Romans
1Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah, 2wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa a cikin Littattafai masu tsarki. 3Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne, 4amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu. 5Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya, 6a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu. 7Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
8Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya. 9Domin kuwa Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu'ata, 10ina addu'a, ko ta ƙaƙa, da yardar Allah, a yanzu kam, in sami arzikin zuwa wurinku. 11Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa. 12Wato ni da ku, mu ƙarfafa juna ta bangaskiyarmu, tawa da taku. 13Ina so ku sani 'yan'uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da yake har yanzu ba a yardar mini ba, domin ku ma in sami amfani a gare ku, kamar yadda na samu a cikin al'ummai. 14Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina. 15Saboda haka a gwargwadon iyawata, ina da himma ku ma in yi muku bisharar, ku da kuke a Roma.
16Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai. 17Gama bishara ɗin ta bayyana wata hanyar samun adalci a gaban Allah, hanyar nan kuwa ta bangaskiya ce, tun daga farko har zuwa ƙarshe, yadda yake a rubuce cewa, “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”
18Gama ana bayyana fushin Allah daga Sama, a kan dukan rashin bin Allah, da aikin mugunta na mutanen da suke danne gaskiya, ta aikin muguntarsu, 19Domin abin da za a iya sani a game da Allah a bayyane yake a gare su, gama Allah ne ya bayyana musu shi. 20Gama tun daga halittar duniya al'amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari. 21Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta. 22Suna da'awa cewa, su masu hikima ne, sai suka zama wawaye. 23Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.
24Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha'awace-sha'awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu, 25saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.
26Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram. 27Haka kuma maza suka bar ma'amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
28Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya. 29Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne, 30da masu yanke, da maƙiyan Allah, da masu cin mutunci, da masu girmankai, da masu ruba, da masu haddasa mugunta, da marasa bin iyaye, 31da marasa fahimta, da masu ta da alkawari, da marasa ƙauna, da marasa tausayi. 32Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.
1Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi. 2Mun dai san hukuncin Allah a kan masu yin haka daidai ne. 3Ya kai mutum, kai da kake ganin laifin masu yin haka, alhali kuwa kai kanka, kana yinsu, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba? 5Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani. 6Allah ne zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa. 7Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami. 8Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda ke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala. 9Duk waɗanda suke aikata mugunta za su sha wahala da masifa, da fari Yahudawa, sa'an nan kuma al'ummai. 10Amma Allah zai ba da daraja, da ɗaukaka, da salama ga dukan waɗanda suke aikata nagarta, da fari ga Yahudawa, sa'an nan ga al'ummai. 11Domin kuwa, Allah ba ya nuna tara.
12Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a rashin sanin Shari'a, za su hallaka na ba tare da Shari'a ba. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a ƙarƙashin Shari'a kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari'a. 13Don ba ta jin shari'ar kawai mutum yake samun kuɓuta ga Allah ba, sai dai masu aikata ta, su ne za su kuɓuta. 14In al'ummai, su da ba su da Shari'a, jikinsu ya ba su suka bi umarnin Shari'a, ko da yake ba su da Shari'ar, ashe kuwa, suna da shari'a ke nan. 15Ayyukansu sun nuna, cewa abin da Shari'a ta umarta a rubuce yake a cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaidawa, tunaninsu kuwa yana zarginsu, ko kuma yana kāre su. 16A wannan rana Allah zai yi wa 'yan adam shari'a a kan asiransu, ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga bishara da nake wa'azinta.
17To, in ka ce kai Bayahude ne, cewa ka dogara da Shari'a, har kana taƙama da Allah, 18ka san abin da yake so, da ya ke kuma ka karantu da Shari'a, ka iya bambancewa da abubuwa mafifita, 19har ka amince kai kanka jagoran makafi ne, haske ga waɗanda suke a cikin duhu, 20mai horon marasa azanci, mai koya wa sababbin shiga, don a cikin Shari'ar kana da ainihin sani da ainihin gaskiya, 21to, kai mai koya wa wani, ba ka koya wa kanka? Kai mai wa'azin kada a yi sata, shin, kai ba ka yi ne? 22Kai mai cewa kada a yi zina, kai ba ka yi ne? Kai mai ƙyamar gumaka, ba ka sata a ɗakin gunki ne? 23Kai mai taƙama da Shari'a, ashe, ba wulakanta Allah kake yi ba ta keta Shari'ar? 24Yadda yake a rubuce cewa, “A sanadinku ne al'ummai suke saɓon sunan Allah.”
25Lalle yin kaciya yana da amfani, in dai kana bin Shari'ar. Amma in kai mai keta shari'ar ne, kaciyarka ba a bakin kome take ba. 26In kuwa marar kaciya yana kiyaye farillan Shari'a, ashe, ba sai a lasafta rashin kaciyarsa a kan kaciya ba? 27Ashe, wanda rashin kaciya al'adarsa ce, ga shi kuwa, yana bin Shari'ar daidai, ba sai ya kāshe ka ba, kai da kake da Shari'a a rubuce da kuma kaciya, amma kana keta Shari'ar? 28Gama Bayahude na ainihi ba mutum ne wanda yake Bayahude bisa siffar jikinsa na fili ba, kaciya ta ainihi kuwa ba kaciya ce ta fili ta fatar jiki ba. 29Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.
1To, ina fifikon Bayahude? Ko kuma ina fa'idar kaciya? 2Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah. 3To, ƙaƙa ke nan in waɗansu sun ci amanar nan? Sai cin amanarsu ya shafe cikar alkawarin Allah? 4A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa, “Don maganarka tă tabbatar da adalcinka, Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”
5In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? In Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.) 6A'a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari'a? 7In kuwa, a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka kara ɗaukaka shi, to, don me har yanzu ake hukunta ni a kan ni mai zunubi ne? 8In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana yanke, cewa haka muke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.
9To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A'a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al'ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su. 10Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,
11Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
12Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya, Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”
13“Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne, Maganarsu ta yaudara ce.” “Masu ciwon baki ne.”
14“Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.” 15“Masu hanzarin zub da jini ne, 16Ta ko'ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki, 17Ba su kuma san hanyar salama ba.” 18“Babu tsoron Allah a cikin sha'aninsu sam.”
19To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take. 20Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.
21A yanzu, ba kuwa a game da shari'a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa suke yi wa shaida. 22Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci, 23gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah. 24Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi. 25Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin ya nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar, 26domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.
27To, ina kuma fariyarmu ta shiga? Ina kuwa! Ta wace hanya aka kawar da ita? Ta aikin lada? A'a, sai dai ta hanyar bangaskiya. 28Domin mun amince, cewa ta bangaskiya ne mutum yake kuɓuta, ba ta kiyaye ayyukan Shari'a ba. 29Wato Allah, Allahn Yahudawa ne kurum? Ashe, ba na al'ummai ba ne kuma? Hakika na al'ummai ne ma, 30tun da yake Allah ɗaya ne, zai kuwa kuɓutar da masu kaciya ta wurin bangaskiya, marasa kaciya ma ta wannan bangaskiya. 31Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.
1To, me ke nan za mu ce a game da Ibrahim, kakan kakanninmu? 2Gama in da Ibrahim ya sami kuɓuta ta aikinsa na lada, ashe kuwa, yana da abin yin taƙama ke nan, amma fa ba a gaban Allah ba. 3To, me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi.” 4Wanda yake aikin lada, ladarsa ba kyauta ba ce, sakamakon aikinsa ce. 5Wanda ba ya aikin lada, amma yana dogararsa ga Allah, wanda yake kuɓutar da masu laifi, akan lasafta bangaskiyar nan tasa adalci ce. 6Haka kuma Dawuda ya yi maganar albarkar da aka yi wa mutumin da Allah yake lasafta adalci a gare shi, ba don ya yi aikin lada ba, 7da ya ce, “Albarka tā tabbata ga waɗanda aka yafe wa laifofinsu, Waɗanda kuma aka shafe zunubansu,
8Albarka tā tabbata ga wanda faufau Ubangiji ba zai lasafta zunubansa ba.”
9To, wannan albarka, masu kaciya ne kawai ake yi wa, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Gama abin da muke cewa shi ne, “Aka lasafta bangaskiyar Ibrahim adalci ce a gare shi.” 10To, a cikin wane hali aka lasafta masa ita? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa tun ba a yi ba? Ai, tun ba a yi ba ne, ba bayan da aka yi ba. 11Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba, 12haka kuma yă zama uban masu kaciya, waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba, har ma suna bin hanyar bangaskiyar nan ta kakanmu Ibrahim, wadda shi ma ya bi, tun ba a yi masa kaciya ba.
13Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa, cewa zai zama magājin duniya, ba ta Shari'a aka yi masa ba, amma domin ya ba da gaskiya ne, shi ya sa Allah ya karɓe shi mai adalci ne. 14In dai masu bin Shari'a su ne magāda, ashe, bangaskiya ta zama banza ke nan, alkawarin nan kuma ya wofinta, 15don Shari'a tana jawo fushin Allah. A inda ba Shari'a kuwa, ba keta umarni ke nan.
16Saboda haka al'amarin ya dogara ga bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri, don kuma a tabbatar da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari'a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda suke da bangaskiya irin Ibrahim, shi da yake ubanmu duka. 17Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na sa ka uban al'ummai da yawa.” Shi ne kuwa ubanmu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato mai raya matattu, shi ne kuma mai kiran marasa kasancewa kamar sun kasance. 18Ibrahim kuwa ko da yake ba halin sa zuciya a gare shi, sai ya yi ta sawa, ya gaskata zai zama uban al'ummai da yawa, kamar yadda aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za ta yawaita.” 19Bangaskiyarsa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi gajiyawar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haihuwa. 20Ba kuwa wata rashin bangaskiyar da ta sa shi shakkar cikar alkawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa ya yi, yana ɗaukaka Allah, 21yana haƙƙaƙewa, cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alkawari. 22Shi ya sa aka lasafta bangaskiyarsa adalci ce a gare shi. 23To, “Lasafta masa” ɗin nan da aka rubuta kuwa, ba saboda Ibrahim kaɗai aka rubuta ba, 24har saboda mu ma, za a lasafta mana, wato mu da muke gaskatawa da wannan da ya ta da Yesu Ubangijinmu daga matattu, 25wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi, domin mu sami kuɓuta ga Allah.
1To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu. 2Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah. 3Banda haka ma, har muna taƙama da shan wuyarmu, da yake mun sani shan wuya take sa jimiri, 4jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya, 5ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.
6Tun muna raunana tukuna, Almasihu ya mutu a daidaitaccen lokaci, domin marasa bin Allah. 7Da ƙyar za a sami wanda zai ba da ransa, saboda mutum mai adalci, ko da yake watakila saboda mutum mai nagarta wani ma sai ya yi kasai da ransa. 8Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu. 9To, tun da yake a yanzu an kuɓutar da mu ta wurin jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan. 10In kuwa tun muna maƙiyan Allah aka sulhunta mu da shi ta mutuwar Ɗansa, to, da yake an sulhunta mu, ashe kuwa, za a fi kāre mu ta wurin rayuwarsa ke nan. 11Banda haka ma, har muna fariya da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami sulhun nan a yanzu.
12To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi. 13Lalle fa zunubi yana nan a duniya tun ba a ba da Shari'a ba, sai dai inda ba shari'a, ba a lasafta zunubi. 14Duk da haka kuwa mutuwa ta mallaka tun daga Adamu har ya zuwa Musa, har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi irin na keta umarnin da adamu ya yi ba, wanda yake shi ne kwatancin mai zuwan nan.
15Amma fa baiwar nan dabam take ƙwarai da laifin nan. Ai, in laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa masu ɗumbun yawa mutuwa, ashe ma, alherin Allah, da kuma baiwar nan, albarkacin alherin Mutum ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga masu ɗumbun yawa fin haka ƙwarai. 16Baiwar nan kuwa dabam take ƙwarai da hakkokin zunubin mutum ɗayan nan. Don kuwa hukuncin da aka yi a kan laifin mutum ɗayan nan, shi ya jawo hukuncin hallaka. Amma baiwar nan da aka yi a sanadin laifofi da yawa, ita take sa kuɓuta ga Allah. 17In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu.
18To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zama wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai. 19Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta wurin biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci. 20Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske. 21Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da ke bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.
1To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah yă haɓaka? 2A'a, ko kusa! Mu da muka mutu ga zunubi, ƙaƙa za mu ƙara rayuwa a cikinsa har yanzu? 3Ashe, ba ku sani ba duk ɗaukacinmu da aka yi wa baftisma a cikin Almasihu Yesu, a cikin mutuwarsa aka yi mana baftismar ba? 4Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.
5Tun da yake mun zama ɗaya da shi wajen kwatancin mutuwarsa, ashe kuwa, za mu zama ɗaya ma a wajen tashinsa. 6Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi. 7Wanda ya yi irin wannan mutuwa kuwa, an kuɓutar da shi daga zunubi ke nan. 8Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun gaskata za mu rayu tare da shi kuma. 9Mun sani tun da yake an ta da Almasihu daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba ke nan, mutuwa ba ta da sauran wani iko a kansa. 10Mutuwar nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari, saboda shafe zunubanmu, amma rayuwar da yake yi, yana rayuwa ne, rayuwa ga Allah. 11Haka ku ma sai ku lasafta kanku kamar ku matattu ne ga zunubi, amma kuna a raye rayuwa ga Allah, ta wurin Almasihu Yesu.
12Saboda haka, kada ku yarda zunubi ya mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha'awarsa. 13Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci. 14Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari'a take iko da ku ba alherin Allah ne.
15To, ƙaƙa? Wato, sai mu yi zunubi don shari'a ba ta iko da mu, sai alherin Allah? A'a, ko kusa! 16Ba ku sani ba, shi wanda kuke miƙa kanku a gare shi domin yi wa biyayya, lalle ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya ɗin (ko bautar zunubi wanda ƙarshensa mutuwa ne, ko bautar biyayya wadda ƙarshenta adalci ce)? 17Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku. 18Da aka 'yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci. 19Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.
20Sa'ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci. 21To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne. 22Amma a yanzu da aka 'yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin Allah, sakamakonku shi ne tsarkakewa, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. 23Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
1Ya 'yan'uwa, ko ba ku sani ba, shari'a tana da iko da mutum, muddin yana raye ne kawai? Da waɗanda suke san shari'a fa nake. 2Misali, mace mai aure, shari'a ta ɗaure ta ga mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar auren ke nan. 3Don haka, muddin mijinta yana da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan aure, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya ba ce.
4Haka kuma 'yan'uwana, kun zama matattu ga Shari'a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah. 5Ai, dā sa'ad da muke zaman halin mutuntaka, muguwar sha'awa wadda faɗakarwar Shari'a ke sa a yi, ita take aiki a gaɓoɓinmu, tă wurin haddasa mutuwa. 6Amma a yanzu mun 'yantu daga Shari'a, mun mutu daga abin da dā ya ɗaure mu ke nan, har muna iya bauta wa Allah da sabon rai da Ruhu, ba da tsofaffin rubutattun ka'idodi ba.
7To, me kuma za mu ce? Shari'a zunubi ce? A'a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari'a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari'a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba. 8Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari'a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri. 9Dā kam, sa'ad da ban san shari'a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu. 10Umarnin nan kuwa, wanda manufarsa a gare ni rai ne, sai ya jawo mini mutuwa. 11Don kuwa zunubi ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta wurinsa kuwa ya kashe ni. 12Domin haka Shari'a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, negari ne.
13Wato, abar nan da take tagari ta jawo mini mutuwa ke nan? A'a, ko kusa! Zunubi ne ya jawo, domin ya bayyana kansa shi zunubi ne, gama ta wurin abar nan tagari ya jawo mini mutuwa, ta dalilin umarnin nan kuma, zunubi ya bayyana matuƙar muninsa. 14Mun dai san Shari'a aba ce ta ruhu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi. 15Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya yi, ba shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi. 16To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari'a aba ce mai kyau. 17Ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne. 18Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu. 19Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa. 20To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.
21Sai na ga, ashe, ya zama mini ka'ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta a tare da ni. 22Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari'ar Allah. 23Amma ina ganin wata ka'ida dabam a gaɓoɓina, wadda take yaƙi da ka'idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa'idar nan ta zunubi wadda take zaune a gaɓoɓina. 24Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa? 25Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari'ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka'idar zunubi nake bauta wa.
1Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu. 2Ka'idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu, Yesu ta 'yanta ni daga ka'idar zunubi da ta mutuwa. 3Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi. 4Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu. 5Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al'amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al'amuran Ruhu. 6Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama. 7Don ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntake gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari'ar Allah, ba kuwa zai iya ba. 8Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.
9Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zauna a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne. 10In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah. 11In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.
12Domin haka, 'yan'uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa. 13In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu. 14Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne 'ya'yan Allah. 15Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A'a, na zaman 'ya'ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!” 16Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne. 17In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.
18Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba. 19Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar 'ya'yan Allah. 20An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya, 21gama za a 'yantar da halitta da kanta ma, daga bautar ruɓewa, domin ta sami 'yancin nan, na ɗaukaka na 'ya'yan Allah. 22Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu. 23Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan. 24Sa'ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu? 25In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.
26Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa. 27Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.
28Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa. 29Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa. 30Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba? 33Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su! 34Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ka kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu! 35Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi? 36Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda kai ne ake kashe mu yini zubur, An lasafta mu kamar tumakin yanka.” 37Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu. 38Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala'iku, ko manyan mala'iku, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko masu iko, 39ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.
1Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida, 2cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata. 3Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila! 4Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne. 5Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.
6Ba cewa Maganar Allah ta fādi ba, don ba duk zuriyar Isra'ila ne suke Isra'ilawa na gaske ba. 7Ba kuwa duk su ne 'ya'yan Ibrahim ba, wai don suna zuriyarsa. Amma an ce, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.” 8Wato, zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama 'ya'yan Allah ba, a'a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. 9Alkawarin kuwa shi ne, “Baɗi war haka zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.” 10Banda haka ma, sa'ad da Rifkatu ta yi ciki da mutumin nan ɗaya, wato, kakanmu Ishaku, 11tun ba ta haifi 'ya'yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyauūdon nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransaū 12aka ce mata, “Wan zai bauta wa ƙanen.” 13Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakubu na so, Isuwa na ƙi.”
14To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? A'a, ko kusa! 15Domin ya ce wa Musa, “Wanda zan yi wa jinƙai, zan yi masa jinƙan, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.” 16Ashe kuwa, abin bai danganta ga nufin mutum ko himma tasa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuna a sanar da sunana a duniya duka.” 18Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.
19Kila ka ce mini, “To, don me har yanzu yake ganin laifi? Wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?” 21Ashe, maginin tukwane ba ya iko da yumɓu, ya gina wata domin aiki mai martaba, wata kuma don kasasshen aiki, duk daga curi ɗaya? 22To, ƙaƙa fa? Allah da yake yana so ya nuna fushinsa, ya kuma bayyana ikonsa, sai ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci fushinsa, suka kuma isa hallaka, 23Nufinsa ne ya bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya yi wa jinƙai, wato, waɗanda dā ma ya yi wa tanadin ɗaukaka? 24Wato, mu ke nan da ya kira, ba kuwa daga cikin Yahudawa kaɗai ba, har ma daga cikin al'ummai. 25Kamar dai yadda ya faɗa a Littafin Yusha'u cewa, “Waɗanda dā ba jama'ata ba, Zan ce da su “‘jama'ata,” Wadda dā ba abar ƙaunata ba kuma, Zan ce da ita “‘abar ƙaunata.”
26“A daidai wurin da aka ce da su, “‘Ku ba jama'ata ba ne,” A nan ne za a kira su “‘'ya'yan Allah Rayayye,”
27A game da Isra'ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake yawan Isra'ilawa ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto. 28Domin Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a duniya, ya gama shi tashi ɗaya.” 29Kamar yadda Ishaya ya yi faɗa cewa, “Da ba domin Ubangijin Runduna ya bar mana zuriya ba, Da mun zama kamar Saduma, An kuma maishe mu kamar Gwamrata.”
30To, me kuma za mu ce? Ga shi, al'ummai da ba su nace da neman adalcin Allah ba, sun samu, wato, sun sami adalcin da yake daga bangaskiya. 31Isra'ila kuwa da suka nace da neman hanyar adalcin Allah, suka kasa samunta. 32Me ya sa? Don ba su neme ta ta hanyar bangaskiya ba, sai dai ta hanyar aikata aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da dutsen tuntuɓe, 33kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ga shi, na sa dutsen sa tuntuɓe a Sihiyona, Da fā na sa faɗuwa. Duk mai gaskatawa da shi, ba zai kunyata ba.”
1Ya 'yan'uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto. 2Na dai shaida su a kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba. 3Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar. 4Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya ya sami adalcin Allah.
5Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta. 6Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu. 7Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” Wato yă ta da Almasihu daga matattu. 8Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi. 9Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa ya sami ceto. 11Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.” 12Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi. 13“Duk wanda kuwa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”
14Amma ta ƙaƙa za su yi addu'a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa'azi? 15Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!” 16Amma ba duka ne suka yi na'am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?” 17Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.
18Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji. “Muryarsu ta gama duniya duka, Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”
19Har wa yau, ina tambaya. Shin, Isra'ila kam, ba su fahimta ba ne? Da farko dai Musa ya ce, “Zan sa ku kishin waɗanda ba al'umma ba ne, Zan kuma sa ku fushi da wata al'ummar marar fahimta.”
20Ishayan kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni. Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”
21Amma a game da isra'ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama'a marasa biyayya, masu tsayayya.”
1To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama'arsa baya ke nan? A'a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba'isra'ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu. 2Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama'arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan isra'ila, ya ce, 3“Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe bagadanka na hadaya. Ni kaɗai ne na ragu, suna kuwa neman raina.” 4Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba'al ba.” 5Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa. 6In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
7To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra'ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare. 8Yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya toshe musu basira, Ya ba su ido, ba na gani ba, Da kuma kunne, ba na ji ba, Har ya zuwa yau.”
9Dawuda kuma ya ce, “Dā ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu, Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.
10Idonsu kuma yă shiga duhu, har su kasa gani, Ka kuma tanƙwara bayansu har abada.”
11Ina kuma tambaya. Faɗuwar da suka yi, sun faɗi ba tashi ke nan? A'a, ko kusa! Sai ma faɗuwarsu ta zama sanadin ceto ga al'ummai, don a sa Isra'ila kishi. 12To, in kuwa duniya ta arzuta da hasararsu, wa zai kimanta yawan albarka, in adadinsu masu ɗungumawa ga Allah ya cika>
13Da ku al'ummai fa nake. Tun da yake ni manzo ne ga al'ummai, ina taƙama da aikina, 14ko ta wane hali in sa kabilata kishin zuci, har in ceci waɗansunsu. 15Domin in an sulhunta duniya ga Allah, saboda yar da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rai daga matattu ba>
16In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma. 17Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai kake ɗauke da saiwar ba, saiwar ce take ɗauke da kai. 19Kila za ka ce, “Ai, an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.” 20Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah. 21Da yake Allah bai bar rassan asalin ba, kai ma ba zai bar ka ba. 22Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka. 23Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su. 24Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali>
25'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nanūwadda ba mai tabbata ba ceūta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika. 26Ta haka nan ne Isra'ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai Ceto zai zo daga Sihiyona, Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”
27“Cikar alkawarina a gare su ke nan, Sa'ad da na ɗauke musu zunubansu.”
28A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu. 29Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi. 30Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu, 31haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku. 32Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.
33Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!
34“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”
35“Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa, Har da za a sāka masa?”
36Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.
1Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi. 2Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.
3Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi. 4Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan'uwansa ne. 6Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu, 7in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa, 8mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, ya bayar hannu sake, shugaba ya yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, ya yi shi da fara'a.
9Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari. 10A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan'uwansa. 11Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji. 12Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a. 13Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.
14Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su. 15Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka. 16Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne. 17Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa. 18In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa. 19Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.” 20Har ma “In maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.” 21Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
1Bari kowa ya yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne. 2Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci. 3Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ba ne ga masu aiki nagari, sai dai ga masu mugun aiki. Kana so kada ka ji tsoron mahukunci? To, sai ka yi nagarta, sai kuwa ya yaba maka. 4Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi. 5Saboda haka wajibi ne ka yi biyayya, ba domin gudun fushi kaɗai ba, amma domin lamiri kuma. 6Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma'aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe. 7Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa. 8Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan. 9Umarnan nan cewa, “Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari'a ce.
11Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa'ad da muka fara ba da gaskiya. 12Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske. 13Mu tafiyar da al'amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba. 14Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.
1A game da wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu biyu, amma ba a game da sukan ra'ayinsa ba. 2Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci. 3To, kada fa mai cin kome ɗin nan ya raina wanda ya ƙi ci, kada kuma wanda ya ƙi cin nan, ya ga laifin mai ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi hannu biyu biyu. 4Kai wane ne har da za ka ga laifin baran wani? Ko dai ya tsaya, ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
5Wani yakan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa. Kowa dai yă zauna a cikin haƙƙaƙewa, a kan ra'ayinsa. 6Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah. 7Duk a cikinmu ba wanda ya isar wa kansa a sha'anin rayuwarsa ko mutuwarsa. 8Ko muna a raye, zaman Ubangiji muke yi, ko mun mutu ma, zaman Ubangiji muke yi. Ashe, ko muna a raye, ko kuma a mace, na Ubangiji ne mu. 9Saboda haka ne musamman Almasihu ya mutu, ya sāke rayuwa, wato, domin ya zama shi ne Ubangijin matattu da na rayayyu duka.
10To, kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan'uwanka? Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan'uwanka? Ai, dukkanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari'ar Allah. 11Domin a rubuce yake, “Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini, Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”
12Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.
13Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu ya zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan'uwansa, 14Na sani, na kuma tabbata, a tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki. 15In kuwa cimarka tana cutar ɗan'uwanka, ashe, ba zaman ƙauna kake yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa. 16Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu. 17Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 18Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin harɓa ne ga Allah, yardajje na kuma ga mutane. 19Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna. 20Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum ya zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci. 21Ya kyauta kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe. 22Kana da bangaskiya? To, ka riƙe ta tsakaninka da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, a game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne. 23Wanda yake shakka, amma kuwa ya ci, ya sani ya yi laifi ke nan, domin ba da bangaskiya ya ci ba. Duk abin da ba na bangaskiya ba ne, zunubi ne.
1To, mu da muke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai. 2Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi. 3Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.” 4Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana. 5Allah mai ba da haƙuri da ta'aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu, 6domin ku ɗaukaka Allah, Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.
7Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah. 8Ina dai gaya muku, Almasihu ya zama bara ga Isra'ila, domin nuna gaskiyar Allah, domin kuma tabbatar da alkawaran nan, da Allah ya yi wa kakannin kakanninmu, 9al'ummai kuma su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa. Yadda yake a rubuce, “Domin haka zan yabe ka a cikin al'ummai, In kuma yi waƙar yabon sunanka.”
10Har wa yau kuma an ce, “Ya ku al'ummai, ku yi ta farin ciki tare da jama'arsa.”
11Da kuma, “Ku yabi Ubangiji, ya ku al'ummai duka, Dukkan kabilai kuma su yabe shi.”
12Ishaya kuma ya ce, “Tsatson Yesse zai bayyana, Wanda zai tashi ya mallaki al'ummai, A gare shi ne al'ummai za su sa zuciya.”
13Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14Ya 'yan'uwana, ni ma da kaina na amince da ku, cewa ku da kanku masu nagarta ne ƙwarai da gaske, masu cikakken sani, kun kuma isa ku gargaɗi juna. 15Duk da haka, a kan waɗansu batatuwan da na rubuto muku, na ƙara ƙarfafawa ƙwarai, domin tuni, saboda alherin da Allah ya yi mini 16da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al'ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al'ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 17Ashe kuwa, ina da dalilin yin alfarma da Almasihu Yesu a game da al'amarin Allah. 18Ba zan kuskura in faɗi kome ba, sai abin da Almasihu ya aikata ta wurina, a wajen sa al'ummai biyayya ta wurin maganata da aikina, 19ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina. 20Har ya zama mini abin buri in sanar da bishara, a inda ba a taɓa sanar da sunan Almasihu ba, don kada in ɗora ginina a kan harsashin wani, 21sai dai kamar yadda yake a rubuce, “Waɗanda ba a taɓa faɗa wa labarinsa ba, za su gane, Waɗanda ba su taɓa jin labarinsa ba ma, za su fahimta.”
22Shi ya sa sau da yawa ban sami sukunin zuwa wurinku ba. 23A yanzu kuwa tun da yake ba sauran wani wuri da ya rage mini a lardin nan, shekaru da yawa kuma ina ɗokin zuwa wurinku, 24ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku. 25Amma a yanzu kam, za ni Urushalima, don in kai wa tsarkaka gudunmawa. 26Mutanen Makidoniya da na Akaya, sun ji daɗin yin gudunmawar daidai gwargwado ga matalauta, a cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27Sun kuwa ji daɗin yin haka, domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin tun da yake al'ummai sun yi tarayya da su a kan ni'imarsu ta ruhu, ashe kuwa, ya kamata su ma su taimake su da ni'imarsu ta duniya. 28In kuwa na gama wannan, na kuma danƙa musu wannan taimako lafiya, sai in bi ta kanku zuwa ƙasar Asbaniya. 29Na kuma sani, in na zo wurinku, zan zo ne a cikin falalar albarkar Almasihu
30Amma ina roƙonku 'yan'uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunar nan da Ruhu yake bayarwa, ku taya ni yin addu'a da naciya ga Allah saboda kaina, 31domin in tsira daga maƙiyan bangaskiya a Yahudiya, don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima, ta zama abar karɓa ga tsarkaka, 32har in Allah ya yarda in iso wurinku da farin ciki, mu wartsake tare. 33Allah mai ba da salama ya kasance tare da ku duka. Amin.
1Ga 'yar'uwarmu Fibi ina sada ku da ita, ita ma kuwa mai hidimar ikilisiya ce a Kankiriya. 2Ku karɓe ta da hannu biyu biyu saboda Ubangiji, ta halin da ya dace da tsarkaka. Ku kuma taimake ta da duk irin abin da ta nemi taimako a gare ku, domin ita ma tā taimaki mutane da yawa, har ma da ni kaina.
3Ku gai da Bilkisu da Akila, abokan aikina a cikin Almasihu Yesu, 4waɗanda suka kasai da ransu saboda ni, ba kuwa ni kaɗai nake gode musu ba, har ma da dukkan ikilisiyoyin al'ummai. 5Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya. 6Ku gai da Maryamu, wadda ta yi muku aiki ƙwarai da gaske. 7Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, 'yan'uwana, abokan ɗaurina, waɗanda suke shahararru a cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu. 8Ku gai da Amfiliyas, ƙaunataccena a cikin Ubangiji. 9Ku gai da Urbanas abokin aikinmu a cikin Almasihu, da kuma ƙaunataccena Istakis. 10Ku kuma gai da Abalis, amintaccen nan a cikin Almasihu. Ku gai da jama'ar Aristobulus. 11Ku gai da 'dan'uwana Hirudiyan. Ku gai da waɗanda suke na Ubangiji a cikin jama'ar Narkisas. 12Ku gai da Tarafina da Tarafusa, masu Ubangiji. Ku gai da Barsisa, ƙaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji ƙwarai da gaske. 13Ku gai da Rufas, fitaccen mai bin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, tawa kuma. 14Ku gai da Asinkiritas, da Filiguna, da Hamisa, da Baturobas, da Hamasa, da kuma 'yan'uwan da suke tare da su. 15Ku gai da Filulugusa, da Yuliya, da Niriyas, da 'yar'uwarsa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkakan da suke tare da su. 16Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. Dukan ikilisiyoyin Almasihu suna gaishe ku.
17Ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai. 19Amma ku kam, ai, kowa ya san biyayyarku, shi ya sa nake farin ciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da yake nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta. 20Allah mai ba da salama kuwa, zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.
21Timoti, abokin aikina, yana gaishe ku, haka kuma Lukiyas da Yason da kuma Susibataras, 'yan'uwana.
22Ni Tartiyas, mai rubuta wasiƙar nan, ina gaishe ku saboda Ubangiji.
23Gayus, mai masaukina, mai kuma saukar da dukan 'yan ikilisiya, yana gaishe ku. Arastas, ma'ajin gari, da kuma ɗan'uwanmu Kawartas, suna gaishe ku. 24Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka. Amin, Amin.
25Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal. 26Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al'ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya. 27Ɗaukaka tă tabbata har abada ga Allah Makaɗaicin hikima ta wurin Yesu Almasihu! Amin, Amin.