Ruth
1A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra'ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da 'ya'yansa maza biyu. 2Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yansu maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can. 3Elimelek, mijin Na'omi, ya rasu, aka bar Na'omi da 'ya'yansu maza biyu. 4Sai suka auri 'yan matan Mowab, Orfa da Rut. Bayan da suka yi wajen shekara goma a can, 5sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.
6Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta. 7Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya. 8Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan. 9Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su. Sai suka fashe da kuka, 10suka ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”
11Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku? 12Sai ku koma, 'ya'yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi 'ya'ya maza, 13za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, 'ya'yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.” 14Suka sāke fashewa da kuka. Sai Orfa ta yi wa surukarta, sumba, ta yi bankwana da ita, amma Rut ta manne mata.
15Na'omi ta ce wa Rut, “Kin ga, 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da wurin gumakanta, sai ki koma, ki bi 'yar'uwarki.”
16Amma Rut ta ce, “Kada ki yi ta roƙona in rabu da ke, ko in bar binki, gama inda za ki tafi, ni ma can zan tafi, inda kuma za ki zauna, ni ma can zan zauna. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna. 17Inda za ki rasu, ni ma can zan rasu, a binne ni. Idan na bar wani abu ya raba ni da ke, in dai ba mutuwa ba, to, Ubangiji ya yi mini hukunci mai zafi!” 18Da Na'omi ta ga Rut ta ƙudura ta tafi tare da ita, sai ta ƙyale ta.
19Su biyu kuwa suka kama hanya har suka isa Baitalami. Da suka isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata suka ce, “Na'omi ce wannan?”
20Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na'omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai. 21Na tafi a wadace, ga shi, Ubangiji ya komo da ni hannu wofi. Don me kuke kirana mai farin ciki da yake Ubangiji Mai Iko Dukka ya wahalshe ni, ya kuma aukar mini da masifa?”
22Haka Na'omi ta koma daga ƙasar Mowab tare da surukarta Rut, mutuniyar Mowab. Suka isa Baitalami a farkon kakar sha'ir.
1Na'omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo'aza, shi kuwa attajiri ne. 2Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.” Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.” 3Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa'a kuwa ta fāɗa a gonar Bo'aza, dangin Elimelek.
4Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.” Suka amsa, “Alaikun salamu.”
5Sa'an nan Bo'aza ya tambayi baransa da yake shugaban masu girbin, ya ce, “'Yar wace ce wannan?”
6Baran ya ce, “Ita 'yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab. 7Ita ce ta ce mana, “‘In kun yarda, ku bar ni in bi bayan masu girbin, ina kala.” Haka ta yi ta kala tun da sassafe har yanzu ba hutu, sai dai 'yar shaƙatawar da ta yi kaɗan.”
8Sa'an nan sai Bo'aza ya ce wa Rut, “Kin ji, 'yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin 'yan matan gidana. 9Ki kula da gonar da suke girbi, ki bi su. Ga shi, na riga na umarci barorina kada su dame ki. Sa'ad da kika ji ƙishirwa, sai ki tafi ki sha ruwa a tuluna, wanda barorin suka ɗebo.”
10Sai Rut ta rusuna har ƙasa, ta ce masa, “Me ya sa na sami tagomashi a gare ka, har da za ka kula da ni, ni da nake baƙuwa?”
11Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā. 12Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”
13Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”
14Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo'aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura. 15Sa'ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo'aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta. 16Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.” 17Ta yi ta kala a gonar har yamma. Ta sussuka abin da ta kalata, ta sami tsaba wajen garwa biyu. 18Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage.
19Surukarta kuma ta ce mata, “A ina kika yi kala yau? A gonar wa kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga wannan mutum wanda ya kula da ke.” Sai ta faɗa mata sunan mutumin da ta yi kala a gonarsa, ta ce, “Sunan mutumin da na yi kala a gonarsa yau, Bo'aza.”
20Na'omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”
21Rut kuma, mutuniyar Mowab, ta ce, “Banda wannan ma, ya ce mini, “‘Ki riƙa bin barorina, har lokacin da suka gama mini girbin.”
22Sa'an nan Na'omi ta ce wa Rut, “Madalla, 'yata, ki riƙa bin 'yan matan gidansa, kada ki tafi wata gona dabam.” 23Sai ta riƙa bin 'yan matan gidan Bo'aza. Ta yi ta kala har aka gama girbin sha'ir da na alkama, tana zaune tare da surukarta, wato Na'omi.
1Wata rana, Na'omi ta ce wa Rut, “'Yata, ya kamata in nemar miki miji don ki sami gida inda za ki huta, ki ji daɗi. 2Bo'aza wanda kika yi aiki da barorinsa danginmu ne. Ga shi, zai tafi sussukar sha'ir a masussuka da maraice. 3Sai ki yi wanka, ki shafa man ƙanshi, ki yafa tufafinki na ado, ki tafi masussukar, amma kada ki bari ya san zuwanki, sai bayan da ya riga ya ci ya sha. 4Sa'ad da ya kwanta, sai ki lura da inda ya kwanta, sa'an nan ki tafi, ki buɗe mayafinsa a wajen ƙafafunsa, ki kwanta a ciki. Zai kuwa faɗa miki abin da za ki yi.”
5Rut ta amsa, “Zan yi dukan abin da kika faɗa.”
6Rut kuwa ta gangara zuwa masussukar, ta yi yadda surukarta ta faɗa mata. 7Sa'ad da Bo'aza ya ci ya sha yana cikin jin daɗi, sai ya je ya kwanta kusa da tsibin tsabar sha'ir. Sa'an nan Rut ta tafi a hankali, ta buɗe mayafin da ya rufa da shi wajen ƙafafunsa, ta kwanta a ciki. 8Da tsakar dare, sai mutumin ya farka a firgice, ya juya, sai ga mace kwance a wajen ƙafafunsa. 9Ya ce, “Wace ce?” Sai ta amsa, “Ni ce Rut, baranyarka, sai ka rufe ni da mayafinka, gama kai dangi ne na kusa.”
10Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba. 11Yanzu dai, 'yata, kada ki damu, zan yi miki dukan abin da kika roƙa, gama dukan mutanen garin sun sani ke macen kirki ce. 12Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni. 13Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.” 14Sai ta kwanta a wajen ƙafafunsa har safiya. Sa'an nan ta tashi tun da jijjifi kafin a iya gane fuskar mutum, gama ba ya so a sani mace ta zo masussukar.
15Bo'aza ya ce mata, “Kawo mayafinki, ki shimfiɗa shi.” Sai ta shimfiɗa mayafin, ya zuba mata sha'ir ya kusa garwa huɗu ya aza mata a kā. Sa'an nan ta koma gari.
16Lokacin da ta zo wurin surukarta, sai surukarta ta ce mata, “'Yata, ina labari?” Sai ta faɗa mata dukan abin da mutumin ya faɗa mata. 17Ta kuma ce, “Ga sha'ir da ya ba ni, gama ya ce, “‘Ba za ki koma wurin surukarki hannu wofi ba.” 18Sai surukarta ta ce, “Ki jira dai, 'yata, har ki ga yadda al'amarin zai zama, gama mutumin ba zai huta ba, sai ya daidaita al'amarin a yau.”
1Bo'aza fa ya tafi, ya zauna a dandalin ƙofar gari. Sai ga wani daga cikin waɗanda hakkinsu ne su ɗauki Rut, shi ne kuwa wanda Bo'aza ya ambata, ya iso. Bo'aza kuwa ya ce masa, “Ratso nan, wāne, ka zauna.” Sai ya ratsa, ya zauna. 2Bo'aza ya kuma kirawo goma daga cikin dattawan gari, ya ce musu, “Ku zauna nan.” Suka kuwa zauna. 3Sa'an nan ya ce wa dangin nan nasa na kusa, “Ga Na'omi wadda ta komo daga ƙasar Mowab, tana so ta sayar da gonar Elimelek danginmu. 4Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.” Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”
5Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”
6Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.”
7Wannan ita ce al'adar Isra'ilawa a dā a kan sha'anin fansa ko musaya, don tabbatar da al'amarin. Sai mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen. Wannan ita ce hanyar tabbatarwa a cikin Isra'ila. 8Saboda haka a sa'ad da dangin nan mafi kusa ya ce wa Bo'aza, “Sai ka saye ta,” sai ya tuɓe takalminsa ya ba Bo'aza. 9Sa'an nan Bo'aza ya ce wa dattawan da dukan jama'ar da suke wurin, “Yau ku ne shaidu, cewa, na sayi dukan abin da yake na Elimelek, da na Kiliyon, da na Malon daga hannun Na'omi. 10Game da wannan kuma Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayi Malon, ta zama matata domin in wanzar da sunan marigayin cikin gādonsa, don kada sunansa ya mutu daga na 'yan'uwansa, da kuma a garinsu. Ku ne fa shaidu a yau.”
11Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji ya sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, ya sa ka yi suna a cikin Baitalami, 12gidanku kuma ya zama kamar gidan Feresa, wanda Tamar ta haifa wa Yahuza, saboda 'ya'yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace.”
13Bo'aza kuwa ya auri Rut, ta zama matarsa. Ya kuma shiga wurinta, Ubangiji kuwa ya sa ta yi ciki, ta haifa masa ɗa. 14Sai mata suka ce wa Na'omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, da bai bar ki bā dangi na kusa ba, Allah ya sa ɗan ya yi suna a cikin Isra'ila. 15Ya zama mai sanyaya miki rai, mai goyon tsufanki, gama surukarki wadda take ƙaunarki, wadda ta fiye miki 'ya'ya maza bakwai, ita ta haife shi.” 16Sa'an nan Na'omi ta ɗauki yaron ta rungume shi a ƙirjinta, ta zama mai renonsa. 17Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na'omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda.
18-22Wannan shi ne asalin zuriyar Dawuda. Aka fara daga Feresa zuwa Dawuda. Feresa ne mahaifin Hesruna, Hesruna kuma ya haifi Arama, Arama ya haifi Amminadab, Amminadab kuma ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon kuma ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obida, Obida kuma ya haifi Yesse, sa'an nan Yesse ya haifi Dawuda.