HIKIMAR ƊAN SIRAK

1. A kan Asirin Hikima

1 Dukan hikima daga wajen Ubangiji take zuwa.

      Yana da ita har abada.

2 Wa zai yi lissafin rairayin teku,

      Ko yawan ruwan sama, ko kwanakin duniya?

3 Wa zai san iyakar tsawon sama,

      Ko faɗin duniya, ko zurfin ƙasa?

4 An halicci hikima gaba da kome,

      Tun fil azal akwai azanci.

5 Ga wanene aka sanar da asalin hikima?

      Wa ya san ayyukanta masu zurfin salō?

6 Ɗaya ne mai hikima, mai bantsoro ƙwarai,

      Yana zaune bisa kursiyi, Ubangiji ne.

7 Shi ya halicci hikima,

      Ya gan ta, ya lura da ita,

8 Ya zuba ta a dukan aikinsa,

      Domin ta zauna wurin dukan yan adam kamar kyautarsa,

      Allah yakan ba da ita ga masu sonsa.

A kan Tsoron Allah

9 in kana da tsoron Allah, ka sami girma, da daraja,

      Na jin daɗi da rawanin farin ciki.

10 Tsoron Ubangiji yana ba da farin zuciya,

      Da jin daɗi, da tsawon rai.

11 Mai tsoron Ubangiji zai sami kyakkyawan ƙarshe,

      Ran da zai mutu zai sami albarka.

12 Tsoron Ubangiji shi ne farkon hikima,

      An halicce ta kuwa gun amintattu tun suna ciki.

13 An yi ta wurin mutane dā,

      Ta ma liƙe wa yayansu.

14 Hikima cikakkiya tsoron Ubangiii ce,

      Tana da yabanya wadda za ta sa mutane su ji daɗi ƙwarai.

15 Tana cika gidajensu da abin da suke so,

      Tana cika rumbunansu da yayanta.

16 Tsoron Ubangiji rawam ne ga mai hikima,

      Yana sa mutane su tashi lafiya da salama.

17 Hikima tana ba da ilimi da ganewa mai yawa kamar ruwan sama,

      Tana ƙara wa masu riƙe ta daraja.

18 Tushen hikima tsoron Ubangiji ne,

      Rassanta tsawon rai ne.

A kan Haƙuri da Kamunkai

19 Haushin marar adalci ba zai kuɓutar da shi ba,

      Nauyin fushinsa shi ya sa zai fāɗi.

20 Mai haƙuri zai jure,

      A ƙarshe farin ciki zai ɓullo masa.

21 Zai yi shiru da shawararsa sai lokaci ya yi,

      Saan nan mutane da yawa za su baza labarin ganewarsa.

A kan Hikima da Adalci

22 Dukiyar hikirna na karɓar kowane ilimin gaskiya,

      Amma mai son zunubi yana raina bautar Allah.

23 In kana begen hikima, sai ka riƙe dokokin Allah,

      Ubangiji zai ba ka ita.

24 Gama hikima da koyo tsoron Ubangiji ne,

      Abin da yake so aminci ne da sanyin hali.

25 Kada ka ƙi tsoron Ubangiji,

      Kada ka tafi wurin Ubangiji da zuciya biyu.

26 Kada ka yi wa mutane munafunci,

      Ka yi hankali da abin da kake faɗa.

27 Kada ka ɗaukaka kanka, don kada a ƙasƙanta ka,

      Ka jawo wa kanka kunya.

28 Idan ba haka ba, Ubangiji zai nuna muguntarka da ka ɓoye,

      Zai hukunta ka a gaban jamaa.

29 Zai ce, Ba ka koyi tsoron Ubangiji ba,

      A zuciyarka akwai cuta.

2. Tsoron Allah Lokacin Gwadawa

1 Ɗana, in kana nufin bauta wa Ubangiji,

      Sai ka shirya kanka don jaraba.

2 Ka mai da zuciyarka daidai, ka ƙarfafa,

      Kada ka firgita a harin wahala.

3 Ka Iiƙe wa Ubangiji, kada ka rabu da shi,

      Nan gaba za ka sami girma.

4 Kowace irin wahala ta same ka, ka karɓe ta,

      In ƙasƙanci ya sāke zuwa, ka yi hakuri da shi.

5 Kamar yadda a kan gwada zinariya da wuta,

      Hakanan kuma a kan gwada mutanen da Allah ya karɓa, a tandar ƙasƙanci.

6 Ka amince da Ubangiji, zai ɗaukaka ka,

      Ka mai da hanyoyinka daidai, ka sa zuciya gare shi.

7 Ku masu. tsoron Ubangiji, ku dakaci jinƙansa,

      Kada ku ratse, don kada ku fāɗi.

8 Ku masu tsoron Ubangiji, ku amince da shi,

      Ba za ku rasa ladanku ba.

9 Ku masu tsoron Ubangiji, ku sa zuciya ga samun abubuwa masu kyau,

      Da farin ciki, da jinƙai madawwami.

10 Ku tuna da mutanen dā, ku gani,

      Wa ya amince da Ubangiji, ya ji kunya?

Ko wa ya riƙa tsoron Ubangiji, bai kula da shi ba?

      Ko wa ya roƙe shi, bai amsa masa ba?

11 To, Ubangiji yana kula da mutanensa, yana jinkansu,

      Yana yafe musu laifofinsu, yana cetonsu a lokacin wahala.

12 Kun shiga uku, ku masu karayar zuciya,

      Kuna da hannuwa, kun kasa aiki,

Kun shiga uku, ku masu laifi,

      Kuna tafiya ta hanya biyu.

13 Kun shiga uku, ku masu karayar zuciya, marasa sa zuciya,

      Don haka ba za a kiyaye ku ba.

14 Kun shiga uku, ku marasa hakuri,

      Me za ku yi ran da Ubangiji zai tambaye ku?

15 Masu tsoron Ubangiji ba za su ƙi maganarsa ba,

      Masu sonsa za su kiyaye dokokinsa.

16 Masu tsoron Ubangiji za su yi abin da yake so,

      Masu sonsa za su wadata da bin shariarsa.

17 Masu tsoron Ubangiji za su shirya zukatansu,

      A gabansa za su ƙasƙantar da kansu.

18 Sai mu fāɗa a ikon Ubangiji,

      Ba a ikon mutane ba.

Kamar yadda ɗaukakarsa take,

      Hakanan jinƙansa yake.

3. Game da Hakkin Iyaye

1 Yara, ku girmama hakkin mahaifanku,

      In kun yi haka, za ku tsira.

2 Gama Ubangiji ya ba uba fiko bisa yayansa,

      Ya ƙarfafa ikon uwa a kan yayanta.

3 Mai girmama mahaifinsa za a shafe masa laifofinsa,

      4 Mai girmama mahaifiyarsa kamar mai tanajin dukiya yake.

5 Mai girmama mahaifinsa zai sami farin ciki daga yayansa,

      In ya yi roƙo za a biya masa bukatarsa.

6 Mai girmama mahaifinsa zai sami tsawon rai,

      Wanda ya girmama mahaifiyarsa mai bin maganar Ubangiji ne.

7 Mai tsoron Ubangiji zai girmama mahaifinsa,

      Zai yi wa iyayensa hidima kamar sarakuna.

8 Ka girmama mahaifinka ta wurin aiki da magana,

      Domin ka sami albarkacinsa.

9 Albarkar uba ita ce tushen gidajen yayansa,

      Amma in uwa ta yi wa yayanta baki, za a tuƙe tushen gidajensu.

10 Kada ka ɗaukaka kanka bisa ƙasƙancin mahaifinka,

      Domin ƙasƙancin mahaifinka ba daraja ba ne gare ka.

11 Gama za a ɗaukaka mutum ta dalilin girman mahaifinsa,

      Ƙasƙancin uwa abin kunya ne ga yayanta.

12 Ɗana, ka taimaki mahaifinka da tsufansa,

      Kada ka wahalar da shi tun yana da rai.

13 Ko da tsohonka ya ruɗe, ka yi haƙuri da shi,

      Kada ka raina shi, saad da kake da ƙarfi.

14 Ba za a mance da jinƙan da ka yi wa mahaifinka ba,

      Wannan zai sa a riƙa yafe maka laifofi masu yawa.

15 Za a tuna da kai ran da kake shan azaba,

      Kamar yadda rana ke narke ƙanƙara,

      Hakanan za a shafe laifofinka.

16 Wanda ya raina mahaifinsa, ya saɓi Allah,

      Wanda ya sa uwa ta yi kuka, laananne ne wajen Ubangiji.

A kan Ƙasƙantar da Kai

17 Ɗana, ka yi aikinka da sanyin hali,

      Za a so ka fiye da mai yin kyautai.

18 Bisa ga girmanka ka ƙasƙanta kanka,

      Za ka sami alheri wajen Ubangiji.

19 Domin ikon Ubangiji mai girma ne,

      Ta wurin mai tawaliu ma za a ɗaukaka shi.

20 Kada ka nemi abubuwan da suka fi ƙarfinka,

      Kada ka yi nazarin abubuwan da ba za ka gane ba.

21 Abin da aka ƙaddara maka, ka yi ƙoƙari ka san shi,

      Domin ba ruwanka da abin da ke ɓoye gare ka.

22 Kada ka damu da abin da ya fi ƙarfinka,

      In an nuna maka abin da ya fi ganewar ɗan adam.

23 Mutane da yawa sun ruɗe a kan tsammaninsu,

      Mugun tunani ya ɓata hankalinsu.

24 Inda ba ido, ba a ganin haske,

      Inda ba ilimi, babu hikima.

Aibin Girmankai

25 Mai taurinkai, wahala ce ƙarshensa,

      Makashin maza, maza su kashe shi.

26 Mai taurinkai yana aza wa kansa baƙin ciki,

      Hakanan mai yin laifi yana kara wa kansa laifi.

27 Mai girmankai ba ya tauso,

      Gama mugunta ta yi wa zuciyarsa kanta.

28 Mai zurfin hankali zai yi naam da misalan gaskiya,

      Masu hikima suna son mai mai da hankali.

Yin Ƙaunar Matalauta

29 Ruwa yakan kashe wutar gobara,

      Hakanan jinƙai yakan shafe laifofi.

30 Wanda ke yin kyautai za a tuna da shi nan gaba,

      Lokacin da zai fāɗi zai sami mai tallabe shi.

4.

1 Ɗana, kada ka ƙi ba matalauci abin da yake bukata don rayuwarsa,

      Kada ka ƙyale mabukaci in yana kallonka.

2 Kada ka ɓata ran mayunwaci,

      Kada ka wulakanta mutum da wahalarsa.

3 Kada ka tura tutu da karan dafi,

      Kada ka yi jinkirin ba mabukaci taimako.

4 Kada ka kori mutum mai shan azaba

      In yana bukatar wani abu gare ka,

      Kada ka kawar da fuskarka daga matalauci.

5 Kada ka runtse idonka daga mai bukatar wani abu,

      Kada ma ka ba shi baya, ya laance ka.

6 Gama in mutum yana da ɓacin rai, har ya laance ka.

      Wanda ya halicce shi zai ji roƙonsa.

7 Ka zama abin so ga jamaa,

      Ka sunkuya ga mai sarauta.

8 Ka kasa kunne ga matalauci,

      Ka amsa masa da salama da sanyin hali.

9 Ka ceci mutum daga hannun mai yi masa zalunci,

      Kada ka yi fargaban aikata gaskiya a hukuncinka.

10 Ka zama kamar uba ga marayu,

      Ka taimaki gwauruwa, wadda mijinta ya rasu.

In ka yi haka, za ka zama kamar ɗan Maɗaukaki,

      Zai so ka fiye da yadda uwarka ke sonka.

Koyarwar Hikima

11 Hikima takan yi renon yayanta,

      Takan lura da masu nemanta.

12 Mai sonta yana son rai,

      Za a cika masu nemanta da farin ciki.

13 Wanda ya riƙe ta zai sami ɗaukaka,

      Ko inda ya zauna Ubangiji zai sa masa albarka.

14 Masu yin hidima gare ta suna yin hidima ga Allah mai tsarki,

      Masoyanta kuwa, Ubangiji yana sonsu.

15 Mai sauraronta zai yi hukunci daidai,

      Mai sa hankalinsa gare ta zai zauna da salama.

16 Idan ya amince da ita, zai same ta,

      Yayansa za su gāje ta.

17 Gama da farko takan raka mutum kamar baƙuwa,

      Tana jaraba shi,

Takan ja masa tsoro da kumamanci,

      Takan ba shi azaba da koyarwarta,

Takan jarraba shi ta neman hakkinta,

      Sai lokacin da ta amince da shi.

18 Daga baya takan mayar da shi ga farin ciki,

      Tana gwada masa asiranta.

19 In ya bauɗe mata, za ta rabu da shi,

      Za ta bar shi a hannun yan fashi.

A kan Kunya da Mugun Ladabi

20 Ɗana, ka waiwayi abin da ya kamata,

      Ka tsare kanka daga mugunta,

      Ba za ka ji kunya ba.

21 Wata kunya tana sa ka yi laifi,

      Wata kunya tana sa maka daraja da alheri.

22 Kada kwarjinin wani ya ba ka tsoro,

      Kada ka ji kunyar wani, har ka hallaka kanka.

23 Kada ka yi shiru lokacin da maganarka za ta yi wa wani amfani,

      Kada ka ɓoye hikimarka,

24 Gama da maganar mutum za a gane hikimarsa,

      Da abin da ya fada za a san abin da aka koya masa.

25 Kada ka yi musun gaskiya,

      In ba haka ba, ka zama kamar wanda yake so ya mai da ruwan kogi baya.

26 Kada ka ji kunyar hurta laifofinka,

      Amma ka ji kunyar rashin ganewarka.

27 Kada ka durƙusa a gaban wawa,

      Kada ma ka ƙi durƙusa wa masu sarauta.

21 Har mutuwa ka dinga ƙoƙari ka aikata gaskiya,

      Ubangiji Allah zai yi maka yaƙi.

29 Kada ka yi maganar gautsi,

      Amma kana ɓad da sawu.

30 Kada ka zama kamar zaki a gidanka,

      Kana kuwa da hainci a aikinka.

31 Kada ka miƙa hannunka domin ka karɓi kyauta,

      Amma kana miƙe hannu domin kada ka bayar.

5. A kan Arziki da Alfarma

1 Kada ka dogara ga dukiyarka,

      Kada ka ce, Da wannan zan iya kome.

2 Kada ka yarda da ƙarfinka,

      Kana bin shaawar zuciyarka.

3 Kada ka ce, Wa zai mallake ni?

      Gama Ubangiji zai rama wannan magana sosai.

4 Kada ka ce, Na yi zunubi, amma ba abin da ya same ni.

      Domin akwai ranar ƙin dillanci.

5 Kada ka tabbata za a gafarta maka

      In kana ƙara laifi bisa laifi.

6 Kada ka ce, Jinkan Ubangiji mai girma ne,

      Zai shafe yawan laifofina.

7 Domin yana da jinƙai da fushi,

      Fushinsa kuwa zai yi ƙuna kan masu laifi.

8 Kada ka makara ka juya kanka ga Ubangiji,

      Kada ka ce, Ba yau ba, sai gobe.

9 Gama ba labari fushin Ubangiji zai zo,

      Za ka halaka a lokacin ramuwarsa.

10 Kada ka dogara ga dukiyar zalunci,

      Ba za ta yi maka amfani a ranar harin Ubangiji ba.

Yin Magana Daidai

11 Kada ka kaɗu cikin kowace iska,

      Kada ka bi kowace hanya.

12 Ka ƙarfafa ganewarka,

      Maganarka ta zama daya.

13 Ka yi marmarin kasa kunne ga abin da ake gaya maka,

      Amma ka yi jinkirin yin jawabi.

14 In ka gane, ka ba mai tambayarka amsa,

      In ba ka gane ba, sai ka kame bakinka.

15 Akwai magana mai darajanta ka,

      Akwai mai wulakanta ka,

      Bakin mutum yakan yanke wuyansa.

16 Kada a kira ka maƙaryaci,

      Kada ma ka yi da wani.

17 Gama kisa shi ne horon ɓarawo,

      Cin mutunci kuma shi ne horon mai gulma.

6.

1 Ka kauce wa manyan laifofi da ƙanana,

      Kada ka zama mai gāba da abokinka.

Gama in ba ka da mutunci, za ka sha zambo da kunya,

      Haka yakan faru ga maƙaryaci.

2 Kada ka biye wa burin zuciyarka,

      Don kada ya cinye ƙarfinka kamar wuta,

3 Ya cinye ganyen zuciyarka, ka yi hasarar yabanyarta,

      Ka zama kamar itace busasshe.

4 Muguwar zuciya za ta hallaka mai ita,

      Za ta mai da shi abin dariya ga abokan gābansa.

A kan Abuta

5 Ɗaɗadar magana tana jawo wa mutum abokai da yawa.

      Mai iya baki na samun gaisuwa masu daɗi.

6 Ka zama mai faraa da kowa,

      Amma abokan shawararka ya zama ɗaya daga cikin dubu.

7 In za ka zama abokin wani, ka gwada shi,

      Kada ka amince da shi da sauri.

8 Gama akwai masoyanka lokacin da kake da abin hannu,

      Amma ba su jurewa a lokacin wahalarka.

9 Akwai masoyanka kuma da sukan zama abokan gābanka,

      Masu zaginka don su kunyata ka a sarari.

10 Akwai kuma masoyanka irin na abinci,

      Amma ba su jurewa a lokacin wahalarka.

11 Irin waɗannan masoya suna yin amfani da dukiyarka,

      Kamar yadda kake yi da ita,

      Suna yin umarni ga barorin gidanka,

12 Amma ran da dukiyarka ta ƙare, su abokan gābanka ne,

      Suna ɓoye wa fuskarka.

13 Ka yi nisa da magabtanka,

      Ka liƙe wa abokanka.

14 Amintaccen aboki babbar mafaka ne,

      Wanda ya same shi ya sami dukiya ke nan.

15 Amintaccen aboki ba za ka iya sayensa ba, kome yawan kuɗinka,

      Ba mai iya auna halin kirkinsa.

16 Amintaccen aboki kamar magani ne don wartsakarwa,

      Masu tsoron Ubangiji za su same shi.

17 Masu tsoron Ubangiji suna aniya,

      Su dace da amintaccen aboki,

      Gama abokan mutum kama da shi suke.

Koyon Hikima

18 Ɗana, ka yi ƙokarin koyo tun kana ƙarami,

      Za ka dinga samun hikima har tsufanka.

19 Ka je wurinta kamar mai huda yana shuka,

      Ka jira yabanyarta mai kyau.

20 Cikin nomanta za ka yi aiki kaɗan,

      Amma za ka ci amfaninta da wuri.

21 Tana da wuya sosai ga marasa horo,

      Mutum marar hankali ba ya jure mata.

22 Tana kama da kayan dutse mai nauyi bisa kansa,

      Ba zai daɗe da ita ba, sai ya yar.

23 Lalle horo yana da wuya,

      Mutane da yawa ba su yin naam da shi.

24 Ji, kai ɗana, ka karɓi gargaɗina,

      Kada ka ƙi bin shawarar da na yi maka.

25 Ka sa ƙafafunka cikin dabaibayin da hikima ta yi maka,

      Ka sa wuyanka cikin ragamar da ta ɓalla maka.

26 Ka sa kafaɗunka, ka ɗauke ta,

      Kada ka damu da ɗaurewarta.

27 Ka tafi wurinta da dukan ranka,

      Ka kiyaye hanyoyinta da dukan ƙarfinka.

28 Ka neme ta, za ka gane ta,

      Ka neme ta, za ka same ta,

      In ka kama ta, kada ka sake ta.

29 Saan nan za ka sami hutawa gare ta,

      Za ta zamar maka abin farin ciki.

30 Ɗamararta za ta zamar maka babbar mafaka,

      Maɗaurinta zai zamar maka kitso mai roho.

31 Za ka sa ta kamar rigar daraja,

      Za ka naɗa ta kamar rawanin girma.

32 Ɗana, in kana so, za ka iya koyo,

      In ka sa ranka, za ka zama mai zurfin salo.

33 In kana so sauraro, za ka koya,

      In ka kasa kunne, za ka zama mai hikima.

34 Ka tsaya cikin taron dattawa,

      In akwai mai hikima, ka liƙe masa.

35 Ka saurari dukan maganar da ke zuwa daga wajen Ubangiji,

      Kada ka rasa gane hikimar karin magana,

36 In ka sani akwai mutum mai ganewa,

      Ka tafi wurinsa tun da sassafe,

Ka dinga zuwa wurinsa,

      Har ka zage dokin ƙofar ɗakinsa da sawayenka.

37 Ka yi tunani a kan umarnan Ubangiji,

      Ka tuna da dokokinsa kullum.

Shi zai haskaka zuciyarka,

      Zai ba ka hikimar da kake bege.

7. Gargaɗi Iri Iri

1 Kada ka yi mugunta,

      Mugunta ba za ta same ka ba,

2 Ka rabu da zalunci,

      Zalunci zai rabu da kai.

3 Kada ka shuka zalunci,

      Ba za ka girbe shi ninki bakwai ba.

4 Kada ka nemi shugabanci a wajen Ubangiji,

      Ko kujerar daraja wurin sarki.

5 Kada ka nuna kai mai adalci ne a gaban Ubangiji,

      Ko mai hikima gaban sarki.

6 Kada ka nemi zaman alkali,

      Kila ba za ka iya hana zalunci ba,

Ko kwarjinin wani mai iko zai ja hankalinka,

      Ka ɓata adalcinka.

7 Kada ka yi wa jamaar gari laifi,

      Don kada ka kā da girmanka gare su.

8 Kada ka sāke yin mugun abu,

      Don laifin da ka yi ya isa a yi maka hukunci.

9 Kada ka yi tsammani, don kana yin sadaka

      Allah zai duba yawan sadakarka,

      Ko don kana hadaya ga Allah Maɗaukaki, zai karɓe ta.

10 Kada ka gaji da roƙon Ubangiji,

      Kada ka daina yin sadaka.

11 Kada ka yi wa wanda ransa ya ɓaci dariya,

      Gama Allah ne mai ƙasƙantar da shi,

      Yana kuma ɗaukaka shi.

12 Kada ka ƙirƙira wa danuwanka ƙarya,

      Kada ma ka yi wa abokin zamanka haka.

13 Ka yi hankali da yin kowace irin ƙarya,

      Domin ba wani abin kirki da zai zo daga wurinta.

14 Kada ka yi surutu a taron dattawa,

      Kada ka yi ta maimaitawar banza in kana addua.

15 Kada ka ƙi yin aiki mai wuya,

      Ko aikin noma wanda Ubangiji ya kafa.

16 Kada ka ce kai ka fi kowa gaskiya,

      In ka yi haka, fushin Ubangiji ba zai makara ba.

17 Ka ƙasƙantar da kanka sosai a gaban Ubangiji,

      Domin mutum mai mutuwa ne kai.

18 Kada ka musayi aboki da kuɗi,

      Ko danuwanka na gaske don zinariya, har irin ta Ofir.

19 Kada ka saki mace mai ganewa,

      Don macen kirki ta fi zinariya daraja,

20 Kada ka wulakanta yaronka mai aiki da gaskiya,

      Ko ɗan ƙodago mai ƙoƙarin aiki.

21 Ka ƙaunaci yaro mai ganewa kamar kanka,

      Kada ka rasa ba shi yancinsa.

A kan Dabbobi, da Yara, da Mata

22 In kana da dabbobi, ka lura da su,

      In suna da amfani gare ka, ka kiyaye su.

23 In kana da yara, ka hore su,

      Ka lanƙwasa wuyansu tun suna ƙanana.

24 In kana da yaya mata, ka hana su yin karuwanci,

      Kada ka sakar musu fuska.

25 In ka kai yarka aure, ka kyauta,

      Amma ka ba mai hankali.

26 In kana da mata, kada ka ƙi ta,

      Amma in ta ƙi ka, ka yi hankali da ita.

A kan Iyaye

27 Da dukan zuciyarka ka girmama mahaifinka,

      Kada ka mance azabar da mahaifiyarka ta sha a kanka.

28 Ka tuna su ne suka haife ka,

      Da me za ka saka musu abin da suka yi maka?

A kan Firistoci

29 Da dukan ranka ka ji tsoron Ubangiji,

      Ka girmama firistoci makusantansa.

30 Da dukan ikonka ka ƙaunaci Mahaliccinka,

      Kada ka ƙyale maaikatansa.

31 Ka ji tsoron Ubangiji, ka girmama firistocinsa,

      Ka ba su rabonsu, kamar yadda sharia ta umarce ka,

Wato tumun fari, da hadaya don laifofi,

      Da naman karfata, hadayar kwana arbain,

      Da yan fari na tsarkakan abubuwa.

A kan Matalauta da Masu Shan Wahala

32 Ka miƙa hannunka ga matalauci,

      Domin ka sami albarka cikakkiya,

33 Sai karamarka ta kai ga dukan masu rai,

      Har ga matattu, kada ka rasa yin alheri.

34 Kada ka rasa taimakon masu damuwa,

      Ka taya masu kuka.

35 Kada ka ji ƙyamar lura da marasa lafiya,

      Ta hanyar yin wannan za a ƙaunace ka.

36 Cikin dukan ayyukanka ka tuna da ƙarshenka,

      Har abada ba za ka yi laifi ba.

8. A kan Hankali da Dabara

1 Kada ka yi faɗa da mai iko,

      Don kada ka faɗi cikin hannuwansa.

2 Kada ka yi faɗa da mai arziki,

      Don kada ya sa a hallaka ka.

Gama zinariya ta hallakar da mutane masu yawa,

      Ta jawo zukatan sarakuna.

3 Kada ka saɓa da mai wayon magana,

      Don kada ka ƙara itace a wutar zuciyarsa.

4 Kada ka yi wasa da marar ladabi,

      Don kada ya zagi kakanninka.

5 Kada ka tsauta wa wanda ya tuba kan laifinsa,

      Ka tuna, dukanmu muna da laifofi.

6 Kada ka raina wanda ya tsufa,

      Domin waɗansunmu ma, za mu tsufa.

7 Kada ka yi murna da mutuwar mutum,

      Ka tuna, dukanmu za mu mutu.

Girmama Gādajjiyar Hikirna

8 Kada ka ƙi maganar masu hikima,

      Ka tuna da misalan gaskiya da, suke fada,

Domin za ka koyi ladabi daga wajensu,

      Yadda ya kamata a yi a gaban manyan mutane.

9 Kada ka raina maganar dattawa,

      Wadda suka koyo daga wajen iyayensu.

Daga wajensu za ka koyi hankali,

      Na yadda za ka ba da amsa a lokacin da ya kamata.

A kan Hankali

10 Kada ka hura garwashin mai yin laifi,

      Don kada a ƙone ka cikin gobararsa.

11 Kada ka yi fargaba a gaban ɗan fashi,

      In ba haka ba, zai ƙara matsa maka lamba.

12 Kada ka ba wanda ya fi ka ƙarfi rance,

      Amma in za ka ba shi, ka fita batunsu.

13 Kada ka tsaya wa wani ga abin da ya fi ƙarfinka,

      Amma in za ka tsaya masa, sai ka shirya ka biya.

14 Kada ka tafi wajen sharia da alƙali,

      Domin za a yi masa sharia bisa ga nufinsa.

15 Kada ka yi tafiya da maƙetaci,

      Don kada ya jawo maka wahala.

Gama zai yi abin da ya ga dama,

      Rashin hankalinsa zai watsa masu taryenku,

16 Kada ka yi faɗa da mai saurin husata,

      Kada ka tafi jeji da shi,

Domin jininka ba kome ba ne a gare shi,

      Wurin da ba mai taimako zai kashe ka.

17 Kada ka yi shawara da wawa,

      Domin ba zai iya rufa maka asiri ba.

18 A gaban wanda ba ka sani ba,

      Kada ka yi abin da yake na asiri,

      Don ba ka san abin da zai ƙera a kai ba.

19 Kada ka bayyana tunanin zuciyarka ga dukan mutane,

      Don kada ka ɓata darajarka.

9. A kan Mata

1 Kada ka yi wa ƙaunatacciyar matarka ƙage,

      Don kada ka koya mata yadda za ta yi maka ƙeta.

2 Kada ka ba matarka wuyan hannunka ta riƙe,

      Don kada ta karya ƙarfinka.

3 Kada ka nemi karuwa,

      Don kada ta cuce ka.

4 Kada ka yi annashuwa da mace mai begenka da waƙa,

      Don kada ta kama ka da tarkon da ta shirya.

5 Kada ka yi Ialata da budurwa,

      Don kada a hukunta ka.

6 Kada ka amince da karuwai,

      Don kada ka ɓata gādonka.

7 Kada ka yi bincike cikin kwararon gari,

      Kada ka yi yawo lungu lungu.

8 Ka kawar da idonka ga mace mai kyan diri,

      Kada ka cika kallon matar wani.

Mutane da yawa sun halaka saboda kyan mace,

      Gama soyayyarta tana ƙuna kamar wuta.

9 Ko kaɗan kada ka zauna da matar aure,

      Ko yin hira da ita, kuna shan giya,

Don kada ta jawo ranka gare ta,

      Har a kashe ka.

A kan Maza

10 Kada ka rabu da abokinka wanda kuka daɗe,

      Gama sabon aboki bai yi kamar wancan ba,

Sabon aboki kamar sabon ruwan inabi yake,

      In ya nuna, za ka sha shi da farin ciki.

11 Kada ka yi hassada a kan saar mai laifi,

      Domin ba ka san abin da zai same shi ba.

12 Kada ka yi murna da cin nasarar mai alfarma,

      Ka tuna, tun kafin ya mutu, za a hukunta shi.

13 Ka yi nisa da wanda ke da iko ya kashe ka,

      Saan nan ba za ka ji tsoron mutuwa ba.

In ka kusace shi, kada ka saɓa masa,

      Don kada ya kashe ka.

Ka tuna, kana tafiya a cikin tarkuna

      Ko tsakanin ashiftu.

14 Bisa ga iyawarka ka ƙarfafa abuta da maƙwabcinka,

      Ka yi shawara da masu hikima.

15 Sai ka yi hirarka da masu hankali,

      Ka yi dukan maganarka a kan shariar Maɗaukaki.

16 Ka ci abinci tare da abokai masu gaskiya,

      Ka yi takamarka da tsoron Ubangiji.

17 Sai ta hannuwan masu fannin aiki aiki zai dace da yabo,

      Hakanan ya kamata shugaban jamaa ya riƙa yin maganar hikima.

18 Mai iya baki, ana tsoronsa a garinsu,

      Amma mai maganar banza za a shi.

Aibin Alfarma

6 Ko ta wane irin laifi, kada ka saka wa maƙwabcinka da mugunta,

      Kada ka yi kome da cin mutunci.

7 Girmankai abin ƙyama ne ga Ubangiji dayan adam,

      Dukansu suna ƙin zalunci.

8 Sarauta tana sauyawa daga kabila zuwa kabila

      Saboda zaluncin masu alfarma.

9 A kan me mutane na turɓaya da toka suke yin alfarma?

      Ko da ya ke suna da rai, yan cikinsu na da wari.

10 Ciwo kaɗan—likita ya yi dariya,

      Sarkin yau—zai mutu gobe.

11 Lokacin da mutum ya mutu zai ruɓe,

      Ya zama rabon ƙwari da tsutsotsi.

12 Farkon alfarma shi ne taurinkai,

      Don zuciyar mutum ta rabu da Mahaliccinta,

13 Gama alfarma ita ce kandamin zunubi,

      Maɓuɓɓuga kuma mai yada abin ƙyama.

Saboda haka Ubangiji ya yi wa irinsu horon mamaki,

      Har ya watsar da su sam.

14 Ubangiii ya tunkuɗe masu alfarma daga gadajen sarautarsu,

      Ya sa masu sanyin hali a kai.

15 Ubangiji yakan cire tushen masu alfarma,

      Yakan dasa masu ƙasƙantar da kai a wurinsu.

16 Ubangiji yakan ƙurme masu alfarma,

      Yakan tuge saiwoyinsu.

17 Yana jirkice masu alfarma daga duniya,

      Ya shafe su, ba a ƙara tunawa da su ba.

18 Ba a halicci alfarma don mutane ba,

      Ko babban fushi don yan adam.

A kan Masu Dacewa da Yabo

19 Wace kabila ce ta dace da yabo?

      Ta yan adam.

Wace kabila ce ke da yabo

      Ta masu tsoron Ubangiji.

Wace kabila ce ba ta dace da yabo ba?

      Ta yan adam.

Wace kabila ce ba ta da yabo?

      Ta masu keta dokoki.

20 Masarauci na samun yabo a tsakanin yanuwansa,

      Mai tsoron Ubangiji na samun yabo a tsakanin mutanensa.

21 Duk matafiya da yan ci rani, da yan ƙodago, da baƙi, da matalauta,

      Suna da abin taƙama da tsoron Ubangiji.

22 Ba daidai ba ne a wulakanta matalauci mai hankali,

      Bai kamata a ɗaukaka mai yin laifi ba.

23 Sarki, da aiƙali, da mai iko, za a ɗaukaka su,

      Amma mai tsoron Ubangiji ya fi su girma.

24 In masu yanci sun yi wa bawa mai ganewa hidima,

      Mai hikima ba zai yi gunaguni ba.

A kan Kaskantar da Kai da Gaskiya

25 Kada ka cika nuna kai gwanin aiki ne,

      Kada ma ka yi wata taƙama in kana shan masifa.

26 Wanda ya yi aiki yana da kome,

      Ya fi wanda ke yawon takama, amma ba abin zaman gari.

27 Ɗana, ɗaukaka kanka da sanyin hali,

      Ka nemi yabon da ya dace da kai.

28 Wanda bai kula da hakkinsa ba, wa zai taimake shi?

      Wanda ke raina kansa, wa zai ɗaukaka shi?

29 Akan ɗaukaka matalauci saboda ganewarsa,

      Akan ɗaukaka mai arziki saboda arzikinsa.

30 Wanda aka ɗaukaka yana talauci,

      In yana da arziki ɗaukakarsa ta fi ta kowa,

Amma wanda aka raina yana arziki,

      In yana da talauci raininsa ya fi na kowa.

11. Kada a Amince da Abin da ake Gani

1 Hikimar matalauci tana sa shi ƙarfin zuciya,

      Tana sa ya zauna a tsakiyar manyan mutane.

2 Kada ka yi yabon mutum saboda kyansa,

      Kada ka yi wa mutum sharri saboda muninsa.

3 Zuma ita ce ƙaramar halitta a cikin ƙwari,

      Amma saƙarta ta fi kome zaƙi.

4 Kada ka yi wa mai tsohuwar tufa baa,

      Kada ma ka yi wa mai shan wahala gori,

Domin ayyukan Ubangiji masu banmamaki ne,

      Sun kuma ɓoye wa mutane.

5 An taɓa zaunar da matalauta a kan gadon sarauta,

      Wanda ba a tsammani zai sami sarauta ba,

      Sai ga shi da rawaninta.

6 An yi wa sarakuna da yawa sharri sosai,

      Masu daraja da yawa kuwa, waɗansu sun mallake su.

A kan Shawara da Tunani

7 Kafin ka sa wa wani laifi, ka yi bincike,

      Yi tunani tukuna saan nan ka yi horo.

8 Kada ka ba da amsa kafin ka ji,

      Kada ka taryi maganar wani tun bai gama ba.

9 Kada ka yi binciken abin da bai shafe ka ba,

      Kada ka shiga faɗan masu saɓo.

10 Dana, kada ka soma ayyuka dabam dabam masu yawa,

      In ka nemi yawan kuɗi, ba za ka bauɗe wa masifa ba,

Ko da ya ke kana neman wadata da sauri ƙwarai,

      Saurinka zai haifi nawā,

      Kome yawan aniyarka, ba za ka same ta ba.

11 Akwai wanda ya yi aiki da sauri da aniya, har ya gaji,

      Duk da haka, abin da yake nema ya ƙara yi masa nisa.

A Dogara ga Allah Kadai

12 Akwai sumbuɗaɗɗe, mai bukatar taimako,

      Ba shi da ƙarfi, yana da wahala sosai,

Amma Ubangiji ya dube shi da kyau,

      Ya ɗaga shi daga juji.

13 Ya ɗaga shi sama,

      Mutane da yawa sun yi mamakinsa.

14 Abubuwa masu kyau da marasa kyau, rai da mutuwa,

      Talauci da arziki,

      Dukansu daga wurin Ubangiji suke.

15 Hikima, da ganewa, da ilimin duniya,

      Da ƙauna, da halin kirki, daga wurin Ubangiji suke.

16 An ƙaddara wa maketata kuskure da duhun kai tun ranar haihuwarsu,

      Haka za su zama har mutuwa.

17 Kyautar Ubangiji tana daɗewa ga masu tsoronsa,

      Alherinsa yana ba su ci gaba har abada.

18 Akwai wanda ya zama mai arziki ta yin rowa,

      Ga sakamakon da zai samu.

19 Inda ya ce, Na sami hutu,

      Yanzu zan ci dukiyata,

Bai san lokacin da zai mutu ba,

      Ya bar dukiyarsa ga waɗansu.

20 Ka tsaya a fannin sanaarka, ka yi aiki da ita,

      Ka kuma daɗe cikin aikinka.

21 Kada ka yi shaawar ayyukan masu yin laifi,

      Ka amince wa Ubangiji, ka jira haskensa,

Domin ba wuya ga Ubangiji

      Ya mayar da matalauci tajiri, ba zato ba tsammani.

22 Albarkar Ubangiji ladan mai tsoronsa ce,

      Albarkarsa za ta yi fure lokacin da ya kamata.

23 Kada ka ce, Ina abin bukatata?

      Nan gaba duk abin da nake so zan samu.

24 Kada kuma ka ce, Abin da nake da shi ya ishe ni,

      Me zai wahalar da, ni nan gaba?

25 Ranar samu ana mancewa da wahala,

      Ranar wahala ana mancewa da samu.

26 Domin lokacin da mutum zai mutu,

      Abu ne mai sauki ga Ubangiii

      Ya biya shi bisa ga ayyukan da ya yi.

27 Wahalar ɗan lokaci kadan

      Tana sa mutum ya mance da daɗin da ya taɓa sha,

      A ƙarshen mutum za a bayyana ayyukansa.

28 Kada ka yi yabon kirkin mutum kafin ya mutu,

      A ƙarshen mutum za a sansance ko shi wane iri ne.

Kada a Amince da Mugun Mutum

29 Ba za a kira kowane mutum gidanka ba,

      Gama tarkunan marikici yawa gare su.

30 Ko da ya ke ya zauna ɗaka kamar tsuntsu cikin keji,

      Yana neman wurin shiga da fita don ya yi maka sata.

31 Mazambaci na mai da abin kirki mugunta,

      Da ɗan tartsatsin wuta yakan ƙone babban kaskon gawayi.

32 Hakanan mai zunubi ke neman damar zubar da jini,

      Yana yin maƙirci, ya kwashe kayanka na ƙāwā.

33 Ka yi hankali da mai mugunta, ƙeta yake haifawa,

      Kada ka ɓata sunanka yadda ba zai gyaru ba.

34 In ka kawo wanda ba ka sani ba, gidanka, zai kawo rudami,

      Zai shiga tsakaninka da mutanen gida.

12. Dokoki a kan Yin Abin Kirki

1 In kana yin abin kirki,

      Ka san wanda kake yi wa,

      Saan nan za a gode maka don kyawawan ayyukanka.

2 Ka yi wa mai gaskiya abin kirki,

      Za ka sami lada,

In ba daga wurinsa ba,

      Hakika daga wurin Maɗaukaki.

3 Ba abin kirki da zai zo wa mutumin da ke agajen mugaye,

      Ai, wannan ba aikin jinƙai ba ne.

4 Ka ba mai gaskiya,

      Kada ka taimaki mai yin laifi.

Ka ƙarfafa wanda ake tsananta,

      Kada ka ba mai alfarma wani abu.

Ka yi abin kirki ga mai ƙasƙantar da kai,

      Kada ka ba marar bin Allah kome.

5 Ka hana shi makamai, kada ka ba shi,

      Kila ya yi maka ɗanɗana kuɗarka da su.

6 Saan nan zai saka maka sau biyu da mugunta,

      Don dukan abin da ka yi masa mai kyau,

7 Domin Maɗaukaki kansa ya ƙi masu zunubi,

      Zai kuma yi wa masu mugunta sakayya da horo.

A kan Abokan Ƙarya da na Gaskiya

8 In kana jin daɗi,

      Ba za ka iya gane abokin gaskiya ba,

Amma in kana shan wahala,

      Abokin gāba ba zai iya ɓoye maka ba.

9 Lokacin da mutum ke jin daɗi

      Har abokan gābansa suna taya shi murna,

Lokacin da yake shan wahala,

      Har aboki ma yakan watsar da shi.

10 Har abada kada ka amince da abokin gāba,

      Kamar yadda jan ƙarfe yakan yi tsatso,

      Hakanan abokin gāba zai yi mugunta.

11 Ko ma ya nuna halin ƙasƙantar da kai,

      Yana durƙusa maka in ya zo,

      Ka yi hankali, ka kiyaye kanka game da shi.

Goge shi kamar yadda kakan goge jan ƙarfe,

      Za ka san yana da sauran tsatsa.

12 Kada ka tsai da shi kusa da kai,

      Watakila ya ture ka, ya ɗau matsayinka.

Kada ka zaunar da shi a na damanka,

      Domin zai nemi matsayinka,

A ƙarshe za ka tabbatar da. gaskiyar kalmomina,

      Za ka ji zafi don ba ka ji gargaɗina ba.

13 Wa ke jin tausayin gardin maciji, in macijin ya sare shi?

      Ko waɗanda ke kusatar mugayen dabbobi?

14 Haka yake ga mutum mai tarayya da mai alfarma,

      Wanda ke taimakonsa yin laifofi.

15 In ka tsaya tsayin daka, ba zai nuna kansa ba,

      Amma in ka karkace sau ɗaya, zai gwada ikonsa,

16 Abokin gāba daɗin baki gare shi,

      Amma a zuciyarsa hanya yake nema ya jefa ka a rami.

Abokin gāba yana iya zubar da kwalla,

      Amma in ya sami sarari,

      Ko fitar da jini ma ba zai ishe shi ba.

17 In ka yi hasara, zai riga ka wurin,

      Kamar mai taimakonka zai kama diddigenka, ka fāɗi,

18 Zai kaɗa kai, ya tāfa hannuwansa,

      Ya yi raɗe‑raɗe, ya yi maka zunɗe.

13. Yin Tarayya da Tsararka

1 Duk wanda ya taɓa kwalta zai kazantu,

      Abokin ɓarawo ma shi ɓarawo ne.

2 Kada ka ɗauki nauyin da ya fi ƙarfinka,

      Kada ka haɗa abuta da wanda ya fi ka wadata.

Me ya haɗa tukunyar yumɓu da ta ƙarfe?

      In ta yumɓu ta yi karo da ta ƙarfe, za ta fashe.

3 Mawadaci, in ya yi laifi, zai yi taƙama da laifinsa,

      Matalauci, in an yi masu laifi, roƙon gafara yake yi.

4 In kana da mamora, mawadaci zai more ka,

      Amma in moriyarka ta ƙare, zai watsar da kai.

5 In kana da samu, zai daddaɗar magana da kai,

      Zai yi maka murmushi ya kara maka buri.

6 In yana bukatarka, zai ribace ka,

      Saan nan zai washe ka, ba zai damu ba.

7 Hannu mai maiƙo shi yake lasa,

      Saan nan sau biyu ko uku zai ciji hannun da ya ba shi abincin.

Daga baya in ya gan ka zai wuce ka,

      Zai kuma yi maka baa.

8 Ka kula kada ka yi fariya,

      Don kada ka yi kama da wawaye.

9 In mai girma ya gayyace ka, nuna kasawa,

      Zai ƙara matsa gayyatarka.

10 Kada ka kutsa kanka gare shi, don kada a ture ka,

      Amma kada ka tsaya nesa, za a mance da kai.

11 Kada ka cika yin magana da shi,

      Kada kuma ka amince da yawan maganarsa,

Tun da ya ke dukan maganarsa yana yi ne don ya gwada ka,

      Ko da yake yin murmushi, yana auna ka.

12 Cikin ƙetarsa zai mai da kai madari,

      Ba zai sawwaƙe maka ta bugu ko ɗauri ba.

13 Ka yi hankali, ka kula sosai,

      Kada ka yi tafiya da masu saurin fushi.

14 Kowane rayayyen abu yana ƙaunar irinsa,

      Kowa kuma ɗan garinsu yake so.

15 Kowace halitta na gauraya da irinta,

      Mutum kuma na liƙe wa irinsa.

16 Ta yaya dila da rago za su haɗu?

      Hakanan yake ga mai laifi da mai ibada.

17 Wane zaman daɗi ke tsakanin kura da kare?

      Wane zaman daɗi kuma ke tsakanin mawadaci da matalauci?

18 Jakunan jeji abin farauta ne ga zakoki,

      Haka ma masu arziki ke farautar matalauta.

19 Tawaliu abin raini ne ga mai alfarma,

      Haka ma matalauci abin raini ne ga mawadaci.

20 In mawadaci ya yi tuntuɓe,

      Abokansa sukan ta da shi,

In matalauci ya faɗi,

      Abokansa sukan ƙara ture shi waje daya.

21 In mawadaci ya yi jawabi,

      Akwai masu goyon bayansa da yawa,

Ko da maganar banza ce, akan ce masa, Barka.

      In matalauci ya yi magana, za a yi masa ihu,

      Ya yi maganar gaskiya, amma ba wanda ya saurara.

22 Mawadaci ya yi magana, kowa ya yi shiru,

      Har suna ɗaga ta ƙwarai a sarari.

Matalauci ya yi magana,

      Mutane sun ce, Wanene wannan?

Saan nan in ya zame,

      Sai su ƙara danne shi ƙasa.

23 Dukiya tana da kyau in ba saɓo,

      Talauci mugun abu ne, in ji marar bin Allah.

24 Zuciyar mutum takan sauya fuskarsa

      Ta yi kyau ko muni.

25 Alamar kyakkyawar zuciya ita ce fuskar farin ciki,

      Fuskar sā ita ce alamar mugun nufi.

14. A kan Farin Cikin Gaskiya

1 Albarka ta tabbata ga wanda bai zame da magana ba,

      Wanda bai taɓa ɓacin rai game da yin laifi ba.

2 Albarka ta tabbata ga wanda ransa bai ba shi laifi ba,

      Wanda bai taɓa karaya ba.

A kan Kishi da Zari

3 Dukiya bai kamata ga mai rowa ba,

      Ina amfanin zinariya ga bahili?

4 Dukiyar da ya hana kansa,

      Ya ajiye wa sauran mutane,

      Sauran mutane za su ji daɗin wadatarsa.

5 In mutum na yi wa kansa ƙeta,

      Wa zai yi wa abin kirki ke nan?

      Ba ya mammore wa abin da ke nasa.

6 Ba wanda ya kai ƙetar mai yi wa kansa rowa,

      Yana horon kansa saboda bahilanci.

7 In kuwa ya yi abin kirki,

      Ya yi shi ba da nufinsa ba,

8 A ƙarshe zai bayyana muguntarsa.

      Mai ganin ƙwanji, rabonsa ba ya wadatarsa,

      9 Yana hana ɗanuwansa, yana hallaka kansa.

10 Ko bahili ya girbi sabon hatsi,

      Ba ya ci sai sūnā.

11 Ɗana, kiwaci kanka da abin hannunka,

      Ka more shi kamar yadda za ka iya.

12 Ka tuna mutuwa ba za ta yi jinkiri ba,

      Ba a kuma bayyana maka ran da aka ƙaddara maka ba.

13 Yi wa abokinka alheri kafin ka mutu,

      Ka sa masa dukiyarka.

14 Kada ka ƙi amsar farin cikin da yau ta mika maka,

      Kada ka har rabon kyakkyawar shaawa ya wuce ka.

15 Ba za ka har amfanin aikinka ga wani ba?

      Ba za a kuma rarraba amfanin wahalarka ta kuria ba?

16 Bayar, ka karɓa, ka yi shakatawarka,

      Domin a cikin kabari ba za a nemi annashuwa ba.

17 Kowane rayayyen abu yakan tsufa kamar tufafi,

      Ƙaddara ce tun fil azal za ka mutu dole.

18 Kamar yawan ganyaye a lafiyayyen itace,

      Wadansu na faduwa, waɗansu na girma,

Haka yake ga zuriyar yan adam.

      Wani ya mutu, a haifi wani.

19 Kowane abin da aka yi yakan ruɓe, ya wargaje,

      Mai yinsa kuma zai bi shi.

A kan Farin Cikin Mai Hikima

20 Albarka ta tabbata ga wanda ke himmantuwa da hikima,

      Wanda yake yin tunani a kan ilimi,

21 Wanda ke koyon hanyoyin hikima a zuciyarsa,

      Da tunanin labinta kuma.

22 Yana binta kamar mafarauci,

      Yana fakō ta hanyarta,

23 Yana leƙe ta tagarta,

      Yana saurare a ƙofarta.

24 Ya yi masauki kusa da gidanta,

      Ya daura alfarwarsa ga bangon gidanta.

25 Ya kafa bukkarsa kusa da ita,

      Ya zauna inda take naam da shi.

26 Ya yi sheƙa cikin itacenta,

      Ya yi zamansa kan rassanta.

17 Ta kanta yake samun mafaka daga zafi,

      A gidanta kuma yake zaune.

15.

1 Duk mai tsoron Ubangiji haka zai yi,

      Duk mai rike sharia kuma zai sami hikima.

2 Za ta zo taryarsa kamar uwa,

      Ta karɓe shi kuma kamar amarya budurwa.

3 Za ta ba shi abincin ganewa ya ci,

      Da ruwan ilimi ya sha.

4 Zai jingina da ita, ba zai faɗi ba,

      Zai dogara kanta, ba zai kunyata ba.

5 Za ta ɗaga shi kan makwabtansa,

      Za ta ba shi fasahar magana a taruwar manyan mutane.

6 Zai sami farin ciki da murna,

      Da madawwamin suna kuma.

7 Wawaye ba za su same ta ba,

      Masu saɓo ma ba za su gan ta ba.

8 Ta tsaya nesa da masu alfarma,

      Makaryata ba za su iya tunawa da ita ba.

9 Yabo bai kyautu a bakin mai saɓo ba.

      Tun da ya ke Ubangiji bai sa shi can ba,

10 Domin yabo ta hikima kaɗai za a faɗe shi,

      Masanin hikima ne kaɗai zai koyar da ita.

Mutum na da Yanci

11 Kada ka ce, Ubangiji ne ya sa na yi saɓo,

      Domin ba ya sa abin da yake ƙi.

12 Kada ka ce, Shi ne ya sa na rantse,

      Domin ba ya son mai saɓo.

13 Ubangiji na ƙin dukan abin ƙyama,

      Yana kāre masu tsoronsa daga irin wannan abu.

14 Shi ne ya halitta mutum da farko,

      Saan nan ya ƙyale shi ga shawarar kansa.

15 In ka so, za ka iya kiyaye dokokin,

      Ka amince da Allah in ka bi nufinsa.

16 An ajiye wuta da ruwa a gabanka,

      Sa hannunka ga wanda kake so.

17 Mutum na da rai da mutuwa a gabansa,

      Wanda ya fi so, shi za a ba shi.

18 Hikimar Ubangiji yawa gare ta,

      Shi mai ƙaƙƙarfan iko ne, yana ganin dukan abu.

19 Yana ganin duk abin da ya halitta,

      Ya san kowane aikin da mutum ke yi.

20 Bai umarci wani ya zama marar bin Allah ba,

      Bai kuma ba wani ƙarfi don yin saɓo ba.

16. Laana ga Masu Keta

1 Kada ka yi begen haifa taron yaran banza,

      Kada ka ji daɗin mugayen yaya.

2 Kome yawansu wurinka, kada ka yi murna da su,

      In ba tsoron Ubangiji gare su.

3 Kada ka tabbata rayuwarsu,

      Kada ka dogara kan daɗewarsu.

Gara ɗaya da dubu,

      Ko ka mutu ba yaya da ka haifi marasa bin Allah.

4 Mutum ɗaya mai hankali yana iya yaɗa birni,

      Amma kabilar kangararru na iya hallaka birnin.

5 Da idanuna na ga abubuwa da yawa kamar haka,

      Da kunnuwan naji abubuwa masu ƙara banmamaki.

6 Za a yaƙi ƙungiyar masu laifi,

      Fushi na ƙuna a kan alumma marar biyayya.

7 Allah bai yafe wa ƙattin dā ba,

      Waɗanda suka yi tawaye da ƙarfinsu.

8 Bai keɓe maƙwabtan Lutu ba,

      Waɗanda ya fi ƙyamarsu saboda alfarmarsu.

9 Bai ji tausayin hallakakkiyar alummar Kananiyawa ba,

      Waɗanda aka watsar saboda laifinsu,

10 Ko sojojin ƙafa dubu dari shida,

      Waɗanda suka halaka saboda alfarmar zuciyarsu.

11 In da a ce mai taurinkai ko ɗaya kawai ne,

      Da abin mamaki ne in ya kuɓuta ba horo,

Tun da ya ke Ubangiji yana da jinƙai da fushi,

      Yakan yafe, ya gafarta, amma yakan husata da mugaye.

12 Jinƙansa girma gare shi, amma tsautawarsa ma haka take da girma,

      Yana sharaanta kowa bisa ga ayyukansa.

13 Mai laifi ba zai kuɓuta da ganimarsa ba,

      Haka ma haƙurin mai ibada ba zai tafi banza ba.

14 Kowa ke aikata gaskiya, zai sami lada,

      Kowa zai karɓa gwargwadon ayyukansa.

Tabbatar Ramuwa

15 Kada ka ce, Na ɓoye wa Ubangiji.

      Wa ke tunawa da ni a can Sama?

Ba a sanina cikin dubbai,

      Menene ni cikin yawan ruhohi marasa ƙirguwa?

16 Duba, sarari da birbishin sama,

      Kasa da zurfin duniya sukan kadu a ziyararsa.

17 Tushen tsaunuka da harsashin duniya

      Sukan girgizu ƙwarai lokacin da ya dube su.

18 To, ba zai ankara da ni ba,

      Wa zai kula da hanyoyina?

19 In na yi laifi, ba idon da zai gan ni?

      In na ci amana a ɓoye, wa zai sani?

20 Wa zai gaya wa Allah ayyukan gaskiya da mutum ke yi?

      Wane lada zan samu a kan aikina na wajibi?

21 Hakanan mai ƙaramin hankali ke tunani,

      Sai marar azanci sangartacce ke tunani haka.

A kan Hikima ta Bayyana a Halitta

22 Saurara, ɗana, ka bi shawarata,

      Ka mai da hankali ga kalmomina.

23 Zan auna maka horo,

      In sanar da kai, ainihin ilimi.

24 Ubangiji ya daidaita taurari tun farko,

      Da ya yi su, ya ƙaddara aikinsu.

25 Ya umarta ayyukansu har abada,

      Kowane da hanyarsa dawwamammiya.

Kada su ji yunwa, balle gajiya,

      Kada kuma su fasa hidimarsa.

26 Ba wanda zai taɓa ture makwabcinsa,

      Ba za su taɓa ƙetare kalmar Allah ba.

27 Bayan haka Ubangiji ya duba duniya,

      Ya cika ta da abubuwa masu kyau,

28 Ya rufe ƙasa da kowace irin dabba,

      Gare ta kuma za su sāke komawa.

17.

1 Ubangiji ya halicci mutane daga ƙasa,

      Ya yi su a kamanninsa.

2 Ya ƙayyade kwanakinsu na daɗewa,

      Daganan sai su koma ƙasa.

3 Ya ba su iko irin nasa,

      Su yi sarauta bisa kome na duniya.

4 Ya cika duk rayayyen abu da tsoron mutane,

      Ya sa su su shugabanci dabbobi da tsuntsaye.

5 Ya siffata musu harshe, da idanu, da kunnuwa,

      Ya ba su zuciya kuma don yin tunani.

6 Ya cika su da ilimi da ganewa,

      Ya kuma bayyana musu nagarta da mugunta.

7 Ya sa haskensa a zukatansu,

      Domin ya nuna musu girman ayyukansa.

8 Domin su faɗi manyan ayyukansa,

      Su kuma yabi sunansa mai tsarki.

9 Ya miƙa musu ilimi,

      Ya ba su gddon sharia don su rayu.

10 Ya kafa madawwamiyar yarjejeniya da su,

      Ya kuma bayyana musu kaidodinsa.

11 Idanunsu sun ga girman ɗaukakarsa,

      Kunnuwansu kuma sun ji ɗaukakar muryarsa.

12 Ya ce musu, Ku yi hankali da yin kowane zalunci,

      Ya ba su umarnai game da maamala da juna.

Allah yana Hukunci

13 Ayyukan mutane kullum a gaban Allah suke,

      Ba za su iya ɓoye wa ganinsa ba.

14 Kan kowace kabila ya sa wani shugaba,

      Amma Israilawa, su mallakar Ubangiji ne.

15 Dukan ayyukansu kamar rana ne a gare shi,

      Kullum yana ganin halayensu.

16 Ayyukansu marasa gaskiya ba a ɓoye suke gare shi ba,

      Dukan laifofinsu na gaban Ubangiji.

17 Ubangiji yana lura da sadakar da mutum yake yi,

      Kamar yadda ake kula da mabuɗin maaji,

Yana lura da baiwar da mutum yake yi,

      Kamar yadda ake kula da ƙwayar ido.

18 Wata rana zai tashi, ya yi musu sakayya,

      Zai dora wa kowa abin da ya cancanta.

18. A kan Girman Allah

1 Wanda ke rayuwa har abada

      Shi ne alkalin kowane abu,

      Ubangiji kadai ne mai adalci.

2 Wanene Allah ya ba damar bayyana

      dukan abubuwan da ya taɓa yi?

3 Wa kuma zai iya binciken manyan ayyukansa?

      Wa zai iya gwada ikonsa mai girma?

4. Wa kuma zai iya ba da labarin jinƙansa?

      Ba mai iya rage abubuwan mamaki na Ubangiji,

Ko ya ƙara su,

      Ba ma mai iya sansance su.

5 In mutum ya gama sansance su, farawa ke nan ya yi,

      In ya tsaya kuma, bai gane kome ba.

A kan Karancin Mutum

6 Menene mutum, me ne amfaninsa kuma?

      Menene kirkinsa, menene muguntarsa?

7 Kwanakin mutum masu yawa ne

      In ya kai shekara ɗari.

8 Kamar ɗigon ruwa ne ga teku,

      Ko ɓarɓashin ƙasa ga duniya.

      Haka mayan shekarun mutum suke ga ranar dawwama.

9 Saboda haka Ubangiji na hakuri da su,

      Yana kwarara musu jinƙansa.

10 Ya sani lalle za su yi mugun ƙarshe,

      Saboda haka sai ya gafarta musu a yalwace.

11 Jinƙan mutum ga danuwansa ne,

      Amma jinƙan Ubangiji ga dukan yan adam ne.

12 Yakan tsawata musu, ya hore su, ya koya musu,

      Yakan dawo da su kamar maƙiyayi da garkensa.

13 Yana da jinƙai ga waɗanda suke yarda da horonsa,

      Da waɗanda ke gaggautawa ga kaidodinsa.

Yadda za a Bayar

14 Ɗana, kada ka ɓata kyawawan ayyukanka,

      Ta yin kyauta da kalmomin baƙin ciki.

15 Kamar yadda ruwa ke rage zafin rana,

      Haka ne magana mai kyau ke inganta kyauta.

16 Hakika, kyakkyawar magana ta fi kyauta,

      Duka biyu, ga mutum mai alheri ake samunsu.

17 Wawa ba ya yin alheri, sai ya yi baƙar magana tukuna,

      Haka ma kyautar marowaci take duhunta fuskar mai karɓa.

A kan Hankah da Rigakafi

18 Kafin ka yi magana, ka koya,

      Kafin ciwo ya iso, ka yi rigakafi.

19 Kafin a sharaanta ka, ka yi abin yabo da ya cancanta,

      A lokacin yin sharia za ka sami mai agaje ka.

20 Ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, don kada ka yi laifi,

      Arnma in ka kai fagen laifi, ka tuba nan da nan.

21 Kada ka jinkirta barin laifofi,

      Kada ka dakata, sai wahala ta same ka.

22 Kada wani abu. ya hana ka biyan alkawarinka a kan kari,

      Kada ka dakata sai lokacin mutuwa, kafin ka cika shi.

23 Kafin yin alkawari, shirya kanka,

      Kada ka zama kamar wanda ke jarrabar Ubangiji.

24 Tuna da fushinsa a ranar mutuwa,

      Da ramuwarsa lokacin da zai kawar da fuska.

25 A lokacin yalwa, yi tunanin lokacin rashi,

      A cikin ranakun wadata, yi tunanin fatara da bukata.

26 Daga safe zuwa yamma yanayi yakan sake,

      Dukan abubuwa sukan tafi da sauri a gaban Ubangiji.

27 Mai hikima yana hankali a kowane abu,

      Lokacin da kowa ke yin laifi yakan kawar da kansa daga mugun abu.

28 Ya kamata kowane mai hankali ya sanar da hikima,

      Wanda kuma ya same ta ya yabe ta.

29 Masanan maganganun hikima, sai su nuna hikimarsu,

      Su yi ta kwararo ta ta karin magana,

      Kamar ruwa mai ba da rai.

A kan Kamunkai

30 Kada ka bi begen burin zuciyarka,

      Amma ka iya kwaɗayinka.

31 In ka ba rankaffin daɗin begen burin zuciya,

      Zai mai da kai abin dariya ga maƙiyanka.

32 Kada ka cika yawan annashuwa,

      In ba haka ba za ta mai da kai tsagwaron matalauci.

33 Kada ka zama mai zari ko mashayi,

      Don kada ka zama marar wuri.

19.

1 Wanda va vi haka ba zai yi arziki ba,

      Marar kula da ƙananan abubuwa,

      Sannu sannu zai tsiyace.

2 Abin sha da mata sukan ɓad da hankali,

      Wanda ya saba da karuwai zai yi ƙurun yin mugun abu.

3 Ruɓa da tsutsotsi za su gaje shi,

      Mai ƙuru a ɗan lokaci kaɗan za a fizge ransa.

4 Wanda ke amince musu da gaggawa ba shi da zurfin tunani,

      Wanda kuma ya biye musu, ya saɓa wa kansa.

Aibun Maganar Banza

5 Mai farin ciki da ƙeta, ƙeta ce za ta same shi,

      Wanda kuma ke maimaita muguwar jita jita,

      Ba shi da azanci.

6 Kada ka maimaita labarin da ka ji a hira,

      Ba za a laanta ka ba.

7 Kada ka gaya wa maƙiyi asirinka, har aboki ma,

      Kada ka tona laifinka ba gaira ba dalili,

8 Don duk wanda ya ji, ba zai amince da kai ba,

      Bayan ɗan lokaci zai ƙi ka.

9 Ka taɓa jin wata maganar asiri?

      Kada ka faɗe ta har mutuwa,

Riƙe ta da mazakuta!

      Ba za ta fasa ka don ta fita ba,

10 In wawa ya ji maganar asiri, zai sha azaba,

      Kamar mace mai naƙuda yake.

11 Yadda mutum ke so ya tsige kibiya daga cinyarsa, in an harɓe shi,

      Haka ma wawa ke son yada jita jita.

Kada a Yarda da kowane Labari

12 Gargaɗi aboki, kila bai yi laifi ba,

      Amma in ya yi, kada ya ƙara yi zuwa gaba.

13 Gargaɗi maƙwabci, kila bai ce kome ba,

      Amma in ya ce, kada ya ƙara cewa.

14 Gargaɗi aboki, don sau tari kushe ne,

      To, kada ka gaskata da dukan abin da ka ji.

15 Kila mutum ya zāme ba da nufinsa ba,

      Wanene bai taɓa yin laifi da harshensa ba?

16 Ka binciki maƙwabcinka kafin ka rabu da shi,

      Ta haka za ka cika shariar Maɗaukaki.

A kan Hikimar Gaskiya da ta Karya

17 Dukan hikima tsoron Ubangiji ce,

      Hikima tana sa a cika sharia kullum.

18 Amma ilimin mugunta ba hikima ba ne,

      Ba basira inda shawarar masu laifi take.

19 Akwai wani wayo wanda ake ƙyama,

      Akwai ma wani dolon da ba shi da laifi.

20 Marar ganewa mai jin tsoron Allah

      Ya fi mai basira wanda ke keta sharia.

21 Akwai wayo wanda yake cikakke,

      Amma ba tare da gaskiya ba,

      Yana murguɗe alheri don a ci nasara a sharia.

22 Akwai mugun mutum wanda ke sunkuyawa don makoki,

      Amma a ciki cike yake da kissa.

23 Ya ɓoye fuskarsa, ya yi bakan,

      Amma in ka kawar da fuska, zai ƙware ka.

24 In ko rashin ƙarfi ya hana shi yi maka laifi,

      To, in ya yi saa zai yi maka ƙeta.

25 Ana sanin mutum ta bayyanarsa,

      Ana sanin mai haziƙanci ta ganin fuskarsa.

16 Tufafin mutum, da dariyarsa, da tafiyarsa,

      Suna nuna halinsa.

20. A kan Magana da yin Shiru

1 Akwai tsawatarwa marar kyan kari,

      Akwai mai hikima kuma wanda ke kame bakinsa.

2 Tsawatarwa ta fi yin fushi,

      Wanda ya hurta laifinsa kuma, ba zai ji kunya ba.

3 Kamar yadda dandaƙaƙke yake ga mata,

      Haka ma mutum yake wanda aka tilasa wa yin aikin gaskiya.

4 Wani ta yin shirunsa a kan same shi mai hikima,

      Amma wani, yawan surutunsa yakan sa a ƙi jininsa.

5 Wani yakan yi shiru don ba shi da amsa,

      Amma wani yakan yi shiru

      Domin ya san amfanin yin magana a kan kari.

6 Mai hikima yakan yi shiru sai lokacin da ya kamata,

      Amma wawa mai fariya yakan zartar a kowane lokaci.

7 Duk mai yawan surutu za a ƙyamace shi,

      Mai tarar aradu da facrin kai ma, za a ƙi shi.

Misalai Masu Nuna Bambanci

8 Akwai shan wuya wadda ke sa albarka,

      Akwai kuma samu wanda ke sa rashi.

9 Akwai yin kyautar da gara babu ita,

      Amma akwai yin wata kyauta da ke kawo maka riɓin alheri.

10 A kan ƙaskanta saboda yawan neman ɗaukaka,

      Amma akwai mutanen da ke ɗaga kansu daga ƙasƙanci.

11 Akwai wanda ke sayen arha ba ta ado,

      Amma ta cinye kuɗin har sau bakwai.

12 Ana ƙaunar mai hikima ta wurin kalmominsa,

      Amma ba mai kula da ladabin wawa.

13 Kyautar wawa ba ta ƙara maka kome,

      Domin zai dame ka, sai ka biya shi har riɓi bakwai.

14 Yakan bayar kadan, ya yi kuka mai yawa,

      Yakan buɗe wagaggen baki kamar maroƙi.

Yakan ba da bashi yau, ya tambaye shi gobe,

      Mutum irin wannan abin ƙi ne.

15 Wawa ba shi da abokai,

      Ba mai godiya a kan kyawawan ayyukansa.

16 Waɗanda suka ci abincinsa ma,

      Suna yi masa zunɗe,

      Suna yi masa baa mai yawa.

A kan Maganar Banza

17 Gwamma a fāɗi ƙasa da a yi suɓul da baka,

      Haka ma sakamakon masu mugunta zai auku nan da nan.

18 Kamar abinci marar daɗi,

      Haka labarin da ba a faɗa a kan kari ba yake,

      Wanda jahili ke faɗa kullum.

19 Ana ƙin karin magana daga bakin wawa,

      Domin bai faɗa a kan kari ba.

20 Rashin wadata yana hana mutum yin saɓo,

      Amma a cikin wannan hali ba shi da kwanciyar rai.

21 Wani na rasa rayuwa ta wurin jin muguwar kunya,

      Yana halaka don wawa ya yi masa kurari.

22 Wani na yi wa aboki alkawari saboda kunya,

      Ta haka ya mai da shi maƙiyi ba gaira ba dalili.

A kan Ƙarya

23 Ƙarya na aibata mutum ƙwarai,

      A bakin jahilai take kullum.

24 Gara ɓarawo da maƙaryaci,

      Amma dukansu biyu za su kunyata.

25 An raina halin makaryaci,

      Kunyarsa kuma tana dawwame gunsa.

Akwai Girma da Hatsari ga Mai Hikima

26 Wanda ke magana da hikima zai ci gaba da samun matsayi mai kyau,

      Manya ma suna jin daɗin mai basira.

27 Duk wanda ya yi noma sosai zai cika rumbuna da amfani,

      Duk wanda manya ke jin daɗinsa kuma,

      Zai kuɓuce wa horon laifi.

28 Kyauta da toshi suna makanta idanu,

      Kamar takunkumi a baka suna kwaɓe tsawatarwa.

29 Hikima da dukiya ɓoyayyu, ina amfaninsu?

      30 Gara a ɓoye wauta da a ɓoye hikima.

21. A kan Laifi Iri Iri

1 Ɗana, ka yi laifi? Kada ka ƙara yi,

      Amma yi addua a kan laifofinka na dā.

2 Ka ji tsoron laifi daidai da maciji,

      Domin in ka matse shi, zai sare ka.

Gama haƙoran laifi kamar na zaki suke,

      Suna hallaka ruhohin mutane.

3 Dukan laifi kamar saran takobi ne,

      ƙauninsa ba ya warkewa.

4 Dukiyar mai alfarma da jan faɗa ba  za su ɗore ba,

      Haka ne ake lalata gidan mai alfarma.

5 Adduar gajiyayye, da ta fita daga bakinsa,

      Za ta shiga kunnen Allah kai tsaye,

      Sai rahamar Allah ta zo da sauri.

6 Duk wanda ba ya so a gyara kuskurensa, masu laifi yake bi,

      Amma mai tsoron Ubangiji zai tuba da zuciyarsa.

7 Mai surutun banza, an san shi tun daga nesa,

      Amma mai hankali, in ya bauɗe,

      Shi da kansa ya sani.

8 Wanda ke gina gida da kuɗin waɗansu

      Kabari yake gina wa kansa.

9 Ƙungiyar masu ƙeta kamar tsofaffin buhuna take,

      Waɗanda ƙarshensu, sai a ƙone,

10 Hanyar masu laifi daɓaɓɓiya ce,

      Amma za ta kai su mahallaka.

A kan Mai Hikima da Wawa

11 Duk wanda ke bin sharia ya mallaki zuciyarsa,

      Ckakken tsoron Ubangiji shi ne hikima.

12 Ba a iya koya wa marar wayo kome,

      Amma wani wayo yana kawo ɓacin rai.

13 Ilimin mai hikima zai ƙaru kamar ambaliyar ruwa,

      Shawararsa tana malala kamar idon ruwa.

14 Tunanin wawa kamar hudajjen tulu ne,

      Ba zai riƙe kome ba.

15 In mai ganewa ya ji maganar mai hikirna,

      Zai yabe ta, ya ƙara da tasa,

Lokacin da wawa ya ji,

      Zai ƙi, ya watsar da maganar.

16 Labarin wawa kamar kaya yake ga mai tafiya,

      Amma ana jin daɗin maganar mai azanci.

17 Za a nemi jawabin mai hankali a cikin taro,

      Za su kuma yi tunanin jawabinsa a zuciyarsu.

18 Kamar gidan da ya rushe, haka ne hikima take a gun wawa,

      A gun jahili kuma hikima kamar maganar aku take.

19 A gun marar hankali koyon ilimi

      Tankar dabaibayi ne a ƙafarsa,

      Kamar ankwa yake a hannunsa na dama.

20 Wawa yakan ɗaga murya in yana dariya,

      Amma mai azanci, sai ya yi murmushi kurum.

21 A gun mai azanci ilimi tankar adon zinariya ne,

      Kamar munduwa yake ma a hannun dama.

22 Wawa yakan shiga gida ba sallama,

      Amma mai azanci, sai an ce masa, Shigo.

23 Wawa zai je ƙofar daki, yana leƙe leƙe,

      Amma mai azanci, sai ya tsaya a waje,

24 Mugun hali ne in mutum na fakon maganar mutane a daka,

      Mai azanci zai guji yin haka saboda kunya.

25 Masu yaɗa jita jita, duk maganar da suka ji suke maimaitawa,

      Amma mai azanci yana auna kowace kalma.

26 Tunanin wawa a baka yake,

      Amma bakin mai hikima a zuciya yake.

27 In mai saɓon Allah ya Iaanci abokin gāba,

      Ya Iaanci kansa.

28 Maraɗi kansa yake ɓatawa,

      An ƙi jininsa ma a unguwarsu.

22. Kwatancin Rago

1 Za a kwatanta rago da dutsen da aka ƙazanta,

      Kowa na yi masa tsaki saboda rashin mutuncinsa.

2 Za a kwatanta rago da guntun kāshi busasshe,

      Kowa ya ɗauke shi, sai ya kakkaɓe hannu.

Yadda Lalatattun Yara Suke

3 Haihuwar da mara kwaɓa abin kunya ne,

      Haihuwarya marar kwaɓa hasara ce,

4 Ya mai hankali abar taƙama ce ga mijinta,

      Amma wadda ta yi abin kunya tana ɓata wa iyaye rai.

5 Shegiyar ya tana ba mijinta da mahaifinta kunya,

      Dukansu biyu kuma za su raina ta.

6 Kamar waƙa lokacin makoki,

      Haka tatsuniya take

      Wadda ba a faɗa a kan kari ba,

Amma in ya kamata, yin bulala da kwaɓa

      Hikima ne a kowane lokaci.

A kan Hikima da Wawanci

7 Wanda ke koya wa wawa,

      Daidai yake da mai dinke tukunya,

Ko wanda ke damun mai jin daɗin barci.

8 Wanda ke ba wawa bayani, yana ba mai jin gyangyaɗi,

      Gama a ƙarshe zai ce, Me ka ce?

9 Ana yin makokin matacce, don ya rasa haske,

      Ana kuma yin makokin wawa, don ya rasa azanci.

10 Kada a yi makokin matacce sosai, don ya kai ga hutu.

      Amma gara mutuwa da rayuwar wawa.

11 Makokin matacce kwana bakwai ne,

      Amma ana yi wa mugun wawa makoki dukan kwanakin ransa.

12 Kada ka yi yawan magana da wawa,

      Kada kuma ka ziyarci marar azanci.

13 Tsare kanka daga wurinsa, don ka  kuɓuta daga wahala,

      Saan nan ba za ka ƙazantu lokacin da ya yi girgiza ba.

Guje masa, za ka sami kwanciyar

      Ba zai dame ka da hauka ba kuma.

14 Me ya fi dalma nauyi?

      Menene sunanta kuma, ba Wauta ba?

15 Yashi, da gishiri, da guntun ƙarfe

      Wawa ya fi su wuyar riƙewa.

16 Miƙaƙƙen itacen da ake yaɓe cikin gini,

      Ba ya sakwarkwacewa don rawar ƙasa,

Haka ma wanda ya ƙwallafa rai gun shawarar kirki yake,

      Ba zai jijjigu ba ko a lokacin masifa.

17 Wanda ya ƙwallafa rai a kan  tunanin kirki,

      Daidai da bangon soro yake wanda aka yi wa ado iri iri.

18 Yashin da ke bisa tsauni, ba zai jure  wa iska ba,

      Haka zuciyar wawa matsoraci take, ba ta iya jure wa kurari.

A Kula da Abuta

19 Wanda ya tsone ido,

      Ido zai fito da ƙwalla,

Haka duk wanda ya tsone zuciya,

      Za ta nuna rashin jin daɗi In wani ya jefi tsuntsaye, za su tashi,

20 In wani ya zagi aboki kuma, ya ɓata abuta.

      Ko ka zare takobi a tsakaninka da  aboki,

21 Kada ka yi tsammani ba sauran  abutarku,

      Domin ana iya sāke ƙulla abutar.

22 In ka yi saɓani da abokinka,

      Kada ka damu, domin ana iya sulhuntawa.

Amma mugun zagi, da raini, da tona  asiri, ko cin amana,

      irin waɗannan abubuwa ne ke raba abuta.

23 Ka nemi amincewar maƙwabcinka tun yana talauci,

      Domin lokacin da ya yi albarka, kai ma za ka wadatu.

24 Hayaƙi shi ne mafarin wuta,

      Haka ma baƙar magana ita ce mafarin zubar da jini.

25 Ba zan ji kunyar kāre abokina ba,

      Ba zan ɓoye masa ba kuma.

26 Amma in wani hatsari ya same ni ta game da shi,

      in kowa ya ji, zai yi nesa da shi.

A yi Hankali da Yin Zunubi

27 Wa zai kwaɓi bakina,

      Ya kulle leɓunana a kan kari?

Domin in kuɓuta daga yin tuntuɓen magana,

      Kada harshena ya hallaka ni.

23.

1 Ya Ubangiji, Sarki mai mulkin raina,

      Kada ka bari in yi tuntuɓe da leɓunana.

2 Wa zai buge ni in na yi muguwar shawara?

      Wa zai hori zuciyata da hikima?

Yadda ba zai bar in ina kuskure ba,

      Ba zai watsar da ni kuma, ina yin  laifi ba,

3 Don kada a yawaita kurakuraina,

      Kada saɓona ya yi yawa,

Kada in fāɗi a gaban makiyana,

      Kada kuma magabcina ya yi kirarin nasara a kaina.

4 Ya Ubangiji, Ubana, Allah na raina,

      Kada ka ƙyale ni in yi saɓo da maganata.

5 Kada ka ba ni idanun alfarma,

      Ka raba ni kuma da mugun bege.

6 Kada ka bari jarabar neman mata ta mallake ni,

      Kada kuma ka sallame ni gun shaawar rashin kunya.

A kan yin Rantsuwa

7 Ku saurara, yayana,

      Ku ji gargaɗina game da yin magana,

      Duk kuwa wanda ya kiyaye shi ba zai bauɗe ba.

8 Ana kama mai laifi ta maganarsa,

      Ta nan ake kama mai ashar da mai girmankai

9 Kada ka saba wa bakinka da rantsuwa,

      Kada kuma kiran sunan Allah mai tsarki a banza ya zama jiki a gare ka.

10 Kamar yadda bawan da ake bincike kullum,

      Kullum kuwa ba zai rasa raunukan dūka ba,

Haka ma, kowa da ke rantsuwa kullum da sunan Allah,

      Kullum ba zai rasa laifi ba.

11 Duk mai yin rantsuwa a kai a kai yana ƙara wa kansa nauyi,

      Wahala kuma ba za ta rabu da gidansa ba.

In ya yi rantsuwa bai cika ba, za ta koma masa,

      In bai tabbata kuma da abin da ya yi wa rantsuwar ba,

      Ya yi laifi biyu ke nan.

In ya yi rantsuwar ƙarya, ba shi da makawa ga laifi,

      Gidansa ma zai cika da masifu.

A kan Ƙazamar Magana

12 Akwai irin maganar da mai faɗarta ya cancanci kisa,

      Dā ma kada a same ta a alummar Yakubu.

Duk wannan irin magana td yi nisa da mutanen Allah,

      Ba za su yi birgima a cikin laifofi ba.

13 Kada ka saba wa bakinka da maganar mashaa,

      Don lalle za ka ƙara yin wani laifi a cikinta.

14 Ka tuna da mahaifinka da mahaifiyarka,

      Lokacin da kake zaune a wurin manyan mutane,

Don kada ka mance ladabinka a gabansu,

      A yi tsammani kai wawa ne saboda halinka,

Saan nan ne za ka ce, Da ma ba a haife ni ba,

      Har kuma ka laanta ranar haihuwarka.

15 Wanda ya saba da yin baƙar magana

      Ba zai kwaɓu ba bar iyakar ransa.

A kan Zinar Namiji

16 Mutane iri biyu ke yaɗa laifi,

      Na ukunsu ke haɗa faɗa,

Garna rai mai yawan shaawa kamar wuta ne,

      Ba zai yi sanyi ba, sai ya ci ya cinye.

Na ɗayansu ne wanda ya saba da yin zinar zuci da jikinsa,

      Da ya fara tunani, ba ya bari sai ya cika.

17 Na biyunsu ne fasiki, a gunsa dukan gauta ja ne,

      Ba zai daina ba, sai in ya mutu.

18 Na ukunsu ne wanda yake yar da alkawarin aurensa,

      Yana ce wa kansa, Wa ke ganina?

Duhu ya rufe ni, bangon ɗaki kuma ya ɓoye ni,

      Ba ma wanda ke ganina, don me zan ji tsoro?

Bai kula da Maɗaukaki ba,

      19 Idanun mutane kawai yake tsoro.

Bai sani ba zatin Ubangiji

      Ya fi hasken rana sau dubun dubbai,

Yana ganin dukan abin da yan adam ke yi,

      Har ma ya san dukan lungu-lungu.

20 Kafin ya halicci abubuwan duniya ya  san su duka,

      Yana ma sane da dukansu bayan sun shuɗe.

21 Za a hori mai zina a ƙofar fada,

      Domin inda bai yi tsammani ba, a nan ne aka kama shi.

A kan Zinar Mace

22 Haka ma za a hori macen

      Da ta samo wa mijinta magaji ba da hannunsa ba.

23 Da fari dai, ta keta dokar Madaukaki,

      Na biyu, ta saɓa wa maigidanta,

Na uku kuma, ta yi zina ta karuwanci,

      Inda bar ta haifa wa wani yaya.

24 Ita ma za a kawo ta ƙofar fada,

      Haryayanta ma za a ba wani su,

      Inda za su yi agolanci.

25 Ba za ta sami tushen yaya ba,

      Rassanta ba za su yi amfani ba.

26 Bayan ta mutu za a riƙa laanta ta,

      Rainin da aka yi mata ba zai ɓace ba.

27 Ta haka dukan mazaunan duniya za  su sani,

      Kowa na kowace kasa zai gane cewa,

Ba abin da ya fi tsoron Ubangiji,

      Ba abin ma da ya fi kiyaye dokokin Allah daɗ.

24. Jawabin Hikima

1 Hikima tana yabon kanta,

      A tsakiyar jamaarta take taƙama.

2 A taron mutanen Maɗaukaki take buɗe baki,

      A gaban Mafifici ne take yin taƙama

3 Sai ta ce, Daga bakin Maɗaukaki na zo,

      Na rufe duniya kamar hazo.

4 Na zauna a maɗaukakan wurare,

      Kursiyina a ginshiƙin gajimare yake.

5 Na kewaya sararin sama, ni kaƙai,

      Na ma yi tafiya cikin zurfin duniya.

6 A kan rakuman ruwa, bisa dukan duniya,

      A kowace kabila da alumma, ina da iko.

7 A tsakanin dukan waɗannan na yi ta neman wurin hutu,

      Ina neman wanda zan zauna a wajensa.

8 Sai Mahaliccin dukan abu ya ba ni umarni,

      Wanda ya halicce ni ya ƙayyade mazaunina.

Ya ce mini, Ki zauna cikin yayan Yakubu,

      Ki karɓi Israila, ƙasarki.

9 Ni ya fara halitta tun fil azal,

      Zan kasance kuma har abada.

10 A masujadarsa tsattsarka na yi masa ibada,

      Ta haka ne na gawurta a Sihiyona.

11 Ya ba ni ƙaunataccen birni, in huta a ciki,

      Wato Urushalima, mulkina ce,

12 Ta haka ne na samo asali wurin alumma mai daraja,

      Waɗanda Ubangiji ya zaɓa su zama nasa.

13 Na yi girma kamar itacen alul a bisa dutsen Lebanon,

      Kamar yadda itacen kasharina yake a tsaunukan Harmon.

14 Na yi girma kamar itacen dabino da ke gundumar Engedi,

      Kamar itacen wardi kuma a birnin Yariko,

Ko kamar kyakkyawan itacen zaitun a gona,

      Na yi tsawo daidai da ɗorowar gefen ruwa, girma.

15 Ina ƙanshi kamar kayan ƙunshi da kirfa,

      Ko kamar zaɓaɓɓen ƙaron dāshi,

Kamar dai ganji da ƙaron maje da ɗaɗɗoya,

      Ko kamar hayaƙin ƙaron lubban cikin Wuri Mai Tsarki.

16 Kamar itacen tsamiya na buɓe rassana,

      ƙassana masu girma ne masu kyau.

17 Kamar itacen inabi na yi fure mai kyau,

      Furena ya zama yaya masu girma, masu daɗi,

18 Ku zo gare ni, ku da ke begena,

      Ku cika cikinku da amfanina.

19 Don tunawa da ni ya fi zuma daɗi,

      Samuna kuma ya fi saƙar zuma, duk da zakinta.

20 Waɗanda suka ci a wunna za su nemi ƙari,

      Waɗanda suka sha a wurina ma za su ƙara jin ƙishi.

21 Duk wanda ya yi mini biyayya ba zai kunyata ba,

      Waɗanda suka yi aiki da taimakona ma ba za su yi laifi ba.

A kan Shariar Allah da Hikima

22 Dukan waɗannan alherai suna ƙunshe a littafin yarjejeniyar Allah Maɗaukaki,

      Sharia ce wadda Musa ya umarce mu da ita,

      Gādo ne na ƙungiyoyin jamaar Yakubu.

23 Sharian nan tana cika mutane da hikima,

      Kamar yawan ruwan kogin Fishon,

      Kamar na Taigiris ma da damuna.

24 Tana ba su cikakkiyar ganewa

      Kamar yawan ruwan kogin Yufiretis,

      Kamar na Urdun ma da kaka.

25 Tana sa ilimi da imani su malala kamar kogin Nilu,

      Kamar kogin Gihon ma a lokacin ɗibar yayan itacen inabi.

26 Wanda ya fara neman hikima bai sakankance ta ba,

      Duk wanda ya bi shi ma ba zai san gabanta ba.

27 Don tunaninta ya fi teku faɗi,

      Shawararta ta fi zurfafan duniya

28 A farko ina kama da wata yar hanyar ruwa daga wurin hikima,

      Na tafi kamar maguɗanar ruwa zuwa lambu.

29 Na ce, Zan shayar da lambuna,

      In antaya wa yar gonata ruwa.

Amma ga shi, hanyar ruwana ta zama kogi,

      Kogi kuma ya zama teku.

30 Haka ne nake sa koyarwata ta haskaka daidai da wayewar gari,

      Har ta haskaka zuwa nesa.

31 Ina kwararo koyarwa daidai da annabci,

      Ina ma barinta kuma ga yan baya.

25. Misalai

1 Abubuwa uku ne ke sanyaya mini rai,

      Suna da kyau kuma a gaban Allah da mutane,

Na ɗayansu ne sulhu tsakanin yanuwa,

      Na biyunsu ne abuta tsakanin makwabta,

Na ukunsu ne jituwa tsakanin mata da miji.

2 Raina na gāba da mutane iri uku,

      Ba na son irin halayen zamansu,

Na ɗayansu ne matalaucin da ke nuna girmankai,

      Na biyunsu ne mawadaci, maƙaryaci,

Na ukunsu ne mazinacin tsoho, marar kangado.

A kan Tsofaffi

3 In ba ka tanaji kome a ƙuruciyarka ba,

      Yaya za ka sami wani abu lokacin tsufanka?

4 Abin madalla ne in an sami azanci wurin masu hurhura,

      Haka ma in tsofaffi suna da shawarar kirki.

5 Abin madalla ne in an sami hikima wurin tsofaffi,

      Haka ma in manyan gari na da ganewa da shawarar kirki.

6 Sanin kangadon duniya rawanin girma ne ga tsofaffi,

      Babbar taƙamarsu a tsoron Ubangiji take.

7 Ina iya tunawa da mutane iri tara masu albarka,

      Zan faɗi na gomansu ma.

Na farko, mai farin ciki da yayansa,

      Na biyu, wanda ya ga hallakar maƙiyansa,

8 Na uku, wanda ke da mata mai azanci,

      Na huɗu, wanda aurensa bai yi kama da haɗa sa da jaki huɗa ba,

Na biyar, wanda harshensa bai sa ya cika baki ba,

      Na shida, wanda ba shi da mai lura da aikinsa wanda ya kasa shi sani,

9 Na bakwai, wanda ya sami aboki mai kangado,

      Na takwas, wanda ake son sauraronsa in yana magana,

10 Na tara, wanda ya sami hikima, lalle yana da girma,

      Amma ba wanda ya fi na gomansu girma,

      Wato mai tsoron Ubangiji.

11 Tsoron Ubangiji ya fi kowane abu,

      Wanda ya riƙe shi kankan ya fi gaban kwatanci.

A kan Mata

12 Akwai rauni iri iri,

      Amma ba wanda ya kai rauni na zuciya,

Akwai ƙeta iri iri,

      Amma ba wadda ta kai ƙetar da mace ke yi.

13 Akwai hari iri iri,

      Amma ba harin da ya kai harin da magabci ke yi,

Akwai ramuwa iri iri,

      Amma ba wadda ta kai ramuwar da magabci ke yi.

14 Ba dafin da ya fi dafin maciji,

      Ba ma fushin da ya fi fushin mace.

15 Gara in zauna da zaki ko ƙaton maciji

      Da in zama da mace mai mugun hali.

16 Halin muguwar mace yakan sa kamanninta ya sake,

      Sai ta ɓata fuskarta kamar ta damisa.

17 In mijinta ya je cin abinci gun makwabta,

      Ba ya iya daina yawan ajiyar zuciya.

18 Kowane shairranci bai kai shaidancin mace ba,

      Da ma irin ramuwar masu laifi ta kama ta!

19 Kamar hawa cikin turɓaya a gun tsoho,

      Haka ma mace mai yawan surutu take a gun miji marar fitina.

20 Kada yawan kyan mace ya ɗauke maka hankali,

      Kada ma ka yi marmarinta.

21 Akwai fushi da shegantaka da babban abin kunya,

      In sai miji ya roƙi mace kuɗi.

22 Baƙanta tunani, da duhunta fuska, da raunana zuciya,

      Muguwar mace ke kawo wa miji.

Langaɓaɓɓen hannu da rashin kwarin gwiwa,

      Mace marar faranta wa miji ce ke kawo su.

23 A gun mace ne saɓo ya samo tushensa,

      Saboda ita ne ma dukanmu muke mutuwa.

24 Kada ka yi wa ruwa hanyar fita,

      Kada ma ka har muguwar mace ta yi abin da ta ga dama.

25 In ba ta yi abin da ka ce ba,

      Sake ta mana, ka huta.

26.

1 Albarka tana gun wanda yake da macen kirki,

      Za a ƙara masa yawan kwanaki a duniya.

2 Mace mai halin kirki takan faranta wa mijinta zuciya,

      Zai cika shekarunsa da salama.

3 Macen kirki babbar albarka ce,

      Za a ba mai tsoron Ubangiji ita.

4 Ko da wadata ko talauci, zuciyarsa fari fat take,

      A koyaushe kuma fuskarsa wasai take.

5 Abubuwa uku ne zuciyata take tsoro,

      Na huɗu yana firgita ni.

Na fari, mutanen gari su ci mini fuska,

      Na biyu, a yi mini sharia a gaban dumbun jamaa,

Na uku, tuhumar karya,

      Mutuwa ba ta kai mugun aibunsu ba.

6 Na hudunsu abin baƙin ciki ne,

      In mace na hamayya da wata,

      Tartsinta na damun kowa.

7 Muguwar mace igiya ce mai cin gadon bayan sā,

      Wanda ya aure ta ya rike ƙunama.

8 In mace mashayiya ta bugu, tana cushe wa miji rai,

      Don ba ta nuna kunyarta.

9 Karuwancin mace na fita ta muguwar shaawar da ke idanunta,

      Sara gira ke sa a san ta.

10 A kula da mace marar kangado,

      Don in ta sami damar yin mugunta, za ta yi.

11 Ka yi hankali in ka gan ta tana sara gira,

      In ba haka ba, kada ka yi mamaki in wani ya ɗauke ta ba da izninka ba.

12 Kamar yadda mai dawowa daga farauta ke buɗe baki,

      Don ya sha duk ruwan da ya samu kusa da shi,

Haka yarinyar take da ke yin naam da sandan kowa da ya zo wurinta,

      Tana buɗe wa kibiyar kowa kwarinta.

13 Daɗin maganar mace na faranta wa mijinta rai,

      Fasaharta kuma na ƙara masa ƙwarin gwiwa.

14 Mace mai kintsi kyautar Allah ce,

      Ba kuma abin da ya kai horarren halinta daraja.

15 Mace mai kunya albarka ce fiye da wata albarka ga mijinta,

      Ba maaunin da zai iya auna darajar mace mai daurin kai.

16 Kamar yadda rana take ɗagowa da safe,

      Haka ma kyan macen kirki yake wurin kintsa gida.

17 Kamar yadda hasken fitila yake kan maɗorinta mai tsarki,

      Haka ma kyan fuska yake bisa kintsattsen jiki.

18 Kamar ginshiƙin zinariya a kan tushen azurfa,

      Haka ma kyawawan ƙafafu suke a kan kintsattsen tafin ƙafa.

19 Zuciyata na baƙin cikin abu biyu,

      Na uku kuma yana ba ni haushi.

Na fari, mai wadata da ya shiga rashi,

      Na biyu, mai azanci da ake gwada wa raini,

Na uku mai adalci da ke koma wa yin saɓo,

      Ubangiji zai shirya shi don kisa!

A kan Kasuwanci

20 Da kyar attajiri zai daina yin cuta,

      Dan kasuwa ma ba zai kuɓuta daga yin saɓo ba.

27.

1 Attaffirai da yawa sun aikata saɓo don cin riba,

      Duk wanda ke neman arziki ido rufe, sai ya yi cuta.

2 Kamar yadda ake kafa maratayi tsakanin duwatsun bangon ɗaki,

      Haka ma saɓo ke shiga a tsakanin saye da sayarwa.

3 In mutum ba shi da kishin zuci da tsoron Ubangiji,

      Za a hamɓarar da gidansa da sauri.

Yi Hankali da Magana

4 In ana tankaɗe gari da rariya,

      Tsaki da kono kaɗai ne za a gani a cikinta,

      Haka ma ƙazantar mutum take bayyana ta wurin yin magana.

5 A matoya ake sanin aikin mai tukwane na ƙwarai,

      Haka ma ake sanin mutum na ƙwarai,

      Wato ta yadda yake yin magana.

6 Yayan itace su ne ke nuna fasahar mai lambu,

      Haka ma maganar mutum ke nuna tunanin zuciyarsa.

7 Kada ka yabi mutum kafin ka ji maganarsa,

      Don ta nan ne ake gane halin mutane.

A kan Kirki

8 In ka nemi adalci, za ka same shi,

      Har ka sa shi a jiki daidai da riga mai darajar gaske.

9 Kowane tsuntsu yana tashi da irin kabilarsu,

      Haka ma gaskiya take bin masu aikata ta.

10 Zaki yana kwanto in yana neman naman da zai kama,

      Haka ma saɓo yake a gun macuta.

11 Maganar mai azanci, kullum tana da hikima,

      Amma wawa, sai ya riƙa sākewa kamar wata.

12 In kana cikin wawaye, sami yadda za ka yi ka sulluɓe musu,

      Amma a cikin masu azanci, ƙara share wurin zama.

13 Maganar wawaye abin ƙyama ce,

      Dariyarsu ma tana da gangancin rashin kunya.

14 Masu magana da yawan rantsuwa suna ta da tsigar jikin wani,

      Jayayyarsu ma tana sa mutum ya doɗe kunne.

15 Jayayyar masu girmankai tana kawo zubar da jini,

      Zage‑zagensu, banhaushi gare su.

Kiyaye Asirai

16 Duk wanda ya tona asiri ya ci amana,

      Ba ya ma ƙara, samun aminin da ya dace da shi.

17 Ka ƙaunaci abokinka, ka amince da shi kuma,

      Amma in ka tona masa asiri, gara ka ƙyale shi.

18 Gama kamar yadda mutum ke hallaka magabcinsa,

      Haka ne ka hallaka abutarka da maƙwabcinka.

19 Sai ka ce ka har tsuntsu ya kuɓuce daga hannunka,

      Haka ne ka har maƙwabcinka ya kuɓuce,

      Ba za ka kara kama shi ba.

20 Kada ka sāke binsa, domin ya yi nisa,

      Gama ya kuɓuce kamar barewa daga tarko.

21 Gama a iya daure rauni, ana iya shiryawa ma bayan zage‑zage,

      Amma duk wanda ya tona asiri, ai, ba shi da wani abin yi.

Aibun Munafunci

22 Duk wanda ya sara gira yana nufin aikata mugun abu,

      Ba kuma wanda zai hana shi yin mugunta.

23 Daɗin baki gare shi a gabanka,

      Yana naam ma da maganarka,

Amma daga baya zai sauya maganarsa,

      Ya ɓata abin da ka ce.

24 Na ƙi jinin abu da dama,

      Amma ba wanda ya kai kamarsa,

      Ubangiji ma zai ƙi jininsa.

25 Duk wanda ya jefa dutse sama, kansa zai dawo,

      Haka ma hainci zai raunata ku, kai da abokinka.

26 Kamar yadda duk wanda ya gina ramin mugunta zai faɗa ciki,

      Wanda kuma ya sa tarko, tarkon ne zai kama shi,

27 Haka ne ma duk mai yin ƙeta, ƙeta za ta komar masa,

      Ba kuma zai san inda ta fito ba.

28 Baa da zagi su ne ladan mai girmankai,

      Amma ramuwa tana jiransa kamar zaki.

29 Waɗanda ke jin daɗin faduwar mutane, a tarko za a kama su.

      Azaba ce ma za ta cinye su kafin su mutu.

Kada a yi Ramuwa

30 Fushi da ramuwa, waɗannan abin ƙyama ne,

      Mai saɓo ne ma ke riƙonsu.

28.

1 Wanda ya yi ramuwa zai sha ramuwa daga wurin Ubangiji,

      Ubangiji zai tuna da dukan laifofinsa.

2 Yafe wa maƙwabcinka in ya yi maka laifi,

      Kai ma za ka sami gafarar laifofinka, in ka yi roƙo.

3 Mutum yana riƙon wani a zuci,

      Saan nan shi ya nemi taimako a gun Ubangiji?

4 In ba shi da tausayi ga ɗanuwansa mutum,

      Zai kuma yi addua saboda nasa laifofi?

5 In shi, da yake ɗan adam, yana riƙon fushi,

      Wa zai gafarta nasa laifofi?

6 Tuna da karshen ranka, ka daina yin ƙiyayya,

      Ka tuna da halaka da mutuwa, ka daina yin saɓo.

7 Tuna da dokoki, kada ka yi fushi da maƙwabcinka,

      Ka tuna da yarjejeniyar Maɗaukaki,

      Ka yafe laifofin da aka yi maka.

Kada a Yi Jayayya

8 Ƙi yin jayayya, za ka rage yin laifi,

      Don mai saurin husata ne ke haddasa jayayya,

9 Yana raba abokai,

      Har ya sa rashin jituwa tsakanin waɗansu da ke zaman salama.

10 Wuta tana kamawa gwargwadon itacen da aka sa mata,

      Haka ma jayayya take, gwargwadon abin da ya sa ta,

Gwargwadon ƙarfin mutum, gwargwadon fushinsa,

      Haka ma gwargwadon wadatar mutum, gwargwadon haukansa.

11 Kwalta da kananzir suke sa wuta, ta haɓaka

      Jayayya mai tsanani ita ke kawo zubar da jini.

12 In ka hura wutar gawayi, za ta kama

      In ka tofa mata yau, za ta mutu,

      Abu biyu ɗin duka daga bakinka suka fito.

Yi Hankali da Harshenka

13 A Iaanci mai raɗa da mai ruɗi,

      Domin sun kawo hamayya gun mutane da yawa da ke zaman salama.

14 Taɗin waiwai yakan girgiza mutane da yawa,

      Yakan warwatsa su. daga alumma zuwa alumma.

Yakan hallaka manyan birane,

      Yakan kife gidan manyan mutane.

15 Shiga hanci da kudundune ya kori mata masu ƙarfin zuciya,

      Ya hana su cin amfanin aikinsu.

16 Duk wanda yake kulawa da taɗin waiwai

      Ba zai sami kwanciyar rai ba,

      Ba ma zai yi zaman salama ba.

17 Bugun bulala yana sa farfashewar fata,

      Amma bugun da harshe ke yi yana karya ƙasusuwa.

18 An kashe mutane da yawa da kaifin takobi,

      Amma ba su kai yawan waɗanda kaifin harshe ya kashe ba.

19 Mai albarka ne wanda aka keɓe daga kaifin harshe,

      Wanda ma ba a kai gun zafin fushin harshen ba,

Wanda bai sha wuyar karkiyar harshen ba,

      Bai ma sha wuyar gigar nasa ba.

20 Domin karkiyar harshe karkiya ce ta ƙarfe,

      Gigar nasa ma gigar ne na tagulla,

21 Ƙetar da harshe ke sawa kamar muguwar mutuwa ce,

      Sai dai mutuwar gaske ba ta kai ta azaba ba.

22 Amma harshen nan ba zai shugabanci masu tsoron Allah ba,

      Ba ma za a ƙona su ta wutarsa ba.

23 Marasa. tsoron Allah, su za su faɗa cikin wutarsa,

      Zai ƙona su, ba zai mutu ba.

Za a aiko musu da shi kamar zaki,

      Zai haɗiye su kamar damisa.

24 Kamar yadda kake yi wa lambunka shinge na ƙaya,

      Haka ma ka kulle bakinka da murfi da sakata.

25 Kamar yadda kake kulle zinariyarka da azurfarka,

      Haka ma ka daidaita kalmominka, ka auna su.

26 Kula, kada ka yi kuskure da harshenka,

      Kada ya zamana ka fāɗa a gaban wanda yake bagonka.

29. A kan Rance

1 Wanda yake da jinƙai ne zai ba maƙwabci rance,

      Wanda ma ya ƙarfafa wa maƙwabci gwiwa,

      Ya kiyaye dokokin Sharia.

2 Ka ranta wa maƙwabcinka lokacin da yake da bukata,

      Kai ma, in wani ya ranta maka, ka biya shi a kan kari.

3 Ka cika alkawarinka, ka riƙe amanarka ta biyan mai ba ka rance,

      Ta kowane hali za ka sami abin da kake bukata.

4 Sau tari wanda ya nemi rance

      Yana ƙara wa waɗanda suka taimake shi nauyi.

5 Mai neman bashi da rarrafe yake zuwa,

      Yana tausasa murya, sai ya sami kuɗin.

Amma ranar biya zai yi rarrashi,

      Zai ce, Ai, kasuwa ta ba mu kashi, dawo gobe.

6 In wanda ya ba da rancen ya matsa masa lamba ma,

      Da ƙyar zai sami rabi,

      In ya sami rabin, zai ce, Kai, na yi hamdala!

In bai matsa ba, wanda ya yi rancen ya yi masa fashin kudin ke nan,

      A nan mai ba da rance ya sami abokin gāba ba gaira ba dalili.

Wanda aka ba rance ya biya da laana da zagi,

      Maimakon ya girmama mai ba shi, sai ya saka da raini.

7 Ba bahilanci ne ya sa mutane da yawa hana rance ba,

      Amma suna jin tsoron haincin ba gaira ba dalili.

Nuna Karamci

8 Ko ta yaya, ka yi haƙuri da wani cikin ƙasƙanci,

      Kada ka dakatar da shi don za ka ba shi sadaka.

9 Ka taimaki matalauci saboda umarnin Allah,

      In yana da bukata, kada ka sallame shi hannu wofi.

10 Kashe kuɗinka saboda danuwa ko aboki,

      Kada ka gina rami, ko ka sa inda za su yi tsatsa.

11 Yi amfani da dukiya bisa ga umarnan Maɗaukaki,

      Saan nan za ta ba ka riba fiye da zinariya.

12 Ka riƙa yin sadaka, Allah zai tuna da ita,

      Za ta fanshe ka daga dukan masifa.

13 Za ta taya ka fada da abokin gābanka,

      Fiye da babbar garkuwa da mashi mai nauyi.

Yin Lamuni

14 Mai kirki zai lamunci maƙwabcinsa,

      Don maƙwabcin ya sami biyan bukatarsa,

      Sai marar kunya zai ci amanar mai ba shi.

15 Kada ka mance da alherin mai lamuninka,

      Domin ya danƙa wa wani ransa saboda kai.

16 Mai yin saɓo ya hallaka dukiyar mai lamuninsa,

      Marar godiya ma zai yar da wanda ya fanshe shi.

17 Yin lamuni ya lahanta mutane da yawa masu wadata,

      Ya girgiza su kamar iskar teku.

18 Ya sa tajirai sun bar gidajensu.

      Suna ta garauniya a ƙasashen duniya.

19 In wani ya ɗauki lamuni, ya ba wani kuma don ya ci riba,

      Za a kai shi sharia a kan ribarsa.

20 Ka taimaki maƙwabeinka bisa ga iyawarka,

      Amma yi hankali, kai ma kada ka faɗi ta yin haka.

Kada a Cika Bin Gidaje

21 Lalle rai ba ya wanzuwa sai da ruwa, da abinci, da tufafi,

      Da ɗaki kuma maganin huntanci.

22 Gara ka zama matalauci a bukkarka

      Da ka ci abinci mai daɗi, kana baƙunci a gidan wani.

23 Ka haƙura da kaɗan ko mai yawa,

      Kada ka kula da wanda ya raina gidanka.

24 Bin gida abu ne mai wuya,

      Inda kake baƙo ba ka da wata magana.

25 In kai baƙo ne, in an ƙosa da kai,

      Duk hidimar da ka yi ba za a gode maka ba,

      Ba kuma abin da za ka ji sai ɓatanci

26 Cewa, Zo nan, bako, ka shirya tebur,

      in ma kana riƙe da wani abu a hannu,

      Za a ce, Ba ni shi in ci.

27 Za a ce kuma, Ba da wuri, baƙo mai daraja ya iso,

      Danuwana ya zo, zai zauna da ni, ina bukatar ɗakina.

28 Abu ne mai wuyar jurewa a gun mai hankali,

      Ya ji ba a marabce shi ba,

      Ko a sallame shi kamar wanda ake bi bashi.

30. Renon Yaya

1 Wanda ke ƙaunar dansa zai buga shi a kai a kai,

      Don wata rana ya yi farin ciki da nagarin dan.

2 Wanda ya hori dansa zai ci ribar ɗan,

      Zai yi taƙama da shi ga idon sani.

3 Wanda ya koya wa ɗansa sani,

      Zai sa abokan gāba kishi,

      Zai ɗaukaka a gaban abokai.

4 Ko uban ya mutu ma, sai ka ce bai mutu ba,

      Domin ya har wanda ya yi kama da shi a duniya.

5 Muddin ransa ya yi farin ciki da ganin ɗan,

      Lokacin da ya mutu ma, ba shi da nadama.

6 Ya har mai ramawa gun abokan gābansa,

      Da mai rama alheri ma gun abokansa.

7 Yana lalata ɗansa,

      Duk wanda ke ɗaure kowane ɗan raunin da ɗansa ya yi,

      Haka ma wanda ke damuwa da kowane kukan da ɗa ke yi.

8 Dokin da ba a hora ba, gardama gare shi,

      Ɗa marar kamunkai ma, taurinkai gare shi.

9 Gwada wa yaro daɗi, zai ma firgita ka,

      Ka yi wasa da shi, zai sa ka baƙin ciki.

10 Kada ka sakar masa fuska,

      Don kada ya sako maka baƙin ciki,

      A bisani za ka ciji yatsa.

11 Kada ka ba shi yancin yin kowane abu lokacin ƙuruciyarsa,

      Kada ma ka ƙyale kurakuransa.

12 Ka tanƙwasa wuyansa tun yana da ƙuruciya,

      Ka ɗanɗana masa tsabga ma tun yana ƙarami,

Don kada ya lalace, ya gagare ka,

      Daganan zai ɓata maka rai.

13 Hori ɗanka, ka sa shi aiki mai yawa,

      Don kada ya wahalar da kai wata rana ta yin rashin kunya.

A kan Lafiyar Jiki

14 Gara matalaucin da yake lafiya lau,

      Da mawadacin da ke yawan ciwo.

14 Ƙarfi da lafiyar jiki sun fi dukan zinariya,

      Kwanciyar rai ma ta fi arziki kome yawansa.

15 Ba dukiyar da ta fi lafiyar jiki,

      Ba ma murnar da ke gaban farin zuciya.

17 Mutuwa ta fi rai baƙin ciki,

      Dawwamammen hutu ma ya fi ciwon da ba ya warkewa.

18 Ba mai zazzafan ciwo abinci mai kyau,

      Kamar ajiye abinci ne a gun kabari.

19 Ina amfanin mika wa gumaka abinci?

      Domin ba su iya ci ko jin ƙanshi.

20 Haka ma wanda yake da cuta yake,

      Gama da ya ga wadata, sai ya yi nishi.

A kan Farin Ciki

21 Kada ka sa wa kanka baƙin ciki,

      Kada ma ka dami kanka da baƙin tunani.

22 Murna a zuciya ita ke sa mutum ya rayu,

      Farin ciki ne ke sa mutum kwanaki da yawa.

23 Daɗaɗa ranka, ka faranta wa zuciyarka,

      Ka yi wa baƙin ciki korar kare,

Domin baƙin ciki ya hallaka mutane da yawa,

      Ba shi ma da amfani.

24 Kishi da fushi suna rage tsawon rai,

      Damuwa ma tana kawo saurin tsufa.

25 In mutum ya ci abinci da farin zuciya,

      Abinci zai ƙara masa lafiya.

31. A kan Dukiya

1 Tashi tsaye a kan dukiya yana watsa karfin mutum,

      Damuwa a kanta ma tana hana barci.

2 Damuwa a kan bukatar rai tana hana hutawa,

      Ciwo mai tsanani ma yana hana barci.

3 Mutum mai arziki yana aiko don dukiyarsa ta ƙaru,

      In ya huta, don ya ji wa ransa daɗi ne.

4 Matalauci yana aiki don ya biya bukatar ransa,

      In ya huta, sai bukata ta kama shi.

5 Mai ƙaunar zinariya ba ya zama marar aibu,

      Wanda ya bi ta kuɗi ma, zai ratse hanya.

6 Zinariya ta ribaci mutane da yawa,

      Ko da ya ke sun yi arba da halaka.

7 Ta sa waɗanda suka makale mata su yi tuntuɓe,

      Ta kama kowane dolo.

8 Albarka ta tabbata a gun mai dukiya,

      Wanda ba a samu da laifi ba,

9 Wanda ma bai cika neman kuɗi ba.

      In mun same shi, za mu ce da shi mai albarka,

      Domin ya yi abubuwan mamaki a tsakiyar mutanensa.

10 Ina wanda aka gwada da zinariya,

      Har aka same shi cikakke?

      Yana da abin taƙama.

Ina wanda ke da ikon aikata saɓo, bai aikata ba,

      Ko yin mugunta, amma bai yi ta ba?

11 Wadatarsa za ta kahu da gindinta,

      Jamaa za su yi ta yabonsa.

A kan Ladabi a Biki

12 In kana cin abinci a gun babban mutum,

      Kada ka nuna zari,

      Kada ma ka ce, Ai, akwai shi da yawa sosai!

13 Ka tuna, idanu masu zari mugun abu ne.

      Me aka halitta wanda ya fi ido zari?

      Yana zubar da ƙwalla a kan duk abin da yake nema.

14 Kada ka miƙa hannu a gun kowane abin da ka gani,

      Kada ma ka yi ruguguwa da danuwanka a gaban gārā.

15 Ka sani, abin da zai dame ka zai dami danuwanka,

      Ka ma yi tunani a kan duk abin da ba ka so.

16 Ka ci abincinka a hankali kamar babban baƙo,

      Kada ka yi hannu baka hannu kwarya, za a ƙi jininka.

17 Ka fara tashi daga kan abinci, don ka nuna kwaɓa,

      Kada ka dinga zubawa, don kada ka ɓata wa mutane rai.

18 In kana zaune cikin jamaa

      Kada ka riga su miƙa hannu.

19 Abu kaɗan yawan gaske gare shi a gun horarren mutum,

      Ba ya ma murde‑murde in ya kwanta.

20 Wahalar rashin barci, da kumallo, da ciwon ciki, suna wurin mai zari.

      Mai matsakancin cin abinci yana jin daɗin barci,

      Yana sammakon tashi da ƙarfi.

21 In an matsa maka kā cika cikinka da abinci

      Tashi, je ka ka yi amai, cikinka zai sassauta.

22 Saurare ni, ɗana, kada kuwa ka raina ni,

      A ƙarshe za ka ji dadin maganata.

Cikin dukan aikinka ka yi matsakanci,

      Za ka kuɓuta daga cuce‑cuce masu yawa.

23 Mutane za su yabi wanda ke ba da abinci hannu sake,

      Shaidar ma da za su yi wa fifikonsa, ai, za ta daɗe.

24 Duk gari zai yiwo caa ga mai rowar abinci,

      Shaidarsu. kuwa a kan rowarsa za ta daɗe.

Shan Giya

25 Kada ka cika taƙamar shan giya,

      Gama giya ta lalata mutane da yawa.

26 Yadda wutar maƙera ke nuna halin ƙarfe,

      Haka ma giya ke gwada zuciyar masu girmankai.

27 Giya kamar rai take gun mutane,

      Amma in sun yi mata matsakancin sha,

Ina daɗin rai ba giya?

      An halitta abin sha don ya faranta wa mutane rai.

28 Shan giya a kan karl

      Yana sa rai ya yi murna, ya faranta zuciya.

29 Shan giya da jayayya

      Suna kawo ciwon kai, da tsokana, da shan kunya.

30 Yawan sha tarko na gun wawa.

      Yana ma rage masa ƙarfi ya ƙara masa raunuka.

31 Kada ka tsauta wa maƙwabcinka a mashayar giya,

      Kada ma ka raina shi in yana walawa.

Kada ka zage shi,

      Kada ma dai ka wahalar da shi gaban sauran mutane.

32. Yin Ladabi a Biki

1 In an sa ka uban biki, kada ka ɗaga kanka,

      Ka tsaya a cikinsu daidai da kowa,

      Ka kula da su tukuna, saan nan ka zauna.

2 in ka gama hidimarka,

      Sami wurin zama domin ka taya su jin daɗi,

      Za ka karɓi rawaninka saboda kamunkai da ka nuna.

3 Ka yi magana, kai wanda ke babba, domin ya kamata ka yi,

      Amma ka faɗi hikimarka a taƙaice,

      Kada ka yi wa yan wasa karambani.

4 Inda ake shan giya kada ka yi jawabi,

      Kada ka nuna gwanintarka ba a kan kari ba.

5 Kamar yadda tsakiya take a zoben zinariya,

      Haka kiɗi yake a mashayan giya.

6 Kamar yadda dutsen zubarjadu yake a cikin tsabar zinariya,

      Haka karin waƙa yake a mashayan giya.

7 Ka yi magana, saurayi, in an bukace ka da yi,

      Amma sai an tambaye ka a ƙalla sau biyu.

8 Ka yi magana da taƙaici,

      Ka faɗi abu da yawa da kalmomi kaɗan,

      Ka yi kamar masani mai kame bakinsa.

9 A cikin manya kada ka ɗauki kanka daidai da su,

      Kada ka yi wa masu sarauta naciya.

10 Kamar walƙiya wadda take riga tsawa zuwa,

      Haka ma mutum mai kasƙantar da kai ke haskakawa a idanun mutane.

11 Ka bi kyakkyawan lokaci, kada ka zama na baya a gidan biki,

      Tafi gida da sauri, ka huta a can.

12 A can ne za ka yi abin da ke a zuciyarka,

      Amma banda saɓo ta maganar girmankai,

13 Amma fiye da kome ka yabi wanda ya halicce ka,

      Ya wadata ka da kyauta masu kyau.

Tsoron Allah

14 Mai tsoron Ubangiji zai yarda da horonsa,

      Masu sammakon nemansa ma, za su sami abin da suke roƙa.

15 Wanda yake koyon sharia zai san ta sosai,

      Amma munafuki zai yi tuntuɓe da ita.

16 Mai tsoron Ubangiji zai gane abin da yake daidai,

      Kome tsakar dare ma zai fitar da shawara mai kyau.

17 Mutum mai laifi zai guji horo,

      Zai murcre sharia ga abin da yake so.

18 Mutum mai hankali zai karɓi shawarar hikima,

      Amma mai tsiwa da mai girmankai ba su da razanar kome.

19 Kada ka aikata kome in ba da shawara ba,

      Don daga baya kada ka ce, Da na sani.

20 Kada ka bi hanyar da ta cika hatsari,

      Kada ka yi tuntuɓe a wurin da ka yi na farko.

21 Kada ka cika gabagaɗi a hanya mai sumul sumul,

      22 Ka yi hankali a kan dukan hanyoyinka.

23 Kula da kanka da dukan aikinka,

      Domin wannan shi ne kiyaye dokokin sharia.

24 Wanda ya gaskata sharia yana kula da kansa,

      Haka ma wanda ya amince da Ubangiji ba zai ji kunya ba.

33.

1 Ba mugun abin da zai fāɗa wa mai tsoron Ubangiji,

      Amma a cikin gwaji zai kuɓuta, ya ƙara kuɓuta.

2 Mai ƙin jinin sharia ba shi da hikima,

      Kamar jirgin ruwa yake a hatsarin raƙuman ruwa.

3 Mai ganewa zai amince wa maganar Ubangiji,

      A gare shi sharia abar dogara ce,

      Kamar ainihin muryar Ubangiji,

4 Ka shirya abin da za ka faɗa, za a saurare ka,

      Ka shiga gandun iliminka, saan nan ka fid da raayinka.

5 Zuciyar wawa daidai da ƙafar keke take,

      Tunaninsa ma sai juyawa yake yi.

6 Aboki mai kushe daidai da doki mai samarya yake,

      Wanda ke haniniya a gun duk wanda ya bau shi.

Bambancin Matsayi

7 Me ya sa wata rana ta fi wata,

      Tun da ya ke hasken shekara duka daga gun rana ne?

8 Shawarar Ubangiji ce take bambanta su,

      Shi ya sa lokaci da idi dabam dabam.

9 Ya ɗaukaka waɗansu ranaku da tsarki,

      Waɗansunsu kuwa ya yi su a ranaku kawai.

10 An yi dukan mutane daga ƙasa,

      Adamu ma daga turɓaya aka halitta shi.

11 Da cikakken sani Ubangiji ya bambanta yan adam,

      Ya ba kowa hanyoyinsa dabam.

12 Ya sa wa waɗansu albarka, ya ɗaukaka su,

      Wadansu kuwa ya tsarkake su, ya kawo kusa da shi,

Amma waɗansunsu ya laanta, ya ƙaskanta,

      Har ya ma sallame su daga matsayinsu na dā.

13 Yadda yumɓu yake a hannun mai yin tukwane,

      Wanda yake siffata su kamar yadda yake so,

Haka ma mutane suke a hannun wanda ya halicce su,

      Yana ba kowa bisa ga abin da ya kaddara.

14 Alheri shi ne kishiyar mugunta,

      Rai ma shi ne kishiyar mutuwa,

      Haka mai zunubi shi ne kishiyar mai tsoron Allah.

15 Duba dukan ayyukan Maɗaukaki,

      Su ma dai kashi kashi ne, wani kishiyar wani.

16 Bayan kowa ya yi barci, ni kuwa ina fadake domin koyon hikima,

      Na yi kama da ɗan kala bayan an kwashe amfani.

17 Albarkar Ubangiji ta fifita ni,

      Na cika kwandona daidai da mai kwasar amfanin.

18 Ku tuna, ban yi aiki don kaina kaɗai ba,

      Amma har don dukan masu neman hikima.

Mulkin Kai

19 Ku saurare ni, ku da kuke manya a jamaa,

      Ku ma shugabannin taro, ku ji,

20 Kada ka yarda da ko mata, ɗanuwa ko aboki

      Su mallake ka muddin ranka.

21 Muddin kana da rai

      Kada ka ba kowa matsayinka.

Kada ma ka danka wa wani wadatarka,

      Kila ka sauye tunaninka yadda dole ne ka tambaye shi.

22 Domin gara yayanka su nema wurinka,

      Da ka zura musu ido su ba ka.

23 Ka mallaki dukan aikinka,

      Kada ka yarda wani ya ɓata maka daraja.

24 Ka bari sai ka tsufa tukuf tukuna,

      Saan nan ka rarrabar da gādo.

A kan Bayi

25 Ga jaki sai ingirici, da bugu, da kaya,

      Da takunkumi, da taiki, da tsabgar mai shi.

26 Ga baran gida, sai abinci, da horo, da aiki,

      Ga mugun bara ma, sai ɗauri da azaba,

27 In ka sa bawanka aiki, zai nemi hutu,

      In ka ƙyale shi, zai nemi yanci.

28 Ka sa shi aiki, kada ya yi zaman banza,

      Gama zaman banza ne ke koya wa mutum mugun abu mai yawa.

29 Ka sa shi aiki, gama aiki ne ya kamace shi,

      In kuwa bai yi ba, ka ɗaure shi bajau.

30 Duk da haka kada. ka zalunci kowa,

      Kada ma ka yi kome da. rashin gaskiya.

31 In kana da baran gida daya, ku sha daularka tare,

      Domin da jiɓinka ka sayo shi.

32 In kana da baran gida daya, mai da shi kamar ƙanenka,

      Gama daidai da ranka yake, za ka bukace shi.

33 In ka gasa masa azaba, har ya ranta ciki na kare,

      Ina ne za ka gane shi?

34. A kan Mafarkai

1 Wawa ne yake begen abin da ba ya samuwa,

      Yana bin duk abin da ya gani a cikin mafarki.

2 Kamar wanda yake ridar inuwa ko bin iska,

      Haka ma wanda ke kulawa da mafarkai yake.

3 Wahayin mafarki siffa ce kawai,

      Ba ainihin gaskiyar abu ba,

      Kama da wane, ba wane ba ce.

4 Me za a samu mai tsabta daga ƙazamin abu?

      Ina ma gaskiyar da za a samu daga maƙaryaci?

5 Zuwan matsafa dūba, da yarda da camfi, da biye wa mafarkai, dukansu wauta ce,

      Abin da ka sa a zuci, shi kake gani.

6 In ba Maɗaukaki ne ya nuna maka wahayi ba,

      Kada ka yarda da shi.

7 Domin mafarkai sun ruɗi mutane da yawa,

      Waɗanda ma suka sa zuciya gare su ba za su sami kome ba.

8 Amma ba wani ruɗu za a cika sharia,

      Masu aminci ne za su sami hikima cikakkiya.

A kan Tafiya

9 Mutum mai ilimi ya san abubuwa da yawa,

      Wanda ya sha duniya ma, zai yi magana da ganewa.

10 Na daka bai yi kallon na waje ba,

      Amma tafiya mabuɗin ilimi ce.

11 Na ga abubuwa da yawa a tafiye-tafiyena,

      Na ma gane abin da ba ya bayyanuwa duka.

12 Sau da yawa ina cikin hatsarin mutuwa,

      Amma na kuɓuta saboda sanin abubuwan nan da na yi.

13 Ruhun waɗanda ke jin tsoron Ubangiji zai rayu,

      Gama suna sa zuciya ga wanda zai cece su.

14 Mai tsoron Ubangiji ba zai razana ba,

      Ba ya ma zama matsoraci, gama ya dogara ga Ubangiji.

15 Albarka ta tabbata ga ruhun mai tsoron Ubangiji!

      Da wa ya dogara? Wanene mai taimakonsa?

16 Ubangiji na ganin waɗanda ke ƙaunarsa,

      Shi ne babban mataimakinsu, madogararsu,

Mai kiyaye su kuma cikin hadiri,

      Mai ba su inuwa daga zafin rana,

Mai hana su tuntuɓe,

      Yana ma tsare su daga hatsari.

17 Yana faranta ran mutane, yana haskaka fuska,

      Yana ba da lafiya, da rai, da albarka.

Yin Hadayu

18 In wani ya yi hadaya da abin da ya samu ta magudi,

      Hadayarsa ba ta inganta ba,

      Allah ba ya karɓar kyautan marasa bin sharia.

19 Maɗaukaki ba ya jin daɗin hadayun masu saɓonsa,

      Saboda ɗumbun hadayu ba ya yafe zunubai.

20 Kamar wanda ya kashe ɗa a gaban mahaifinsa,

      Haka ma wanda ya miƙa hadaya da kayan matalauci yake.

21 Tuwon sadaka shi ne rayuwar matalauci

      Duk wanda ya hana shi kuwa yana kisankai.

22 Duk wanda ya ɗauke wa maƙwabci kayan rayuwa ya kashe shi,

      Wanda ya hana maaikaci albashinsa ma, ya zubar da jininsa.

23 In wani ya gina, wani ya rushe,

      Ribar me suka ci? Sai aikin da suka sha.

24 In wani ya yi addua, wani ya laanta,

      Muryar wa Ubangiji zai saurara?

25 Idan mutum ya yi wanka bayan ya taɓa gawa,

      Ya sāke taɓa ta,

      Ina amfanin wankan da ya yi?

26 To, in mutum ya yi azumi saboda zunubansa,

      In ya koma ya sāke yin zunuban,

Wa zai saurari adduarsa?

      Ina ma amfanin tubansa?

35.

1 Wanda ya kiyaye sharia ya yi hadayu masu yawa,

      Wanda ya kula da dokoki ma, ya miƙa hadayun godiya.

2 Wanda ya saka alheri, hadayar garin alkama mai kyau ya miƙa,

      Wanda ma ya ba da sadaka, hadayun yabo ne ya miƙa.

3 Yin nesa da mugunta yana sanyaya wa Ubangiji rai,

      Gama barin yin rashin gaskiya yana shafe sauran laifofi.

4 Kada ka tafi gaban Ubangiji hannu wofi,

      Gama an yi umarnin yin dukan waɗannan abubuwa.

5 Miƙawar mai gaskiya tana nashe bagade,

      Turaren ƙanshinta ma, har gun Maɗaukaki yake zuwa.

6 Hadayar mai gaskiya abin karɓa ce,

      Ba ma za a daina tunawa da ita ba.

7 Ka ɗaukaka Ubangiji da karamci,

      Kada ma ka hana tumun fari na amfanin gonarka.

8 Ka yi dukan baiwarka da fuska mai haske,

      Ka fitar da zakarka da murna.

9 Ka ba Maɗaukaki kamar yadda ya ba ka,

      Ka bayar hannu sake bisa ga iyawarka.

10 Gama Ubangiji shi ne mai sakawa,

      Zai saka maka har riɓi bakwai.

Adalcin Allah

11 Kada ka miƙa wa Ubangiji cin hanci,

      Gama ba zai amsa ba,

      Ba ya ma yarda da hadayar ganima.

12 Gama Ubangiji mai shariar gaskiya ne,

      Shi ba ya nuna son zuciya.

13 Ko da ya ke ba ya nuna son zuciya kan matalauci,

      Yana sauraron adduar wanda aka yi wa laifi.

14 Ba zai ƙyale roƙon marayu ba,

      Gwauruwa ma ba zai ƙyale ta ba, in ta faɗi damuwarta.

15 Kukan gwauruwa da ƙwallan da take zubarwa

      Ba laanta wanda ya cuce ta suke yi ba?

16 Wanda ya yi hidimar Ubangiji da zuciya ɗaya zai sami karɓuwa,

      Ubangiji zai ji roƙonsa.

17 Adduar mai ƙaskantar da kai keta sararin sama take yi,

      Ba za ta tsaya ba, sai ta kai ga Ubangiji.

18 Ba ma za ta koma ba sai Maɗaukaki ya saurare ta,

      Ya zartar da sharia da gaskiya.

19 Ubangiji ba zai yi jinkiri ba,

      Kamar jarumi yake, ba zai yi haƙuri ba.

20 Sai ya ragargaje marasa jinƙai,

      Ya yi sakayya a kan masu girmankai,

21 Ya kawar da taro na masu tsiwa,

      Ya hanhamɓare ƙarfin mugaye,

22 Ya yi wa mutum sakayya gwargwadon aikinsa,

      Ya biya yan adam ma, gwargwadon dabarunsu,

23 Ya sharaanta lamirin mutanensa,

      Ya sa su ji daɗin jinƙansa.

24 Ana neman jinƙansa a lokacin wahala

      Kamar gizagizan ruwa lokacin fari.

36. Addua domin Ceton Jamaar Allah

1 Ka cece mu, ya Ubangiji, Allah na dukan halitta,

      Ka dube mu da rahama,

      Ka sa sauran alumma su ii tsoronka.

2 Ka nuna wa maƙwabtan alummai ƙarfi,

      Domin su ga ikonka zahiri.

3 Yadda ka hore mu domin ka nuna musu tsarkinka,

      Ka hore su, su ma, domin ka nuna mana ɗaukakarka.

4 Ka sa su san ka, yadda muka san ka,

      Su sani, ba wani Allah sai dai kai.

5 Ka koma wa aikinka na alajabi, ka yi sababbin alamu,

      Tashi, ka gwada dantsenka.

6 Ka ta da fushinka, ka kwararo azabarka,

      Ka hallaka maƙiyi, ka wartaki magabci.

7-9 Ka zo da hanzari, ka aikata nufinka da sauri,

      Ka ragargaje kawunan sarakunan abokan gāba.

Magabcin da ya gudu daga fagen fama

      Ka sa wuta ta lashe shi,

      Ka sa masu laanta mutanenka su halaka.

10 Ka tara dukan kabilan Yakubu,

      Don su gaji ƙasarsu, kamar yadda yake a dā.

11 Ka yi jinƙai, ya Ubangiji,

      a kan alummar da ake kira da sunanka,

      a kan Israila wanda ka kira ɗan farinka.

12 Ka ji tausayin tsattsarkan birninka,

      Urushalima, mazaunin zatinka.

13 Ka cika Sihiyona da darajarka mai girma,

      Ɗakin ibadarka kuma da ɗaukakarka.

14 Ka gwada mana irin aikinka na dā,

      Ka aikata annabcin da aka yi da sunanka.

15 Ka saka wa masu begenka,

      Ka sa maganar da annabawanka suka yi ta wanzu.

16 Ka saurara, ya Ubangiji, ga adduar da bayinka suke yi,

      Saboda jinƙanka ga jamaarka.

17 Ta haka ne dukan mutanen duniya za su sani

      Kai Allah ne madawwami.

Sanin Halayen Mutane

18 Kome aka ba ciki, zai yi naam da shi,

      Duk da haka wani abinci ya fi wani daɗi, in ji baƙi.

19 Kamar yadda harshe ke sakankance naman farauta,

      Haka ma mai azanci ke gane maganar giri.

20 Mai ɗaura gira zai kawo wahala,

      Amma mai ganewa zai yi masa

      Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya.

21 Wata mace za ta yarda da kowane namiji,

      Amma namiji zai fi son wata ya fiye da wata.

22 Kyan mace yana sa fuskar mijinta haske,

      Gama ya fi duk abin da ake gani faranta rai.

23 In kuma tana da magana mai daɗi,

      Mijinta ya fi sauran yan adam saa.

24 Wanda ya auri budurwa ya sami tushen arziki,

      Gama ya sami mataimaƙiya mai dacewa, abin takama gare shi.

25 Lambun da ba shi da shinge zai zama ganima,

      Mutum marar mata ma zai yi ta bin gari yana zaman gilo.

26 Wa zai amince wa yan fashi

      Waɗanda ke zirga zirga daga wannan birni zuwa wancan?

Wa ma zai amince wa marar lakabi,

      Wanda ke kwana duk inda dare ya yi masa?

37. A kan Abokan Karya

1 Kowane aboki zai ce, Ai, ni abokinka ne,

      Amma waɗansu abokai, abokai ne ta suna kawai.

2 Ba abin baƙin ciki ba ne ƙwarai,

      In amini ya zama abokin gāba ba?

3 Kash! abokina, don me ka wanzu?

      Don ka cika duniya da ruɗu?

4 Abokin ƙarya yana taya ka farin ciki,

      Amma da wahala ta same ka, sai ya ja da baya.

5 Abokin gaske zai taya ka yaƙi da abokan gāba,

      Zai tare maƙiyanka.

6 Kada ka watsar da abokinka a yaƙi,

      Kada ma ka mance da shi lokacin da ka sami ganima.

Yi Hankali da Masu Ba ka Shawara

7 Kowane mai ba da nasiha zai nuna hanya,

      Amma waɗansunsu nasihar kansu kawai suke yi.

8 Ka bi mai ba da shawara a hankali,

      Ka san manufarsa tukuna,

Domin kila ya yi maka shawara ta son zuciyarsa,

      Don me za ka bi shawarar da za ta yi masa amfani, ba kai ba?

9 Kila zai ce maka, Ai, abin da za ka yi mai kyau ne,

      Amma in abin ya jawo maka wahala, ido kawai zai zuba.

10 Wanda bai yarda da kai ba, kada ka nemi nasiharsa,

      Kada ka bayyana nufinka gun masu ƙyashinka.

11 Kada ka tambayi mace shawara game da kishiyarta,

      Ko matsoraci game da yaƙi,

Ko ɗan kasuwa game da araha,

      Ko mai saye game da darajar abu,

Ko mai haɗama game da yin karamci,

      Ko maƙetaci game da yin jinƙai,

Ko rago game da aikin yi,

      Ko ɗan ƙodago game da ƙarewar aiki,

Ko malalacin baran gida game da aiki mai yawa,

      Kada ka kula da shawarar ko ɗaya daga cikin irin waɗannan.

12 Amma kullum ka liƙe wa mai tsoron Allah,

      Wanda ka sani yana rike da dokoki,

Wanda raayinku ya zo ɗaya,

      Wanda zai yi baƙin ciki in ka bauɗe.

13 Ka ma shawarci zuciyarka,

      Gama ba wanda ya fi amincewa da kai kamarta.

14 Zuciyar mutum tana iya gaya masa irin shirin tsare kan da zai yi,

      Fiye da masu tsaro bakwai da ke tsaye a hasumiya.

15 Gaba da kome, ka roƙi Maɗaukaki,

      Domin ya bi da kai da hanyar gaskiya.

A kan Hikimar Gaskiya da ta Ƙarya

16 Dabara ita ce tushen kowane shaani,

      A yi shawara kafin a yi kowane aiki.

17 Zuciya ce tushen dukan shawara,

      Tana fitar da rassa iri huɗu,

18 Alheri da mugunta, rayuwa da mutuwa,

      Bakin mutum yake jawo wanda zai same shi daga cikin huɗun nan.

19 Akwai wani mai hikima wanda ke amfanar mutane da yawa,

      Amma ya gaza amfana wa kansa kome.

20 Akwai wani mai hikima ya yi magana,

      Amma mutane suka ƙi shi,

      Har ya rasa abin da zai ci.

21 Akwai wani mai hikima ta shaanin kansa,

      Hikimarsa ta amfane shi shi kaɗai.

22 Akwai wani mai hikima don shaanin mutanensa,

      Ai kuwa, ba za a daina jin daɗin amfanin hikimarsa ba.

23 Kwanakin ran mutum suna da iyaka,

      Amma kwanakin alummar Israila ba su da iyaka.

24 Mai hikima ta shaanin kansa yana morewa,

      Da an gan shi za a yabe shi.

25 Mai hikima don shaanin mutanensa,

      Rabo zai wuce dukan tsararsa,

      Sunansa ma zai dore har abada.

Yin Matsakancin Abu

26 Ɗana, tun kana lafiya kada ka cika yawan shaawa,

      Ka yi hankali kada ka ba ranka abin da zai yi maka lahani.

27 Gama abincin wani, dafin wani ne,

      Ba kowa ne ke jin daɗin kome ba.

28 Kada ka biye wa dukan abu mai daɗi,

      Game da kyan abinci, kada ka zama lahira‑baki‑cika.

29 Gama mugun ci yana kawo ciwo,

      Zari ma yana kawo ƙwannafi.

30 Zari ya kashe mutane da yawa,

      Amma duk wanda ya guje wa zari, zai ƙara tsawon rai.

38. A kan Magani da Ciwo

1 Ka girmama likita, domin kana bukatarsa,

      Gama Ubangiji ne ya tabbatar da aikinsa.

2 Ubangiji ne ya ba likita hikimarsa,

      Sarki ma yana ba shi albashi.

3 Gwanintar likita ce ke ɗaukaka shi,

      Ita ce ma ke ba shi damar yin maamala da manyan mutane,

4 Ubangiji ya sa ƙasa ta fitar da magunguna,

      Mai hankali ma ba zai raina su ba.

5 Ba Musa ne ya tsoma ɗan reshen itace a ruwa ba,

      Ya mai da shi zazzaƙa,

      Domin mutane su san ikon Allah?

6 Ubangiji ya ba mutane fasaha,

      Domin su ɗaukaka ayyukansa masu bamnamaki.

7 Likita ma yake yin amfani da magunguna,

      Don ya rage raɗaɗin jiki,

      Mai haɗa magani kuma yana ɗibar albarkar ƙasa iri iri a aikinsa.

8 Haka ne aikin Allah ke ci gaba kullum,

      Lafiyar jamaa tana dawwama a fuskar duniya.

9 Ɗana, in ba ka lafiya, kada ka yi jinkiri,

      Amma ka roƙi Allah, zai warkar da kai.

10 Guji mugunta, kada hannunka ya aikata rashin adalci,

      Ka tsabtace zuciyarka daga kowane saɓo.

11 Ka miƙa hadaya mai dadin ƙanshi tare da roƙonka,

      Da kyauta mai tsoka gwargwadon wadatarka.

12 Ka ba likita damar yin aikinsa,

      Don kada ya watsar da kai, gama kana bukatarsa.

13 Akwai lokatan da ba ka warkewa,

      Sai likita ya lura da kai,

14 Shi ma roƙon Allah yake yi

      Don ya gane asalin ciwonka,

      Aikinsa kuma ya kawo warkewarka.

15 Wanda ba ya girmama wa Mahalicci,

      Ba zai yarda da aikin likita ba faufau.

16 Ɗana, ka zubar da ƙwalla saboda matacce,

      Ka yi kuka da makoki mai zafi,

Abin da ya kamata ma, ka shirya gawar,

      Kada ka kawo hujar guje wa janaizarsa.

17 Yi kuka mai zafi, yi baƙin ciki matuƙa,

      Ka yi gaisuwarka ta taaziyya,

      Yadda ta kamaci mataccen.

18 Yi kwana ɗaya ko biyu kana makokin,

      Saan nan ka washe, ba wanda zai sa maka laifi.

19 Gama baƙin ciki yana zama lahani,

      Ɓacin rai ma yana hallaka lafiyar mutum.

20 Ka daina tunaninsa,

      Ka mance da shi, amma ka yi tunanin mutuwarka.

21 Kada ka tuna da shi, gama ba zai dawo ba,

      Tunawar ba za ta taimake shi ba,

      Sai ma kai za ta yi wa lahani.

22 Ka tuna, ƙaddarar da ta kawo tasa mutuwa, ita za ta kawo taka,

      Gama jiya tasa ta same shi, kai kuwa yau.

23 Da kawar da matacce, tunaninsa ya fita zuciyarka,

      Da ransa ya fita, ka mai da ƙarfin halinka.

A kan Fannin Aikin Hannu

24 Gwanancewar malami tana ƙara masa hikima,

      Duk wanda harkoki ba su tsone wa ido ba,

      Zai iya zama mai hikima.

25 Ta yaya bawan gona zai iya zama masani,

      Shi da ke farin cikin aiki da shanun huɗarsa kullum?

Ya je gona da hurtumai, ya dawo da su,

      Bai damu da kome ba, sai shanunsa.

26 Ya yini yana ta ɗawainiya da huɗa,

      Da yamma ya yi ban dusa da kwanan garke.

27 Haka ma da kowane gwanin zāne yake,

      Yana aiki dare da rana,

Yana shirya sassaƙaƙƙun hatimai,

      Burinsa ya yi su iri dabam dabam,

Nufinsa dai zanensa ya fita tangaran,

      Yana aikin zanensa, ba dare ba rana, sai ya gama.

28 Haka ma maƙeri yake aikinsa da uwar makera,

      Yana bi da ɗanyen ƙarfe.

Zafin wuta yana ƙona jikinsa,

      Duk da haka yana aiki cikin zafin wuta.

Ƙarar masaba tana doɗe masa kunne,

      Yana ƙura wa ma aikacin da yake yi ido.

Niyyarsa ya gama aikinsa,

      Yana lura sai ya yi shi daidai wa daida.

29 Haka ma maginin tukwane in ya zauna bakin aiki,

      Yana sa niyya ga aiki,

Gama aikin yin tukwane ya sa gaba,

      Yana kuwa yinsu da yawa.

30 Da hannu yake mulmula yumɓun,

      Ya tausasa shi da ƙafa,

Yana kula yadda zai ƙayata su da ado,

      Yana kuma lura da wutar toya tukwanen.

31 Dukan mutanen nan haziƙai ne wajen aikin hannuwansu,

      Kowane dayansu gwani ne a kan aikinsa.

32 In ba game da su ba, ba garin da zai zaunu,

      Duk inda suka zauna ma, ba za su ji yunwa ba.

33 Amma ba su iya zama alƙalai,

      Ba su ma da muhimmanci a taron jamaa,

Ba su yanke sharia ko shawara,

      Ba a ma samunsu a cikin sarakuna.

34 Duk da haka suna kula da aikin ci gaban duniya,

      Ba abin da suke so sai su aikata gwanintarsu.

39. A kan Amfanin Marubuta

1 Ai, zai bambanta da saura,

      Wanda ya kwallafa ransa domin ya koyi Shariar Maɗaukaki!

Yana gano hikimar mutanen dā,

      Yana ta nazarin littattafan annabawa.

2 Yana darajanta jawaban mashahurai,

      Har ma ya gane maanar karin maganganu masu zurfi.

3 Yana koyon misalai masu wuyar ganewa,

      Yana aikin neman ɓoyayyen nufi na labarun hikima.

4 Yana iya zuwa wurin manya,

      Yana da hanya ma a gun sarakuna.

5 Yana yawo a ƙasashen waje,

      Domin ya koyi abin da ke nagari da mugu game da mutane.

6 Abin kularsa ya nemi Ubangiji, Mahaliccinsa,

      Ya roƙi Maɗaukaki.

Yana ta yin addua

      Domin ya nemi gafarar laifinsa.

Saan nan, in Ubangiji Mai Iko Dukka ya yarda,

      Mai hikiman nan zai cika da ganewa,

Zai kwararo maganar hikima,

      Da addua kuma zai yi wa Ubangiji godiya.

7 Mai hikiman nan zai shirya iliminsa da shawararsa,

      Yana bibiya asiran Ubangiji.

8 Zai nuna kwaɓar da aka koya masa,

      Zai yi takama da shariar yarjejeniyar da Ubangiji ya yi da jamaarsa.

9 Mutane da yawa za su yabi ganewarsa,

      Sunansa ba ya shahuwa har abada.

Za a ma dinga tunawa da shi,

      Sunansa zai wanzu a cikin mutanen dukan zamanai.

10 Alummai za su riƙa maganar hikimarsa,

      A cikin taro ma za su riƙa kaɗa takensa.

11 In yana raye, an sa sunansa fiye da na dubbai,

      Ba za a daina faɗar sunansa ba ma lokacin da ya mutu.

Yabon Allah Mahalicci

12 Zan sake sa zancena

      Ya yi haske kamar wata a gamyarsa.

13 Ku saurara, ku yayana masu tsarki, ku buɗe kunnuwanku

      Kamar furen wardin da aka dasa a maguɗanar ruwa.

14 Ku yi turaren ƙonawa mai ƙanshi,

      Ku kawo fure mai ƙanshi kamar furen kadanya.

Ku yi amo mai daɗi na waƙarku ta yabo,

      Ku yabi Ubangiji saboda dukan abin da ya yi.

15 Ku bayyana girman sunan Ubangiji,

      Ku yi waƙar yabonsa da karfi.

Ku yi yabonsa da molo da sauran dukan kayan yabo masu tsarkiya,

      Ku yi waƙar farin ciki, ku faɗi haka.

16 Dukan aikin Allah mai kyau ne,

      Yana biyan kowace bukata a lokacinta.

17 Da umarninsa ne ruwaye suka tsaya cik, kamar a ƙcwarya,

      Da dai ya yi magana, sai suka tattaru a tekuna.

18 Da ya yi umarni sai nufinsa ya wanzu,

      Ba abin da ke iya hana shi cika aikinsa.

19 A gabansa dukan aikin yan adam yake,

      Ba abin da zai ɓoye masa.

20 Yana kallon abin da aka yi dā, na yau, da na gobe,

      A gare shi ba wani abin da ke ba zato ba tsammani.

21 Ba hujar cewa, Ina dalilin wannan abu?

      Gama Allah ya zaɓi kowane abu don ya biya bukata.

22 Albarkarsa tana malala kamar kogin Nilu,

      Kamar kogin Yufiretis tana arzuta fuskar ƙasa,

23 Amma wani lokaci fushinsa yana hallaka alumma,

      Yana mai da ƙasa mai taki ta zama fako.

24 Ga masu nagarta hanyar Ubangiji bai ɗaya take,

      Ga masu girmankai hanyar Ubangiji ta cika tudu da kwari.

25 Ya shirya wa masu nagarta tsabar abubuwan alheri tun fil azal,

      Amma masu girmankai ya gauraya musu alheri da mugunta.

26 A bukatar rai abubuwan farko su ne,

      Ruwa da wuta, ƙarfe da gishiri,

Alkama, da madara, da zuma,

      Ruwan inabi, da mai, da tufaft.

27 Ga masu nagarta waɗannan duk suna da kyau,

      Amma ga mugaye, ai, waɗannan mugayen abubuwa ne.

28 Akwai iskar hadiri da aka umarta ta yi horo,

      Wadda da fushinta tana iya jijige dutse.

In za ta yi taadi,

      Sai ta yi daniniya da ƙarfi har ta gama,

      Domin ta rarrashi husatar Mahaliccinta.

29 A cikin taskarsa kowane abu da lokacinsa.

      Wuta da ƙanƙara, yunwa da cuta,

30 Mayunwatan dabbobi, su kunama, da kububuwa,

      Da takobi, dukansu don a hallaka masu aika mugunta.

31 Waɗannan kayan ramuwa suna murna da aikata nufin Ubangiji,

      Duk abin da aka ce su yi, ba za su ƙetare shi ba.

32 Tuntuni na tabbata,

      Na gane, saan nan na rubuta,

33 Dukan aikin Allah mai kyau ne,

      Yana biyan kowace bukata a lokacinta.

34 Ba hujar cewa, Ai, wannan ba shi da kyau kamar wancan,

      Gama kowanne yana nuna cancantarsa a lokacinta.

35 To, yanzu, cike da farin ciki, sai ku yi yabo,

      Ku yabi sunan Maɗaukaki.

40. Wahalar Yan Adam

1 Allah ya danƙa wa yan adam

      Damuwa mai yawa da babban aikin wahala,

Tun ran gini ran zāne,

      Har ranar komawa turɓaya.

2 Tunanin dukansu, da tsoron zuciyarsu,

      Da damuwarsu har ran mutuwa,

3 Ko su sarakuna ne masu gidajen alfarma,

      Ko talakawa marasa wurin kwanan kirki,

4 Ko suna da tufatin ƙawā,

      Ko suna yafa tsumma,

5 Duk na fushi ne, da kishi, da wahala, da tsoro,

      Da razanar mutuwa, da harzuka, da jayayya.

Lokacin da suka kwanta domin su huta,

      Damuwarsu za ta hana su yin barci.

6 Gajeren hutunsu ya fi ba shi,

      Sai su fara mafarki,

Suna yin ɗawainiya yadda suka yi da rana,

      Suna firgita da abin da idonsu ya gani

      Kamar waɗanda ake fafara.

7 Da sun isa maɓoya, sai su farka,

      Suna mamaki don ba wani abin tsoro.

8 Haka yake ga dukan halitta, mutum da dabba,

      Amma masu saɓo, nasu sai an ƙara  har ninki bakwai.

9 Annoba, da zubar da jini, da fushi, da yaƙi,

      Da ƙwace, da hasara, da yunwa, da mutuwa,

10 A ainihin gaskiya waɗannan an yi su don mugaye,

      Mugaye ne ma, ke sa sauran mutane halaka.

11 Duk abin da ya fito daga ƙasa, ƙasa zai koma,

      Abin da ya fito daga sama ma, sama zai koma.

Gargadi Iri Iri

12 Duk abin da ya zo daga cin hanci da rashin adalci zai dai daidaice,

      Amma biyayya za ta wanzu har abada.

13 Dukiyar sharri kamar ruwan kwazari ne,

      Kamar babban rafi lokacin tsululun, damuna,

14 Ruwan da, a gudunsa, yake mirgina duwatsu,

      Amma ba zato ba tsammani sai ya ƙafe.

15 Dashen mugu ba zai tashi ba,

      Gama tushen masu saɓon Allah kan dutse yake, ba ƙasa.

16 Su ma kamar jan rauno suke,

      Wanda ke riga sauran hakukuwa bushewa.

17 Amma alheri ba ya dushewa,

      Gaskiya tana ɗorewa har abada.

Yar ajiya da albashi suke sa rai ya ji daɗi,

      Amma su biyu, tsintuwa mai tsoka ta fi su.

18 Haifa ɗa ko kafa birni zai sa sunan wani ya ɗore,

      Amma su biyu, samun hikima ya fi su.

19 Garken tumaki da lambuna suna kawo yaɗuwar dukiya,

      Amma su biyu, amintacciyar mata ta fi su.

20 Giya da kiɗi suna sa rai jin daɗi,

      Amma su biyu, aure mai dacewa ya fi su.

21 Sarēwa da garaya suna da amo mai daɗi,

      Amma su biyu maganar gaskiya ta fi su.

22 Kayan ado da gyara jiki suna da daɗin gani,

      Amma su biyu, furen itacen jeji ya fi su.

23 Aboki da maƙwabci abokan fāɗi‑ka-tashi ne,

      Amma su biyu mace mai hankali ta fi su.

24 Ɗanuwa da mataimaki suna yin taimako lokacin matsuwa,

      Amma su biyu ladan da ake samu don yin sadaka ya fi su.

25 Zinariya da azurfa suna sa mutum ya yi albarka,

      Amma su biyu, tunanin kirki ya fi su.

26 Laftya da wadata suna sa mutum ya amince da kansa,

      Amma su biyu, tsoron Allah ya fi su.

Mai tsoron Ubangiji ba zai rasa kome ba,

      Wanda yake da tsoronsa,

      Ba sai ya nemi wani taimako dabam ba.

27 Mai tsoron Ubangiji cikin aljannar albarka yake,

      Dukan abubuwa masu daraja sun kewaye shi.

Yin Bara

28 Ɗana, kada ka yi zaman duniya irin na mabaraci,

      Gara mutuwa da a zauna a yi ta roƙo.

29 In sai mutum ya yi koraka kullum,

      Bai ji daɗin zaman duniya ba.

Cin kyakkyawan abincin koraka abin ƙyama ne

      Gun wanda ya san kunya.

30 A gun marar kunya abincin roƙo daɗi gare shi,

      Amma yana da damuwa a zuci.

41. A kan Mutuwa

1 Haba mutuwa! Ai, tunawa da ke ba shi da daɗi

      A gun mutum, wanda ke zaman salama a kan mallakarsa,

Ga matashin ƙarfi wanda ke da arziki ta kowace hanya,

      Wanda ke da ganiyar more wa duniya.

2 Haba mutuwa, ai, hukuncinki mai daɗi ne

      Ga matalauci marar karfi,

Gama yana tafiya yana tangaɗi da tuntuɓe,

      Ba ya ma gani sosai, ba shi da buri.

3 Kada ka ji tsoron ajalinka,

      Ka tuna mutuwa ta kwashe waɗanda suka riga ka zuwa, da na bayanka.

4 Haka ne Allah ya ƙaddara wa dukan yan adam,

      Saboda me za ka ƙi nufin Maɗaukaki?

Ko mutum ya zauna a duniya shekaru dubu, ko dari, ko goma,

      Bayan mutuwarsa ba shi da ikon cewa, Zan koma duniya.

Abin da zai Sami Masu Saɓo

5 Ana raina yayan masu ƙeta,

      Wawayen yaya suna cikin gidajen masu mugunta.

6 A kan gādon yayan masu saɓo sata ta ci sata,

      Zargin zuriyarsu ma ake ta yi.

7 Yaya suna laanta mamuguncin mahaifinsu,

      Gama ana kunyata su saboda shi.

8 Taku ta ƙare, masu saɓo,

      Ku da kuka watsar da shariar Maɗaukaki.

9 In kuna da yaya, balai zai auko musu,

      Kun haife su don su sha wahala kawai.

In kun yi tuntuɓe, ai, mutane za su yi ta tsalle,

      Ko bayan mutuwarku za a laance ku.

10 Ai, abin da ke banza wofi zai koma,

      Mai saɓon Allah ma zai fi rashi rashi.

11 Jikin mutum ba ya ɗorewa,

      Amma sunan mai nagari ba ya ɓacewa ko kaɗan.

12 Ka kula da sunanka, zai yi maka amfani,

      Gama ya fi dukiya daraja, kome yawanta.

13 Tsawon rai kwanaki ne masu iyaka,

      Amma suna mai kyau kwanakinsa ba su da iyaka.

A kan Jin Kunya

14 Yayana, ku bi jawabina game da jin kunya,

      Ku saurare ni, ku ji abin kunya da wanda ba na kunya ba.

Gama bai kamata a ji kunya kullum ba,

      Bai ma dace ba, kullum a kawar da kai.

15 Ka ji kunyar yin zina a gaban mahaifinka,

      A gaban maigidanka ma, ko uwargidanka, ka ji kunyar ƙarya.

16 A gaban sarki ko hakimi ka ji kunyar yin daɗin baki,

      A cikin taron jamaa ma, ka ji kunyar yin babban laifi.

17 A gaban abokinka ko maƙwabci ka ji kunyar cin amana,

      Ko ta da rantsuwa ko ƙin cika alkawari.

18 Ka ji kunyar yin sata a masaukinka,

      Ko nuna zari a gun abinci.

19 Ka ji kunyar hana abu in an roke ka,

      Ko yin hainci a kan rabon wani.

20 Ka ji kunyar ƙin amsar gaisuwa,

      Ko raina aboki.

21 Ka ji kunyar zuba wa macen aure ido,

      Ko tunanin nishaɗi da matar wani.

Ka ji kunyar yin barazana da baiwarka,

      Ko kwana da ita.

22 Ka ji kunyar yi wa abokai baƙar magana,

      Ko zaginsu bayan ka yi musu kyauta.

23 Ka ji kunyar maimaita abin da ka ji,

      Ko tona shawarar asiri.

24 Waɗannan su ne abubuwan da za ka guɗana saboda kunya,

      In kana so kowa ya gan ka da daraja.

42.

1 Amma akwai waɗansu abubuwa da ba za ka ji kunya ba,

      Don kada ka yi saɓo saboda bangirman yan adam.

2 Ɗaya daga cikinsu ita ce shariar Maɗaukaki da dokokinsa,

      Ko hukunta mai yin saɓo,

3 Ko biya kuɗin taimakon kai da kai a kan aiki ko tafiya,

      Ko raba gādo ko dukiya daidai,

4 Ko gyara mudu da maauni daidai wa daida,

      Ko daidaita kwanon gwaje da awon nauyi,

5 Ko samun abu mai yawa, ko kaɗan,

      Ko yin tataccen ciniki da ɗan kasuwa,

Ko koya wa. yara. da kwaɓa kullum,

      Ko mangarin bawa mai hainci,

6 Ko kulle shakiyiyar mace,

      Ko aɗana kaya daga wurin da mutane suke yawan shiga da fita,

7 Ko ƙidaya abin da aka tara,

      Ko rubuta dukan abin da aka bayar ko aka karɓa,

8 Ko yi wa marar kangado da wawa bulala,

      Ko horon jairin tsoho saboda yin zina.

In ka yi haka za ka zama mai hankalin gaske,

      Kowa zai gane kai mai kangado ne.

Yadda Uba zai Kula da Yarsa

9 Ya dukiya ce da ke hana mahaifinta kai barcinsa,

      Kula da ita ma yana hana shi cikakken hutu,

Don kada ta wuce gaɓar aurenta,

      In ta yi auren ma, kada ta zama abin ƙi,

10 Kafin ta yi aure kuma, kada a lalata ta,

      In ta yi aure ma, kada ta riƙa bin mazan duniya,

A gidan mahaifinta kuma kada a yi mata cikin shege,

      A wurin mijinta ma kada ta zama juya.

11 Ka lura da yarka sosai,

      Kada ta mai da kai madari a gun maƙiyanka,

Kada ta mai da kai abin hira cikin birni,

      Abin zargi cikin jamaa,

      Ka zama abin baa a taron mutane.

Kada ka ba ta ɗaki mai taga a kan hanya,

      Ko ɗakin ƙofar gida.

12 Kada ka ƙyale ta ta zaga gari neman samari,

      Kada ma ka yarda ta ɗauki tsabiar matan aure.

13 Gama kamar yadda kurukuru ke ɓata tufafi,

      Haka ma mata ke ɓata mata.

14 Gara yawan faɗan miji, da matarsa ta riƙa yin lalata,

      Gara tsoratacciyar ya, da ya mai kawo wa uba raini.

A kan Aikin Allah na Halitta

15 Yanzu zan ambaci ayyukan Allah,

      Abin da na gani zan bayyana shi.

Da Allah ya yi magana, sai ayyukansa suka wanzu,

      Suna cika nufinsa yadda ya ƙaddara su.

16 Kamar yadda hasken rana ke haskaka kowa,

      Haka ma ɗaukakar Ubangiji take cika dukan ayyukansa.

17 Tsarkakan malaiku na Ubangiji ma,

      Ba su iya ƙidaya abin mamakinsa,

Ko da ya ke Allah ya ƙarfafa wannan runduna tasa

      Domin ta tsaya tsayin daka gaban ɗaukakarsa.

18 Allah yana hangen zurfafan duniya da abin da ke zuciyar yan adam,

      Ya ma san duk shawararsu ta asiri.

Maɗaukaki ke da dukan sani,

      Shi ne ke ganin dukan abin da zai je ya zo.

19 Shi ne ke sanar da abin da aka yi dā da na gaba,

      Yana ma tono boyayyun asiran duniya.

20 Ba abin da bai sani ba,

      Ko abu ɗaya ba zai kuɓuce masa ba.

21 Hikimarsa dawwamammiya ce,

      Tun fil azal ɗaya ne shi.

22 Ba a rage shi, ba a ƙara shi,

      Ba ya ma bukatar mashawarci.

23 Kai! Ayyukan Ubangiji da kyau suke,

      Ga su nan dai daga hasken rana har ɓarɓashin wuta.

24 Sama da kasa za su ɗore har abada,

      Allah ya kiyaye kowace halitta domin ta biya wata bukata.

25 Dukansu suna da bambanci, wani dabam da wani,

      Duk da haka Allah ba ya halittar banza,

Gama kowanne yana da kyau a lokacinsa,

      Wanene zai iya gajiya da ganin tsananin darajarsu?

43. Ga Rana

1 Tangarewar sararin sama da kyan gani take,

      Kamar aIjanna ce ma da kanta, da wahayin ɗaukaka.

2 Da rana ta leƙo da sassafe, sai ta watso wa duniya haske.

      Kai! wannan abin alajabi ne da Maɗaukaki ya yi.

3 Da ta ɗaga sai ta haske dukan rasa,

      Wa ma ke iya ɗaure wa zafinta?

4 Kamar wutar maƙera mai watso zafi,

      Haka rana take kwararo zafinta, har duwatsu suna ƙonuwa.

Da tsananin zafinta take cinye ƙasa,

      Har idanu suna dushewa saboda haskenta.

5 Ubangiji da girma yake, tun da ya halicci rana,

      Da ikonsa ne take ratsa hanyarta.

Ga Wata

6 Wata ma yana aiki da sauyar lokaci,

      Yana nuna rani da damuna, shekara biye da shekara.

7 Ta wurin wata ne muke sanin ranakun idi da ranakun biki da muka sa,

      Domin farin wata yana shiga duhu a bisa kaaidarsa,

8 Kamar yadda sunan ke nufi, duk wata yana mutuwa, yana hawa,

      Wannan sauya, ai, da banmamaki yake!

Ga Taurari

9 Taurari su ne ado da ɗaukaka ga sararin sama,

      Su ne ke ƙayata samaniyar Allah da haskensu.

10 Da umarnin Allah kowannensu ke zaune inda yake,

      Ba su yin saku da aikinsu.

Su ne ma suke yi wa taskar ruwa a sama datsi kullum,

      Suna haskaka sararin sama da haskensu.

Ga Bakan Gizo

11 Ga bakan gizo, ku yabi Mahaliccinsa,

      Gama yana da ɗaukakar gaske.

12 Yana ɗane sararin sama da ɗaukakarsa,

      Bakan nan ikon Allah ne ya tanƙwasa shi.

Ga Sauran Abubuwan Duniya Masu Banmamaki

13 Da tsawatawarsa ne Allah yake aika walƙiya,

      Yana sakinta kamar kibiya don ta yi hukunci.

14 Saboda haka ne yake buɗe gidan gizagizansa,

      Suna yin rigyangyanto zuwa waje kamar ungulai.

15 Da girmansa ne yake ba hadiri ikonsa,

      Yana ma zubo da ƙanƙara.

16 Tsawar muryarsa tana sa ƙasa magōwa,

      A gaban ikonsa duwatsu suke rawa.

17 Maganarsa tana koro iskar kudu,

      Da iskar arewa, da gawurtaccen hadiri.

18 Yana yayyafa farin dusan ƙanƙara

      Kamar kaɗawar ganye lokacin iska,

      Yana sauka kamar dandazon ɗango.

19 Ƙyallinsa yana dushe idanu,

      Yana fadowa bi da bi.

20 Allah yana kwararo jauro kamar gishirin beza,

      Tana haske kamar dandazon balbelu a kan itace.

21 Yana aiko da iskar arewa mai tsananin sanyi,

      Wadda take mai da ruwan tafki curin ƙanƙara.

Yana sa fuskar kowane ruwan kogi ta daskare,

      Yana mai da ruwan tafki kamar daɓe.

22 Da zafin rana Allah yake sa haki na kan tsauni ya bushe,

      Yana ma sa ciyawar karkara ta bushe kamar an ƙone.

23 Amma daga baya, sai ya aiko da ruwan sama,

      Duk ciyayi su farfado,

      Yana ma sa raɓa ta arzuta kasa.

24 Nufinsa ke kwantar da motsin manyan tekuna,

      Yana ma kafa yan tsibirai a cikinsu.

25 Waɗanda suka yawata teku da jirgin ruwa,

      Su ne ke gutsura labarinta,

      Da mun ji abin da suka ce da sai mu gigice.

26 Gama cikin teku halittan Allah suke,

      Masu banmamaki kwarai,

Halitta iri iri ga ta nan,

      Da ƙaton mugun naman ruwa.

27 Allah ne yake sa kowace halittarsa ta cika aikinta,

      Da umarninsa ne suke aikata. nufinsa.

28 Abin da muka faɗa ya isa haka,

      Daga bisani za mu ce, Ikon Allah ya baibaye duniya!

29 Mu ƙara masa yabo, tun da ba ya misaltuwa,

      Gama ya fi dukan ayyukansa girma.

30 Ai! Ɗaukakar Ubangiji da bantsoro take,

      Ikonsa kuma da banmamaki yake.

31 Ku ɗaga murya domin ku girmama Ubangiji,

      Ko da ya ke ba za ku iya yi masa cikakken yabo ba.

32 Ku girmama shi da sabon ƙarfi,

      Kada ku gaji, ko da ya ke ba za ku iya yabonsa ba tutur.

33 Gama wanene zai iya ganin Allah,

      Har ya ba da labarinsa?

      Wanene ma zai iya yabon Allah yadda yake?

34 Ai, sauran ayyukan Allah masu yawa an ɓoye su.,

      Ɗan kima ne kawai muka gani.

35 Ubangiji ne ya halicci dukan kome,

      Yana ba waɗanda ke tsoronsa hikima.

44. Yabon Kakanni Kakannin Israilawa

1 Yanzu zan yabi shugabannin kakanninmu, mutanen kirki,

      Kowannensu a nasa zamani.

2 Jamaar Maɗaukaki tana yin taƙama da su kwarai,

      Alummar da Allah ya zaɓa tun dā tana ta yabonsu.

Shugabannin kakanninmu ne suka ƙwace ƙasar,

      Suka kafa fadarsu,

      Mutane ne masu suna saboda jaruntakarsu.

3 Waɗansu mashawarta ne na kirki,

      Ko masu gane dukan abu a kan annabci.

4 Waɗansu sarakunan mutanensu ne masu himma,

      Ko hakimai masu iko.

Waɗansu mawallafa ne, gwanayin rubutu,

      Ko masu ƙago karin maganar hikima.

5 Waɗansu mawallafa ne na Zabura masu daɗin amo,

      Ko marubuta jawaban hikima.

6 WaDansu masu abin kai ne,

      Waɗanda suka kahu da gindinsu,

      Suna zaman natsuwa a kan mallakarsu.

7 Dukan mutanen nan an ɗaukaka su a zamaninsu,

      Kowannensu mashahuri ne a cikin kwanakinsa.

8 Waɗansunsu sun yi suna,

      Jamaa ma suna ta yin yabon cancantar aikinsu.

9 Amma waɗansu masu kirki, an mance da su sam,

      Da suka shuɗe sun shuɗe ke nan,

Kamar ma ba su zo duniya ba,

      Da su da yayansu.

10 Ai, dukan mutanen nan masu alheri ne,

      Nagartarsu sai gaba take yi.

11 Dukiyarsu ta koma hannun iyalinsu,

      Abin da suke da shi yana gun jikokinsu.

12 Saboda yarjejeniyar da Allah ya yi da su,

      Iyalinsu za su ɗore,

      Yayansu ma za su sami albarkar iyaye.

13 Har matuƙar zamani jikokinsu za su ɗore,

      Ɗaukakarsu ma ba ta mantuwa.

14 Sun mutu, jikinsu ya kwanta lafiya,

      Amma sunansu zai yi ta yin gaba gaba.

15 A jamaa ana ta faɗar hikimarsu,

      A taron mutane ma ana raira yabonsu.

Ga Anuhu

16 Anuhn ya yi tafiya da Ubangiji,

      Aka ɗauke shi sama kuma,

      Domin tsara mai zuwa ta yi koyi da misalinsa.

Ga Nuhu

17 Nubu, da Allah ya samu cikakke, mai adalci,

      Ya sabunta kabilar yan adam a lokacin Ruwan Tsufana.

Saboda cancantar Nuhu aka rage waɗansu mutane su rayu,

      Allah ya nuna masa alama, cewa ambaliyar ruwa ta wuce.

18 Allah ya yi yarjejeniya da Nuhu, cewa

      Ba zai ƙara hallaka duniya da ruwa ba.

Ga Ibrahim

19 Ibrahim, uban alumma mai girma,

      Ya riƙe darajarsa ba muni.

20 Ya kiyaye dokokin Maɗaukaki

      Allah ma ya yi yarjejeniya da shi.

Yarjejeniyar ta ƙullu saad da Allah ya sa Ibrahim ya yi kaciya,

      Lokacin da aka gwada shi kuma,

      An same shi mai aminci.

21 Saboda haka Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa, cewa

      Daga zuriyarsa alummai za su yi albarka.

Ya ce ma zai mai da zuriyarsa kamar yawan rairayin teku,

      Kabilarsa za ta yi yawa kamar taurarin sama.

Ya ba su ƙasa daga wannan teku zuwa waccan,

      Daga kogi har iyakar duniya.

Ga Ishaku da Yakubu

A kan Ishaku Allah ya sāke sabunta yarjejeniyar,

      Saboda mahaifinsa Ibrahim.

Allah ya yi yarjejeniyar da Ishaku, masu ado,

      Yadda ya yi ta da dukan kakannin da suka riga shi,

      Ishaku ma ya danƙa wa Yakubu albarka.

23 Allah ya mai da Yakubu kamar ɗan Ishaku na fari,

      Ya ba shi dukan gādo.

Ya yi wa kowace jiha iyaka a kabilan Yakubu,

      Ya raba su goma sha biyu.

45. Ga Musa

1 Daga jikokin Yakubu Allah ya yi wani mutum,

      Wanda ya sami tagomashin dukan mutane,

Abin ƙauna ne a gun Allah da mutane,

      Wato Musa, wanda ake ta bimbinin kirkinsa.

2 Ubangiji ya ba shi laƙabi Na Allah,

      Ya ƙarfafa shi da iko mai bantsoro.

3 Allah ya aika alajabai ta maganar Musa nan take,

      Ya ba shi gaba tsaye a gaban Firauna.

Daga baya Musa ya karɓo dokoki saboda mutanensa,

      Kai! ya ga ɗaukakar Allah zahin.

4 Saboda amincinsa da tawaliunsa ne

      Allah ya zaɓe shi daga tsakanin dukan yan adam.

5 Ya ma yardar wa Musa ya ji muryarsa,

      Ya kai shi har cikin girgije,

Inda ya ba shi dokoki fuska da fuska,

      Wato sharia ta rai da ta fahimta,

Domin Musa ya koya wa yayan Yakubu dokokin Allah,

      Ya kuma sanar da Israilawa umarnan Allah da kaidodinsa.

Ga Haruna

6 Allah ya zaɓi wani mai kirki ma, kamar Musa,

      Haruna ne, wan Musa, daga kabilar Lawiyawa.

7 Allah ya ba Haruna matsayi mai ɗorewa

      Lokacin da ya naɗa shi firist na Israilawa.

Ya naɗa shi da daraja kwarai,

      Ya ba shi mafificin rawanin sarauta.

8 Allah ya suturta Haruna da tufafi masu ado,

      Ya ɗaukaka shi da tufafin ibada masu ƙawa.

Tufafin, su ne wando, da taguwa,

      Da alkyabba mai kalmasar zānannun rumman.

9 An kuma daje kewayen kalmasar

      alkyabbarsa da gwarje masu yawa,

Waɗanda suke yin ƙara mai daɗi

      duk saad da ya ɗaga ƙafa.

Jamaar da ke waje sunajinsa can cikin Wuri Mafi Tsarki,

      Sa wannan alkyabba ya zama alada a gun jikokin Haruna.

10 An gyara tufafinsa na ibada da launin zinariya,

      Da jar garura da ja ja wur,

      Har ma da maƙalawa.

An kuma sa masa rataye da efod da ke nuna nufin Allah,

      Da ƙyallen rataya wa wuya mai damara, sunansa efod.

11 An saƙa alaben da efod da zare ja ja wur.

      Suna da duwatsu kuma masu daraja,

      Waɗanda aka matsa cikin zinariya.

A kan fuskar duwatsun

      An rubuta sunayen kowace kabila ta Israilawa.

12 A rawanin Haruna akwai ta zinariya,

      A kanta an rubuta, Keɓaɓɓe a tsarkake ga Ubangiji.

Allon nan mai kwarjini ce da ɗaukaka da suna mai girma,

      Tana faranta ido da mafificin kyanta.

13 Banda Haruna, ba wanda aka ɗaukaka da waɗannan abubuwa,

      Ba ma za a yi wanda zai rataya irinsa ba dadai,

Sai dai yayansa, su kadai kuwa,

      Tsara biye da tsara, har dukan zamanai.

14 Haruna yana ƙone garin hatsinsa na miƙawa ƙurmus,

      Duk saad da yake yin hadayar safe da ta yamma.

15 Gama Musa ne ya naɗa shi,

      Ya shafe shi da mai mai tsarki.

An yi yarjejeniya mai ɗorewa da Haruna da iyalinsa,

      Mai ƙarƙo ce kamar sararin sama,

Domin ya yi wa Allah hidimar firist,

      Ya kuma sa wa mutanensa albarka da sunan Ubangiji.

16 Allah ya zaɓe shi daga dukan yan adam,

      Don ya miƙa hadayun ƙonawa masu kitse,

Ya ƙona turare mai ƙanshi yadda za a yi ta yin gaba,

      Ya kuma yi hadayar kafarar laifi saboda Israilawa.

17 Allah ya ba shi dokoki,

      Da iko ya yi umarni, ya kuma sharaanta,

Ya koya wa Israilawa kaidodin Allah,

      Ya bayyana musu dokokin sharia.

18 Amma sauran gidajen Israilawa suka hangula da shi,

      Suna jin ƙyashinsa cikin hamada.

Mabiyan Datan, da Abiram, da yan ƙungiyar Kora,

      Sai suka yi zanga‑zanga.

19 Amma Ubangiji ya hangi wannan, ya husata kuma,

      Ya hallakar da su da fushi mai zati.

Ya yi wani abin alajabi a kansu,

      Inda ya sa wutar fushinsa ta ƙone su. ƙurmus.

20 Saan nan sai ya ƙara wa Haruna girma,

      Ya mayar masa da dukiyarsa.

Allah ya ba shi tsarkakakkun hadayun da aka miƙa,

      Da gurasar ajiyewa.

21 Hadayun da ake yi wa Ubangiji su ne abincinsa,

      Su kyauta ce a gunsa da yayansa.

22 Amma Haruna ba shi da gona cikin jamaa,

      Bai sami tasa jiha ba,

Gama Ubangiji ne nasa rabo,

      Ubangiji ne dukiyarsa a tsakanin Israilawa.

Ga Finehas

23 Finehas, ɗan Eleazara ma,

      Shi ne na uku a masu ƙarfin hali na tsararsa.

Yana da himma mai yawa saboda Allah Mamallaki,

      Ya yi ƙuru, ya tsare mutanensa daga annoba.

Yana bin abin da zuciyarsa ta ƙuta masa,

      Ya yi kafarar laifi saboda Israilawa.

24 Saboda haka Allah ya yi yarjejeniyar abuta da shi,

      Ya ba shi aikin kula da masujada,

Domin shi da jikokinsa

      Su gāji baiwar yin aikin firist har matuƙa.

25 Yarjejeniyarsa ma da Dawuda,

      Ɗan Yesse na kabilar Yahuza,

Gādo ne da da ɗaya kawai ke samu a cikin yaya,

      Amma gādon Haruna saboda dukan yayansa ne.

26 Ku yayan Haruna, yanzu sai ku yabi Ubangiji,

      Wanda ya nada muku rawanin ɗaukaka!

Domin ya ba ku zuciya mai hikimar gaske,

      Ku mallaki jamaarsa da adalci,

Don kada ku mance da lafiyar zamansu,

      Ko ku shagala da ikonku wanda zai dore har matuƙa.

46. Ga Joshuwa

1 Joshuwa ɗan Nun jarumin shugaba ne,

      Mataimakin Musa game da aikin annabci.

An mai da shi, kamar yadda sunansa ya nuna,

      Maceci mai girma na zaɓaɓɓun Allah,

Don ya hori abokan hamayya,

      Don ya ƙwato wa Israilawa ƙasa,

2 Kai, ya ba da mamaki lokacin da ya wanke hannu,

      Ya auka wa birni da mashi.

3 Wanene ya iya ɗauko fansa gunsa,

      A lokacin da ya yi yaƙin Ubangiji?

4 Ba da ikonsa ba ne ya tsai da rana,

      Inda kwana ɗaya ya zama biyu?

5 Taimakon Allah Maɗaukaki ya nema,

      Lokacin da abokan gdba suka yi masa zobe.

Allah Maɗaukaki ma ya amsa masa

      Da ƙanƙara banƙam‑banƙam mai azaba du abokan gaba da ikon gaske.

6 Allah ya aiko da ƙanƙara a kan rukunin sojojin abokan gāba,

      Har da ya hallaka su a kan tudun da suke,

Domin sauran laantattun alummai su sani,

      Cewa Ubangiji yana lura da yaƙin jamaarsa.

Joshuwa shi baran Allah ne na gaske,

      7 A zamanin Musa ma ya nuna aminci.

Ga Kalibu

Joshuwa da Kalibu ɗan Yefunne,

      Lokacin da ba su goyi bayan taron yan tawaye ba,

Suka kāre mutane daga fushin Allah,

      Suka kuma tsai da mugun musun da jamaar ke yi.

8 Saboda haka sai su biyu kaɗai suka tsira

      Daga cikin jamaa dubu dari shida balagaggu

Don su yi wa yayan jamaa jagora zuwa ƙasar alkawari,

      Ƙasar da ke da yawan albarka.

9 Ƙarfin da Allah ya ba Kalibu kuwa

      Sai ya ɗore har tsufansa,

Sai da ya sami gonarsa ta tsaunukan ƙasar alkawari,

      Wurin da ya zama gādon iyalinsa,

10 Domin dukan jamaar Yakubu su ga

      Faidar bin Allah da gaske, ba da tantama ba.

Ga Sarakan Yaƙi, Hakimai

11 Sarakan yaƙi ma, kowannensu bai bauɗe ba,

      Ba su yar da Allah ba,

      Albarka ta ɗore a kansu.

12 Sun sāke rayuwa a bayan mutuwarsu,

      Gama sunayensu sun koma a kan yayansu.

Ga Samaila

13 Abin ƙauna a gun mutanensa,

      Mahaliccinsa yana sonsa,

Zaɓaɓɓe daga cikin mahaifiyarsa,

      Naɗaɗɗe ga Ubangiji domin ya yi annabci,

      Samaila sarkin yaƙi ne, firist kuma.

Saboda umarnin Allah ne ya kafa mulki,

      Yana shafe sarakunansa da mai,

      Su yi mulkin jamaar Allah.

14 Ta shariar Ubangiji yake hukunta alumma

      A lokacin da ya ziyarci gidajen yayan Yakubu.

15 An zaɓe shi annabi mai gaskiya,

      Sai kuma kalmominsa suka nuna annabcinsa zahiri.

16 Ai, shi sunan Allah ne ya kira,

      Ya miƙa hadayar kiwataccen ɗan rago.

17 Saan nan sai Ubangiji ya yi tsawa daga sama,

      Aka kuma ji gawurtacciyar muryarsa,

18 Ya ƙasƙanta sarakuna, abokan gāba,

      Ya hallakar da dukan hakiman Filistiyawa.

19 Lokacin da Samaila ya doso ƙarshen ransa,

      Sai ya yi shaida a gaban Ubangiji da sarki Shawulu,

      Wanda ya naɗa, inda ya ce,

Ban taɓa karɓar toshi ko kyauta a asirce daga kowa ba.

      Ba kuwa wanda ya yi masa mūsū.

20 Har bayan mutuwarsa ma an nemi shawararsa,

      Ya gaya wa sarki abin da zai same shi.

Har daga cikin kabari ma ya daga muryar annabci,

      Don ya murƙushe aikin ƙeta.

47. Ga Natan

1 Da Samaila ya mutu, sai Natan ya gaje shi,

      Wanda ya yi annabci a gaban Dawuda.

Ga Dawuda

2 Kamar ƙanshin kitsen turkakkiyar dabbar hadaya,

      Haka Dawuda yake a gun Israilawa.

3 Yana yin wasa da zakoki kamar yan awaki,

      Yana yi da beyar, sai ka ce yan tumaki.

4 A samartakarsa Dawuda ya kashe jarumin abokan gāba,

      Ya kawar da rainin da ake yi wa Israilawa.

Da majajawa ya yi harbi,

      Ya yar da Goliyat mai alfarma, matacce.

5 Tun da ya ke ya yi kira da sunan Maɗaukaki, Allah,

      Allah ya ba shi ƙarfin gwiwa,

Don ya ci gwanin yaƙi,

      Ya ƙarfafa mutanensa.

6 Saboda haka ne mata suka yi masa waka,

      Inda suka ce Dawuda ya kashe dubbai bisa dubbai.

      Da ya hau gadon mulki, sai ya yi ta yaƙe‑yaƙe,

7 Yana tanƙwashe marciya ta kowace fuska.

      Ya hallaka abokan gāba na Filistiyawa,

Ya wajajagar da ikonsu,

      Ba su sāke haɗuwa ba har kwanan gobe.

8 Yana yi wa Allah Maɗaukaki godiya,

      Duk lokacin da zai yi wani abu da kalmomin yabo.

Yana ƙaunar Mahaliccinsa da dukan zuciyarsa,

      Yana ma yin waƙar yabon Allah kowace rana.

9 Ya ƙara bunkasa idi,

      Ya girmama idodin godiyar Allah na kowace shekara,

Yana yin waƙar molo a gaban bagade,

      Da waƙa mai daɗi ta Zabura,

10 Domin a yi yabon suna mai tsarki na Allah,

      Sai masujada ya cika da waƙoƙi tun da asuba.

Ubangiji ya yafe wa Dawuda laifofinsa,

      Ya kuma ɗaukaka shi da iko mai ɗorewa.

Ubangiji ya ba shi gadon sarauta,

      Ya girka tushen sarautarsa cikin Israilawa.

Ga Sulemanu

12 Saboda kirkinsa an ba Dawuda magaji,

      Wayayyen ɗa wanda ya yi zamansa hankali kwance.

Gama a lokacin da Sulemanu yake a gadon sarauta hankalin kowa na kwance,

      Domin Allah ya kintsar da wuraren da Sulemanu ke yin mulki.

Sai ya gina Haikali,

      Ya kafa tushen Wuri Mai Tsarki mai ɗorewa.

14 Ai, kana da wayo a lokacin ƙuruciyarka

      Iliminka yana ambaliya kamar kogin Nilu.

15 Fahimtarka ta baibaye duniya,

      Saninka ma. ya cika duniya kamar yadda ruwa ke cika teku.

16 Sunanka ya yi nisa a duniya,

      Mutane daga wurare dabam dabam

      Suna zuwa domin su ji hikimarka.

17 Saboda waƙarka, da labarinka,

      Da tatsuniyoyinka da amsoshinka,

      Kana ba sauran alumma mamaki.

18 Ana kiranka da suna Kaunatacce na Ubangiji,

      Wanda aka sa wa alummar Israila.

Ka tara zinariya kamar dumbun ƙarfe,

      Ka yi tari‑tarin azurfa sai ka ce darma.

19 Amma ka cika shaawar mata,

      Har ma ka sallama musu jikinka.

20 Ka kawo wa kyakkyawan sunanka raini

      Da kunya a kan yawan aure‑aurenka.

Ka jawo wa yayanka cin mutunci,

      Ka ma kawo wa mulkinka yawan saɓani.

21 Ta haka ne mulkin ya kasu biyu,

      Sai mutanen Ifraimu suka zuƙe,

      Suka kafa tasu sarauta.

22 Amma Allah bai yar da jinƙansa ba,

      Ko ɗaya ma daga cikin alkawaransa bai yar ba.

Bai tuge yayan zaɓaɓɓensa Yakubu ba,

      Bai ma hallaka dukan yayan amininsa Dawuda ba.

Don haka ya sa waɗansu daga cikin jikokin Yakubu su wanzu,

      Ya bai wa Dawuda tushen waɗansu daga cikin jikokinsa.

Ga Rehobowam

23 Daga bisani sai Sulemanu ya rasu, kurwarsa ta tafi gun mahaifansa,

      Ɗaya daga cikin yayan Sulemanu ya gāje shi,

Rehobowam, mai gayyar ɓaro, marar isasshen hankali,

      Da siyasarsa ne ya sa mutane suka yi tawaye.

Ga Yerobowam

Sai da wani baran ya hau gado,

      Wanda bai ma kamata a ko tuna da sunansa ba,

Mai saɓo, wanda ya sa dukan Israilawa suka yi saɓo.

      Shi ne ma ya kawo rushewar yayan Ifraimu,

      24 Ya sa aka kore su daga ƙasarsu.

Ga Iliya

25 Saɓonsu, sai ya yi ta yin gaba gaba,

      Sai suka duƙufa a kan aikata kowace irin ƙeta.

48.

1Sai da annabi Iliya ya kunno kai kamar wuta,

      Ya bazo kalmominsa kamar wutar maƙera.

2 Ya hana damuna faɗuwa, sun sha lama da yunwa,

      Ya yi musu ƙasƙanci da himmarsa.

3 Ta kalmar Allah ya hana ruwan sama,

      Amma sau uku yana kiran wuta daga sama.

4 Kai! Iliya, da iko kake!

      Wanene yake da ɗaukaka irin taka?

5 Ta ikon Ubangiji ka sake raya wanda ya mutu,

      Ka ta da shi daga kabari.

6 Ka aika da sarki fagen fama inda aka hallaka shi,

      Wani sarki ma, da jikinsa ya motsu,

      Ka aika da shi Lahira.

7 Ka ji tsawatawa a Sinai,

      A Horeb kuwa ka ji yadda Allah ya zartar da hukuncin ramuwa.

8 Ka naɗa sarakunan da za su yi ramuwa,

      Har da annabi Elisha ma wanda ya gāje ka.

9 An ɗauke ka a cikin guguwa,

      A keken dawakai mai gudun gaske.

10 A rubuce yake an ƙaddara nan gaba,

      Za ka kwantar da hankalin mutane

      Kafin ranar da Ubangiji zai zo,

Za ka sulhunta tsakanin iyaye da yayansu,

      Za ka sāke kafa kabilan Yakubu.

11 Mai albarka ne shi, duk wanda zai gan ka kafin ya mutu.

      12 Haba Iliya, kai da ka hau sama ta cikin guguwa!

Ga Elisha

Elisha ma, wanda ya gaji rabon annabci mai yawa na ruhun Iliya,

      Ai, ya yi abin alajabi mai yawa ta maganar baka kawai.

A zamaninsa ba yajin tsoron kowa,

      Ba ma wanda ke iya burgarsa don ya sāke nufi.

13 Ba abin da ya fi ƙarfinsa,

      Shi ma ya dawo da matacce.

14 Ya yi abubuwa na mamaki,

      Har bayan mutuwarsa ma ba a daina ganinsu ba.

Saɓo da Horo na Israilawa

15 Amma ko da ya ke sun ga abubuwan nan,

      Mutane ba su tuba sun bi Allah ba,

Ba su ma daina yin saɓo ba,

      Sai dai da aka hamɓare su daga ƙasarsu tukuna,

      Aka warwatsa su koina a duniya.

Amma aka rage kaɗan daga na Yahuza,

      Su da sarakunansu daga cikin jikokin Dawuda.

16 Waɗansu daga cikin sarakunan nan sun yi abin nagari,

      Amma waɗansunsu sun yi mugun saɓo.

Ga Hezekiya

17 Sarki Hezekiya ya gyara birninsa,

      Ya wadata shi da ruwan sha,

Gama da kayan ƙarfe ya haƙa maguɗanar ruwa a cikin dutse,

      Ya kuma gina matarar ruwa.

18 A zamanin mulkinsa ne, Sennakerib ya shugabanci wani mai kai hari,

      Inda ya aiki jaruminsa,

Ya yi wa birnin Sihiyona daƙuwa,

      Yana yi wa Allah saɓo da girmankai.

19 Sai rayukan mutane suka dugunzuma,

      Suna baƙin ciki kamar mace a lokacin haihuwa.

20 Amma mutanen suka yi ta kiran sunan Allah Maɗaukaki,

      Suka duƙufa yin addua,

Sai Allah ya ji adduar da suka yi,

      Ya cece su ta hannun Ishaya.

21 Sai Allah ya yi kaca kaca da sansanin Assuriyawa,

      Ya tumɓuke su da annoba.

22 Gama Hezekiya ya yi abin kirki,

      Yana biye da hanyar Dawuda,

Kamar yadda mashahurin annabin nan Ishaya ya umarce shi,

      Wanda ya ga gaskiya zahiri a cikin wahayi.

23 A zamanin sarki Hezekiya, Ishaya ya tsauta wa rana,

      Ya kuma ƙara wa sarki tsawon rai.

24 Ta ikon ruhunsa yana duban abin da ke gaba,

      Ya ma taazantar da masu makokin Sihiyona,

25 Ya faɗi yadda abu zai faru zuwa gaba,

      Irin ɓoyayyun abubuwa da dole ne su cika.

49. Ga Yosiya

Sunan nan Yosiya kamar gaurayayyen turare yake,

      Wanda gwanin yin turare ya hada don ya dade.

Ana tunawa da Yosiya kamar zakin zuma,

      Kamar kiɗe‑kiɗe kuma a wurin biki.

2 Gama ba ya jin daɗin ayyukan kakanninmu na hainci,

      Yana hamɓare gumakansu masu banƙyama.

3 Ya sa dukan zuciyarsa a gun Allah,

      Ko da ya ke mugun zamani ne,

      Shi ba abin da yake yi sai abin kirki.

Ga Sauran Sarakuna da Annabawa

4 Banda Dawuda, da Hezekiya da Yosiya,

      Sauran sarakunan Yahudawa ba su da abin nagari,

Domin dukansu sun watsar da shariar Madaukaki

      Daga na asali har na karshensu.

5 Don haka sai Allah ya ƙwace ikonsu, ya ba waɗansu,

      Ɗaukakarsu kuma ya ba wata baƙuwar alumma marar kamunkai,

6 Waɗanda suka ƙone birni mai tsarki,

      Suka mai da shi kamar kufai,

      Kamar yadda Irmiya ya ce,

7 Gama sun gasa wa Irmiya azaba,

      Wanda tun yake ciki aka ƙaddara ya zama annabi

Domin ya tumɓuke, ya hamɓarar, ya kacaccala,

      Saan nan ya sāke ginawa, ya dasa.

8 Annabi Ezekiyel ya bayyana wahayi,

      Inda ya ga halittu dabam dabam, masu jan keken dawakai.

9 Kullum ma yana bin misalin Ayuba,

      Wanda ya yi ta bin hanyar Ubangiji, bai bauɗe ba,

10 Saan nan annabawan nan goma sha biyu,

      Allah ya saka musu a wurin yayansu da alheri! Amin.

Su ne suka ƙarfafa wa yayan Yakubu gwiwa,

      Ta bangaskiyarsu da bege ga Allah ne suka ceci yayan Yakubu.

Ga Zarubabal da Yoshuwa

11 Ƙaƙa za mu yi wa Zarubabal yabon da ya dace da shi,

      Wanda yake kamar zoben zinariya a yatsan hannun dama?

12 Shi da Yoshuwa ɗan Yehozadak

      Sun gina Haikali,

Su ne suka sāke ginin babban tsattsarkan Haikali na Allah,

      Ƙaddararre mai ɗorewa da ɗaukaka.

Ga Nehemiya

13 Allah ya saka wa Nehemiya da alheri, shi ma!

      Shi ne ya sāke gina garimmu,

Shi ne ma ya sāke gina hasumiyarmu ta tsaron kai,

      Ya gina ƙofofin gari, ya sa musu ƙyamare masu dirkokin ƙarfe don kullewa.

Labarin Mutanen Farko

14 Kaɗan ne za a samu a duniya waɗanda suka kai kamar Anuhu,

      Gama shi, duk da jikinsa ɗungum, aka ɗauke shi zuwa Sama.

15 An taɓa haihuwar wani ma kamar Yusufu?

      Gawarsa ma sai da aka yi mata babban tanaji.

16 Ai, Shem, da Shitu, da Enos, su ma mashahurai ne,

      Amma Adamu ya kere wa duk wani ɗan adam a duniyan nan.

50. Ga Saminu ɗan Yahaya

1 Wanda ya yanuwansa girma nesa, jamaarsa kuma suna dokinsa,

      Shi ne Saminu ɗan Yahaya.

A lokacinsa ne aka gyara Haikalin Allah,

      A zamaninsa ne aka ƙarfafa babban wurin ibadar Allah.

2 A lokacinsa ne ma aka gina garu

      Da kauraran hasumiyoyi na Haikalin Allah.

3 A lokacinsa ne aka gina wurin tara ruwa,

      Tafki mai girma, sai ka ce teku.

4 Shi ne ya yi wa mutanensa maganin yan fashi,

      Yana hana abokan gāba shigowa birninsa.

5 Ai, Saminu da kyan diri yake lokacin da yake fitowa daga alfarwar Allah,

      Daga bayan labulen Wuri Mai Tsarki.

6 Yana haske kamar tauraro mai fitowa daga bayan gizagizai,

      Kamar cikakken farin wata ma yake a ranar idi.

7 Yana haske kamar hasken rana a kan babban Haikalin Allah,

      Kamar bakan gizo ma a gizagizan sararin sama.

8 Yana kama da furen itace a lokacin bazara,

      Ko bado a kan ruwan tafki,

      Kamar ma itatuwan ƙasar Lebanon da damuna,

9 Kamar wutar turaren ƙanshi a loton yin hadaya,

      Sai ka ce ma, kwanon zinariya

      Wanda aka daje da duwatsu masu daraja,

10 Kamar itacen zaitun wanda yayansa suke da tsoka,

      Kamar ma itacen maɗaci wanda ya yi kyan diri.

11 Ya sa kayansa na hidimar Ubangiji, masu ƙawa,

      Ya kuma ɗora tufafin sujada masu daraja.

Lokacin da yake hawan wurin bagade mai daraja,

      Duk sai ya sa Wuri Mai Tsarki ya darajanta.

12 A lokacin da yake karɓar dabbobin yin hadaya da firistoci suka yanka,

      Yana tsaye a gaban itacen ƙona hadayar,

Sai yanuwansa su yi masa ƙawanya, sai ka ce kwandon fure,

      Kamar ma dirarren itacen alul a tsaunin Lebanon.

13 Dukan yayan Haruna cikin darajarsu

      Sai su kewaye shi kamar itatuwan rimaye,

Kowarmensu yana riƙe da hadayar da zai ba Ubangiji,

      A gaban dukan taron jamaar Israilawa.

14 Shi kuwa da ya gama hidima kwatakwata a gaban bagade,

      Da hadayun da aka shirya wa Maɗaukaki,

15 Sai ya mika hannu

      Don ya ɗauki ƙoƙon ruwan inabi na hadaya,

Ya zubar da shi a gindin bagade,

      Sai wuri ya ɓuIlo da ƙanshi mai daɗi saboda Allah Maɗaukaki.

16 A lokacin nan sai yayan Haruna su kwarara busa,

      Firistoci kuma, sai su busa algaitunsu na ƙarfe.

Amon nan yana da ƙarar gaske,

      Wadda take jawo hankalin mutane a gaban Maɗaukaki.

17 Nan take sai dukan jamaa

      Su kwanta rubda ciki,

Suna yi wa Maɗaukaki sujada,

      Mai Tsarki na Israila.

18 Saan nan kuma sai a faso waƙofci,

      Sai taron jamaa su ɗauki sowar yabo mai daɗi,

19 Dukan jamaar ƙasar suna yin waƙan nan da murna,

      Suna roƙon Mai Jinƙai.

Bayan da firist ya gama hadaya kwatakwata,

      Ya kuma miƙa wa Allah abin da ke nasa,

20 Sai ya sauka daga Wuri Mai Tsarki,

      Ya ɗaga hannuwansa a bisa taron Israilawa,

Yana sa musu albarkar Ubangiji,

      Yana girmama sunan Ubangiji.

21 Yana yin haka ke nan,

      Sai jamaa suka sāke yin sujada,

      Domin su karɓi albarkar Maɗaukaki.

Gargaɗi

22 To, yanzu sai ku yabi Allah na dukan halitta,

      Wanda yake aikata alajabai a duniyan nan,

Wanda yake yin tallafin ran mutane tun cikin cikin iyayensu,

      Yana shirya su ma bisa ga nufinsa,

23 Dā ma ya ba ku zuciya kamar alli,

      Ya kuma kwararo salama a tsakaninku.

24 Da ma ya sa alherinsa ya ɗore a kanmu, mu Israilawa,

      Kamar yadda sararin sama yake ɗorewa.

Karin Magana na Lissafi

25 Ni dai raina bai kwanta da alumma biyu ba,

      Ta ukunsu kuwa bai ma cancanta a ce mata alumma ba sam.

26 Biyun su ne waɗanda suke zaune a Seyir da Filistiya,

      Ta ukunsu ce watsattsiyar alumman nan da ke zaune a Shekem.

Karshen Jawabi

27 A wannan littafi na sa

      Koyarwar hikima da karin maganganunta.

Ni, Yesu ɗan Eleazara ɗan Sirak ne, na rubuta su

      Kamar yadda suka ɓulɓullo daga cikin ganewar zuciyata.

28 Albarka ta tabbata ga wanda yake bibiya waɗannan abubuwa,

      Wanda ma yake riƙonsu a zuciya mai hikima ne.

29 Lalle in yana aiki da su, ba abin da zai gagare shi,

      Domin tsoron Ubangiji ne fitilarsa.

51. Waƙar Godiya

1 Zan yi maka godiya, ya Allah na mahaifina,

      Zan yabe ka, ya Allah Mai Cetona!

2 Zan ma yabi sunanka, ya mafakar raina,

      Gama kana taimakona a kan maƙiyana,

Ka raba ni da mutuwa,

      Ka ceci jikina daga zuzzurfan rami,

      Ka fizge ni daga bakin kabari,

3 Ka ƙwace di da jinƙanka mai girma,

      Ka ma keɓe ni daga bakin masu kushewa,

Har ma daga leɓunan masu shaidar zur,

      Daga tarkon masu so su ga na tuntsure,

Daga hannun masu neman raina ma,

      Gama ka cece ni daga hatsarin da ya fi baƙin bunu yawa,

4 Ka ƙwace ni daga harsunan wutar da suka yi mini zobe,

      Ka sure ni daga tsakanin wuta marar ragowa.

5 Ka ƙwace ni don kada kabari ya haɗiye ni,

      Ka kāre ni daga maruɗa maƙaryata,

6 Ka ƙwace ni daga kibiyoyin masu kushe,

      Saad da suke niyyar kashe ni

      A lokacin da aka wawari raina.

7 Na waiga koina, amma ba mataimaki kusa,

      Na nemi mai agajena, amma ba kowa.

8 Amma nan take sai jinƙan Ubangiji ya faɗo mini a rai,

      Na tuna da rahamarsa ta tun dā,

Gama yana ƙwatar waɗanda suka je neman mafaka a wurinsa,

      Yana cetonsu daga hannun kowane mākiri.

9 Don haka sai na ɗaga kukana daga ƙasa, ina neman taimako,

      Na yi ƙūgi a ƙofar kabari,

Sai na ce, Ya Ubangiji, kai ne ubana,

      Kai ne jarumin Mai Cetona,

Kada ka yar da ni lokacin ƙunci,

      Da lokacin wahala, da hatsari.

11 Zan yi ta yabon sunanka ba fasawa,

      Zan ma dinga roƙonka kullayaumin.

Sai ūbangiji ya yi roƙona,

      Ya saurari kokena,

12 Yana cetona daga kowane irin rikici,

      Yana tsame ni ma daga cikin wahala.

Saboda haka nake yi masa yabo da godiya,

      Ina yi wa sunan Ubangiji yabo.

Waka a kan Neman Hikima

13 A cikin ƙuruciyata ba ni da aibi,

      Sai na yi ta neman hikima.

14 Sai ta yi mini farin zuwa kuwa,

      Har ƙarshen raina zan yi ta nemanta.

15 Kamar yadda fure yake zama yayan itace,

      Waɗanda ke faranta zuciya,

Hakanan na yi ta bin hanyar hikima ɗoɗar,

      Domin na saba da ita tun ina yaro.

16 A ɗan lokacin da na yarda da ita.

      Ai, ta ba ni matuƙar ganewa da kwaɓa.

17 Ta haka ne na ƙaru ƙwarai,

      Zan yi wa malamata yabo na farin ciki.

18 Sai na danƙa mata kaina ɗungum,

      Kullum ina ta neman kyanta.

19 Da gawurtaccen bege na nema ta,

      Ba na juya mata baya.

Na kuwa sa raina a kanta,

      Ban ma taɓa ƙosawa da yabonta ba.

20 Saboda ita har tafin ƙafata ma, sai da na tsarkake shi,

      Ai, ba na matsarta da dauɗa.

Karonmu na fari da ita, sai ta kwantaro mini ganewa,

      Saboda haka ba ni da damar juya mata baya.

Lokacin da nake yin koyo a kanta,

      Soyayyarta tana sa tsigar jikina tashi,

      Saboda haka ne na mai da ita dukiyata mai daraja.

22 Ubangiji ya ba ni kaifin baki, ladan neman hikima,

      Saboda haka leɓunana suna ta yin yabo ga Ubangiji.

23 Ku zo guna mana, ku marasa wayo,

      Ku zauna a makarantata.

24 Har zuwa wane lokaci ne za ku hana kanku abincin hikima?

      Har zuwa wane lokaci ne za ku ɗaure wa kishinta mai kisa?

25 Ina yi muku gargaɗi a kanta

      Domin ku sami hikima kyauta.

26 Ku ba bori kai

      Don tunaninku ya yi naam da koyonta.

Gama tana gab da masu nemanta,

      Mai himma ma, ai, yake samunta.

27 Ku duba, ku ma! Kaɗan ne na yi aiki,

      Amma sai na same ta kandam.

2 Ku yi ɗan aiki kima, ku koye ta,

      Za ku sami azurfa da zinariya ta wurinta.

21 Ku sa ranku ya yi farin ciki da jinƙan Allah,

      Kada ku ji kunyar yabonsa.

Ku yi aikinku a kan kari,

      Allah zai yi maka sakamako a lokacin da ya dace.

*      *      *      *      *
*      *      *
*