin ciki, mu yi biki!
25Ka cece mu, ya Ubangiji, ka cece mu! Ka ba mu nasara, ya Ubangiji!
26Allah yakan sa wa wanda ya zo da sunan Ubangiji albarka! Daga Haikalin Ubangiji muke yabonka!
27Ubangiji shi ne Allah, yana yi mana alheri, Ku ɗauki hadayunku ku yi ta idi, Ku ɗaura su a zankayen bagade.
28Kai ne Allahna, kai nake yi wa godiya, Zan yi shelar girmanka.
29Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne, Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.
1Masu farin ciki ne marasa laifi cikin zamansu, Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.
2Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa, Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.
3Hakika ba su yin laifi, Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.
4Kai ka ba mu dokokinka, Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.
5Na sa zuciya zan yi aminci, Game da kiyaye dokokinka!
6Idan na kula da dukan umarnanka, To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.
7Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya, A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.
8Zan yi biyayya da dokokinka, Ko kusa kada ka kashe ni!
9Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki? Sai ta wurin biyayya da umarnanka.
10Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka, Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!
11Na riƙe maganarka a zuciyata, Don kada in yi maka zunubi.
12Ina yabonka, Ya Ubangiji, Ka koya mini ka'idodinka!
13Zan ta da murya, In maimaita dukan dokokin da ka bayar.
14Ina murna da bin umarnanka, Fiye da samun dukiya mai yawa.
15Nakan yi nazarin umarnanka, Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.
16Ina murna da dokokinka, Ba zan manta da umarnanka ba.
17Ka yi mini alheri, ni bawanka, Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.
18Ka buɗe idona Domin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.
19Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne. Kada ka ɓoye mini umarnanka!
20Zuciyata ta ƙosa saboda marmari, A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.
21Kakan tsauta wa masu girmankai, La'anannu ne waɗanda suka ƙi bin umarnanka.
22Ka kuɓutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu, Domin na kiyaye dokokinka.
23Ko da sarakuna za su taru Su shirya mini maƙarƙashiya, Duka da haka, ni bawanka, Zan yi nazarin ka'idodinka.
24Umarnanka suna faranta mini rai, Su ne mashawartana.
25Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni, Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!
26Na hurta dukan abin da na aikata, ka kuwa amsa mini, Ka koya mini ka'idodinka!
27Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka, In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.
28Ɓacin rai ya ci ƙarfina, Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.
29Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya, Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.
30Na yi niyya in yi biyayya, Na mai da hankali ga ka'idodinka.
31Na bi umarnanka, ya Ubangiji, Kada ka sa in kasa ci wa burina!
32Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka, Gama za ka ƙara mini fahimi.
33Ka koya mini ma'anar dokokinka, ya Ubangiji, Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.
34Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita, Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.
35Ka bishe ni a hanyar umarnanka, Domin a cikinsu nakan sami fari ciki
36Ka sa ni in so yin biyayya da ka'idodinka, Fiye da samun dukiya.
37Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani, Ka yi mini alheri kamar yadda ka alkawarta.
38Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka, Irin wanda kakan yi wa waɗanda suke tsoronka.
39Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro, Ka'idodinka suna da amfani ƙwarai!
40Ina so in yi biyayya da umarnanka, Gama kai mai adalci ne, Ka yi mini alheri!
41Ka nuna mini yawan ƙaunar da kake yi mini, ya Ubangiji, Ka cece ni bisa ga alkawarinka.
42Sa'an nan zan amsa wa waɗanda suke cin mutuncina, Domin na dogara ga maganarka.
43Ka ba ni iko in iyar da saƙonka na gaskiya a kowane lokaci, Gama sa zuciyata tana ga hukuntanka.
44Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!
45Zan rayu da cikakken 'yanci, Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka'idodinka.
46Zan hurta umarnanka ga sarakuna, Ba kuwa zan ji kunya ba.
47Ina murna in yi biyayya da umarnanka, Saboda in ƙaunarsu.
48Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu, Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.
49Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka, Ka ƙarfafa zuciyata.
50Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni, Saboda alkawarinka yana rayar da ni.
51Masu girmankai suna raina ni, Amma ban rabu da dokarka ba.
52Na tuna da koyarwar da ka yi mini a dā, Sukan kuwa ta'azantar da ni, ya Ubangiji.
53Haushi ya kama ni sosai, Sa'ad da na ga mugaye suna keta dokarka.
54Ina zaune can nesa da gidana na ainihi, Sai na ƙago waƙoƙi a kan umarnanka.
55Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji, Ina kuwa kiyaye dokarka.
56Wannan shi ne farin cikina, In yi biyayya da umarnanka.
57Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji, Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.
58Ina roƙonka da zuciya ɗaya, Ka yi mini jinƙai kamar yadda ka alkawarta!
59Na yi tunani a kan ayyukana, Na yi alkawari in bi ka'idodinka.
60Ba tare da ɓata lokaci ba, Zan gaggauta in kiyaye umarnanka.
61Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi, Amma ba zan manta da dokarka ba.
62Da tsakar dare nakan farka, In yabe ka saboda hukuntanka masu adalci.
63Ina abuta da duk waɗanda suke bauta maka, Da duk waɗanda suke kiyaye dokokinka.
64Ya Ubangiji, duniya ta cika da madawwamiyar ƙaunarka, Ka koya mini umarnanka!
65Kana cika alkawarinka, ya Ubangiji, Kana kuwa yi mini alheri, ni bawanka.
66Ka ba ni hikima da ilimi Domin ina dogara ga umarnanka.
67Kafin ka hore ni nakan yi kuskure, Amma yanzu ina biyayya da maganarka.
68Managarci ne kai, mai alheri ne kuma, Ka koya mini umarnanka!
69Masu girmankai sun faɗi ƙarairayi a kaina, Amma da zuciya ɗaya nake biyayya da ka'idodinka.
70Waɗannan mutane ba su da ganewa, Amma ni ina murna da dokarka.
71Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.
72Dokar da ka yi Muhimmiya ce a gare ni, Fiye da dukan dukiyar duniya.
73Kai ne ka halicce ni, ka kuma kiyaye ni lafiya, Ka ba ni ganewa, don in koyi dokokinka.
74Waɗanda suke tsoronka za su yi murna sa'ad da suka gan ni, Saboda ina dogara ga alkawarinka.
75Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji, Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.
76Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta ta'azantar da ni, Kamar yadda ka alkawarta mini, ni bawanka.
77Ka yi mini jinƙai, zan rayu, Saboda ina murna da dokarka.
78Ka kunyatar da masu girmankai Saboda sun ba da shaidar zur a kaina, Amma ni, zan yi tunani a kan ka'idodinka.
79Ka sa waɗanda suke tsoronka su zo gare ni, Da waɗanda suka san umarnanka.
80Ka sa in yi cikakkiyar biyayya da umarnanka, Sa'an nan zan tsere wa shan kunyar fāɗuwa.
81Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni, Na dogara ga maganarka.
82Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka. Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”
83Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita, Duk da haka ban manta da umarnanka ba.
84Har yaushe zan yi ta jira? Yaushe za ka yi wa waɗanda suke tsananta mini hukunci>
85Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka, Sun haƙa wushefe don su kama ni.
86Umarnanka duka, abin dogara ne, Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi, Ka taimake ni!
87Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni, Amma ban raina ka'idodinka ba.
88Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri, Domin in yi biyayya da dokokinka.
89Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji, A kafe take a Sama.
90Amincinka ya tabbata har abada, Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.
91Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninka, Domin su duka bayinka ne.
92Da ba domin dokarka ita ce sanadin farin cikina ba, Da na mutu saboda hukuncin da na sha.
93Faufau ba zan raina ka'idodinka ba, Gama saboda su ka bar ni da rai.
94Ni naka ne, ka cece ni! Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.
95Mugaye suna jira su kashe ni, Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka.
96Na koya, cewa ba wani abu da yake cikakke, Amma umarninka ba shi da iyaka.
97Ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina ta tunani a kanta dukan yini.
98Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci, Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.
99Ganewata ta fi ta dukan malamaina, Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.
100Na fi tsofaffi hikima, Saboda ina biyayya da umarnanka.
101Nakan guje wa halin mugunta Saboda ina so in yi biyayya da maganarka.
102Ban raina koyarwarka ba Saboda kai ne ka koya mini.
103Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi, Har sun fi zuma zaƙi!
104Na ƙaru da hikima daga dokokinka, Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.
105Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni, Haske ne kuma a kan hanyata.
106Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.
107Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa, Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!
108Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji, Ka koya mini umarnanka.
109Kullum a shirye nake in kasai da raina, Ban manta da umarninka ba.
110Mugaye sun kafa mini tarko, Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.
111Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.
112Na ƙudura zan yi biyayya da ka'idodinka, Har ranar mutuwata.
113Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci, Amma ina ƙaunar dokarka.
114Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni, Ina sa zuciya ga alkawarinka.
115Ku rabu da ni, ku masu zunubi! Zan yi biyayya da umarnan Allahna.
116Ka ƙarfafa ni kamar yadda ka alkawarta, zan kuwa rayu, Kada ka bar ni in kasa ci wa burina!
117Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya, Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.
118Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka, Dabarunsu na yaudara banza ne.
119Kakan yi banza da duk mai mugunta, Don haka ina ƙaunar koyarwarka.
120Saboda kai, nake jin tsoro, Na cika da tsoro saboda shari'unka.
121Na yi abin da yake daidai mai kyau, Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!
122Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka, Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!
123Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka, Ceton da ka alkawarta.
124Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka, Ka koya mini umarnanka.
125Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa, Don in san koyarwarka.
126Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu, Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!
127Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya, Fiye da zinariya tsantsa.
128Saboda haka ina bin dukan koyarwarka, Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.
129Koyarwarka tana da ban al'ajabi, Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.
130Fassarar koyarwarka takan da ba haske, Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.
131Ina haki da baki a buɗe, Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.
132Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai, Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.
133Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta, Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.
134Ka cece ni daga waɗanda suke zaluntata, Domin in yi biyayya da umarnanka.
135Ka sa mini albarka da kasancewarka tare da ni, Ka koya mini dokokinka.
136Hawayena suna malalowa kamar kogi, Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.
137Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, Dokokinka kuma daidai ne,
138Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne, Daidai ne kuwa.
139Fushi yana cina kamar wuta, Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.
140Alkawarinka ba ya tashi! Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!
141Ni ba kome ba ne, rainanne ne, Amma ban ƙi kula da ka'idodinka ba.
142Adalcinka zai tabbata har abada, Dokarka gaskiya ce koyaushe.
143A cike nake da wahala da damuwa, Amma umarnanka suna faranta zuciyata.
144Koyarwarka masu adalci ne har abada, Ka ba ni ganewa domin in rayu.
145Ina kira gare ka da zuciya ɗaya, Ka amsa mini, ya Ubangiji, Zan yi biyayya da umarnanka!
146Ina kira gare ka, Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!
147Tun kafin fitowar rana ina kira gare ka neman taimako, Na sa zuciya ga alkawarinka.
148Dare farai ban yi barci ba, Ina ta bimbini a kan koyarwarka.
149Ka ji ni, ya Ubangiji, bisa ga madawwamiyar ƙaunarka, Ka kiyaye raina bisa ga alherinka!
150Mugayen nan waɗanda suke tsananta mini sun matso kusa, Mutanen da ba su taɓa kiyaye dokarka ba.
151Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji, Dukan alkawaranka gaskiya ne.
152Tuntuni na ji labarin koyarwarka, Ka sa su tabbata har abada.
153Ka dubi wahalata, ka cece ni, Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.
154Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni, Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
155Ba za a ceci mugaye ba, Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.
156Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji, Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.
157Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa, Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.
158Sa'ad da na dubi waɗannan maciya amana, Sai in ji ƙyama ƙwarai, Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.
159Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji! Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
160Cibiyar dokarka gaskiya ce, Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.
161Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili, Amma maganarka ce nake girmamawa.
162In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka, Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.
163Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu, Amma ina ƙaunar dokarka.
164A kowace rana nakan gode maka sau bakwai, Saboda shari'unka masu adalci ne.
165Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya, Ba wani abin da zai sa su fāɗi.
166Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji, Ina aikata abin da ka umarta.
167Ina biyayya da ka'idodinka, Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.
168Ina biyayya da umarnanka da koyarwarka, Kana kuwa ganin dukan abin da nake yi.
169Bari kukana ya kai gare ka, ya Ubangiji! Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.
170Bari addu'ata ta zo gare ka, Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
171Zan yabe ka kullayaumin Domin ka koya mini ka'idodinka.
172Zan raira waƙa a kan alkawarinka, Domin umarnanka a gaskiya ne.
173Kullum a shirye kake domin ka taimake ni, Saboda ina bin umarnanka.
174Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarka.
175Ka rayar da ni don in yabe ka, Ka sa koyarwarka su taimake ni!
176Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya, Ka zo ka neme ni, ni bawanka, Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.
1Sa'ad da nake shan wahala, Na yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa amsa mini.
2Ka cece ni, ya Ubangiji, Daga maƙaryata da masu ruɗi!
3Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku? Yaya zai hukunta ku>
4Da kibau masu tsini na mayaƙa, Da garwashin wuta zai hukunta ku!
5Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek, Ko tare da mutanen Kedar!
6Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!
7Sa'ad da nake maganar salama, Su sai su yi ta yaƙi.
1Na duba wajen duwatsu, Daga ina taimakona zai zo>
2Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
3Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
4Makiyayin Isra'ila, Ba ya gyangyaɗi ko barci!
5Ubangiji zai lura da kai, Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka.
6Ba za ka sha rana ba, Ko farin wata da dare.
7Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari, Zai sa ka zauna lafiya.
8Zai kiyaye shigarka da fitarka, Tun daga yanzu har abada.
1Na yi murna sa'ad da suka ce mini, “Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”
2Ga shi kuwa, mun iso, Muna tsaye a ƙofofin Urushalima!
3Urushalima birni ce wadda aka maido ta yadda take dā, Da kyakkyawan tsari, a shirye!
4A nan kabilai sukan zo, Kabilan Isra'ila, Domin su yi godiya ga Ubangiji, Kamar yadda ya umarce su.
5A nan majalisu suke, Wurin da sarki yake yi wa jama'arsa shari'a.
6Ku yi wa Urushalima addu'ar salama! “Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!
7Salama ta samu a garukanki, Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”
8Saboda abokaina da aminaina, Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”
9Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu, Ina addu'a domin ki arzuta.
1Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka, A Sama inda kake mulki.
2Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa, Baranya kuma ga uwargijiyarta, Hakanan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu, Har mu sami jinƙanka.
3Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, An gwada mana wulakanci matuƙa!
4Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a, Azzalumai masu girmankai sun raina mu!
1Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, Da me zai faru? Ba da amsa, ya Isra'ila!
2“Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,
3Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan, Saboda zafin fushi da suke yi da mu,
4Da rigyawa ta kwashe mu, Da ruwa yi ci mu,
5Kwararowar ruwa da nutsar da mu.”
6Sai mu gode wa Ubangiji, Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.
7Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta, Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!
8Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi wanda ya yi sama da duniya.
1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.
2Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima, Hakanan Ubangiji zai kewaye jama'arsa, Daga yanzu har abada.
3Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba, Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi.
4Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri, Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!
5Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu, Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta! Salama ta kasance tare da Isra'ila!
1Sa'ad da Ubangiji ya komar da mu cikin Sihiyona, Sai abin ya zama kamar mafarki!
2Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki, Sa'an nan sai sauran al'umma suka ambace mu, suka ce, “Ubangiji ya yi manyan al'amura masu girma, sabili da su!”
3Hakika ya aikata manyan al'amura sabili da mu, Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!
4Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmu Kamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,
5Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe, Su tattara albarkar kaka da farin ciki!
6Su waɗanda suka yi kuka a sa'ad da suka fita suna ɗauke da iri, Za su komo ɗauke da albarkar kaka, Suna raira waƙa don farin ciki!
1Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba, Aikin magina banza ne. Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba, Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.
2Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci, A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya, Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.
3'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, Albarka ce ta musamman.
4'Ya'ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsa Kamar kibau suke a hannun mayaƙi.
5Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa! Faufau ba za a ci nasara a kansa ba, Sa'ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari'a.
1Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!
2Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka, Za ka yi farin ciki ka arzuta.
3Matarka za ta zama kamar kurangar inabi Mai 'ya'ya a gidanka, 'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitun Suna kewaye da teburinka.
4Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya, Hakika za a sa masa albarka kamar haka.
5Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona! Ya sa ka ga Urushalima ta arzuta Dukan kwanakinka!
6Ya kuma sa ka ka ga jikokinka! Salama ta kasance ga Isra'ila!
1Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntar Da maƙiyanka suka tsananta maka da ita, Tun kana ƙarami!
2“Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta, Tun ina ƙarami, Amma ba su yi nasara da ni ba.
3Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana, Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.
4Amma Ubangiji mai adalci, Ya 'yantar da ni daga bauta.”
5Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona, A yi nasara da su a kuma kore su!
6Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye, Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.
7Ba wanda zai tattara ta, Ya ɗaure ta dami dami.
8Duk waɗanda suke wucewa a hanya ba za su ce, “Ubangiji ya sa maka albarka!” ba, Ko su ce, “Muna sa maka albarka da sunan Ubangiji!”
1A cikin fid da zuciyata, Na yi kira gare ka, ya Ubangiji.
2Ka ji kukana, ya Ubangiji, Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako!
3Idan kana yin lissafin zunubanmu, Wa zai kuɓuta daga hukunci>
4Amma kakan gafarta mana, Domin mu zama masu tsoronka.
5Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji, Ga maganarsa na dogara.
6Ina jiran Ubangiji, Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir, I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir.
7Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji, Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce, A koyaushe yana da nufin yin gafara.
8Zai fanshi jama'arsa Isra'ila Daga dukan zunubansu.
1'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai, Na bar yin fāriya, Ba ruwana da manyan al'amura, Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.
2Amma na haƙura, raina a kwance, Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa, Haka zuciyata take kwance.
3Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji, Daga yanzu har abada!
1Ya Ubangiji, kada ka manta da Dawuda Da dukan irin aikin da ya yi.
2Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi, Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra'ila,
3“Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,
4Ba zan huta, ko in yi barci ba,
5Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri, Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra'ila.”
6Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami, Amma muka same shi a kurmi.
7Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji, Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”
8Ka zo wurin hutawarka, ya Ubangiji, Tare da akwatin alkawari, Alama ce ta ikonka.
9Ka suturta firistoci da adalci, Ka sa dukan jama'arka su yi sowa ta farin ciki!
10Ka yi wa bawanka Dawuda alkawari, Kada ka rabu da zaɓaɓɓen sarkinka, ya Ubangiji!
11Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari, Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba. Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza ya zama sarki, Zai yi mulki a bayanka.
12Idan 'ya'yanka maza za su amince da alkawarina, Da umarnan da na yi musu, 'Ya'yansu maza kuma za su bi bayanka su zama sarakuna, A dukan lokaci.”
13Ubangiji za yaɓi Sihiyona, A can yake so ya gina Haikalinsa, ya ce,
14“A nan zan zauna har abada. A nan kuma nake so in yi mulki.
15Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace, Zan ƙosar da matalautanta da abinci.
16Zan sa firistocinta su yi shela, Cewa ina yin ceto, Jama'ata kuma za su raira waƙa, Suna sowa don farin ciki.
17A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda Ya zama babban sarki, A nan ne kuma zan wanzar da Mulkin zaɓaɓɓen sarkina.
18Zan sa maƙiyansa su sha kunya, Amma mulkinsa zai arzuta. Ya kuma kahu.”
1Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!
2Yana kama da man zaitun mai daraja, Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa, Har zuwa wuyan riganunsa.
3Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon, Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona. A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa, Rai na har abada.
1Ku zo mu yabi Ubangiji, Dukanku bayinsa, Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima, A cikin Haikalinsa da dare.
2Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu'a a Haikali, Ku yabi Ubangiji!
3Ubangiji wanda ya yi sama da duniya, Ya sa muku albarka daga Sihiyona.
1Ku yabi Ubangiji! Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,
2Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji, A wuri mai tsarki na Allahnmu.
3Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi, Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.
4Ya zaɓar wa kansa Yakubu, Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.
5Na sani Ubangijinmu mai girma ne, Ya fi dukan alloli girma.
6Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya, A tekuna, da kuma zurfafan da ke ƙarƙas.
7Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya, Yakan yi walƙiya domin hadura, Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.
8A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.
9A can ne ya aikata mu'ujizai da al'ajabai, Domin ya hukunta Fir'auna da dukan hukumar ƙasarsa.
10Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa, Ya karkashe sarakuna masu iko, wato
11Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan, Da dukan sarakunan Kan'ana.
12Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa, Ya ba da ita ga Isra'ila.
13Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah, Dukan tsararraki za su tuna da kai.
14Ubangiji zai ji juyayin mutanensa, Zai 'yantar da bayinsa.
15Gumakan al'ummai, da azurfa da zinariya aka yi su, Hannuwan mutane ne suka siffata su.
16Suna da bakuna, amma ba sa magana, Da idanu, amma ba sa gani.
17Suna da kunnuwa, amma ba sa ji, Ba kuma numfashi a bakinsu.
18Ka sa su waɗanda suka yi su, Da dukan waɗanda suke dogara gare su, Su zama kamar gumakan da suka yi!
19Ku yabi Ubangiji, ya jama'ar Isra'ila, Ku yabe shi, ya ku firistocin Allah!
20Ku yabi Ubangiji, ya ku Lawiyawa, Ku yabe shi, dukanku da kuke tsoronsa!
21Ku yabi Ubangiji a Sihiyona da a Urushalima, wato a Haikalinsa. Ku yabi Ubangiji!
1Ku gode wa Ubangiji domin shi mai alheri ne, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
2Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
3Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
4Shi kaɗai ne yake aikata mu'ujizai masu girma, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
5Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
6Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
7Shi ne ya halicci rana da wata, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
8Rana don ta yi mulkin yini, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
9Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
10Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
11Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
12Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
13Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
14Shi ya bi da jama'arsa ta cikin tekun, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
15Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
16Ya bi da jama'arsa cikin hamada, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
17Ya karkashe sarakuna masu iko, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
18Ya karkashe shahararrun sarakuna, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
19Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
20Ya kashe Og, Sarkin Bashan, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
21Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
22Ya ba da ita ga bawansa Isra'ila, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
23Bai manta da mu sa'ad da aka yi nasara da mu ba, Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.
24Ya 'yantar da mu daga abokan gābanmu, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
25Yana ba da abinci ga dukan mutane da dabbobi, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
26Ku yi wa Allah sa Sama godiya, Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.
1A bakin kogunan Babila Muka zauna muka yi ta kuka, Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.
2A rassan itatuwan wardi da suke kusa da mu Muka rataye garayunmu.
3Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa, Suka ce mana, “Ku yi mana shagali Da waƙar da aka raira wa Sihiyona!”
4Kaƙa za mu raira waƙar Ubangiji A baƙuwar ƙasa>
5Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya, Idan na manta da ke, Urushalima!
6Da ma kada in ƙara iya raira waƙa, Idan na manta da ke, Idan ban tuna ke ce Babbar abar farin ciki ba!
7Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!”
8Babila, za a hallaka ki! Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki Bisa ga abin da kika yi mana.
9Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jariranki Yi fyaɗa su a kan duwatsu!
1Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji, Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.
2Na durƙusa a gaban tsattsarkan Haikalinka Ina yabon sunanka. Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka, Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.
3Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka, Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.
4Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji, Gama sun riga sun ji alkawaranka.
5Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi, Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.
6Ko da yake Ubangiji yana can Sama, Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici. Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.
7Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata, Za ka kuwa cece ni da ikonka.
8Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini, Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada. Ka cikasa aikin da ka fara.
1Ya Ubangiji, ka jarraba ni, ka san ni.
2Ka sa dukan abin da nake yi, Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.
3Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa, Ka san dukan ayyukana.
4Tun kafin in yi magana Ka riga ka san abin da zan faɗa.
5Kana kewaye da ni a kowane sashe, Ka kiyaye ni da ikonka.
6Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana, Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.
7Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka? Ina zan gudu in tsere maka>
8Idan na hau cikin samaniya kana can, In na kwanta a lahira kana can,
9In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas, Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,
10Kana can domin ka bi da ni, Kana can domin ka taimake ni.
11Da na iya roƙon duhu ya ɓoye ni, Ko haske da yake kewaye da ni Ya zama dare,
12Amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka, Dare kuwa haskensa kamar na rana ne. Duhu da haske, duk ɗaya ne gare ka.
13Kai ne ka halicci kowace gaɓa ta jikina, Kai ne ka harhaɗa ni a cikin mahaifiyata.
14Ina yabonka gama kai abin tsoro ne, Dukan abin da ka yi sabo ne, mai banmamaki. Da zuciya ɗaya na san haka ne.
15Ka ga lokacin da ƙasusuwana suke siffatuwa, Sa'ad da kuma ake harhaɗa su a hankali A cikin mahaifiyata, Lokacin da nake girma a asirce.
16Ka gan ni kafin a haife ni. Ka ƙididdige kwanakin da ka ƙaddara mini, Duka an rubuta su a littafinka, Tun kafin faruwar ko wannensu.
17Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni, Ba su da iyaka!
18In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi, Sa'ad da na farka, har yanzu ina tare da kai.
19Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye! 'Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!
20Suna ambaton mugayen abubuwa a kanka, Suna faɗar mugayen abubuwa gāba da sunanka.
21Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka, Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!
22Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha, Na ɗauke su, su abokan gābana ne.
23Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina, Gwada ni, ka gane damuwata.
24Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni, Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.
1Ka cece ni daga mugaye, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni daga mutane masu hargitsi.
2Kullum suna shirya mugunta, Kullum suna kawo tashin hankali.
3Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi, Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.
4Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali, Waɗanda suke shirya fāɗuwata.
5Masu girmankai sun kafa mini tarko, Sun shimfiɗa ragar igiya, Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
6Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna. Ka ji kukana ne neman taimako, ya Ubangiji!
7Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi, Kā kiyaye ni cikin yaƙi.
8Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu, Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!
9“Kada ka bar maƙiyana su sami nasara, Ka sa kashedin da suke yi mini ya koma kansu.
10Ka sa garwashin wuta ya zubo a kansu, Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.
11Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace, Kada su yi nasara. Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”
12Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa, Da hakkin matalauta.
13Hakika adalai za su yabe ka, Za su zauna a gabanka.
1Ina kira gare ka, ya Ubangiji, Ka taimake ni yanzu! Ka saurare ni sa'ad da na kira gare ka.
2Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa, Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.
3Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina, Ka sa mai tsaro a leɓunana.
4Ka tsare ni daga son yin mugunta, Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu, Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu!
5Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.
6Mutane za su yarda, cewa maganata gaskiya ce, Sa'ad da aka jefo da masu mulkinsu ƙasa, daga ƙwanƙolin dutse,
7Kamar itacen da aka faskare, aka daddatse, Haka aka watsar da ƙasusuwansu a gefen kabari.
8Amma ni, ya Ubangiji Allah, da nake dogara a gare ka, Ina neman kiyayewarka, Kada ka bar ni in hallaka!
9Ka kiyaye ni daga tarkunan da suka kafa mini, Daga ashibtar masu aikata mugunta.
10Ka sa mugaye su fāɗa cikin tarkunansu, Ni kuwa in zo in wuce lafiya.
1Ina kira ga Ubangiji don neman taimako, Ina roƙonsa.
2Na kawo masa dukan koke-kokena, Na faɗa masa dukan wahalaina.
3Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya, Ya san abin da zan yi. A kan hanyar da zan bi Maƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.
4Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni, Ba wanda zai kiyaye ni, Ba kuwa wanda ya kula da ni.
5Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako, Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni, Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.
6Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako, Gama na nutsa cikin fid da zuciya. Ka cece ni daga maƙiyana Waɗanda suka fi ƙarfina.
7Ka cece ni daga cikin wahalata, Sa'an nan zan yabe ka cikin taron jama'arka, Domin ka yi mini alheri.
1Ya Ubangiji ka ji addu'ata, Ka kasa kunne ga roƙona! Kai adali ne mai aminci, Don haka ka amsa mini!
2Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a, Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.
3Maƙiyina ya tsananta mini, Ya kore ni fata-fata. Ya sa ni a kurkuku mai duhu, Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa,
4Don haka ina niyya in fid da zuciya, Ina cikin damuwa mai zurfi.
5Na tuna kwanakin baya, Na tuna da dukan abin da ka yi, Na tuna da dukan ayyukanka.
6Na ɗaga hannuwana sama, ina addu'a gare ka, Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka.
7Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji! Na fid da zuciya duka! Kada ka ɓuya mini, Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.
8A gare ka nake dogara, Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka. Addu'ata ta hau zuwa gare ka, Ka nuna mini hanyar da zan bi.
9Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji, Ka cece ni daga maƙiyana.
10Kai ne Allahna, Ka koya mini in aikata nufinka. Ka sa in sami alherin Ruhunka. Ka bi da ni a hanyar lafiya.
11Ka cece ni, ya Ubangiji, kamar yadda ka alkawarta. Saboda alherinka ka tsamo ni daga wahalaina!
12Saboda ƙaunar da kake yi mini, Ka kashe maƙiyana. Ka hallakar da dukan waɗanda suke zaluntata. Gama ni bawanka ne.
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji, mai kiyaye ni, Ya hore ni don yaƙi, Ya kuwa shirya ni don yaƙi.
2Shi yake kiyaye ni, Shi yake kāre ni, Shi ne mafakata da Mai Cetona, Wanda nake dogara gare shi Don samun zaman lafiya. Shi ne ya ɗora ni a kan al'ummai.
3Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi? Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi>
4Shi kamar hucin iska yake, Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.
5Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko, Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.
6Ka aiko da walƙiyar tsawa ta warwatsa maƙiyanka, Ka harba kibanka, ka sa su sheƙa a guje!
7Ka sunkuyo daga Sama, Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni, Ka cece ni daga ikon baƙi,
8Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba, Sukan yi rantsuwar ƙarya.
9Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah, Zan kaɗa garaya in raira maka waƙa.
10Ka ba sarakuna nasara, Ka kuma ceci bawanka Dawuda.
11Ka cece ni daga mugayen abokan gābana, Ka ƙwato ni daga ikon baƙi, Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba, Sukan yi rantsuwar ƙarya.
12Ka sa 'ya'yanmu maza waɗanda suke cikin samartaka, Su zama kamar itatuwan da suke girma da ƙarfi. Ka sa 'ya'yanmu mata Su zama kamar al'amudai, Waɗanda suke adanta kusurwoyin fāda.
13Ka sa rumbunanmu su cika Da kowane irin amfanin gona. Ka sa tumakin da yake cikin saurukanmu Su hayayyafa dubu dubu har sau goma,
14Ka sa shanunmu su hayayyafa, Kada su yi ɓari ko su ɓace. Ka sa kada a ji kukan damuwa a kan titunanmu!
15Mai farin ciki ce al'ummar Da abin nan da aka faɗa ya zama gaskiya a gare ta. Masu farin ciki ne jama'ar da Allahnsu shi ne Ubangiji!
1Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina, Zan yi maka godiya har abada abadin.
2Kowace rana zan yi maka godiya, Zan yabe ka har abada abadin.
3Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa, Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.
4Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara, Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.
5Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka, Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
6Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka, Ni kuwa zan yi shelar girmanka.
7Za su ba da labarin girmanka duka, Su kuma raira waƙa a kan alherinka.
8Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar ƙauna.
9Shi mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin dukan abin da ya halitta.
10Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka, Jama'arka kuma za su yi maka godiya!
11Za su yi maganar darajar mulkinka, Su ba da labarin ikonka,
12Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka, Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.
13Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada.
14Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda suke shan wahala, Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.
15Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,
16Yana kuwa ba su isasshe, Yakan biya bukatarsu duka.
17Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka, Mai jinƙai ne a ayyukansa duka.
18Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi, Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.
19Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa, Yakan ji kukansu, ya cece su.
20Yakan kiyaye dukan waɗanda suke ƙaunarsa, Amma zai hallaka mugaye duka.
21A kullum zan yabi Ubangiji, Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada!
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ka yabi Ubanigji, ya raina!
2Zan yabe shi muddin raina. Zan raira waƙa ga Allahna dukan kwanakina.
3Kada ka dogara ga shugabanni, Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba.
4Sa'ad da suka mutu sai su koma turɓaya, A wannan rana dukan shirye-shiryensu sun ƙare.
5Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa,
6Wanda ya halicci sama, da duniya, da teku, Da dukan abin da yake cikinsu. Kullum yakan cika alkawaransa.
7A yanke shari'arsa yakan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan kuɓutar da ɗaurarru.
8Yakan ba makafi ganin gari. Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta. Yana ƙaunar jama'arsa, adalai.
9Yakan kiyaye baƙi waɗanda suke zaune a ƙasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye.
10Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamanai! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Abu mai kyau ne mu yabi Allahnmu, Abu mai daɗi ne, daidai ne kuma, a yabe shi.
2Ubangiji yana rayar da Urushalima, Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.
3Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya, Yakan ɗaure raunukansu.
4Ya ƙididdige yawan taurari, Yakan kira kowanne da sunansa.
5Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka, Saninsa ya fi gaban aunawa.
6Yakan ɗaukaka masu tawali'u, Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.
7Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji, Ku yabi Allah da garaya.
8Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi. Ya tanada wa duniya ruwan sama, Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.
9Yakan ba dabbobi abincinsu, Yakan ciyar da 'ya'yan hankaki sa'ad da suka yi kuka gare shi.
10Ba ya jin daɗin ƙarfafan dawakai, Ba ya murna da jarumawan mayaƙa.
11Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa, Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.
12Ya Urushalima, ki yabi Ubangiji, Ya Sihiyona, ki yabi Allahnki.
13Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi, Yakan sa wa jama'arki albarka.
14Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya, Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
15Yakan ba da umarni, Nan da nan umarnin yakan iso duniya.
16Yakan aiko da dusar ƙanƙara mai kauri kamar ulu, Ya watsa jaura kamar ƙura.
17Yakan aiko da ƙanƙara kamar duwatsu, Ba wanda yake iya jurewa da sanyin da yakan aiko!
18Sa'an nan yakan ba da umarni, Ƙanƙara kuwa ta narke, Yakan aiko da iska, ruwa kuwa yakan gudu.
19Yana ba Yakubu saƙonsa, Koyarwarsa da dokokinsa kuma ga Isra'ila.
20Bai yi wa sauran al'umma wannan ba, Domin ba su san dokokinsa ba. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji daga sama, Ku da kuke zaune a tuddan sama.
2Ku yabe shi dukanku mala'ikunsa, Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!
3Ku yabe shi, ku rana da wata, Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!
4Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi duka! Ku yabe shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama!
5Bari su duka su yabi sunan Ubangiji! Ya umarta, sai suka kasance.
6Ta wurin umarninsa aka kafa su A wurarensu har abada, Ba su kuwa da ikon ƙi.
7Ku yabi Ubangiji daga duniya, Ku yabi Ubangiji, ku dodanin ruwa da dukan zurfafan teku.
8Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara, Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!
9Ku yabe shi, ku tuddai da duwatsu, Da itatuwa 'ya'ya da kurama.
10Ku yabe shi dukanku dabbobi, na gida da na jeji, Masu rarrafe da tsuntsaye!
11Ku yabe shi, ku sarakuna da dukan kabilai, Ku yabe shi, ku shugabanni da dukan hukumomi.
12Ku yabe shi ku samari da 'yan mata! Ku yabe shi, ku tsoffafi da yara!
13Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji, Sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma, Ɗaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!
14Ya sa al'ummarsa ta yi ƙarfi, Domin dukan jama'arsa su yabe shi Jama'arsa Isra'ila, wadda yake ƙauna ƙwarai! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji Ku yabe shi cikin taron jama'arsa masu aminci!
2Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki, Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!
3Ku yabi sunansa, kuna taka rawa, Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa.
4Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa, Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara.
5Bari jama'ar Allah su yi farin ciki saboda cin nasararsu, Su raira waƙa don farin ciki.
6Bari su yi sowa da ƙarfi Sa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.
7Don su ci nasara bisa al'ummai, Su kuma hukunta wa jama'a,
8Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi, Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,
9Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta. Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa! Ku yabi ƙarfinsa a sama!
2Ku yabe shi saboda manyan abubuwa Waɗanda ya aikata! Ku yabi mafificin girmansa!
3Ku yabe shi da kakaki! Ku yabe shi da garayu da molaye!
4Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa! Ku yabe shi da garayu da sarewa!
5Ku yabe shi da kuge! Ku yabe shi da kuge masu amo!
6Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!