Song of Songs
1Ga waƙar Sulemanu mafi daɗi.
2Leɓunanka sun lulluɓe ni da sumba, Ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3Akwai ƙanshi kuma kewaye da kai, Jin amon sunanka yana tunasar da ni. Ba wata matar da za ta ƙi ƙaunarka.
4Ka ɗauke ni mana, mu gudu, Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka. Da yake kana nan za mu yi farin ciki, Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki. Ya dace a ƙaunace ka!
5Rana ta sa na zama akawala kyakkyawa. Matan Urushalima, bisa ga launi, ni ƙasa ƙasa ce, Kamar alfarwar hamada, Kamar labulen fādar Sulemanu.
6Kada ka raina ni saboda launina, Domin rana ta dafe ni. 'Yan'uwana suna fushi da ni, Sun sa ni aiki a gonar inabi. Ba ni da zarafin da zan lura da kaina.
7Faɗa mini, ƙaunataccena, Ina za ka kai garkenka kiwo? Ina za su huta sa'ad da rana ta take? Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya>
8Mafi kyau cikin mata, ashe, ba ki san wurin ba? Tafi, ki bi garken, Ki samar wa awakinki wurin kiwo Kusa da alfarwan makiyaya.
9Ke ƙaunatacciyata, kina ɗauke hankalina Kamar yadda goɗiya take ɗauke hankalin ingarmun karusan Fir'auna.
10Kitsonki yana da kyau a kumatunki, Ya sauka a wuyanki kamar lu'ulu'ai.
11Mu kuma za mu ƙera miki sarƙar zinariya, A yi miki ado da azurfa.
12A sa'ad da sarki yake kan kujerarsa, Yana jin daɗin ƙanshin turarena ƙwarai.
13Ƙaunataccena yana da ƙanshin mur Lokacin da yake kwance a ƙirjina.
14Ƙaunataccena kamar furen jeji yake Wanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.
15Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata, Idonki suna haskaka da ƙauna.
16Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha'awa. Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.
17Itatuwan al'ul su ne jigajigan gidanmu, Itatuwan fir su ne rufin gidan
1Ni fure ce na Sharon, Furen bi-rana na cikin kwari.
2Kamar yadda furen bi-rana yake a cikin ƙayayuwa, Haka ƙaunatacciyata take a cikin sauran mata.
3Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji, Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza. Da farin ciki na zauna a inuwarsa, Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.
4Ya kai ni babban ɗakin da ake liyafa, Ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5Ka ciyar da ni da wainar zabibi, Ka ba ni 'ya'yan gawasa in sha in wartsake! Gama na cika da sha'awarka.
6Bari ka ta da kaina da hannun hagunka, Ka rungume ni da hannun damanka.
7Ku 'yan matan Urushalima, Ku rantse da bareyi, da batsiyoyi, Ba za ku shiga tsakaninmu ba, Ku bar ta kurum.
8Na ji muryar ƙaunataccena! Ya zo a guje daga kan tuddai, Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.
9Ƙaunataccena kamar barewa yake, Kamar sagarin kishimi. Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu. Yana leƙe ta tagogi, Yana kallona ta cikin asabari.
10Ƙaunataccena ya yi magana da ni. Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa.
11Gama lokacin sanyi ya wuce, Ruwa kuma ya ɗauke.
12Furanni suna hudowa a itatuwa ko'ina. Lokacin raira WAƘOƘI ya yi, Lokacin da kurciyoyi yake kuka ya yi.
13'Ya'yan ɓaure sun nuna, Tohon inabi yana ƙanshi. Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa!
14Ya kurciyata kina zaune a kogon dutse mai tsayi. Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryarki, Gama muryarki tana da daɗin ji, Fuskarki kuma tana da kyan gani.
15Ku kama mana 'yan ƙananan diloli Waɗanda suke ɓata gonakin inabi, Gama gonakin inabinmu sun yi fure.
16Ƙaunataccena nawa ne, ni ma tasa ce, Yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana,
17Har hurowar iskar safiya, Sa'ad da duhu ya kawu. Komo ya ƙaunataccena, yi kamar barewa, Kamar sagarin kishimi a kan duwatsu.
1Ina kwance a gadona dukan dare, Ina mafarki da ƙaunataccena, Na neme shi, amma ban same shi ba. Na kira shi, amma ba amsa.
2Bari in tashi yanzu in shiga birni, In bi titi-titi, in bi dandali-dandali, In nemi wanda raina yake ƙauna. Na neme shi, amma ban same shi ba.
3Da matsaran da suke kai da kawowa cikin birni suka gan ni, Sai na tambaye su ko sun ga ƙaunataccena.
4Rabuwata da matsaran ke nan, Sai na yi kaciɓis da ƙaunataccena. Na riƙe shi, ban sake shi ba, Na kai shi gidanmu, har ɗakin mahaifiyata.
5Ku 'yan matan Urushalima, Ku rantse da bareyi da batsiyoyi, Ba za ka shiga tsakaninmu ba, Ku bar ta kurum.
6Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji, Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake>
7Ai, duba suna ɗauke da karaga wadda aka shirya domin Sulemanu, Dakarai sittin na kewaye da karagar, Zaɓaɓɓun sojoji daga cikin Isra'ila.
8Dukansu gwanayen yaƙi da takobi ne, gogaggu ne na aikin soja, Kowannensu yana da takobi, Suna tsaro don kada a hume su da dare.
9Ana ɗauke da sarki Sulemanu a karagar da aka shirya da itace mafi kyau.
10An dalaye ginshiƙanta da azurfa, An rufe ta da zane da aka yi wa ado da zinariya. An lulluɓe wurin zama da zanen shunayya. Matan Urushalima sun yi mata irin yayin da ake yi na ƙauna.
11Matan Sihiyona, ku fito ku ga sarki Sulemanu Ya sa kambin sarauta, Wanda uwarsa ta sa masa, a ranar aurensa, A ranarsa ta murna da farin ciki.
1Kyakkyawa ce ke ƙaunatacciyata. Idonki kamar na kurciya, suna haskakawa daga cikin lulluɓi. Gashinki yana zarya kamar garken awaki Da yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
2Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya, Aka yi mata wanka nan da nan. Ba giɓi, suna nan shar. An jera su tantsai.
3Leɓunanki ja wur kamar kin shafa jan-baki. Maganarki tana faranta zuciya. Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
4Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul, Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.
5Mamanki kamar bareyi biyu ne, Wato tagwayen barewa, suna kiwo cikin furen bi-rana.
6Har iskar safiya ta huro, Duhu kuma ya kawu, Zan zauna a kan tudun mur, Wato tudun kayan ƙanshi.
7Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata, Ba wanda zai kushe ki!
8Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon, Taho daga Lebanon. Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana, Da Dutsen Senir da Harmon, Inda zakuna da damisoshi suke zaune.
9Kallon idonki, budurwata, amaryata, Da duwatsun da suke wuyanki Sun sace zuciyata.
10Ƙaunarki abar murna ce, ya budurwata, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi. Ƙanshinki ya fi kowane irin turare ƙanshi.
11Zaƙin leɓunanki kamar zuma ne, ya budurwata, A gare ni harshenki madara ne da zuma. Tufafinki suna ƙanshi kamar turaren da yake cikin Dutsen Lebanon.
12Budurwata, amaryata, ke asirtaccen lambu ce, Lambu mai katanga, asirtacciyar maɓuɓɓuga.
13Shuke-shuke suna girma sosai. Suna girma kamar gonar itatuwan rumman. Suna ba da 'ya'ya mafi kyau Da kayan shafe-shafe kamar su lalle da nardi.
14Nardi, da asfaran, da kalamus, da kirfa, Da dukan itatuwan da suke ba da kayan ƙanshi, Da mur, da aloyes, da dukan turare mafi ƙanshi.
15Maɓuɓɓugai suna ba lambun ruwa, ruwan rafuffuka suna gudu, Ƙoramu suna bulbulo ruwa daga Dutsen Lebanon.
16Farka, ya iskar arewa. Ki hura a kan lambuna, ke iskar kudu. Iska ta cika da ƙanshi. Bari ƙaunataccena ya zo lambunsa, Ya ce 'ya'yan itatuwa mafi kyau.
1Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata, Ina tattara mur da ƙaro. Ina shan zuma da kakinsa. Ina shan ruwan inabi da madara kuma. Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!
2Ina barci, amma zuciyata na a farke, Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata, Wadda ba wanda zai kushe ki. Kaina ya jiƙe da raɓa, Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.
3Na riga na tuɓe tufafina, in sāke sa su kuma? Na wanke ƙafafuna, in sāke ɓata su>
4Ƙaunataccena ya janye hannunsa daga ƙofa, Zuciyata kuwa tana kansa.
5Sai na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, ya shigo. Hannuna sharkaf da mur, Yatsuna suna ɗiga da mur sa'ad da na kama hannun ƙofar.
6Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ya riga ya tafi! Na so in ji muryarsa ƙwarai! Na neme shi, amma ban same shi ba. Na yi kiransa, amma ba amsa.
7Matsara masu kai da kawowa cikin birni suka same ni, Suka doke ni suka yi mini rauni. Matsaran da suke kan garu suka fige gyalena.
8Ku yi mini alkawari ku matan Urushalima, Idan kun ga ƙaunataccena, Ku faɗa masa na yi suwu saboda ƙauna.
9Ke mafi kyau cikin mata, Ki faɗi yadda ƙaunatacce naki yake. Wane abin sha'awa yake gare shi, Har da za mu yi miki alkawari>
10Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.
11Gashin kansa dogaye ne suna zarya, Baƙi wulik kamar jikin shaya. Kansa ya fi zinariya daraja.
12Idanunsa kamar na kurciyoyi a bakin ƙorama, Waɗanda suka yi wanka da madara suna tsaye a bakin rafi.
13Kumatunsa kyawawa ne kamar lambu, Wanda yake cike da tsire-tsire da kayan yaji. Leɓunansa kamar furen bi-rana ne, suna bulbulo da mur.
14Hannuwansa kyawawa ne, Saye da ƙawanen da aka yi musu ado da duwatsu masu daraja. Ƙugu nasa sumul sumul ne kamar hauren giwa da aka manne da yakutu.
15Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta, Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya. Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne, Da itatuwan al'ul ɗinsa mafi kyau.
16Bakinsa yana da daɗin sumbata, Kome nasa yana faranta mini rai. Matan Urushalima, yadda ƙaunataccena yake ke nan.
1Ke mafi kyau cikin matan, Ina ƙaunatacce naki ya tafi? Wace hanya ƙaunatacce naki ya bi? Za mu taimake ki nemansa.
2Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke. Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.
3Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce, Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.
4Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima, Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza, Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.
5Ki daina dubana gama idanunki suna rinjayata, Gashinki yana zarya kamar garken awaki Da yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
6Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya Aka yi mata wanka nan da nan. Ba giɓi, suna nan shar. An jera su tantsai.
7Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
8Ina da matan aure sittin, kowace kuwa sarauniya ce, Da ƙwaraƙwarai tamanin, da 'yan mata kuwa ba a magana!
9Amma ɗaya kaɗai nake ƙauna, Ita kyakkyawa ce kamar kurciya. Tilo ce ga mahaifiyarta, 'yar lele ce ga mahaifiyarta. Mata duk sukan dube ta, su yaba. Matan sarki da ƙwaraƙwaransa suka raira waƙa suka yabe ta.
10Wace ce wannan, kamar ketowar alfijir? Ita kyakkyawa ce mai haske, kamar hasken rana, Ko na wata mai kashe ido.
11Na gangara zuwa cikin itatuwan almond Domin in ga ƙananan itatuwan da suke a kwarin, Domin in ga ganyayen inabi Da furannin itatuwan rumman.
12Ina karkaɗuwa, don kin sa in ƙosa saboda ƙauna, Kamar mai korar dawakan karusar yaƙi.
13Komo, ki komo, ke Bashulamiya, Ki komo, ki komo domin mu ƙara dubanki. Me ya sa kuke so ku dubi Bashulamiya, Sa'ad da take taka rawar zamanin dā>
1Ƙafafunki suna da kyau da takalmi, Ke mafificiyar budurwa! Tsarin cinyoyinki kamar aikin gwanin sassaƙa ne.
2Cibinki kamar finjali ne, wanda bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi a ciki ba. Kwankwasonki kamar damin alkama ne a tsakiyar bi-rana.
3Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.
4Wuyanki kamar hasumiyar hauren giwa ne. Idonki kamar tafki ne cikin birnin Heshbon, Kusa da ƙofar Bat-rabbim. Hancinki kyakkyawa ne kamar hasumiyar Lebanon ta tsaron Dimashƙu.
5Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel. Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne, Yakan kama hankalin sarki.
6Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata, Kina sa ni jin daɗi a rai.
7Kina da kyan gani kamar itacen dabino, Mamanki kamar nonnan dabino.
8Zan hau itacen dabino in tsinko 'ya'yan. Mamanki kamar nonnan inabi suke a gare ni. Numfashinki kamar ƙanshin gawasa ne.
9Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne. Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena, Ya gangara leɓunan masu barci.
10Ni ta ƙaunataccena ce, yana bukatata.
11Zo saurayina, bari mu tafi waje, Mu kwana a karkara.
12Za mu tashi da sassafe, mu duba kurangun inabi, Mu ga ko sun fara tohowa, Ko furanni sun fara buɗewa. Mu ga ko itatuwan rumman sun yi fure. A can zan bayyana maka ƙaunata.
13Za ka ji ƙanshin shuke-shuke Da na dukan 'ya'yan itatuwa masu daɗi. Na adana maka jin daɗi na dā da na yanzu, ya ƙaunataccena.
1Da ma a ce kai ɗan'uwana ne, wanda mahaifiyata ta goya, Da in na gamu da kai a titi, Sai in sumbace ka, ba wanda zai kula.
2Sai in kai ka gidan mahaifiyata, In ba ka gaurayayyen ruwan inabina wanda aka yi da rumman, ka sha.
3In ta da kai da hannun hagunka, Ka rungume ni da hannun damanka.
4Ku yi mini alkawari, ku matan Urushalima, Ba za ku shiga tsakaninmu ba.
5Wace ce take zuwa daga cikin jeji, Kafaɗa da kafaɗa da ƙaunataccenta? A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, A wurin da aka haife ki, Wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
6Kada ki ƙaunaci kowa sai ni, Kada ki rungume kowa sai ni. Ikon ƙauna kamar na mutuwa ne, Ƙarfin kishin ƙauna kamar na mutuwa ne. Yakan kama kamar wuta, Yakan ci kamar gagarumar wuta.
7Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba. Ba rigyawar da za ta nutsar da ita. Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya, Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.
8Muna da 'yar'uwa ƙunƙuma. Me za mu yi idan wani saurayi ya ce yana sonta>
9Da a ce ita bango ce, da mun gina mata hasumiyar azurfa. Da a ce ita ƙofa ce, da mun yi mata ƙyaure da itacen al'ul.
10Ni bango ce, doguwa, mamana tantsai tantsai, Na sami kwarjini wurin ƙaunataccena.
11Sulemanu yana da gonar inabi A Ba'al-hamon, wato wuri mai yawan albarka. Ya yi ijara da waɗansu zaɓaɓɓun manoma. Kowannensu yana biyansa kuɗi, azurfa dubu.
12Ni ma ina da gonar inabi ta kaina. Kai Sulemanu zan ba ka kuɗi azurfa dubu, Sauran ma'aikata kuma zan ba kowanne ɗari biyu.
13Aminaina suna kasa kunne ga ƙaunataccena. Ina so in ji muryarka daga cikin lambun.
14Ya ƙaunataccena, ka zo wurina da sauri, kamar batsiya, Ko sagarin kishimi a kan duwatsu inda kayan yaji suke tsirowa.